Halysaah Page 209 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 209…Bayan Magrib Ajay suka isa hotel din da suka yi lodging a cikin garin Benue, Jay dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba ganin ya biyo sa hotel room dinsa, tare suka yi sallah a dakin sannan Ajay ya fita zuwa ya siyo masu abinci, Ajay na fita Jay ya dau wayarsa dake ringing ya ga Khaleesat ce ke kiran sa, picking call din yayi ya kai kunne, daga daya bangaren tace “Ya Jawwad i want to ask you for something pls” Jay dake sauraronta yace “Ina jin ki” Tace “Ina son zan siya wani abu ne, pls i need 100k cash, ban taho da Atm card dina ba, kuma wayar da nake transfer na bar sa Bauchi sanda za mu yi tafiya” Jay yace “Me za ki siya?” Kame kame ta fara yi, ya bari ta gama kame kamen ta sannan yace “Halysaah” Ta ɓata fuska tace “Na’am” Yace “In dai kika saka kafa kika bar hotel din nan babu ruwana da ke on a serious note, so duk abinda na gaya maki sun shiga ta right ear din ki sun fita ta left ko?” Khaleesat dai ta hade rai bata ce komai ba, yace “Yanda muka taho tare haka za mu koma tare….” Ta dake don kar tayi kukan dake neman kubuce mata tace “To ni ai ban ce tafiya zan yi ba, kawai wani abu nace maka zan siya fa” Yace “Abinda za ki siya ba shi da suna?” Da kyar tace “Shikenan, i will buy it tomorrow” Yace “Better” Katse wayar yayi, Khaleesat da taji wani abu ya tokare mata a zuciya ta kife kanta ta fara kuka a hankali, all this while sai yanxu tayi kuka, sosai take jin zuciyarta na mata zafi, a haka Ajay ya shigo dakin, dama tana jin ya bude kofa ta dena kukan da take ta goge hawayenta da sauri tayi kwanciyarta, ya karaso cikin dakin ya ajiye ledan takeaway din abincin hannunsa sannan ya kalleta yace “Ga abinci” Bata kalli inda yake ba balle ta tanka sa, ya juya ya fita daga dakin, dakin Jay ya koma, Jay ya bi sa da ido har ya gama cire kayan jikinsa, ya dau sabulun Jay ya shiga banɗaki, bayan Ajay ya fito wanka ya shirya zai kwanta Jay yace “I don’t understand?” Ajay ya kallesa yace “You don’t understand what?” Jay ya gyara zama yace “Tun da muka tafi America har zuwa yanxu da muka dawo ni da kai muna kwana daki daya ne dama?” Ajay yace “So?” Jay yace “Wallahi baza ka kwanta min a nan ba, tafi inda ka kwana jiya” Ajay yayi dariyar da bai yi niyya ba yayi kwanciyarsa, Jay ya hade rai yace “Billah baza ka kwanta a nan ba da gaske” Ajay yace “Ai kuma sai kayi, naga dai ni na biya hotel rooms din, so duk inda nake son kwanciya nan zan kwanta” Jay yace “Da katin wa ka biya hotel room din” Ajay yayi dariya don ya mance da katin Jay yayi payment a hotel din, shi Atm card dinsa ko tafiya da shi America bai yi ba, Jay yace “Seriously ka tashi ka tafi wajen matar ka” Ajay yace “I am sleeping here, so kar ka bata bakin ka” Jay bai sake ce masa komai ba, after a while ya bude abincin da Ajay ya kawo masa yace “Kai ina abincin naka?” Ajay yace “I am full” Jay yace “Ka ci shinkafa da kifi why won’t you be full, Wai Ajay where is ur OCD?” Ajay yayi murmushi a hankali yace “I got the right therapy to it, but ai har yanxu ba ko ina nake cin abinci ba, these people where part of me for 2 years….” Jay bai ce masa komai ba, can yace “Ai bana shan drink din nan da ka siyo min” Ajay yace “Sai ka bar shi” Mikewa Jay yayi yace “Mu je in siyo drink da gasasshen kaza” Ajay yace “I don’t think I have the strength to go out now” Jay yace “Dalla Malam ka tashi mu je” Kamar Ajay bazai tashi ba daga karshe dai ya sauka daga kan gadon, zai dau Atm card Jay ya rigasa dauka ya nufi kofa ya fita Ajay na biye da shi a baya, tsaye Jay yayi a corridor din dakunan hotel din with the room key a hannunsa yana jiran fitowar Ajay, bayan Ajay ya fito Jay yace “Let me get my phone….” Komawa cikin dakin yayi ya kulle kofar ya sa makulli yace “Good night, ai jiya ba dakin nan ka kwana ba” Ajay yayi murmushi ya jingina da bango yana shafa gashin kansa, a lokacin da ace da Atm card a hannunsa wani dakin kawai zai biya ya shiga ya kwanta, ya fi minti biyar jingine da bango bai dai ce ma Jay komai ba, can ya gyada kai kawai ya nufi dakin da Khaleesat take, bude kofar yayi ya shiga ciki, tana kwance yanda ya bar ta, tana jin shigowarsu ta dena kukan da take kuma bata juya ba, ya karasa yayi kwanciyarsa other side of the bed, tana ganin haka ta dau pillow ta sauka ƙasan tiles ta kwanta fuskarta a murtuke, shi dai kallonta kawai yake, kamar bazai ce komai ba, kawai dai yace “Koma kan gadon ki ni zan kwanta a kasa” Kamar jira take ta mike a fusace tace “Kar ka sake min magana” Yace “Ohk….” Ta dake kar ta fashe da kukan da ya zo mata tace “Dama saboda ka walakanta ni ka taho da ni garin nan ashe….” kamar Ajay bazai tanka ta ba, after some seconds yace “Idan baki gode ma mutanen nan ba baza ki je kina frowning masu fuska ba Jeeddah, why are you taking every little thing too personal? Mutanen nan sun yi deserving kiyi masu abinda kika yi?” A fusace tace “Na dauka personal din, ok in gode masu rungumar ka da aka yi kake nufi ko? to ai ni ban ma yi zaton zaka bar garin yau ba, na zata can zaka kwana kana lallashin yarinyar tunda rayuwarta tsayawa yayi cak bayan ka bar garin” Calmly Ajay yace “Ai da na sani na kwana can din, tunda shekara biyu nayi ina kwana gidan so ba sabon abu bane, kuma ko na kwana ina lallashin yarinyar she deserves it….” Mikewa Khaleesat tayi ta dau hijab dinta ta fice daga dakin, direct dakin da Jay yake ta nufa ta kwankwasa, duk zaton Jay Ajay ne ke knocking yaki tankawa, har sai da tace “Ya Jawwad” Jay ya mike ya nufi kofar dakin ya bude yana kallonta, kawai ta bi gefensa ta shige cikin dakin ta fashe da kuka, ya bi ta da kallon mamaki yace “Me ya faru?” Taki ce masa komai ta fada kan gadon tana rera kuka kamar an aikota, Jay ya fita daga dakin ya nufi other room din, bude kofar dakin yayi yana kallon Ajay yace “What did you say to her?” Ajay yaki tankasa, har sai da Jay yace “Junaid….” Ajay ya kallesa yace “Abinda ta ce maka shi nace mata, pls first thing tomorrow morning kawai ka dauketa ku yi tafiyar ku gida, idan na gama abinda nake zan biyo ku” Kallonsa Jay ya dinga yi yace “You must be joking, no matter her tantrums ai sai kayi enduring since you know her condition” Ajay yace “Enduring din ne yasa har yau ban taɓa complain ba ai, ba wani condition, after all she is not the first woman to get pregnant, she just derive joy in creating issues out of nothing” Yana fadin haka ya mike ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa alamar baya ma son maganar, Jay ya kunna wutan yace “Ina ma magana zaka kashe wuta” Ajay ya lumshe idonsa bai sake tanka Jay ba, har sai da Jay ya gaji ya fita daga dakin, lallashin duniya sai da Jay yayi ma Khaleesat amma kamar kara tunzura ta yake, daga karshe ya koma can dakin ya tarar Ajay har yayi bacci abun sa, kwanciya yayi shi ma a dakin ya bar mata can dakin. Tunda Khaleesat ta kyallara ido ta ga Atm card din Jay a daki take ta Allah Allah karfe biyar na asuba yayi, ko baccin kirki bata yi ba wannan daren, karfe biyar nayi ta shiga bandaki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, ta shirya ta dau Atm card din da cash din dubu biyar da ta gani ta fice daga dakin, tsaf tana rike da pin din Jay a kanta don duk abinda suka siya a hanya sanda za su taho Benue da Atm card din suke using, ta tare ɗan sahu tace ya kai ta tashan da zata hau mota zuwa Abuja, a motor park ta shimfida ɗankwalinta tayi sallah, ta ciri kudi ta biya kudin mota me zuwa Abuja, bayan ɗan lokaci suka dau hanya. Karfe bakwai na safe Jay ya ga debit din kudin da Khaleesat ta cire a wayarsa, mamaki ne ya cikasa, ya juya ya kalli Ajay da ya koma bacci bayan sallan asuba, ya mike da sauri ya fita daga dakin, knocking yayi dakin da take amma ya ji shiru, hakan yasa ya bude kofar dakin yaga babu ita babu Atm card dinsa da cash din da ke hade da katin kudin, ya fi minti uku tsaye a dakin Khaleesat ta gama cikasa da mamaki, it was funny and at the same time not funny don ta tafi da Atm card ta bar su stranded a garin Benue, wato su karata, numberta yayi dialing yaji switch off, ya juya ya fita daga dakin, yana shiga daya dakin ya kai ma Ajay duka yace “Malam tashi zaka yi, baka ga ta bacci ba” Ajay ya bude ido yana kallonsa, Jay yace “Matar ka tayi tafiyarta da Atm card” Ajay ya dinga kallon Jay, can ya mike zaune yace “Sai kaje banki kayi using cheque ka cire kudi” Jay yayi masa wani kallo yace “Ranan Saturday din ne zan je bank? Kuma ta kama hanya ita ba isasshen lafiya ba amma kai maganar aje bank a cire kudi kake” Ajay yace “Ai daga jiya ta samu sauki, da za mu dawo da yamma kaga ta kara langwabewa?” Jay yace “On a serious note this is way too early in ur marriage, kai baka san yanda zaka bi da matar ka ba? What if cikin jikinta ya samu matsala, public transport fa ta bi” Ajay yace “Wait Jay…. Tell me what my fault is in here? So tayi nima in daure fuska yanda tayi masu a garin? Did she know how dear those souls are to me?” Jay dai kallonsa kawai yake…. Duk da yanda Khaleesat ta wahala a 6 hours journey din da suka yi from Benue to Abuja haka nan ta kara hawa wata mota zuwa Kano daga Abujan, ai ko ta ji jiki ba kadan ba, har ta mance rabon ta jigata haka, ta dinga amai a hanya gashi babu komai cikinta, wannan yasa duk ta fita hayyacinta zazzaɓi ya rufeta, mutanen cikin motar na ta tausayinta suna bata attention, a haka suka isa Kano bayan isha’i mutane biyu daga cikin motar suka samar mata adaidaita sahu har zuwa tudun Yola, tun daga park aka biya mai adaidaita sahun kudinsa, wannan yasa yana parking a inda Khaleesat ta nuna masa a kofar gidansu tayi using strength dinta na karshe ta shiga cikin gida ko gaida Mai gadin gidan dake zaune bakin gate da shi da Ɗan mijin Hajiya Zaliha bata yi ba, Mama Zubaida na zaune barandan Chalet dinta tana waya da er uwarta tayi saurin mikewa ganin mutum ya fadi a tsakar gida rigijib, da sauri ta sauka kasa tace “Subhanallahi, Khaleesat, innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, me ya same ki?” Dagota tayi ganin kamar suma tayi yasa ta fara kwala ma mutanen gidan kira su fito su kawo agaji, wannan yasa Mai gadi da Haiydar suka shigo compound din da sauri, Nenne ce ta fara fitowa a kidime ta saki salati ganin Khaleesat a hannun Mama Zubaida bata motsi, jiki na rawa ta isa kusa da su tace “Mun shiga uku mun lalace, me ya sami Junaidun kuma, wani iftila’in ya kara samun sa, ku kira min Parida jama’a, wayyo Allah na” Umma da Mama Shatu duk suka fito tsakar gidan da sauri, Umma was shock ganin Khaleesat a haka, ta ma kasa karasawa kusa da ita, Haiydar ya sa Mai gadi ya bude masa gate ya shigo da motarsa dake kofar gida don a sa ta a motar su tafi asibiti, su Mama Shatu ne suka dagata suka sakata a bayan motar, tuni Nenne ta shige motar babu ko takalmi balle gyale, Haiydar ya sa Mama Shatu ta shiga gaban motar sannan suka dau hanyar asibiti…. Sai wajen karfe sha daya da rabi na dare Khaleesat ta bude idonta da suka yi mata nauyi, Nenne dake zaune sai zuba uban gyangyadi take a gefenta ta bude ido da sauri jin motsin ta, da sauri Nenne ta mike ta fita ta kira likita don dama sun ce tana farkawa ayi masu magana, Khaleesat ta cire drip din hannunta cause she was pressed, da kyar ta sauka daga saman gadon ta shiga bandakin dake ward din, ko da ta fito ta tarar da likitan da Nenne a ward din, Likitan na kallonta yace “Sannu Hajiya, how are you feeling now?” Khaleesat ta sauke idonta tana dafa bango ta isa har kusa da gadon don jiri take gani, likitan dake kallonta yace “Tell me how you are feeling, ya jikin?” Khaleesat ta dafe gadon ward din ta duka a hankali tace “I saw spotting when i went to ease my self” Likitan ya ɗan bude ido yace “Really? Light or heavy spotting?” Cikin sanyin murya tace “Light” Likitan yace “Do you know the gestational age of the pregnancy?” Ta girgiza masa kai, yace “Baki yi scanning ba har yanxu kenan?” Ta gyada kai, yace “When last did you see ur period?” Khaleesat ta sauke idonta tace “Almost 6 to 7 weeks now” Nenne dake gwale ido tana bin ko wannen su da kallo tace “Wai me ke faruwa ne? Sikanin din me za ayi? Ba na ce maka tana da juna biyu ba ku san irin alluran da za ku mata? Na fa gaya maka tun kan ku taɓa min jikata” Likitan yace “Baaba tunda kika ce tana da juna biyu ai mu mun san aikin mu….” Ya kalli Khaleesat yace “Ki kwanta Hajiya, ina zuwa” Juyawa yayi ya fita daga ward din, Nenne ta kalli Khaleesat tace “Menene yake faruwa ake maganar gwaji” Khaleesat ta hau saman gadon a hankali tace “Jini na gani da naje fitsari” Nenne ta dafe kirji tace “Mun shiga uku mun lalace, jinin uban me, jinin al’ada ko me?” Khaleesat taki tanka Nenne ta kwanta kan gadon, Nenne ta kara zaro ido tace “Kaddai cikin ne ya zube Khaleesat?” Hawaye ya cika idon Khaleesat taki cewa komai kawai ta fashe da kuka sosai, Sai ga likitan ya shigo da Nurses biyu, likitan yace “Kin taɓa ɓari ne?” Nenne da duk ta rude tace “Tayi ɓari shekara biyu da suka wuce, likita ka gaya min lalacewa cikin yayi ne?” Bata jira me likitan zai ce ba ta figi wayarta dake ruri ta daga ta kai kunne hankali tashe, Jay yayi mata sallama daga daya bangaren yace “Kaka ya sunan asibitin, mun shigo Kano yanxu” Nenne ta rushe da matsanancin kuka tace “Wallahi yanxun nan likitan ke gaya mana wai tayi ɓari Jawwal, cikin dai ya zube” Daga Nurses din har likitan sai da suka juya da sauri suna kallon Nenne baki sake, Sai da Jay yaji wani dum a kansa jin abinda Nenne tace, tana fadin haka kuma ta katse wayar tana rusa kuka, Ajay dake kallon Jay ganin yanda yayi stiff a gaban motar ko motsi bai yi, lokaci daya yaji gabansa ya wani fadi, bai san sanda ya fixgosa ba zuciyarsa na bugawa yace “Me ya faru Jawwad?”


