Hausa novels

Harijin Sarki Page 4 Romantic Hausa Novel

Shuuuu…… Kamar ɗaukewar ruwan sama taji wannan murya me amon sauti irin na sadaukai ta ɗauke, Zuciyarta taci gaba dayi mata luguden dukan data fara tun farkon buɗe file ɗin, jikinta na rawa irin ta wanda ya haɗu da bazata ta rashin tsammani tare da juyawar kai da tunani a lokaci guda. Daƙyar kamar wacce aka jonawa shorck aka cire ta iya jan jikinta ta ɗaga hannunta cike da firgici ta rufe wannan File ta kai hannu ta ɗaukeshi a ɗan karfafe ta nufi inda yake ajiye tun farko ta ɗorashi ta koma ta zauna bisa kujerarta tayi tsaiii cike da zullumi fargaba da tashin hankalin wannan abu da aka sanar da ita daga buɗe File, ta kasa taɓuka komai duk lakar jikinta ta tsinke haka ta yini a wannan office hatta petiant ɗinta yau gani take musu na wanda yake bukatar a ganshi shima.Fahimtar idan ta cika takurawa gangar jikinta wani ciwon zai iya ratsa garkuwarta ya sabbaba mata kai juriyarta ƙasa yasata Miƙewa daidai lokacin da agogo ke buga huɗu da kwata, ƙofar ta buɗe tana shirin fitowa ana turo ƙofar tayi baya da sauri jikinta na ɗaukar wata rawa saboda shigar idanunta cikin na wani ƙasaitaccen mutum me fuskar mazan fama wanda yake sanye da kaya irin na Mafarauta fuskarsa a ɗaure tamau kamar tasowar hadari, ta ratse ta bashi hanya ya shiga yana ƙarewa office ɗin kallo Tsaf ya sauke idanunsa a kan Samha da yanayin mutumin ya firgitata, amma ta dake don nuna jarumtarta, takowa yayi a sannu a hankali ya iso gabanta yace “Gaisuwa da fatan alkhairi yake wannan ƙwararriyar likita tabbas ɗazu muna zaman fada Sultan ya ganki cikin idanunsa saƙo yazo masa kamar yanda yazo masa, an tabbatar masa warakarsa na hannunki kamar yanda kema duk ƙasar Morocco shi kaɗai ne zaki samu sakamakon bincikenki a tattare dashi, ya umarceni da na taho dake Amzir yanzu domin ki bashi maganin matsalarsa” Ja tayi da baya da sauri, wannan mutum yayi murmushi me nuna izza ya shafa gashin bakinsa yace “Sunana Yadam babban hadimin Sultan Rashid muna bukatarki tabbas muna buƙatarki sannan zamu ninka Miki albashinki” janyewa tayi, wasu siraran hawaye na shirin zubo mata tayi saurin tarewa a gun ta kuka rauni ne bata son sakar rauninta ga kowa, da wannan tace “Zan…. Zan iya neman izini a wajen shugabanni na?” Jinjina mata kai yayi ta kuwa fice da sauri yabi bayanta.Office ɗin Dr Razeen suka shiga yana ganinta ya miƙe idanunsa yayi ja ya nunata da yatsa yace “Meyesa kike da taurin kai da rashin bin umarni? Saida nace Miki Karki buɗe wannan kundin bayanai amma Saida kika buɗe, me zan iya yi Miki Samha? Banda abinyi a gareki, hatsarin dake tattare da wannan file yasa ban haɗa Miki dashi ba ke kuma kikaga hakan baiyi Miki ba tabbas kinyi ganganci kinyi kuskure” rikicewa tayi da kalaman Dr Razeen tace “Wlh banyi tsammanin akwai wani ɓoyayyen duhu cikin wannan file ba, na ɗauka shima Normal rashin lafiya ce, don Allah Yallaɓai…..” Ɗaga mata hannu yayi yana kallon fuskar Yadam da ke kallon agogon hannunsa yace “Lokacinki ya ƙare Likita Sultan baison jira” kallon Dr Razeen tayi da yayi ƙasa da kanta hawaye ya shirin zubo mata tace “Dama haka aiki A babban Asibitin ƙasa yake rayuwa da rashin ƴanci rashin zaɓi da rashin makoma, indai hakane Yallaɓai na haƙura da aikin gabaɗaya zan cike takardar barin aiki….” Murmushi Yadam yayi yace “Idan kikayi hakan zamuji daɗi kuma zamu gasƙata kinsan aikinki dama aiki biyu a lokaci guda bazai yiwu gareki ba” kallon Yadam tayi ta kuma kallon Razeen cike da sallamawa ta juya ta fita da sauri, Yadam ya riƙo hannunta ya nufi wata mota ya buɗe ya sanyata a ciki ya shiga, yana shirin tada motar Dr Razeen ya iso ɗauke da wannan File ya ɗora mata a cinyarta ta ɗago suka haɗa idanu ya ɗaga mata hannu cike da tausayin wannan aiki me wahala data ɗaukowa kanta, koda yake zataji daɗi a lokacin da tsoro ya saketa ta gane ɓangaren da takeson yin bincike akai ne, da wannan Yadam yaja mota suka lula titi Zuciyarta cike da saƙe saƙe tare da kudurcewa a ranta zatayi aikin ne kawai in taga zata iya idan bazata iya ba kuma zata barshi ta kama harkar gabanta.A hankali sautin Muryar ɗazu ya fara dawo mata cikin ƙwaƙwalwa, zata je ta tunkari ƙaddarar data buɗota da hannunta, zata haɗu da kaddarori mai kyau da mara kyau, to wacce irin ƙaddara ce a cikin duba mara lafiya? Gabanta ne yabada wani dam lokacin da Muryar ta dawo mata tana sanar da ita Yanada matan aure uku yanada Kwarkwara huɗu daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana yana kwanciya da dukkanin matan nan nasa guda bakwai kuma kowacce mace saita fita daga hayyacinta sannan ake fitowa da ita wata ta shiga, yanzu haka matarsa ta aure ɗaya ta mutu hakama Kwarkwara ɗaya saboda wahalar da sukesha wajen kusanci dashi”………Shigarsu Emirates Road ya dawo da ita hayyacinta gurin iyakar hasashe bazai fasalta haɗuwarsa ba an ƙawata gefe da gefe da tsakiyar titin da manyan bishiyun dabino masu kyau waɗanda akayiwa kwalliya da fenti kala kala masu burge ido da ƙawata zuciya An zuba shimfiɗun carpert don takawar me tafiyar kafa ga wasu manyan fitilun zinariya da Andalusian tiles sai ɗaukar idanu sukeyi kamar a masallacin Alhambra, iya wannan titi aka Barka da kallo to shakka babu zaka nemi damuwa a zuciyarka ka rasa domin duk wata nau’i na damuwa zai ɗauketa.Kowacce kusurwa ta wannan Titi soji ne da dukkan wani nau’i na jami’an tsaro suke gadin wannan Daula, wata katafariyar ƙofa da iya bayani bazai wassafawa mai karatu haɗuwarta ba, nan Yadam yayi Horn Sarakan ƙofa suka buɗe suka shiga nan Samha ta tabbatar da ita yar ƙauye ce haihuwarta a Fes ba yana nufin itan wayayyiya bace domin kuwa kanta juyewa yayi saboda kallon wannan alatu da ke narke cikin wannan gida na sarauta.Sunyi tafiya me tsayin gaske daga farkon wannan get aka kuma buɗe wani suka shiga aka kuma buɗe wani suka kuma shiga, cikin na ƙarshen harda Roundabout haɗaɗɗe wanda aka ƙawatashi da wata haɗaɗiyar takobi, sukayi wani shataletale suka kuma nausawa sannan suka shiga Fadar Harem wadda anan ne Sultan da iyalansa suke zaune, tunda suka shigo wannan area ta Iyalan Sultan suka fara cin karo da Barori bayi da kuyangi sunata kai kawo gashinan gini ne sashi sashi a wajen bayan an wangame musu ƙaton get ɗin sun shiga kenan, nan ma basu tsaya ko ina ba Saida suka dangana da wani ɓangare aka sake buɗe musu get suka shiga wayyoh Allah aljannar duniya.Tuni Dr Samha ta manta da wata damuwa ta dolen da akayi mata na zuwa wannan fada ta farajin a ranta lallai itan zaɓaɓɓiya ce cikin zaɓaɓɓun bayin Allah da ta kasance a wannan guri, parking Yadam yayi ya kalleta yace “Ma iya shiga likita, babu musu kuwa ta fito domin ta matsu taje ƙarshen gidan. Takawa suka farayi tana rungume da file ɗin da Dr Razeen ya bata da kuma system ɗinta suka fara tattaki abinda ya bata mamaki babu kowa a harabar wannan guri, wata haɗaɗɗiyar ƙofa da aka ƙawata adonta da zallar ruwan gold da Azurfa suka nufa suna zuwa Yadam ya taɓa Bell sau ɗaya ƙofar ta buɗe suka shiga ciki wani irin haske ne me saukarwa da zuciya nutsuwa da kasala haɗe da wani sirrintaccen ƙamshi me kashe zuciya da sanyi me sanya bacci suka ratsa gangar jiki da ruhin Samha ashe ba nan kallo yake ba Saida suka ratsa suka shiga wani parlourn shima yana yafi na baya a haka Saida suka ratsa parlour uku a na huɗun ne Samha ta daidaita nutsuwarta jiyo Muryar wata mace tana ihun neman agaji tana kuka tana faɗin wallahi tallahi na gama auren nan Sultan Na gama aurenka wayyoh Allah Pupsy na wayyoh shikenan yau ma ya farkamin Pupsy……..”

Back to top button