Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 11 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na goma sha ɗaya_

…….Tun daga lokacin bata da wani buri sai na ganin ta samu ciki, amma shiru kake ji malam yaci shirwa. Tun tana irga wattani har aka koma shekaru babu amo babu labari. Kwaɗayin samun jika ya fara damun Hajiya Maryam, da kanta ta saka Kainaat da Abaan gaba suka bar ƙasar zuwa asibi. Doctor ya tabbatar musu Kainaat nada ƴar matsala a cikin mahaifa, dan wani ƙurji ne ya fito mata, zasu iya mata aiki, sai dai akwai haɗari gaskiya, zakuma su iya ɗorata akan magani idan da rabo a hakan ma ciki zai iya samuwa. Jin batun haɗari yasa Hajiya Maryam cewa a bata magani kawai, yayinda Kainaat tace ai mata aikin ita dai, dan tana buƙatar haihuwa tako wane hali. Amma sai Abaan ya nuna mata bata isa ba, maganar mahaifiyarsa za’abi. Hakan ya mata ciwo matuƙa suka tattaro suka dawo gida Nigeria ta fara shan magani. Sai dai a hakan shekaru biyu suka sake shuɗewa babu labari, dan haka Hajiya Maryam tace Abaan ya ƙara aure, idan da rabo watarana itama Kainaat ɗin zata haifa musu. Tofa babbar magana, wannan zance ya hargitsa kan Kainaat matuƙa, dan a duniya bayan son haihuwa abu na biyu shine mugun son Abaan da Kainaat keyi. Tana kishinsa na hauka da ko ita mahaifiyar tasa da ƙamwarsa baso take taga ya raɓesu ba, tana dannewa ne kawai saboda irin son da suke nuna mata ga dukiya mai yawa ta mallaka ta dalilinsu. A dalilin wannan batun aure Kainaat ta fara fiddo da wasu sabbin halaye a gidan marasa ƙyau, tun Hajiya Maryam na kauda kai har dai ta fara magana, sai Kainaat ta fara mata rashin kunya. Abu kamar wasa ya fara zame musu kamar gaba a tsakaninsu, har Kainaat na neman raba Abaan da su. Hankalin Hajiya Maryam ya tashi matuƙa, tako miƙe kan ɗanta da addu’a ta kuma hanashi cin abincin Kainaat dan Noor ta kamata tana zuba masa abu ranar a kitchen. Rikici tun yana ƙarami har ya zama babba, a haka akai auren Abaan da sabuwar amaryarsa. Sai dai tunda akai aure Abaan ya gagara kusantar matar tasa, daga baya ma ta fara wani irin ciwo maiban tashin hankali har sai da aka raba auren. Ana cikin wannan rikici labari yazo ma Hajiya Maryam kan ainahin iyayen Kainaat da alaƙarta da mahaifiyar Nadwa. Nan fa aka sake kwasar wani sabon rikici ta tsare Abaan akan ya saketa, dan ba matar aure bace. Wadda zata iya gudun iyayenta saboda suna talakawa ta canja iyaye ai komai zata iya aikatawa idan ta samu dama. Abaan baya ƙetare maganar Mamah, dan haka babu wani ja’in ja yayma Kainaat one shika (🤣inji gwanja ba). Baƙin ciki da ruɗani suka rufe idanun Kainaat ta hau zagin Hajiya Maryam da tabbatar mata sai ta sakata nadama akan raba auren nan, Noor batama san sanda ta wawwanka mata mari ba, yayinda a take nan Abaan ya ƙara mata saki biyu suka zama uku ciff. Abin kamar almara haka suka koro Kainaat a gidan, sai dai da yake bayin ALLAH nan sun gaji arziƙi duk abinda suka mallaka mata basu ƙwace ba, hakama wanda ta sata duk suka barta dan su irin arziƙine gadonsa sukai ba haye ba. Wannan shine dalilin rabuwar Abaan da Kainaat, tunda ta fito kuma bata dai nema iyayentan ba, saima gida data saya ta tare a ciki, suka kuma cigaba da mu’amula da su Nadwa, ga company da Abaan ya bata na kawo mata kuɗu sosai, wanda a yanzu haka shine Dafeeq ke a ciki da kuma burin mallaka shima. Yayinda Kainaat ta aureshi da burin yin auren kisan wuta, tare da wani burin kuma data baima zuciyarta ita kaɗai. Babban burinta kuma shine komawa gidan Abaan, kullum saita masa text message naban haƙuri da safe, da dare kuma na good night daban haƙurin dai. Bai taɓa nuna alamar ya gani ba balle ya kulata, bata iya kiransa kuma alamar ya tosheta, ya kuma ɗauki matakin hana baƙuwar number kiransa. hakama duk wani shifinsa na yanar gizo ya tosheta, amma hakan bai hanata cigaba da bibiyar duk wani motsinsa ta hanyar yaransa ba…..

★★★_____

   Ƴan gidan Baba Hakimi ne sukaima Khadijah karar taruwa a gidan sunata kwantar mata da hankali, dan a cikin kwana biyun nan ta sake wata irin rama da baƙi tamkar ba ita ba. Bata da aiki sai kuka, dan gaskiya tana jin kishin mijinta matuƙa. Matsala ta biyu yanda ya tattarata ya sake watsarwa tun randa ya sanar mata zancen auren zamansu ya sake ɗaukar zafi. Takai yama bar cin abincin nata, ya kuma daina yini a gidan gaba ɗaya, ya koma kwana a doguwar kujera a falo. Hatta yau da zai tafi ɗaurin aurensa harya gama shirinsa ya fito ko kallonta baiyi ba. Sai itace ke binsa da kallo kamar zata cinyesa. Dan yayi mata masifar ƙyau cikin ɗanyar shaddar da ya saka fara tass. Ga hula ya kafa sai ƙyalli yake kamar namijin ɗawusu.
Ana ɗaura auren ya tura mata saƙo kamar haka _(Duk baƙin cikin tanda dai sai munci waina. Masu hassada sai a haɗiyi zuciya a mutu. Dafeeq ya zama angon Hajiya Kainaat. Zaɓi ya rage mutum ya kwantar da hankalinsa a zauna lafiya yaci arziƙi shima ko ya yanki ticket ƙofa a buɗe take)_ sosai jikin Khadijah ya dinga rawa da ganin wannan saƙo, dole ta shige bedroom ɗinta jin zata faɗi ga mutane a gida. Kuka taci sosai tana sake karanta saƙon kamar mai bitar karatu, mamakin Dafeeq na neman halakata. Shin dama haka yake ko yanzu ne ya canja saboda kuɗi? Dan ita saima yanzu take jin wacece ya aura ɗin a wajen ƴaƴan baba hakimi. Sai dai har suka gama hirarsu batace komai ba. Jin kanta na neman fashewa ta haƙura da kukan ta gyara fuskarta ta fito, duk da ba hira take ba tana zaune a cikin su Aunty Kareema dai daketa cigaba da mata nasiha. Gab da magrib suna shirin wucewa gidajensu Dafeeq ya dawo gidan. Daka ganshi kaga sabon ango, dan sai ƙamshi yake bazawa. Sama-sama ya amsa tsokanar da suke masa babu kunya ya shige bayi yin wanka bayan ya shiga ya cire kayan jikinsa yasa jallabiya. Ganin hankalinsa ma ba’a kansu yake ba suka tattara suka wuce zukatansu cike da tausayin Khadijah. Koda ya fito bai kalleta ba, sai ma a gadarance yace ya tashi ta ɗiba kaya a akwati su wuce. Da mamaki ta ce “Ina kuma?”.
A zafafe ya amsa mata da “Ban sani ba. Ban san rainin hankali. Ina faɗa miki ki tashi ki shirya kina tambayata ma ina?”.
Karan farko taji bazata iya haɗiyewa ba ta ja masa tsaki, a tsiwace ta ce, “Babu inda zanje to, aikin banza makwaɗaici kaw….”.
Kafin ta rufe baki taji saukar mari. Bata gama dawowa a hayyacinta ba ga sake sauke mata wani. Sai da yay mata uku a jere masu gigitarwa sannan ya nunata da yatsa yana magana tamkar zai haɗiyi harshensa. “K! Dan uwar ubanki har kin isa kirana kwaɗayayye? To ubanki mai ƙaton kan nan da shegen miskilanci ne kwaɗayayye dan uwarki ƴar iska. An gaya miki nima da sona zan ɗaukeki zuwa inda nake ne banza daƙiƙiya baƙauya da ko secondary bata iya ya gama ba akan saurayi. Wlhy badan Hajiya ta dage atare dake gidan can ba na tafi sai kinyi wata bama ki ganni ba balle ki iya mun rashin kunyarki na rashin tarbiyya. Zan kuma tabbatar miki dani ƙwaɗayayyen ne ƴar baƙin ciki da hassadar cigaban wasu. Yanda ubanki ya ƙare a talauce haka kike fata nima na ƙare ko. To sai dai ke ki ƙare a wahale wlhy, dan sai kinje, kuma zakiga hukuncin da zan miki”.
Wani irin kuka mai cin rai da zuciya Khadijah ta durƙushe tanayi. A karo na farko tunda suka baro gida take jin kewar yin nisa da iyayenta. Gatan da sukai musu ita da ƴan uwanta ya shiga dawo mata a rai. A wannan halin Dafeeq ya fito cikin sabon ɗanyar shadda yana baza ƙamshi….

_________★

Tuni anguwar su JJ ta ɗauki ɗumi akan abinda ya faru daren jiya. Dan su baba da wanda suka bisu gulma da ƙyar suka sami kansu a safiyar yau. Masu baƙin surutu suka kasa haƙuri suka shiga bada labari. Kowa jinjina al’amarin yake da mamakin mi JJ ya aikata haka shi kuwa da zafi? Babu mai basu amsar nan sai JJ ɗin, shi kuma yana kwance babu lafiya. Dan mafi yawansu ana idar da sallar asuba mazan anguwa da sama suka shiga gaisheshi kamar yanda al’adar anguwar take. In dai baka da lafiya aka kuma sani to maza kan shiga dubaka bayan kowacce salla daga massalaci.
Duk wanda ya shiga yakan samu JJ na kuka da ihun jikinsa naci da wuta. A taimakesa a zuba masa ruwan sanyi kada ya ƙone. A zahiri kam babu wani abinda ke faruwa da shi. Hankalin ahalinsa gaba ɗaya ya ƙara tashi, a take yara da manya suka taru a kansa ana masa addu’a. Da ƙyar aka samu kansa kusan sha ɗaya na safe. Yay shiru sai wani irin mugun zufa da yake yi dan cikin duk bayan mintuna ashirin yakam jiƙe abinda aka shimfiɗa masa kamar wanda aka watsama ruwa, sai an ɗauke an canja da wani. Yayi wata irin muguwar rama ta tashin hankali jikinsa yayi baƙi sosai duk da kuwa JJ fari ne sol da shi. Tuni ƙyawun fuskar nan tashi ta gushe, baƙin sajen nan dake ɗaukar hankalin ƴammata kamar ma ya fara furfurar wahala. Baka iya hangen komai a tattare da JJ sai ƙwala-ƙwalan idanu da haƙora tamkar dillalin aljanu. Baba dake share hawaye cikin kasa daurewa ya ce, “Jazool mika jawoma kanka haka ne da zafi? Mika aikata ne da har muma yake neman shafarmu? Jibeka dan ALLAH cikin kwanaki uku kacal halittarka ta canja gaba ɗaya. Jazool ka faɗa mana mika aikatama bayin ALLAHn nan? Wacece Anoosha? Miye haɗinka da ita da ka shiga irin wannan bala’i a dalilinta ne?”.
Duk da azabar dake ratsa JJ da wahalar ciwo a firgice ya kalli Baba jin ya ambaci sunan Anoosh. Yaya Inusa ne ya karɓe da faɗin, “Ba kallonsa zakai ba Jazool, ka sanar mana wacece Anoosh? Kamar yanda baba ya buƙata. Minene haɗinka da ita? Dan bayin ALLAHn nan sun tabbatar mana da har sai ka sanar mana wacece Anoosh sannan zasu bada matarka. Dan ALLAH ka sanar mana ko muma ƴan uwanka zamu sami nutsuwar zukata da kwanciyar hankali. Jiba kaga Baba ko taka ƙafarsa baya iya yi saboda wahalar da mukasha tsakanin safiyar jiya zuwa yammaci. Jibi fuskar Mujetapha yanda ya kwaye kumatu saboda gudun ceton rai. Kalleni kaga raunuka biyu naji a tsakanin hannu da gefen cikina duk a dalilin gudun kuɓuta daga gidanka. Dolene akwai abinda ka aikata Jazool, in ba hakaba miyyasa saboda kai duk zamu shiga bala’in nan. Hatta su baba liman basu tsira ba suna gidajensu suna jiyyar kansu. Mazan anguwar da gidanka yake ɗai-ɗaine jiya basuyi fitsari a wando ba banda tashin hankalin da idanunmu ya gani. Jazool wacece Anoosh! Mika aikata mata ne!!”.  Yaya Inusa ya faɗa cikin ƙaraji da kaushin murya jikinsa har yana rawa. Shima JJ ɗin rawa jikinsa ya farayi yana mai kallon duk wanda ke ɗakin. A ƙufule Yaya Mujee ya amshe da faɗin, “Garama ka faɗa Jazool, kai dolene ma saika faɗa mana mika aikata. Dan tace idan ma ka ɓoye wani abu tana anan tare damu dan akoda yaushe tana kusa da kai. Ya rage naka ka faɗa da arziƙi koka faɗa da wahala. Dan kaga dai yanda ka koma a cikin kwana uku kacal tamkar wani dilallin aljanu. Har muma ana neman sabauta mana rayuwa a dalilinka”.
Wasu irin hawayene masu zafi suka shiga ziraroma JJ a idanu. Tamkar wanda ake controlling murya na rawa ya ce, “Anoosh budurwata ce. Mun haɗu a ranar babbar salla ta shekarar 2020 da ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Dan fitowarmu da ga salla kenan ni da su MB a anguwar su Gwaggonsa da mukaje gaidawa…….”✍️

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 12 By Billyn Abdull Complete

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button