Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 35 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)


KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


                                                                     Fitowa tayi tana faman yarfar da ruwan alwalar dake hannunta,hijab da sallaya ta ɗauka a wardrobe, ta shimfiɗasu tare da kabbara sallah,bayan ta kammala tabar darduman anan saboda in an kira isha’e, hijab ɗin ta cire tare da ajiye shi saman gadon sai ta ɗauki Mayafinta, ta yafa shi akanta, 

Fitowa tayi kai tsaye ta wuce dining, a lokacin junaid ma yana a wurin tare da Haroon sai kanal Yusif duk suna zaune, yayin da Azmee ke faman ɗawainiyar Zuba masu abinci,

   Ƙarasawa tayi tare da cewa “Sannu da aiki Aunty Azmee,” 

Juyowa azmee tayi tare da kallonta tace”Yawwa mutuniyar sarkin kuka, Lamarinki naban mamaki kamar me iska,” 

   Sunnar da kai Sehrish tayi tana ɗan Murmushi kafin daga bisani ta gaishe da Kanal yusif da fara’arsa yace “Our Princess,duk yau ban saki a idona ba, Yakamata ace kina sakewa da ƴan uwanki sosai,” 

   Murmushi kawai Sehrish tayi tare da zama kusa da junaid suna facing ɗin kanal yusif da haroon ta hannun dama,

   Zuba mata abinci azmee ta soma yi a plate, junaid dake a gefenta yace”Da ace baki fito ba ko, da bazanci komai ba Allah,”

   Kafin sehrish tace wani abu haroon yayi saurin cewa “Saboda ciki ɗaya kuka fito ko? murmushi junaid yayi tare da cewa “Yaya Haroon yadda na ɗauƙi Sehrish ta wuce haka a wurina,” ta6e baki Haroon yayi yana kallonta, Harara Sehrish taɗan wurga masa tare da murguɗa masa baki, jinjina kansa yayi tare da cewa “An fa samu freedom of sitting the same table da Ƴa’ƴan masu gida dole ayi iya shege,

   Jin wannan maganar ta Haroon ta sanya junaid ɗaure fuska lokaci guda yace “Yaya haroon me kake nufi da hakan?

   Haroon yace “Abunda ranka yabaka”

  Dakatawa kanal yusif yayi daga cin abincin da yakeyi ya ɗan bubbuga plate ɗin dake gabansa da cokalin hannunsa ya bada sauti sannan ya aza idonsa akan na Haroon, Ganin irin kallon da kanal yusif ya jefa masa ne yasa shi, yin tsit ya shiga taitayinsa,

   Mayar da idonsa yayi kan Sehrish yace”Sister Yaushe ne zaki fara zuwa school ɗin? yayi hakan ne donya mantar da ita maganar haroon, ganin yarda tayi sanyi lokaci guda,

  daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa “Gobe ne insha Allah,”

  Kanal yusif yace “Masha Allah,A matsayina na yayan ki, akwai wani jan hankali da nakeso nayi maki, kin ga gobe zaki fara zuwa, kuma zaki fara haɗuwa da sababbin ƙawaye iri-iri,akwai good friends waɗanda zasu dunga ƙarfafa maki guiwa akan karatu ta hanyar baki shawarwari masu kyau,bayan su kuma akwai bad friends gur6atattu waɗanda majority ɗinsu ba karatu ya kaisu ba,Asarar kuɗin iyayensu kawai suke yi, basa karatu ƴan abi yarima asha kiɗane,babban ma tashin hankalin yanzu majority na irin waɗannan ƙawayen ƴan Lesbian ne,fitsararru marasa kunya waɗanda suka gagari iyayensu da malamansu, burinsu kawai su 6ata tarbiyyar wasu, bana so ki kasance ɗaya daga cikin irin waɗannan ko kusa, dayawa wasu suna kuskuren yin abota da irin waɗannan bad friends ɗin, sai suce ae basu suke aikatawa ba,sun manta cewa zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai,to koda gigin wasa bana so ko fira ta haɗaki da irin waɗan gur6atattun balle harku ƙulla Abota, Ina gargaɗin ki akan hakan ! And i want u to know that Ke yanzu kina ɗaya daga cikin Mutuncin gidan nan!! Kuma kinsan yarda sunan family ɗinmu ya karaɗe ko’ina, ba inda ba’asan Jinin SALAHUDDEEN HUSSEIN ba, don haka yazama dole ki kiyaye mutuncin family ɗinmu da kuma ƙimarsa, ina fata kina fahimtar abunda nake cewa”? Ya tambaya yana kallon sehrish wadda ta natsu tana sauraronsa cikin sauri tace “Ina fahimtar duk wani abu da kace yaya yusif, kuma insha Allah zan kiyaye faruwar hakan,kuma naji daɗi sosai harma baxan iya misaltawa ba,saboda na samu ɗan uwa nagari wanda yake mun nasiha akan na tsira da mutunci,babu wanda ya tunasar dani akan hakan sai kai, kuma insha Allah bazan ta6a baku kunya ba, zan kasance ɗaya daga cikin abun Alfaharin gidan nan,”

  taƙarasa maganar yayin da idonta suka ciko da kwalla, gaba ɗaya Azmee da Junaid sun kasa kunne suna sauraron maganar tasu, dukansu babu wanda baiji daɗin maganar Kanal yusif ba, Illa mutun ɗaya Wato Haroon wanda ke ta faman tur6une fuska yana faman hura hanci aransa yana cewa “Insha Allah ni kuma bazan taba barin ki ki xama abun alfaharin gidan nan ba, balle har ki samu matsayi acikinsa, saina san yarda zanyi in tarwatsa komai har inyi sanadiyar korarki acikin gidan nan,” ya faɗi yana kallon sehrish rai a6ace yana faman tura dambun nama abakinsa har yana shaƙewa,

   Kanal yusif kuwa murmushi ya saki sannan yaci gaba da cewa “Allah ya yarda Sehrish,Nima inason ki zama Abun alfaharin mu gaba ɗaya,” ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu ya ɗauki glass cup dake ɗauke da Lemu mai sanyi yakai bakinsa yana kur6a,

  ƙasa-ƙasa da murya junaid yayi tare da cewa “sehrish nima fa naso nayi maki nasiha akan zuwanki makaranta, amma kash sai gashi Yaya yousouf ya riga ni, amma duk da haka ban makara ba, don Allah sehrish karki canzamun koda kin fara zuwa school don nasan zaki ƙara wayewa sosai……….’

  Murmushi sehrish ta saki jin abunda junaid yace, kafin tace “Insha Allah junaid hakan baxata ta6a faruwa ba,mu aminnan juna ne zamu kasance atare ako wane hali na rayuwa, kaine abokin shawara na,”

  ajiyar zuciya junaid ya saki aransa yana ƙara samun kwanciyar hankali jin bayanan da sehrish tayi masa,

  wayar haroon ce dake acikin aljihunsa ta soma ringing taken waƙar nan da ake cewa “ɗan duniya hayaƙin taba,” jin ringing ɗin wayar yasa kanal yusif girgiza kai tare da cewa “Allah ya shirya ka,”

  Haroon yace “Ameen don son Annabi,” sannan yayi saurin tashi daga dining ɗin yakama hanyar fita daga falon yana zaro wayar daga aljihun wandonsa, ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnansa yana cewa “Shegen bisa ashe har ka isa hotel ɗin, ae ko gani nan zuwa Yanzun nan Allah yasa ka taho mana da harkar nan……….’ ya yi maganar da dariya a fuskarsa kafin yasa kai ya fuce,

  Bayan sun kammala dinner ɗin junaid suka wuce masallaci tare da kanal yousouf jin ana kiran isha’e,. 

   Itama Sehrish bayan ta kammala dinner ɗin tare da azmee suka kwashe kayan da sukayi amfani dasu izuwa kitchen, Sehrish ce ta wawwanke su tare da jerasu a ma’ajiyarsu, 

  Bayan ta fito suka ci karo da azmee tace ” Inaso naje na kwanta,pls kada ki bari bacci ya kwashe ki, idan Twins sun dawo ki tabbatar kin kai masu dinner ɗinsu, Shima Abbansu pls ki kaimasa nasan ƙila sai wurin 12 zasu shigo,.  

  Sehrish tace “To aunty azmee insha Allah baxanyi bacci ba, zan kai masu in sun dawo,”

   daga nan azmee ta wuce ɗakinta, itama sehrish bedroom ɗinta tashiga, sai da tafara shiga toilet ta kuskure bakinta, dama da alwalarta,

   Fitowa tayi ta ɗauki hijab ɗinta da ta ajiye saman gadonta, ta kabbara sallah

_________________________________________________

Tuni General ishaq ya iso gidan ya cika tab da mutane tare da jami’an sojoji da suka rakosa, su Aunty babba sai faman rawar kai akeyi miji ya iso gari, a lokacin hafsat har ta shirya kanta itama tsaf ta kimtsa cikin haɗaɗɗen cord lace Ash colour mai adon duwatsu,rigar mai dogon hannu sai skirt ba ƙaramin kyau kayan su kayi mata ba, gashi dama takware wurin iya kashe kallabi, tare da Mommyn nata da wasu daga cikin abokanan aunty babba da suka zo dana hafsat suke taimakawa wurin tarbar baƙi da abunsha dana ci,

   “Jahad ya Omar shiru kodai ya manta damu ne”? Hussana ta faɗi fuska tamkar zatayi kuka tana kallon jahad suna zaune dab da juna daga gefen gadon hafsat,

   “Hussana bana tunanin hakan, Ya Omar yana son mu sosai ni ina da tabbacin yana sane damu,kuma zaizo ne insha Allah,” acewar jahad

Hussana tace “Ni inajin tsoron a rabamu da ya Omar, wlh banso banso….’ 

  Kamar daga sama suka ji Muryar Aunty babba tace “Saboda ƙanin ubanki ne ko? ta faɗi ayayin da take shigowa, arazane suka miƙe tsaye su duka suna kallonta, su biyu suka shigo cikin ɗakin ita da wata hajiya, amma ita ta tsaya daga baya

   Kusa dasu taje sannan tasoma magana “Ko da gigin wasa bana so wata daga cikin ta leƙo da kanta daga cikin ɗakin nan ! Saboda Mijina ya dawo kuma banaso ya gan ku, ina fata kun gane?

  Cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa “Insha Allah aunty bazamu fito ba,”

   ta6e baki tayi sannan ta juya bayanta ta kalli matar da suka shigo tare tace “Hajjaju gafa yaran nan da nake faɗa baki, Omar yakawo min cikin gidana,”

   ƙarasa shigo wa ciki matar tayi jikinta na sanye da shadda gezna green colour tasha uban aiki a wuyan rigar, tayi ɗaurin ɗan kwalin ture kaga tsiya sannan ta yarfa gyalenta a kafaɗarta,

   Alokacin da matar ta ƙaraso Jahad taganta nan take gabanta yayi wani irin bugu zaro ido tayi tana kallonta saboda son tuna inda tasan fuskarta, 

  Hajjaju kuwa tana ganin su hussana da jahad farat ɗaya ta gane su, a ɗan razane ta dafe ƙirji tare da cewa “Kaiii !!!” taja maganar da ƙarfin tana kallonsu cikin mamaki da al’ajabin wannan Ikon Allahn,

  tuni aunty babba tagama ruɗewa ganin yadda hajjaju ta razana da ganinsu, da kuma yarda jahad ta firgita itama wannan alama ce dake nuni da sun san juna kenan ko yaya,

  Cike da mamaki Aunty babba tace “Wai meke faruwa ne hajiya rabi? kinsan su ne?

  Cikin sauri hajjaju tace “A’a bansan su ba, Kamar dae nata6a ganin mai kama dasu ne,”

   tayi maganar tare da ruƙe hannun Aunty babba taja ta, suka fuce daga ɗakin,

   Kallon jahad hussana tayi tare da cewa “Jahad wacece wannan matar? Naga kin razana da ganinta,”

   “Nima so nake na tuna inda nasanta,” Jahad ta faɗi tana faman cizon akaifar hannunta da takai abakinta,

  Hajjaju kuwa da taja Aunty babba suka fuce can suka nufa wurin kitchen suka tsaya, ga mutane sai faman shige da fuce suke,.

  “Dan Allah ki faɗamun gaskiya hajjaju raina na bani cewa kinsan yaran can ko? Aunty babba ta tambaya tana kallonta cike da son jin ƙarin bayani daga wurinta,

  Jinjina kai Hajjaju tayi tare da cewa “Yau naga ikon Allah, Lallai ne duk zakaran da Allah ya nufa da cara,to fa sai yayi ta, haƙiƙa nayi matuƙar mamakin yarda akai har Allah ya haɗa Omar da waɗannan yaran , kai kaga wani ikon Allah nan ! mai matuƙar ban mamaki da Al’ajabi?

  Hajjaju tayi maganar cikin nuna mamakinta,

Aunty babba kuwa cewa take yi “Hajjaju kin barni acikin duhu, wlh har kinsa hantar cikina ta kaɗa dan Allah kisanar dani me kika sani agame dasu?

  dariya hajjaJu tayi tare da tafa hannayenta tace “Ana bura’uba a lagos! yo ke laila da kike cewa zaki sa a zubar maki da waɗannan yaran don ki nisanta su da Omar, idan Kin toshe wannan hanyar to ita waccen ɗayar hanyar da ta ruga isa inda bakya so ya zakiyi da ita? 

   gaba ɗaya fa Aunty babba ta gama rikicewa da bayanin hajjaju, cikin tashin hankali tace “wai me kike nufi ne hajjau, kiyimun bayani mana yadda zan fahimta !!!

   ta faɗi tare da ɗan jan guntun tsoki, Murmushi hajjaju tasaki sannan tace “Ni baza kiji mutuwar sarki abakina ba!kawai abunda nakeso ki sani shine babu wanda ya isa ya hana ruwa gudu sai Allah! Bakin alƙalami dai ya ruga daya bushe, Amma fa waɗannan yaran da kike gani wlh ikon Allah ne su, tunda har Allah ya haɗasu da Omar aikuwa magana ta ƙare, Yakamata kisan abunyi,’

  Hajjaju tayi maganar tare da wuce wa ciki tabar Aunty babba tsaye abakin kitchen baki asake, lokaci guda taji ta ƙara tsanarsu hussana da jahad tabbas suna tattare da wani abu yaran, duk da bata fahimci inda maganar hajjaju ta dosa ba, 

  ranta ya gama 6aci tsoki ta buga tare da cewa “ta tsaya tayimun bayani amma ta tsaya yimun wasu sambatun banza dana wofi,ni duk tasa hankalina ya ƙara tashi, kuma wlh goben nan zansa a Kwashe mun su aje can azubar dasu tsakar daji, sai dae abunda bangane ba acikin maganar hajjaju wacece ɗayar hanyar da take nufi wadda ta isa inda banaso!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!? ta tambayi kanta sai dae kash babu amsa hakanan ta koma ciki tana faman sambatu aranta,

    Zumbur !! Jahad tayi tare da kallon husana tace “Wlh nasanta!! Nagane ta !! Itace matar da ta taimaka mana a asibiti har ta biya kuɗin gadon Ki husana, wlh itace matar da tasama ma SEHRISH aiki, hakan na nufin ta son inda sehrish take…..!!

  Cikin tsananin farin ciki jahad tayi maganar, hussana ma aɗan raxane tace “dagaske jahad itace tasama ma sehrish aiki? Ke nan itace kawai zata iya faɗa mana inda ƴar uwarmu take kenan,.  

   jahad tace “eh itace, nagane ta yanzu ya za’ayi muyi magana da ita, gashi aunty ta hanamu fita, amma ni dae inason magana da ita kodan saboda ta faɗa mana inda sehrish take,’ jahad tayi maganar fuskarta tamkar zatayi kuka,

   Cikin sanyin murya hussana tace “Jahad kada ma musa rai don nasan bazata faɗa mana ba, ita fa ƙawar Aunty ce, kuma kinsan muguwace idan halinsu ɗaya fa? Bazata ta6a faɗa mana ba, Ni tsorona ma kada ta faɗa ma wannan muguwar auntyn inda sehrish take, suna iya zuwa su cutar da ita, Allah yasa sehrish tana lafiya banaso wani abu yasame ta………'” tayi maganar cikin shessheƙar kuka,

   “Da gaskiyar hosana,Nima ina tunanin hakan Allah yasa karta faɗama auntyncan inda ƴar uwarmu take, amma dai ni inason naga matar na roƙeta akan ta faɗa mana inda sehrish take,yakamata musan inda take, wane hali take ciki, gashi yanzu sai mutuwa akeyi Ya Allah kasa sehrish tana araye har mu haɗu,” tayi maganar idonta cike tab da hawaye,

  daga bisani ta kalli hosana tace “ki zauna hosana kada ki fito bari ni naje nayi magana da matar na roƙe ta, ta faɗamun inda rishi take,”

  Hosana tace “toh,” sannan tasamu wuri ta zauna gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya,

  Cikin sanɗa jahad ta futo daga kopar ɗakin ta tsaya tana ɗan leƙa kanta, mutane tagani gasu nan sai faman zarya sukeyi acikin babban falon,

   A hankali ta miƙi hanya ta soma tafiya tana faman waige-waigen neman hajjaju, ta ɗanyi nisa a tafiyar ta ta, tajiyo magana daga bayanta ana cewa “Nasan cewa ni kike nema ko”?

Cikin sauri jahad ta juyo bayanta, hajjaju ce tsaye tana kallonta fuska ɗauke da murmushi,

Ajiyar zuciya jahad ta saki sannan itama ta mayar mata martanin murmushin tare da gaishe ta, hajjaju ta amsa mata da cewa “Nayi mamakin ganin ku, anan gidan ko ba’a faɗamun ba nasan cewa kunsha wahalar rayuwa don nasan Laila sarai muguwace bata da Imani,kuma tana sanar dani game daku a waya sai dai bansan cewa ku bane,”

Jinjina kai Jahad tayi tare da cewa “Munsha Wahala sosai tamkar ba zamu rayuwa ba,dan Allah ki faɗa mana ina Sehrish take? Munyi kewarta sosai, rabon mu da ita, tun da ta tafi aikin nan da kika sama mata,bayan wasu kwanaki hosana ta 6atar mana da wayar da muke amfani da ita wurin kiranta, shikenan rabuwarmu da ita……’ jahad ta ƙarasa maganar idonta cike tab da kwalla,

   ɗan shuru hajjaju tayi tana kallonta gwanin ban tausayi kafin tace “Kiyi haƙuri, amma bazan iya shaida a ina sehrish take ba nikaina,saboda nasaba hulɗa da yara ina sama musu aiki, bazan iya tuna a wane gari nakai sehrish ba, bazan iya tunawa ba……’

  Jin hakan yasa Jahad fashe wa da kuka mai cin rai, matsawa hajjaju ta ƙara yi gab da jahad tasanya hannunta tare da dafa kafaɗunta tace”kiyi haƙuri Jahad, ina mai matuƙar jin takaicin gaza taimaka maku akan halin da kuke ciki, haƙika kun ga rayuwa, amma ni abunda nakeson sani taya akai kuka haɗu da Omar? bayan naji labarin rasuwar tsohuwa ya gigita ni matuƙa, sannan naji labarin cewa ana zargin cewa kune kuka bata poison amma bansan ya ƙarshen labarin yake ba,’.  

  Cikin shessheƙar kuka jahad tace “bayan tsohuwa ta rasu, mutane suka ce mune muka kashe ta alhalin mu bamu da masaniya akan mutuwarta, shine aka kaimu police station, munsha Wahala sosai saboda bamu da sheda, ana shirye shiryen za’a miƙa case ɗinmu kotu, hussana tayi rashin lafiya shine dalilin dayasa ƴan sanda suka tafi da ita asibiti tare dani, Acan ne Allah ya haɗamu da yaya Omar shine ya kwace mu daga hannun police ɗin kuma ya kashe case ɗin gaba ɗaya……’ ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya,

  Murmushi hajjaju tasa ki tare da cewa “Allah sarki Omar mutumin kirki ne sosai, yana da tausayi inama ace tunfarko ba nan ya kawo ku ba, wlh da kun more rayuwarku,amma sai dai kash yayi kuskuren jefa rayuwarku cikin haɗari batare da sanin shi ba, Amma insha Allah Laila bazata ta6a cin nasara akanku ba,’

  Jinjina kai kawai Jahad ke yi, bayan sun ɗanyi shiru hajjaju tace “Muje ɗakin da kuke,ina son ganin ƴar uwarki danaji kin kirata da hussana, bazan manta ba itace a lokacin kwance saman medical bed ansa mata oxygen tana shaƙar numfashi cikin mawuyacin hali, Amma yanzu naganta taji sauƙi sosai jiki yayi kyau,’ hajjaju ta faɗi da ɗan murmushi a fuskarta yayin da suke nufar ɗakin hafsat atare,

   Suna shiga suka samu hussana atsaye sai faman zirga-zirga take yi burinta kawai jahad tadawo kusa da ita,

   Tsayawa tayi ganin sun shigo tare da matar, Murmushi hajjaju ta sakar ma hussana tare da ƙarasawa inda take ta rungumo ajikinta, tana ɗan bubbuga bayanta tace “nasan ke baki sanni ba,sabosa lokacin kina kwance rai hannun Allah, amma ni nasan ki saboda naganki a lokacin, naji daɗi sosai dana ganki cikin ƙoshin lafiya,

   Hajjaju ta ƙarasa maganar tare da janye hussana daga jikinta, ita dai hosana kallonta kawai take yi don batasan ta ba, mayar da idonta tayi kan jahad tace “ta faɗa maki inda sehrish take? 

  Jahad tace “a’a hosana, tace itama ta manta inda takaita aiki saboda ta saba kai yara aiki bazata iya tuna inda takai su ba,”

   Jin haka yasa Hosana fashewa da kuka tana cewa “..yanzu shikenan bazamu ƙara ganin sehrish ba….

  Hajjaju tace “Ki daina kuka hosana,wayace maki bazaku sake ganin sehrish ba? Ki daina wannan tunanin Insha Allah zaku haɗu da ƴar uwarku, abunda nakeso daku kawai ku cigaba da addu’a insha Allah zaku dace,”

  Jahad tace “kullum muna cikin yin addu’a,Kuma zamu cigaba da yi har illa masha Allah” 

    Murmushi hajjaju ta kuma yi sannan tace “Ni zan wuce,Ku kula da kan ku,Allah ya Albarkanci rayuwarku, yaci gaba da tsare ku aduk inda zaku kasance arayuwar nan,” 

  Suka amsa mata da “Amin,” sannan tasa kai ta fuce tana mai jin rashin daɗin gaza taimaka masu da tayi na ƙin faɗa masu inda ƴar uwarsu take, bayan ta son inda take,

  Komawa sukayi atare suka zauna jikinsu amace, Shin mai zai biyo baya?😥

Bayan wasu lokutta, duka baƙin da suka zo suka tafi gidan yayi tsit ba hayani, suna cikin wannan zaman na jimamin Ga samu ga rashi, na hajjaju da suka haɗu da ita yau, sun son itace kaɗai zata faɗa masu inda Sehrish take gashi itama tace bata sani ba, hakan ba ƙaramin kashe musu zuciya yayi ba, daker suka samu bacci ya ɗauke su,

_______________________

Fitowa daga wanka general ishaq yayi jikinsa sanye da gajeran wando, Closet ɗinsa ya nufa tare da sa hannu ya buɗe ya ɗauko jallabiya ya zumbula ajikin shi, Sarai yasan cewa tana ɗakin Amma sai yayi tamkar bai ganta ba, sai da ya kammala kimtsa kansa sannan yace “Ya Rashin Ji”? Ya tambaya yana kallon kansa acikin Mirror, mamaki ne ya kama aunty babba jin abunda yace, tana zaune daga gefen gadonsa tace “Nifa ce ba hafsat ba,” ta faɗi tana kallonsa

  Ishaq yace”Nasani ae, dake nake magana, duk rashin jin hafsat ae bata kai ki ba, kefa tamkar 6eran gida kike wurin 6arna da rashin ji,”

  ɗaure fuska tayi jin abunda yace rai a6ace tace “Alamu sun nuna cewa ba kayi kewata ba ko? shiyasa kake gayamin magana, ko da yake dama kai ae ba ka iya soyayya ba, Iya ruƙe bindiga kaɗae ka sani,” 

……juyowa Ishaq yayi yaɗan kalle ta tare da ta6e bakinsa yace “ban iya soyayya ba, amma gashi nan har kin haifi hafsat dani ko? Naga wannan ma ae wani sashe ne na soyayya,” 

    ya ƙarasa maganar tare da wuto wa ya haye saman gadonsa ya kwanta yana cewa “Idan kin tashi fita daga ɗakin kada ki manta, ki kashe mun hasken inaso nayi bacci,”

   a ƙule aunty babba ke kallon shi, can kuma ta miƙe fuuuuu ta nufi hanyar fita har takai bakin ƙopar ɗakin ta kuma tsaya tare da juyowa tana kallonsa, abun mamaki sai ta same shi yana ta faman tiƙar dariya,

 Bakomai yasa ta tsayawa ba face tsananin son kasancewa dashi da take yi, 

   dakatawa da dariyar yayi sannan yace “nifa ba korarki nayi ba, zaki iya dawowa kiyi zaman ki,” 

   murguɗa masa baki tayi aranta tace “shashasha dama nasani ae dole ka buƙace ni,”

  shi kuma aransa yace “Mayya, Jibi yarda take ta hau hawa kamar buhun harawa, duk an cinye mun abincin gidana,” 😂

 Kamar taji mi yace ta ɗan kallesa tare da jinjina kanta tace “bari na kawo maka Tea,” 

  “Ok i wll be waiting for u,” ya faɗi yana faman yin dariya ƙasa-ƙasa, general ishaq kenan tamkar Abbansu haka yake indai wurin iya zolaya ne,

******************************

A 6angaren sehrish kuwa, sam taƙi bari bacci ya ɗauke ta sai faman gyangyaɗi take yi tana zaune asaman kujerar dake gaban mirror burinta kawai su twins su dawo ko tasamu ta kai masu abincinsu, sune kawai suka rage mata takai mawa, domin kuwa ta jima da kaima Abbansu nashi tunda ya dawo,

Basu tashi dawo wa cikin gidan ba sai wuraren ƙarfe Sha biyu da rabi suka shigo suka shigo cikin falon kai tsaye ɗakinsu suka wuce, shaf shaf suka shiga rage kayan jikinsu, sai da ya rage daga su sai shorts ajikinsu, sannan suka shige toilet donyin wanka, sun jima aciki kafin daga bisa ni suka fito kowannansu ɗaure da towel a waist ɗinsa, closet ɗinsu suka buɗe jerin kayansu ne ajere komai iri ɗaya, kamar yadda suke tagwaye haka komai nasu yake iri ɗaya, kimtsawa su kayi cikin sleeping dress riga da wando milk colour,

faɗawa su kayi saman gadon Su tare da rungume junansu suka ci gaba da abunda suka saba, kamar injina haka suke sam basa gajiya,abun ya zamar masu jangwangwam,

 Kwankwasa ƙopar bedroom ɗinsu akayi, kusan sau uku basu ji ba, sai ana huɗun Jahan yace “Wai Uban wanene yake buga ma mutane ƙopa? Atunaninsa Sehrish ce tazo kawo masu dinner ɗinsu, 

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

 Amma sai yaji akasin hakan Muryar haroon yaji yace “Ubanka ne shege, zoka buɗe mun ƙopa in shigo,” Uban tsoki Jahan yasaki tare da  ƙara ƙanƙame Ayaan ajikinsa yana cewa “wlh bazan buɗe masa ƙopar ba, bansan uban me yakawo shi bedroom ɗinmu ba,”

   Ayaan yace “Amma sweet heart baka tunanin wani abu mai mahimmanci ya kawo shi”? ya faɗi yana faman lumshe idonsa akan Jahan,

   guntun tsoki jahan yaja tare da cewa “Wlh bazan buɗe masa ba, yazo yayi disturbing ɗinmu ne kawai,”

  duk abunda suke cewa a kunnan haroon dake tsaye abakin ƙopar ɗakin nasu, Jinjina kansa yayi yace “Yara kenan dani kuke magana,” hannunsa ya tura cikin aljihunsa tare da zaro wayarsa yaci gaba da daddanata na wani lokaci, daga bisani ya mayar da wayar cikin aljihunsa sannan ya ɗaga murya tare da cewa “tunda bazaku buɗe mun ƙopar ba, ku duba wayoyin ku acikin whatsapp ɗinku na turo maku wani saƙo mai mahimmanci,”

  Jin hakan yasa su dakatawa gaba ɗayansu cikin sauri jahan ya zura hannunsa asaman side drawer ya ɗauko wayarsa da hanzari ya miƙe zaune, whatsapp ɗinsa yashiga mamaki ne yakamasa ganin Numbar da yayi saving da yaya Haroon ya turo masa Video, cikin sauri yashiga chat ɗin tare da danna video ɗin ya buɗe………..lokaci guda jahan yayi wata irin Zabura sai gashi tsaye saman gadon hannunsa na kerma gaba ɗayama jikinsa, nan take kuma wata irin Zufa ta shiga wanko masa duk da sanyin A.c in dake ɗakin, Zazzaro idonsa yayi hankali a matuƙar tashe yace “AYAAN MUN SHIGA UKU!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!

 jin hakan yasa Ayaan tasowa shima ya miƙe tsaye yana cewa “jahan menene ya faru na ga duk ka razana,”

  Miƙa masa wayar yayi batare da yace komai ba, amsa Ayaan yayi yana duba video ɗin, porn video ɗinsu ne shida Jahad, gasunan kwance saman gado a ɗakin hotel ɗin da suka kama, tsantsar mamaki ne a fuskar Ayaaan a ruɗe yace”Jahan taya yaya haroon ya samu wannan video ɗin?

  “Nima shine abunda ban sani ba,” Jahan ya faɗi cikin tashin hankali,

    Muryar haroon ce ta dakatar dasu da cewa “Oya, azo abuɗe mun ƙopar,”

  A hanzare suka diro daga saman gadon tare da nufar ƙopar suka buɗe masa,

  shigowa yayi yana faman sakin shu’umin murmushi yace”Ƴan duniya, fararen Balbelu tun yaushe kuka fara wannan harkar bansani, ahhh gaskiya wannan anyi mun nisa

  har suna haɗa baki wurin cewa “yaya Haroon ba yin kan mu bane, dan Allah ka rufa mana asiri,”

atsiyace yabi su da wani irin kallo kafin yace “taya kuke tunanin zan iya rufa muku asiri hakanan siddin ragadan ku ci banza!!? nifa dama nasani duk kaf zuri’armu babu fasiƙai irin ƴa’ƴan mommynku, masu jaza mana bala’e acikin zuri’armu,’  yayi maganar fuska aɗaure yana kallonsu

   Jin wannan magana ta haroon ya sanya su jin wani irin ɗaci aransu,

Ci gaba da magana haroon yayi “kai nifa tunda Mommynku ta nuna ta tsane ni bataso na, Nima naji cewa bana ƙaunarku! bama wannan ba adalilin ku yasa abba yadaina so na kwata-kwata nazama abun ƙyara acikin gidan nan, don hak wannan babbar dama ce agare ni, Idan har na ɗaura wannan videon a Social media, Abban mu ya gani to tabbas  nan take zuciyarsa zata buga ya mutu! idan kuma babban yayan ku ya gani hohohoho ku kunsan mai zai faru, Idan Ammi tagani shikenan zata rabaku da mahaifinku ne na har Abada dama ba sonku take ba, tabbas wannan babbar dama ce agare ni !!! Ya faɗi da dariya a fuskarshi

  tuni Ayaan da Jahan sun zube agabansa saman guiwowinsu idonsu cike tab da hawaye, tabbas sunyi mamakin Kalaman haroon yadda ya nuna irin tsanar da yayi masu tamkar ba jininsu ba,

   cikin tsananin ƙunci suke cewa “Yaya Haroon pls ka rufa mana asiri dan Allah, kada kace za kayi amfani da wannan damar wurin tarwatsa farin cikin gidan nan, kaifa ɗan uwan mu na jinin mu dan Allah yaya haroon ka dubi girman Allah kada kayi mana haka,”

  Fashewa da dariya haroon yayi yana binsu da wani irin kallo na ƙasƙanci yace “Au haba? Ashe nifa jinin ku ne? Amma taya akai bamu kama? Ikon Allah sai yau kukasan da hakan? kaiiiii ! Ni saima yanzu na lura wai yau ƴa’ƴan Alexandra ne durkushe saman guiwowinsu agabana suna neman afwa hada matsar kwalla kodai mafarki nake yi ne?

  Yayi maganar tare da sa hannunsa yana murza idanunsa wai donya tabbatar ba mafarki yake yi ba,

   shiru su kayi gaba ɗaya jikinsu ya mutu sai uwar zufa dake wanko masu, ga jikinsu dake ta faman kerma yayin da idanunsu suka ciko tab da kwalla, gwanin ban tausayi

  Murya na Rawa Ayaan yace “Ka faɗi komai kake so za muyi maka donka rufa mana asiri,” 

    Haroon yace”yanzu naji magana, Anzo dai-dai wurin dana fi so,”

   ya faɗi tare da ƙara gyara tsayuwarsa yace “Abu biyu nake buƙata muddin kukayi mun hakan to shikenan zamu raba jaha daku,”.  

  Cikin sauri suka amsa masa da cewa “muna sauraronka,”

    wani irin bazawarin murmushi ya saki kafin yace “Nima fa kwararrene a irin wannan harkar taku! gashi kuma dama na jima ina sha’awarku musamman junaid, Kai yaron akwai sirrin kyau atattare dashi kuma daga gani zaiyi ni’ima sosai……..’

  a firgice jahan ya daka masa tsawa tare da cewa “Ya isa haka!! Komai za kayi ka tsaya a iya kan mu kawai, amma koda gigin wasa kada ka ƙara kiran Sunan junaid da waɗannan munanan kalaman naka! saboda ba zaka ta6a samun abunda kake so agame dashi………..’ cikin sauri Ayaan ya rufe ma jahan baki muryarsa cikin kuka yace “Jahan dan Allah kayi shiru, kada ka ƙara ja mana wani bala’en, ka bari muji da wanda muke ciki,” shiru jahan yayi yana faman sakin Huci ji yake tamkar ya tashi ya shaƙe wuyan Haroon, 

  Hannu haroon yasa abaki irin mamakin nan yace “Wow wai meyasa kowa yake ma junaid irin wannan zazzafar soyayyar har haka? Gaskiya anyi mun nisa kaina na cikin duhu, farin jinin junaid yayi yawa ina kishi da hakan,” ya faɗi yana dafe saitin zuciyarshi

.  Ayaan yace “Ba son junaid muke ba, Ƙaunarsa muke yi saboda shi ɗin jinin mu ne,”

   ta6e baki haroon yayi tare da ɗan jinjina kai yace “hmmmm ni wannan ba damuwata bace ba, abu biyu nake buƙata daga gare ku, inaso ku gamsar dani acikin daren nan, saboda inji irin naku salon, Sannan abu na biyu kuɗi nake so kimanin naira miliyan 50, in kun mun hakan zaku zauna lafiya,

Wani irin kallo suke bin shi dashi, Jahan yace “50m fa kace? Ina zamu same su? ka ruga da kasan iya salary ɗin mu, kuma ba tarawa muke yi ba, kashewa muke yi,”

   haroon yace “Wannan ba damuwa ta bace, in kun so there’s many way da zaku samu waɗannan kuɗin ! Yayan ku fa billionare ne! Mahaifiyarku ma billionaire ce, yadda take son ku ɗin nan, da zarar kun mata waya kunce kuna son Ƴan silalla zata turo maku,” 

  Murya a sanyaye Ayaan yace “mun ji zamu samu kuɗin mu baka amma dan Allah kada kace zaka aikata wannan abun damu, wlh bazamu iya ba, iya mu biyu ne kawai ba kowa muke bi ba, ka faɗi mashi jahan kada ya cutar da rayuwarmu bazamu iya jurewa ba……………………”

  bugun ƙopar da akayi ne ya hana Ayaan ƙarasa maganarsa, Cikin sauri Haroon yayi tsalle yashige bayan labule ya 6oye,

    tashi su kayi atare suna faman sa hannu suna goge hawayen dake fuskarsu, sannan jahan yayi ƙoƙarin cewa “Wanene?

  Sehrish dake tsaye ruƙe da tray a hannunta tace “Ni ce sehrish,”

   Ayaan yace “Shigo ciki,”  

  Tura ƙopar tayi da tray ɗin hannunta mai ɗauke da food wermers tare da kayan tea ta shiga ciki, tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki ganin yadda fuskokinsu sukayi Jawur, idanunsu sun Canza launi alamar sunsha kuka,

  Muryarta na rawa tace “Dama………….’ bata ƙarasa ba Jahan ya katse ta da cewa “Ki barshi kawai, bazamu iya cin komai ba, ki koma da kayan,”

   Shiru tayi aranta tana mai mamakin jin yadda Jahan ke mata magana cikin sanyin Murya, shi da kullum atsiwace yake mata magana,

   Jinjina kai tayi tare da yin juyi zata futa karaf idonta suka sauka kan ƙafafun haroon dake 6oye bayan labule, tana ganinsu tagane cewa ƙafafunsa ne kamar na shebur haka suke, tsananin tsoro da mamaki ne suka kamata daker ta iya fuce wa daga ɗakin,

  Kai har ta futa tana waiwayen ɗakin nasu, cikin mamaki take cewa “Meke faruwa ne? Naga fuskar Ayaan da jahan jawur alaman sunsha kuka, kuma menene yakai ƙafafun haroon ɗakin, hakan na nufin shine 6oye bayan labule? ko uban me yakaisa ɗakin hada su 6oyewa abayan labule, gaskiya akwai wani mummunan abu dake faruwa, Nashiga ukuna Allah yasa dae Haroon kada ya cutar dasu don nasan halinsa ba ƙaramin shaiɗani bane………..’ ta ƙarasa zancan Zucin nata ayayin da take saukowa down daga saman stairs ɗin,

  Kitchen ta shiga ta ajiye tray ɗin, sannan ta wuce bedroom ɗinta cike da zullumin abunda tagani, 

A daren ranar haroon sai da ya tabbatar ya wulaƙantar da rayuwar Ayaan da jahan domin kuwa har sai da Ayaan Ya sume sannan ya ƙyalesu ya fuce yana ƙara jaddada masu maganar kuɗinsa, bayan ya fita jahan ya fashe da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali yana jijjiga jikin Ayaan dake sume aƙasa 😭

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

Back to top button