Fentin Zina Page 34 Hausa Novel
34.Tana zaune a shagonta da misalin karfe hudu da minti arba’in na yamma wayarta tayi kara alamar shigowar sako, kamar bazata dubaba sai tasa hannu a gajiye ta dauki wayar ta kai dubanta zuwa kan screen din wayar taga bakuwar lamba ce don haka bata damu da ta duba meke kunshe da sakon ba ta mayar da wayar ta ajiye inda ta dauke ta, sai can wata zuciyar ta ce mata gara ki duba ko ta yiwu customer ne kiyi asara. Da wannan tunanin ta dauki wayar ta bude sakon ta fara karantawa, mikewa tsaye tayi tana girgiza kai kana cikin hanzari ta fada cikin gida tana kwalawa fateema dake wanke-wanke kira. Da sauri fateema ta ajiye kopin data ke rike dashi ta wanke hannunta ta nufo Ameena cikin zakuwa da son sanin dalilin kiran nata tace Adda meya faru kike mun irin wannan kiran kamar ba lafiya ba.Kallonta Ameena tayi kamar mai nazartar ta tace duba wannan sakon kiga. Ta fada tana juya mata fuskar wayarta. Karba fateema tayi ta duba sai ta saki murmushin gefen baki tace munafuki kenan, har ya samu labari a kanki zai kara dawowa da wata sabuwar yaudarar sai kuma aka ce mishi yana da gurin zama a cikin gidan nan? Wallahi yayi karya, ki kwantar da hankalin ki adda babu abunda zai faru dake face alkhairi da izinin Allah ta’ala.Ajiyar zuciya Ameena ta sauke tana cewa ai fateema na tsorata ne gaba daya kin san mutum mara amana tsoro kake ya rabe ka bare kuma wannan da yake da irin wata suffa da babu mutumin kirkin da zaiso a kamanta shi da ita.Fateema ta dafa kafadarta tace adda ki kwantar da hankalin ki insha Allah babu abunda zai faru sai alkhairi ke dai ki ci gabda addu’ah Allah zai ci gaba da kare ki dagako wani irin sharri.Allah yasa fateema amma jikina yayi sanyi ne daman sai dai kuma na gode sosai da kulawar ki, ina kaunar.*****Abdul a lokutan nan wata iriyar soyayyar Ameenace suke ratsa zuciyar shi kuma har yau ya kasa tuna cewar saki uku ya mata babu kome,, sai dai wataran ya zauna ya dafekai da duka hannayen shi guda biyu ya lula duniyar tunani, wani lokacin ma har hawaye yake zubarwa ata dalilin kaunar tadake azalzalar sa cikin kankanin lokaci ya rame yayi duhu abu ya hadu mai goma da ashirin ga rashin Ameena ga azabar Maryam wanda kullum baya hutawa da ita, bata samar masa natsuwa. Yayi dana sanin sakin Ameena bila adadin a rayuwar sa yayi nadama da batada riba, koda mamarsa taji labarin ya saki ameena hamdala tayi a ganinta ta rabu da ala kakai, amma tunda maryam ta fito da halayenta rabinsu nan da nan ita ma ta soma Nada mar auren maryam da Abdul yayi sai dai kuma har yanzu tana jin dadin sakin da aka yiwa Ameena.Abdul yaturawa Ameena sakonni masu yawan gaske amma bata ko dubawa bare ya saka ran samun amsa ko sakin fuska daga gare ta.Yau dai ya shirya zaije gidansu Ameena ya fuskanci zahirin rayuwar shi ya kuma roketa afuwa ta dawo su ci gaba da zama a matsayin ma’aurata, don haka shirin shi yayi mai kyau ya sanya jamfar data fito da tsabar ramar da yayi da kuma duhu, sallama yayiwa maryam akan zai fita gidan su mama ya fice kai tsaye ba tare da yajira tace wani abu ba tunda ma yasan baza ta ce din ba..*****Ameena shigarta shago kenan ta zauna bayan ta baro gurin Ameena dake cikin gida, taga gilmawar mota tamkar motar Abdul, bata gama tunani ba tagan shi tsaye a bakin kofar shagon ya harde hannayen sa a kirji yana dubanta irin wanda ke bayyanar da tsantsar kewar ta data addabe shi, share shi tayi bata ko kalli inda yake ba tun kallon data masa lokacin da ya tsaya a gurin. Yaji babu dadi ganin irin kallon data mishi tamkar bata taba sanin shi ba. Yunkurawa yayi zai shiga ta daka mai tsawar da saida fateema ta jiyota daga cikin gida ta leko da gudu tayi turus a bakin kofa tana kallon Abdul din irin duban kaskanci da me kazo yi.Ganin babu wanda yayi magana a cikin Ameena da fateema dai ya soma cewa, Ameena na rokeki da girman Allah ki saurare ni kada ki juya mun baya nayi nadamar laifin dana aikata duk dama ke kika janyo da kika tsaya kika saurari wani wanda ba muharramin ki ba dan Allah ki mun afuwa.Dakata……….Fateema tace sannan ta cigaba, malam kai waye kuma daga ina kake sannan waya turo ka? Tun wuri kaja kafafun ka kabar kofar gidan nan idan ba haka ba wallahi zamu hadu ni da ita mu saba maka, kuma bari kaji da kake maganar addata ta tsaya da wani kai wani irin tunani gare ka da bazaka iya tsayawa kayi bincike akan abuba said kawai ka dau hukunci, wannan mutumin da kake magana nice nan wacce ya biyo kuma ban tsaya sauraren shi ba saboda sanin halin bakar zuciyar ka kada ka haure mun ‘yar uwa da fada amma duk da haka bata tsira ba koda ya suffanta maka kamanninta bai kamata ka tsaya kayi nazari ba? Duba da kamannin da muke da shi ni da ita? Amma ka sani rabuwarku da ita bai rage ta da komai ba face alkhairin daya zamar mata kuma ina mai gargadin ka da babbar murya akan zuwa kofar gidan nan domin bamuda wata alaka da kai ina fatan ka fahimta….Dumbin mamakine da tsoro suka kama shi ganin yadda fateema yarinyar da a baya take girmama shi take fada mishi maganganu son ranta cikin izza da isa, amma koba komai shiya ja ma kansa sannan abunda ya dada sanyaya zuciyar shi shine fadin data yi cewar Ameena bata da alaka da wancan mutumin daya saketa domin shi sai hakan ya zakwanye duka sauran kwarin gwiwar shi, basu ankara ba said ganin shi sukayi gurfane a gaban Ameena yayi kneeling gwiwowin sa duka a kasa ya hade hannayensa guri guda kwalla suna taruwa a idanunsa yace Ameena na yadda na amince nayi kuskure na kuma zartar da hukunci cikin gaggawa da rashin sani amma wallahi bana nufin ki da sharri har cikin zuciyata ki yarda dani ki dawo mu gina sabuwar rayuwa mai tsafta na miki alkawarin zan sauya duk dabi’un da baki so a tattare dani dan Allah.Kamar bazata ce wani abu ba amma tayi karfin halin fadin, Abdul kenan. Ta fada tare da sakin karamin murmushi ta dora da cewa ina kyautata zaton ka manta saki nawa ne a tsakanin mu ba domin haka ba na tabbata baza ka zo gabana kana irin wadannan maganganun ba zai fi maka sauki ka tashi ka wuce saboda babu sauran zama a tsakanin mu koda ma akwai bazan iya komawa gidan kaba. Tana gama fadin hakan ta juya masa baya ta hau aikin da bata shirya ma yi ba. Hankalin shine ya soma tashi sosai jin wai babu sauran zama a tsakanin su cikin muryar tashin hankali yace, fateema dan Allah ki tayani bata hakuri ki taya ni lallashinta nasan bacin raine yasa take fadan haka amma ai zamu iya komawa auren mu ko malamai zan bincika don ki kara yadda dani amma dan Allah kada ki mun haka ki taimake ni idan babuke a cikin rayuwata zata zama babu amfani…..Fateema tayi caraf tace babu ruwana a cikin zancen ku, da can kasan da hakan ka aikata abunda ka aikata din?…………. .KUYI HAKURI INA CIKIN UZURI NE SHIYASA NA DAGE NA RUBUTA WANNAN DIN KUYI MANAGE DIN WANNAN PLS, INA KAUNAR KU HAR KULLUM.EESHERT ADAMU



