Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 10 Hausa Novel

“Hohohooo! Da ma an gaya min za ki dawo, za ki dawo da shirin ki da ya ci uwar na da kuma sai ga ki, to idan ma junanki sammako ni a tafe na kwana yarinyaa! Namana guba a bakin ki dodanniyar Mayu!”Yadda yake maganan a kan muryarshi ya sa tuni su inna Asabe suka yo waje, abin ka da ƙaramin ƙauye tuni maƙota ma sun fara leƙowa, daga Salim har Afeefah sun kasa ko da motsi ne barin ma ita da wani tsoro ya sake rufe ta. Tuni matasa suka shiga neman makami don ma kayan sojoji ne jikin salim kuma harda ƙaramar bindigar shi a gefen ƙugunshi.Kawu ya nufa da yake zaro maganganu tamkar sabon kamu wai enchanting words ɗin kariya yake daga Mayu ya furta”Haba Malam! Ba ka gane ta bane? Ya duk ka firgice kaman wanda yayi karo da zaki?”Kawu ya gyaɗa kai ya kuma girgiza yace “Hayyyaa yaro yaro ne! Ni ko na santa farin sani, kai ma na tabbatar da ka san wacece ita babu abin da zai sa ka bari ta shiga motarka. Wannan mayyar da ta cinye min zuri’a ta je ta cinye na uwarta shine ka dawo min da ita kofar gida?”Waigawa salim yayi ya kalleta har lokacin tana kafe kyam kaman mutum-mutumi ya waigo ga kawu hes very confused da kalaman da ake jefa mata gwara wanchan ta ce mijin yapendonta ne amma wannan dake wa ga mahaifinta? Ji abin da yake kaman sabon kamun hauka?”Amma malam ka kuwa san yadda shari’ar maita take? Me yasa za ka jefeta da wannan kalma ta Ƙazafi? Ita ɗin fa ‘ya ce a gareka kuma addini kai ya ɗora wa kulawa da ita da bata kariya tunda mahaifinta baya raye amma don Allah dubi abin da kake yi na ƙarancin ilimi, duk ka tara mana mutane? Me yayi zafi haka?””Wuta! Na ce wuta ne yayi zafi, wallahi idan baka daina haɗa ni da wannan yarinyar ba kai ma sai na rotsa kan ka da wannan sandar bar ganin ka da kayan sojoji, tun muna shaida juna ka ɗauke ta sawunku a likkafa ka mayar da ita inda ka ɗauko ta ai Zainabun ma sai da na gargaɗeta taurin kanta ya ja mata… Ni ma zaman da nayi da ita shekarun baya ban huta ba da neman kariya da yanzu babu wanda za ka tarar anan da duk ta lashe kurwowinmu”Ya hayayyaƙo wa salim da baƙin ciki haɗe da wani irin takaicin su ke shirin kashewa, ita dai ban da kuka babu abin da take kaman ranta zai fita hannayenta duk biyu bisa kanta jikinta na wani irin rawa.Ya godewa Allah da ba da Rayyan ya zo ba yau da kuwa yanzu wani zancen ake ba wannan ba, duk haƙurin salim sai da su kawu suka kai shi bango, ya kaɗa ya rawa a kan su karɓeta sai dai cin mutunci kawai suka karta musu da kalamai masu zafi suka ma fara yunkurin far musu da sunan haushin ta dama suke ji haka ya dauƙeta suka wuce suka bar garin gudun fitinar da zai iya kunno kai idan suka ci gaba da tsayuwa. Shiru ne ya ratsa motar sama da awa guda sai tsula uban gudu yake ita kuma tana ta aikin kuka.”Afeefah ya isa haka don girman Allah ki yi haƙuri, ki karɓi wannan ma a jarabawa. Akwai inda zan kai ki kuma?”Yayi maganan yana kallonta, ɗago ido tayi ta kalleshi sai da ya ji wani yarrr a jikinshi ganin yadda idanunta suka koma tsabar kuka, ɗauke kai yayi har ƙasan Ranshi yana jin ɗacin da bai sani ba baƙin cikin su kawu ne ko menene oho.”Ba Za ka tambayi wacece ni ba? Ba ka ji kana son sanin ni ɗin Mayyar ce da gaske ko akasin hakan ba? Ba ka ji kana tsoro da shakkar taimakona ba?”Ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta har lokacin idanunta na a kanshi.Ya samu wuri yayi parking kan ya waigo gabaɗaya yana kallonta “Ki gane wani abu Afeefah, Na riga na saka a raina taimakon ki ya zama min dole. Batun sanin ko ke wacece ba zan ce miki bana son ji ba amma ba na son tilasta ki ba ni labarinki, idan muna tare watarana zan sani. Ba na tsoron ki don ke ɗin ba Abar tsoron ba ce ba kuma na Fatan yin da na sanin taimakon ki”Yana kallon cikin idanunta ya ƙarasa maganar, zuciyarta ne ya sake karyewa hawayen da suka tsagaita sai suka fara shirin dawowa sabo, kaman da wasa ta shiga sanar mishi da tarihin rayuwarta daki-daki tun daga farko har kawo ranar da ta sha guba don ta kashe kanta. Numfashi ta ja sam bata duba yanayin shi ba ta cigaba da cewa “Na gode kwarai da taimakon ka da kuma yarda da ni da kayi ba tare da ka san ni din wacece ba, ba na so in sake ɗora maka wani nauyi ko damuwa ba kuma na son wani abu ya same ka ta dalilina. Za ka iya ajiye ni anan kawai ka bar ni ka koma gida Na gode sossai…”Idanunshi da suka sauya sossai suka cika da tarin kwallar tsananin tausayinta da rauni ya ɗauke bisa kanta yana lumshe su da ƙarfi, ya rasa ma kalar tunanin da zai yi wani irin tausayinta ke bin gaɓoɓin jikinshi yana kassara su, ji yake kaman ya taya ta kukan ta ɗauki abubuwa dayawa fiye da shekarunta, tabbas dole tayi yunkurin kashe kanta don duniyar bata dandana mata daaɗi ba sai akasin hakan, hakika ya yabawa hakurin ta da tarin juriyarta da wani ne ko guba bai kashe shi ba damuwa sai yayi bindiga da zuciyarshi.Sama da mintuna uku ta sauƙe numfashi ta sa hannu ta buɗe kofan tana shirin sauƙa ta ji ya kira sunanta “Afeefah!”Waigowa tayi tana kallonshi, ya rankwafa ya janyo murfin da ta buɗe ya rufe kirib kan ya kalleta “Ba zan iya barin ki anan ba Afeefah! In na ce ma ki sauƙa anan za ki yarda?”Ta Yi shiru ya sauƙe numfashi kan ya ta da motar yana mayar da idanunshi bisa titi ya shiga ja a hankali.”Sunana Salim Mahmud ni haifaffen nan jahar ne na Kaduna, ni ne ɗa na farko a wurin iyayena kuma namiji tilo ina da ƙanne mata uku Sadiqa ke bi na Dukda akwai tazarar shekaru masu dama tsakanin mu sai Sameerah kan Auta Samha dukkansu suna jami’a ne presently. Tun Samha na da shekaru uku a duniya muka rasa mahaifin mu ya saura daga mu sai mommy, dangin mahaifin mu suka watsar da al’amurranmu duk da kasancewar mahaifina mai karamin ƙarfi bai tara mai yawa ba, kuma duk yawan da zai tara akwai hidimomi gabanmu ya sa tun ba a je ko ina ba komai ya ƙare, mahaifiyar mu ta matukar shan wahala da mu kuma ta yi ɗawainiya mai yawa da ba don tayi karatu ba ma da bamu san halin da muke ciki ba a yanzu, bata huta ba sai da ta ga ta kafa ni ta yadda zan iya taimakon ƙanne na. Mahaifiyar mu macece mai tausayi sai dai duniya kuma ta koya mata son nata don bata haɗa soyayyar yaranta da kowa ba.Ban sani ba ko za ki iya zama cikinmu idan kin amince zan je na roƙe ta, zan bata labarinki za ta ji tauaayinki kuma in shaa Allah za ta haɗa ki da su Samha ta rungume mu cigaba da rayuwa har Allah ya kawo miki miji ki yi aure”.Kuka take mishi mai sanyi, ashe har tana da zaɓi a yadda taken nan? Har sai ta ce ta amince zata zauna da su ko da naman jikinta za su dinga yankewa da tayi bulayi a titi? Kalaman godiya tayi ta jera mishi yana hana ta don gabaɗaya rauni da tausayinta sun sassara mishi gaɓoɓi da yake jin zai iya joining ɗinta su yi kuka tare.Yamma sossai suka dawo cikin Kaduna, daga ita har shi babu mai magana idanunta zube a titi, masu hidimar komawa gida kawai take kallo Dukda zuciyarta ya jima cikin nashi duniyar, kwakwalwanta ya zurfafa a tunanin wani irin ƙaddara ne kuma ya dawo da ita cikin Kaduna? Shin za su amshe ta bayan sun ji labarinta ko za su kore ta? Idan suka kore ta ina ta nufa? Akwai mai sake mutuwa sanadiyar ta? Anya ta yi mishi adalci da ta biyo shi? Har suka isa cikin Unguwar rimi bata sani ba, jin ƙarar horn na mota ya sa ta ɗan yi firgigit ta dawo da hankalinta kan inda suke sai ta tsince su a wani layi mai jerin rukunin gidaje iri ɗaya.Gidaje ne masu kala ɗaya kusan komai na gidajen Layin iri ɗaya ne bambancin kawai lambobin da ke maƙale gefen kyauren ko wani gida, Baƙin gate ɗin aka zuge wani matashi ya shiga yiwa salim ɗin barka da dawowa hakora a washe, Salim ya tsaya suka gaisa kan ya nausa cikin tsararren madaidaicin gidan da ya tafi da imaninta, harabar shimfide da interlocks an ƙawata gidan da shukoki jajaye, shudi, kore da ma wasu kalolin ma su ban sha’awa. Ginin da kaman an zana ne ba a gine yake ba saboda yadda yayi mata kyau gidan sama ne, harabar gidan shiru babu kowa har ya shigar da motar cikin ma’ajiyarta tsakanin wasu motoci madaidaita guda biyu. Hamdala yayi yana zare keyn ya dube ta “Mu je ko?”Babu musu ta gyaɗa kai ta buɗe kofan ta sauƙa, shi ya buɗe bayan da ya fito ya zaro ledar da ‘yan kayanta ke ciki suka nufi cikin gidan yana gaba tana biye da shi a sanyaye, a gaban mashigar gidan suka dakata ya danna doorbell, babu jimawa aka buɗe Brown security door ɗin wata kyakyawar yarinya da za ta iya girme mata ta gani tsaye, haɗa idanu da suka yi da Salim ya sa ta saki ƙarar murna kan ta sauƙo da gudunta ta faɗa mishi tana dariya sossai shima yana murmushi ya tarbeta ya ɗan yi hugging ɗinta kaɗan ya sake ta “Welcome home bro””thanks Autar Hajiya mommy”Ta saki murmushi tare da jan hannunshi suka yi ciki tana ihun sanar da isowarshi, hakan ya sa wasu ‘yan mata biyu suka fito su ma a guje suna mishi maraba, yanayin kamanninsu ya sa ta tabbatar da su ne ƙannenshi da ya bata labari, murmushi take saki don sun matuƙar burgeta har tana jin ina ma da ba ita kaɗai aka haifa ba, ita kam ba ta da wannan gatan Allah bai ba ta ba bata gama tunanin ta da murmushi ba ta ga Fitowar wata dattijuwar mace da suke matukar kama, fuskarta cike da fara’a har hakwaranta biyu na hajji na bayyanuwa, doguwa ce kaman su salim da suke dogaye, haka ba ta da wani ƙiba don idan ba a yanayin fuska da ya bayyana girma ba ba za ka ce ta haife su ba.Ganinta ya sa salim ya ture ƙannenshi ya isa yayi hugging nata”Oyoyo Mommyna””Welcome home my son, idonka kenan?”Ya sake ta yana ɗan shafa kai, ta saki murmushi ta san ya kan shigo cikin Kaduna amma sungulollinshi ba ko yaushe yake bari ya ƙaraso gida ba, kusan satin shi uku zuwa huɗu rabon shi da su sai a waya.”Wannan kuma wacece yaya? A ina ka samo ta?”Samha da tun bayan gama murnar su ta ƙure Afeefar kur da idanu tayi tambayar.”Samha Afeefah sunanta, ki kaita ɗakin ki ta yi sallah ki ba ta abinci idan na sauƙo bayan isha za mu yi magana”Babu wanda ya sake tankawa a cikin su har ya haye sama inda nan ne sashen shi, ta duƙa ta shiga gaishe su ɗaya bayan ɗaya sai ƙare mata kallo suke suka amsa ba yabo ba fallasa.”Mu je”Samha ta furta mata, ledan ta da samhar salim ya ajiyewa ta ɗauka mata ta nuna mata, babu musu ta sa hannu ta ɗauka ta bi bayanta. Bayi ta nuna mata ta shige a lokacin har an fara kiraye kirayen Sallar Magrib, Allah ma ya sa ta zauna da Aunty zee da take da ‘yan abubuwan zamani Dukda bai kai na gidan ba amma ta iya ta buɗe tayi alwala ta fito. Samhar na zaune bakin gado tana latsa waya ganin Fitowar ta ya sa ta nuna mata gabas ba tare da ta bata sallaya ko ta motsa daga inda take zaune ba, sai da Afeefar ta shimfide dankwalinta a saman tiles ɗin kan Samha ta miƙe ta shige bayin. Afeefah na sallah ta ji samhar na wanke bayin ko da ta idar samhar ta fito ta shimfida sallaya daga chan nesa ta tada Sallar ta, ko motsi Afeefah bata yi ba tana ta Adu’a da roƙon Allah a kan wannan rayuwa da za ta yi a wannan gida, har aka kira isha kan ta miƙe ta gabatar Adu’a ta cigaba da yi a kan kar Allah ya kawo ajalin wani tana cikin gidan, tun bayan Magrib Samha ta fice daga ɗakin bata wani jima da idar da Sallar ba tana zaune kawai sai ga samhar ta turo kofa ta shigo.Plate na shinkafa jollof ne ta ajiye mata da wani karami mai dauke da ruwan leda guda biyu.”Na gode”Ta faɗa, kai kawai ta gyaɗa ba tare da ta buɗi baki ta amsa ba ta sake ficewa.A chan parlor kuwa bayan salim ya shigo daga Sallar isha suka ajiye mishi nashi tray ɗin dake ɗauke da plate na shinkafar da wani an yi wrapping salad da wani saucer mai ɗauke da pepper chicken da ke fidda kamshi haɗe da zobo jug guda. Bismillah yayi ya shiga ci a natse don ya tara yunwa sossai a cikin nashi, sai da ya gama yayi hamdala hajiyar su da tuntuni idanunta ke kanshi ta ce “Salim yarinyar chan da ka shigo da ita daga ina haka? Meyasa take a waje har bayan Magrib ba za’a nemeta a gida ba?”Ya ɗan gyara zaman shi “Wallahi Mommy yarinyar ce rayuwarta abin tausayi, na rasa me yasa mutanen mu suke haka a wannan rayuwa ashe don ajalin bawa yayi ya amsa ƙira sai ya zama lallai lallai wani ɗan uwansa mutum ne ya kashe shi? Duk mun manta cewa idan ajali ya zo babu mai jinkirta wa ko da da second guda ne sai ya tafi?”Hajiyar ta gyara zama tana katse mishi hanzari “Hakane idan har mutum ya mutu ajalin shi ne ya riga yayi amma a komai akwai sanadi”Ya ɗan yi jimmm yana kallonta for seconds kan ya shiga magana”Mommy Afeefah Marainiya ce! Mahaifinta ya rasu tun tana ciki, mahaifiyarta ta rasu wurin haihuwar ta….”A hankali ya cigaba da ba su labarin Afeefah kaman zai zub da ƙwallah har kawo yanzu, yana sauke aya Samha ta miƙe hannunta duk biyu dafe da ƙirji idanu waje ta ce”Mayya Yaya Salim???”

Back to top button