Mijin Haneefa Hausa Novel
Mijin Haneefa Hausa Novel Complete Document By Sameena Aliyu
Description/Story:
Mijin Haneefa Hausa Novel
Written By Sameena Aliyu
Description Of Mijin Haneefa Hausa Novel
A guje suka shigo cikin parlorn sai faman haki suke, Inna dake cikin daki ta fito tana gyara daurin zani tana tambayansu lafia, cikinsu babu wacce ta iya amsa mata saima kokarin fadawa bedroom dinta sukayi hade da kullo kofan,
“Danmasani ne ya shigo cikin parlorn yana fadin “wllhi Inna gwarama ki fito dasu don yaukam wllhi bazan hakura ba, “Inna ta gyra daurin kwalinta tace haba ‘Danmasani wai kai bakada hakuri ne, yaran nn fa kannenka ne, ko me suka maka ai hakuri zakana yi inyi, waima me suka maka yau kuma, ta tambaya tana kokarin karya goro,
“Tayan keken abokina suka huda haka kawai don sun rainani,
“Kai ni na daukama wani babban abun sukayi, ta jawo drawer din dake jikin center table ta ciro dari biyar ta mika mishi, maza wuce ka kai mishi ya gyara dan nasan dagaji dan gidan matsiyata ne,
“Inaga ya tafi kuzo mu fita, Shema’u ta fadi haka
“Lallaima mu fita ya cafke mu, kinsan shi da shegen la6el kaman 6aro, cewan Sumayya,
“Barin dubo mana toh, Sadiya ta fadi tana kokarin isa bakin kofa,
“Ke dalla wace irin banzace kawai zaki 6ata mana plan, Haneefa ta fadi cikin tsaurin da ta saba,
“Cikin kuluwa Sadiya tace ke wllhi yarinyan nn kin faye raini saikace ba kece karaman mu ba,
“Hehehe su karama manya, mammy tace shekara daya ne tsakaninmu, shekara daya bayan an mata CS an cireku ‘yan uku ta haifo ni, Shema tace kunzo mu fita Inna ta sallame shi, a tare suka nufi kofa suna sanda kaman 6arayi
“Toh ja’irai ai sai ku fice mun daga daki koh tunda ya tafi, Haneefa ta turo baki tace ke Kakus dinnan kin faye mita, you talk too much wllhi,
“Rufe mun baki da karyan turancinki, sai tsiwa da tsaurin ido kika iya, ga dan karen tsoro, ku wuce ku fice kar wacce ta kuma dawo mun, har sun fice Sumy ta leko tace kakus muna nn dawowa don’t shut your door kinji, ku kuka sani jarabbabu inna ta fadi tana kokarin kunna Tv….
Misalin karfe biyar da rabi suna zaune suna kallo Mamy ta shigo fuskanta babu walwala,
“Sannu da shigowa Mamy, suka fadi gaba dayansu,
“A takaice ta amsa kaman bazata ce komai ba sai kuma tace wato ku baza a muku magana kuji ba ko, sau nawa zan raba ku da shiga hidiman ‘Danmasani, yanzu abun naku ya fada har kan abokansa ko, wllhi ina raba ku da rashin jin maga, haka jiya aka kawo karanku kunyi duka ma wata yarinya a islamiya, ga malam Habu ma kun takura masa bayada kata6us a gidan nn, kune fasa mishi buta kune karya mishi benci, toh wllhi tun wuri gwara ku shiga hankalinku, sai kunyi laifi ku gudu wajen Inna koh ko kuma Abban ku ya hana a dake ku, toh bari kuji yayanku na hanya gobe duk wani rashin jin da kukeyi sai sanar dashi, Sady dake kokarin kai cokali baki tayi saurin ajiyewa ta shiga magiya tana rokon mamy kar ta fadawa wa Ya Haydar,
“Shema ta daura hanu a ka tana fadin shiknn yanzu gidan nn zai zama mana like Hell, mun shiga uku, Mamy dan Allah kice Ya Haydar yayi zamansa a can Lagos din,
“Hany ta turo baki ba tare da tace komai ba,
“Sumy ta mike tana fadin uhm barinje nayi assignment din Chemistry na,
Sanye yake cikin Kaki na Nigerian Navy, Fari ne kal kakin, sai hulan mai ratsin baki, wanda yake kaman facing cap, gaban rigan an rubuta *Captain A.A,*, wato Aliyu Abubakar, kayakyawan saurayi dan kimanin shekaru ishirin da shida, very young Navy, farine sol dogo, bashida kiba snn bashi layin sirara, gashin kanshi bakine sosai saidai bai bar gemu ba, kasancewarshi soja amma na ruwa, Tafe yake a babban filin saman Lagos wato *Murtala Muhammed International Airport* tafiyan nashi yafi kama da sarsarfa irin dai yanda sojoji ke tafiya, mintuna kadan aka fara kiran sunayen garuruwa, ana kiran garin Kano Captain AA naga ya nufi jirgin, nan da nn aka kar6i luggage dinshi aka ajiye don basai anyi checking dinshi saboda uniform dake jikin shi, shigan su da mintoci jirginsu ta tashi zuwa jihar na dabo.
“Misalin karfe 2pm jirgin su Captain A A tayi landing a babban filin jirgin saman *Malam Aminu Kano International Airport* bai 6ata lokaci ba ya dauki drop zuwa gida,
“Malam Habu mai gadi na ganin shi ya karaso da sauri yana fadin ah ah maraba da sojan ruwa, ya mika hanu zai kar6i luggage din shi, da fari’an Haidar suka gaisa da Malam Habu, cikin girmamawa Haidar yaki mika jakan kayan shi wa malam Habu, ya karasa ciki fuskan shi dauke da murmushi.
“Wani indian film suke kalla mai suna *mad about dance*sun kure volume suna sauraren wakan, Haneefa ta mike tana kwaikwayan rawan da suke a wakan, su shema kuma sai dariya suke mata wai bata iya ba.
“Daga bakin kofa ya tsaya ya hade rai kaman bai ta6a murmushi ba, Shema’u ne ta fara ganinshi cak ta daina dariyan da take, Sumayya ma ta shiru sakamakon ganin shi da tayi ta shiga ta6a Sadiya a hankali,
“Ke dalla ki kyaleni…. muryan Sadiya ya sarke sakamakon tozali da tayi da shi.
“Meye duk kuka wani yi shiru ko ban iya rawan bane…. juyowan dazatayi taga Ya Haidar tsaye bakin kofa, da sauri Shema taje ta kashe tv din cikin inn inna take fadin sann… sannu da zuwa yaya, shiru yayi baice komai ba har ya karasa shigowa cikin parlorn, a tare suka shiga gaishe shi, ya amsa a dake snn yace kuzo nan,
“Ba musu suka karasa gaban shi, suka tsaya cirko cirko, tsawa ya daka musu basu san sanda suka zuba gwiwoyinsu a kasa ba,
“Saboda bakuda hankali kun mayar da gida kaman club, waima yaushe kuka fara kallan irin wadannan films din, ya nuna Haneefa yace wato kece tantiriya har kwaikwayan rawan da suke kike ko, shiru Haneefa tayi ta kasa cewa komai,
“cikin tsawa yace ko wacce ta riqe kunnenta, snn yaci gaba da cewa
“This should be the first and the last warning, idan na kuma ganin kuna kallon such film a gidan nn sai na karya yarinya, ku 6ace mun da gani useless kawai,
“Gaba daya suka mike har suna tuntu6e, Haneefa ta turo baki a zuciyanta tace the devil is back dan ita tsaurin ido ne da ita, dai dai stirs sukayi karo da mamy ko waccensu tana kunkuni,
“Meye haka kuma, kuda wa, mamy ta tambaya, Sady tace ya Haidar yadawo, nan da nn fari’an mamy ya karu cikin sauri ta karasa downstairs,
“Haidar na ganinta ya mike da sauri ya tareta da fari’an shi, rungumeshi mamy tayi tana mishi sannu da hanya.
“Suna shiga daki Haneefa tace wai yanzu shiknn wnn mugun ya dawo knn,
“Sadiya tace ke Hany watch your tongue, he’s still your brother, bai kamata ki fadi haka ba,
“Toh ai saiki mun wa’azi, karya na fadi, ba mugun bane cewan Haneefah
“Sadiya tace oho dai you can’t change the fact that he’s your brother, kuma dole kiyi respecting dinshi idan ba haka ba jiki yayi tsami,
“Whatever, Haneefah ta fadi yayinda take kokarin kwanciya bisa gado,
“Heheehe you guys are funny walla, baku zama inuwa daya sai kun kasa hali,cewan Shema dake zaune hanun kujera
“Sumy ‘yar salihan cikinsu tace gaskiya muyi avoiding duk wani rashinji yanzu, if not a banza ya Haidar zai rinka jibganmu, kun san soja ba imani ne dasu ba,
“Ke dalla sarkin tsoro wllhi babu abunda zamu fasa tunda munada Inna da Abba, Haneefah ta fadi haka cikin tsiwa…
“Inna na zaune saman dardumanta ta idar da sllan la’asar Haidar yayi sallama,
“Lale lale da soja, sannu da zuwa Ali, ya karaso yana murmushi ya nemi gefenta ya zauna, bayan sun gaisa Haidar dubi Inna yace matar ashe dai baki karasa tafiya ba, ai na dauka bazaki ganeni ba sai an dauko miki tocila kin haska,
“Inna ta kai mishi dukan wasa tace ja’iri wann ido nawa da kake gani ras yake don yafi nakama, ta mike tana fadin barin kawo maka wani abu ka ta6a,
“Haidar yace Inna da kin barshi na riga naci abinci,
“Bazan bari ba dole kaci nawa, shegen iyayi naku na ‘yan boko, yanzu sai kace baza kaci abincin tsohuwa ba, toh ai naga daga wajen Mariyan aka kawo ko, kai ko Habubakar bai isa na bashi abinci yaki ci ba,
“Haidar dai yayi shiru yana sauraren ban bamin Inna, a hankali yace God mutum ya dawo knn, wnn tsohuwa will never change,
‘Daga can tace magana ne kake Ali?,
“A’a bance komai ba ya fadi yana kokarin ciro wayan shi a aljihu…
File Name | Mijin Haneefa Hausa Novel |
Title | Mijin Haneefa Hausa Novel |
Author | Sameena Aliyu |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 27/08/2024 |
File Size | 600KB |
Format Size | TXT |
Book Price | Free |
Phone No | 08138873799 |
Download Mijin Haneefa Hausa Novel By Sameena Aliyu
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.