Novel Document

A Mafarki Na Santa Hausa Novel Wattpad

A Mafarki Na Santa Complete Novel Pdf By Faeezah

Description/Story:

A Mafarki Na Santa Complete Hausa Novel Document Written By Faeezah BG

 

Description

Natsatssiyar budurwa ce ke tafiya anatse bata kallon komai face inda take sanya kafafunta, tayi nisa acikin tafiyarta kenan ta tsinkayi muryar wata budurwa na kwala kiran Halee! Halee! da jin wannan murya ta budurwar dake kwala kiran Sunan halee ko ba,a fada mata ba tasan khady ce tsayuwar ta da minti biyu sai ga khady ta iso inda take atsaye.
Isowar khady keda wuya ta furta haba Halee kinsan bakya da issashiyar lafiya ya za,ayi kije Aiken baba ta ta maimakon ki fada mata gaskiyar cewa baki da lafiya nasan zata k’yaleki ni sai intafi kinga ko yanzu gudo wa nayi bayan bayan tashiga bandaki,nasan da kin sanar mata da ni sai intafi koh haka ke da dadi ga uwar rana gashi bakya da lafiya,har taga ma mitar ta kyakkyawar budurwar nan da aka kira da halee bata tanka mata ba.. Daga ni dai yarinyar miskila ce😄 chan bayan kamar minti biyu haka ta cigaba da tafiyar ta kamar bataji abunda khady ke fada ba duk da kuwa tana jinta rass kuma tasan tabbas ko ba,a fada ba khady gudowa tayi tabiyo ta.
Da khady taga alamar ba tsayawa zatayi tabata kudin aikar ba na baaba tsaibe,kuma taga alamar yan miskillancin sun motsa dole haka tabita suka cigaba da tafiya atare har suka iso kantin da zasu yi siyayyar ta kayan miya
Sallama sukayi atare amsa musu sallamar tsohon dake tsaye akan tebir na kayan miyan yayi cikin sakin fuska Dan dama baba tsohon yasan su musamman halee ya saba da ita sosai tunda kusan kullum sai an aike ta yin cefane da sauran aikace aikacen akasuwa.
Washe baki tsohon yayi yana furta a,ah Haleematu sadiya ce kayataccen murmushinta tasaki jin ya ambaci cikakken sunanta Wanda mutun daya ne ke kiranta da wannan Sunan sai kuma mutun daya Wanda bata San ko wanene shi agareta ba Amma tabbas aka ambaci cikakken sunanta tana jin wani iri ajikinta
Muryar baba tsohon ce tadawo da hankalinta agaresa yana furta na nawa za,a bada cikin Dan murmushi ta furta baba tsohon ina wuni lafiya,ita ma halee haka amsa musu yayi duka yana dariyar halee aransa najin ga tambayar da yayi mata ga abunda ta furta masa shiyasa yarinyar tashiga ransa Dan akwai tarbiya gata kamila anatse kara mai maitawa yayi” na nawa za,a bada”cikin Dan yin kasa da kai ta furta acikin zazzakar muryar kamar ana busa sarewa ko algaitu gata da sanyi Wanda intana magana zakaji har tsikar jikin ka natashi na Dari uku da ta furta ne yasanya ni dawo wa daga sumar tsayen danayi tun lokacin da ta buda baki ta gaisar da tsohon.
Toh baba tsohon ya furta aleda ya saka musu baka ya mika musu sallama sukayi masa sukayi wucewar su, suna tafiya khady na zuba uban surutu alokacin da ita kuma Halee take ta zullumin komawar ta gida Dan tasan gamuwar su da Babah Asabe bamai kyau bace dan tasan sai ta mata fadan dadewar ta duk da dama ta saba,Amma yau da yakasance batajin dadin jikinta tana fama da matsanancin ciwon kai sai take jin shakkun yadda zata iske gidan,tana cikin wannan tunani sai ga hawaye shar😢 a idanunta gwanin tausayi Khady data lura da yanayin da take ciki ne duk da ba bakonta ganinta hakan Dan danan hankalinta yatashi Dan tana mugun son halee kamar jinin jikinta,da tausayinta cikin tausayinta ta furta haba Halee meyafu kuma, dan Allah kitsaida hawayen nan suna Sosa mun rai kuma kinga kan hanya muke kiyi hakuri nasan damuwar da kike ciki bata wuce sanin ko ke wacece bah da damuwar baabah ta ‘baaba Asabe’ kiyi hakuri in sha Allah komai zai zamo tarihi Halee nah hawayenta ta share mata wayenda ke tsiyaya a I danunta tana girgiza mata kai alamar ta tsayar dasu da kyar ta tsayar da hawayen ta ganin damuwa kwance akan fuskar Yar uwarta!tafiya suka cigaba da yi kowa da abun da yake sakawa aransa,babu Wanda yakara furta uffan har suka iso gidan,
Dan madaidaicin gidane suka tsaya kafin su shiga cikin dar dar musamman Halee gidane dai dai na talaka mai rufin asiri ginin bulo da filista zauren gidan suka tsaya suna shawarar Wanda zai fara shiga domin gudun abunda zasu tarar dakyar dai dukansu sukayi shahadar shiga da sallama abakunan su
Sallamar su ta ta katse ganin Baba Asabe na mitar rashin dawowar Halee akan lokaci da kuma fitar Khady bada saninta ba,
A hankali halee take ta durkusa gurin Yar matashiyar matar da bazata wuce shekara talatin da uku ba a duniya!Baba Asabe kenan wadda Sunan ta yake Lauratu amma mafi yawan mutane suna kiranta da Asabe saboda masifarta da ankira Baba Asabe za,a San itace Dan Sunan ta kaf ya bace.
Cikin sanyin muryarta da yazame mata jiki tace baaba ga kayan miyar kinga na dad’e koh wallahi Baba tsohon ne mun tarar da layi agurin sh…uwar hararar da baba Asabe ke sakar mata ce tasan ya ta yin shiru badan ta shiryawa hakan ba,dama kanta adone yake dan bata son kallon cikin idanun manyanta musamman ma na Baba Asabe ….taci karo da hararar da take sakar mata,bata ida ganin tsawon hararar ba ta kara done kanta kasa cikin tsoron abun da zai biyo baya..
Kiran Sunan Allah take yi a zuciyarta Dan tasan yau tata takare sai ta sha rankwashi akai da gori kala kala da zagin da bata so zuciyarta ce taji tsinke tausayin kanta da kanta yakamata.
Bata ida gama tunaninta ba ta tsinkayi muryar Baba Asabe nama khady fadan binta da takeyi abaya inta aiketa duk da kullum haka suke muddin Baba asabe ta aiki Halee to tabbas in Khady tadawo sai ta bita sundawo tare koda kuwa dawowar su daga makaranta ne aka tura Haleen sai ta yi sand’a ta bita…
Baba asabe ce take furta wallahi Hadiza ki shiga taitayinki Dan ubanki na fahimci bakya game zancen da nake maki ace ke kullin sai kinsaka ni yakar baki ehh~bakinta har kunfa yakeyi saboda masifar da ke cinta dama Baba Aabe masifaffiya ce ta bugawa ajarida.

Wai nikam nace dama haka masu suna Lauratu suke ne??😂
Hankalin khady (Hadiza) yayi dubun tashi bata kanta takeyi ba Dan tasan karshen masifar kan halee zai kare. Ahankali ta furta innata kiyi hakuri ke dallah rufe mun baki sha shar banza kawai ana miki gata kina botsarewa,inji cewar Baba Asabe , aikullun haka kike cewa ayi hakuri tau Dan ubanki ki kara kiga yadda yadda zanyi da suyar namanki agidan nan takai karshen maganar tana ban kamata harara
Kiwuce ki cire uniform dinki kizo ki Debi ruwan zafi gasu chan nadora miki amadafa.
Toh Khady ta furta cikin tutse bakinta mai makon ta wuce sai ta tsaya taga yadda za,a kwashe da Halee tana jin tsoron tashin ciwon Yar uwarta Wanda take ganin hard a damuwa kesanya tashin sa,tana mugun son ta da tausayinta, gashi yanzu haka tana fama da kan daya zame mata al ada dan duk yatashi tana wahala sosai wasu lokuttan har suma takeyi inyatashi saboda yadda take samun high temperature.

File Name   A Mafarki Na Santa… Hausa Novel Doc.
Title    A Mafarki Na Santa
Author    Faeezah BG
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Love Story
Published Date    29/04/2024
File Size    325Kb
Format Size    TXT
Phone No
Download A Mafarki Na Santa Complete Novel Document By Momyn Faeezah BG

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button