Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 60 End

Ta tashi ta dawo daya gefen gadon ta zauna ta zuba tagumi; tabbas zasu yi rigima da Mustapha don ba zai yiwu ba ya dinga zagayawa wajen tsohuwar matarsa suna raina mata hankali.Sai wajen karfe tara na dare ya hawo saman, lokacin ya je sallar isha’i ya dawo kuma sun gama cin abinci da yara. Zuwa lokacin itama ta gama duk abinda take yi ta kwantar da yara tana kwance a kan gadon dakinsa sanye da rigar bacci ta mike kafa tana kallo a waya ya shiga daki. Bayan ta masa sallamarsa ta mayar da hankali kan wayar hannunta. Kai tsaye ya wuce ciki ya canza kayansa sannan ya zauna a kan carpet din dake gaban gadon ya mike kafa ya janyo computer dinsa ya kunna ya kama aiki.Yawanci idan dai har yana da aiki to ya kan kai dare sosai a zaune yana aikin, ita kuma ba zata iya jira ba. Don haka ta mike ta zauna ta ajiye wayar da take hannunta tayi gyaran murya sannan tace ‘Uhm, na ga wata takarda, wai Maman Hammad ka biyawa Makka?’Bai yi mamakin jin tambayar daga gareta ba duk da bai sa rai da ita ba, amma dai ya san ya manta ya ajiye takardun a kan mudubinsa. Ba tare da ya bar aikinsa ba yace ‘Eh ita na biyawa, akwai matsala ne.’Cike da neman rigima tace ‘To kuma a yanzu meye tsakaninka da ita tunda naga dai babu aure. Ko kuma kun mayar da auren ne nice ban sani ba.’Har yanzu hankalinsa yana kan aikin yace ‘Bamu mayar ba muna dai kan hanya.’‘To shine kuma ka biya mata Hajji.’Ya dago ya dubeta yace ‘Eh, akwai matsala ne?’‘Gani dai nayi bai dace ba tunda babu aure a tsakaninku.’‘Wannan ra’ayinki kenan.’Ta kula so yake yayi mata wulakanci don haka ta mike ta zauna sosai tace ‘Ina fatan dai ka san yanzu ita din ba muharramarka bace, kuma ina fatan ka san ba zai yiwu ina nan gida ina maka biyayya wai ni matar aureba ka dinga zagayewa wajen tsohuwar matarka wadda ka saka da hannunka, ba zan dauka ba gaskiya.’Ya dago ya kalleta rai a bace yace ‘Sai ki dau mataki a kai.’Ta kula kamar haushinta yake ji sai dai bata san dalili ba, don lafiya kalau suka rabu da safe ya ajiyeta a office sannan ya fice; to meye ya harzukoshi hakan daga yin magana?‘Kada fa ka gaya min magana daga tambaya, na dai gaya maka ba zai yiwu ba ina nan ka kulleni a gidanka a dinga ganinka a gari kana yawo da wata matar banzan.’ Ta fada tana mikewa tsaye.A fusace yace ‘Khadeejan kike cewa matar banza saboda wulakanci?’Sai dai kafin ya rufe bakinsa ta fice daga dakin ta rufe masa kofar; wanda wannan dabi’arta ce idan dai ya bata mata rai sai ta gaya masa magana mai zafi sannan take fita daga inda yake.Yayi tsaki ya cigaba da aikinsa don so yake ya gama aikin kafin ya kwanta.Haka rayuwarsu ta cigaba. Khadeeja taki yarda a mayar da aurensu sannan shi kuma ya kasa tunkarar Baffanta da maganar don ya san ba za a yi mata auren dole ba. Amm kuma ya ki ya daina bibiyarta; har ta kai baya iya sati bai nemeta yaganta ba. Idan ya je gidansu wajen Hammad ta ki fitowa to tabbas zai sameta a office. Waya kuwa daman bata yankewa don idan ma ta ki dauka haka zai yi ta kiranta har sai ta gaji ta dauka. Duk wata kalma da zai yi amfani da ita wajen ganar da ita ta yarda su mayar da aurensu yayi amma ta sanar da shi ba zata iya komawa ba.Duk lokacin da ta ji kamar zata hakura su koma idan ta tuna yanda yake banzatar da ita a gidan kuma ta tuna yanzun ma sai da ya rasa yanda zai yi da gidan sannan ya fara nemanta sai kawai ta ji ta fasa. Tana sane da duk wata rigima da ta faru a gidan tunda kusan duk asabar a wajenta Habib yake wuni, duk abinda ya dameshi sai ya je ya sameta ya gaya mata.Lokaci zuwa lokaci tana samun masu nuna sha’awar aurenta sai dai auren gaba daya ya fice mata daga rai; don haka yawancinsu bata ma bari su zo gidansu. Kuma duk inda taje idan dai ba an santa a wajen ba to tana gabatar da kkanta ne a matsayin matar aure don ma kada wani ya zo mata da wata magana; don haka mutanen da suka santa sai suka kasu kashi biyu, wasu suna ganin tana da aure wasu kuma suna ganin bata da aure. Amma kuma yawancin mutane kasa tambayarta sukeyi.______EPILOGUEBayan shekaru 3.An yi auren Afaf an kaita gidanta, yaron da ta aura kanin abokin Abbanta ne. da kanta taje ta kaiwa Khadeeja katin bikin nata wanda ta karba cike da girmamawa. Tayi mata magiya a kan taje amma duk da haka ba taje ba, domin bata son abinda zai hadata da Naja da dangin Mustapha a cikin taro. Kuma duk yanda Mustapha ya so ya sakata a cikin shawarar bikin Afaf din da inda zai sayi furniture haka ta zame da wayo da dabara har ya gaji ya rabu da ita.Yana nan dai yana bibiya da kuma addu’ar ta yarda su mayar da aurensu. Kuma a yanda yake fuskanta tabbas hakansa ya kusa cimma ruwa.Yana zaune a dakinsa a kan dadduma yana hutawa bayan sallar la’asar kwana biyu bayan auren Afaf haka kawai ya dauki waya ya kirawo Khadeeja. Ya gyara zama ya jingina da bangon da kofar dakin take jiki ta yanda idan aka budo kofar aka shigo zai zama yana bayan kofar kenan.Bayan ta amsa suka gaisa suka shiga hirarrakinsu, tana tambayarsa labarin biki. A haka har yace ‘Kin ga da kin yarda ai da tare da namu za adaura.’Tayi dariya tace ‘Kai kuwa ka ki ka bar maganar nan.’‘Ba zan bari ba Khadija, har sai kin amince. Ko na tsufa ma sai na dawo dake ko da takaba ne kya yi min sai mu hadu a aljannah.’Dariya kawai tayi don bata da amsar da zata bashi. Suka yi shiru na dan lokaci sannan yace ‘Duk wani condition da kike so Khadeeja ki saka nayi miki alkawarin zan cika in dai zaki zama mata ta. Just one more chance Khadeeja, ki daina wahalar da zuciyata haka.’Tayi murmushi mai sauti ba tare da ta ce masa komai ba; tabbas yana nema ya gamsar da ita ta sake amincewa da aurensa, amma a halin yanzu bata san amsar da zata bashi ba. Ya gaji da shirun kuma yana ji a jikinsa cewa kalamansa sun fara yi mata tasiri. Ya katse shirun yace ‘Gobe da safe zan shigo, ok?’‘Ok, Allah ya kai mu. Amma ina da programme da safe so ka bari sai bayan azahar.’‘Ok, I will take you out to lunch then. No execuses.’Tayi dariya ‘Ka dai san ba zan je ba ko? Kada ma ka fara wata rigimar da ban.’‘In dai rigima ce ai a wajenki na koya. I will see you tomorrow at lunch.’ Ya ajiye wayar ba tare da ya bari tace wani abu ba.Ko da ba zata yarda ya fita da ita lunch din ba ya fi so ta barshi ya kwana da murnan zai fita da Khadeeja gobe, in ya so idan yaje office din suyi fadan da suka saba.Tana tsaye a jikin kofar dakin tana jinsa, duk abinda ya fada tana ji. Sai da ya ajiye wayar sannan ta banka dakin ta shiga a fusace. Firgigit ya juyo ya kalli kofar da aka mako, yace ‘Ya haka kamar zaki fizge kofar? Me ya faru ne? ko wani abun ya biyoki?’Ta tsaya tana masa kallon raini tana jijjiga, sai da gaji da kallon nasa sannan a fusace tace ‘Mustapha na gaji da wulakancin da kake mina akna matar nan, shekara hudu ana abu daya saboda tsohon naci. Wallahi babu ruwan Allah da kun taba aure alakarku haramtacciya ce. Kuma idan ma zina kuke Allah zai kama ku.’Fadan nata bai harzukashi don ya saba ji, idan ma bata ji yana waya da Khadeejan ba kulllum cikin duba masa waya take. Basa magana ta whatsapp don haka kullum cikin duna calls take, da zarar ta ga call din Khadeeja to sai tayi wannan masifar. Ya mike ya nade daddumar yana cewa ‘Kada ki kuskura ki jefi khadeeja da wannan kalmar yanzu ranki zai baci, kuma kin sani.’Ta rike kugu tana dan zare ido tana cewa ‘Ohh! Yanzu kai ka fi son Khadeeja kenan da kanka, kai na jefe ka da koma menene amm kada na jefi Khadeeja ko? To wallahi da kai da ita baku isa ba….’‘Ke kika sani.’ Ya fada tun kafin ta karasa fadin abinda take fada, ya ajiye daddumar ya kewayeta ya fice daga dakin yana murmushi don yana ji a jiki sa kwanan nan Khadeeja zata dawoTa juyo ta bi bayansa da kallo cike da takaici sannan ta wuce ta zauna a gefen gado ta zuba fuskarta a tafukan hannunta ta fashe da kuka. Wannan wane irin wulakanci ne, tana murna ya saki kishiyarta amma kullum suna tare, ita kuma tana nan ya kulleta a gida. Wannan wace irin musiba ce? So take ta ware rana taje ta sami Khadeejan a office din nata ta tara mata mutane amma dai tana tsoron kada Mustapha ya saketa a kan hakan; don yanzu taga kamar ma ba a haiyacinsa yake ba. To yanzu babu aure a tsakaninsu yana mata wannan tsohon nacin idan kuma ta dawo ya za ayi? Ita menene makomarta ya dawo da rabin ransa me kaunar ‘yayansa.Ta dora hannu a ka ta sake rushewa da kuka. END

Back to top button