Novel Document

Ni Dake Complete Novel Document

Ni Dake Complete Novel Document By Amnah El Yaqoub

Description/Story:

Ni Dake Complete Novel Document

Written By Amnah El Yaqoub

 

Description

Tafiya take cikin nutsuwa Kamar de yanda tasaba, baqar abayace a jikinta,duk da rigar tanada Dan fadi hakan bai hana surar jikinta baiyanaba, yayinda fuskarta take sanye da niqab shima baqi, idan kaganta dole zakayi tunanin wata balarabiya ce yar qasar saudia, kasancewar suma haka suke tasu shigar.

Agogon dake daure ahannunta ta kalla Dan nera dari hudu, hannun nata na kalla fari tas dashi tareda dogayan yatsun hannunta zara zara.

Tana gama ganin _time_ cikin faduwar gaba ta furta “subhanallah” sannan taqara sauri ganin takusa makara.

Zaune suke akan Mota Kamar kullum, susu uku ne, kullum tazo wucewa sai sunyi mata magana ta share su, idan zasu kirata sau dari haka take sharesu sau dari, yi take Kamar ma da qasa suke magana ba itaba.

Daya daga cikinsu ne yace:

” _Dude_ ga yarinyar nanfa yar renin hankali tana isowa”

Wanda aka kira da _Dude_ yace “kuna bani mamaki sau dayawa wallahi, saide magana, bazaku iya zuwa gareta gaba da gaba kuyi mata abinda kukaga dama ba”

Na ukun ne yace “a a fa Anwar, ni gaskiya kwarjini yarinyar takemin, bayan hakama bamusan ita din ko ‘yar wacece ba”

“yar wacece kuwa Data wuce yar gidan Malam Shehu, takalmin kafarta kadai zaka kallah shine zai tabbatar maka dacewa talauci yasamu matsugunni agidan iyayenta”

Gaba dayansu suka kwashe da daria, tareda tafawa, daya daga cikinsu yace ” _oh boyyyyy_ ” irin na tantiran yan iskan nan.

Adede lokacin tazo saitinsu zata wuce.

Anwar yaduro daga kan motar dayake kai yace _let_ _me_ kuga yanda Zan mata yau, yau saina yaye wannan abin _face_ din nata, munafukai ne irin wannan yaran, su suna qare maka kallo, amma kai bakada damar ganinsu.

Zuciyarta daya tana tafiya, sai ganin mutum tayi agabanta Kamar wadda aka jefoshi, kadan yarage qirjinsu yahadu.

Masifar tsoro ne da ita, lokaci daya gabanta ya tsananta faduwa, idanunta yayi wuri-wuri, cikin zazzaqar muryarta tace “A’uzubillahi…

Idanunta yakallah farare kar , qwayar cikin idon datake baqa saita qara qawata cikin idanun nata.

Shida kansa saida yahango tsakanin tsoro a ‘idonta.

” keni shaidan ne dazaki nemi tsari dani”

“to waye zaiyi abinda kayi yanzu inba shaidan ba”?

Nunaata yayi da hannu yace “Karki kuskura kisake dangantani da shaidan, inba hakaba wallahi sai nayi miki abinda bazaki taba mantawa dani ba har abada”

Gabanta ne yaci gaba da faduwa jin wannan furucin nasa, Ahankali tace “Allah yahdika… Kafin takarasa ya fizgi hannunta yace” Wato ke ina magana kina maidamin ko”?

Cikin sauri ta fizge hannun ta, ta matsa gefensa zata wuce, yasake shan gabanta yakai hannunsa zai yaye mata niqab dinta

Abinka da mutum Mai hakuri, kuma aka qureshi aka kaishi bango, itama hakance ta kasance awajanta, batayi wata wataba tadaga hannu ta sharara masa kyakykyawan mari 😳🙆🏻

Cikin tsananin mamakinta yadora hannu akumatunsa, lokaci daya Idanunsa yakada yayi jajir, yau mace ce ta mareshi, macenma wannan qanqanuwar, wadda daga gani ba ‘yar kowan kowa bace face ‘yar baqaqen talakawa.

Cikin fishi tace “angaya maka ni ‘yar isakace, ko angayamaka ni irin shashakan yanmatan dakuke hulda dasu ne? To Zan iyayin komai domin kare mutuncin kaina kagane? Tana fadar haka ta matsa gefensa ta wuce cikin sauri tana qarasawa bakin tete domin tare _keke napep_ zuwa makaranta.

Gaba daya jikinta ‘bari yake, hatta hannunta datayi marin dashi karkarwa yake, Innalillah.. Meyakaita marin namiji, namijin ma marar mutunci irin wannan datake masa kallan d’an tasha.

Gaba daya a tsorace take, domin kuwa idan Mota tayi qwaqwqwarar _Hon_ zata iya zurawa aguje🤣

Tana wannan tunanin me adedeta ya tsaya agabanta.

“Hajiya ina zaki je”?

Cikin in-ina tace B.. B.. BUK zaka kaine _new site_

Yace”hau Muje”

Cikin sauri tashige tazauna tana sakin ajiyar zuciya, shi kansa me adedetan saida yajuyo ya kalleta cike da mamaki.

 

** *** **

Daria suke masa gaba dayansu, daya daga cikinsu yasaka hannu abakinsa yasaki fito.

Yace “aisai kadawo, dama mena fadama? Kullum kaine kake cika mana baki akan yarinyar nan, yanzu gashi ka karbi rabonka, yarinya qarama ta wanka ma mari, kuma katsaya agabanta kakasa tabuka komai sai riqe kumatu🤣

Tsaki nabeel yaja yace” Dan Allah jazy kadena wannan maganar kaifa dama can nalura tsoron yarinyar kake, yadubi Anwar yace gaye kawai kabasar kazo mu wuce, Allah yasomu babu yara, da tuni ta watsar mana da _class_ ”

Cikin jin zafi yace” nabasar fa kace nabeel, ni wannan yarinyar zata mara? Tana nufin taci banza kenan? Inaaa _Impossible_

Motarsa yashiga yajata atsiyace yabar wajan, yabude _friends_ din nasa da qura

Jazy ya kalli nabeel yace “gaskiya ran gayen nan yabaci dayawa”

Nabeel yace “ai dole, kaikuwa mari fa”

“gaskiya ina tausayin yarinyar nan, _because of_ bazaidau qaramin mataki akanta ba,”

Kafada nabeel yad’aga tare fadin 🤷🏻‍♂ ” _Whatever_ ”

 

*** *** ***

Dede gate din yasauketa ta bashi kudinsa tashige cikin sauri.

kai tsaye _department_ dinsu ta nufa, saide tana zuwa taga _already_ _lacturer_ din Yarufe kofar, dama haka dabi’arsa take, muddin yarigaka shiga da minti biyar to zai rufe kofar ne saide kayi hakuri.

Agogon hannunta ta kallah ta dafe kanta🤦🏻‍♀ 11:16 shadaya yakamata ace tazo, yanzu gashi taqara har minti goma sha shida.

Wasu yanmata ne atsaye abakin kofar hall din sunkai su biyar, daya daga cikinsu tace “wallahi malamin nan baisan darajar mata ba, inba hakaba yabarmu atsaye, anbashi hakuri Yaqi kulamu”

Watama tace”ke bashida aure fa, shiyasa yake rashin mutunci ”

(kunsan yanmata _most_ _of_ _them_ dinsu dazaran malami yahanasu shiga hall yanzu zakuji sun fara cewa baisan darajar mace ba 🤣🤣🤣 musanman malamai marasa aure)

Wata kuma taci uban gayu tadaga murya yanda zai iya juyosu tace” Malam innallaha ma’assabirin ”

Duk yana jinsu ya sharesu.

Itama ganin sun cikata da surutu bama tajin abinda yake fada yasa tajuya takoma daya bangaren ta tsaya ajikin _window_ tana saurarensa.

Shikuwa yana ganin ta yayi mata alama da hannu akan tashigo hall din, saboda daga ganinta zakasan tafisu nutsuwa da sanin darajar karatu.

Aikuwa nan kallo ya koma sama, dalibai aka fara qus-qus.

duk yana ganinsu kawai ya girgiza kai, shide yasan bata wata manufa yayi hakan ba, saboda yarinyar fuskarta ma arufe take bare ace kyanta yagani ko kuma wata sura ta jikinta yasa yabarta tashigo.

Haka yaci gaba da bayani har lokaci yacika sannan yafita.

Qawarta ce taqaraso wajanta tace ” _Beauty_ meyasa bakizo da wuri ba kinsan halin malamin nan, koda yake danma naga ke yau Allah yadoraki akansa”

Ajiyar zuciya tasaki “besty wallahi matsala aka samu ahanya, _that’s_ _why_ nazo _late_ ,”

“Ok to kinga tashi Muje musai wani abun muci sai nayi miki bayanin Inda yayi mana bakya nan”

Tace “to besty na Muje”

Lemo suka siyo Limca Dan nera dari🤣 suka samu waje suka zauna sunasha dayar tanayi mata bayani.

Wayarta ce tayi qara qirar VIVO 🤣🤣Fara yar qarama, tana ganin me kiran taja tsaki tareda _rejecting_ _call_ din.

“Beauty kina bani mamaki, meyasa bazaki bashi dama bane shima adama dashi?

Cikin _serious_ _voice_ tace Nasrin, Dan Allah kidenamin maganar wannan mutumin, wallahi bana sansa, ko ganinsa bansan yi”

Murmushi tayi tace” toshikkenan qawata, wai kenan yar jami’ah ko? Taqarasa maganar cikin zolaya 😉”

Tace” uhm ina abin yake besty, _level_ 1 din? ”

Dukkaninsu suka saki Murmushi har time din shigar wani malamin yayi suka koma _hall_

 

*** *** ***

Angaya maka ni ‘yar isakace, ko angayamaka ni irin shashakan yanmatan dakuke hulda dasu ne? To Zan iyayin komai domin kare mutuncin kaina kagane_ ?

Wani irin wawan tsaki yasaki tareda fatali da kwalbar lemon dake gabansa, _glass cup_ din dake kusa da lemon yafadi aqasan _tiles_ din falon ya tarwatse.

Maganganunta ne suke masa yawo a qwaqwalwarsa, cikin masifa yace “Baki isaba!!!!

Qaran cup din daya fashe ne yadauki hankalinta zuwa falon, cikin takunsu na manyan mata Wanda suka jiqu da naira ta qaraso wajansa tace” _my_ _son_ , kaida waye “?

Huci yake shi kadai batare daya bata amsaba.

Ajiyar zuciya tasauke tareda zama akan kujera itama sannan tace” nasan cewa kaida wata yarinyar ne, Anwar wai sai yaushe ne zaka nutsu kayi hankali Dan Allah? Karka Manta fa mace ce ta haifeka, a kullum bakada Burin daya wuce kaci zarafin mata, sannan matan ma Wanda basujiba basu ganiba, ‘ya’ yan talakawa, karka Manta matsayin mahaifinka agarin nan, abu daya zakayi yataba masa siyasar sa, koba haka bama duk abinda kayiwa ‘yar wani shi za’ ayiwa taka, koma fin haka,sannan…..

“Sadaqallahul Azeem”

Dasauri tajuya takai kallanta gareshi, ta sunkuyar da kanta batare Data cigaba da fadan datake yiwa yaron ba.

Yace “Hajiya kina kokari wajan yiwa Anwar nasiha, bakya gajia abin har mamaki yake bani,” yadubi Anwar yaci gaba da fadin ” _my_ _son_ , kayi abinda ranka yakeso kaji ko? Gwamnati ahannun mu take, kowa yayi laifi katakashi,”

Tace “amma alhaji…”

” _but_ _what_ hajiya? Kinga ni yanzu Zan wuce _Kuwait_ , akwai _meeting_ din da zamuyi gobe da yaron uban gidanmu, ya kalli dansa yace _my_ _son_ , jeka shirya mutafi tare, sai kasha iska kafin nagama abinda yakaimu, inkuma wata qasar kakesan wucewa saika wuce tacan.

Cikin shagwaba yace ” _dad_ gaskiya babu Inda zani, akwai _birthday_ _friend_ dinmu da zamuyi goben.

Cikin rashin damuwa yace” toshikkenan _my_ _son_ kaje dakina akwai kudi a _bedside_ _drower_ kadauki abinda yama.

Tsalle yayi gami da rungume uban yayi cikin dakin dagudu.

Girgiza kai hajiya tayi tace “to alhaji kwana nawa zakuyi”?

Yace “2 to 3 _day’s_ insha Allah”

“to Allah yadawo daku lafiya Alhaji”

 

** *** **

 

Hudu da kwata suka futo daga _lacture_ dasuka shiga, ta dubi aminiyar tata tace “besty saimun hadu gobe, yunwa nakeji wallahi Ga bamuyi sallah ba,”

Tace “Beauty nima nagaji wallahi, saimun yi waya kawai”

Daganan sukai sallama kowa yashiga adedeta yawuce Gida.

Saida suka dau hanyar Gida, abinda yafaru dasafe yafado mata arai.

Tsoro ne yakamata, cikin ranta tace “Allah ka rufamin Asiri kasa wad’ancan sakarkarun basa nan”

Tana cikin wannan zulumin aka sauketa abakin titin, ta bashi kudinsa sannan tayi cikin layin nasu, wannan tafiyar datake Ahankali denawa tayi, taware qafarta tana zuba uban sauri🤣, hartazo wajan dasuka tareta da safe, amma tsabar tsoro tama kasa kallan wajan, yayinda gabanta yaketa lugudan faduwa, sai tafiya take fiya-fiya hartazo wajan dayake da yalwar mutane.

“laaaa Affan kaga wasu baqaqen motoci masu kyau, daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida, bakwai, takwas, tara… Laaa affan wallahi guda goma ne”

Wanda aka kira da affan ne yakalli motocin nan take ya nuna guda daya yace “nida wannan”

Shima dayan yace “wallahi baka isaba na rigaka, wannan tawace🤣🤣🤣”

Ko juyowa batayi ta kalli wadannan yaran dasuke fira abayan taba bare ta kalli motocin dasuke magana akansu, fatan ta daya shine taganta agida ta rama sallar datake kanta.

Wani me mashin ne yashawo kwanar aguje, baisan tana gabansa ba,gadan gadan yayi kanta, ita kuma batajiba saboda hankalinta gaba daya yayi Gida.

Kasancewar kowa yasanta a unguwar, kuma ansan cewa itace ma’abociyar wannan shigar shiyasa wadannan yaran na bayanta suka dora hannu aka, cikin kaduwa da qara suka hada baki wajan fadin ” YAYA BABY bayanki!!!” 🙆🏻‍♂

“bayanki yaya Baby!!!” 🙆🏻‍♂

Lokaci daya me _machine_ din yataka wani wawan birki, jikake quuuuu.

Adede lokacin daya daga cikin _Escort_ dinsa yabude masa kofa yafuto, yayi bala’in kyau cikin farin yadi, had’eda babbar riga, yanda yaci manyan kaya zaka iya rantsewa wani Babban magidancin ne, fari ne tas, kallo daya zaka masa kashaida cewa shidin cikakken bafulatani ne, zagayaiyen sajen daya bari a fuskar sa, shine zaisa dayawa daga cikin mutane zasuyi masa kallan wani balarabe ne.

Duk abinda yake faruwa akan idonsa.

Duk yanda taso kaucewa saida mashin din yabigeta kad’an, tai wani irin juyi, niqab dinta yadage har zuwa wajan hancinta.

Tace “Wayyo” saigata da’bar aqasa🤣🤣

_Pink_ _lips_ dinta sirara masu kyau yabi da kallo, yanda ta motsa bakinta tace ” _wayyo_ ” dinnan shine yafi komai daukar hankalin sa, cikin ransa yafurta kalmar ” _Cutie_ ”

Dama a _Nigerian_ yankin Arewa akwai irin wadannan yaran masu kama da jinsin larabawa?

Duk da baiga _face_ dinta dukaba yasan cewa Allah yayiwa yarinyar baiwar kyau.

Ita kuwa tashi tayi tana karkade jikinta, me mashin din yace “Qanwata Dan Allah kiyi hakuri, wallahi ban kula bane, kiyi hakuri dan Allah”

Dagowa tayi daga kad’e jikin nata tace masa “babu komai wallahi, ai banji ciwoba,”

Tana fadar haka taci gaba da tafiya,ance juma’ar dazatai kyau tun daga laraba ake ganeta, ita kam tasan cewa yau bata futo a sa’ah ba🤣😃

Me mashin yafara buga abinsa zai tafi, shikuma yana tsaye yana kallan ikon Allah, kakade mutum ba dabba ba, amma kabarshi yatafi, ai kamata yayi ka tsugunna har qasa kabata hakuri😳😳,, inta baka damar tafiya shikkenan saika tafi, Dan haka cikin sauri yafara cewa “ka dakata!”

Amma inaaaaa, baijishi ba,binsa yafara yi yasake cewa “nace ka dakata”, amma tuni me mashin yayi gaba abinsa, to dama maganar ce gata Ga yanda take, ba’a qwala da karfi yanda za’a jiba, mukuwa mun saba sai an bude mana murya😂🤣🤣

Daya daga cikin _guard_ dinsa ne yabiyoshi “yallabai kana san magana dashi ne abishi adauko shi ?”

Yace ” _no_ ” tare dakai dubansa inda yarinyar take, ‘bat ya nemeta yarasa babu ita babu alamar ta🤗

Cikin ransa yake cewa “wacce irin yarinya ce wannan me hakuri? Ankadeki amma ko ajikinki kitashi kici gaba da tafiya, yanzu Data tsaya aida sunje _hospital_ aqalla ko lafiyarta ne aduba😱, amma tayi qanqanta da daukar wannan _Prager_ din tayi qarama dayawa

“Yallabai ga lungun dazamu shiga can, anan gidan yake”

Juyowa yayi ya kalli Wanda yayi masa maganar sannan ya kalli lungun.

“wai kana nufin wannan wajan zamu shiga?”

“Sai hakuri yallabai, anan gidan yake,”

Babbar rigarsa yafara tattarewa Kamar Wanda zai tsallaka ruwa 🤣🤣sannan yace ” _Ok_ ” yayi gaba sukuma suka take masa baya, sai zare ido suke suna kalle-kalle.

Kofar gidan dasuka nufa acike take da mutane kowa yana zaune a tabarma anyi shiru.

Suna zuwa yacire takalminsa fari qirar italy,sannan yafara bawa mutanan wajan hannu suna gaisawa daya bayan daya.

Matsawa yayi wajan wani dattijo suka sake gaisawa cikin girmamawa yace “yaya qarin hakurin mu?”

Mutumin yace “hakuri sai ma’aiki,”

“Allah yaji qanta, Allah yasa tahuta”

Yace “Amin Amin, MUHAMMADU ne yaron wajan Alhaji KABEER ko?

Saida yayi qasa da kansa sannan yace” eh nine baba ”

Mutumin yace” ikon Allah, kaduba kaga yanda Muhammadu yagirma yayi hankali, Muhammadu ashe zamuga wannan ranar? Kawai saiya fashe da kuka yaci gaba da cewa Allah yajiqan Alhaji Kabiru, Allah yakai haske kabarinsa, ubangiji Allah yasa can tafi nan, oh, mutum Mai taimakon takalawa, Mai basu gudunmawa…

Mutanan wajan ne suka fara bashi hakuri, sannan yagoge hawayen idonsa yace “nagode sosai Muhammadu”

Shima Ahankali yace “babu komai ai baba, yiwa kaine, yasa hannu a aljihun Babbar rigarsa yadauko kudi masu yawa ya ajiye agaban mutumin” Ga wannan ayi mata sadaka, Allah yaji qanta”

Atake duk wajan suka amsa da Ameen.

Yayi musu sallama yatafi, muqarrabansa na take masa baya, kana ganinsa kaida kanka zaka tabbatarda cewa shidin wani me fad’a ajin ne a wannan qasar, suna zuwa wajan dasukai Parking motocinsu aka bude masa domin yashiga, kafin yashiga saida yasake kallan wajan da aka kad’eta kozai sake ganinta, amma shiru kakeji.

Wani daga cikinsu ne yalura dashi, cikin sauri ya qaraso gamida rissinawa yace “yallabai ko akwai damuwa ne?”

Bece masa komai ba, kawai girgiza kansa yayi alamar babu, sannan yashiga suka rufe, sun fara tafiyama amma sai waiwayen wajan yake.

Sunyi nisa sosai Ahanya, driver yajuyo yace” yallabai ina muka nufa? ”

” kashiga wancan layin, akwai Wanda nakesan gani ”

Umarninsa _driver_ yabi, suna zuwa wani kofar Gida yace” ya’isa”

Wasu samari ne guda biyu azaune a kofar gidan, gaba daya suka maida hankalin su kacokam akan motocin dasuka tsaya.

Ana bude masa yafuto, Dasauri daya daga cikin samarin nan yamiqe tsaye yace “wanake gani Kamar MK”

Shima cikin mamaki yace “yasir kaine ka koma haka?nayi tunanin kun tashi daga gidan nan ashe har yanzu kuna nan? _But_ yasir meyake faruwa hak…

Dasauri yasir yakatse shi “labarin yanada tsawo, mushiga ciki mana, na barka a tsaye”

“No_ yasir, ina kan hanya ne, _latter_ zamu samu lokaci mu tattauna, dama kawai ka fadomin ne naji ina san ganinka, wanne aiki kakeyi yanzu?

Kansa ya girgiza” babu aiki ”

” _Ok to Ga _Email_ dina nan, katuramin ducument dinka gaba daya, zan nemeka insha Allah ”

Yadauko kudi _bundle_ daya ya bashi” kabawa su baba, kai kuma zaka jini ”

Godia yasir yafara zuba masa,, sannan sukai _Exchanging number_

Daga haka sukai sallama, yana shiga motar ya lumshe idonsa, dole ne yanemi _pracitamol_ _because_ _of_ yayi surutu dayawa kansa ciwo yake.

Wayarsa ce tayi qara, batare daya bude idonsa ba yadaga kiran saboda _ringing_ dinta daban yake dana kowa.

“Barka da wannan lokaci ummi”

Daga d’aya bangaren tace “Zakazo Gida ne kafin katafi?”

“No_ Ummi _Already_ akwai jirgin dayake jirana, ina ganin zan wuce _Kuwait_ , akwai mutanan danake son ganawa dasu gobe, _so_ bazan samu damar Shigowa Abuja ba.”

“To saika dawo, _take_ _care of your self_”

Bece maata komai ba yakashe wayar

 

***********

 

Tana shiga Gida tayi _ball_ da butar datake gabanta, umma datake zaune tana wanke kwanuka tace “kanki daya kuwa Baby?”

Umma wallahi banganiba , bnda nutsuwa ne, ka’deni akai da mashin.

Kallanta tayi dakyau tace “kina ta shegen tunanin naki har aka bigeki ko, yamiki kyau, saikije kicire kayan kuje _chemist_ abaki magani”

Awajan tacire niqab din nata, tacire dankwalin abayar datayi _rolling_ sannan tazare abayar ma gaaba dayanta.

Qananan kayane a jikinta, wandon _three_ _quater_ ne yawuce gwiwarta da kadan, amma ya kamata, saida riga marar hannu Kamar _vest_

Surar jikinta ce ta bayyana, fara ce sosai, me matuqar kyau, _long_ _face_ gareta, tanada madedetan _breast_ yayinda _hips_ dinta yacika wondon jikinta taf, cikin ta ashafe Kamar batacin komai.

Harara umma tasaki tace “amma yau kinyi gamo ko?”

Cikin sigar shagwaba tace “umma Allah nagaji, kuma jikina ciwo yake”

Cikin tsawa tace “Baby wallahi zanci ubanki kinji ko, kwashe kayanki kibar kaina, kin wani baza gashi saikace mahaukaciya”

Tsugunnawa tayi tadora kanta akan cinyar uwar tace to umma dauremin”

Girgiza kai tayi sannan ta kama dogon gashinta tadaure mata, tace jeki abincinki yana daki, karna qara Ga kin zauna haka atsakar gidannan nafada miki”

Batace komai ba ta wuce dakinsu.

Tana shiga tahada Ruwan zafi tayi wanka, tarama sallolin dake kanta sannan taci abinci ta kwanta, saida tajira akai sallar isha’i sannan ta kwanta,batare dataje chemist din da umma tace tajeba.

Wani yaro ne yashigo dakin yace “yaya Baby kince zakibaan wayarki idan kindawo daga school”

Tace “mus’ab banda chargi, jeka Dan Allah kabarni nahuta kaji ko”

Yaron nafita, bacci yadauketa.

Washe gari karfe takwas daidai tabar Gida, sunada lacture takwas da rabi, bayan sun gaisa da babanta yabata kudin Mota tatafi, lafiya kalau yau ta wuce babu su Anwar a hanyar, hartaje school lafiya.

Sosai ta fahimci karatun nasu nayau saboda hankalin ta akwance yake, basu tashi da wuri ba yau sai karfe biyar na yamma, minti goma sha biyar ta dauka ahanya aka sauketa adede layin unguwarsu, cikin nutsuwa take tafiya Kamar yanda tasaba.

Ruf taji anrufe mata ido, andagata sama.

Ihu tafara tana nemaan temako amma babu Wanda yaji, asalima daga fuskar ta har hancinta zuwa bakinta arufe suke.

Harbe Harbe take da qafafunta tanaso takwace amma takasa, saida suka koma can gefe sannan suka direta.

Yaye mata fuska sukai, anan ta ganshi, gabanta ne yafadi, lokaci daya jikinta yafara rawa, tace “Dan Allah kuyi hakuri, karku cutar Dani, Dan Allah Dan annabi karku lalatamin rayuwa”

Daria sukasa gaba dayansu.

Yace “ke har kin isa ki mareni ki zauna kalau?” kina tunanin kinci banza ne? To yau Zan nuna miki niba tsaranki bane, zan takaki inga uban daya tsaya miki.

Wata kwalba ya nuna mata yace “kinga wannan? To _acid_ ne aciki, zan lalata miki fuskar dakike taqama da ita har kike marin maza akanta,”

Gabanta ne yayi mugun faduwa ” _acid_ ”

Tace “na shiga uku, Dan Allah kayi hakuri, wallahi tallahi natuba bazan sake ba,”

“bakince zaki iya yin komai saboda ki kare mutuncin kanki ba? To ai Ga wajan nan kiyi nagani _NI DAKE…d’an halak kafasa_

Yadubi abokansa biyu yace “nabeel ku riqemin ita”

Lokaci daya suka kamata tana fiffizgewa, haka suka riqeta kowa yakama hannunta daya, shikuma yabude murfin kwalbar yanufota dashi.

Ganin zai lalata mata fuska tanaji tana gani yasa tasaka kafarta tabige kwalbar.

Ruwan ciki yazube aqasa, take qasar wajan tafara kumfa.

Yace “iyeeeee nizaki yiwa iskanci? Tass ya wanka mata mari, yajuya zuwa wajan motar sa Dasauri, yadawo da Shaltos a hannunsa.

Cikin tsawa yace” kuriqemin ita nace ”

Sake riqeta sukai, tanata kawar da fuskar ta, amma haka ya matso ya gwale mata cikin idonta.

Haqorinta tasa tana kawo masa cizo amma haka yacire murfin Shaltos din yafesa mata a idonta, lokaci daya ganinta ganinta ya dauke.

Yayinda tasaki wata irin qara tafadi awajan

Cikin tsoro jazy yace “gaye karfa Muje tamutu, yasaka hannunsa aka 🙆🏻‍♂na shiga uku idan akaji agidan mu”

Anwar yace “to Dan matsoraciya, dalla kuzo mu ware”

Cikin sauri suka shiga Mota sukabar wajan

Acan Gida kuwa umma takasa zaune takasa tsaye, har ana kiran sallar magrib amma shiru Baby bata dawo Gida ba.

“Ke kuma lafiya Tun dazu nashigo inata sallama kinyi shiru”

Kamar da ita yake magana ta yi burum tafuto daga Dakinta tace “rashin kawaici ne kawai irinna yaya, Tun dazu Baby bata dawo daga makaranta ba shine ta daga hankalin ta, ita Babyn yarinyar goye ce daza’a tsaya ana d’aga hankali akanta”

Abba yace”badake nakeba Mariya, kidenamin katsalandan “yajuya ya kalli umma yace” ke Safiya karfe nawa take dawowa yau? ”

“Karfe biyar, wani lokacin biyar da kwata, kuma tabar wayarta agida saboda batada chaji.

Jinjina kansa yayi yace” to bari Muje dasu salisu abi sawunta, ”

Mayafinta tazara tace” maigida hankalina bazai kwanta ba Muje ”

Fita sukai gaba dayansu, Mariya tatabe baki takoma daki.

Da salisu da qannanta maza guda biyu dakuma umma suka tafi hanyar domin dubata.

Kasancewar duhu yafara yasa suka fara haskawa, shiru basu gantaba, saida suka duba layin duka basu gantaba.

Kamar wasa umma ta haska gefenta, taga baqi awajan Kamar abayar jikinta, sake haskawa tayi, gabanta yana faduwa, cikin sauri tayi wajan taga ‘yarta ayashe aqasa

Salati tasaki cikin kururuwa tace “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un Alhaji gata anan, ai suna jin haka sukai wajanta gaba dayansu.

Jijjigata umma tafarayi amma shiru bata numfashi, lokaci daya umma tasaki kuka” alhaji munshiga uku bata motsi, Jijjigata tasake yi da karfi tace “Innalillahi…”NAWAL”

Ni Dake Complete Novel Document Txt

File Name Ni Dake… Hausa Novel Doc.
Title Ni Dake Complete Novel Document 
Author   Amnah El Yaqoub
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    27/11/2024
File Size    350KB
Format Size     TXT
Book Price     Free
Phone No      NIL
Download Ni Dake Complete Novel Document By Amnah El Yaqoub

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button