Labarai

Mashahuri Book 1 Complete

Description/Story:

Mashahuri Book 1  Complete Hausa Novel Document Written By Binta Umar Abbale

 

Description

 

*1*

 

 

Nutsastiyar yarinya ce take tafiya gefan titi tana sanye da kayan makaranta Wanda kana ganin su kasan na isilamiya ne yadin toyobo blue black Riga doguwa da dogon hijab har ‘kasa kafarta cikin safa fara da takalmi plate baka ganin komai a jikinta sai ‘kwayar idonta cikin nutsuwa take bin gefan titi domin isa gidan su dake cikin unguwar Shagari Qutears tafiya take a tsarge! Domin tasan kallon da jama’ar gari suke wa masu irin shigar su mussaman matasan unguwar su in suka zo shigewa har ihu! Suke musu suna fad’in”Allah a baki fir’auna a zuci! Sam basa tanka musu sanin da suka yi cewar yin hakan zubewar mutumci ne, to shiyasa take tafiya tana hard’ewa kasancewar a bokiyar tafiyar ta bata zo ba, anyi musu mutuwa a cikin gari sun tafi gaisuwa ita da ‘yan gidan su. Aikuwa tana shigowa cikin layin su matansa da suke zaman kashe wando suka fara yi mata d’an kira! “Hi ke ‘yar gidan Arrama Sarkin ‘kauli Allah yace Annabi yace hahahahaha.”! Suka ‘karashe maganar tasu suna dariya cike da sha’kiyan ci.

Hanifa taji zuciyar ta na yi mata wani irin suya ta rasa me mahaifinta yayi wa jama’ar unguwar su suka d’auki karan tsana suka d’ora masa yaran su da manyan su, ko Dan ya kasance mutum mai tsoron Allah mai hana aikata ‘barna kullum yana tunasar dasu abunda Allah da Annabi suka umarci bawa yayi, shine dalilin da yasa suka tsane shi, ita kad’ai take wannan zancan cikin zuciyar ta har ta isa gida.

Tun daga soron gidan nasu take jin saurin muryar mahaifin nata yana karatun al’kurani mai girma cikin ‘kira’a mai da d’in saurare.

Cikin nutsuwa ta tu’be takalman ta a gefe guda ta zare safunan ‘kafarta a hankali ta shige shi, cikin rumfar su ta shiga inda ta tadda mahaifiyar ta wacce suke kira da Ammi tana zaune kan kafet din dake shimfede a rumfar da farantin wake a cinyar ta tana gyarawa, cikin nutsuwa tace” Ammi sannu da gida.”

A nutse mahaifiyar ta ta tace”Yawwa Hanifa kin dawo.” Tana ‘kokarin cire ni’kaf din fuskarta tace”Eh Ammi yau ni kad’ai naje makaranta na dawo gida ni kad’ai.! Cikin shagwab’a ta fad’i maganar.

A hankali Ammi tace”Mu bari Abbu ya kammala karatun alk’urani sai muyi maganar.” Hanifa ta d’an zumb’ura ‘karamin bakinta cikin shagwa’ba ta mi’ke d’akin dake cikin rumfar ta shige domin cire uniporm d’in jikin ta.

 

 

 

*2*

Abbu sai da ya had’a izifi biyar sannan ya rufe al’kurani kana yayi addu’a kamar yanda ya saba ya mik’e a nutse yaje ya d’auki buta dake cike da ruwa a tsaya jikin window yana duba a suwakin sa. Alwala yake so ya d’aura ganin lokacin sallahr magriba ya gabato saura bai fi minti goma ba a yi kiran sallah.

Jin motsinsa jikin window d’in yasa Ammi mi’kewa da sauri ta futo tsagar gidan hannunta ri’ke da da a suwakin nasa tasan shi yake lalube jikin window din tace” Abbu ga asuwakin naka na d’auke maka d’azu Dana ga ‘kwarika suna yawo a gurin.”

“Masha Allah Halimatu Allah yayi miki albarka ina mutukar alfahari da kasancewar ki mata a gare ni ha’kika kina d’aya daga cikin matayen da manzon Allah (Slw) ya fad’a saboda duk suffofin ki sun nuna ke d’in mace ta gari ce.”
Abbu ya fad’i maganar bayan ta ‘karbi a suwakin hannunta fuskar sa cike da annuri.

A ko da yaushe kalmomin yabo da godiya ne suke futowa daga bakin mijinta zuwa gare ta. Baka ta ta’ba zama da Abbu na minti biyar bai fad’a maka Allah da annbi sunyi hani da aikata fajirci ba, tunda suka yi aure dashi basu ta’ba samun sa’bani ba a tsakanin su a ko da yaushe suna zaman lafiya da juna har Allah yasa suka haifi yara biyu kacal namiji d’aya mace d’aya Nasir shine babba sai Hanifa tsakaninsu akwai tazara sosai shekaru goma sha biyu ne a tsakinsu A halin yanzu Hafiz yana da shekaru ashirin da bakwai a duniya ita Hanifa Yanzu shekarun ta goma sha bakwai a duniya kuma har yanzu Ammi bata ‘kara haihuwa ba ko b’atan wata bata ‘kara yi ba tun bayan haihuwar Hanifa haka suke yin rayuwar su cikin ilimin addini da sanin ya kamata.

Kamar yanda ya saba bayan idar da sallahr isha’i yana zama ‘kofar gidan shi yaja carbi kuma yana kallon yanayin yanda matasan unguwar suke yin rayuwar su, mutukar yaga abunda bai yi masa ba ko yaga ana ‘kokarin a sa’bi Allah to babu shakka sai yayi magana akai, ta inda su kuma zasu fara yi masa dariya kamar yanda suka saba suna nuna shi da hannu cikin sha’kiyan ci. To yauma hakace ta kasance yana zaune kam daddumar shi wasu matasa uku suka ‘karaso gurin da yake ko wanne da littafi na addini a hannunsa, kamar gaske suka mik’a masa hannu shima ya mi’ka masa nashi suka yi musabaha kamar yanda addini ya tada na, Abbu ya nuna musu gurin zama da hannunshi yana fadin “Masha Allah bisimillah Ku zauna mana.” Zama suka yi kamar yanda ya umarce su, suna sinne kai domin sun San da sha’kiyan cin da suka zo gurin sa. Shi kuwa Abbu tufafin jikinsu yake kallo gami da yanda suka tara uban gashi a tsakiyar Kansu yayi wani irin tozo biyu daga cikin su ma har da d’an kunne a kunne su abun ya bashi mamaki sosai

Cikin nazarin su Abbu yace.” Alhamdullahi ala kulli halin! Samari me yake tafe daku? Da alama kun zo d’aukar darasi ne.”? D’aya daga cikin su yace.” ‘Kwarai kuwa Arrama munzo mu samu ilimin jima’i a gurun ka Wanda a hausance kuke kira da saduwa turawa kuma suke kiran abun da sexcual.”

Abbu yaji wani irin nauyi da kunyar maganar ta rufe shi ko da wasa bai tsammaci wannan maganar ba daga gare su. Sunkuyar da kansa yayi yana nazari.

Wanda yayi maganar yace.” Arrama! Munzo a shirye gamu da littafan mu muna ‘bukatar d’aukar darussa kan harkar.”

Abbu ya d’ago kansa a nutse Yana so yaga fuskar yaron da yake masa wannan maganar me tsauri. Kasancewar gurin babu wadattacan haske yasa bai ga fuskarsa sosai ba, sai ya d’auki wayar shi dake aje gefe ya kunna torchlight d’in Yana haska su. Take ya gane yaron…. Bazai tab’a mance abunda ya faru tsakanin sa da yaron ba shekaru hud’u da suka wuce fuskar yaron baza ta ta’ba ‘bace masa ba.

Gyaran murya yayi yace.” Masha Allah na ainihin wato idan na fahimci abunda kuke nufi kuna so ki samu ilimi da zaku zauna da iyalan Ku lafiya shine abunda kuke nufi ko.”?

 

Shi d’in ne dai ya ‘kara magana a karo na uku yace.” ‘Kwarai kuwa Arrama muna so ka fed’e mana biri har bindinsa domin mun samu labari a gurin jama’ar gari cewa kana bada darasi iri-iri.”

Abbu maganar tayi masa tsauri! Mutu’ka wato sharrin mutanan gari har ta kai sun fara yawo dashi a gari yana koyar da ilimin jima’i babu shi a tunanin sa suna so su ‘bata masa suna ne tunda har ta kai tsagerun yara sun fara zuwa gabanshi suna yi masa maganar banza. Daurewa zuciyar sa yayi yace.” Cikin ku waye zaiyi aure da har kuke so Ku San ilimin jima’i.”

Shi d’in ne dai ya ‘kara magana kamar d’azu a tsaye yace.” Sanin waye zai yi aure a cikin mu bai dame ka ba Arrama mu dai kawai munzo nan domin ka warware mana komai akan harkar mu biya kud’in ka Ya shaik.”! Ya k’arashe maganar sa cike da sha’kiyan ci

Abbu ya d’ago kansa a nutse yana kallonsa, shi d’in ma kallonsa yake da tsayyayun idanunsa na mashahuran ‘yan duniya tsayayyun ‘yayan gata Wanda suka samu d’aurin gindi a gurin iyayen su.

File Name   Mashahuri Book 1 … Hausa Novel
Title   Mashahuri Book 1 Complete
Author    Binta Umar Abbale
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    1/11/2024
File Size    214 KB
Format Size    TXT
Book Price    Paid
Phone No 08089965176
Download Mashahuri Complete Novel Document By Binta Umar

Click the below green button to read the novel online

READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button