Novel Document

Matar Damisa Book 2 Complete

Matar Damisa Book 2 Complete Novel By Asmeeta

Description/Story:

Matar Damisa Book 2 Complete

By Asma’u Muhammad Auwal

 

Description

Ayusher ashe ke mahaukaciya ce bansani ba, ban taɓa sanin ke wawuya bace sai yau, ina kika kai iliminki da kuma hankalinki? shin kinsan abunda kika aikata kuwa…”

Ayush tana kuka tace “Uma ki gafarce ni amma bazan iya Auran Yaya Junaid a haka ba…” “yi mun shuru shashasha kawai..” Uma ce ta darara mata tsawa tare da faɗin “ki sani wannan shine dama ɗaya da kike dashi idan kuwa ya suɓuce miki kin rasa har abada, inaso ki sani Junaid ba mutumin banza bane sannan ba manemin mata bane, yana sonki ne yasa har ya fito bainar jama’a ya sanar wa kowa amma ke dakika tashi sai kika watsa masa ƙasa a ido, duk abunda zakiyi ki rinƙa hango gaba domin baya ya rigada ya wuce, burina bai wuce ki Auri Junaid ba saboda zaifi samun nutsuwa a wajenki kuma haka mahaifiyarsa a duniya bata da burin daya wuce Junaid ya Aure ki,

inaso ki sani cewa wannan baikon da aka haɗa mahaifiyar Junaid ce ta yanke wannan hukunci, kuma tin ba yau ba take son haɗa soyayyarku, Ayush ki mata adalci mana ko dan ita ki Auri Junaid mana, tana matuƙar ƙaunarki duk da har yanzu basu san asalin ki ba…”

miƙe wa Ayush tayi tana kuka tace “yanzu Uma kin goyi bayan na Auri Yaya Junaid?..”

ajiyar zuciya Uma tayi sannan tace “ba shawara nake baki ba, umarni nake baki, idan kuwa kika tsallake ki sani babu ni babu ke kuma bazaki sake ganina ba har abada….” Ayush kuka ne ya kuɓuce mata sosai jin abunda Umanta tace, suna cikin wannan halin suka jiyo takun takalmi an nufo ɗakin,

da sauri Uma ta shige cikin toilet, ita kuma Ayush zama tayi a bakin gado ga hawaye caɓa-caɓa a fuska,

turo ƙofar ɗakin akayi,

rai a ɓace Angel tayo kan Ayush tana faɗin “Ayush wai mekika aikata haka? haba dan Allah yanzu kin kyauta kenam, nasan Ogah Junaid yana matuƙar ƙaunar amma kika rufe ido kika ci masa mutunci a cikin mutane, wallahi da abunda kika masa gwara ki zabga masa mari kiyi tafowarki, ya amshi soyayyarki da ƙwarin gwiwa amma kee….” ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye, miƙewa Angel tayi tareda faɗin “sakamakon abunda kika aikata ya jawo ciwon heart ɗin mommy ya tashi yanzu haka sun nufi hospital da ita, shi kuma Junaid ganin yanda mommy take amar da jini yasa shima ya faɗi sumamme saboda tin baya likita ya sanar masa cewa idan zuciyar mommy ta sake bugawa zata iya rasa rayuwarta, ki duba ki gani duk ata sanadiyarki ki ruguza farin cikin dubban al’umma, masu Allah wadar da halinki su sukafi yawa, banji daɗi ba sam….”

tana kaiwa ƙarshe tayi ficewar ta..

 

Ayush ba abunda take sai kuka fuskarta yayi jawur, Uma ce ta fito daga toilet itama tana kuka tace “kin kyauta Ayush aikinki na kyau, amma inaso ki sani indai mommy ta mutu zaman cikin gidan nan ya ƙare miki, kuma kinyi rashin babban ɗan uwanki, jininki kuma masoyinki, ki sani duk wanda zaki aura bazai kai Junaid ba domin shi ɗin farin cikin rayuwarki ne…”

Ayush ta buɗe baki zatayi magana Uma tayi saurin ɗaga mata hannu tareda faɗin “sai anjuma..” ficewa tayi itama daga ɗakin, tana fita ta murɗa zoben hannunta lokaci ƙanƙani ta ɓace ɓat…

 

bayan fitar Uma daga cikin ɗakin Ayush hannu ta ɗora a kayi ta rusa wani irin gigitaccen ihu! kuka take sosai na fitar hankali,

 

Mommy har zuwa yanzu bata daina amar da jini ba, tana kwance a gadon asibiti likitoci sun fi biyar akanta, wasu suna danna mata ƙirji sakamakon harbawa da yake da ƙarfin gaske, cikin gaggawa aka ɗaura mata ledar jini, idonta sun fiffito waje tana shaƙar numfashi daƙer, dasauri aka sanya mata oxygen still ana daddanna mata ƙirjinta ta saitin zuciya..

 

and other room Junaid ne yake ƙwance shima an ɗaura masa ledar ruwa sakamakon zafin da jikinsa ya ɗau duk ruwan jikinsa ya yi low, a wannan lokacin shima bai samu farfaɗowa ba, ata waje kuma Rumana ce da Aditi suke zaune zaman jiran farfaɗowarsu,

Doctor Hasheem shima yana daga cikin likitocin da suke duba mommy,

 

abokatan Junaid duk suma suna nan, Angel ce ta shugo asibitin da saurin ta hawaye duk ya wanke mata fuska, guri ta samu itama ta zauna a kujerar da su Aditi suke a zaune,

babu wanda aka bari a gida sai iya Ayush…

 

tana kwance a saman gadonta sai faman rera kuka take, a ranta bata so hakan ta faru ba, inda tasan Mommy ce ta haɗa da batayi gangancin lalata shirin ba,

ji tayi an dafa bayanta, da sauri Ayush ta zabura ta tashi zaune ido duk yayi dishi dishin jaa tana kallon Laylah wacce take zaune a bakin gadonta,

 

murmushi Laylah tayi sannan tace “kukan mai kike yi? saboda kin faɗi abunda ke ranki shine kike ƙoƙarin kashe kanki? ni banga laifinki ba don kin fito fili kin sanar cewa bakya son abunda ake shirin ƙaƙuma miki” ajiyar zuciya Laylah tayi sannan ta kuma cewa “ni yanzu dai ba wannan ne ya kawoni ba, nazo ne akan na baki haƙuri akan abunda ya faru abaya, nasan nayi kuskure kuma nayi nadamar yin haka, please Aunty Ayush kiyi haƙuri dan Allah…”

 

Ayush share hawayen fuskarta tayi daƙer take motsa baki tace “ba komai ya wuce..” fuska duk ya kumbura!

 

Laylah tace “are you sure my Aunty?”

Ayush ɗaga mata kai kawai tayi saboda bata son magana a halin yanzu..

Laylah tace “ok thanks, kinsha kuka sosai nasan kanki dole zaiyi ciwo, ki kwantar da hankalinki su mommy zasu dawo gida cikin kwanciyar hankali, yanzu dai ga wannan maganin ciwon kai ne kisha sai ki samu yin bacci ko?…”

Laylah buɗe jakar ta tayi ta ɗauko wani magani ƙananu ta ɓare ta bawa Ayush tareda buɗe murfin gorar ruwa dake hannunta, Ayush karɓa tayi tana faɗin “nagode..”

Laylah tace “ba komai nima ina fama da ciwon kai ne shiyasa nake yawo da maganin”

ta ƙarasa maganar tana kallon Ayush ta wutsiryar ido tareda cije leɓɓen bakinta..

 

bayan Ayush tasha maganin gaba ɗayansu shuru sukayi ba wanda yace wa wani ƙala acikinsu,

after 5 minute dishi-dishi Ayush ta fara gani, idonta yana shirin rufuwa, gani tayi kwakwalwarta ta fara juyawa, nan take ta nemi hankalinta ta rasa, miƙewa tayi tsaye tana tangal-tangal murya na rawa tace “meyake faruwa dani ne, gajimare nake gani, ga can wasu da dokuna suna taho wa…”

 

ganin Ayush yanzu babu wani hankali a jikinta yasa Laylah ta tintsire da dariya tana tafa hannayenta biyu tareda faɗin “yaro man kaza, yaro bai san wuta ba saiya taka, Ayush kenam ni ba kanwar lasar ki bace, duk wanda ya raɓi jikin Junaid sai yanda ƙarfina ya ƙare wallahi, nasan wannan abunda ya faru yanzu bashi zaisa Junaid ya rabu dake ba, koda ace shi baya yinki nasan mommy saitayi kinibibin haɗa ku kuma duk da nasan a yanzun ma ita take shirin haɗa auren nan, amma yanzu zan kawo ƙarshen komai, zan dasa tsanarki a cikin zuciyar Ogah Junaid wanda ko kallonki bazai so ya yi ba, zansa ya rinƙa ƙyamarki…” tana kaiwa ƙarshe ta ƙwashe da dariya,

 

ita kuma Ayush zama tayi a kusa da Laylah tana ta faman shafa ta, tareda rungumota tana faɗin “inasonka sosai da sosai bazan iya rabuwa da kai ba masoyi, dan Allah ka bani kulawarka a gareni..” tana maganar kamar wata ƴar maye..

 

mirmushin gefen baki Laylah tayi sannan ta ɗauki wayarta ta kara a kunne bayan tayi dialing call,

“Hello sauro ka shugo yanzu ina jiranka, ɗakin dana kwatanta maka nan zaka shugo, kayi sauri kaga ba kowa a gidan..” tana kaiwa ƙarshe ta katse ƙiran, ga kuma yanda Ayush ta rungumeta sosai a jikinta…

 

Laylah wani magani ta bawa Ayush na fitar da mutum daga hayyacinsa sannan ya dasa masa mungun sha’awa, ta ƙira wani ɗan daba ne domin yazo yayi mata aiki akan Ayush..

 

ba jumawa saiga mutumin nan ya shugo cikin ɗakin Ayush yana ɗaure da fuska irin nan ba mutunci, rufe ƙofar yayi sannan ya danna sakata tareda cire kayan jikinsa ya zauna daga shi sai short nicket iya cinyarsa wato pant na maza..

ƙaƙƙarfan namiji ne irin zabgegen mazan nan, yana zuwa ya haura saman gadon tare da janyo Ayush ya cire mata kayan jikinta ya barta daga ita sai braziya da kuma gajeran wando baije mata gwiwa bama,

ita kuma sai shafa jikinsa take duk gargasa yayi curɓu-curɓu ba kyan gani, amma da haka Ayush take rungumarsa tare da shafa shi tana ta surutai “ina sonka, bazan rabu da kai ba, dan Allah karka ƙyaleni, inason kasancewa tare da kaii..” shima shafa ta yake ta ko ina, yana cusa hannunsa cikin breziyar ta tareda kissing ɗinta akan ƙirjinta,

 

Laylah kuwa tana tsaye ba abunda take sai video, tana musu ɗauka na gaske gashi sun fito sosai, har muryar Ayush ta fito yanda take ta surutai duk a rashin sani,

 

Laylah ganin mutumin yana shirin cire sauran kayan Ayush da kuma nashi ta danna stop sannan tace “kai sauro dakata nifa bance kayi mata komai ba, romance kawai nace kayi da ita..”

cikin ƙatuwar murya yace “na bar miki kuɗin da zaki bani, kawai ki barni nayi amfani da ita, wannan kyakykyawar budurwa zankaɗeɗiya wazai gani ya ƙyale….”

 

Laylah tace “kaga sauro ba haka mukayi dakai ba saboda haka kayi yanda nace, kuɗinka zan baka amma kada ka kuskura kayi mata wani abu, ina tausayin ƴan uwana mata saboda haka bazanso a cutar da rayuwarta ba,

ka hau kanta kawai kana kissing ɗinta, kaga ba lokaci..”

yanda tace kuwa haka yayi amma ba’a son ransa ba,

ta cigaba da musu video, shi kuwa kwantar da ita yayi ya hau kanta yana sumbatarta ta ko ina, itama Ayush tana ƙanƙame dashi hannayenta yana zagaye ta bayansa, bakinta kuwa ya kasa rufuwa sai sambatu take tana faɗan maganganun batsa ta yanda zaiyi amfani da ita…”

 

daga ƙarshe Laylah ta bashi umarnin ya sauƙa haka, tayi saved video tana cije leɓɓenta,

saka kayansa yayi sannan yace “ƴanmata ni zan tafi saina ji alart, ɗaga masa kai kawai tayi sannan tace “yanzu ma kuwa..”

yana tafiya tayi masa transfer 50,000,

Ayush kuwa nan danan wani irin mungun bacci ya ɗauketa, dariya Laylah tayi tace “wooo ni Laylah Amaryar Ogah Junaid, Ayush kenam daga yau soyayyarki bazata ƙara zama a cikin zuciyar Ogah Junaid ba, nasan dai bayan kin farfaɗo bazaki tuna abunda ya faru ba, sai dai ki ganki acikin wannan yanayinda kike ciki, na barki lafiya…”

 

Laylah ce itama tayi ficewar ta a ɗakin, cike da farin ciki ta bar gidan gaba ɗaya….

Matar Damisa Book 2 Complete txt

File Name   Matar Damisa Book 2… Hausa Novel Doc.
Title   Matar Damisa Book 2 Complete
Author    Asma’u Muhd Auwal
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/09/2024
File Size    400KB
Format Size    TXT
Book Price    300
Phone No   09065443871
Download Matar Damisa Book 2 Complete By Asma’u Muhammad Auwal 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button