Hausa novels

Halysaah Page 72 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 72…Khaleesat ta sauke idonta daga kallonsa ganin for almost 2 minute bai lura da ita ba kallon ball kawai yake da duk attention dinsa, ta ɗan yi kasa da murya tayi masa sallama, juyawa yayi da sauri suna hada ido ya gyara zamansa don kishingide yake saman kujeran, nan da nan yayi keeping straight face ya ci gaba da shan grape dinsa idonsa a kan TV, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlon ta tsaya jikin kujera trying to gather up courage tace “Good evening…” Ya ɗan kalleta, sai kuma yace “Yes?” Ta ɗan langwabar da kai tana kara rungume handbag dinta tace “Ina son zan maka magana ne pls” a takaice yace “I am busy as you can see….” Ta kalli football din da yake kallo, a hankali tace “To shikenan, sai anjima” Tana fadin haka ta juya zata bar parlon yace “Ke…. awa daya zaki yi using kiyi min maganar ne, say what u want to say in few seconds i am listening” Tayi shiru tana kallonsa, after few seconds ta zagayo ta zauna kan 1 sitter tana kallonsa, har a sannan kusan duk hankalinsa na kan TV din kamar baya son missing kwallon da yake kallo, bayan kusan minti biyar ya juya ya kalleta, shi har ya mance tana wajen, yace “Kee fadi abinda ya kawo ki and stop staring at me that way” Tace “To ai naga kallo kake” Yace “Ido ke ji ko kunne? Ina ruwanki da kallon da nake yi?” Ɗan taɓe baki tayi, ita shi yasa bata ma son abu yana hadata da shi, komai sai yayi masifa, ta sauke idonta cikin sanyin murya tace “Dama Abdul ne ya biyoni school yau…” Lokaci daya ya juya ya kalleta, ta sunkuyar da kai, can yace “Waye Abdul?” Ta ɗan kallesa taga kallonta yake, tayi karfin halin cewa “My ex” Shiru ya sake yi, after some seconds yace “In zaki min bayani in details ki bude baki kiyi min and stop wasting my time” Ta ɗan saita kanta ta yanda zata fara koro masa duk abinda Safiyyah tace ta gaya masa, tayi inhaling numfashi sannan ta fara masa bayanin exactly yanda Safiyyah tace tayi, ya rage volume din TV, yana sauraronta attentively amma ba kallonta yake ba, har ta kai aya tana kallonsa, bai ce komai ba for almost a minute as if yana processing duk bayanin nata a kansa, still not looking at her yace “So now what did you want me to do?” Shiru Khaleesat tayi don bata san me zata ce ba, can taji yace “Saki nawa yayi maki?” Ta sauke idonta a hankali tace “Kawai ce min yayi ya sakeni, bayan da na dawo gida kuma aka aiko takarda daga gidansu da saki uku a jiki, amma ba rubutunsa bane” Ajay ya wani kalleta yace “Rubutun ki ne kenan?” Sunkuyar da kanta tayi, ya sauke idonsa kan zoben hannunta dake kyalli, ta ɗan saci kallonsa taga he is still looking at her, dauke kansa yayi bai sake cewa komai ba na ɗan lokaci, sai kuma taji yace “So what did you want me to do now da kika zo kika gaya min?” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kallesa, lkci daya jikinta yayi sanyi, yace “Ko nan gidan kike son ince ki dawo?” Ta girgiza masa kai tace “A’a, i will cope in sha Allah, kawai na gaya maka ne” Sai kuma ta mike a hankali tace “Nagode, i am going back home” Ya watsa mata wani kallo yace “Are you okay? Ina maki magana zaki mike tsaye? Ni nace ki tashi?” Ta sunkuyar da kanta sai kuma ta koma ta zauna, nan da nan taji hawaye ya cika idonta, da ta sani kawai da Housemate dinta ta gaya ma duk da Safiyyah tace kar ta gaya masa, Ajay ya dau grape dinsa yana ci yace “Shi Guardian din naki me ya hanaki gaya masa sai ni? Baki fi kusa da shi ba a kaina zaki tsallakesa ki zo ki sameni? Am i ur Bodyguard?” Jin tayi shiru ya juya ya kalleta, hawaye ya gani a idonta, ta kai hannunta tana goge hawayen, bai sake cewa komai ba idonsa a kan grape din gabansa, after almost 30 seconds ya kalleta yace “Ya ma kike da suna, Yaushe zaku fara exams?” Bata dago kanta ba cikin sanyin murya tace “In less than a month time” Yace “Amma kinga silly frnd din nan taki wataran sai ta jefa kanta masifar da bazata iya fita ba, har ke sai ta jefa cikin matsala, shi tout din ta tsaya take exchanging words da saboda rashin kamun kai….” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Ajay bai sake cewa komai ba a parlon yana nazarin how to tackle the issue, shi ya dade bai ga ɗan iska kamar Abdul ba, amma zai yi maganinsa, shafa kansa yayi still thinking of where to start from, a yanxu dai baza su fara cewa ta zauna a gidan nasu ba don Mai martaba went on a trip to Toronto, kwanansa hudu kenan a can kuma basu san ko zai biyo ta Amurka ba, infact zai ma biyo don in dai ya taho overseas komin nisan inda yaje da Amurka dole sai ya zo Maryland in har suna kasar to check on them, so they won’t take the risk of accommodating her in the house, assuming the semester isn’t late da kawai sun mata applying for On-campus residence halls a cikin makarantar ta zauna, Ajay ya daga kai yana kallon Cousin brother dinsa Mukhtar that was coming towards the parlor, Mukhtar yayi kasa da murya yace “Tare mu ke da Mai martaba….” Ajay bai san sanda ya mike tsaye ba dai dai sanda yayi ido hudu da Abbansa dake biye da Mukhtar a baya, ƙamewa yayi a inda yake tsaye with surprise, what a bad coincidences this is, Mai martaba ya shigo parlon with a broad smile on his face yayi kamar ma bai ga Khaleesat ba, Ajay ya sauke kansa kamar wanda ruwa ya cinye a wajen, at first ya ma rasa abun cewa, can kuma yayi karfin halin cewa “Barka da zuwa ranka shi dade…..” Khaleesat ta daga kai tana kallon Mai martaba sai kuma ta sunkuyar da kanta ta zamo kasan carpet ta gaishesa cikin sanyin murya, sai a sannan mai martaba ya kalleta still smiling ya amsa gaisuwarta, Mukhtar yayi offering masa kujera ganin bai zauna ba, Mai martaba yace “I am fine Mukhtar…” Sai kuma ya kalli Ajay da ya kasa kallonsa har sannan yace “Ina Jawwad?” A hankali Ajay yace “I think he went out just now…” Mai martaba yace “Ohk” Mikewa Khaleesat tayi da niyyar barin parlon, Mai martaba ya kalleta yace “No yi zamanki yarinya, ya sunanki?” Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta koma ta zauna a hankali tace “Sunana Jiddah” Yayi nodding kai yace “Maa sha Allah, ke er Nijar ce?” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tana wasa da gyalenta tace “A’a, er Nigeria ce” Mai martaba yace “That’s good, Nigeria wani state?” Tace “Kano” Ajay dai yaki daga kansa yana jin zufa na karyo masa a forehead, can kawai ya juya ya bar parlon yana tafiya a hankali, Mai martaba ya zauna saman kujera still looking at Khaleesat yace “Karatu kike a kasar nan Jiddah?” Khaleesat tace “Eh karatu nake” Yace “That’s good, wace makarantar?” A hankali Khaleesat tace “John Hopkins university…” Mai martaba na jinjina kai yace “Maa sha Allah, kano a wani unguwa iyayenki suke?” Khaleesat tace “Muna mariri ne” Shi dai Mukhtar na ta tsaye a parlon yana mamakin yanda Mai martaba ya tsaya ya bada lokaci yana conversing da Khaleesat bringing her down to his level, Ita kanta Khaleesat bata yi tunanin sarki bane shi duk zaton ta ko dai brother din babansu ne shi din, Mai martaba yace “Maa sha Allah Jiddah, Allah ya bada sa’an karatu” Tace “Ameen Abba Nagode” Mikewa tayi zata bar parlon ya kalli Mukhtar yace “A bata dala dubu biyar Mukhtar” Mukhtar ya ɗan risina kai da ladabi yace “To ranka shi dade” Khaleesat na kallon Mai martaba a hankali tace “Abba Nagode, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma” Daga mata hannu kawai yayi with smile, sannan ta mike ta bi bayan Mukhtar, tun basu fita parlon ba sai ga Jay ya shigo, kasa karasowa yayi bayan yayi ido hudu da Khaleesat ga Mai martaba zaune a parlon, can ya kalli Mukhtar da ya daga masa hannu alamar gaisuwa, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam ya sunkuyar da kai walking slowly, a hankali tace “Sai anjima” Murmushin karfin hali kawai yayi mata without saying anything, ta bi bayan Mukhtar suka bar parlon, Jay ya karasa har cikin parlon ya zauna kasan carpet yana gaida Mai martaba da ladabi, Mai martaba ya amsa yace “Ina Ahmad din?” Jay ya mike ya bar parlon zai kira Ajay, ba a dau lokaci ba suka dawo tare, shi dai Ajay ya kasa hada ido da mahaifin nasa, ya zauna kan carpet gefen Jay, sae kuma yayi karfin halin cewa “Ya hanya ranka shi dade?” Cikin nutsuwa Mai martaba yace “Alhamdulillah….” Daga haka mai martaba bai sake cewa komai ba, Jay da Ajay ma duk suka yi shiru kamar masu jiran hukunci a gabansa, after a while Mai martaba ya kalli Ajay yace “Ita ce yarinyar da za aje gidansu kenan…” Ajay ya ɗaga kai yana kallon Abban nasa, can ya ɗan sosa kai yana murmushin karfin hali yace “Abba ai budurwar Jawwad ce, wajensa ta zo ba wajena ba” Mai martaba ya kalli Jay da bai dago kai ba, Can Abba yace “Budurwar Jawwad kuma na gan ku zaune tare a parlor” Ajay ya gyara zama yace “Ranka shi dade abinda na fada gaskiya ne, ba wajena ta zo ba wajensa ta zo” Mai martaba ya kalli Jay, cikin nutsuwa yace “Jawwad” Jay ya dago kai amma ya kasa hada ido da mai martaba, jin mai martaba yayi shiru yasan bayani yake jiran ji daga garesa, hakan yasa ya fara magana with calm yace “Gaskiya ya fada Abba, haka ne…” Mai martaba yayi shiru na kusan minti daya kafin yace “Ita Hadiyar fa?” Jay ya kasa cewa komai, Mai martaba sam bai yarda da abinda suka ce masa ba don gani yake kamar Jay is covering for Ajay, after some minutes cikin hikima Mai martaba yace “Ko hakan yasa kake ta jan maganar Hadiyah?” Jay ya gyada masa kai still not looking at him, Mai martaba ya numfasa speaking with calmness yace “So ta yaya zan yarda da ku yanxu? Don na fara kokonton ka yanxu Jawwad, a da dai baka min karya amma yanxu ka fara” Jay yayi karfin halin cewa “Allah ya taimake ka, believe me ba karya nayi maka ba” Mai martaba yace “Ai shi ne nake tambayarka ta yaya zan yarda da hakan? Yanxu nema maka auren yarinyar zan sa ayi idan na koma Nigeria so i can clear away my doubt?” Jay ya daga idanuwansa ya kallesa, a hankali yace “Da zan yi farin ciki da hakan ranka shi dade” Mai martaba yace “To batun Hadiyah fa?” Jay ya rasa abinda zai ce, after few seconds yace “I will be glad idan aka amince min na janye daga batun auren Hadiyah” Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace “Ai bazan maka dole ba Jawwad, ya rage naka kayi ma iyayenka mata bayani su bar maganar Hadiyah tunda kana da yarinyar da kake so da aure, don waƙa a bakin me ita tafi dadi, in kuma kaga zaka hadasu su biyun it’s fine, as far as zaka yi adalci… By so doing iyayenka mata baza su dau lamarin da zafi ba tunda duk sun saka ran auren ka da Hadiyah” A hankali Jay yace “But i am afraid za su yi shunning batun idan na kai masu ranka shi dade” Mai martaba yace “Not when i am alive Jawwad, duk abinda kake so shi zan maka in sha Allah” A hankali Jay yace “Allah ya kara girma ranka shi dade….” Mai martaba ya kalli Ajay yace “Kai kuma ina sauraron ka har yanzu” Mikewa Mai martaba yayi ya bar parlon, bayan tafiyarsa suna ta zaune kamar wa enda aka yi planting a wajen sai dai ko wannensu akwai abinda yake tunani a ransa, Ajay ya ɗan kalli Jay sai kuma yayi breaking silence din yace “Allah ya sanya alkhairi me mata biyu” Jay ya wani kallesa, Mikewa Ajay yayi zai bar wajen Jay ya sa masa kafa sai gashi timmm ya fada kan kujera, juyowa yayi ya hade rai yana kallon Jay da ya fara dariya, yaushe rabon su zauna waje daya a gidan, har magana ma sama sama suke yi… Jay ya dakata da dariyan da yake, sai kuma yayi kasa da murya yace “So what did you think about all this?” Ajay yace “About what?” Jay ya juya ya kallesa bai ce komai ba, Ajay yace “Getting married to ur Ward?” Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay ya ɗan yi murmushi yace “All this while ka zata wataran zan so ta ne da kake creating attitude a gidan nan? Saboda me ma zan so ta? Dama shi son haka yake very cheap? Ai ba class dita bace yarinyar nan, i like nothing about her most especially her silly cry, duk abinda nake mata saboda kai nake mata, if not because you bazan taɓa saninta from anywhere ba, ba ma abinda zai sa nayi crossing path da ita, so chill bruh…. Just that har na fara hango maka challenges din da zaka yi facing a wannan familyn naka, considering the fact that ta taɓa aure, sannan she is a nobody, familynka kuwa basa son someone that is a nobody not to talk of bazawara, kaga you have to tighten up ur belt kayi facing all the up and downs that will approach you…. Wishing you the very best of luck” Yana kai wa nan ya mike ya nufi dakinsa, Jay dai ya bi sa da kallo, sai kuma Ajay ya tsaya sannan ya juya yace “In addition, tsohon mijinta na bibiyanta yanxu haka, that was why she was here earlier on” Daga haka Ajay yayi tafiyarsa Bedroom dinsa ya bar Jay da ya mike tsaye jin abinda Ajay yace. Ajay na shiga dakinsa ya tafi jikin window ya tsaya yana kallon Neighborhood dinsu, everywhere was so silent and calm as usual, sai kuma ya sauke idonsa ya juya ya tafi ya dau wayarsa ya koma jikin windon ya tsaya, number Khaleesat yayi dialing, yana fara ringing tayi picking, yace “Where are you?” Khaleesat dake cikin Lyft tace “Ina cikin mota” Yace “Za ki ina?” Kallon wayarta tayi jin shigowar kira taga Jay ne ke kiranta, ta maida wayar kunne a hankali tace “Gidansu Safiyyah zan je” Yace “Ohk, remain there idan kin je, do not go back to ur apartment….” Yana kai wa nan ya katse wayarsa, Khaleesat tayi picking call din Jay don bai katse ba har sannan yace “Kina ina Halysaah?” Tace “Ina hanya” Yace “Kar ki koma apartment din ki, wait for me somewhere, i will be on my way now” A hankali tace “Dama gidansu Safiyyah zan je” Yace “Ohk to ki je, zan same ki a can” Tace “To Nagode” Katse wayar tayi ta mayar cikin jakanta, wai yau ita ce zata kai kanta gidansu Safiyyah yau saboda rashin choice, to ya zata yi, ko zaginta Surayyah tayi ai sai dai kawai ta bata hakuri in dai zata barta ta zauna a gidan, a haka ta isa gidan, bayan ta sauka Lyft ta nufi kofar apartment din ta danna bell…… *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*07087865788

Back to top button