Hausa novels

Wace Ce Ita (Who is she) Chapter 66 Hausa Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

SIXTY-SIX📍

Umm batasan lokacin data mike tsaye da karfi tace;
“What are you saying Dr Max?”….
Dariya yayi daga daya bangaren yace;
“Of course you heard me right Dr Jam”…..
“How? When? I don’t understand?”….
Umm ta fada unbelievably tana saka wayar a hands free yanda mami da anna zasuji dan kanta ita takai baze iya daukan zancen ba…..
Labari tiryan tiryan Dr Max ya bata tindaga lokacin da deen ya kirasa ya fadamasa tayi passing out and result din reads that her kidney is damaged completely, ya rokeshi ayi musu shifting appointment dinsu yau, da yanda yayi mamakin ganinsu su biyu a tinaninsa da ita za azo, a lokacin ne kuma deen ke fadamasa yarta ce wacce za’ayiwa suggery din, da yanda suka cire kidney dinsa sukayi mata implanting bisa umarninsa har Allah ya taimakesu everything went successfully, sai yanzu bayan komai ya kammala deen ke fadamasa babu wanda ya sani because he doesn’t want them to panick…
Hannu umm tasa ta dauke hawayen daya silalo mata, cikin rawar murya tace;
“Pass the phone to him please”…..
Mikawa deen wayar Dr max yayi, deen ya karba yasa a kunne……
Yana dora wayar a kunne umm cikin rawar murya tace;
“Saifuddeen! Saifuddeen! Saifuddeen!”…..
Kuka ne yaci karfinta ta saka fadan abinda takeso ta fada….
Deen na jin haka yayi saurin kashe wayar saboda yanda yakejin sautin kukanta har cikin ransa, Allah ne kadai yasan yanda yakejin matar aransa da yanda yake gudin bacin ranta har zuciyarsa……
Mikawa Dr Max wayarsa yayi ya koma ya kwanta, fita Dr Max yayi yana kara jinjinawa deen aransa…….
Ajiyar zuciya deen ya sauke wani murmushi me ciwo yana kwace masa, tabbas burinsa ya cika yau saboda a duniya bashida wani buri illa yaga baby tee cikin koshin lafiya kamar kowa, ko kadan baya danasanin bata kidney dinsa dayayi koda hakan yana nufin rasa balance dinsa kenan, yanzu tinda Allah yasa burinsa ya cika sai ya cika alkawarin daya daukarwa kansa, alkawarin shine ze fita daga sabgar baby tee completely dan yayiwa umm alkawari bazata kara kamasu da wani lefin ba and he really mean it, yasan it’s not going to be easy share baby tee amma zeyi, atleast he has a huge memory to behold wato ‘that plane kiss’ , a memorable moment to behold, he can’t believe he’s still feeling her soft lips that tasted like a nectar, and he has realize yanda take attracting dinshi dangerously which is another reason daya kamata ya guje mata, worse of it tasha fada a gaban idonsa ita khaleel kawai takeso, shima kuma khaleel din from the look of things yana sonta so gwara ya barsu suyi rayuwarsu….
Sannan at this stage shi da kansa ya yarda yana tsananin bukatar yin aure, but the problem is wa ze aura? Shi fa har yau ya kasa samun wacce ta masa, Allah ya sani kuma in dai ya auri wacce bayaso toh ko feeling ne ze kashesa sai dai ya kashesa amma baze iya tabata ba, ko hannun mace kyankyamin rikewa yake masa bare intimacy, shiyasa kome zasu fadamasa akan eesha baze taba aurenta ba saboda kallon yar lesbian yake mata, koda ba haka bane ba saidai tayi hakuri dan ya riga ya zauna akan abinda zuciyarsa ta dorasa, ko baby tee da yake iya tabawa yasan saboda yar uwarsa ce, yar uwar ma from his beloved umm ta ina ko zeji kyamar ta?, tambayar kansa yayi kodan baya kallon mata ne ya kasa samun wacce ta masa? Inko haka ne daga yau ze bude ido ko Allah zesa ya samu wacce yakeso, sannan yayiwa kansa alkawarin focusing akan cigaban rayuwarsa, ze maida hankalinsa completely akan aikinsa, hospitals dinsa da companies nasa ya rabu da duk wani shirme da yakeyi, he’ll be that responsible man umm always want him to be……..
And that’s how the his new life began!…

Kankame mami umm tayi tana fashewa da kukan farinciki, farin cikin irin wanda ta dade batayi irinsa ba, da ace za’a iya bude zuciyarta aga irin farincikin da take tabbas ko wanda yake cikin kunci sai ya tayata farin ciki, she has always been proud of saif, tasan kuma ba’a banza take bala’in jinsa aranta ba, ashe he’s their savior, itako ina zatasa ranta taji dadi yau, like the joy is just too much she can’t even take, yau da ace deen ze bata wani green light guda daya da wallahi sai ta aura masa baby tee koda bataso ta kuma mata Allah ya isa idan bata masa biyayya ba, amma inaa yace bayaso, ita kuma bazata iya masa dole ba, tana dai yiwa baby tee takaicin rashin samun miji irin deen….
Call din Abby ne ya katseta, sakin mami tayi tana kallon screen din wayar hannunta na rawa, karban wayar mami tayi ta dauka tasa a speaker, good news ya basu akan india sukaje be san ma sunji ba, bayanin da aka samo masa ya basu kamar yanda Dr Max ya fada musu baby tee aka yiwa imaplanting kidney din deen, cike da farin ciki itama mami ta basa labarin sun samu information daga bakin Dr Max din, sai yace musu kawai su shirya su tafi Indian gabadaya su samesu achan, ya kuma fadamusu yayi magana da dad yanzu zasu shirya tafiyan saboda haka su zama cikin shiri nan da one hour, sallama sukayi akan bari su sanar da sauran mutane kafin lokacin…..

Four hours later….
A hankali ta bude kyawawan idanuwanta masu sheki da daukan ido, saurin rufe idon tayi saboda hasken fitila daya dashe mata idon, kokarin tashi tayi idonta a rufe taji wani irin severe pain a abdominal part dinta, dole ta hakura ta koma ta kwanta, sake bude idon tayi amma kadan yanda hasken baze dameta ba tashiga rarraba idanu tana neman ta ina zata hangosa amma wayam babu alamun mutum a dakin, kasa hakura tayi ta daure ta tashi zaune dukda pain din da takeji wai ko zata gansa a wani angle din saboda sarai tasan ze iya yin shiru kuma yana dakin, amma ina bataga kowa ba, hankalinta ne ya tashi because if she’s not mistaken tare sukazo asibitin nan, infact ita batasan meya kawosu bama, tasan dai anshiga da ita wani daki deen ya mata wata allura da kansa, daganan kuma bata kara sanin inda kanta yake ba sai yanzu data tashi tanajin ciwo a gurin cikinta sai idanuwanta da takejin sun mata nauyi ga wani sarawa da kanta yakeyi, amma duk wannan abun bashi bane damuwarta ba, damuwarta kawai tagansa ko hankalinta ze kwanta.
Knocking din Dr Max tare da shigowarsa bayan na’urar da suke saitawa yayi alarming dinsu idan suggery patient ya farka ne ya dawo da ita daga duniyar tinanin neman deen data shiga, murmushi me kyau Dr max ya mata yace;
“I’m glad you’re finally awake, how’re you feeling dear? Any pain in anywhere?”…..
“Where is my brother? I want to see him”…..
Shine tambayar data jeho masa…..
“Oh your lovely bro that sacrificed his kidney for you?, he’s in the rest room”….
Dr Max ya fada bada nufin komai ba…
Cikin rashin fahimta baby tee tace;
“I don’t understand he sacrificed his kidney for me? What do you mean?”….
“Oh yeah! You just undergone a kidney implant due to failure of your two kidneys and yes your brother’s healthy kidney was implanted in you!”……
Dip taji komai ya dauke mata gabadaya, tasan dai ya taba fada mata kidney dinta is failing ranar dayace tana da HIV, amma har ga Allah bata wani yarda ba, gani take kamar bayanda za’ayi duka kidney dinta suyi failing, ashe dagaske ne? Gashi ma wai anmata implant din batasan anyi ba, kuma koda wasa be fadamata abinda suka zo yi ba, sannan shi ya bata kidney dinsa? And if she listened well taji Dr din yace healthy kidney dinsa, so what does that mean? Meyasa ze mata irin wannan sacrifice din? Does she really deserve all this?…
Kokarin mikewa tayi tana fadin;
“I want to see him, please take me to him now”….
Mai da ita Dr Max yayi yace;
“No please you haven’t even heal at all, let me call him for you, you need a very good rest before any voluntary activity please”…….
Sai da ya tabbatar ta koma ta kwanta sannan ya fita kiran deen, mamaki ne ya kamasa ganin deen baya rest room din daya barshi, shi be taba ganin strong mutum irin deen ba, tinda yace ayi laparoscopy din idansa biyu ya sallama masa, yanzu kuma yayi ficewarsa abinda a ka’ida anaso mutum yayi good ten hours a kwance….. A reception ya tsincesa, yana zaune yana danna waya hankali kwance kai bazaka ce patient bane shi, hannu Dr Max ya mika masa suka sake gaisawa sannan ya fada masa kanwarsa ta tashi kuma tana son ganinsa, okay kawai yace ya mike yabi bayansa, sai da Dr Max ya sadasa da kofar dakin da take sannan ya juya ya koma office……
Da sallama ciki ciki ya shiga dakin yana danna wayarsa, baby tee na kwance ta hango shigowarsa dan bataji sallamar dayayi ba, yunkura tayi zata tashi cike da farincikin ganinsa, da sauri ya mai da ita cikin tsawa yace;
“Baki da hankali ne zaki tashi? Ko baki ji ciwo a jikinki bane?”….
Lumshe ido tayi tanajin wani abu me daci a ranta na tsawar daya mata, amma sam bataji haushi ba saboda abinda ya mata yafi karfin dan karamin tsawa ya bata mata rai, bazama ta iya kwatanta yanda take jinsa a lokacin ba, gani take kamar ba iya kodarsa aka sa mata ba harda shi karan kansa gabadaya aka dasa mata…..
Bata hakura ba idonta a lumshe ta kamo hannunsa murya na rawa tace;
“I can’t thank you enough and…”….
Fizge hannunsa yayi murya a dake yace;
“Hold your thank you to yourself! Ni badan ki gode min ko wani abu nayi ba and last warning karki kuskura ki kara tabani! Kije chan ki taba wanda kikeso, don’t try me!”….

KARANTA>>> Dr Bobby Hausa Novel Document – Aihausanovels

Kuka ta fashe dashi daga kwancen da take tace;
“Yaya mena maka? Dan Allah idan na maka wani abu ka fadamin in baka hakuri, dan Allah”…..
Juyawa yayi ya fice daga dakin yana jin wani irin zafi aransa, sincerely he can’t withstand seeing her crying but it’s the best for them both if not they’ll never stop getting into trouble and zuciyar wanchan ragon zata iya bugawa ace shine sila, iska me zafi ya furzar beneath is breath yace;
“I’m sorry baby girl, this is the only way I can get over you”.
Direct office din Dr Max ya tafi saboda hankalinsa baze taba kwanciya ba inya tuno ya barta tana kuka, yana zuwa yace masa yanaso a mata allurar bacci saboda ta dage sai ta tashi zaune and it’s not good for her health, ba musu Dr Max ya tura wata nurse ta mata saboda shima ganau ne ba jiyau ba, karewarta ma shi a zaune ya sameta……
Wani kuka me cin rai ta fashe dashi bayan fitarsa, tinda yake mata tsawa da rashin mutunci bata tabajin abun ya tabata ba kamar ranar, hakan kuma baya rasa nasaba da shiri da take nema a gurinsa, a yanzu tafi bukatar shiri sosai tsakaninta dashi akan komai, so take kawai ya bata brother figure, irin brother din da you can confide in da bazaka iya boyewa komai naka ba, da yasan yanda take tsananin son ganinsa a kusa da ita yanzu daya tausaya mata ya zauna, bata taba tinanin this is how it feels kanaso mutum ya kulaka ba shi kuma yana maka wulakanci, she can’t believe harda ce mata tarike godiyarta bayaso sannan karta kara tabashi sai kace wata yar iska? The last time she checked shi yace mata ‘can I kiss you’? Be tsaya yaji amsarta bama yayi son ransa kuma ya sata ta biyemasa bata sani ba, toh meye ya chanzasa all of a sudden haka? Is it because she kissed him back? ‘Nooo’ ta fada tana girgiza kai tuno da har ce mata yayi ‘where would she want to kiss him again?’ meaning yaji dadin hakan, to meya chanzasa?
“Why? Why?”..,,
Ta fada da karfi tana jin kamar kanta zeyi exploding…..
Daidai lokacin nurse tashigo dakin, ganin halin da take ciki nurse din duk a tinaninta zafin ciwo ne yasata saurin yi mata allurar bacci sannan ta fita…..
Wani hawaye me zafi ne ya silalowa baby tee sannan wani bacci me nauyi ya dauketa…..

Sai gurin azahar suka karaso India, mutane dayawa sun so su biyosu amma bappa ya dakatar dasu yace su bari sufara zuwa tukun, iya su bakwai ne kawai suka tawo, bappa, anna, mami, umm, abby, dad sai khaleel daya dage sai ya biyosu bayan abby yasanar dashi abinda ake ciki, bayanda abby beyi dashi akan ya zauna ya kara samun lafiya ba yace sam dhi sai yazo yaga halin da wifey dinsa take ciki….

KARANTA>>> Mafarkin Ruwan Sama 

Direct asibitin suka nufa bisa jagoranci umm data taba zuwa, Dr Max din bayanan lokacin da sukaje amma ya bar note, wani VIP waiting room kamar normal sitting room aka kaisu bisa ga umarnin Dr Max, cike yake da kayan alatu iri iri na indiyawa, suna zuwa suka tarar da deen a zaune a ciki, sam beyi niyar zama ba Dr Max ya matsa masa wai sai ya zauna ya jirasu a ciki……
Umm ce ta fara hango deen dake itace gaba tinda itace lead dinsu, da sauri ta nufesa ganin haka shima ya mike tsaye, rungumesa tayi ta fashe da kuka tace;
“Saif I have a lot to say but I have been short of words tin cikin dare, saif ka fadamin dame zan saka maka? Wallahi sai ka fada, tell me something please”….
Dagota yayi ya share mata hawayen fuskarta sannan ya kama hannunta suka bar daga dakin, wani quiet place ya kaisu suka zauna, sai da yaga ta tsagaita kukan sannan yayi facing dinta yace;
“Umm a kullum in naji kince dame zaki sakamin sai naji kamar baki daukeni da’ ba, nifa dan uwanta ne na jini meye a ciki dan na bata kidney dina? Trust me zan iya bawa baby tee abinda yafi kidney ma, umm ko rayuwata take bukata ta rayu wallahi zan bata, ni dai burina kawai kanwata tayi farinciki”…
Sosai maganar ta daki umm har batasan sanda wani hawayen ya sake zubo mata ba, tabbas yau ta tabbatar baby tee bata da babban masoyi sama da deen a duniya, yayi abinda ko su da suke iyayanta basuyi ba, itako in bata samu abinda zata saka masa ba ta ina zataji dadi, murmushi tayi me tare da hawaye tace;
“Kasani uwa ma tana yiwa danta kyauta idan yayi matukar faranta mata, shiyasa nima nake matukar so na faranta maka, saif ko a yau Allah ya dauki raina nasan baby tee bazatayi maraici ba because you’re every picture she needs, nasan zaka zama uwarta da ubanta badan su mami basa nan ba, saif na baka amanar baby tee ba dan mun mutu ba”…
Murmushi yayi me kayatarwa yana goge mata hawayen da suka zubo yace;
“Na karbi wannan amana hannu bibbiyu, nifa umm kukan nan da kike kina badani wallahi, dan Allah karki bari azo wucewa a mana dariya”….
Ya karashe da tsokana…..
Dariyar da bata shirya ba tayi ta masa dakuwa tace;
“Zakaci gidanku fa, kukan farinciki kuma yanzu na fara”….
“Hahaha bari na kira mami in rakaku ku ganta, nasan bazasu bari a shiga gaba daya ba”…..
Ya fadi hakanne saboda ya datse zancen….
Zuwa yayi ya kira mami ya rakasu dakin, sosai umm ta zubarwa da baby tee hawayen farinciki mara iyaka, bini bini sai ta juyo ta cewa deen me yakeso ta masa a duniya taji dadi, har mami saida ta zubar da tata kwallar a boye saboda ganin yanda umm take farinciki kadai is enough for her, deen yayi niyar guduwa umm tace be isa ba……
Suna zaune Dr Max ya shigo dakin, mikawa umm hannu yayi cikin fara’a yace;
“You’re highly welcome Dr Jam”…
Hannu ta mika masa sukayi shaking tace;
“Thank you Dr Max, I really appreciate your effort”…..
Nuna deen yayi yana murmushi yace;
“Appreciate this gentle man more”..
“Sure, he’s my hero!”….
Ta fada tana taba deen…..
Dr Max na fita deen ya hade rai ya juyo ya kalli umm yace;
“Umm be kamata ba!”….
Cikin rashin fahimta tace;
“Meye be kamata ba?”…
Karap mami tace;
“Ya wuce yace handshake din da kikayi da Dr Max, shi gashi shugaban mallaman sunnan duniya da suka fi kowa kishi, kaidai matarka ta shiga uku”……
Deen na jin haka yayi sauri ya tashi ya fice saboda hakan yake nufi dama, toh akanme zatayi shaking din mutumin da ba muharraminta ba?……
Dariya umm tayi tace;
“Toh ai gaskiya ya fada, Allah dai ya yafe mana”…..
“Hmmmmm”…..
Shine kawai abinda mami tace taja bakinta tayi shiru….

KARANTA>>> Yar Harka Complete Hausa Novel Document

Farkawa kawai baby tee tayi taga umm tsaye akanta, bude idonta tayi tana mamakin yanda akayi tazo, cike da farinciki umm ta sunkuya tayi kissing forehead dinta da kumatunta sannan ta dago tace;
“Kin tashi, how’re you feeling sweetheart?”….
Budar bakin baby tee kawai tace;
“Umm ina yaya saif?”….

Back to top button