Novel Document

Rubutaccen Al’amari Complete Novel Document

Rubutaccen Al'amari Complete Novel By Aisha Aliyu Garkuwa

Description/Story:

Rubutaccen Al’amari Complete Novel Document

Written By Aisha Aliyu Garkuwa 

 

Description

*Tayi wani irin firgitaccen zabura cikin tsananin razana ta yunkura da karfi zata tashi tana wani irin gurnani, ganin haka cikin karfin hali da firgici Ammi da ya Usman sukai saurin rik’ota suna mata addu’a, ita kuwa gaba d’aya jikinta rawa yake kar-kar hatta d’an cikin ta sai motsi yake da k’arfi ta zazzaro ido tana waige-waige kamar me neman wani abu, dakyar ya Usman ya kamo kanta da hannu biyu ya kwantar da ita a kan cinyar shi dan yadda take fisge-fisge Ammi bazata iya control enta ba, ita kuwa Ammin sai shafa bayanta takeyi a hankali kwalla cike a idon ta tana furta, “hasbunallahu wa ni’imal wakil”.

Shiko ya Usman yana ruggume da ita a jikin shi gaba d’aya jikin nashi sai kerma yake a karo na forko da yaji rauni da tausayin kanshi da kanshi ga taussyin halin rayuwar da Ummul ke ciki a zahiri yasan kuka rahama ne in dai da k’una a zuci amman shi kuka ya k’aura cewa rayuwarsa tunda Hamma enshi ya bar duniya baya gane halin rayuwar da yake ciki dazaran k’unan rai da k’uncin rayuwar sun tokare mai zuciya sai yayi ta aman jini yana murza kai da k’irji inko dere yayi sai ya tashi ya kwana nafilfili da nemawa d’an uwanshi rahamar Allah a hakan ne Adam ya gano wani abu daya shiga rayuwar Usman da zaran ya kad’aice sai ya rink’a juya kai yana mirgina kan nashi kan kafad’un shi kamar yadda yayi tayi lokacin daya zauna gaban gawar Hamma Umar abin a hankali ya zamewa Usman wani narkarwa ciwo mai zafi a ranshi da rayuwarshi da zaran ya tuno yadda yaga gawar d’an uwanshi sai kawai yayi ta juya kai jiki na rawa hakan yasa yanzu da zaran hankalin shi ya tashi ko ranshi ya baci sai ya rink’a wannan abun, so yanzuma da Ummul take ta fisge-fisge da gurnani yana ruggume da ita duk da ba wanda yake gane me take fad’a hakan yasa sai ya rink’a juya kai yana murza k’afafunshi dan zafin da zuciyarshi ke mishi, ita kuwa Ummul sai gurnanin takeyi Ammi kuwa duk sai zuciyarta ta d’anyace ta tasasu a gaba ta kife kanta tana kuka mai cike da dafi a zuciya.

Ya Adam ne ya k’araso cikin d’akin da sauri ya d’ago Ya Usman wanda ya kife kai a kan bakin gado yana jan numfashi da a wahalce,

Abba da yanzu ya iso da su Nenne da Hajjajo da su ya Sadik sai Aliyu suka shigo saboda jiyo k’arar da Ummul tayine, cikin karfin hali Abba yace,

“Adam, d’aukemin Usman daga nan”.

Usman najin haka cikin rawar murya da juya kai ya fara magana,

“Abba ku kyaleni dan Allah kubarni inkula da amanar d’an uwana ku barni in kula da amanar da Hamma na ya barmin”.

sai kuma yasa hannu biyu ya rik’e kanshi yana juya kan a wahale yana k’ollah murya na rawa yace,

“Nanne ina zankai Ummul ? mezan mata ta sami sauki? Ammi ina soro kar d’an d’an uwana ya cutu ya zanyi na kare mutunci da lafiyar Iyalan Hamma na?”.

sai kuma ya kife kai ya saki wani irin kuka mai k’arya zuciyar mai sauraro kuka yake har numfashin sa na cizga duk jikin shi sai b’ari yakeyi tamkar mazari,

Aliyu ne ya dafa kafad’ar shi cikin matsanancin kuka yace, “ya Usman tashi muje muyi nafila muroka mata sauki,

Hamma Umar yace min duk damuwa tanada magani a gun Allah, kutashi muyi musu addu’a zata samu sauk’i kullum Hamma Umar nace min Aliyu duk tsanani yana tare da sauki,

nasha in sameshi yana kuka in nace mishi Hamma Umar me yasa ka kuka? sai yace min Aliyu Usman baida lfy ina kukane wa ubangijina ina nemawa Usman lafiya a gun mai bada lafiyar,

dan haka muma muje mu nemawa Ummul lafiya a gun mahaliccinmu”.

Yana kaiwa nan yaja hannun ya Usman suka fice suka nufi part insu al’wala sukayi sannan su fara nafilfili tare da karatun qura’an,

haka kowa na gidan yai alwala suka dukufa nemawa Ummul sauki gurin Allah,

Ammi kuwa na rungume da Ummul tana shafa bayanta a hankali tana tofa mata addu’o ‘i har tasami bacci wanda takan razana duk mintina kad’an.

 

Haka rayuwa tacigaba da tafiya cikin rashin wal-wala da kuncin zuciya yayinda kowanne ke buya yayi kuka san ranshi daga Abba, Hajjajo, Nanne, Adam, Sadiq, Aliyu, wanda b’angaren Ya Usman kuwa abun sai rahamar Allah kullum yana cikin aman jini ba k’ak’k’autawa kuma yanzu ya samu sauk’i yana iya kuka hakan yasa da zaran ya fara kuka kuma sai tari sai aman,

Ammi kuwa tamik’a lamuran ga Allah tadage wajen kula da Ummul wadda tazamo tamkar mutum mutumi duk da ansami cigaba a yanayin ta takan d’an sha tea duk da sai Ammi tasha rarrashi wonka kuwa sai Usman ya zauna gabanta yayi ta lallashi wani lokacin ya kife kai yayi ta kuka kafin ta yarda Nenne ko Ammi su mata wonka abu kamar wasa a zahiri Ummul ta zama tamkar zaucecciya komai sai an sata kuma tun randa Hamma Umar ya rasu har yau Ummul Allah bai bata bakin manana ba kullum kuma in dere yayi toh tashin hankali ya tashi kab zuriyar tasu basu da konciyar hankali da zaran an shiga za’a konta sai Ummul tayi ta firgice-firgice tana razana tana son guduwa sai ta rink’a b’uya ko tana k’ok’arin shiga duk inda taga luggu,

Usman kuwa haka zai zauna yayi ta kuka yana ga ya kasa tallafawa iyalan d’an uwan nashi a haka ciwon zuciyarshi ya tashi.

Yau Jumma’a da yamma,

ya Usman ne zaune gefan Nanne ya Adam yana tsaye Aliyu kuwa yana durk’ushe gaban Ummul sai kuka yakeyi duk sun zubawa Ammi da take bawa Ummul ruwan zam-zam da aka tofawa addu’oi wanda yanzu shine ruwan shanta,

domin samun sauki da sassaucin kuncin zuciya,

d’an ture hannun Ammi tayi sai kuma ta rink’a binsu da kallo d’aya bayan d’aya kai ta sunkuyar tana kallon k’aton cikin ta da d’an yaketa wintsil-wuntsul a hankali ta mik’awa Aliyu dake zaune yasata gaba yana kuka,

hannu alamar ya d’agata da sauri fuskarshi cike da mamaki yace,

“In d’agaki?”.

dakai tamai alamar eh, aiko cikin jin dadi yamike yasa hannu ya d’agota ta mike sannan yasa hannu yana gyara mata d’aurin zaninta yana mai zubda k’ollah,

Ya Usman kuwa cikin saurin ya je bayanta ganin tana tangad’i kamar zata fad’i,

cikin k’arfin hali tafara takawa wanda hakan yasa dukkansu dake d’akin jin dadi kasan cewar tun dawowarsu basuga hakan daga garetaba,

a hankali suke tafiya Aliyu na rik’e da hannunta har suka fita daga d’akin,

da hannu taiwa Aliyu nuni da hanyar inda Hamma Umar ke zama dan duba marasa lafiya dake zuwa gida,

haka sukaita tafiya sanayi a hankali har suka isa gurin,

d’an juyowa tayi ta yafito ya Sadiq da suketa binsu a baya tunda suka fito ta nunamai carpet dake jingine agun da hannun ta,

shiko jiki na rawa yace, “in shimfid’a?”.

Kai ta kad’a, aiko ya shimfida nan da nan, kwace hannunta tayi dagana Aliyu ta juya kamar tana neman wani abu, Ya Usman dake tsaye a bayanta kamar body guard’ yace, “me kike so?”.

itako Ummul Ammi ta nuna da hannu takuma nuna mata carpet da aka shimfid’a,

cikin sanyin jiki Ammi ta zauna kan carpet d’in, Ummul tasa hannu ta rik’o hannun Aliyu shiko yasa daya hannun yakuma rik’ota ya taimaka mata ta zauna sannan ta matsa kad’an ta jingina bayanta da jikin Ammi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta lumshe ido sannan ta kalli Ya Usman daya zuba mata ido tamai nuni da ya zauna.

zama yayi sannan taiwa Ya sadiq nuni shima ya zauna, ta kalli Aliyu tamai alama da hannunta daya yazo yazauna kusa da ita haka taiwa kowa nuni suka zauna harda Hajjajo,

Ya Adam yasa tafin hannunsa ya goge hawayansa a dai dai lokacin da Ummul taimai nuni daya zauna shima,

Haka suka zauna agun itako Ummul tanata kallon su da dai-dai kamar bata tab’a ganin suba saida aka kira magrib sannan suka koma cikin gida.

 

 

Kwanci tashi cikin Ummul ya isa haihuwa dan haka aka shirya komawa kasar egypt da taimakon adalin gwamnan gwamnoni, gwamna daya d’au rayuwar talakawan jahar shi da muhimmanci gwamnan jahar yobe.

Anyi tafiyar ne da Ammi, Abba da ya Usman sabida yanada buk’atar ganin likita akan yawan aman jinin da yake kowane lokaci, isar su da kwanaki uku

aka gama bincike kan zuciyar Usman inda cikin ikon Allah doctor ya shaida musu za’a cire na’urar dake tallafa zuciyar Usman domin sanadin wani tsoro da tsinkewar zuciya daya samu yasa zuciyar ta harba cikin tsoron to daga nan yanzu ita da kanta take aikin harba jinin kuma in anbar na’urar zata iya maida zuciyar ta cushe dan haka cirewa za’ayi,

abin ba k’aramin Al’ajabi ya bawa Ammi da Abba da Adam ba haka Abba da Ammi suka sa’a hannun,

ita kuwa Ummul bayan magun guna da allurai da likitoci keta bata ne akai shirin shiga yimata aiki saboda babu halin haihuwa dakanta sakamakon sanyin da zuciyar ta tayi dan bugun zuciyarta tayi k’asa sosai haka yasa rana d’aya za’ayiwa Usman da Ummul aiki

Abba kam da Ammi da Adam sai Addu’oi sukeyi Abba ya kira Daddy da Uncle dinsu Usman da sukaje saudi ya shaida musu su tayasu da Addu’a.

K’arfe 8:00 dai-dai babban likitan da zai jagoranci aikin yakira Abba da Adam a office din shi,

bayan yad’anyi rubuce rubucen shi ya d’ago kanshi ya sauke farin glass dinshi kasan hancin shi yace,

“Alh Hassan, zamu shiga aiki da yaranka muna kuma bukatar addu’ar ku kasancewar ita yarinyar aiki zamu me cike da hatsari domin kuwa bamuda tabbacin zuciyarta zata tsaya yanda muke bukata har mu gama aikin”.

Abba yai ajiyar zuciya yace,

“to Allah ya bada sa’a”. Likitan ya mik’o musu form da zasu saka hannu dan yin aikin, Abba yasa hannu ya janyo takardar ya juya ya kalli Adam da ya sunkuyar da kai k’asa ya dafa kafad’ar shi yace,

“Adamu kadaure kasa hannu aima k’anwarka aiki ni zansa hannu akan aikin Usman”.

a razane ya Adam ya d’ago yana kallon Abba da takardar,

a hankali Abba yasake d’agamai kai da lumshe ido cikin sanyi Adam yasa hannu ya janyo takardar yad’auki biron sannan ya d’ago kai ya kalli likitan daya zubamai ido yana kallonshi, cikin tausayawa likitan yace, “Insha Allah zamuyi aiki cikin nasara”.

shi kam Adam ido cike da k’ollah yasa hannu tsoro tab zuciyarshi yana jin tausayin Usman a ranshi yana jin tsoron kar wani abu ya faru da su kuma a zuriyar tasu,

hannu na rawa Adam yasa hannu a takardar yana zubar da kwallah, likitan yasa hannu yaja takardar yace, “good, be prayerful”.

da haka yatashi yafita sukabi bayanshi jiki ba kwari, karfe 9:00 dai-dai aka shiga da Ummul d’akin tiyata ya Usman kuwa aka shiga dashi d’akin dashen zuciya,

akabar Abba da Ammi ,

tsaye suna karanto kowacce irin addu a da suka iya zuk’atan su cike da zulumi.

Har k’arfe 11:30 suna ta zirga-zirga bawanda yake magana kowanne da irin tuna ninda yake a ranshi, bude k’ofar dakin da akema Ummul aiki ya tattaro hankalinsu, ya Adam ya dafe kirjin shi da hannu yabi bayan likitan daya wucesu yanufi office d’inshi,

a lokacin kuma aka fito da ya Usman shi an gama aikin nashi,

Adam kuwa a office d’in doctor saida ya zauna a kujerar shi sannan yad’anyi murmushi yace,

“congratulation”. Allah yayi ikon shi da taimakon y’an uwana likitoci anciro baby boy,

yaro yana cikin koshin lafiya sannan insha Allah itama zata farka babu wata matsala”.

cikin jin sauk’in razanar Adam ya dago rinannun idanunshi dasukai jawur yace,

“Alhamdullah Masha Allah”.

Sanna ya mike ya fito ya nufi d’akin da yaga Abban na shiga wanda ya haggo ana shigar da Usman,

suna shiga kuma sai ga ita Ummul an shigo da ita haka aka kontar dasu d’aki d’aya gadon Usman na gefen na Ummul Ammi kuwa waje ta fita ruggume da yaron tana kukan abubuwa da dama kukan tuno d’anta kukan fargabar halin da Ummul da Usman ke ciki kukan tausayin yaro maraya tun yana ciki an kashe mai uba haka tayita kuka gwanin ban tausayi.

Bayan awanni shida Ummul na kwance kan gadon hutu na asibitin, shiko Usman yana kwance kan d’ayan gadon dake kallon nata yasanya jinjirin gaba yanata kallo dan yariga ta farfad’owa,

yayinda Abba ke zaune a kan kujera a gaban gadon Usman kusa dashi kuwa Dr Bashir ne suna kallon yanda Ummul kedan motsa k’afarta a hankali,

Ammi ko tana zaune bakin gadon da ummul ke kwance tana rik’e da hannun ta idon ta ya na kanta,

yun kurin bude idonta tafarayi a hankali tanajin yamata nauyi,

da hannu Ammi taiwa Dr Bashir nuni aiko tare suka taso sukayo bakin gadon,

Tana bud’e idonta da kyar ta d’aga hannun ta da kyar ta shafi cikinta dan jin yayi mata wayam aiko saita d’an kara zaro idonta tabud’e baki da kyar murya nara voice a disashe a hankali tace,

“In in inaaaa cikin?”. Hamdala suka rink’a jerawa cikin tsananin happy dan tunda Hamma Umar ya rasu sai yau Ummul ta iya magana,

ya Usman kuwa juya kanshi yayi a hankali wasu irin hawaye masu zafi suna bin fuskarsa,

Ammi ce ta mik’e da sauri ta d’auko babyn da yaketa bacci a gaba Usman shiko Usman sai kallon yaron yake cikin tsananin k’auna yana jin son yaro fiye da kowa a duniyar nan,

a hankali Ammi tace, “gashi nan Ummul, ga d’anki wanda Allah ya azurtaki dashi keda Faruoq na amman ke Allah ya nunawa shi shi kam Umar ya rasu da begen wannan rana ya rasu da kumfar rashin ganin d’anshi Ummul ga d’anki maraya zai tashi maraya kamar yadda iyayenshi suka tashi marayu”.

Daga kwance tasa hannu ta d’ora akan yaron ta kuramai idanu tanajin k’aunar shi na ratsa zuciyar ta da dukkan jikinta sai kuma tayi kurui tana kallon Usman dake konce yana hawaye cikin sanyi yace,

“Ammi yaron nan bazaiyi maraiciba Insha Allah bazai yi kukan rashin mahaifiba Ammi da izinin Allah indai ina raye yaronan bazai zubda k’ollah”.

sai kuma ya rink’a kuka yana rik’e da hannun Abba,

shima Abban kuka yake Ammi kuwa zuwa yanzu hawayenta sun fara k’agewa,

Adam ma gaba d’aya ya zama mai raguwar zuciya abu kad’an sai Kuka amman shi tausayi Usman ke addabar rayuwarshi,

haka Dr Bashir kuwa da sauran doctors din sukayi ta kula da Usman da Ummul da jaririnta k’ato fari tas kekyawa, sukaita kula dasu cikin ikon Allah kuwa Ummul da Usman duk Alhamdulillah jiki yayi kyau Ummul kuwa tun randa tayi magana bata kuma yiba.

Doctors sun bada tabbacin zuciyar Usman zata iya aikin da ake but’ata amman a guji b’acin ransa sosai sukayi kashedin gudun b’acin ran shi,

a gefen Ummul Kuwa sunce kar a damu da rashin maganarta sunce a koda yaushe maganarta zata iya dawowa amman kuma a duk randa suka tsinci Ummul na kuka toh karsuyi yunk’urin hanata a barta domin a cewarsu yin kukan zai iya maida tunaninta dai-dai har ta fara magana kuma sanyin da zuciyarta tayi harda rashin kukan.

Bayan kwanaki shida dayin aikin aka sallamesu da sharadin kulawa da bawa Ummul da Usman magunguna don cigaba da samarwa zuciyoyin su lafiya, da haka suka tattaro suka dungumo sai gida Nigeria.

Randa suka dawo gaba d’aya zuriyar Shuwa sun cika da farin ciki domin samun lafiyar Usman da Ummul ga jariri da ya zamo magajin Hamma Umar kowa zaizo da Happy amman abin fargaba har yanzu Ummul bata mgn,

Nenne takan buya tayi ta kuka,

Ummul kuwa in banda bawa yaro nono da da tasashi a gaba tayi ta kallo ba abinda takeyi da kanta sai an tasa a gaba wani lokacin sai ta wuni ta kwana bataci komaiba inko yaronta na kuka sai tai ta rawan jiki ta gigice,

in tak’i cin abinci da wonka Usman yakan zauna a gabanta yayi ta magiya har ya fara zubda k’ollah to da zaran taga yana kuka sai ta zauna ta fara cin abincin.

A haka rayuwa tayi ta juyawa har sukayi kwana 9 da dawowa, yau asabar da safe bayan sun gama aiyu kansu,

Abba da kanshi ya shiga d’akin da Ammin ke zaune da Ummul a nan ya samu Usman da Nenne da Adam Ummul ruggume da yaron, bayan sun gaisa cikin kula Abba ya kalli Usman yace,

“ni kam Usman me sunan yaron ne har yau baka gaya min

ba? “.

Cikin mamaki Usman yace,

“Abba baka yiwa yoron huduba bane dama ni yamin ka gaya mai sunanshi ai”.

a hankali Abba yace,

“A a Usman ya za’ayi haka yaro yau kwana 14 kuma ashe ba’a mai huduba ba”.

Ammi ce ta kallesu a hankali tace,

“mahaifiyarshi ta mishi huduba tun randa yayi kwana uku amman har yau bata gaya min sunan shiba”.

usman d’in ya zuba mata ido cikin sanyi yace,

“Ummul kiyi hak’uri mana ki ruggumi k’addararki ki rink’ayi mana magana yanzu tsakanin ki da Hamma kiyi mishi gatan Addu’a ki bawa d’anshi tarbiya to amman a hakan zakiyi wad’an nan abubuwan”?.

shiru tayi tana jinshi karo na forko da ida nunta suka ciwo da hawaye tab,

Abba ne ya kalleta a raunane yace,

“Me sunan yaron?”.

murya can k’asa cikin rauni da tsananin k’una a zuciya tace,

“Washe garin za’a kashe Hamma na yace min in namiji na haifa ya bani dama nasa sunan wanda nafiso a duniya wanda duk duniya bani da kamarshi”.

sai kuma ta saki wani irin kuka ta ruggumo yaron tana kallon shi,

Usman ma kukan ya fara a hankali yace,

“Ummul me sunan yaron?”.

cikin tsananin kuka tazo ta durk’usa gaban Abba murya a disashe tace,

“Abba ina sonshi Abba ina sonshi ina sonshi Abba duk duniya bani da kamarshi Abba ina son Hamma Umar Abba ina zan ganshi Abba sun kashe min Hamma na a gabana Abba ina son Hamma Umar”.

sai kuma ta kife kanta a cinyar mahaifin nata cikin rauni da tausayawa rayuwarta,

shiko Abba a hankali yace,

“Me sunan yaron kika saka? “.

cikin tsananin kuka tace,

“Sunan shi *Umar Faruoq*”.

tana fad’in haka Usman ya……..

Rubutaccen Al'amari Complete Novel Document Txt

File Name Rubutaccen Al’amari… Hausa Novel Doc.
Title Rubutaccen Al’amari Complete Document 
Author   Aisha Aliyu Garkuwa
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    07/12/2024
File Size    700KB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No     NIL
Download Rubutaccen Al’amari Complete Novel Document By Aisha Aliyu Garkuwa

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button