Hausa novels

Matar Hariji Page 25 Romantic Hausa Novel

Shafa fuskarta Inna tayi tace “yaushe Ina aka tabayin haka autar wuro goggonki bata zuwa sunan danki ai Baffa kuwa baya gari yana Maqarfi” gefe tayi ta riqe qugu ta zube a qasa ta kama kuka rarrashin duniya taqi yin shiru saida aka Kira Lameer yana yan awaki ya tafi siyan abin hakika aka fada masa sarqa me rikicin gangan ta rikice fah.Babu shiri ya basu kudin ragunan daya siya aka sanya masa a mota suka tafi Salees yanata yimasa tsiya yayi murmushi yace “bakasan yanda nakeji bane nasan tabata akayi kuma bari muje kaji yanzu idan bani dinba ko waye zaizo bazatayi shiru ba yini zatayi tana kuka”Dariya sosai Salees yayi yace “wannan raino naka bansan yaushe zai qare ba kayi rainon yaya kayi rainon uwar yaya” shidai bai qara cewa komai ba har suka isa gdan ya qyale Salees da sauke ragunan ya shige ciki ya hangota can qarshen dakin ta hade kai da gwiwa tanata kukanta.Matsawa yayi ya riqota tanajinsa ta sake rushewa da kuka tace “ni ka daina tabani nama daina sonka na daina kulaka kullum kai babu ruwanka da damuwata to wlh babu ruwana da danka nima Gwaggona da Baffana nakeson gani shine kace kada a tahomin dasu ko?” Ta fada tare da kafesa da jajayen idanunta fuskarta harta tasa abinka da farar fata yayi murmushi kawai ya sanya hanunsa ya dagata cak ya nufi dakinta da ita tana zamewa tana cewa ka sakeni banaso ni banaso kowama ya tafi banason ganinsa Gwaggona nakeson gani”Bai direta ba saida yakaita har dakin ya sauketa a gadon ta miqe zata fice yayi saurin cafkota ya kulle qofar ya mayar da ita ya kwantar ya kwanta a jikinta yayi qasa da muryarsa yace “ke bansan yaushe zakiyi hankali ba kema fa uwace yanzu haka Zaki rinqa yimin idan natafi dake American?” Ajiyar zuciya tayi tace “ni bazani ba Gwaggona kawai nakeson gani” kwantar da kansa yayi a kafadarta yace “yanzu kuma shine saikin tashi hankalin kowa a gidannan kina gani su Inna ko ruwa sun kasa shs daga zuwansu kin fara nuna musu halinki wato kinaso suje suce har yanzu bakiyi wayo ba a birnin ko?” Shiru tayi batace masa komai ba yayi murmushi yace “banason shirmenki wannan ni dakene zan kaiki kije kiyi sati a gurin Gwaggonki kafin mu tafi amma sai kinyi hankali idan bakiyi hankali ba bazakije ba” Saurin qaqalo dariya tayi tace “namayi daga yau bazan qara ba” kissing dinta yayi yace “yawwa kin bawa Noor abincinsa kuwa?” Qasa tayi da kanta yayi murmushi yace “baki basa ba ko?” Daga Kai tayi yayi murmushi ya fita ya karbo yaron ya miqa mata ya saita mata kansa ta kalleshi ta kalli yaron tace “kamarku daya dashi”Murmushi yayi yace “ba abinda na tambayeki ba kenan ki bawa dana nono nagani” noqe kafada tayi tace “kaje zan bashi ni basai ka….” Wani kallo da yake mata yasata hadiye mgnr ya sanya hannunsa ya zuge zip din rigar ya sanyawa yaron nono ya kama da sauri.Qara tayi saboda zafin da taji, yayi murmushi yace “kokefa amma danki na cikinki ki rinqa yimasa horon yunwa” hawaye takeyi tace “ni kaje banason surutu” miqewa yayi yace “babu komai na gode” ficewa yayi yaci gaba da harkokinsa bai samu zama ba sai da gama da baqinsa sannan ya wucce gdansu yayi wanka ya kwanta.Wayarta ya kira tana gani taqi dagawa yayi dariya itafa a dole laifi yayi mata yasata ta bawa danta nono, yananan kwance yanata tunanin wautarta da rikicinta yanata dariya har bacci ya daukeshi.Tun asuba daya fita bai dawo gdanba gidansu ya tafi ya shiga gurin mahaifinsa suka gaisa yayi masa addu’ar Allah ya raya musu Muhammad Nuraddeen sai lkcn su Inna sukaji ashe Ardo akayiwa takwara sukayita murna kuwa basu taba zataba.Shagalin suna sosai akayi ranar su Inna sunga ikon Allah yanda aka rinqa girmamasu a gidan abin ya tsaya musu a rai musamman Hajiya data rasa inda zata ajiyesu komai nasu na dabanne me jego ta shiga ta fita an kece raini anyi hotuna na uban ubansu.Washegarin suna su Inna sukace sufa tafiya zasuyi sosai Lameer da Hajiya sukaso su bari su qara kwana biyu amma sukaqi hakanan suka hada musu goma ta arziqi Hauwah na kuka suka tafi suka barta kan cewa sai tazo kawo musu Baffa.Sake bada mota yayi da kudi me yawa da kayan sawa atamfofi da lasina yace akaisu har gda, aikuwa yasha ruwan albarka suna tafiya a gaban Hajiya ya sunkuceta yana juyawa da ita itakam Hajiya ta gaji da ganin rashin kunyar Lameer saboda haka ta nufi cikin gda ta barsa da ita tasan indai Hauwah ce ba qarewa zasuyi qlau ba balle yanzu da take ganin yan uwanta sun tafi sun barta……………Direta yayi ya Kama hannunta suka shiga ciki ya zaunar da ita a kujera yace “meye na damuwar nan da yan kwanaki kema zakije kiyi sati guda”murmushi tayi ta saki ranta suka fara hirarsu kafin ya tashi ya fice.Haka kwanaki sukayita tafiya Noor yanata girmansa gwanin sha’awa kyakkyawa dashi son kowa Lameer yana bata kulawa sosai lkcn da tayi arba’in kamar zai saceta haka yakeji saboda qauna a ranar yazo wai yazo ya dauketa ita kuma Hajiya ta kafe akan bazai dauketa ba sai sunje Rugar Sambajo sun dawo, dolece kawai tasa ya hqr saboda bayason tsayawa yana jayayya da Hajiyan amma a matse yake da iyalinsa.Kwananta biyu da arba’in ya shirya musu tafiya hardashi akayi tafiyar zuwa rugar Sambajo itadai Hauwah har sukaje bata iya gane qauyen nasu ba saboda cigaba da qauyen ya samu an zuba musu kwalta har gaban gidansu an dasa musu turakun lantarki gashi memakon taga bukkoki sai taga gidaje ginin zamani duk an zagayesu da bulo, mamaki yasata sakin baki tana kallon ikon Allah Saida taji ana qoqarin karbe mata da sannan ta dawo nutsuwarta ta juyo kadai sai taga baffanta aikuwa tayi wani ihu ta rungushi.Dukka gurin suka kamayi Mata dariya ya tureta yace “kaji yar qaniya da bazatayi hankali ba zata karyani kinje kinci cimar birni kin zama bukekiya dake kauce ki bani guri ni takwarana nakeson gani”Turo baki tayi tace “aidai saida aka sameni sannan aka samu takwaran badanni ba bazaa sameshi ba” sanda Ardo ya wawuro yace “aifa dama nace duk ranar da kikazomin nan saina rade miki qafafu” nan fa suka fara zagaye gurin har Allah ya bata saa ta dafe bayan Lameer Baffa yace “ai shima me laifine ya sacemin autata ya tafi da ita birni ta manta damu lamuni daya zanyi muku da kukayimin takwara”Sauke Hauwah yayi sunata dariya wasan dake tsakanin Hauwah da mahaifinta yafi komai birgesu Hajiya suna shiga dakin Gwaggonta tayi tsalle ta fada gadon Gwaggo tana dariya tace “shekara biyu da rabi ban hau gadon nan ba tun Ina yar qwailata yau gani hard….” Gwabe Mata baki Gwaggo tayi tace “bantaba ganin mara kunyar yarinya irinki ba a gaban mijinki da surukarki zakice danki ko?” Rufe idonta tayi tana dariya Hajiya tace.“Ai rainon Lameer ce abinda yafi hakama zatayi nikam na sabada da rashin kunyarsu kune dai zakusha fama”Kunyace ta lullube Lameer ya kalli hauwa da taketa lalube lalubenta tayi masa gwalo yace “ni kikewa gwalo ko?” Dagowa tayi tace “lahhhh Allah sarki ni baiwar Allah ni ko kallonsa ma banyi ba kiji wai Hajiya nice nakeyi masa gwalo”Inna ce tace “hajiya kina kallon tabara” murmushi tayi tace ai sababbune wadannan yayanma nakeji” Haka suka yini yana manne da ita shammatarsa Hajiya yayi yajata yace “zo ki rakani gdan gonata mugani nakwana biyu banje ba” da haka suka fice yaja motar sukabar qofar gdan dama Noor yana gurin Ardo suna zuwa ya shiga dasu yayi parking suka rinqa zagayawa.Tanata santin gurin yayi murmushi yace “nakine wannan halak malak” juyowa tayi a sukwane tace “ni kuma Abban Noor?” Daga Mata kai yayi yace tukuicin kyautar da da kikayimin kenan, inasonki Hauwah ji nakeyi kamar bazan iya rayuwa babuke ba” Wasu hawayene masu zafi suka zubo Mata ta rungumeshi tana kuka tace “bansan dame zan saka maka ba Abban Noor bansan me zanyi maka ya zama tukuicin halaccinka gareni ba wanne irinso kakeyimin da baya baka damar ganin laifina?”Dagata yayi cak ya nufi wata qofa da ita ya bude ya shiga dakine babba a gyare tsaf katifar ya dauketa ya janye mayafinta ya kwantar da ita yasa hannu zai zuge mata zip ta riqeshi ya dago idanunsa da suka kada sukayi jajir ya kada Mata kai.Hawayene ya zubo Mata yace “ba zanyi miki komai ba Amma idan kin bani hadin kai” bazata iyayi masa musu ba tabbas sunyi qoqari daga ita har shi watansu na hudu kenan wani abu bai shiga tsakaninsu ba sosai suka tsotsi albarkar jikin junansu.Koda Lameer yakai qarshe yaso shigarta Amma taqi ta ma sanya masa kuka iyakar rarrashinsa taqi yimasa Shiru dolensa yayi yan dabaru ya samu yayi release ya miqe ya shiga yayi wanka ya fito yace.“Ai saiki tashi kije kiyi wanka mu tafi” turo baki tayi tace “ni bazanyi wanka anan ba kawai mu tafi” bai kulata ba ya dauki key dinsa yayi waje itama ta miqe ta mayar da kayanta suka fita yaja motar suka tafi bata taba bata masa raiba irin yau.Qiri² yaga samu yaga rashi data barshi da yasamu nutsuwa amma yanzu banda sha’awa babu abinda ta qara masa murmushi yayi na qeta ya kalleta yace “jibi zaki dawo ko?” Wani kallo tayi masa yayi murmushi yace “bazaki wucce hakan ba idan kuma kikayimin wata mgn wlh ranki baci zaiyi kuma a yau sai mun koma dake” Mirgina kai kawai tayi ta rinqa hadiye kukanta suna zuwa ta bude motar ta fice ya tabe baki shima ya fita gurin su Baffa ya tsaya suka qara gaisawa sosai Baffa yakejin kunyar Lameer saboda irin abubuwan da yakeyi musu bazasu qirguba shine ya shige gaba wajen kawo musu titin kwalta da wutar lantarki qauyen nasu shine ya gine musu qauyen yayi musu gidaje na zamani musamman gidan baffan sannan duk watan duniya saiya kawo musu kayan abinci da kudin cefane tun baffa baya karba har ya fara karba.Yanzu gashi yayi masa takwara kuma fada tsakanin manoma da makiyaya ya qare ya shiga ya fita ya sasanta dangin mahaifinsa gidan sarkin Alqalawa da gdan Moddibo Durange kakan Hauwah har an fara hada surukuta bayan tashi da Ardo.Har bakin mota Hauwah ta rako Hajiya tace Mata “saimun taho Hajiya agaida Alhaji har ta juya zata tafi ya cafkota bai wani damu da yawan mutanen dake gurin ba ya hadeta da jikinsa ya dago kanta ya dora bakinsa saman nata ya sauke Mata wani hot kiss.Numfashi yaja da qarfi da saida kowa yajishi ya saketa cikin sarqewar murya yace “ki shirya da wuri zanzo na daukeki” itadai kunya bata bata damar bashi amsa ba ya zaro kudi masu yawa ya tura Mata a hannunta yayi mata bye bye ya wucce ya shige yaja motar suka tafi Hajiya na daga Mata hannu.

Back to top button