Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 9 Complete Hausa Novel

 

Tsayawa Jalila tayi daga inda take a tsakanin flowers tana kallon su Jawwad Ilham ce takarasa shigowa gidan 

Su Jalal ke kokarin shiga mota Ilham ta danyi sauri ta je gabansu

“Yaya Jalal ina zaka ne?, inason zamuyi magana da kai”

Dama tunda tafara suspecting Jalila ke son Jalal ta dena kula Jawwad, yarasa me yayi mata

“Yaushe kika zama uwata dazaki ce kina son magana dani, kokuma yaushe kikazama ISP da kike tuhumata ina zani”

Jalal ya tamvayeta

Dan tabe baki tayi sannan tafara magana cikin shagwaba “two minutes kawai Dan Allah”

Bude mota yayi ya shige ya batta a gurin kaman gunki

Jawwad ne ya kalleshi, “haba bros Dan Allah fa tace, ka saurareta mana kasan mezata gaya maka”

“Indai wannan yarinyar ce babu wani abu me amfani dazata fada, komai nata daga shirme se hauka, bawani abun hankali a lamuranta”

Ya karasa shigewa motar ya kulle kofa ya batta a tsaye

Jalila daga inda take tana jin abunda suke cewa mamakine yacika Jalila tun wancan lokacin har yanzu Ilham ba ta dena son Jalal ba kuma har yanzu yana wulakanta ta amma tana manne dashi, tirkashi Allah kayi mana tsari da wahalalliyar soyayya dama wani mutumin arzikin ne takeso da da sauki amma Jalal wannan Dan wulakancin uban shaye²

Wayar da Jalila ta tabaji Ilham tayi a wancan zuwan nata ta tuna

“” ZANCIGABA DA HAKURI HAR LOKACIN DA BURINMU ZE CIKA AKAN JALAL DA MOMMYNSA””

Jalila bata manta ba wannan sune abunda taji Ilham tafada shekaru biyu dasuka wuce,

“Lallai akwai wani abu a kasa ba a banza Ilham take jure wannan wahalalliyar soyayya ba”

Ringing din wayarta ne ya fargar da ita daga dogon tunanin data tafi, lambar Siyama ce da sauri ta daga seda suka sha hira, takira Ummi ma suka gaisa sannan ta mike ta koma cikin Gida

Dakinsu ta nufa don aje wayarta tana shiga ta tarar da Ilham da Nana suna hira kuma dai ga dukkan alamu hirar akan Jalal ne, cikin dakin ta shiga tana fadin

“Juliet ta Romeo kokuma ince laila majnun, ya labarin soyayyar takune, domin labarin soyayyar nan akwai kayatarwa”

Jalila ta karasa maganar tana zama a gaban Ilham tareda yimata murmushi

Hade rai Ilham tayi kaman taga mutuwarta tareda tsurawa Jalila ido na wani lokaci, JALILA ma kallonta take kafin daga baya tace 

“Manyan yan mata a cikin garin kano wannan kallon fa”

Wani mugun kishine ya tokarewa Ilham ganin Jalila takuma girma ta kara kyau, maganarta ma gwanin burgewa, Nana ce tai farat tace “Ilham Jalila fa ta dawo kano da zama, tabar garin Kaduna, anan zata cigaba da zama damu”

Ras!Ras!!Ra’s!!! Ilham taji gabanta ya fadi

“Ta dawo kano da zama?”

“Eh mana munkara yawa”

Dagawa Ilham gira Jalila tayi

“Ko ba kya farinciki da zuwana in koma”

(Mhmm kaman ba Jalila data gama kuka akan zuwa kano ba kunga harta ware tafara sana ar Neman magana 😂😉)

Wani matsiyacin kallo Ilham takewa Jalila aranta take fadin

“Lallai yarinyar nan muguwar Yar rainin hankali ce ga yadda take pretending kaman ba wani abu a ranta game da Jalal”

A zahiri kuma cewa Nana tayi 

“Kinga mubar zancen nan mayi wataran, in mun sake haduwa”

Tai maganar tana yinkurin tashi tsaye riketa Jalila tayi

“No baza ayi hakaba ina lefin kice in baku guri, sha zamanki ai Jalila ba bakuwar zafi bace”

Jalila ta tashi tsaye ta bar musu dakin

Ta koma Kitchen tayi wanke² ta gyara kitchen din ta dawo parlour tana gyarawa, sallama akayi ta amsa wata budurwa ce wadda bata fi Sa arsu ba dauke da bagcco a hannu ta

amsawa Jalila tayi tareda yimata sannu da zuwa, yarinyar

Ta kalli Jalila tace “ina mutan gidan ne?”

“Suna ciki wani abunne?”

Jalila ta tambayeta 

“A a dama dawowa nayi”

“Kokece Halima”

“Eh nice”

“Allah sarki sannu da zuwa karasa suna ciki”

“To nagode”

Dakinta halima ta nufa taje ta aje kayanta ta fito domin fara aikace² taga kusan an gama komai 

Jalila ta kalleta “kije ki huta mana dagani kinyo tafiya”

“A a kaida ba Hutu kazo ba ina batun Hutu”

“Jikin Dan Adam yana bukatar hutu, ni nagama komai na dauke miki aikin yau”

Suna cikin haka Nana ta fito ita da Ilham, Nana ce ta kalli halima “sarkin biki, suna, ko mutuwa, se yau kinje kinyi zamanki a kauye ko”

“Wallahi bahaka bane Nana ni dince na danyi jinya”

“Haka dai kika iya kin barni aikin Gida kaman ya kasheni”

“Kai Nana Dan Allah wani irin aiki kaman ya kasheki ina aikin anan”

Jalila tafada tana hararan Nana

“Kenima wallahi in Yar aikin mummy ta tafi bana iya wannan wahalan tuni nake sawa a sallamesu a canza wata bana son shirme”

Ilham tayi maganar tanayiwa Halima kallon banza

Jalila kuwa kwashewa tayi da dariya a ranta tace kaga Yar masu Gida hada sawa a kori me aikin a fili kuwa cewa tayi 

“Halima kyalesu na dauke miki aikin yau jeki sha zamanki”

  “Mtseww shirme kawai”

Inji Ilham, “nice ma ke, akan shirme” Jalila ta bata amsa

“Enough please narasa wannan rashin jituwa a tsakaninku, Ku indai zaku hadu sekunyi fada, wuce muje”

Nana tafada tana tura Ilham

“Muje zuwa zangane abinda kike kullawa ne Ilham narasa inda kika dosa,”

Jalila tayi maganar a zuciyarta ta nufi dakin maama, da sallama ta shiga Maama ta amsa mata da kyar amma dayake Jalila ta iya siyasa se ta nuna kaman bata San abinda Maama take mata ba, ta karasa kusa da ita ta zauna “Hajiya Maama hutawa kike? Me za a dafa miki yau”

“Kinga ban saki ba balle Abbansu Jawwad yace daga zuwaanki an fara takura miki”

“Haba Maama wani irin takura, aikin Gida ai dolene ga ya mace ba batun takura”

“Kinga ga kitchen din nan jeki abinda kika gadama”

Maama ta karasa maganar cikin kosawa”

Mikewa Jalila tayi ta fito ta bata guri, ta nufi kitchen, ta tarar da halima tana kokarin dora abinci tare sukayi komai da Jalila sukayi girkin suka gama suka gyara kitchen din Jalila tanayiwa Halima gyare² a wasu abubuwan

Yayinda Nana tana daki a kwance tana chatting Jalila ce ta shigo ta sameta “Nana gaskiya mijinki ze sha fama”

Dan kallonta Nana tayi

“Kaman ya?” “Kallifa tunda garin Allah ya waye daga chatting se bacci haba Nanancy gaba fa akeji ba yanzu ba”

“Jalila kenan in Allah ya nufi ka huta kawai ka huta, kema ke kikasa kanki, wannan wahalar shikenan mutum baze huta ba”

“To naji tashi ki kaiwa Yaya Jawwad Abincinsa, in munyi salla se muci namu”

“Ba inda zani, in yanason ci in sun dawo daga yawon yazo ya dauka”

“Kai Nana Yaya Jawwad din?”

“Eh shidin, ina zuwa ze fara Sani aiki yana min masifa, bakiyi kazaba, wannan ba dai² bane, ga Yaya Jalal ma yaitawa mutum wani gani² mistake kadan seyace bazeci abincin ba, kuma in beciba Yaya Jawwad ma baze Ciba, shiyasa Halima ce take kaimasa itama haliman in basu gadama ba in ta kai bazasu Ciba, Yaya Jalal yafi kowa wannan tsirfan, kokuma yanzu susaki dafa wani abincin, shiyasa ko yazo ya dauka da kansa,ko halima ta kaimusu, bana son wahala”

“Tabdijan indai Yaya Jawwad ne meye a ciki se in masa amma Jalal kam yayikadan”

Dariya sosai Nana tayi, 

“Tab cakwakiya Ashe kuwa zakuiyi fada da Yaya Jawwad”

“Ke ni bari in wanka in yazo se ya shigo ya dauka,abincin”

“Kin temaki kanki kema seki huta”

    Se bayan sallar la’asar sannan su Jawwad suka dawo ko ina sukaje? Oho nima bansaniba Jalila tana tareda halima sunata hira, Jalila ta sha mamaki da halima tace mata ta taba aure amma tasha wahala gashi auren dole akayi mata, tanata bata labarin kauye

Yaya Jawwad ne ya shigo ya tarar dasu a parlour, cikin grimamawa halima ta gaida Jawwad ya amsa mata a mutunce sannan ya kalli Jalila

“Baby mun dawo, atemaki cikin gayu, munajin yunwa”

“To babban Yaya yanzu kuwa bari in kai”

“God bless you my sister”

“Ameen Yaya Jawwad”

“Bari in shiga in duba Maama”

“To Yaya a fito lafiya”

Ta mike ta nufi kitchen ta shirya kayan abincin akan tray ta dauka tayi hanyar waje

A kashingide ya tarar da Maama tana waya Dan haka yajira ta gama sannan ya Dan dubeta

“Maama mun dawo”

“To sannunku, ina fatan komai lafiya?”

“Komai normal Maama, kayan ma suna boot”

“To shikenan Bari zan tura Nana ta kai musu”

“To shikenan Maama nasa JALILA ta kaimana abinci mun debo yunwa”

Yafada yana mikewa

“Yawwa dawo ka zauna zamuyi magana”

Guri ya nema ya zauna ya bata attention dinsa

“Ba kaga yarinyar nan ta dawo gidan nan ba, bana son shishshige mata daka keyi, wannan rawar kan da kake akanta kana wani janta a jiki duk banaso, ga Yar uwaka nan cikinku daya ta isheka bana son yayime² da cusa kai kanajina ko?”

Mamakine ya cika Jawwad wai Jalila ce yayime² Allah sarki Jalila itama Yar uwassu ce ai suke nan ba yawane dasu ba amma meyasa Maama har yanzu batason alakar my da Jalila, ya numfasa sannan yace

“To Maama za ayi yadda kika ce, insha Allah za a kiyaye”

“Gara dai itama Nana zan mata magana naga zakewar taku tayi yawa, Tashi kabani guri” mikewa yayi ya fito, jikinsa a sanyaye

Jalila ta kai Abinci part din Jawwad kaman dazu yanzuma Jalal yana nan amma bata kulashi ba be kulata ba ta ajiye zata fita, taga wani key holder akan center table da keys na mota a jiki dakuma wasu keys din, key holder din yayi kyau wani Dan Teddy ne a jiki me kyau, kai tsaye Jalila taje ta Sa hannu ta dauka, ta jujjuya shi yayi mata kyau sosai, tafara kokarin cire teddyn jiki, ita a tunaninta na Jawwad ne, Jalal ne yake satar kallonta yaga ikon Allah, seda ta cireshi tsaf daga jiki, tabar keys din haka ta mayar kan center table din ta ajiye, ta dau Dan Teddy zata fito Jawwad ne ya shigo dakin jikinsa a sanyaye sakamakon maganganun da Maama tayi masa

“Kinkawo abincinne”? 

“Eh na kawo gashi can”

“Mungode sosai”

Murmushi yayi, hannunta ya kalla, yaga abin key holder din Jalal,

“Baby waya baki wannan”? 

“Yaya sonake a jikin keys dinka naganshi”

“To wayace miki nawane?”

“To ai duk abunda yake dakin nan nakane”

“Dagaske”?

” eh mana duk abunda ya shigo cikin dakin nan yazama Naka”

Dariya Jawwad yayi “to na oga ne dafatan kin tambayeshi kafin ki dauka”?

Dan zaro ido Jalila tayi

” waiwa kake nufi”

Da ido ya nuna mata Jalal, Dan bude baki tayi 

“Ni cirewa kawai nayi, na dauka nakane”

Kwaikwayonta Jawwad yayi

“Eyya na Yaya Jalal ne a tambaye shi tukuna”

Jalal yana jinsu yayi musu banza ya sakko ya fara kokarin zuba abincinsa salad din data hada ya bude tayi masa wani decoration yayi kyau sosai,, maida hankali yayi yafara zuba abincinsa 

“Jeki tambayeshi mana?”

Jawwad ya maimaita, noke kafada tayi,

“Meyasa bazaki tambayeshi ba”

Dan tura baki tayi “ai nakane”

Jawwad ne yadan kalli Jalal yaga shi ta abinci yake, Jalila  ta shammaci Jawwad tayi waje abunta da Dan Teddy a hannunta

A parlour ta tarar da Maama tana lissafawa Nana Atamfofi da less

“Yawwa Jalila zomuje tare, kayan nan zan kaiwa mommy Jalal”

“To shikenan Ku gama kirgawa”

Akagama kirgawa suka zuba a manyan leda suka dauka suka nufi gidansu Jalal 

Shigarsu yayi dai² da fitowar Mummy daga part dinta, Dan bude baki mummy tayi, “yan mata saukar yaushe?”

Durkusawa Jalila tayi ta gaisheta ta amsa da fara a “kinzo mana Hutu kenan””

Nana tai farat tace”a a mummy ta dawo nan gaba daya”

“Masha Allah hakan yayi kyau, ya Maman naki?”

“Lafiya kalau ta bata amsa”

“Masha Allah toku shigo ciki mana”

suka shiga cikin parlour shima yasha gyara kaman parlour amarya, 

kayan suka zube agabanta, dubawa ta shigayi dayake suna business sosai tsakaninsu da Maama

“Kai amma lesses din nan sunyi kyau, kafin akaisu bari Ilham tazo ta zaba, Jalila Dan kirawo Ilham tana dakin ta “

Ba musu JALILA ta tashi ta tafi dakin Ilham, tayi ruf da ciki tana jin music a wayarta, duk tasaka Bluetooth a kunnenta, tana bin wakar a hankali, tayi ruf da ciki tabada attention dinta akan waya shiyasa bataji shigowar Jalila ba 

Bakin gadon Jalila ta karasa ta Dan leka wayar Ilham, hotunan Jalal, takewa wannan kallon kurillan,

Jinjina kai Jalila tayi tareda furta

“Yar wahala, kina nan kina shirme yana can yana shagalinsa”

Hannu Jalila ta kai ta girgizata

“To uwar soyayya kije ana kiranki”

Dan dagowa Ilham tayi ta kalleta a wulakance, jitayi kamar hannun Jalila na kamshin turaren Jalal zumbur ta mike tana kallon Jalila

“Meye haka? Kin shigomin ba sallama”

“Kina can kina ibadar dababu lada taya zakisan nazo”

Hannun Jalila ta kalla taga teddyn jikin key holder din Jalal

Kwalalo ido Ilham tayi ta kai hannu kan abun tareda fadin

“Wayabaki wannan aina Jalal ne”

“Kamarya waya bani? Dan na Jalal ne kuma shi kadai akayiwa? Kinji mace kinga ni cewa akayi kawai nakiraki”

“Inba nasa bane ya akai naji kamshinsa, kamshin turaren Jalal ne a jiki fa, kuma tabbas nasane”

“Au Jalal din har wani kamshi yake na daban, banda warin hayaki meyakeyi, kullum cikin zukar hayakin taba har wani kanshi yake”

Mikewa Ilham tayi tsaye tana kallon Jalila sannan ta nunata da yatsa

“Naga wannan karon kin karo wulakanci, kuma wallahi bazan saurara miki ba koni ko ke, tuntuni nagane take² ki, se yanzu nagane inda kika dosa, am ready for you”

Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa

          -MY FIRST NOVEL-

Yatsan da Ilham ta nuna Jalila dashi, Jalila tasa hannu ta sauke yatsan Ilham

“Dukda Ban gane inda kalamanki suka dosaba, banga abunda nayi miki kike tada jijiyoyin wuya hakaba, sedai bansaniba ko kema Jalal yafara baki giyar saboda naga alama daga wannan maganganun naki, yanzu dai kije matar gidan tana kiranki”

Jalila na zuwa nan a zancenta tasaki hannun Ilham, tayi waje abunta 

“Ina Ilham din?”

Mummy ta tambaya “nagaya mata amma naga kaman batajin dadine amma nagaya mata”

“Bata jin dadi kuma? “Meyasameta dazun nan fa tabar palour”

Ita dai Jalila shiru tayi,

Jalila na fita Ilham ta koma kan gadon ta zauna kanta kaman ya fashe ta rike kanta lallai ma wato Jalal har yayi sakewar da abunsa ze shiga hannun Jalila,

Wato Jalila tayi galabar fara soyayya da Jalal, kuma kalli yadda takemin kamar bata San metayiba to ni ina me hakan yake shirin faruwa impossible Ilham tafada da karfi

Muryar mummy taji tana kiran sunanta Dan haka da sauri ta kwanta akan gadonta ta rufe ido, cikin dakin Ilham mummy ta shigo ta ganta a kwance “ke Ilham meyasa meki”

Bata juyoba bata bude Ido ba tabata amsa

“Kaina kemin ciwo”

“To bazaki sha magani ba, se kizo ki kwanta”

“Nasha fa”

“To Allah ya sawwake, in bedena ba kiyi magana akaiki Asibiti dama kaya aka kawo nakeso ki dauka bari insa abarsu anan in kinji sauki seki duba ki zaba”

“to”

Shine abinda Ilham itace, mummy ta juya zata fita Ilham taraka bayan mummy da harara tareda yin kwafa, tana fita ta mike taje ta kulle kofarta tasa key ta dawo kan gadonta ta zauna “munafukan banza zanga bayanku daya bayan daya, gara in fara kauda wannan banzar yarinyar gefe tukuna, naga zakewarta tayi yawa inna bari tayi galaba, abunda ake gudu yafaru to shirinmu gaba daya ya rushe,”

Mummy ce tafito tace musu subar mata kayan anan zata aiko da Wanda ba a siyaba suka mike suka fito 

Itakam Jalila mamakine ya cikata metayiwa Ilham takemata wannan maganganun harata na wani zatayi maganinta, lallai bata sanni ba kafin tayi maganina zanyi maganinta idan na gano metake kullawa

Nana ce ta Dan kalli JALILA

“Baby wai ko kunyi fadan da kuka saba ne naga da fara a kika shiga gurin Ilham amma kin fito wani iri ko akwai matsalane?”

“Bakomai me zatamin daze Sani bacin rai aitayi kadan”

“Nikam narasa meyasa ba kwa jituwa da ita”

Murmushi Jalila tayi 

“Niba abunda yahadamu da ita kawai dai tanada saurin fushi ne”

“Kekuma kinada tsokana ba”

Nana tafada a tare sukayi dariya suka shiga Gida Jalal ne yazo ya giftasu yana waya,

“Bazan fito ba dan uwa yace, kar in sake in fito, dan haka yau ina gida kayi hakuri”

Dan shiru yayi sannan ya cigaba

“Wani mamaki zaka bani, nayiwa Jawwad rakiya duk nagaji,

Wai dole yau kakeso in zo abari se gobe zanzo kwana zanyi a gurin”

Jalila ce ta Dan tsaya yayinda Nana take kokarin Janta su tafi dan kwace hannunta tayi daga na Nana 

“Yi gaba zan amsa wayane”

“Waya kuma waya kiraki a waya? Anfara kiran sallar magariba ki zo mu shiga basekiyi wayar a ciki ba”

“Ke dai kiyi gaba yanzu zan karaso,”

Wucewa Nana tayi abinta, yayinda Jalila tabi bayan Jalal, ta tsaya nesa kadan dashi amma tana jin meyake cewa

“Hannah kuma, Hanna ta fiye rigima, mezatayi a gurin nan da daddare in dai zata gurin nan bazanzo ba, dazu naga kiranta ban dauka ba, muna tareda Jawwad indai zata ganni a guri seta fitineni, nikuma banason shirme”

Shiru ya dan kumayi Jalila batajin me ake cewa daga daya bangaren

“Waiku meyasa kuka takura lallai senazo, taya zan taho karfe biyu na dare, ina laifin afara ten agama one

Anyway zanyi kokari in fito”

Karfe biyun dare mezeje yayi karfe biyu a wani guri shikadai

JALILA tai maganar a zuciyarta gyaran murya tayi Wanda hakan yasashi waigowa dukda duhu yafara amma yagane Jalila ce,

“Karfe biyun dareko zaka fita, Allah yatemake ka kafita, kai ko tausayin iyayenka bakayi, ga dan uwana kullum bashi da cikakken kwanciyar hankali saboda kai, yakamata ka tausaya masa”

Ta karaso inda yake ta miko masa dan teddy nan

“Ungo abunka kanwarka zatamin hauka dan taga wannan abun banzan a hannuna,”

Dan kurawa Jalila ido yayi, na yan sakanni bece komai ba kawai ya juya ya fita

“Yan wahala kai da kanwartaka Allah yayiwa Yaya Jawwad tsari da kai da fitinarka, dan kai Jarrabawane a rayuwarsa, ba dangin iya ba na Baba amma kullum hankalinsa ba akwanceba saboda kai kuma ko tausayinsa bakaji, wallahi in kaje gurin nan aka maka wani abu Alhakin Yaya Jawwad base barkaba”

Cak Jalal ya tsaya jiyayi kaman Jalila ta soka masa mashi a zuciyarsa

Girgiza kai yayi ya nufi hanyar gate,

“Allah yasa kar ya FIta”

Jalila tafada a fili son jikinta nabata wannan fitar ba alheri bace akwai abunda aka shirya yi masa

Ta wuce cikin gida ta tarar da Halima a zaune a palour tana kallo “Anty Haleema kallo ake haka anyi sallar magariba fa”

“Wallahi inkikacemin Anty kunya kike bani”

“Kunya kuma saboda me nake baki kunya”

“Ina aiki a gidanku, kumafa watakila kin girmeni amma kidinga cemin Anty”

Dariya JALILA tayi “haba leemart har aure fa kikayi kuma kin haihu kin cancanci a girmamaki”

“Wannan sunan yan gayunfa dakikace yanzu”

“Ya miki dadine?”

“Eh wallahi”

“To shikenan, bari inje inyi salla kema kije kiyi, inzo kibani labarin kauye”

“To shikenan bari intashi”

Jalila taje ta tarar da Nana tana salla dan haka ta ajiye wayarta itama taje tayi alwala zata tada salla tana kallin Nana tana idar da salla ba Azkar ba komai ta shafa fuskarta, taja gefe ta dau wayarta ta kama sana’ar tata ta chatting

Har Jalila ta idar da sallah tayi Azkar dinta, sannan ta waigo ta kalli Nana “waini Nana mekike a cikin wayar nan haka ne ke idonki baya miki ciwo”

Dariya Nana tayi “lallaima wani irin ciwo kuma ba wani ciwo”

Gyda kai Jalila tayi ta tashi ta tafi dakin halima itama ta idar da sallar tana ninkin kaya

“Yawwa gani nazo zo kibani labarin kauye”

“Kekam Jalila meyasa kikeson kauye”

“Wallahi inaso inje amma bantaba zuwa ba kauye yana birgeni”

“Tab kinemi tsari da rayuwar kauye, yanada dadi in kayi dace da mutanen kirki a garin

Amma kinganni nasha wahalar zaman kauye ga maraici ga rashin gata, ina Jss 2 akamin auren dole da dan hakimi ga jarabar kishiyoyi da yayansu, uwargidansa ma takusa Sa ar kakata”

“Zaro ido Jalila tayi Sa ar kakarki, keko waya aura mikishi”

“Kanin mahaifina Jalila, matan mutumin nan su hadu sumin duka, shi kansa jibgata yake a haka nasamu ciki ga laulayi, amma babu tausayi ranar aikina senayi, wanke² ma kawai na gidan nan bala’i ne balle girki”

“Subhanallah kuma kanin mahaifin naki yasan halin dakike ciki”

Jalila tayi maganar kaman tayi kuka

“Wallahi yasani Jalila, an azabtar dani a rayuwata maraici babu dadi, danginmu suna kallo amma babu me iyayi masa magana”

Jalila kaman ta fashe da kuka saboda tausayin halima, nan Takara jinjina rikon Amana irin na abban Jawwad ko mahaifinta yana raye tasan iyakar dawainiyar daze da ita kenan, bata taba kukan rasa wani abuba saboda maraici”

Tana wannann tunanin JAWWAD ya kirata

“Baby atemaka da coffee please”

“To Yaya ban yan mintuna”

“To shikenan”

Ta kashe wayar ta kalli halima “leemarta bari inje in hadawa Yaya coffee, amma zan dawo, ko in taho miki dashi” girgiza kai halima tayi

“A a ni ban iya wannan ciye² yan gayun ba, kedai sekin dawo”

Murmushi Jalila tayi ta fita

Murmushi halima tayi itama gaskiya Jalila tanada kirki yadda take sakin jiki da ita bata ISA ta zauna Inda Nana takeba mussaman insuna tareda Ilham, taita zigata tayi mata rashin mutunci,

Kokuma taita sakata aiki kaman baiwa

Jalila tahada coffee ta tafi ta kaiwa Jawwad, wannan karon shikadaine a parlour 

“Yawwa sisy nagode sosai, dama Jalal ne ya kirani yacemin yanaso shiyasa nasaki, nagode”

“Kutmelesi JALAL nema ze sha, wallahi Dana San shine bazan hada ba” Jalila tayi maganar a zuciyarta a fili kuma hanyar fita tayi ta koma cikin gida

  Jawwad ya kaiwa Jalal coffee din jiyayi yafi na ko yaushe dadi

“Waya hada tea din nan?”

“Jalila ce, ita nasa ta hada maka, kasan Nana in batasa kanta abu ba se a hankali, JALILA ce komai kasata ba kyuya zatayi maka a nutse”

Jalal be kuma cewa komaiba yacigaba da shan coffee dinsa, seda ya kammalla tukuna sannan Jawwad ya dauki flask din ze fita, har yayi hanyar fita ya dawo,

“Jalal dan Allah karka fita ko INA yau kazauna ka hutawa ranka karkaje gurin shan giyar nan yau dan Allah”

Yakarasa maganar da sigar rarrashi, tausayinsa ne Yakama Jalal gaskiyar kanwarsa datace ba dangin iya ba na baba amma kullum hankalinsa a tashe saboda ni

Ajiyar zuciya yayi, “ba inda zanje insha Allah, ina gida”

“Are you sure” Jawwad ya tambayeshi, murmushi Jalal yayi masa “am sure, bros ba inda zan fita yau”

“Thank you very much, Allah ya tashemu lafiya”

“Ameen” Jalal ya amsa, sannan Jawwad ya fita ya koma gida

Bayan fitar Jawwad ne, Jalal yafada tunani,

Tabbas Jawwad ya dade yana dawainiya dashi, kullum bashi da kwanciyar hankali saboda shi, abokansu da Dama suna kyamarsa basa mu’amala dashi saboda halinsa, iyaye dayawa sunyiwa yayan su Katanga tsakaninsu da Jalal saboda miyagun halayensa, amma Jawwad be guje shiba tabbas wani abu yasamu rayuwarsa hakkin Jawwad baze barshiba

“Mummy why kalli halin da danki yakeciki, ga rayuwar danakeyi mummy saboda ke ga yadda ake kyamata mummy why meyasa kika aikata haka a rayuwarki, abun Yakoma kaina”.

Haka Jalal ya dinga surutai hawaye nafita daga idonsa, ” Thank you very much Jawwad bazan iya biyanka wannan kaunar ba”

Ya furta a hankali

Jalila bayan takoma cikin gida bata koma gurin halima ba Ummi takira a waya suka sha hira take tambayar Ummi yaushe zatayi tafiyar ne?

“Se nan da wani dan lokaci, akwai shirye² danakeyi sonake sena gama”

“Ummi wani shirye² kuma, nifa sonake kije ki dawo, in dawo gida mucigaba da zama tare”

“Hmm Jalila kenan in na tashi tafiya kafin in tafi zanzo kano muyi sallama”

“Yawwa Ummina har naji dadi wallahi dama inkinzo ki daukeni mutafi tare”

“Mutafi ina, bana son rigima, ai bahaka mukayi dakeba senaje na dawo tukuna semuje tare”

“To shikenan ummi, Allah ya kaimu lokacin”

“Ameen ya Allah, ki gaida mutan gidan naku”

“To ummi zasuji insha Allah”

Haka sukayi ta hira da Ummi kaman bazasu dena ba kafin daga baya sukayi sallama, Nana ce ta shigo da kwano a hannunta 

“Babyn ummi dawa kike wayane?”

“Nida ummine wallahi”

“Au ai na dauka da wani gayen kike waya”

Dan zare ido Jalila tayi “rufamin asiri gaye kuma”

“Eh mana karya kike dai kice baki da saurayi”

Hararta Jalila tayi “au tambayata ma kike”

“Au tuba nake ai namanta, na dauka an masa kishiyane”

“Nana kinfiye shirme, mekike da kwano haka”

“Abinci zanci”

“To aci lafiya ni kwanciya zanyi”

Jalila ta bude akwatinta ta dakko kayan bacci, Nana ta kalleta

“Jalila nayiwa Abba magana za acanza mana wardrobe, semu maida kayanmu ciki, naga kayannaki dayawa”

“Kin doramasa nauyi, dakin bari se inbar wasu a akwatin ba ai duk dayane”

“Hmm Jalila kenan kome zakice nidai nagaya masa”

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Jalila tasamu guri ta kwanta, 

Bacci ya gagari Jalal se tunani yake, Jeje ya kirashi a waya ta dinga ringing amma yaki dagawa

Ya kalli wayar yaga yadda sunan Jeje ke yawo akan screen din wayarsa,

Yasan batun party nan ze masa tsaki yayi

“Kaine mafarin komai”

Yayi tsaki ya kashe wayarsa gaba daya ya zame ya dan kashingida ya runtse idonsa yana tunanin abubuwa da dama dasuka wuce a haka bacci barawo ya dauke shi

Washe gari da asuba bayan  Jalila ta idar da sallar asuba, tanaso ta danyi tilawa amma taga Nana na kokarin komawa bacci dan haka saboda karta takuramata seta koma palour ta fara karatunta cikin sautin muryarta me dadi, seda gari yayi haske sosai sannan ta tashi da nufin shiga kitchen Halimace ta fito ta kalli Jalila 

“Barka da safiya sayyada Jalila”

“Rufamin asiri inani ina zama sayyada Jalila dai”

“Haba wannan karatu haka, kuma daka fa kikayi dama nice na iya”

“Kema zaki iya in kinaso”

Halima ta dan zaro ido “dagaske?” 

“Dagaske mana”

“To ta yaya?”

“Yanzu dai bari mu kammalla aikin gida semuyi maganar”

“To shikenan bari inje in fara gyara kitchen din kafin kifito”

“To shikenan bari in maida sallayar nan daki”

Yadda ta tabar Nana haka ta dawo ta tarar da ita, a dukunkune tana bacci a cikin bargo, dan girgiza kai Jalila tayi ta aje hijjabin ta da sallayar ta fito palour, a kitchen suka hade da halima  suka cigaba da aikin breakfast dinsu suna hira, koko da kosai sukayi 

“Anya mutan gidan nan za suci koko da kosai, ko kowa zeci wannan abokin Jawwad din, me Suma a tsartsaye, gashi duk yayiwa gashinsa kala, gashi jarababbe da kyar yaci wallahi dan ya fiye iyayi,”

Halima tayi maganar tana kallon Jalila

“Wai Jalal kike nufi?”

“Eh shi wallahi, jarababbe ne, har fargabar kaimusu abinci nake”

“Aikuwa sedai kar yaci din, yatafi gidansu mana yaci, ai naga gidansu ma akwai abincin”

Dan zare ido halima tayi

“Tab ba ruwana,”

Haka suka gama girki suka gyara ko ina 

Se bayan karfe Tara na safe mutan gidan suka dinga tashi daya bayan daya

Sunyi farinciki da ganin abincin da akayi kowa yacika cikinsa suna murnar wannan sakakken abincin da Jalila tayi musu

Karfe taran nan ta nufi part din Jawwad kai  Abinci amma seta kai na mutum daya iya na Jawwad banda Jalal.

dan jaraba da sassafen nan yana sashen Jawwad daga harabar part din Jawwad akan kujera yanata shan taba, da ganin yanayin shigarsa kaman motsa jiki yagama,

Seda Jalila tazo gifta shi sannan tace

“Dan Jaraba da sassafen nan mutum be karya da komaiba se hayaki”

Ko kallonta beba yacigaba da shan tabar Sa

Cikin palour Jawwad ta kai abincin amma baya palour, bedroom din Jawwad taje ta danyi knocking amma shiru, ta tura kofar bedroom din ta Dan bude zubar ruwa taji a toilet alamun yana wanka

Dan haka ta fito har tazo zata kuma gifta Jalal takoma gaban Jalal sannan tace masa 

“In Yaya Jawwad ya fito kace masa ga abincin Sa nan, in yagama ya kirani zan gyara masa daki”

Ko motsi beba balle ya kalleta yacigaba da aikin shan tabarsa, ga kwalin wata tabar da lighter akan table din gabansa

Har zata wuce ta dawo, tasa hannu ta dauke kwalin tabar da lighter ta fizge na hannunsa

“Wai kai wani irin mutum ne, baka San wannan abar illa ce ga lafiyaba da sassafe baka zubawa cikinka komai ba se hayaki, karka kuma shamana wannan abar a cikin gida, inzaka sha ka zauna ka sha a gidanku, dan uwana yafika cutuwa da wannan hayakin dakake busawa ba yau ba gobe”

Dagowa yayi ya kafeta da Jajayen idanuwansa kyar ko kiftawa bayayi

Seda gaban Jalila yafadi tozali da wannan idanuwan na Jalal masu kama da garwashi dagani ransa a bace yake

Dukda ta razana, ta dauka ze mareta ne, ta dake ta juya ta bude dustbin ta watsasu ciki tayi hanyar cikin gida bin bayan Jalila yayi da kallo ya kai makura a tunani bayajin komai tunaninsa yayi zurfi sosai, jiyayi an dafa shi yadaga kai Jawwad yagani a tsaye “

dan uwa zomuje mu karya naga baby takawo abinci”

Girgiza kai Jalal yayi “banaci”

Yafada a takaice tareda mikewa tsaye “kamar ya bakaci Abincin ne beyimakaba kokuwa wani abun Jalila tayi maka”?

Girgiza masa kai Jalal yayi, yana kokarin tafiya, dakatar dashi Jawwad yakumayi 

“Haba Jalal kagayamin me akayi maka mana, na lura tunjiya da magariba baka walwala, meyasane”?

Dan kurawa Jawwad ido yayi yaga yadda yadamu 

“Calm down ba abunda yake damuna jinayi kawai bana son cin Abincin”

“No Jalal ban yaddaba”

Juyawa Jalal yayi ya tafi, yabar Jawwad a tsaye,

“Ohh God, meyake damunsa ne”

Komawa Jawwad yayi ya duba abincin kunun gyadane da kosai

Mikewa yayi yabi Jalal gidansu, Jalal yakoma gida yaje, ya kwanta akan gadonsa ya lumshe ido

Jawwad ya karasa ya zauna gefen gadon ya dafa Jalal “dan uwana kagayamin meyake damunka?, lokaci daya duk ka canzamin, kagayamin ko Jalila ce tayi maka wani abun” dan bude ido Jalal yayi ya kalli Jawwad, idonsa Yakuma yin Ja girgiza masa kai Jalal yayi

“To yanzu kayi hakuri, kazo muje kaci abinci”

Mikewa zaune jalal yayi “Jawwad ba abunda yake damuna, kaje kaci abinci ni na koshi, karka damu dani banajin cin Abincin nan”

Mikewa Jawwad yayi ya koma gida yana tunanin meyafaru da Jalal, 

yaje ya tarar da Jalila a part din Sa tana kokarin gyarawa

yana shigowa Jalila ta kalleshi 

“Yaya Jawwad bakaci Abincin ba meyafaru”

“Baby ko kinyiwa Jalal wani abune naga yaki cin Abincin kuma ya tafi gida”

“Cemaka yayi nayi masa wani abun?”

“A a becemin ba amma naga yanayinsa ya canza tun jiya”

“To tunda bayaci kaikaci naka karabu dashi mana”

Dan zaro ido Jawwad yayi

“A a baby bazan iyaba akwai abunda yake damunsa amma yaki gayamin”

“To Allah ya kyauta, dama gyara maka dakin zanyi”

“Ke ba kya gajiyane? Kije ki huta”

“Karka wani damu bawata gajiya gyaran part din naka ai ba wani lokaci ze dauka ba”

“Bani da bakin godiya baby Allah yayi miki Albarka”

“Ameen yayan”

Flask din kunun gayadan da cups ya dauka yayi waje, Jalila ta girgiza kai Abincin ne baze iya Ciba in Jalal baeci ba tab agaida Yaya Jawwad

Nan da nan Jalila ta gyara part din ta kukkuna tiraren wuta se kamshi yake ta rufo ta koma cikin gida Maama ta tarar a palour da nail cutter tana kokarin yanke farce, Nana kuma na kan two seater tana kallo, karasawa tayi gurin Maama ta karbi nail cutter din 

“Kawo in yanke mini, inna gama sekice Allah yayi min Albarka”

Ta karba takama hannun Maama ta na kokarin yanke mata farce, kallon Jalila Maama takeyi “wannan wace irin yarinyace dabata San wulakanciba, duk hade mata ran danake taki ta nuna tasan inayi balle taji haushi”

Haka Jalila ta yanke mata farce tsaf, sannan tabar palour

Jawwad da kyar ya lallaba Jalal yaci abincin safe kusan karfe daya na rana, amma dukda haka Jalal baya walwala, daurewa kawai yake ya boye damuwarsa saboda Jawwad, 

  Kwana biyu Hannah Sam bata ganin Jalal, baya daga kiranta, ta dan shiga damuwa saboda haka ta yanke shawarar kiran Jeje tagaya masa, shima complaints din da yayi mata kusan kwana biyar bega Jalal ga kuma baya daga wayarsa, yaje gidansu baya nan besamu ganinsa ba yarasa meyake damun Jalal

Haka take ma gurin Jawwad kowa yarasa ganewa Jalal abinci se Jawwad ya takura masa sannan zeci, baya walwala yadena shiga gidansu Jawwad sam, Jawwad yarasa dalili, Jalal ya dena zuwa ko ina se zaman daki

Yau kusan satin Jalila biyu a kano amma har yanzu Ummi batayi tafiyar nan ba, tun JALILA tana tambayar Ummi har tagaji ta kyaleta,

Jalila tana rayuwa a kano ba yabo ba fallasa, Jawwad da Nana da Abbansu suna kaunarta, yayinda Maama Sam babu ruwanta da ita, bata shiga sabgar Jalila kwata² hakan bayamata dadi amma bayadda ta iya

Tun ranar da Jalila suka samu wannan sabanin da Ilham bata kuma haduwa da ita ba

Jalila tana zaune a palour tana chatting da Hanan, Halima ta fito sanye da hijabi Jalila ta Dan dubeta

“Anty halima ina zuwa haka?”

“Kinga Hajiya ce ta aikeni zan kai kayan nan, gidan wata kawarta”

“Bari in tambayeta se in rakaki”

“To shikenan tambayota semuje”

Dakin Maama Jalila taje ta ganta tana waya ta jirata tagama sannan tace

“Maama naga kin aiki halima zan rakata Dan Allah”

Kallonta Maama tayi a wulakance ta dauke kai

“Ba a karkashina kike zaune ba yadda kika gadama kiyi”

Kallonta Jalila tayi ta Dan girgiza kai, ta mike ta bar dakin ta fito ta tarar da halima,

“Bari insaka mayafi in rakaki”

“To ina jiranki”

Jalila taje ta dakko gyalenta tayi rolling ta fito

Ba karamin kyau Jalila tayi ba doguwar Riga tasa baka tayi rolling da Jan mayafi suna shirin fita Nana suka shigo ita da Ilham

“Wow looking so masha Allah sister kina wuta kinga kyan da kikayi kuwa, ina zuwa haka”?

Murmushi Jalila tayi ” bana son zolaya Nana, Halima zanyiwa rakiya”

Banda aikin harar Jalila da kallon banza ba abunda Ilham takeyiwa Jalila

“Gaskiya kinyi kyau, sekun dawo, amma gaskiya ayi a hankali karki hada go slow a hanya”

Nana ta fada tana kashemata ido

“Nana kenan ba kya rabo da tsokana”

Jalila ta Dan kalli Ilham

“Kawata Ilham ba fada me yakawo gaba, fatan kina lafiya”

“Nakasa kika gani a jikina kokuma, a kwance kika ganni kike tambaya ina lafiya”

“Ba ko daya na dai ga kaman u are psychologically abnormal”

Tana zuwa nan a zancenta tanufi hanyar waje, tabar ILHAM a tsaye sororo, tama rasa mezatayi,

Halima tabi bayan Jalila, Nana kam gimtse dariyarta tayi ta kalli Ilham

“Don’t mind her please, muje ciki”

“Wallahi Nana badan ina jin kunyarki ba da na Dade da ketawa Jalila rashin mutunci, nizata kalla tace am looking psychologically abnormal”

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

“Yi hakuri, nidai bazan gaji da Baku hakuri ba, sannan kidena nuna mata kinji haushi

Yanzu dai bar batun Jalila ban labari meyake faruwa ne”

“Mtseww meyema be faru ba kwana hudu kenan banga yaya Jalal ba, idan naje part dinsa a kulle duk na damu, ko yau mukayi aure da Yaya Jalal na azabtu Nana”

“Calm down, Jalal ba karamin yaro bane, maybe yana tare da Yaya Jawwad, sannan tunda ba wata budurwar CE dashi ba ki kwantar da hankalinki, a hankali komai ze wuce, kinsman yanada gaddama”

“Wani irin hakurine banyiba, narasa meyake damunsa, kullum shine tension dina, kina batun bashi da budurwa to yanada ita kuma nasanta indai na haifu senasata tayi danasanin Sanin Jalal da tayi”

Dan zare ido Nana tayi

“Are you serious Jalal yanada budurwa, Dan Allah wace wannan”?

“Ai ba sonta yakeba ita take masa shishshigi, da zarginta nake yanzu na tabbatar da wacece, zan dau mataki na karshe, daze kawo karshen komai”

“Wani mataki kenan?”

Nana ta fada a tsorace

“Just watch, bari inkoma Gida anjima zanzo in tambayi Yaya Jawwad ko yasan Inda yake”

Tana gama fadin haka ta mike tayi waje da sauri

Jawwad be fushi ba yakoma gurin Jalal amma ya tarar ya rufe kofar palour Sa Jawwad yayi iya kokarinsa da rarrashi amma JALAL yaki budewa, gashi tun safiyar ranar beci komai ba haka Jawwad yagaji yakoma gida

Shikuwa Jalal yana ciki yanajin Jawwad yaki bude kofar tabbas Jalila tayi gaskiya yakamata ya bar Jawwad ya huta haka tsawon shekaru yana fama dashi da matsalolinsa

“Wai meyasa nake hakane, meyasa bazan yi rayuwa kaman sauran mutane ba”

Jiyayi zuciyarsa tana tafasa, kaman zata tsga kirjinsa ga wani nauyi da kansa yayi kaman ya fashe yai jifa da Wayne cups din kan karamin table din dakinsa, ya dinga jifa da duk abunda yaci karo da shi ya dinga jifa da abubuwa, da kwalaben giyar da ya shanye

Yakoma ya zauna idonsa suka kara Ja, ya runtse idonsa yanajin kansa yana juyawa

Mikewa yayi zumbur yabi takan fasassun kwalaben nan ya dauki keys din motarsa ya fito a sukwane, motarsa ya nufa ya Shiga ya fisgeta da gudu yayi waje

Su Jalila dake daf da bakin Layin suna tafe suna hira itada halima, sukaga motar Jalal ya dannota a guje, ga uban kura ya tayar ko gane motar ba ayi saboda gudu

“Tab anya Jalal kansa daya, wannan gudun yanzu inya bige wani fa?”  Jalila tayi maganar cike da mamakin wannan mahaukacin tukin na Jalal

“Hmm kema dai kya fada, shi kota ransa ma ba yayi”

“To Allah ya shirya”

“Ameen”

Haka sukaje inda zasuje suka dawo, daf da magariba ne Dan haka suna idar da salla suka Dora sanwar dare

Ana idar da sallar magariba Jawwad Yakoma gurin Jalal yaga ya bude kofar, da sauri ya shiga amma Jalal baya ciki, ya duba bedroom dinsa da toilet baya cikin, se tarin kwalaben giyarsa, ya sha wasu, ya zubarda wasu, ya farfasa wasu kwalaben yayi kaca² da dakin tundaga palour har bedroom

“Ya salam”

Jawwad ya furta ya dakko wayarsa ya fara kiran Jalal amma seyaji wayar tana ringing a kasan pillows akan gado

Cikin gidansu Jalal ya shiga a rude, ya tarar da mummy tana kallo a palour

“Mummy Dan Allah kokinsan inda Jalal yake?”

“Kamarya nasan Inda yake, ai kai yakamata in tambaya, baya part dinsa?”

“Baya can na duba, kamaar akwai abunda yake damunsa mummy tun jiya baya cikin nutsuwa,”

“Ni rabona da shi yau kusan kwana hudu”

Dan zaro ido Jawwad yayi

“Kwana hudu mummy, kuma baki nemeshiba yana part dinsa baya zuwa ko ina, yau kawai yafita kuma be gayaminba”

“To kai kenan daya daukeka da mahimmanci kana sanin inda yake, ni ko inda nake seya ga dama zezo, ina gani kuma Duk inda yaje ze dawo”

Jikin Jawwad ne yayi sanyi jin abinda mummy ta fada, 

Da sauri Ilham ta karaso palour da sauri

“Au wai kaima baka San inda yakeba, na dauka kana tare da shi”

Ilham tai maganar a firgice

“Eh amma ki kwantar da hankalinki zanje nemansa insha Allah ze dawo nasan ba nisa yayi ba, ni abinda yafi dagamin hankali dana je na tarar ya farfasa abubuwa a dakinsa”

Zare ido mummy tayi

“Haba dai?”

“Eh mummy shiyasa ma nazo na tambayeki, narasa meyake damunsa”

“Watakila giyar ya sha tagaya masa karya, amma muje bangaren nasa”

Tare suka tafi da mummy da Ilham suna zuwa suka tarar da mugun aika² da Jalal yayi duk wani abu me fashewa Jalal ya fasashi, hankalin mummy ya ta shi sosai

“Na shiga uku Jawwad meyasami Jalal hakane? Be taba irin wannan abunba fa”

Ita kanta Ilham abun yabata mamaki sekace dakin mahaukaci ya farfasa abubuwa

Jawwad ne cikin muryar rarrashi yafara magana

“Ki kwantar da hankalinki mummy, insha Allah ze dawo gida, amma yanzu bari in fita in dudduba inda yake zuwa na San tabbas akwai abunda yake damunsa”

Gyada kai mummy tayi tana share hawaye

  Bayan mummy da Ilham sun koma cikin gidane mummy se kuka take “Allah yasa yaron nan ba haukacewa yayi ba,”

“Haba mummy ya kike fadin hakane, insha Allah lafiyarsa kalau”

Ilham ta fada cike da kwarin gwiwa sannan ta nufi dakinta tana zuwa dakin ta kule tasaka masa key

Sannan ta kira mahaifiyarta

“Hello maami”

“Na am Ilham, yakike akwai labarine”

“Eh Mami, Jalal ne ya haukace fa”

“Kamar ya ya haukace ban gane me kike nufi ba,”

“To hauka mana kwana hudu yana kulle kansa a daki Jawwad kawai yake budewa, yau kuma shima din be bude masa ba, ya fita dazu da yamma, amma duk ya farfasa kayan dakinsa bakiga dakinba kamar mahaukaci”

“Ina baze yiwuba, bahaka nakeso ya kasance ba, ba hauka nakeso yayi ba, idan yayi hauka Dan gatan mahaukaci ze zama,

Sonake se yazo hannunmu mun wulakanta hadiza, mun tozarta ta, setayi kuka fiye da Wanda tayi a baya”

“Amma Mami ta Yaya kina gani kullum shirinmu rushewa yake, abinda ya kawoni gidan nan shekara da shekaru mun kasa samu”

“Amma kinsan duk laifinkine da rashin kokari Ilham ni narasa ma zaman me kikeyi abu yakici yaki cinyewa tsawon shekaru”

“Maami dukfa abinda kikasani inayi, amma kinsanshi muguwar gaddama CE dashi gashi jarababbe”

“Hakane amma zankoma gurin malamin nan inji mekuma zecemana”

“To Mami, yadda kukayi kya gayamin, amma da gani nake kawai inyi me gaba dayan nan ina fargabar aikinmu ya lalace”

“Har yanzu kina ganin alamar yana da budurwa ne?”

“Eh mana Mami shiyasa duk na tsorata fa”

“Ki kwantar da hankalinki babu abunda ze faru just focus”

“To mamina nagode, amma bakiga kukan da mummy tayiba”

“Ita tasani ni be dameniba”

Haka sukayi sallama da mamanta

Jalila ce ta fito harabar gidan da parker a hannunta taga Jawwad a sukwane ze bude motarsa, da sauri Jalila taje gurinsa

“Yaya lafiya ina Zaka haka naganka a firgice”

“Jalila Jalal ne banganiba gashi ya farfasa abubuwa a dakinsa bansan inda ya tafiba, shi zan tafi nema”

“To ai dazu da nafita raka halima naga fitarsa a mota kamar ze tashi sama, yana ta gudu a mota”

“Are u serious?”

“Of course naganshi dazu, amma Yaya Jawwad ka nutsu mana, duk ka tayar da hankalinka”

“Jalila, Jalal be taba hakaba bakiga dakinsaba kamar ba dakin Dan Adam ba ya fasa komai”

Gabanta ne yafadi “to ko in raka ka ?”

“No kizauna bari inje”

“To adawo lafiya Allah ya kiyaye, amma kayi driving a hankali”

Gyada mata kai yayi ya shige motar yajata da sauri.

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button