Zamantakewar Aure

Dabarun Yadda Matan Aure Za Su Tarairayar Miji Cikin Sauki

Dabarun Yadda Matan Aure Za Su Tarairayar Miji Cikin Sauki

Akwai wasu abubuwa da idan matan aure suna yiwa mazajensu za su kara samun kula da soyayya a wajen su. Shi namiji yana son tarairaya daga wajen mace domin hakan yana kara masa kwanciyar hankali da kara bayar da kulawa ga matarsa.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

1. Biyayya ga dukkan abun da ya ce ko ya fada muddin bai saba hankali da ka’idar addini ba, ko da ba kya so bai miki dadi ba kar ki yi masa jayayya a lokacin, ki bari a nutse ki same shi cikin lallashi ki ce ni kuwa masoyina/baban wane/darling dinnan idan an yi fa da matsala da za ka amince ayi kaza.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

2. Idan za ki tambaye shi abu ki tambaya cikin kissa da Jan hankali kuma lokacin da kika fuskanci yana cikin nutsuwa.

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

3. Kada ki dinga shige masa a lokacin da kika ga yana bukatar kadaici ki bar shi zai gaya miki ko menene daga baya.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

4. Idan ya hayayyako yana fada ke kar ki biye masa amma ki karanci waye shi yana son idan yana fada a ba shi hakuri ko kuma shiru ya ke son ayi a saurara shi, idan ya gama lokacin da ya huce sai ki mssa bayanin uzurinki ko ki ba shi hakuri da lallashi, kar ki yadda ki yi fishi lokacin da ya yi fishi.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata

5. Namiji bai son na ci, idan ki ka lallashe shi akan abu ya ki yadda to ki hakura karki nace sai dai ki samo wata hanyar kuma, idan ba haka ba kuma za ku fara zubar da girmanki a gurinsa.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

Kadan daga hanyar lallashin miji da matan aure ke yiwa mazajensu, amma da saura,  daga karshe ki sani lallashi yana samuwa idan da soyayya da kauna, idan namiji bai son ki lokacin da ki ke lallashinsa ma zai iya kulawa ya kara bijrewa maimakon a samu daidaito sai abun ya lalace.

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

Back to top button