Ruwan Zuma Page 50 Hausa Novel
(50) Kafin asuba Laila ta yi nisa a nak’uda amma ta k’i su tafi asibiti a cewarta bata son su je a ce su dawo gida haihuwar ba yanzu ba, wannan kuma zai zama kaman abun kunya a gareta da girmanta ace ta kasa ganewa. Haydar kasa bacci yayi duk da cewa Laila ta ce yayi kwanciyarsa haihuwar ba yanzu ba ne. Duk wani nuk’urkusu da dukan bango da take yi yana jinshi ne har cikin ranshi, tausayinta kuma ya cika mishi zuciya har yana dana sanin yi mata ciki. Ita ce mai wahala amma shine mai tara kwalla a idanunsa yana maimaita sannu har Laila ta fara jin haushinsa. “Don girman Allah ka daina mini sannun nan ya isa haka. Ni idan ka fad’a ma k’ara mini ciwon yake…… Hasbunallahu wa….waa… Wayyo Allah na.” Ta fad’a da k’arfi tana damk’e kan kujeran mirrow tamkar zata 6allata. Tsayawa tayi cak idonta a zare dalilin irin azabar da ya mamaye duk ilahirin jikinta kamar an watsa mata ruwan dalma. Haydar da yake gefenta yayi saurin isowa gurinta a razane yana cewa, “Yanzu kam abun ya isa haka dole mu tafi asibiti, ki duba irin azabar da kike sha amma kina cewa baza mu tafi ba. Ta yaya zaki ce this is normal?” Tsayawa yayi a gabanta zai ta6ata tayi saurin d’aga mishi hannun tace, “Bani hijabi, saka mini hijabi mu tafi.” Ai dama kamar jira yake yi ya bud’e wardrobe ya d’auko hijabin ya sanya mata sannan ya kama hannunta suka fara takawa d’aid’ai har zuwa bakin motarsa in da kayan jaririn yake adane tun wancan satin. Gudu yake shararawa wanda cikin mintuna kalilan suka isa asibiti aka tayar da Nurses suka shiga da Laila labour room. Haydar ya zaro wayarsa ya kira Mas’ud wanda ringing d’aya ya d’auka yana cewa, “Haihuwar ne?” “Eh, yanzu muka zo asibiti. Don Allah ka je ka d’auko Kalti Ajidde ta zo ta ga halin da Laila take ciki ko akwai abun da zata mata, wannan nak’udan ya fara bani tsoro fa.” Ya dubi bakin d’akin nak’udar in da wata Nurse ta fito tana cewa, “Ina kayan haihuwar?” Haydar da yake cikin rud’u har ya manta da wani kayan haihuwa, ashe dai zasu buk’ata. “Yana cikin mota. Ta haihu ne?” Yayi saurin tambaya domin baya son ya k’ara jin Laila ta wahala irin wanda ya gani a gida. “Ta kusa. Ka d’auko da sauri.” Ta tsaya a nan shi kuma ya je ya kawo mata ta k’ara shigewa ciki. Minti ashirin da haka Mas’ud ya shigo tare da Kalti Ajidde wacce tana ganin halin da Haydar yake ciki ta fara mishi tsiya duk da cewa shi d’in a matsayin d’anta yake kuma surkinta. “Kai ma kana nak’udan ne na ganka kamar mai kuka?” “Kalti Ajidde ki shiga ki duba ko akwai abun da za’a iya mata, wallahi tana wahala sosai.” Ya yi maganar kamar mai shirin zubar da kwalla. Kalti Ajidde da ta lura da gaske Haydar ya shiga damuwa sai ta nemi kwantar mishi da hankali ta ce “Ka kwantar da hankalinka sannan kayi ta mata addu’a don shi ta fi buk’ata a yanzu. Sannan kasa a ranka cewa kowacce mace haka take wahala idan zata haihu sai dai na wata ya fi na wata. Bari in shiga.” Itama ta kutsa kai cikin d’akin inda ya jiyo muryar Laila tana addu’a cikin sauri-sauri, sai dai ana rufe k’ofar ya daina jiyo muryarta. Mas’ud da yake gefe yana zaune a wani benci dake bakin d’akin yace, “Haydar ka zo ka zauna.” Girgiza kai kawai Haydar yayi domin addu’a yake yi baya son abun da zai sa ya tsaya. Minti biyar da haka Kalti Ajidde ta lek’o fuskarta cike da annuri da kuma murna ta ce, “Ta haihu an samu yaro d’a namiji kuma duk suna cikin k’oshin lafiya. Idan aka gyara yaron za’a kawo maka, sai ka ganshi wollah kyakkyawa Masha Allah.” Fad’in murnar da Haydar yayi har ba’a cewa komai domin Kalti Ajidde kam kunya ya bata ta shige ciki tana mishi dariya. “Ta haihu, ta haihu Mas’ud. Alhamdulillah, Allah nagode maka.” Haka yayi ta fad’a yana kaiwa da kawowa. Can kuma ya je bakin k’ofar ya kasa kunnensa wai ko zai ji kukan yaron. Mas’ud ma yayi farin ciki bakinshi a washe yake kallon murnar da Haydar yake yi yana cewa, “Allah abun godiya wai Haydar da d’a.” Sai da Haydar ya nitsu sannan ya kira Ammi wacce tashinta kenan zata yi sallahn asuba ta ga kiran nashi. Tana d’auka ya sanar da ita abun farin ciki wanda itama nan take fuskarta ta washe ta koma bakin gado ta zauna hawaye na cika mata ido. “Ali na samu jika. Kai Alhamdulillah Mun godewa Allah da wannan kyauta. Ina Lailan take?” Ta tambayeshi tana duban Baba wanda ya fito daga band’aki cikin tsorita jin tana waya da farar asuba haka, ganinta da yayi tana hawaye tana dariya yasa ya gane abun da ya faru. Kafin Haydar ya bata amsa Baba ya kar6i wayar yana cewa, “Me aka samu? Da fatan dukkansu suna lafiya?” “An samu d’a namiji Baba sannan suna lafiya babu wata matsala.” “Kai Alhamdulillah, Alhamdulillah. Wannan abu yayi dad’i sosai, anjima zamu dawo Kano Insha Allah na san Amminka zata hanani sukuni in bata kalli d’an Alinta ba.” “Allah ya tsare hanya sai kun zo.” Fad’in Haydar yana dariya. Sai a lokacin Baba ya mik’awa Ammi wayar ta k’arba tana maimaita tambayarta, “Tana ciki basu fito ba. Sannan lafiyansu kalau.” Ya amsa mata. “Masha Allah, Allah ya bata lafiyar shayarwa ya kuma raya mana d’an Ali.” “Amin Amin Ammi. Sai kun zo.” Suna tsaye Kalti Ajidde ta fito da jaririn lullu6e a cikin zani an saka mishi kaya har da hula sai motsi yake yi yana juya kansa idan hannunshi ya ta6a bakinshi. Haydar ta fara mik’awa wanda sai da ya zauna sannan ya k’ar6eshi hawaye na taruwa a idanunshi. “My bundle of joy.” Yayi maganar wacce bata buk’atar martani illa murmushin da suka bishi dashi. “Ni kam ban ga suna kama ba.” Fad’in Mas’ud yana lek’en Jaririn. “D’an hassada. Ka jira naka sai mu ga ko zai yi kama da kai.” Haydar ya harareshi sannan ya mayar da dubansa ga d’ansa wanda ke bibiyar hannunsa zai tsotsa. “Kar ka mini gori saboda ka san nima watanni kad’ai nake jira in rik’e nawa bundle of joy din.” “Allah ya nuna mana ya kuma sauk’eta lafiya itama.” “Amin.” Mas’ud ya amsa yana tuna matarsa Naana mai d’auke da cikin watanni biyar. “Ka mishi addu’a a mayar dashi gurin mamanshi ta bashi nono, daga ganin yanda yake bin hannunsa yunwa yake ji.” Fad’in Kalti Ajidde tana janye yatsar yaron daga bakinshi. “Yaushe zata fito? Ko zan iya shiga yanzu?” Haydar ya kasa hak’uri ya tambaya don ya kosa ya ga jarumarsa Laila. “Tana hutawa ne, zuwa anjima da safe zasu sallameta.” Gyad’a kai yayi kana ya d’ago Baby ya fara kiran sallah a kunnenshi yana jin kamar mafarki yake yi zai kuma tashi nan ba da dad’ewa ba. Mas’ud da hakan ya burgeshi ya saita wayarshi kansu ya fara musu video yana cewa, “Allahu Akbar ga d’an Ammi da d’ansa.” Haydar murmushi yake yi har ya gama kana ya mik’a jaririn ga Kalti Ajidde ta shige dashi ciki yana jin kamar kar ta tafi bai gaji da rik’e yaron ba. “Ka tashi mu je muyi sallah kar mu rasa jam’i.” Mas’ud ya yi gaba shima Haydar ya bishi a baya suka tafi masallacin dake cikin asibitin, bayan sun idar da sallah suka wuce wajen biyan kud’in asibiti Haydar ya biya sannan suka dawo bakin labour room suka tsaya. Suna isa aka fito da Laila a kan wheelchair hannunta rik’e da Baby tana shafa fuskarsa. D’ago da kanta da zata yi ta hango Haydar tsaye a can nesa hannunsa cikin aljihun wandonsa, murmushi kuma shimfid’e a fuskarsa yana aiko mata da kallon k’auna da wani abun daban wanda ita kad’ai ta iya ganewa. “Ba zaka k’ara mini wayo ba.” Ta fad’i hakan a hankali yanda ita kad’ai ta ji kayanta. “Maman Baby.” Ya furta yana takowa ya iso gurinta kana ya tsugunna yana duban fuskarta wacce take nuna alamun gajiya da son bacci. “Baban Baby.” Ta amsa tana murmusawa. “Thank you, Allah ya biyaki da Aljannah.” Hawaye ne ya taru a idanunta ta dubeshi cikin so da k’auna tace, “Amin tare da kai da Baby.” “Ban da mu kenan?” Mas’ud ya 6ata musu moment d’insu. Sunkuyar da kai Haydar yayi k’asa yana dariya kana ya d’ago yace, “Mas’ud you are annoying wallahi. Wai me kake jira a nan ne baka tafi ba?” “Kar kasa in zageka, uban waye ya kirani in ba kai ba.” “Nine na kiraka amma tun da kayi aikinka ai sai ka tafi.” “Ba zan tafi ba. Fad’in Mas’ud yana isowa gurinsu ya d’auki jaririn a cinyar Laila yayi gaba abunsa. Kalti Ajidde dama tun da ta hango Haydar na tahowa ta bar gurin tana rik’e da akwatin haihuwar. “I will take it from here.” Haydar ya fad’awa Nurse d’in dake tura Laila ya rik’e handle d’in wheelchair ya fara turata zuwa parking space. “Haydar haihuwa da wahala.” “Ba laifi kam, kuma na ga k’ok’arin ki ba kad’an ba. Thank you once again.” “Har d’inki aka mini fa.” Ta k’ara fad’a don so take ya gane ta wahala sosai. “Wow, kenan idan sun ga mace ta wahala sosai sai mu mata d’inki? Shi zaki saka a ranar suna kenan ko wanda aka d’inka miki?” Dariya mai k’arfi ne ya su6ucewa Laila amma ta yi saurin yin shiru dalilin d’inkinta da yake sabo tana tsoron kar ya kunce. “You are so innocent amma not so innocent in bed.” “I will take this as a compliment.” Ya fad’a cikin jin kanshi irin an yabeshin nan. “Big head.” “Baki da kunya ko?” Ya ture kanta kad’an ta juyo tana hararanshi ta ce, “Ka dinga bina a hankali fa, haihuwa na yi.” “Don kin yi rashin kunya an miki hukunci?” “I love you Haydar.” Ta fad’i hakan with sincerity in her words tana shagala da kallonshi. “I love you more Laila. I love you so much.” Bayan sun koma gida aka fara yiwa jaririn wanka Haydar na tsaye a kan Kalti Ajidde yana cewa ta yi a hankali kar ta karya mishi d’a. “Haydar ka fice ka bani guri ko ni in baka wankan ka mishi.” “Ki yi hak’uri amma dai kiyi a hankali nace, ki duba yanda kanshi yake tangal-tangal an ya kuwa ba karyewa yayi ba?” Laila dake cikin band’aki tana wanka ta kwashe da dariya don yau Haydar na bata dariya ba kad’an ba. Kalti Ajidde tashi tayi tsaye jariri a hannunta d’aya yana callara ihu ta tisa k’eyar Haydar ya fita daga d’akin kamar zai yi kuka. Yana fita ta rufe k’ofar har da mak’ulli tana banbamin fad’a wai Haydar bashi da kunya yana saka mata ido a aikinta. Shi kuma tsayawa yayi a bak’in k’ofar yana sauraran kukan d’anshi kamar ya shiga ya kwatoshi. A nan Mas’ud da Naana suka shigo suka sameshi yana kaiwa da komawa, Naana ta gaisheshi tare da mishi murna tana tambayar ina Laila ta ke, ya fad’a mata tana wanka. Suna zaune a falo Sabrin ta shigo cikin sauri bakinta har kunne tana tambayar ina Mamanta take da Jaririn, “Suna d’aki.” Haydar ya bata amsa yana jin dad’in yanda take nuna murnar ta a fili. Sai a lokacin ta nitsu ta gaishesu amma bata zauna ba don isa bakin k’ofar tayi ta kwankwasa, Kalti Ajidde ta bud’e mata ta shiga ita da Naana aka sake rufewa. Haydar da Mas’ud suna hira Sabrin ta fito hannunta d’auke da jaririn ta mik’awa Haydar wanda dama yana ganin an fito dashi ya gyara zamanshi bakinshi har kunne yana murmushi. An yiwa yaron wanka an saka mishi kaya farare masu kyau sai k’amshin Johnson Baby powder yake yi. Shinshinar shi Haydar yayi k’amshin na mishi dad’i yace, “My bundle of joy.” K’arar camera ya ji ya d’ago kanshi ya duba Sabrin ce ta mishi hoto kana ta tura family group d’in su na zuriya gaba d’aya da caption d’in ‘My stepfather da Bundle of joy d’insa.’ A ranar ‘yan uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa barka, Madu da matarsa Hajja tare da ‘yayansu su ma sun zo, dangin Haydar na wajen uba irin su Aunty Aisha da su Hajiya Hadiza da matan Alhaji Shettima suma sun zo tare da alk’awarin sauran dangi ma suna hanya. Sai su Hajiya Shatu da Hajiya Maryam suma sun zo suna tsokanar Laila wai ta sake jiki yaro ya mata ciki. “Tun da har ya iya yin cikin shi ba yaro bane kenan.” Ta basu amsa ganin babu kowa a d’akin sai su kad’ai. “Ni dai kin k’i bani labarin ya abun yake.” Fad’in Hajiya Shatu tana dariya. “Allah ya shiryeki matan nan, zawarci yasa kin koyi maganar banza wallahi.” Fad’in Laila itama tana dariya Hajiya Maryam na tayata tana cewa, “Wai baki san meya faru ba, kwanaki wani abokin mijina ya nemi aurenta amma matan nan kallo d’aya ta mishi tace bata so. Saboda sanin halinshi na kirki ne yasa nayi ta damunta ina bata baki a kan kar ta bari ya su6uce mata, da taga na takura mata sai ta fito fili 6aro-6aro wai tumbinshi yayi k’ato ya shanye abun auren.” Wani wawan dariya Laila ta saka har hawaye na taruwa a idanunta tana rufe bakinta da hannunta, Hajiya Maryam ma sai da tayi maganar ta ji abun ya bata dariya itama ta saka tata. Hajiya Shatu ta harari Hajiya Maryam tace, “Ke ba’a sirri da ke wallahi. Kin ga tashi mu tafi kar dare ya mini a hanya gwara ke kina da aure, yau tun safe muke gidan nan mun kasa tafiya.” Da haka suka tashi suka shirya suna tsokanar juna Hajiya Maryam dai ta kasa ajiye jaririn sai kallonshi take yi tana jin son haihuwa a ranta, amma tunanin abun da haihuwar zai iya jawo mata yasa ta ji ba zata iya ba. Laila ta gane halin da k’awar tata take ciki tace, “Ki cire implant ki samu albarkar aure Hajjajo, tun zuwanki na lura kina rik’e da yaron nan ko an kar6eshi zai dawo hannunki.” “Ni da nake shirin aurar da ‘ya ne zan sake haihuwa? Yaran yanzun nan basa son su ga iyayen su sun girma kuma suna haihuwa, wasu zasu iya bud’an baki su ce miki hakan abun kunya ne, kad’an daga cikinsu ne zasu yi supporting d’inki kuma su kwantar miki da hankali har ki haihu su kuma so k’anin nasu ba tare da sun ji kunyar fita dashi ba.” Fad’in Hajiya Maryam tana girgiza kai. Laila ta dafa kafad’arta tace, “Abun da nayi learning a rayuwa shine duk abun da zaka yi in dai bai kauce Shari’a ba kuma ba zai cuci kowa ba ka aikatashi in har ranka yana so. Menene ba’a fad’a ba akan aurena da Haydar? Wace irin fitina ce ban gani ba akan hakan? A dalilin wannan auren d’ana ya lalace amma saboda a kan gaskiya nake sai Allah bai barni haka ba ya dafa mini ya kuma kwato mini hak’k’ina a kan duk wanda ya cuceni Ya kuma shirya mini d’ana. Idan kina son haihuwar ki nema sannan ki toshe kunnenki ga duk masu sukarki tun da ba cikin shege kike yawo dashi ba. Yara kuma ke kike haifesu basu isa su tsara miki rayuwarki ba. Sau da dama muna barin farin cikinmu don gudun maganar mutane, sai dai duk da hakan bama tsira wallahi sai an samu masu zaginmu ta wani gurin. Wani abun mamaki kuwa shine; su kansu masu zagin da aibatamun basu tsira ba, kuma don rashin tsoron Allah a hakan sai kiji suna cewa an saka musu ido ana musu hassada ko makamantasu, alhali sun manta da cewa duk abun da ka yiwa wani sai an rama mishi watakila ma wanda yafi wanda ka mishi.” “Kuma kin yi gaskiya Hajiya Laila. Har ga Allah ina son haihuwa amma mijin nawa ne baya son tara yara, yace guda hud’un da muke dasu sun ishemu ba don ba zai iya kula dasu ba, a’a, sai don wai haka tsarinsa yake. Amma wallahi zan cire implant d’in in sake haihuwa ko sau d’aya ne in yaso duk abun da zai yi yayi.” “Baki ta6a fad’a mana cewa shine baya so ba, na yi zaton duk shekarun nan da kika d’auka baki haihu ba kece bakya so.” Fad’in Hajiya Shatu cikin tausayawa k’awartata. “Bana son yin maganar ne shiyasa na 6oye muku, amma yanzu kam wallahi sai dai ya ji na fara zuwa Anti Natal idan har Allah ya bani.” “Kar hakan ya jawo muku matsala fa Hajiya Maryam.” Fad’in Laila tana ji wa k’awar tata abun da haihuwar zai iya jawo mata. “Allah zai dafa mini kamar yanda kema ya dafa miki.” Ta amsa mata tana murmushi cikin dakewa. “Allah ya kawo mai albarka ya k’ara yiwa wanda muke dasu albarka.” Laila ta musu addu’a suka amsa da Amin, kana suka mata sallama suka tafi. A daren ranar misalin k’arfe goma bak’i ‘yan barka suka watse hatta Sabrin da tace kwana zata yi sai da Laila ta koreta ta saka Salman ya zo ya d’auketa. Laila tana cikin d’akinta tare da Haydar yayin da Kalti Ajidde kuma ke falo tana kallo duk da cewa bacci take ji amma Haydar ya k’i fita balle ta samu ta kwanta. Haydar kwance yake a gefen Laila ya d’aura yaron a saman k’irjinshi yana bacci suna hira a hankali gudun kar yaron ya farka. “Ammi bata ji dad’in rashin samun flight ba gani take yi gobe ya mata nisa, tace kowa ya ga jaririn ita bata gani ba.” Fad’in Laila tana kallon yanda Haydar ke shafa bayan d’ansa. “Ai ta damu ba kad’an ba, da ba don k’afan Baba yana ciwo ba da babu abun da zai hanata zuwa a mota. Ni fa bacci nake ji, ki gyarawa Bundle of Joy kwanciyarsa mu yi bacci.” “A ina d’in?” Laila ta tambayeshi tana tashi zaune. “Ban gane ba.” Fuskarsa cike da rashin fahimta. “A ina zaka kwana kake nufi?” “A nan mana! Da a ina nake kwana Laila?” Yayi maganar yana harararta kad’an. “To ita Kalti Ajidde a ina zata kwana?” Sai a lokacin ya tuna wai ashe tana falo, ya ta6e baki yace, “Ta kwana a d’akin Sabrin mana, akwai d’akuna da yawa a gidan nan ai.” Laila nitsuwa tayi ta lankwasa kanta kad’an kamar abun tausayi don ta san maganar da zata mishi ba lalle bane ta mishi dad’i ko kuma ya d’auka ba, ta ce, “Haydar zai fi kyautuwa ka koma can side d’inka ni kuma in dinga kwana da Kalti Ajidde a nan. Zaman ka a nan d’akin zai takurata sannan masu zuwa barka a ina zasu zauna? Ai babu dad’i a dinga ganin kana shiga da fice a d’akin nan. Kar kace zaka yi fushi don Allah ka fahimceni, mai d’aura ruwan wanka jego ita ke kwana da wacce ta haihu.” “Na ji. D’aukeshi in tattara kayana.” Ya fad’a ranshi a 6ace. “Na had’a maka tun d’azu da rana na kai maka can side d’in.” Ta sa hannu ta d’auki jaririn ta rik’eshi a hannunta ganin ya farka yana lalu6en nono zai fara kuka. Yana callara k’ara Laila ta saka mishi nono a baki ya fara sha tana jin zogi har cikin ranta domin a take mararta zai fara ciwo kamar mai nak’uda, wanda Kalti Ajidde ta ce hakan yana faruwa ne idan mahaifar na komawa normal shape in jaririn ya fara tsotson nono. Zuba musu ido Haydar yayi can ya had’iye yawu yace, “Manya basa sha ne?” Hararanshi tayi tace, “Baka san ya nake ji bane shiyasa har kayi tunanin hakan. Azaba nake ji wallahi ga yaron nan ya fiye tsotso kamar wanda dama lokacin da yake cikin nawa nonon yake sha.” Ta k’arisa maganan tana kallon yanda jaririn yake ware yatsunsa yana shilla kafanshi a hankali idonshi a rufe. “Sai da safe.” Fad’in Haydar yana tashi daga kan gadon. Rage tsayinsa yayi ya sunkuya ya yiwa jaririn kiss a kumatu sannan ya matsar da bakinsa ya ciji Laila. “Wash Haydar!!” Ta fad’a tana zare nonon daga bakin yaron wanda kamar jira yake yi ya bud’e baki ya fara kuka wanda babu shiri ta mayar mishi nonon tana shafa in da Haydar ya cijeta. “Cizo na kayi fa! A nan!” Ta fad’i hakan cikin rashin yarda tana nuna mishi gurin. “Nima ki ji abun da na ji.” Kasa magana tayi illa kwafa da tayi ta juyar da kanta gefe tana tura baki gaba alamar ta yi fushi. Bai kulata ba ya je bakin k’ofa ya tsaya yace, “Sai da safe Bundle of joy. Mamanka ta mini rowar kwana da kai kuma zan had’u da ita idan aka yi suna kowa ya watse.” “Zaka jima kuwa, saboda wannan had’uwar sai an yi wata biyar kafin a yi ta.” “Karya ne wallahi.” Ya fad’a flatly amma sai da zuciyarsa ta buga domin watakila maganarta ne gaskiya saboda bashi da masaniya a kan irin wad’annan abubuwan. D’inkin da tace an mata ma sai d’azu ta mishi bayani ya nemi ya gani ta hanashi. Murmusa kawai tayi tana kad’a kai alamar abun ya mata dad’i tace, “Ka bincika ka ji.” “Sai da safe.” Ya k’ara maimaitawa ya fice daga d’akin zuwa falo inda Kalti Ajidde ke gyangyad’i. Fitowanshi yasa ta farka tace, “Ka gama ne ko zaka k’ara komawa?” “Ta hanani ai.” Ya bata amsa wanda yasa ta murmusa tana girgiza kanta tace, “Sai da safe.” “Allah ya tashemu.” Ya amsa yana kashe kayan kallon ya wuce sashensa. A can ya samu Laila ta gyara mishi da’kin sai k’amshi yake yi, ta kuma adana mishi kayanshi tsaf a cikin wardrobe tare da takalma sa. Kwanciya yayi a katifar ya ji kamar yasa ihu, ba rashin lafiya ba ba komai ba saboda wata banzar al’ada wai ba zai kwana da matarsa da d’ansa ba? Ai shi ma yasan menene haihuwa kuma ba zai ta6a neman Laila ta biya mishi buk’atarsa ba in ma hakan suke gudu. Tsaki ya ja mai sauti kana ya jawo wayarsa ya shiga Google ya fara rubutu kamar haka… ‘Sex after pregnancy’ Article d’in da ya fara cin karo dashi yasa yaji kamar ya had’a wayar da gini, don wani gurin an ce sai bayan sati hud’u ko shida, wani gurin ma cewa aka yi wata uku ko hud’u. Dama gaskiya Laila take fad’a kenan ba karya ba? Ya jima a haka yana tunane-tunanensa sannan ya k’ara jawo wayar ya kirata. Sallama ta mishi a hankali tace, “Baka yi bacci ba? Lafiya kam?” “Lafiya kalau. Na duba na gani ashe gaskiya kike fad’a.” “Uhm.” Kawai tace. “Ke hakan ya miki kenan?” Kafin ta amsa yaji muryar Kalti Ajidde na magana, Laila kuma tace mishi ‘sai da safe’ ta kashe wayar. Ajiye wayar yayi a gefe ya rufe idanunsa yana rok’an Allah yasa bacci yayi saurin d’aukarsa. A can kuma d’akin Laila, Kalti Ajidde ce ke fad’a kamar dama jira take yi, “Tun d’azu kuna tare ban takuraku ba har sai da kuka hak’ura don kanku ya fito ban yi magana ba, yanzu kuma na zo zan kwanta shine zaku dameni da waya? A kan ku aka fara soyayya ko kuma menene? Idan bakwa son zaman nawa sai in canja d’aki ko kuma in tafi gidana in da ake sona, ai gadonki bai fi gadona dad’i ba amma a haka na hak’ura na zo kula dake da jaririnki. Wallahi idan kika biyewa yaron nan da bak’ar jarabarsa sai kin yi wani cikin kafin ki yi arba’in Laila. Ki kiyayi kanki in ba haka ba ke zaki wahala shi namiji babu ruwansa.” Laila dai hak’uri kawai take ta bawa Kalti Ajidde don ta lura ta d’auki zafi ba kad’an ba, sai dai tunawa da tayi cewa tun asuba Kalti Ajidden take kanta suka dawo gida ta d’aura mata ruwan wanka ta yiwa jaririn ma wanka, sannan take kaiwa da kawowa tsakanin kitchen da d’akin jegon don tace ita zata dinga yiwa Laila girki don bata yarda da girkin masu aikinta ba wai baya nuna yana jawo basir. Dole ne tana buk’atar hutawa amma ta biyewa Haydar suka hanata bacci har yanzu. “Kiyi hak’uri Insha Allah ba zamu sake ba. D’okin jaririn yasa yake haka wallahi amma ba halinsa bane.” “Kwa ji dashi dai. Yaro sai rawar kai kaman angon kare, Allah ya kawo Ammi gobe, wallahi zan fad’a mata matukar bai canja halinsa ba.” “Kiyi hak’uri abun bai kai haka ba Kalti Ajidde. Allah ya huci zuciyarki.Idan kina karatun littafina kina jin dad’in sa kuma a kyauta kike karantawa please support me, next time idan nayi book ki saya ba sai kin jira an fitar muku ki karanta ba. A yanzun ma ban yi Allah ya isa ko mummunar addu’a ga kowa ba saboda ba halina bane. All I ask is for you to support me in samu na sayan data. Yanzu ma Zaki iya biyan kudin Ruwan Zuma ba zan k’i ba 😄. Thank you.
Mum Fateey 👌


