Novel Document

Munafikin Miji Complete Wattpard

Munafikin Miji Hausa Novel Complete Document

Description/Story:

Munafikin Miji Complete Wattpard Written By Na’ima Sulaiman Sarauta 

Description Of Munafikin Miji Complete Wattpard

Ganin abin na Ustaz azumin ne ya saka Mahmah kama hannun Nadra ta ce “Mu je ciki”

 

“Ki haɗa da Junior”

 

Tajuddeen ɗin ya furta da ƙyar yana jin wani abu mai zafi na tsaya masa a ƙahon zuciya, mene ya shiga tunanin Ustaz har haka? Mene tsakaninsa da Ridayya girman tuzuruntakar tasa har ya kai ya fara kama yaran mutane? Gabaɗaya tunanin Tajj ya tsaya wani abu mai kama da zullumi ya fara kawo masa ziyara.

 

Miƙewa ya yi tare da yin waje ya bi bayan Sadauki domin ya lura da shigowar tasa da kuma sauyin daya gani tattare da shi ɗin.

 

Bakin Ridayya ne ya fara rawa idanunta a fuskar Ustaz har yanzu ta kasa kallon cikin idanunsa wanda kuma hakan shi yake buƙata, jininta na rawa tana jin saukar numfashinsa a fuskarta yana saukar mata saboda fuskarsa dake ɗan rakaɓe da nata ya kasa furta komai. Da sauri kuma ta yi saurin zame fuskar tana yin baya tare da ƙare masa kallo.

 

Sai kuma ta shiga girgiza kai while hawaye running down on her face. Ta buɗe baki cikin firgitaccen yanayi ta ce

 

“Mafarki nake da gaske mafarki ba kai nake gani ba, irin mafarkin dana saba yi ne a kullum a koyaushe ba zaka taɓa zuwa gare ni bakai bane you’re not my father…… My Abbiey is dead, he is in the grave”

 

Baki Ustaz ya buɗe zai yi magana ya kasa ta yi saurin cewa

 

“Me zaka ce? Shiru ko na san mafarki nake ni kaɗai ce bani da kowa sai wanda yaga Allah ya taimaki rayuwata me ya sa zaka bar ruhinka ya fito domin ya firgitar dani Abbiey why why why?”

 

“Don Allah ka yi magana ka ce kai ne ka dawo gare ni baka mutu ba, wayyo Allah wayyo ni Ridayya na shiga uku”

 

Ji ya yi kamar an saka sofa glue tare da manne masa laɓɓansa ya kasa buɗe baki balle furta komai ya kasa nufar inda yake da tunanin idan ya riƙe ta da hannayensa zata dawo cikin hayyacinta da nutsuwarta. Duk dauriyarsa da yadda ya so riƙe kansa kasawa ya yi jikinsa ya shiga ɓari hatta laɓɓansa rawa yake baya son tunkararta kai tsaye domin a farkon ma, tsananin ta’ajjuji ya saka shi yin hakan da son fahimtar da gaske ita ɗin ce tsaye a gabansa shekaru nawa? Wata nawa? Kwanaki nawa? Mintunawa nawa? Daƙiƙo nawa ya shafe yana jiran wannan ranar?

 

Abu biyu ne zai faru idan ya ƙarasa wajan wanda kuma a yanzu bai isa ya hana zuciyarsa da gangar jikinsa hana afkuwar hakan ba, domin baya da iko da su a yanzu sune suke jan ragamar shi. Idan bai riƙe Ustaza ya sanyata cikin jikinsa ta jiyo ɗuminsa wanda ta saba da shi tun tana ƙaramar, to idan bai hakan ba yasan sauran abinda zai biyo baya shi kansa bai sani ba yana tabbacin sahihiyar runguma ce zata samu matsayin tarba a gare shi.

 

Yana kallo ta juya tare da shigewa ɗaki ta rufe ƙofar kai tsaye kuma zaman dirshen ta yi saman carpet ta saki wani irin raunataccen kuka na ƙuncin rayuwarta. Tunanin Abbiey har ya kai ya dinga zuwar mata idanu biyu? Ya fito daga kabarinsa yana wasa da tunaninsa tasan tunda ya kasa furta komai to wannan mutum mutuminsa ne kuka take da iya ƙarfinta har sai da ta ga ji ta fara shassheƙa tare da kwanciya saman carpet ɗin duniyar ta mata zafi cikin wani irin sounds na fitar hayayci ta ce

 

“Allah ya isa Zameer Allah ya isa ka rusa mini rayuwata ka hanani sukuni da jin daɗi na yi regretting sanin ka a rayuwa, ka yi amfani da rashin gata na, rashin farin ciki, kushe da zunɗen da ake mini a kan halittar da Ubangiji ya yi mini ka yi amfani da son da nake maka ka rabani da jin daɗina ban san haka ɗabi’unka suke ba ashe kura ce da fatar akuya ashe kyan ɗan’maciji ka yi ka zame mini ƙarfen ƙafa bani da sukuni sai na fargabar abinda za ka iya yi mini. Ka zame mini MUNAFUKIN MIJI ba tare dana fargaba ka yi mini illa ka yi mini shamaki da dukkan wani ɗa’namiji babu mai dubana idan ya ji zumubin dana aikata saboda soyayya!”

 

Wani irin ɗaci take ji a duk sanda ta tuna lokacin data bawa Zameer kanta wai saboda kar ya daina son ta ya koma wajan wata ko ya fasa aurenta. Batun bidiyon da ya yi musu ya fi komai ɗaga mata hankali video ne da zai iya taɓa career ɗinta dana iyayenta da suna raye a ranta take jin ko zai yi sanadin da kowa zai guje ta; ta zama mujiya ba zata taɓa komawa auren Giɗaɗo ba.

 

A tsaye nan Mahmah ta fito ta ruske Ustaz ya gama haɗa zufa fuskarsa ta yi jajur wanda yau ne kaɗai ta taɓa ganinsa cikin hakan, dukda ba komai ta sani game da Muhammad ɗin ba. Ta kalle shi ta ce

 

“Babban Mutum ka zauna mana, ina fatan yau zaka tsaya kaci abinci ko?”

 

Numfashi ya haɗiye zuwa cikin bakinsa kafin ya yi magana Tajj ya shigo ya nuna kamar bai ga komai ba ya ce

 

“Saboda Allah ka mayar da hanyar Leges da Kano kamar wajan wasan yara? Kodayake kuɗi ke ake shiga jirgi baya yi maka wahala”

 

“Ni ai na ji daɗin hakan ya fi samun nutsuwar zuciya gabaɗaya ya sauya tamkar ba shi ba” cewar Mahmah.

 

Ustaz ya tattare nutsuwarsa yana juyawa zai fita, sai da ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce

 

“Zan buɗe baki a nan in sha Allah Mahmah,

Bari na je muga?”

 

” To to ma sha Allah babu laifi a dawo lafiya, yau na tarki sa a” Murmushin yaƙe kawai Tajj ya yi yana bin Ustaz da idanu tare da mamakin abubuwan da suka faru a yanzu ɗin kamar gilmawar walƙiyya.

 

“Wacece Ridayya mene haɗin ta da Bilal abinda ya faru ya yi confusing ɗina, dana juya naga Little na ƙara kallon Ustaz sai tsoro ya kamani kamannin Muhammad-Bilal nake gani kwance a fuskar Little hakan ya tabbatar mini akwai alaƙa mai ƙarfi ta jini a tattare dasu duka biyun, da Ustaz ya yi aure zan iya cewa wannan yaron jininsa ce ya fito ne daga ƙwan halittar Ustaz na haihuwa”

 

“Tajuddeen ina magana”

 

Mahmah ta faɗa tana taɓo Tajj daya zurfafa a tunani, ya tuna sanda Majnun yake cewa Ridayya ita ce wacce ta bashi tsoro a lokacin a area ɗin su Ustaz ne, ya tuna sanda ya yi mata gani na biyu furucin data faɗa ta kira sunan “Abbiey” abu mai muhimmanci kamannin Ustaz da Little da yadda Ustaz ya riƙe fuskar Ridayya ɗin banda yana da kusanci da ita ko farcenta ba zai taɓa ba. What is going on? Meke ɓoye?

 

Ya miƙe tsaye yana ƙara zurfafa tunaninsa a matsayinsa na police mai rang ɗin DCP a firgice yana dafe kansa ya ce “Bilal’s adopted daughter?”

 

“No! But how ya akai ban taɓa tsayawa na yi tunani a kan haka ba? Why Tajuddeen mene ya saka duk wannan wahalar da Ustaz yake sha na neman yarinyar nan ashe ina tare da ita? No wonder Ustaz ya damu da batun Junior ashe jininsa ne tsatson shi” Tajj ya shiga damuwa lokaci guda amma daya tuna wani abu sai ya ji damuwar ta kau babu ita dole ya idda nufinsa a kan buƙatar zuciyarsa.

Zama ya yi tare da yi wa Mahmah bayanin komai ta jinjina kai ta ce

 

“Allah Alhakkamu sarki gagara misali Ubangiji ya sa ƙarshen wahalar kenan, Allah ya jiƙan iyayensu da rahama gaskiya na yi wa Muhammad murna da farin ciki dole ya ruɗe sosai shekarun da yawa kuma akwai shaƙuwa tsakanin zuciyoyin guda biyu”

 

Ustaz na fita motar da yake amfani da ita idan ya zo Kano ya shiga, ya jima yana sauke numfashi da tunanin ta inda zai ɓulluwa lamarin Ustaza da kalaman da zai yi amfani da su wajan rarrashinta na nesan ta kansa da ya yi da ita, zai ɗauki duka laifi ya ɗorawa kansa ita ɗin yarinya ce kuma macace mai tarin rauni da ƙalubale bata da wani zaɓi zai amshi laifin da hannu bibbiyu.

Ya miƙa hannu da ƙyar ya daɗo gudun a.cn motar tare da kunna karatu duk dan ya samu nutsuwa zai ciccije bakinsa yake komai na Ustaz special ne daga yanayin kallonsa zuwa buɗe baki da sarrafa harshensa. Ya ɗauki lokaci kafin ya zame hular kansa ya ajjiye a gefe sumar kansa ta baje ta sakko wacce ta sha gyara da saloon ya yi key tare da yin Bismillah ya bar gidan bakiɗaya.

 

Har bayan la’asar Ridayya bata daina kuka ba, kewar Abbiey ya dame ta domin da gaske bata yar da shi ta gani a ɗazon ba. Tana zaune ta idar da sallah tana karatun Alkur’ani ko ta ji sauƙin raɗaɗin da zuciyarta ke yi mata wayarta ta fara ringing ta duba a hankali taga an saka “Sahibi”

 

Ta lumshe idanunta ƙofofin zuciyarta na buɗewa ba zata manta ba shi ne ya yi saved number a haka ta ɗauki kiran tana manna wayar a kunnenta.

“Hello”

 

“Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Hamza Hamdan Hamish barka da yamma Shanshan”

 

Ya faɗa a kasalance ta cikin wayar yana sauke ajjiyar zuciya. Ridayya ta ɗan juya idanunta a nutse ta ce

 

“Ina yini ya mother?”

 

“Ni ba ki tambayi ya nake ba sai mother, ni da mother waya fara saninki Shanshan?”

 

“Yi haƙuri to ya kake?”

 

Ya mirigna daga hagu zuwa dama yana rungume pillown kusa da shi a hankali muryarsa very slowly and sadness ya ce

 

“Cewa za ki Mijina ya zuciyarka take ba ya nake ba” Ta yi shiru.

 

Cikin serious magana ya ce “Ridayya”

 

“Na’am”

 

“Waye naga ya riƙe ki ɗazo? Ya riƙe miki kafaɗu?” Ta ɗan yi jim tana tunani ita kam ai babu wanda ya riƙe ta yaushe ma ya zo gidan?

 

“Ina magana” a hankali ta ce “Babu kowa”

 

Wata razananniyar tsawa mai lafiya ya daka mata ta cikin wayar wacce ta kaɗa hantar cikin Ridayya tana mugun tsoron tsawa ko ihu a ka yanzu zata gigice. Nan da nan ta ruɗe tana ƙoƙarin kashe wayar a hargitse kuma a kasashe ya ce

 

“Don’t try it” kuka ta fashe da shi sosai ta kasa magana yana ji tana kukan bai ce komai ba can dai ya kashe wayar.

 

Tsakanin minti biyar da kukan ya kira taƙi ɗagawa saboda tsoro ya yi mata DM da

 

_”Idan na ruske ki gidan Mahmah abin ba zai mana kyau ba ni da ke Shanshan. So pick my call”_

 

Tana gama karantawa ya kira hannunta na rawa ta ɗauka ta kasa magana bisa mamakinta sai ta ji ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya mai ƙarfi kuma muryarsa can ƙasa kamar ba Sadauki ba ya ce

 

“I am sorry Shanshan kar ki yi fushi dani” Ta yi shiru ya ce

 

“Ridayya ina da zuciya a nan ɗina” Ya nuna saitin ƙirjinsa dukda bata ganinsa “Yeah! Ina da zuciya kuma ina da masifar kishi a kan abinda nake so, idan da akwai abinda Ubangiji ya jarabce ni da shi a kwanakin nan bai shige ba, ke ɗin ƙaddarata ce kuma wallahi tallahi ba ki isa ki zama ƙaddarata ba sai dai mu zama ƙaddara juna. Ki saka a ranki duk inda kika sanya ƙafa za ki ga Sadauki a wajan, kuma ni na fi ƙaunar duk abinda yake bani wahala ko yake nuna mini ƙi so don’t ever trying to reject me kar ki ce za ki bani wahala don sai dai mu wahalar da juna, yadda bana iya bacci ba zan barki ki runtsa ba sai dai idan ya kasance kina gefena ina jin saukar numfashinki a ƙirjina ina riƙe dake yadda na san ba za ki guje mini ba”

 

Tsoro ya kama Ridayya da ƙyar ta ce “Me ya kawo maganar nan Sadauki i think it’s over between us, everything is over between us…..,”

 

“Uhm ko?” Shiru ta yi zuciyarta na bugawa dukda bata ganinsa tsoro da fargabar abinda zuciyarta ke ƙoƙarin ɗarsa mata a kan Sadaukin ya fara gigitata dukda ƙoƙarin da take na danne hakan bata son yarda ko gasgata hakan bata so bata shirya ba, ha dan komai ba sai dan illar da namiji ya yi mata a rayuwa a cikin kunnenta ta tsinkayi kalmar daya faɗa

 

“I have a feelings for you Ridayya no fall in love with you”

 

“Sadauki please, the game is over ka je wajanta ka faɗa mata”

 

A hankali cikin muryar tausayi ya ce “E zani, amma ke za ki rakani na faɗa mata yanzu ma ai ina rihazal ne”

 

Ta sauke numfashi ya ce “Ki yi haƙuri please na miki tsawa ban so ba” nan ma ta yi shiru ta ɗauka ba zai sake magana ba ne sai ta ji ya ce

 

“Zan zo fa, ba rana kawai ki jira zuwana bye ki kula mini da kan ki Shanshan ki shafa mini kan Son”

 

“To” kashe kiran ya yi ta jingina tana lumshe idanunta gabaɗaya abinda bata taɓa ji ba shi ke ƙoƙarin mamaye ta tare da yi mata shigar saurayi Sadauki yana da rigima kuma da saurin shiga rai don dole tana jin daɗin yadda yake ƙaunar Little har zuciyarta.

 

Sadauki na gama wayar ya miƙe ya nufi down stairs ya iske mother zaune tana kallo ya ƙarasa kusa da ita ya yi shiru yana kallon waje guda abu ne mai wahala Sadauki ya zo kusa da mother ya mata surutu ba shirun nasa ya bata mamaki ta ɗan taɓa jikinsa ta zare ido ta ce

 

“Baka da lafiya Sadauki?”

 

Ya girgiza kai kawai bai ma san me yake ba “Ya zaka girgiza kai bayan ga jikinka nan ya yi zafi, daman tunda ka shigo ka shige ɗaki na lura ko abinci baka ci ba what is the matter? Meke damun Sadaukina?”

 

“Ki yi mini addu’a mother ki sani cikin addu’arki don Allah” Ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da ɗage girarsa kansa na yi masa wani irin ciwo ga zazzaɓin daya rufe jikinsa lokaci guda

 

“Addu’a kullum cikin yi maka nake ita Sadauki shi ya sa bana son ka saka abu a rai ka ƙwallafa na ci a kai. Ka yi ta addu’a ka ji ko komai ya yi zafi maganinsa Allah duk wata jarrabawa tana tare da nasara”

 

“In sha Allah love thanks”

 

Da daddare bayan sallar issha Ridayya na kwance a kan gado damuwarta ta dawo sabuwa fil ga tunanin rashin gata da iyaye ga tunanin Zameer da fargabar abinda zai iya aikatawa a kanta. Ga tunanin video idan ya fita da wanne idanu zata kalli Junior? Ta yi masa bayani ga al’ummar gari da suka shayar da ita maɗaci ga tunanin Sadauki da rigimarsa da sauyin da ya yi na lokaci guda idan ta tuna kalar rayuwar da ta yi a gidan aurenta sai ta ji a duniya ba abinda data tsana irin namiji da kuma aure idan ta tuna ƙauyen Batsari sai ta ji ko sunan Katsina bata ƙaunar ji.

 

A hankali take jiyo sautin muryar Tajj yana magana yanayin yadda yake shiru ya bata tabbacin bashi kaɗai bane a parlourn koma shi da waye muryar Tajj ɗin ita ce a sama wancan ɗin kuma maganar tasa gajeriya ce domin sai Tajj ya jima yana magana kafin ta ji ya yi shiru.

Yunwar da ta ci ƙarfinta ne ya sanya ta miƙe bisa dole ta sanya slippers tare da ɗora hula ta fito duguwar rigar bacci ce a jikinta wacce ta kwanta ta haska dark black skin ɗinta hasken idanunta da jajayen laɓɓanta kawai ake gani sai tulin gashin girarta.

 

Magana yake a nutse hannunsa riƙe da cup yana ɗan juyawa kaɗan saboda zumar dake ƙasan kofin fararen ƙafafuwansa gabaɗaya ya zuba su saman table ɗin da aka jera masa abin buɗe baki daman haka ɗabi’arsa take ko ya tanƙwashe ƙafafuwansa ko ya miƙar dasu saman abu. Kaɗa ƙafar yake a hankali yana jin Tajj na cewa

 

“Ai ni dole ya zame mini na yi maka biyayya babban yaya duk yadda ka ce haka za a yi amma nasu ka bari ba yanzu ba ko zuwa next week ne”

 

“Tajuddeen ina buƙatar hakan da ganin gilmawarta, ita ɗin wasiyya ce so a yi hakan”

 

“Ba zaka barta ta ƙara satin guda ɗin ba?”

 

Wani irin kallo Ustaz ya yi wa Tajj irin ai ko kwana guda ban ƙara barin Ustaza ta yi a Kano.

 

“Akwai aikin da zan gabatar na kwana uku zuwa huɗu haka. Zan jira bisa dole na gode da ɗawainiyya Allah ya yi maka Albarka”

 

Tajj ya yi dariyar dole ya ce “Amin Babana Abbiey”

 

Tsit ya yi kamar ruwa ya cinye shi bai san ta fito ba sautin da ƙirjinta ke bayarwa ya alamta masa hakan. Ya miƙa hannu ya kashe hasken ɓangaren shi tare da yin baya ya kwanta jikin kujerar idanunsa zube a kanta ganin yadda take tafiya kamar bata so Tajj ma ya bita da Idanu da kalar nasa tunanin ba jimawa ta fito ɗauke ta kofin shayi mai madara sosai ta nufi cikin bedroom ɗin da ƙyar ta ƙarasa domin ta kusa kifawa a jikinta ta ji kallonta ake.

 

Sun jima dukda tun tafiyar Ridayya ko tari Ustaz bai kuma yi ba. 12 daidai ya miƙe hannunsa riƙe da babbar rigarsa da key ɗin mota hular ma a hannunsa ya riƙe sumar kansa nata lilo a gefen fuska da wuyansa.

 

“Ba a nan zaka kwana ba dama? An gyara ɗaya part ɗin”

 

Ustaz ya yi kicin-kicin da fuska yana ƙanƙance idanunsa a hankali ya ce

 

“Ubangiji ga Tajuddeen ka yafe masa da tunanin Muhammad-Bilal zai kwana gidan mutane”

 

“Ya yafe maka dai Babban yaya kuma babbanmu”

 

Ustaz bai kula shi ba ya nufi bedroom ɗin da Ridayya ke ciki bakinsa ɗauke da sallama can ciki yasan abu ne mai wahala ba ta yi bacci ba, bata kaiwa haka ido biyu. Haske ya gauraye ɗakin tana tsakiyar gadon ta rungume Little ya ƙarasa jikinsa na yin sanyi bai kalli fuskarta ita ɗin dai yake kallo ya kalli shayin data ajjiye ya ɗauka ya kurɓa da ƙyar ya haɗiye yana runtse Idanu

 

“Iyayi dai Ustaza iyayi ne hakan da gaske suger ya miki yawa”

 

Ya dinga bin ɗakin ko wacce kusurwa da addu’a bayan ya gama ya saka hannu ya rage mata sanyin ɗakin yana jinjina wawtar Ridayya da bata san illar sanyi ba ya ja mata fargo a hankali ya durƙusa dab da fuskarta sai kuma ya janye jikinta yana kashe hasken ɗakin.

 

Washegari kiran Sadauki ne ya fara shigowa wayarta ta ɗauka da ƙyar kafin ta yi magana ya ce

 

“Subhi ce Shanshan kina ta bacci abinki”

 

“Abbiey” ta furta domin shi ne ya zo bakinta saboda ƙamshin shi ta ji

 

“Mijinki ne wannan ba Abbiey oyya wake up sweetheart”

 

“Oh bari na yi sallah”

 

“I’ll call you later ki yi mana addu’a Allah subhanahu wata’ala ya ji tausayin Sadauki ya mallaka miki ke matsayin mata” Murmushi kawai ta yi ta kashe wayar.

 

Manyan mutane ne a cikin haɗaɗɗen parlourn duk wanda ka gani kasan sunansa ya yi amo ko wani shi a jihar. Zama suke na musamman wanda ya shafi yaran jam’iyya da shugaban jam’iyyar gabaɗaya.

 

Ya gyara zama cikin nusa iko da jin daɗin abinda yake faruwa ya ce

 

“Mu hakan ya yi mana kyau, su yi ta gwara kansu ya su ya su, za mu yi amfani da wannan damar wajan cimma manufarmu”

 

Hon. Mubarak Nas ya numfasa ya ce “Mene manufar ta mu madugu? Kaga kawo yanzu sun fi mu ƙarfin jam’iyya tun da ba mu jima da sauya wannan jam’iyyar ba”

 

“Na gode Allah da ka ce ƙarfin jam’iyya suka fi mu ba masoya da magoya baya ba, za mu yi musu kwantar ɓauna mu fid da ƴan’takarkaru kama da ga Gwamana mataimaki ɗan’majilissa na jiha dana tarayya, ƙasar ai ta mu ce ƴan’uba muka samu dole kuma zata dawo hannunmu”

 

Hon Iyantama ya ce

 

“Wannan haka yake kuma za a samu ƴan’anti fati kawai mu tsayar da kyakkawar manufa kar mu yi lako lakon da za a yi mana irin ta shekarun baya a ƙwace mana mulki mu shiga court a banza tunda kaga har koton ƙoli mun shiga amma result ɗin ɗaya ne, Shitu Bala shi ne Gwamna talakawa an saka musu tsoron fitowa sake bin wani layi domin kaɗa kuri’a”

 

Madugu ya ce “Wannan tsoron za mu cire musu mu tabbata sun tsaya akan a ƙidarsu da kwatar ƴan’ci ba wani dalili da zai zo a watsa musu hatsi kamar kaji su bi su tsince”

 

Hon. Mubarak Nas da Hon Iyantama duk sukai ma’ana da maganar uban jam’iyya madugu.

 

“Prof ana ta magana ka yi shiru?” Prof Hamdan Hamish ya ce “Gare ni komai yana going well”

 

“Prof ai shi ne ɗan’takararmu na ɗan majalisar Jiha ina fatan baka da wani abu a ɓoye wanda zai kawowa kujerarka tsaiko yana da kyau mu kawo ko wacce kujera”

 

Prof ya yi shiru sai kuma ya ce “Ba wata matsala, yanzu waye zai zama ɗan’takarar Gwamna a jam’iyya T.D.A?”

 

Madugu ya miƙe tsaye yana ɗan takawa cike da ƙarfin qiwwa kafin ya ce “Wanda za mu bawa kujerar Gwamna ba lallai ya amince ba, amma dole mu sanya masa ƙaunar hakan a zuciyarsa yana da farin jinin al’umma kuma bashi da wani tsaiko ko mugun halin da zai kawo barazana a kujerar da jam’iyya bakiɗaya ganinsa zan binka ai yana gari dole ya dawo mahaifarsa ya ceceta”

 

Da haka taron ya watse Prof na hanyar zuwa gida saboda kiran da Sadauki ya yi masa secretary ya tura saƙo kamar yadda yake nuna musu namiji da sauri ya juya kan motar zuwa hotel ɗin da suka saba haɗuwa.

 

Hajiya ta tashi Mai ran ƙarfe shi da wani mutumin nemawa Ustaz auren Mardiyya bayan sun je kawun Mardiyya ya yi mamakin jin Ustaz na son Mardiyya ya yi farin ciki da hakan domin ya san waye Ustaz girmama mutane sadaƙa da tausayi da ƙare hakƙin addini. Ya ce su je za su yi bincike kuma su zauna da yarinyar domin jin ta bakinta. Haka aka yi nan take Mardiyya ta ce tana son Ustaz kamar rai kuma ta amince. Suka ce za su kawo kuɗin na gani ina so da sadaki da lefe lokaci guda kuma a baki sun saka aure sati uku kacal as soon as Ustaz ya dawo Legas zai zo gaishe su kuma za a haɗu da komai na biki kawai yarinya ta zama cikin shiri ta faɗi duk mai take buƙata shi Ustaz na can Kano bai san meke faruwa ba.

 

Kwana huɗu Ridayya bata kuma saka Ustaz a idanunta ba tama manta da hakan tun abinda ya faru shima Ustaz tun daren bai ƙara zuwa ba abubuwa sun ɗan sha masa kai ƙoƙarin ajjiye matsayin Md yake a fidelity bank ɗin.

 

Yana zaune wani baƙin yadin kaftani ne a jikinsa mai kyau da laushi ya kwanta a jikinsa sosai ya ƙara haska farar fatar da har wani yellow take saboda haske. Babu babbar riga yau hannun rigar ma half ne saboda ciwon da kansa yake masa ya saka ya ajjiye zanna bukar ɗin a gefe sama-sama yake jin maganar Tajj suna zaune har a ka yi sallama.

 

“Sadauki wai yaushe gidan Mahmah ya zama gidan zuwanka?”

 

Sadauki yana kaɗa ɗan’mukullin motarsa brown ɗin wagambari ne a jikinsa ɗinkin 3 fisis na maza an jera masa bottles a tsakiya ya ɗora jaddara a kansa ya yi miskilin murmushi ya ce

 

“Uhm Commissioner kenan”

 

“Kira ni da sunan Hamza ai kaɗan daga cikin aikinka”

 

Sadauki ya girgiza kai ya ce “Ni yau ba faɗa na zo yi ba, unguwa za a rakani”

 

“Ikon Allah Mahmah ɗin ce zata rakaka unguwa ko Nadra?”

 

Sadauki ya gyatsina fuska ya ce “Me zan ɗauka da wannan ƴar’taka mai surutun tsiya, kuma ai ba su kaɗai bane Ridayya na zo ta rakani”

 

Cak Ustaz ya tsaya da danna wayar da yake yana nanata sunan wacce yaron ya kira yaushe Ustaza ta zama haka? Har take wa maza rakiya? A zahiri ba zaka taɓa cewa Ustaz ya san me suke cewa ba.

 

Tajj ya kasa cewa komai. Sadauki ya ɗauki waya ya kira numberta tana ɗakko ya sauke ajjiyar zuciya ya ce “Shanshan ina parlour ina jiranki, magana za mu yi very important a hanya, na nemi izinin Commissioner karki ji tsoron wannan bogin bindigar tasa, waiting for you”

 

Kashe wayar ya yi babu jimawa sai ga Ridayya ta fito cikin wata pink ɗin abaya mai kyau ta yi rolling kanta da vail ta yi ƙiba amma kana ganinta kasan bata cikin nutsuwa.

 

Tajj na jin lokacin da Sadauki ya sauke numfashi ya ce

 

“Rest of my life, i so much love you my ride or die”

 

Kanta a ƙasa ta ƙarasa tana ta wasa da yatsun hannunta “shall we?” Sadauki ya faɗa

 

“Abban Nadra zan raka S…..”

 

Tajj ya yi murmushi a ransa yana cewa wannan faɗan da umarnin ba nawa bane.

 

Ridayya kowa maganar ce ta tsaya mata lokacin da idanunta ya sauka a kan Ustaz so da gaske shi ɗinne? Ta dinga kallonsa jikinta na rawa Sadauki ya ja mata masifa gashi ko inda take Ustaz bai kalla ba kuma tasan sarai ya ji muryarta.

 

“Mu je mana?” Cewar Sadauki ya faɗa yana miƙewa tare da kallonta

 

Ta kasa motsawa kanta a ƙasa a ɗan hargitse Sadauki ya ce “What are you afraid of…….,?”

 

Jin Sadauki na neman fasa masa kai ya saka Ustaz ajjiye wayar tare da ɗaga fararen idanunsa yana shigar da su ciki ya kalli Ridayya sosai da kyau sai ya ɗauke ganinsa

 

“Koma ciki”

 

Ya faɗa cikin nuna umarni da sauri ta juya Sadauki takaici kamar ya fashe waye wannan ɗin da zai nuna masa iko da Ridayya?.

Ustaz ya miƙe yana ajjiye wayarsa ya nufi ɗakin Ridayya ya murɗa ya shiga tare da saka key ya zare ya cillar saman wardrobe. Jikin Ridayya sai rawa yake da ɓari bakinta na karkarwa

 

“Abbiey da gaske kai ne? Ko mafarki nake yi Abbiey nane?”

 

Kallonta kawai yake yana nufar inda take tsaye bai san me yake ba shi dai ya tsinci kansa a gabanta ne hawayen fuskarta sun jiƙa masa tafin hannu kuka ta fashe da shi tana yin baya gani take har yanzu mafarki ne

 

“Daman nasan mafarki ne ba Abbiey bane me ya sa kasan ba kai bane zaka kora ni ka hanani bin Sadauki?”

 

Sai a lokacin ta girgiza kai yana jin kalamar Sadauki a kansa a fili ya ce “Ba ki da kai Ustaza”

 

“Innalillahi wai mafarki nake ko Idanu biyu muryar Abbiey nake ji Abbiey..m.,” bata ƙarasa maganar ba ta ji ya cafko hannunta tare da haɗe ta da jikinsa ya riƙe ta gam a ƙirjinsa ba daidai kunnenta yana sauke numfashi ya ce “Ustaza Oum-Bilal” ya faɗa yana yi mata wata kyakkawar rungumar da shi kansa bai san ya yi ba…Munafikin Miji Complete Wattpard txt

File Name   Munafikin Miji… Hausa Novel Doc.
Title   Munafikin Miji Complete Wattpard
Author    Na’ima Sulaiman (Sarauta)
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    True Life Story
Published Date    20/07/2024
File Size    999Kb
Format Size    TXT
Phone No    08164069385
Download Munafikin Miji Complete Wattpard By Na’ima Sulaiman Sarauta 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL MUNAFIKIN MIJI COMPLETE WATTPARD


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button