Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 13 Complete Hausa Novel

 

Suna fita mama ta maida hankalin ta ga Abie dake zaune yana ɗan nazarin abubuwa, tace

“Amma malam lafia naga ka tawo da zainab?”

Hular kan shi ya cire ya ahe a gefe, tukun yace

“Gidan  baze zaunun musu ba sam, 

tsohon gida ne da sun riga da sun samu matsuguni a cikin sa, sanda zata shiga mu kuma ba muyi tunanin aje a kore su ba, shiyasa har yanzu bamu samu mafita ba akan matsalar”

Shiru mama tayi tana sauraren Abie

Can ya ɗora da

“Shiyasa na kira Baban shi yazo ya tafi da shi, 

Dole zan sa ayi saukar alƙur’ani a gidan, sannan shima ya kamata ayi mishi ruƙiya sosan gaske dan abun ya wuce gona da iri”

Jiki a sanyaye mama tace

“Allah yasa muji alkairi dai, Allah kuma ya kawo mana ƙarshen abubuwan nan”

Da “Amin” Abie ya amsa yana sake kishingiɗa.

*****Uku saura na dare Abdul ya farka daga nannauyen baccin da yake, a hankali ya fara buɗe idon shi tare da kai hannu yana shafa gefen shi, jin be jita a inda ya saba jin ta ba ya ƙarashe buɗe idon shi da sauri yana tashi zaune

Waige waige ya fara yi, nan ya tabbatar da ba a ɗakin su yake ba, a ɗakin Abbah yake

A hankali ya sakko daga kan gadon, daidai nan Abbah ya turo ƙofar ɗakin ya shigo

A sanyaye Abbah yace “ka tashi?”

Be jira cewar shi ba yace “kaje ka gabatar da sallolin da suka wuce ka, yanzu uku da wani abu na dare yanzu”

Da sauri Abdul ya ɗago kan shi ya kalli Abbah, jin yace uku na dare yanzu yace

“Abbah ina zainab to?”

Kai tsaye Abbah yace “tana gidan iyayen ta”

dummmm, haka gaban Abdul ya bada sound, a tsorace ya ce

“Tace bazata iya zama dani ba ko Abbah?”

Dafa kafaɗar shi Abbah yayi, sannan yace

“Bata ce haka ba, muna so a samar muku mafita ne kafun ku koma gidan ku inshaAllah”

Marairaice fuska ya sake yi, yace

“Amma meyasa bata tawo nan gidan ba ta tafi can gidan?”

Sosai Abbah ya kalle shi, yace

“yanzu ba lokacin wannan maganar bace, kaje ka rama sallolin ka sannan kazo ko tea ne kasha se ka koma”

Ba musu ya juya ya shiga toilet ɗin ɗakin Abbah

Ya ɗan jima sosai a ciki, har Abbah ya fara tunanin ko lafia? se ga shi ya fito jikin shi da alamun wanka yayi

A nan ya kabbara sallar shi, duk ya ramosu, kafin ya zarce da nafiloli

Sosai yake kaima ubangiji kukan shi, damuwar shi da kuma ɗorewar zama na har abada da matar shi kuma farin cikin shi 

Daga ƙarshe ya roƙar ma Ammahn shi gafara, sannan ya roƙan ma kanshi kyakkyawan ƙarshe.

Tunda ya idar da sallar nan yake jin wata nutsuwa da sanyi na ratsa shi, har wani lumshe idanu yake.

Matsawa gefen kujera yayi,

Yayi shiru yana tunanin ya zainab take a wannan daren

Can idanun shi suka kai ga ƙur’ani dake aje gefen gadon Abbah

Abinda ya jima, jimawan gaske be ɗauka ba kenan, kamar wanda ake fizgar hannun shi zuwa ga ƙur’anin, 

A hankali ya ɗauko shi ya dawo kan dardumar da yayi sallah ya zauna, 

Kamar wasa ya buɗe shafin farko, se gashi ya fara karatu cikin sauti me daɗin sauraro

Abbah kanshi da ɗumbin mamaki yake kallon abunda ya jima be gani ba, dan bejin Abdul na da ƙur’ani wanda ze bugi ƙirji yace yana ɗaukan shi ya karanta.

Shi kanshi Abdul ɗin da wani irin mamaki yake karatun 

Dan baze manta ba, tun a da in ya ɗauki ƙur’ani da niyar karatu, to tabbas bacci ne ze ɗauke shi, ko kuma gaba ɗaya ya dena gane rubutun ciki, ko kuma ya rinƙa jin kanshi na juyawa har se ya aje shi tukun yake samun sauƙin abin

Tun yana kwatantawa har yazo ya haƙura gaba ɗaya, amma wai yau shine ke karatu

Kafin ma yayi nisa a karatun kuka yaci ƙarfin shi, shi kan shi Abbah yana gefe yana sharar nashi ƙwallar, jin sautin kukan Abdul ɗin ne ya ƙarashe karyar ma da Abbah zuciya suka haɗu sukai tayi

Ba wani be lallashin wani a cikin su

(Hummm duk abinda kuka ga maza na zubar mishi da hawaye, to tabbas ba kaɗan bane wannan abun, Allah kasa mu dace.)

Har seda aka kira sallah tukun Abdul ya dakata, 

Raka’atanul fajir suka yi, sannan suka wuce masallaci a tare.

Ta ɓangaren gidan Abie kuwa, washe gari da safe, wajajen goma na safe

Yana zaune a ɗakin shi ya sa mama tayi mishi kiran zainab,

Zainab na can suna kwasar ta da IYA mama ta kira ta.

Da sallama ta shiga ɗakin, zaune ta iske Abie ya aje manya-manyan jarkoki a gaban shi, ga ɗakin ya baɗe da ƙamshin magungu na kala-kala

A zuciyar ta tace “chaɓ kace abun na yi ne ni jikar IYA”

zama tayi kusa da shi, tana jiran taji ta inda za’a fara

Kallon ta Abie yayi yace

“Nasan kin yi ƙoƙari na dakiya da nuna jarumta, yanzu ma ina son ki nin ka akan na da zainab,”

Janyo galan ɗin gefen shi yayi yace, 

“kije da wannan ɗakin ki, daga yau zuwa jibi ina son ki karance min waɗan nan surorin tas” 

Ya miƙa mata takardar da ya rubuta sunan surorin.

Hannu biyu ta saka ta karɓa, dubawa ta hau yi, 

Seda ta gama dubawa sannan ta ɗaga kai tace

“Ai zan iya gama su zuwa dare Abie”

Ta ƙarashe maganar tana ɗaga wa mama gira

Dariya mama tayi, tace “Kin maida ni kakar ki wallahi”

Abie ma dariya yayi, dan sarai yaga lokacin da ta ɗaga girar, 

Gyaɗa kai yayi yace

“Auta na bata ƙyale kowa ba, 

Ni da na samar miki enough lokaci ne da zakiyi ki huta, sannan kiyi tsokanar ki se kici gaba daga baya”

Dariya sosai zainab tayi, 

sannan tace “Basu da yawa ai Abie, zan iya, yanzun nan zanje IYA ta tayani yi” 

Daƙuwa Abie yayi mata, shima yana dariya

Da kanta ta ɗauki ɗan madedecin galon ɗin ta fito ɗakin.

A gefen IYA ta aje galon ɗin, sannan ta kwanta

Kallon galon ɗin IYA tayi tace

“meye wannan zainabu?”

Idon zainab a rufe tace

“Ruwa ne da zam-zam a ciki”

IYA na jin haka tayi muƙut da bakin ta, ba yau ta fara ganin wannan ba, sarai ta san ɓe ake da shi.

Jin tayi shiru yasa zainab buɗe idon ta tace

“IYA ta, zaki taya ni yin tofin a ciki?”

Ba uhm, ba a’a IYA taja ɗankwalin ta taɗaura, ta miƙe tsam daga kusa da ita tayi hanyar fita,

Seda ta kusa ficewa ta waigo tace

“Ai inshaAllahu na gama shiga lukutar masifa ta dalilin ke da ɗayan jinsin naku, in ma kiranye zaki yi nidai bana wajen ballanta na ga abunda ze hana ni rintsawa.”

Murmushi kawai zainab tayi, ita gaba ɗaya so take ta san ya Abdul yake, shin ya ma tashi daga wannan baccin ko kuwa har yanzu bata ga dama ta rabu da shi ba?

Tayi tsaki yafi cikin ɗakin nan, 

Kujera dama IYA ta saka daga ɗan gaban ɗakin ta zauna, duk tsakin da zainab keyi tana jin ta

Da dai ta gaji da ji ne ta ɗaga labulen tace

“Naga tsaka ƙarshen tsaki”

Banza Zainab tayi mata bata ce mata uffan ba.

Jin zainab shirun zainab da yawa yasa IYa ta shi kamar warce aka tsikare ta takoma ɗakin

Zama tayi a kusa da ita ta dafa ta, murya ƙasa-ƙasa IYA tace

“meke damun ki ne wai, ko dai hasashe na ya tabbata ne?”

Tashi zaune zainab tayi tana kallon Iya, tace

“Hasashen me IYA?”

Taɓe baki IYA tayi tace “saki mana”

Kwashewa da dariya zainab tayi tace

“lallai IYA, so kike ashe na koma ƙaramar bazawara ko?, To albishirin ki?”

Baki a washe iya tace “goro fari ƙal zainabu na”

Harda gyara zama.

Seda zainab ta saƙalo hannun ta a kafaɗar iya sannan tace

“Sunan wannan auren namu mutu ka raba Iya ta”

Ture ta tayi daga jikin ta, sannan ta sake cewa

“To uban me ya dawo dake inba sakin ki yayi ba? ni ban taɓa ganin inda ake aure irin naku ba, aure ko wata beyi ba ace har an fara zuwa gida kwana? to wallahi Allah ya tsayar a iyakacin kanku”

Ƙara matsowa zainab tayi itama tayi ƙasa da murya kamar yarda Iya kanyi in zatayi magana tace

“tsaya in baki labarin abunda yasa na tawo gida”

Gyara zama Iya tayi, a duniya IYA na son labari,

Tun kafin zainab ta fara bata labarin dariya ke cin ta, haka nan ta daure tace

“Hummm, ta bakin ki IYA, nima jiyan nan naga lukutar masifar da kike yawan faɗa,………………. tsaf zainab ta bata labarin macijiya me sauya suffofi da suka gani jiya, ai kafin zainab ta kai ƙarshe IYA ta jiƙe sharkaf da zufa, babu inda baya tsuma a jikin ta, murya na rawa tace

“Kinga wannan narkekiyar masifar har kika dawo gidan nan da rayuwar ko zainabu?

To wallahi inda ni nayi wannan gamon da yau na taras da ajalina,”

Dariya zainab keta kwasa tana kallon yarda iya ke sharce zufa, 

Can Iya ta miƙe tace

“Tuna min addu’ar shiga bayan gida, dan dole inje in sauke wannan abun da ciki na ya ɗura”

Ganin zata ɓata mata lokaci da dariyar ta yasa tayi gaba da sauri ta shige bayi.

***Tun kafin azzahar Abie ya tura alarammomin da ya yarda da su zuwa gidan Abdul, 

Nan suka kwana, sauka ƙur’ani sunyi ta daga jiya zuwa yau yafi sau biyar, kuma Abie yace so goma yake son a sauke ƙur’anin

Daga nan gidan Abie ake musu girki me rai da lafia akai musu

Sannan magungunan da Abie ya haɗa da kanshi, 

Shi da kanshi ya kwashe su a cikin mota yaje har gidan, sannan yayi ma Abbah bayanin yarda zeyi amfani da su na kwana ukun, kuma ko da wasa kar ya fita waje, 

Sannan galon ɗin da zainab tayi ma tofi a ciki, bayan ta gama, Abie ya karɓa ya zuba wasu turarika a ciki, sannan ya rufe

Shi kuma yace ya rinƙa wanka da shi, amma ba a toilet ba, ya rinƙa shimfiɗa towel se ya hau kai ruwan ya rinƙa zuba akan towel ɗin.

Sosai Abie ya jaddada ma Abbah da shi kan shi Abdul ɗin, ban da fita ko’ina

Dukan su sunji, sedai Abdul ne dake ta kame-kame son ya tambayi ya zainab take

Sarai Abie ya gane, amma ya basar, yayi musu sallama sannan ya tafi.

A daren ranar Abdul ya kasa jure rashin ganin zainab, shi kawai so yake yaji ya take, a wani hali take a ciki

Shi inda da waya damuwar shi ba zata kai haka ba

Yana zaune bayan ya gama wankan magani wata dabara ta faɗo mishi, 

Fitowa palo yayi ya iske su Amal zaune suna kallo, kusa da Amal ya zauna yace

“Ara min wayar ki”

Ba musu ta ɗakko ta miƙa mishi, yana amsa ya juya ya koma palon Abbah

Number muslim ya saka ya kira

Kira biyu muslim ya ɗaga, 

“guy, kana lafia?”

Ihu muslim ya buga yace “angooo, halan ka canza number ne, jiya naso kawo maka ziyara wallahi amma wayar ka a kashe”

Murmushi Abdul yayi yace “Ƙarya da ciwo”

Dariya suka yi gaba ɗayan su, can Abdul yace

“Kira ni, katin wannan wayar ze ƙare”

Kafin ma ya rufe baki ya ƙaren

Seconds kaɗan kiran muslim ya shigo, 

Kai tsaye Abdul yaca

“In baka komi dan Allah waya nake son ka ɗan je ka siyo min, se ka kawo min nan gidan mu”

Da mamaki muslim yace “waya kuma?”

“eh, guda biyu iri ɗaya zaka siyo, irin samsung ɗina da ka so ka rabani da ita pls”

Da mamaki muslim yace “taka fa guru?”

Ƙosawa da maganar Abdul yayi yace

“kai dai ka siyo, ka kawo min dan Allah, sannan ka ɗan tura min kati ta wannan layin, se ka turo min number Abubakar Hamza”

Da “to” muslim ya amsa, dama ya shirya zuwa wajen zuwairiya ne, thank God bece mata yana zuwa ba daman.

Number ya fara tura mishi kafin daga baya ya turo katin.

Abdul na ganin katin ya ɗanna ma yaya Abubakar kira

Bata wani jima tana ringing ba ya ɗaga, 

Dariya yaya Abubakar yayi yace “haba ka wuce haka a waje na ai, se ka jini”

Godiya Abdul yayi yana jin wani farinciki na ratsa shi

yana aje wayar yayi maza ya tashi ya saka kaya sannan yayi wanka da turaruka masu ƙamshi, nashi da na Abbah duk ya haɗa yayi wanka da su

Se kallon fuskar shi yake a mudubi yana zuba murmushi kamar wani sakarai.

Seda ya gama shiryawa tsaf tukun ya fito palo inda ahalin gidan ke zaune ya miƙa ma Amal wayar ta.

Kallon shi ummie tayi da ɗan murmushi a fuskar ta tace

“wannan murnar fa Abdul, kamar wanda akai ma albishir da wani abun”

shima murmushin yayi yace

“bakomai ummie”.

Direct bayan ya fito daga gidan su yaya Abida gidan su yayo

Seda yaya Abubakar ya fara gaya wa Abie kafin ya samu Zainab dake kwance tana tunanin Abdul ɗin ta.

Yace “Zo muje ki raka ni zainab”

Jiki a sanyaye zainab ta tashi ta fito, tace “gani”

Murya ƙasa-ƙasa yace “ki je ki gyara fuskar ki  wajen Abdul zamu je”

Zaro idanu waje zainab tayi tace

“Abie baze yi faɗa ba?”

“Ke dai je ki shirya, na gaya mishi” yana gama faɗa ya juya ya fice

Tun safe dama mama bata nan, taje gidan su anyi rasuwa daga IYA se zainab a gidan

Iya na ta lazimi taga zainab na shafa powder bayan ta canza kaya

Kallon ta tayi tace

“ina zaki je kike canza kaya zainabi?”

Shiru zainab tayi, tasan sarai IYA zata iya mata terere bata shirya ba, 

Can dabara ta faɗo mata tace

” zanbi yaya Abubakar zuwa gaishe da yaya Abida ne”

Zuruf Iya ta miƙe tana gyara hijabin ta tace

“Nima tunda bala’in nan ya afkamana banje na duba ta ba, baiwar Allah tasha jibgar samudawan aljanu,

Muje a samu ladar dani”

Ɓata rai zainab tayi tace

“Dan Allah kiyi zaman ki IYA, kinga gidan ze zama ba kowa fa”

Suna a haka Abie ya shigo, ɗaga labulen yayi yace

“yana ta jiran ki fa a waje auta”

Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsun ta, 

kallon Abie Iya tayi tace

“Tana min baƙin cikin samun ladan duba mara lafia ne, nace wai zan bisu, shine tace in zauna inyi gadin gida dan kuturun raini, koma ba wannan ba ai zanso insha iskar waje nima”

Kallon zainab Abie yayi yace

“kuje tare mana, ai ba laifi”

“to” kawai zainab tace, tayi gaba 

IYa tabi ta a baya, hada aukin faɗin se mun dawo.

koda yaya Abubakar yaga sun fito tare da IYA bece komi ba, 

Suna shiga yaja mota suka tafi, ba wanda ke magana a cikin su, har suka ƙarasa gidan, dama ba wani nisa bane da su.

Iya na ganin an tsaya a tace 

“Nan suka dawo kuma?”

Yaya Abubakar be jita ba, hankalin shi na ga waya da suke da mama, akan yaje ya ɗakko ta, zainab ce kawai taji abinda tace, kuma ta amsa mata “eh”

Suna sauka yaya Abubakar ya juya bayan yace musu su shiga ze je ya dawo

Yana aje wayar mama, layin da Abdul ya kira shi ya danna ma kira yace “ga su nan a waje, zanje ne in dawo”

Da sauri Abdul ya fito palo ya ce

“Amal, leƙa ki shigo da baƙi”

Da sauri ummie ta kalli Amal da har ta miƙe tana gyara gyalen kanta

Ko me ta tuna oho, ta  juwa ta maida hankalin ta ga TV

Su zainab na a tsaye Amal ta buɗe ƙofa, ta na ganin zainab ta fasa ihu da ƙarfi ta rungume ta

Rumgume juna sukai suna murna, sororo Iya ta tsaya tana kallon Amal, 

A ranta tace, “Kai ido na ne, ba ita bace”

Sakin zainab tayi taje ta rungume IYa itama tana mata sannu da zuwa

IYA se faman aikin yaƙe take, dan gani take idon ta kamar ba dai-dai yake ba.

Amal ce tayi musu jagora har cikin palon

Da fara’a sosai ummie ta tarbe su, kankace me an cika musu gaban su da kayan ciye-ciye da ruwa.

Zama ummie tayi suka gaisa da IYA, 

 Ɗan russinawa zainab tayi itama ta gaishe ta tana tambayar me jiki

Ummie tace “ai yaji sauƙi sosai wallahi, yanzu ya bar nan,”   kiran Amal tayi tace ” shigar da ita wajen shi”

A ɗan kunyace zainab ta tashi tabi bayan Amal zuwa palon Abbah 

Sakato IYA tayi tana kallon kowa, dan sun saka ta a duhu ita kam

Abdul na ciki ya kasa zaune ya kasa tsaye

Suna shiga lungun da ze sada ka da palon Abbah, Amal ta tsaya tace 

“ki shiga aunty zee, yana ciki”

Murmushi zainab tayi ma Amal, sannan ta ƙarasa shiga palon bakin ta ɗauke da sallama

Tana saka ƙafar ta a palon Abdul na tarban ta, har yaso ya ɗan tsorata ta

Cike da farin ciki Abdul ya rungume ta a ƙirjin shi yana sauke wata ajiyar zuciya me sanyi, murya ƙasa-ƙasa yace

“i missed you wife”

Murmushi tayi itama tana ƙara lafewa a jikin shi

Sun daɗe sosai a tsaye rungume da juna kafin daga baya su zauna a kan kujera ɗaya jikin su na gugar na juna

Duk sun kasa ce ma juna komi, se faman zuba murmushi suke.

Bayan shigewar zainab ne ummie ta kalli Iya tace 

“Bisimillah mama, baki sha ruwa ba”

Amal ce ta zauna kusa da Iya ta janyo kofi ta tsiyaya mata lemu sannan ta miƙa mata

Cike da shakkun inda take ta amsa ta fara sha a hankali itama ta tsura ma TV idanu kamar yarda taga kowa yayi.

Suna zaune dukan su, muslim yayi sallama ya shigo palon, idon shi direct akan IYA, 

Itama ɗaga idon da zatai suka yi ido biyu da shi, ai tuni ƙwaƙwalwar IYA ta dawo aiki,

A take ta sheda fuskar shi,

Da sauri ta waiga ta kalli Amal dake gaishe da muslim,

Murya a bayyane tace

“Anyi tsiyar, da gaske nan suka kawo ni”

Muslim da ya san me Iya ke nufi ya kwashe da dariya 

Ummie kam da mamaki take kallon yarda IYa tayi tsuru-tsuru da idanu tana kallon kowa ɗai-ɗai

“Ah, wai lafia?

Muslim da ya kasa ɓoye dariyar shi yace

“Barka da dare ummie, Abdul yana nan ne?”

Tsaf ummie ta manta da zainab na wajen Abdul tace

“Yana can palon Abbahn shi”

Komawa IYA tayi ta zauna ta kame a waje ɗaya, da ka ganta zaka san a ɗarare take, kiris take jira ta fella da gudu.

Kai tsaye muslim yasa kanshi cikin palon murmushi ɗauke a fuskar shi

Yana saka kanshi yayi maza ya dawo da baya yana yin gyaran murya

Zainab dake rungume jikin Abdul tayi sauri ta ja da baya, 

Abdul kam ko a jikin shi, 

Idon shi a kan ƙofa yace 

“Bana son gulma guy, kawai ka shigo”

ƙarasowa yayi yana kanne ma Abdul ido ɗaya

Basarwa Abdul yayi kamar be gani ba

Zainab kanta na a ƙasa, ji take ina ƙasa take ta shige saboda kunya

Muslim ne ya fara gaishe ta, kafin ta gaishe shi a kunyace.

Kallon Abdul yayi yace

“ina ta knocking a ƙofar ka naji shiru, ashe kana nan” yayi maganar haɗe da miƙa mishi ledar hannun shi.

Karɓa Abdul yayi yace “ai ina nan kusan kwana uku kenan”

Hankalin ta gaba ɗaya ta maida shi ga TV, Abdul ya taɓota

waigowa tayi, kafin yayi magana ta rigashi 

“ya kamata mu tafi gida fa, tare da Iya muka zo”

Ɓata rai Abdul yayi yace

“yarinya anan zaki kwana, Iya kuma za’a maida ta gida”

Bata san sanda ta galla mishi harara ba.

Dariya yayi yasa hannu ya dungure mata kai, sannan ya miƙa mata kwalin wayoyin, yace

“ɗauki ɗaya”

Kallon shi tayi, shi kuma ya ɗaga mata gira ɗaya, yasan sarai abinda zata yi kenan, 

Sosai abin ya bata dariya, daurewa kawai tayi ta ɗan murmusa kaɗan, sannan ta ɗauki ta hannun daman shi.

Murya a nutse tace

“JAZAKALLAHU KHAIRAN, DA LAFIA ME ƊOREWA”

Salon yarda tayi maganar, ba wai Abdul kaɗai ba, har muslim dake gefe yayi pretending kamar basu yake kallon ba seda ya burge shi ƙwarai

Ballanta na gogan naku

Murmushi me wahalar ɓacewa ga zuciya ya sakar mata, haɗe da faɗin “Amin Zainabu Abu me tagwayen suna”

Murmushi dukan su sukayi,

Dai-dai nan Amal tayi sallama ta shigo riƙe da wayar ta tana miƙa ma Abdul

Karɓab wayar yayi yana karawa a kunne, shiru yayi yana sauraran shi, can yace 

“Gasu nan zuwa”

Kallon muslim yayi, yayi mishi signal da ido, 

Shima signal yayi mishi ya tashi ya fito, yace

“A fito lafia amaryar mu”

Zainab bata ce komi, dan tunda taji yaya Abubakar ɗin ya iso ta miƙe tsaye

Muslim na fita ya sake janyo ta jikin shi, seda ya bata lafiyayyun sumba tukun ya saka hannun shi a aljihu ya ciro mata simcard ɗin ta na warcen wayar ya damƙa mata a hannu

“in kinje gida ki sa wayar caji, zan kira ki”

Kanta a ƙasa taƙi yarda ta ɗago kan tace “to”

Hannun ta ya kama, jerowa suka yi, suka fito a tare

Suna fitowa tayi maza ta ƙwace hannun ta daga nashi, tana ƙara sunne kai ƙasa

Iya na ɗaga kai taga zainab tare da Abdul, da sauri ta sadda kanta ƙasa tana da mutsu-mutsu da baki

Gaishe ta Abdul yake, amma sam taƙi yarda ta ɗago da kanta  balle ta amsa

Dariya kawai yayi yace

“shikenan iya, se nazo gidan da kaina, se muyi sabuwar gaisuwa” yana maganar yana murmushi, shi har ga Allah matar burgeshi take

har ƙasa zainab ta tsugunna tace

“zamu tafi ummie, Allah ya ƙara sauƙi”

Sosai ummie ta saka mata albarka,

Kafin ma ummie ta waiga saitin IYA, tuni tayi waje da sauri

Sosai abun ya ba kowa dariya, Amal ce ma ta bita a baya tana faɗin “ki jira to nayi maki rakiya”

Har bakin ƙofar palon Abdul ya rako zainab dake ta sunkuyar da kai, 

A nan sukai sallama da niyar zasuyi waya anjima

Ta fita, shi kuma ya koma ciki

Gab da zata fita gate muslim ya shigo, yaje sun gaisa da yaya Abubakar

Cike da girmamawa tayi mishi sallama ta fita

A ranta tace “lokacin da kowa ke gudun Abdul ɗina kai baka kuje shi ba, dole inga girman ka”

Tana fita ta taras da Iya har ta shige mota, Amal na tsaye ta saitin ta.

Ƙara rungume juna sukai sannan sukayi sallama, zainab ta buɗe gidan gaba ta shiga.

Zainab na zama bayan ta rufo ƙofar taji saukar azababben ranƙwashi a kanta

Da sauri tai ƙasa da kanta tana aza hannun ta ɗaya a kai

Waigowa tayi taga yarda Iya ke ta cika tana batsewa, kafin zainab tace komi iya ta rigata da cewa

“wallahi ba zan mutu ba se in lokaci na yayi, wannan ai yaudara ce, tun farko in da kince min gidan mijin ki zamu zo kin san ko ana ha maza ha mata ba zuwa zanyi ba, amma dan kin dena sona shine kikace wai Abida za’aje gaisarwa, to ta Allah bata ku ba wallahi, Allah yasa ban mance addu’o’in da kika koya min ba, haka nai ta zubo su har Allah yasa na fito lafia”

Banza tayi da ita, dan ba ƙaramin zafin ranƙwashin nan taji ba, a haka har suka ƙarasa gida Iya bata dena ƙorafin an yaudare ta ba.

WASHE GARI

Tun asuba alarammomin da Abie ya saka a gidan Abdul suke jin wani irin kuka me tayar da hankali, su kan su hankalin su yayi masifar tashi da jin irin sautin kukan

Duk da a cikin ruɗani suke, hakan be hana su ci gaba da karatun su ba, 

amma dukkan ɗan’adam ɗin da zeji wannan kukan tabbas tsiga jikin shi ta rinƙa tashi duk sanda ya tuna shi.

Wajen shaɗaya na safe kukan ya ɗauƙe ɗif, baka jin sautin komi se sautin karatun junan su, duk da hakan seda suka kai inda ya kamata su tsaya, sannan suka tsaya.

A JIYA

 zainab na shiga gida ta kaima mama wayar da Abdul ya bata, 

Karɓa mama tayi ta gani ta saka albarka sannan ta mayar mata.

Wayar maman zainab ta ɗauƙa ta saka layin ta a ciki, sannan ta saka tata sabuwar a caji

Maƙale wayar tayi a jikin ta, seda tayi sallar isha’i sannan ta lafe a lungu tana danna wayar, tana ta tunanin kome yake yi a yanzu

Number shi ta nemo tana ta kallo, se tayi kamar ta kira se ta fasa, 

haka tai ta kwatantawa, daga baya dai ta haƙura ta aje wayar a gefen ta ko ze kira bata ji ba.

Tsakanin zainab da Iya se dai kallo, tun a hanya ba wanda ya sake yi ma wani magana, kowa na fushi da ɗan’uwan sa.

Can har bacci ya fara ɗaukan zainab taji ringing ɗin wayar, seda ta kusa tsinkewa  tukun ta ɗaga murya ƙasa-ƙasa.

Sun kusan raba dare suna waya da Abdul, soyayya ce tsantsa a ke zubawa ba ƙarya, 

Sosai ya ƙara fahimtar ta, itama ta sake fahimtar wani abu daga cikin rayuwar shi  wanda be sanar da ita ba

Anan ne ma take jin, gobe ne ƙa’idar cikan kwanakin da Abie ya bashi na maganin shi

Sosai zainab tayi murna da jin hakan, nan yake sanar da ita ze shigo ya sake ganin ta.

Duk juyin da IYA zata yi se ta ja tsaki, ita wai an hana ta bacci, daga ƙarshe ma data gaji cewa tayi

“Wayasani koma da matar shi kike firar tayi miki basaja irin na su na hatsabibai ba da shi ba”

Banza zainab tayi da ita, amma maganar seda taso bata dariya, dakewa kawai tayi.

Daga can Abdul ke tambayar ta “waye ke magana”

Da gayya zainab tace

“Iyace da bata gani tayi shiru”

Da sauri IYA ta miƙe zaune tana kallon zainab da tayi kamar bata ganta ba tace

“Fitina dai a kwance take, kuma Allah ya tsine wa me tayar da ita wallahi”

Bata sake cewa komi ba, ta yi a’uziyar ta, sanan ta tofa a gabas da yamma, kudu da arewa, tukun ta juya ma zainab ɗin baya taci gaba da baccin ta.

****wajen ƙarfe biyu, bayan sun idar da sallar azzahar suka fara jin taku alamun sawun ƙafafu da yawa, da kuma sautin kukan ɗazu da safe yana tashi a hankali ba kamar ɗazu da akeyi da ƙarfi ba

Kasa hakuri sukayi, seda ɗaya daga cikin su ya ɗauki waya ya danna ma Abie kira

Dai-dai lokacin da Abie ke sallamar baƙon shi wayar su ta shigo ta shi wayar

A fili ya furta “tun jiya daman nake jiran kiran naku”

Da sallama ya ɗaga call ɗin, tare da sauraren maganar ta ɗaya ɓangaren

Tas seda suka gama mishi bayani

Murmushi kawai na gani a fuskar Abie, can da ya gama ji se yace

“Kar ku tsaya da abinda kuke yi, nima ina tafe da izinin ubangiji”

Bayan sun yi sallama, Abie ya sauya akalar kiran ga Abbah da shima be daɗe da shiga gida ba, yana ɗagawa Abie yace

“Ina son mu haɗu da kai a can gidan Abdul’aziz”   tas Abie yayi mishi bayanin Abinda yake expecting

Shiru Abbah yayi, shima yana jin tsiga jikin shi na tashi, amma haka nan ya dake yace

“Zan iya zuwa da meɗaki na?”

Shiru kaɗan Abie yayi, har yayi niyar cewa a’a, can dai yace “zaku iya zuwa, ba matsala”

Sallama su kayi sannan kowa ya aje wayar shi.

Tsaf Zainab da mama suka kammala girkin da za’a kai ma alarammomin su ka haɗa komi da komi da ya kamata a waje ɗaya.

Abie na shiga gidan yace

“Ki shirya, sannan zainab ma ta shirya zamu je can gidan nata”

Ba wanda yace komi a cikin su, se “to” da suka amsa da shi.

Zainab na shiga ɗaki ta iske missed calls ɗin Abdul da yawa, 

Ɗaukan wayar tayi zata kira shi, kafin ta kira call ɗin shi ya sakw shigowa

Tana ɗagawa yace

“Ina matata ta shige?”

Murmushi tayi tace

“Ina aiki ne, wayar na ɗaki”

Abdul ya sake cewa

“Dama zan gaya miki ne karki jira ni, zamu fita da su Abbah ne, in mun dawo zan zo”

“Allah ya dawo da ku lafia,” har suka gama wayar ta manta bata gaya mishi suma zasu fitan ba, ajewa kawai tayi ta shiga wanka da sauri.

Koda su Abdul suka isa gidan basu shiga ba, suna zaune a mota,

Ummie har ta gaji da tambayar ina ne nan, suna zaune dukkan su motar yaya Abubakar tayi parcking a gefen ta su

Abie ne ya fara fitowa kafin Abbah da Abdul su fito suma

Kafe shi da idanu zainab tayi, kallon shi take ko ƙyaftawa babu har mama na mata magana ba ta ji ba

Seda Abie yace su fito tukun Abdul ya san da zainab ɗin akazo

Tunda ya ganta ya kasa samun sukuni, bini-bini ya waigo ya ɗan kashe mata ido ya juya

Ummie kam se a yanzu ta gane inda sukazo, gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi, dan bata san dalilin da yasa Abbahn Abdul yace ta shirya su zo ba

Sosai akai gaisuwar mutumci tsakanin mama da ummie, basu taɓa ganin juna ba se yau

Abie da Abbah ne a gaba, se Abdul da yaya Abubakar, sannan matan  a baya suka shiga gidan.

Sautin karatu ne kawai ke tashi har ta haraban gidan ana jiyowa, 

A hankali zainab ta sake matsawa kusa da mama, murya ƙasa-ƙasa tace

“wai dama basu gama ba mama?”

Shiru mama tayi, bata ce komi ba har suka shiga palon

Alarammomin na ganin su Abie, suka samu waje suka tsaya da karatun

Sosai kukan da suke ji ya sake yawa, ganin shigowar su Abie gidan

Tunda matan nan suka ji wannan sauti hankalin su ya fara tashi

Dole ko kaine kaji sautin kukan nan hankalin ka ya tashi

Tsuru-tsuru ummie tayi tana kalle-kalle taga ta ina ne kukan ke fitowa,

Iyakacin kallon ta bata hango komi ba, 

sedai ta haƙura ta sadda kanta ƙasa kamar yarda taga zainab da mama sun yi suma.

A nutse Abie ya yi bisimillah sannan ya kalli Abbah yace

“Alhamdulillah, abinda yasa nace mu haɗu a nan shine dan ku gane ma idanun ku abinda na faɗa muku”

Tsit palon yayi, daga muryar Abie se kukan dake tashi kaɗan-kaɗan ake ji a palon

Gyara zama sosai Abie yayi yace

“Aziza!”

Seda Abie ya kira sunan ta sau kusan uku tukun ta amsa a galabaice da

“Inajin ka malam”

Ummi najin muryar ta tasake lafewa a jikin Abbah, tana ta faman baza idanu

Abie ya sake cewa 

“nasan kina jina ai, kin shirya tafiya ke da tawagar ki ko kuwa mu ɗora daga inda muka tsaya??”

cikin muryar kuka sarauniya aziza tace

“Na shirya malam, kun riga da kun min illa, kunyi ma duk wani makusanci na illa, naso tun ranar in tafi ba se ka dawo ka iske ni ba, amma kasa an kamamu an hana mu guduwa, dan Allah ku barmu da raunin da ka ji mana muje muyi jinyar sa”

Ɓata rai Abie yayi yace

“kuje kuyi jinya sannan ki dawo da ƙarfin ki dan ki hana bawan Allah saƙat ko??”

Ya ƙarashe maganar cikin tsawa

Cikin kuka tace

“Wallahi ba haka bane, in har ka barni na tafi bazan ƙara dawowa ba, zanyi nisa sosai da nan, ayi mana afuwa dai”

Shiru Abie yayi, can daga baya yace

“Yanzu jikin shi da kike yawan zama ai kin san kin mishi illa ko?, shima duk kina nufin in barki ki tafi da alhakin wannan?”

Sosai sautin kukan ta ya ƙara sama, kamar ba zatayi magana ba, can dai tace

“Wallahi, tallahi ban taɓa shiga jikin AZIZ ba, kuma ban taɓa bawa wani damar shiga jikin shi ba, abinda nake so ne fa, ni kawai na kula da shi ne a lokacin da bashi da me kula da shi, 

a dalilin tausayin shi ne har ƙaunar shi ta shiga cikin raina, amma ni ban taɓa cutar shi ba dai’dai na kwana ɗaya seda naga ana ƙoƙarin raba ni da shi ƙarfi da yaji yasa na fara bugar da shi da sarewa ta, amma ni ban taɓa huda jikin shi ba”

Tunda Aziza ta fara maganar a dalilin kulawar da ta bashi ne ta fara son shi, ummie ke kuka, kuka sosai, kukan nadama da ta jima tana yin shi a ɓoye.

Duk wanda ke cikin palon nan jikin shi yayi sanyi matuƙa

Gyaran murya Abie ya sake yi a karo na da dama yace

“Zan rabu da ke amma a bisa wasu sharuɗa da zan gindaya miki yanzu,

Na farko, kar na kuskura na sake jin ɗuriyar ki ko wani naki a nan, sannan kin san nasan ƙulunboton munafurcin ku ko?, to in har na kama ki da ɗaya daga cikin su, wallahi, wallahi in har kika kuskura na ƙara kamaki bazan taɓa sakin ki ba”

Murya a sanyaye itama tace

“Na amince, amma ina neman alfarma ɗaya malam”

Abie yace “faɗi”

Kuka na son yaci ƙarfin ta tace

“ina son inyi magana da AZIZ, yanzu bani da wannan damar raɓar shi seda izinin ka”

Abie yace

“Faɗi kome zaki faɗa anan kowa yaji”

Shiru tayi, dan har an fitar da ran cewa zatayi magana, can dai tace

“ina son ka Abdul, sannan amsa ɗaya da ka kasa samun ta tun wancen lokacin, to zan faɗa maka amsar ka” ba ta jira cewar shi ba taci gaba

“Shedar daka saka a kan ƙabarin mahaifiyar ka, da jikin bishiyar nan, ba kowa ne ya cire su ba se ni, nasan kayi tunanin ko Abbahn ka ne ya cire, to tabbas bashi bane, ni na cire ta saboda wasu daga jinsin mu da suke ƙoƙarin kawo maka hari, to na tabbata da in kazo ka dena gane wajen zaka dena zuwa maƙabartar gaba ɗaya, 

Abu na ƙarshe da zance shine, ka yafe min a in har kaga akwai cutarwa a cikin zaman da nayi tare da kai

Sannan kaba matar ka haƙuri na hanata sukuni da nayi na ƴankwanakin data yi a gidan ka, Allah ya dauwamar da farin ciki a cikin rayuwar ka ya sake haɗa mu da alkairin sa ko ba anan gidan duniya ba”

Sosai zainab ke kuka, gaba ɗaya wani tausayin tane ya kamata, 

Abdul kam idanun shi sun kaɗa sunyi jajir ga kukan zainab daga gefe yana ƙara tunzira mishi zuciya

Duk ɗan’adam ɗin dake palon jikin shi yayi sanyi matuƙa, sun ɗau ɗan lokaci a haka kafin daga  bisani Abie ya ce

“zaku iya tafiya dukan ku”

Suna nan a zaune, abun mamaki suka rinƙa jin takun tafiya ƙafafu da yawa, har wata iske ke tashi saboda yarda suke tafiyar

Ga wata hayaniya da ke tashi, amma baka gane me ake cewa

Sun kai kusan awa ɗaya suna jin wannan tafiya da hayaniya kafin daga baya suji ɗif, ba takun tafiyar, ba kuma hayaniyar.

Abdul yayi, yayi ya haɗa ido da zainab amma taƙi yarda, 

Duk wani iri yake ji ganin yarda take kuka

A ranshi faɗi yake 

“Allah yasa su Abie suce suyi zaman su ba se sun wani koma can ba”

Be gama tunanin ba yaji muryar Abie na cewa

“Alhamdulillah, insha Allah komi yazo ƙarshe,” waigawa yayi saitin inda mama ke zaune yace

“Dalilin da yasa nace kizo, dan ki ganewa idanun ki abunda ze faru ne, ba dan komi ba se dan hankalin ki ya sake kwanciya a matsayin ki na uwa me son ƴarta”

Haka zalika kema haka zainab, dan ki sake samun nutsuwa da kwanciyar hankalin zama a gidan mijin ki.

Miƙa ma Abbah hannu yayi suka gaisa, tukun yace

“Nace kaima kazo ne dan hankalin ka dana iyalan ka su sake kwanciya akan lamuran, 

Hausawa suka ce gani ya kori ji ko?”

Gaba ɗaya sukai murmushi, sannan Abie ya sake cewa

“Zamu tafi, se a barsu su ƙarashe sauƙar su ta yau, zuwa dare inshaAllah kai Abdul’aziz se kazo gida ka ɗauki matar ka,

Sannan ku riƙe addu’a da azkar ɗin safe da yamma, inshaAllah ba wani abokin halitta da ya isa ya cutar da ku, Allah yayi muku albarka”

Da amin suka amsa gaba ɗayan su, banda zainab dake ta faman ajiyar zuciya

Kafin su tafin, Abbah seda ya sake jaddada godiyar shi ga Abie a bisa namijin ƙoƙari da yayi a rayuwar ɗan shi

Murmushi Abie yayi yana ƙara bashi hannu sannan yace “Duk yiwa kaine, ɗa na kowa ne ai”

Da haka suka fito, Abbah suka shiga motar Abdul, 

Abie kuma da nashi iyalan suka shiga motar Abubakar, kowa ya kama hanyar gidan su.

Tunda ummie ta shiga motar take kuka, 

Daga Abbah har Abdul ba wanda yace mata uffan, shi Abdul ma gaba ɗaya hankalin shi na ga ƴar zainabun shi, so yake yasan kukan me take, kukan murna ne ko kuma kukan wani abunne daban?.

Har cikin gida Abdul ya shiga da motar, sannan Abbah ya buɗe side ɗin shi ya fita, so yake ya dangane da ɗakin shi shima ya sauke kukan dake cin shi tun a gidan Abdul.

Ganin Ummie bata fito ba yasa Abdul ya zagaya ya buɗe mata ƙofar da kanshi, ya kamo mata hannu suka shiga cikin palon

Su Amal duk suna zaune, sun gama aikin data saka su, sannu da zuwa suka fara yi musu, amma ganin yarda ummie ke ta risgar kuka yasa sukai tsuru-tsuru suma

Seda Abdul ya kai ummie har kan kujera tukun ya juya ze tafi

A hankali ta buɗe baki, murya cikin kuka tace

“Abdul”

Waigowa Abdul yayi yana kallon ta

Jiki a sanyaye ta tashi daga inda take taje kusa da shi

Yana jiran yaji me zatace da shi, kawai yaji ta rungume shi ƙam a jikin ta, tana ƙara fashewa da kuka me cin zuciya

Hannu biyu ya saka ya rungume ta shima tsam a jikin shi yana sauke wata ajiyar zuciya

Murya na rawa ummie tace

“ka yafe min Abdul, ka yafe ma ummin ka dan Allah!!”

Da ƙarfi Abdul ya rumtse idanun shi, yana jin wani iri a cikin ranshi

A hankali ya buɗe idanun shi yaga su Amal suma kukan suke, sun riƙe hannun juna ita da fauza

Murya a sanyaye yace

“Duniya da lahira na yafe miki ummie, ban taɓa riƙeƙi ba dai-dai da kwana ɗaya a rayuwa ta, dan haka ki dena bani haƙuri dan Allah”

Da sauri Abbah ya saki labulen ɗakin shi dan kar su ganshi yana leƙen su.

Ɗaya bayan ɗaya Abdul ya rungume ƙannen nashi.

Wasa-wasa seda Abdul ya ɓata lokaci anan, har seda yaga ummie tayi dariya kafin ya tashi ya ɗauro alwalar sallar la’asar, suka wuce masallaci shi da Abbah.

A hanya su Abie kafin su kai gida, suna ta ƙara tattauna maganar shi da mama da yaya Abubakar, 

Zainab dai bata saka musu baki ba tana gefe tayi shiru

Tana zaune a hakan alamar saƙo ya shigo wayar ta

Kamar bazata kula ba, ta dai ɗauka ta buɗe

“kukan me kike yi?”

Taga an rubuta da emoji na sad a gaba

murmushi kawai tayi ta rubuta “nothing” da emojin zare ido a gaba

Can wani saƙon ya sake shigowa  “anjima zaki bani labari ai yarinya”

Aje wayar tayi bata sake replying shi ba, suna zuwa gida direct ɗaki ta wuce tayi kwanciyar ta

Kallon ta IYA tayi tace

“Me akayi miki ne zainabu na?”

Ɓata rai zainab tayi tace

“Ni ba komai”

Sam IYA bata ƙaunar taga damuwa ko kaɗan a tare da ita, ballanta na har taga tayi kuka

Matsowa kusa da ita tayi tace

“sedai in ba zaki gaya min ba dai, amma daga ganin idanun ki kin sha kuka ne, ko dai wani ne ya mutu?”

Cikin gajiya zainab tace

“Bafa wanda ya mutu IYA, kawai tausayin wata ne ya saka ni kuka wallahi”

Tagumi IYA ta zabga tana kallon zainab yarda idanun nata ya sake kawo kwalla tace

“Tunda naga kince hakan, tabbas abun a tausaya ne, wacece wannan?”

Da kamar zainab ba zata ce komi ba, can dai tace

“Kin san Allah IYA, wallahi dan dai abinda nake tunani baze taɓa kasancewa ba, amma da se ince aljanar nan tazo mu zauna tare da ita, se a bata ɗaki ɗaya”

Salati me ƙarfi IYA ta buga tana ƙoƙarin tashi tsaye, amma ta kasa yunƙurwa tsabar yarda taji cikin ta ya murda mata

da ƙyar da bisimillah Iya ta yunƙura ta tashi, ko kallon zainab bata yi ba tayi waje da sauri tana ɗan ɗingisa ƙafar ta data riƙe tai hanyar palon mama

“Binta, ina mijin ki?, Abie dake zaune can gefe ya tashi yace

“IYA lafia kuwa?”

“ina fa lafia, wallahi kuje can ɗaki na ku duba, da wiya ba gamo na sake yi ba, in ko ba gamo nayi ba to  tabbas zainab ta rikiɗe ta zama wani jinsin daban”

Zaunar da IYA Abie yayi ya bata labarin duk wani abu da ya faru be ɓoye mata ba

Ƙwale IYA tayi tana mamaki maganar ɗan nata

Seda Abie ya gama bata labarin tas, tukun yayi shiru

Numfasawa IYA tayi ta haɗe miyau da ƙyar sannan tace

“wallahi in wani ya faɗa min wannan maganar bazan taɓa yarda ba, amma tun da a bakin ka naji na yarda”

Chan ta ƙara numfasawa tace

“Oh su Binta yau kun ga lukutayen masifu kuma?”

Ta ƙara da ” in da nasan ta lalama aka rabu da na shirya na biku wallahi, in gane ma idanu na yarda zan fi Iya bada labari ko anan gaba, duk da hakan ma zan ƙaras tunda abun da muga gani har abada bazaku taɓa jurewa ba in kune kuka gani”

Abie da mama basuce komi ba, 

Iya har ta tashi zata fita daga ɗakin ta dawo tace

“Banda zainabu na ta rigada ta ci tafashen kyankyasai na jinsin waɗan can, ta gama rikiɗewa, ina ita ina jin wani tausayin ta, halittun da jin su kawai tashin hankali ne ballanta na har kai bawa kayi tunanin haɗa matsuguni da su, to Allah ya tsayar iyakacin kanta”

Ta juya ta fice abunta ta koma ɗakin da har bacci ya fara ɗaukar zainab.

Kusa da Zainab ɗin ta zaune tace

“Tashi zainabu na,”

Tashi zainab tayi tana kallon IYA da idanun ta da suka nuna bacci sosai, tace

“Barka zainabu na, nayi murna ƙwarai da gaske da labarin da naji a wajen baban ki”

Shiru zainab tayi tana ɗan murza idon ta

Ƙasa IYA ta sake yi da muryar ta tace

“Amma ban da abunki ina ke ina wani jin tausayin ta, kedai ki gode ma Allah da ni kaina ba zaune nake akan ki ba, addu’a ce nake banko maki ta ko’ina, sannan mahaifin ki ya ƙarashe aikin da na fara”

Da ƙarfi zainab ta kwashe da daria tana kallon IYA da tai wuƙi-wiƙi da idanu jin dariyar zainab ɗin

Ɓata rai IYA tayi tace

“Kin ga ki nutsu ki dena irin wannan dariyar wallahi, tsab mutum se yayi tunanin kin rikiɗe gaba ɗaya”

Ganin zainab taki barin dariyar ne yasa IYA tashi ta bata waje.

Gab da za’a kira sallah magariba mama ta sake saka zainab tayi wanka ta shirya tsab a sabon ɗinkin da maman tasa akayi mata

Ta ko’ina zuba ƙamshi take, 

IYA da kanta ta haɗa mata kayan ta da ta zo da su a jaka

Magana ce fal a bakin IYA amma ta kasa yin ta.

Tun kafin akira sallah Abdul ya baro gida, yayi ma ummie sallama, amma be yarda ya haɗu da Abbah ba, ya saɓar ya nufi unguwar su zainab

Yana isa ana kiran sallah, dama da alwalar shi, masallacin kawai ya shige akayi sallah da shi.

Bayan sun idar da sallar, tare da Abie suka ƙarasa cikin gidan inda ya buɗe mishi palon shi yace ya zauna

Shiga yayi ya zauna ya zuba ma ƙofa ido yaga ta ina matar shi zata ɓullo

Abie na shiga cikin gidan ya ƙwala ma zainab dake ɗakin mama zaune tana ɗan tunasar da ita abubuwa kira.

Amsawa tayi, kafin ta fito shi ya shigo ɗakin

Shima ɗan nashi nasihar ya ɗora da ita, tukun yace taje yana jiran ta a palo

Shiru zainab tayi tana ɗan jin wani iri haka

IYA ce ta ƙaraso ɗauke da jakar kayan zainab a hannun ta, itama jikin ta duk yayi sanyi tace

“muje na kaiki mota zainabu na”

Da kallo kawai mama da Abie suka bi su, har suka fice IYA na mata magana ƙasa-ƙasa wanda koni kaina banji me take ce mata ba.

Sanda suka fito Abdul har ya fita ya tsaya a jikin motar shi

Har gaban shi IYA ta kai zainab, ta kamo hannun ta sannan ta riƙo nashi ta danƙa mishi

Idon ta akan shi tace

“Ga zainabu na nan amana wallahi,

Sannan na maka murna ance ka saki ɗayar matar ko?”

Dariya Abdul yayi yana ƙara riƙe hannun zainab ƙam a nashi yace

“Allah yayi ta sake ni kam, dan ba ni na sake ta ba”

Taɓe baki IYA tayi tace

“Dole dai ayi maku barka kun rabu da alaƙaƙai”

Ta ɗora da “kuyi ku tafi iska gari kar ta gama kaɗe ɗan turaren da zainabu na ta fesa”

Zumɓura baki Zainab tayi tace

“Kai IYA, ai se ayi tunanin mutum baya sakawa”

Dariya Abdul yayi ya karɓi jakar hannun iya ya saka a sit ɗin baya, sannan ya zagaya ya buɗe ma zainab gaba ta shiga

Hannu ya saka ya ɗakko kuɗi a aljihun shi ya kama hannun IYA ya saka mata yace

“Ga tukuicin rako min mata da kika yi hajiya IYA”

Har IYA ta karɓa ta fara godiya, kome ta tuna, tayi saurin jawo hannun shi ta saka mishi kuɗin ta tace

“Riƙe abunka kar azo ban sani ba nan gaba labari ya canza ace an taɓa bani sadaki kuma na karɓe ayi ta kai ruwa rana”

Sarai Abdul ya gane me take nufi, dariya kawai yayi yace

“Shikenan IYA, se kinzo cin girkin amarya ta”

Ya juya ya shige mota ya bar IYA a nan tsaye tana kallon su.

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/12/kishi-da-aljan-chapter-9-complete-hausa.html

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU🤲

KISHI DA ALJANA👹

NA MRS SULAIMAN(ZAINAB FALALU)

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg42 A

Suna fara tafiya ya ɗan waiwayo ya kalle ta, sannan ya maida idon shi a hanya yace

“Baki gaya min kukan da kike ba ɗazu?”

Shiru zainab tayi tana ƙara tuna moment ɗin ɗazun

Murya a sanyaye tace

“wallahi azizar nan ta bani tausayi, tana son ka da yawa gaskiya, wallahi da mutum ce zan iya yarda mu zauna tare da ita”

Ƙara waigowa yayi ya kalle ta, murmushi kawai yayi sannan yace

“shine kukan da kike yin?”

Gyaɗa kanta kawai  tayi itama taci gaba da kallon hanya

Ajiyar zuciya ya sauke, murya a sanyaye yace

“Allah ya jiƙan Ammah na, ita kuma Allah ya bata ladan abinda ta aikata”

A hankali zainab ta amsa da “amin”

Shiru motar ta sake ɗauka, 

Gab da zasu karya kwanar gidan su Abdul yayi parcking a daidai wajen masu gasa daƙwa-daƙwan kaji

Seda ya daidaita tsayuwar motar tukun ya waigo ya kalli zainab da idon ta ke a kan wayar ta yace

“ina zuwa jikar IYA”

Ɗago kanta tayi ta kanne mishi ido ɗaya murmushi ɗauke a fuskar ta

Shima murmushin yayi yana mayar mata da martanin ɗaga girar da tayi.

Manya-manyan kaji guda biyu ya zaɓa, bayan an sake gasa mishi su aka naɗe mishi aka saka a lede, 

Yana zuwa a sit ɗin baya ya buɗe ya saka, sannan ya zagaya ya shiga motar

Tunda zainab taji ƙamshin kazar nan take haɗiye miyau, haka nan dai ta daure har suka ƙarasa gidan

Da kan shi ya fita ya tura gate ɗin, sannan ya dawo ya shigar da motar, 

Seda ya daidaita ta a inda ya dace sannan ya sake fitowa ya rufe ƙofar gidan

Zainab na zaune tana kallon shi, idon ta a kanshi

Gani tayi bayan ya tura ƙofar ya ɗan jima a wajen 

Murmushi kawai tayi sannan tace

“Alhamdulillah”

Seda ya gama addu’ar shi tukun ya dawo inda ya barta a tsaye, bayan motar ya buɗe ya ciro ledojin da tun kafin ya je ɗakko zainab ɗin ya tsaya yayi siye-siyen shi

Ganin ledojin sun mishi yawa yasa ta karɓi wasu itama ta riƙe

Da hannu ɗaya ya saka ya kulle motar sannan ya kama hannun ta suka wuce ciki.

Suna shiga ciki zainab ta tsaya tana kallon palon da mamaki

Waigowa Abdul yayi ya kalle ta yace

“ya kika tsaya a nan?”

Still da mamaki a fuskar ta tace

“Baka ji yarda palon ke ƙamshi bane?, ga ko ina yana ta ƙyalli fes-fes”

dariya yayi me ɗan sauti, 

seda ya aje ledojin hannun shi tukun ya dawo ya karɓi na hannun ta ya kai ya ajiye, sannan ya janyo hannun ta ya ƙarasa shigowa da ita yace

“A haka kike cewa dama a bata ɗaki, bayan kina tsoron ta a fake?”

Zumɓura baki tayi, sannan tace

“Ni ai ba wannan maganar nayi ba”

Dungure mata kai yayi yace

“To ba ita bace ta gyara wajen, ɗazu bayan mun koma gida ummie tasa aka zo aka gyara ko’ina”

Ɗage mata duka girar shi yayi sannan yace

“Shikenan ko?”

Murmushi zainab tayi ta ɗan kauda kanta gefe.

Shigar su kenan aka kira sallar isha’i

Idon shi na kan TV yace

“je kiyo alwala miyi sallar isha’i”

Hankalin ta na ga game ɗin data fara tace

“Ina da alwala”

Anan palon sukayi sallar, sannan suka haɗa da nafilar su raka’a biyu

Sosai suka yi addu’a haɗe da sake miƙa godiyar su ga ubangiji.

Seda suka gama Abdul ya kalle ta yana shafa cikin shi

Itama kallon shi tayi tace

“Ya akayi?”

Da ido ya nuna mata ledojin da suka shigo dasu, yace

“ɗakko mana muci, tsabar ɗokin ganin matata yasa banci wani abinci kirki ba yau”

A nutse ta miƙe, har ta fara yafiya ya kirata ta dawo

Da kanshi ya kama hijabin jikin ta ya cire mata, 

Bata ce komi ba ta juya ta nufi kitchen

Plate da cups ta ɗakko, seda ta ɗauraye su tukun ta ɗora su akan wani ɗan madedecin tray sannan ta fito

Aje su tayi a gaban shi, ta wuce ta kwaso ledojin suma ta zube su anan

Bubbuɗewa tayi ta ware wanda zasu iya amfani da su, sannan ta kwashe sauran ta kai kitchen, ta aje na ajiye wa, sannan tasa na fridge tukun ta fito.

Wasa-wasa, tun tana jin kunyar cin kazar nan, seda Abdul yasa ta ajiye wata kunya can gefe ta kwashe ya yarda ya kamata

Suna ci suna hira, mafi akasarin firar, labarin IYA ne zainab ke bashi

Aikuwa Abdul yaci dariya harda su shaƙewa

Seda suka gama ci a tare suka ɗauke komi suka kai kitchen, wanke hannayen su sukayi sannan suka dawo palon

Seda suka zauna Abdul ya waiga ya kalle ta yace

“wallahi kema kin yi masters a shaƙiyan ci”

 A tare suka kwashe da dariya, suna ɗaga gira a tare

Can Abdul ya sake cewa

“shikenan yarinyar nan ta koya min ɗaga gira “

Murmushi zainab tayi tace

“Ba ruwan jikar IYA”

Mamutsota yayi da ƙarfi, har seda tayi ƴar ƙara, yace

“in babu ruwan jikar IYA, ai akwai ruwan matar Abdul ko?”

Murmushi kawai tayi, tana ƙara kwanciya sosai a jikin shi, wata nutsuwa da farin ciki na ƙara kamata.

Sun kai wajen goman dare zaune, 

Su tsokani juna, suyi kallo sannan ayi fira.

Shaɗaya saura Abdul yace

“dare yayi malama, ya kamata muje mu kwanta”

Bata ce komi ba, sedai ta tashi zaune dage kishingiɗan data yi

Da kanshi ya kashe komi da komi da ya dace a kashe

Hannu ya miƙa mata, ba musu ta ɗora nata hannun akan nashi, ɗagota yayi, sannan ya saka ɗayan hannun ya ɗauki hijabin ta dake ajiye, suka haura sama

Suna haurawa ta miƙa mishi hannun ta

Da ido ya tambaye ta me ze bata?

Itama da ido ta nuna mishi hijabin ta dake hannun shi

Murmushi kawai yayi ya bata

Kallon shi tayi a ido tace

“Good night, kar ka manta da addu’a Guru”

Tana faɗin haka ta kwasa da gudu ta shige ɗakin da su IYA suka fara kaita

Sosai Abdul ya tsaya ya kwashi dariyar shi, dariyar data fara bashi shine na kiran shi da “guru” datayi, se kuma gudun data kwasa ta shige ɗaki.

Ba laifi, seda ya dara sosai sanan ya juya shima ya shige ɗayan ɗakin ranshi fari tass.

Itama seda ta gama kwasar dariyar tukun ta kunna heater

Kafin ruwan yayi zafi, seda ta sake kunna bunner ta zuba turaren wuta me ƙamshi, sannan ta cire kaya ta janyo towel akan ƙofar toilet ta ɗaura

Ninke kayan ta tayi, ta maida cikin walldrob sannan ta ɗauki rigar bacci a cikin irin wanda yaya Abida taje sabon gari ta kwaso mata

Seda ta zaɓi me kyau sannan ta ciro ta, ta ajiye ta a gefen gado, tukun ta shiga wanka

Sosai zainab ta zauna ta zazzage cikin ta, tukunna ta shiga ta yi wanka da ruwa masu ɗumi sosai

Tas ta goge jikin ta bayan ta gama, sannan ta wanke bakin ta 

(ƳAN’UWA NA MATA, A DAURE A RINƘA WANKA KULLUM KAFIN A KWANTA BARCI,  SANNAN TSABTAR BAKI MA KAR KUYI WASA DA ITA,

TSAFTA NA KANKARO MA MACE DA AJI DA KUMA ƘIMA A IDON MEGIDA, 

KANKAT DAGA HADISI INGANTACCE YACE “ANNAZAFATU MINAL IMAAN” MA’ANA, “TSAFTA TANA DAGA CIKIN IMANI”)

Zama tayi a gaban mirrow ta shafa mai sama-sama, sannan ta ɗauki turaren ta me mai me kuma daɗi da sanyin ƙamshi tabi lungu da saƙo na jikin ta da shi

Sannan tazo ta ɗora da humrar ta me daɗin ƙamshi itama

Turaren miski ta ɗakko ta shafa matsematsin cinyar ta da ɗan gefen marar ta kaɗan, tukun ta janyo rigar ta feshe ta da turaren element shime me sanyin ƙamshi da kuma daɗi, sannan ta saka

Gaba ɗaya ɗakin ya hautsine da ƙamshin lotion ɗin ta, da kuma na turaruka  data shafa, uwa uba ga turaren wutan da shima ya gauraye da sauran turarukan

Se ɗakin ya bada wani ƙamshi me aji da daɗin shaƙa

Remote ɗin Ac ta ɗauka ta daidaita temprature n ta, tukun ta haye gadon ta haɗe da sauke ajiyar zuciya me sanyi.

Ta ɓangaren Abdul ma hakan ce ta kasance

Yana shiga wanka da brush ya fara yi, 

Sama-sama ya shafa mai, sannan ya shafa roll on, 

Sabon boxers dal ya ɗauka ya saka, sannan ya ɗora jallabiya a kai

Wayoyin shi ya ɗauka bayan ya saka su a silent, tukun ya kashe wutar ɗakin ya janyo shi

Kanshi tsaye ya tura ƙofar ɗakin zainab ya shiga

Yana shiga ya wani lumshe ido yarda ƙamshin ɗakin ya bige shi

Abdul dama ba baya ba wajen son ƙamshi

Zainab najin ya buɗe ɗakin tayi shiru tana ƙara lafewa a cikin bargo

A hankali ya saɗaɗa ya haye gadon shima ya damƙota da ƙarfi

Ƴar ƙara ta saki, dariya ya kwashe da ita yace

“Dama na san baki isa yin bacci ba yanzu yarinyar”

Banza tayi mishi ta ƙara lafewa, tana wani sinne kai 

Hannun shi ya zira ta cikin bargon ya fara mata cakulkuli

Aikuwa nan da nan zainab ta haukace mishi da dariya tana tutture shi

Sosai sukai ta dariya kamar wasu wanda suka zare

Sun jima suna wasan su kafin daga baya su nutsu su kwanta.

Hummmmmmmmmmmmmmmm!!!!! A wannan dare Abdul ya zama zainab,

Zainab kuma ta zama Abdul, duk da dai ansha fama da jikar IYA amma sanin hukuncin komi a addini yasa komi yazo ma Abdul da sauƙi.

ASUBAH TA GARI ANGO DA AMARYA.

*****Tun da Abbah ya farka yake murmushi da murna, 

Gefen shi ummie ta zauna tace

“wannan murmushi haka Abbahn Abdul, ko dai ta samu ne?”

Itama tayi maganar tana ɗan murmusawa

Murmushin ya sake yi yace

“kawai nayi mafarkin Abdul da murjanatu ne, muna ta murna da nishaɗi a wani ƙayataccen waje me kyau da tsari”

Murmushi ummie ta sake yi tace

“ah lallai, dole kayi ta murna haka Abbahn Abdul, to Allah yasa alkairi ne”

Kallon ta yayi yace “inshaAllah alkairi ne”.

****Abdul ne ya fara farkawa daga baccin da tunda yake a rayuwar shi be taɓa yin makamancin shi ba,

Da sunan Allah a bakin shi ya farka, yana ƙara tabbatar da lallai bafa a mafarki komi ya faru ba

Murmushi me yalwa yayi yace

“Da gaske ne wallahi”

Shiru yayi ya kafe ta da idanu yana kallon yarda idonta ke mar-mar alamun idon ta biyu

yatsar shi ya ɗora akan idon ta ɗaya, da sauri ta bige hannun shi 

Dariya yayi ya kara bakin shi saitin kunneta yayi maganar da ni kaina banji me yace ba

Da ƙarfi zainab ta ƙwalla ƙara tace

“wayyo IYA ta”

Sosai ya shiga yin dariya yana jan kumatun ta, 

Cikin nutsuwa yace

“Tashi to, lokacin salla  ze wuce mu”

Shiru tayi, taƙi yarda ta tashi balle ta buɗe idon ta, 

Seda taga be da niyar ƙyaleta, ga kuma da gaske lokacin sallar na wucewa yasa ta buɗe bakin ta a hankali tace

“Ka tafi can ɗakin, ni kuma zan shiga na nan ɗakin”

A saitin kunnen ta yace

“Naƙi yarinya, da wannan toilet ɗin zamuyi amfani dukan mu”

Sosai zainab ta kafe akan bazata tashi ba se ya fita

Ganin yarda ta kafe ɗin, ga kuma time na wucewa yasa ya tashi ya ɗauki jallabiyar shi ya saka, sannan yayi kissing forehead ɗinta tukun ya fice

Yana fita ta yunƙura da ƙyar ta saka ma ƙofar key, sannan tayi hanyar toilet bakin nan a zumɓure kamar shantu.

Sosai ta jima a toilet ɗin, 

Babu inda bata gasa ba a jikin ta, ɗaɗɗaurewar da jikin ta yayi se ruwan ɗumin ya temaka wajen sakewar shi

Tana zaune a cikin ruwan taji knocking ɗin Abdul, banza da shi tayi, seda ta gama kimtsa kanta tayi abinda ya dace, tukun tayi wankan tsarki sannan ta fito

Da ƙyar ta shafa mai, da ɗan turare, sannan ta samu doguwar riga mara nauyi ta saka ta ɗora hijabi a sama tukun ta ƙarasa bakin ƙofar ta buɗe

Tana buɗewa ta ganshi a tsaye da alamu shima ko sallar be yi ba

Kallon ta yayi yace

“kinyi sallar ne?”

Gyaɗa kai kawai tayi, bakin yana nan a yarda yake a zumɓure

Murmushi yayi ya kama hannun ta suka koma cikin ɗakin

Da kan shi ya shimfiɗa mu darduma, sannan ya tada iƙama, ya kabbara salla

Gajerun ayoyi ya ja musu ganin yarda take a takure, sukayi suka gama

suna idarwa tayi kwanciyar ta anan kan abun sallar, 

A hankali ya ɗagota zuwa jikin shi yace

“daure muyi azkar se ki kwanta kiyi baccin ki zainabun Abdul da IYA”

seda ta ɗan murmusa yarda yayi maganar cikin zolaya

ƙin tashi tayi ta lafe a jikin shi sannan suka fara karanto azkar ɗin safiya a tare kuma da ɗan sauti

أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ. 

اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَىْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ

‘A ‘oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem. 

Allaahu laa ‘ilaaha ‘illaa Huwal-Hayyul-Qayyoom, laa ta’khuthuhu sinatun wa laa nawm, lahu maa fis-samaawaati wa maa fil-‘ardh, man thai-lathee yashfa’u ‘indahu ‘illaa bi’ithnih, ya’lamu maa bayna ‘aydeehim wa maa khalfahum, wa laa yuheetoona bishay’im-min ‘ilmihi ‘illaa bimaa shaa’a, wasi’a kursiyyuhus samaawaati wal’ardh, wa laa ya’ooduhu hifdhuhumaa, wa Huwal- ‘Aliyyul- ‘Adheem.

 ikhlas 3

 suratul falaq 3

 suratul nas 3

أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ الْمُلْكُ لِلَّهِ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِيْ هَذَا الْيَوْمِ وَخَيْرَ مَا بَعْدَهُ، وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذَا الْيَوْمِ وَشَرِّ مَا بَعْدَهُ، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ، وَسُوءِ الْكِبَرِ، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِيْ النَّارِ وَعَذَابٍ فِيْ الْقَبْرِ

‘Asbahnaa wa ‘asbahal-mulku  lillaahi walhamdu lillaahi, laa ‘ilaaha ‘illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa Huwa ‘alaa kulli shay’in Qadeer. Rabbi ‘as’aluka khayra maa fee haathal-yawmi wa khayra maa ba’dahu wa ‘a’oothu bika min sharri maa fee haathal-yawmi wa sharri maa ba’dahu, Rabbi ‘a’oothu bika minal-kasali, wa soo’il-kibari, Rabbi ‘a’oothu bika min ‘athaabin fin-naari wa ‘athaabin fil-qabri.

اللَّهُمَّ بِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ أَمْسَيْنَا وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ، وَإِلَيْكَ النُّشُورُ

Allaahumma bika ‘asbahnaa, wa bika ‘amsaynaa, wa bika nahyaa, wa bika namootu wa ‘ilaykan-nushoor.

اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا أَمَتُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِر لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ

Allaahumma ‘Anta Rabbee laa ‘ilaaha ‘illaa ‘Anta, khalaqtanee wa ‘anaa ‘abduka, wa ‘anaa ‘alaa ‘ahdika wa wa’dika mas-tata’tu, ‘a’oothu bika min sharri maa sana’tu, ‘aboo’u laka bini’matika ‘alayya, wa ‘aboo’u bithanbee faghfir lee fa’innahu laa yaghfiruth-thunooba ‘illaa ‘Anta.

اللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ أُشْهِدُكَ وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ، وَمَلَائِكَتَكَ وَجَمِيعَ خَلْقِكَ، أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ وَحْدَكَ لَا شَرِيكَ لَكَ، وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُكَ وَرَسُولُك (×4)

Allaahumma ‘innee ‘asbahtu ‘ush-hiduka wa ‘ush-hidu hamalata ‘arshika, wa malaa’ikataka wajamee’a khalqika, ‘annaka ‘Antallaahu laa ‘ilaaha ‘illaa ‘Anta wahdaka laa shareeka laka, wa ‘anna Muhammadan ‘abduka wa Rasooluka. 

( Sau huɗu )

اللَّهُمَّ مَا أَصْبَحَ بِي مِنْ نِعْمَةٍ أَوْ بِأَحَدٍ مِنْ خَلْقِكَ فَمِنْكَ وَحْدَكَ لَا شَرِيكَ لَكَ، فَلَكَ الْحَمْدُ وَلَكَ الشُّكْرُ

Allaahumma maa ‘asbaha bee min ni’matin ‘aw bi’ahadin min khalqika faminka wahdaka laa shareeka laka, falakal-hamdu wa lakash-shukru. 

اللَّهُمَّ عَافِـني فِي بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِـنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لَا إِلَهَ إلاَّ أَنْتَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنَ الْكُفْر، وَالفَقْرِ، وَأَعُوذُبِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ ، لَا إلَهَ إلاَّ أَنْت(sau uku)

Allaahumma ‘aafinee fee badanee, Allaahumma ‘aafinee fee sam’ee, Allaahumma ‘aafinee fee basaree, laa ‘ilaaha ‘illaa ‘Anta (three times).

Allaahumma ‘innee ‘a’oothu bika minal-kufri, walfaqri, wa ‘a’oothu bika min ‘athaabil-qabri, laa ‘ilaaha ‘illaa ‘Anta.

 (Three times)

حَسْبِيَ اللَّهُ لَآ إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ (sau bakwai )

Hasbiyallaahu laa ‘ilaaha ‘illaa

 Huwa ‘alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Adheem .

 (Sau bakwai )

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي، وَدُنْيَايَ، وَأَهْلِي، وَمَالِي، اللَّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَاتِي، وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ، وَمِنْ خَلْفِي، وَعَنْ يَمِينِي، وَعَنْ شِمَالِي، وَمِنْ فَوْقِي، وَأَعُوذُ بِعَظَمَتِكَ أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِيَ

Allaahumma ‘innee ‘as’alukal-afiyata fid-dunyaa wal’aakhirati, Allaahumma ‘innee ‘as’alukal-‘afwa wal’aafiyata fee deenee wa dunyaaya wa ‘ahlee,/ wa maalee , Allaahum-mastur ‘awraatee, wa ‘aamin raw’aatee, Allaahum-mahfadhnee min bayni yadayya, wa min khalfee, wa ‘an yameenee, wa ‘an shimaalee, wa min fawqee, wa ‘a’oothu bi’adhamatika ‘an ‘ughtaala min tahtee. 

اللَّهُمَّ عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّماوَاتِ وَالْأَرْضِ، رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي، وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطَانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءاً أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ

Allaahumma ‘Aalimal-ghaybi wash-shahaadati faatiras-samaawaati wal’ardhi, Rabba kulli shay’in wa maleekahu, ‘ash-hadu ‘an laa ‘ilaaha ‘illaa ‘Anta, ‘a’oothu bika min sharri nafsee, wa min sharrish-shaytaani wa shirkihi, wa ‘an ‘aqtarifa ‘alaa nafsee soo’an, ‘aw ‘ajurrahu ‘ilaa Muslimin.

بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الَْأرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ (×3)

Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma’as-mihi shay’un fil-‘ardhi wa laa fis-samaa’i wa Huwas-Samee ‘ul- ‘Aleem.

 (Three times)

رَضِيتُ باللَّهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِيناً، وَبِمُحَمَّدٍ صَلَى اللَّهُ عَلِيهِ وَسَلَّمَ نَبِيَّاً (×3)

Radheetu billaahi Rabban, wa bil-‘Islaami deenan, wa bi-Muhammadin (sallallaahu ‘alayhi wa sallama) Nabiyyan.

 (sau uku)

يَاحَيُّ، يَا قَيُّومُ، بِرَحْمَتِكَ أَسْتَغِيثُ، أَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ، وَلَا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ

Yaa Hayyu yaa Qayyoomu birahmatika ‘astagheethu ‘aslih lee sha’nee kullahu wa laa takilnee ‘ilaa nafsee tarfata ‘aynin.

أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ  الْمُلْكُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، اللَّهُمَّ إِنِّـي أَسْأَلُكَ خَـيْرَ هَذَا الْـيَوْمِ ، فَتْحَهُ، وَنَصْرَهُ، وَنُورَهُ وَبَرَكَتَهُ، وَهُدَاهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِيهِ وَشَرِّ مَا بَعْدَهُ

Asbahnaa wa ‘asbahal-mulku lillaahi Rabbil-‘aalameen, Allaahumma ‘innee ‘as’aluka khayra haathal-yawmi , Fathahu wa nasrahu wa noorahu, wa barakatahu, wa hudaahu, wa’a’oothu bika min sharri maafeehi wa sharri maa ba’dahu.

أَصْبَحْنَا عَلَى فِطْرَةِ الْإِسْلَامِ، وَعَلَى كَلِمَةِ الإِخْلَاصِ، وَعَلَى دِينِ نَبِـيِّنَا مُحَمَّدٍ، وَعَاـَى مِلَّـةِ أَبِينَا إِبْـرَاهِيـمَ، حَنِيفاً مُسْلِماً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ

‘Asbahnaa ‘alaa fitratil-‘Islaami wa ‘alaa kalimatil-‘ikhlaasi, wa ‘alaa deeni Nabiyyinaa Muhammadin, wa ‘alaa millati ‘abeenaa ‘Ibraaheema, haneefan Musliman wa maa kaana minal-mushrikeen.

سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ sau ɗari)

Subhaanallaahi wa bihamdihi.

 (hundred times)

لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِي(sauɗari)

Laa ‘ilaaha ‘illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa Huwa ‘alaa kulli shay’in Qadeer.

 (10 times or 100 times )

سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ عَدَدَ خَلْقِهِ، وَرِضَا نَفْسِهِ، وَزِنَةَ عَرْشِهِ وَمِدَادَ كَلِمَاتِهِ ( ×3 )

Subhaanallaahi wa bihamdihi: ‘Adada khalqihi, wa ridhaa nafsihi, wa zinata ‘arshihi wa midaada kalimaatihi.

 (Three times )

للَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْماً نَافِعاً، وَ رِزْقاً طَيِّباً، وَ عَمَلاً مُتَقَبَّلاً

Allaahumma ‘innee ‘as’aluka ‘ilman naafi’an, wa rizqan tayyiban, wa ‘amalan mutaqabbalan.

أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ وَأَتُوبُ إِلَيْهِ ( ×100 )

Salatin Manzon Allah sau 10 ko sau 100.

اللهم صلى على محمد وعلى آل محمد كما صليت على ابراهيم وعلى آل ابراهيم إنك حميد مجيد ،

اللهم بارك على محمد وعلى آل محمد كما باركت على ابراهيم وعلى آل ابراهيم إنك حميد مجيد

Allahumma salli Ala Muhammad wa ala A’li Muhammad kama sallaita Ala Ibrahim wa Ala A’li Ibrahim innaka Hamidun majeed.

Allahumma ba’rik Ala Muhammad wa ala A’li Muhammad kama ba’rakta Ala Ibrahim wa ala A’li Ibrahim innaka Hamidun majeed.

Wannan shine salatin da manzon Allah ya koya wa sahabban shi.

(DAN ALLAH MU DAURE MU RINƘA YI, DOMIN KARIYAR KANMU)

Seda suka gama tas, tukun Abdul ya ƙyale zainab, da kanshi ya temaka mata ta hau gado bayan ya ɗan kakkaɓe mata shi.

Duk inda Abdul ya gifta binshi da ido take, mamaki sosai take,

Dama yana da wannan makamin a hannun shi ya zauna har Aziza taci galaba akan shi?

Can kuma da tayi wani tunanin tace

“ba laifin shi bane”

A gefen gadon ya zauna, ƙafafun ta ya ɗauka aza akan cinyar shi ya hau danna mata su a hankali har bacci ya ɗauke ta.

Seda ya tabbatar da baccin ya ɗauke ta tukun ya tashi, sumbatar goshin ta da kumatun ta yayi sannan ya fice a ɗakin

Direct ƙasa ya sauka, duba ko ina yayi yaga ba wani abun da zeyi, tunda ko’ina a gyare yake fes

Yanke shawarar shiga kitchen yayi, kawai ya fara haɗa musu breakfast.

Ruwan tea ya dafa ya saka a flasks se chips ɗan daidai da ya soya, sannan yayi warming sauran kazar jiya, duk ya shirya su a dining, se wajen takwas da wani abu tukun ya fito kitchen ɗin, ya haura saman

ya shiga da niyar sake wanka, amma kawai ya ɓige da kwanciya, aikuwa nan da nan bacci yayi awon gaba da shi.

Wajajen ƙarfe goma zainab ta farka, ji tayi cikin ta na ƙwaƙula, a daddafe ta sake gasa jikin ta, sosai taji daɗin hakan

Bayan ta gama ƴan shafe-shafen da zatayi ta ɗakko jar a atamfa a cikin kayan ta, ta saka, sosai ɗinkin ya zauna a jikin ta sosai

Zainabu gwana ce wajen ɗauri dama, haka ta murza ɗaurin nan ya zauna ɗas a kanta, sannan ta sake ɗaukan turaren ta na element ta feshe jikin ta da shi.

Duk da yunwar data ke ji hakan be hanata gyara gadon ta ba, tas ta liliye shi, ta kunna turaren wuta sannan ta fito ɗakin

Tana buɗe ƙofa shima yana buɗe tashi ƙofar

A tare suka ɗaga ma juna gira, kuma suka kwashe da dariya

Abdul ne ya riga ta ƙarasowa inda take, seda yayi huging ta sannan ya sumbaci goshin ta haɗe da faɗin

“Kinyi kyau sosai, Allah yayi miki albarka”

Murmushi tayi, tace “kaima kayi kyau”

Da kanshi ya ja hannun ta suka sauka, ita dake tunanin shiga kitchen taga ya jata zuwa wajen dinnig 

Kallon shi tayi, kafin tace komi, ya riga ta da

“Da kaina na dafa, a dena min kallon tuhuma”

Murmushi tayi tana zama akan kujerar da ya ja mata, a yangance tace

“kaga laifi na?”

Da saurin shi kuwa yace “sam, ai amarya bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida”

A tare suka zauna sukayi breakfast, zainab nata zolayar shi wai “zasu buɗe gidan abinci”

A haka suna tsokanar juna har suka ga ci, 

Hana ta ɗaukan komi yayi, seda ya kaita kan kujera ya kunna mata TV, sannan yaje ya kwashe kwanukan da kan shi ya kai kitchen ya dawo suka zauna

Sabon babin soyayya me wahalar ɓacewa a rai suka ɗora.

Haka rayuwar su taci gaba da tafiya cike da so da ƙaunar juna, basu taɓa bari suyi dogon fushi da junan su

A haka Abdul ya koma bakin aikin shi cikin kulawar zainab da soyayyar ta me tsayawa a rai.

BAYAN SHEKARA UKU DA RABI

Abdul ne riƙe da ganyen darbejiya a hannun shi, fuskar nan ta shi kamar yayi kuka, yace

“Dan girman Allah IYA ki bar min mata ta huta, daga dawowa daga asibiti  bata ko huta ba zaki fara lafta mata wannan abun da 

Da sauri IYA ta katse shi tana waftar ganyen a hannun shi, tace

“Ba ruwa na da kai likita ne, mu da akai mana ai da bamu kawo wannan lokacin ba” Ta juya ta shige ɗakin

Bin bayanta Abdul yayi ya shiga ɗakin da zainab ke ɗauke da babyn ta tana bata nono

IYA bata tsaya anan ba, direct toilet ta shige ta aje ganyen

Signal zainab tayi mishi da ido ta yafito shi

Murya ƙasa-ƙasa tace

“Rabu da ita, na sirka ruwan ai”

Dariya sukai suka sha hannu

Da ƙyar ta tashi, ta miƙa mishi ƴar jaririyar me kama da ita saka ta shiga toilet ɗin inda IYA ke tsaye tana jiran ta.

Yarda ƴan’uwa da abokan arziki ke tururuwar zuwa barka yasa Abdul barin gidan ba dan ya gaji da kallon kyautar da Allah yayi mishi ba

Se bayan magariba tukun sahun mutane ya ɗauke, lokacin Abdul ya dawo

A nan palon zainab ta shirya mishi abinci, IYA na zaune tana ta lazimi, zainab kuma na gefe ɗauke da ƴarta a hannu

Seda Abdul ya gama cin abincin shi sannan yayi joining su a palon

karɓar ɗiyar shi yayi ya kalli zainab da se wani sheƙin jego take, yace

“wani suna kike so a saka mata

IYA na jin su bata ce komi

Kallon shi zainab tayi tace

“me ze hana muyi ma AZIZA takwara”

Da ƙarfi IYA ta buga salati tana tafa hannayen ta, tace

“la’ila hailllallahu ni jikar Dije yau naga lukutar masifa da idanu na, zainabu na anya baki taɓu ba wajen naƙudar nan kuwa”

Me Abdul zeyi banda dariya, haukacewa suka yi shi da zainab sukai ta ma IYA dariya

IYA kam bilhaƙƙi da gaskiya faɗi take

“wallahi tafiya zanyi, ba zan zauna nayi jegon takwarar aljana ba, nifa na jima da faɗin kin rikiɗe amma se ace min ba haka ba”

Tsabar dariya yasa suka kasa magana

Da ƙyar Abdul ya tsaida dariyar shi yace

“Shaƙiyancin ta ne kawai fa IYA”

Da ƙyar suka samu IYA ta zauna, 

Seda suka nutsu tukun zainab ta kalli IYA tace

“Ina ƙaunar ki IYA ta, ai na riga da na zaɓi suna, sunan Ammah nace a saka min tun kafin na haihu ma”

Shiru Abdul yayi yana ƙara jin so da ƙaunar zainab a cikin ranshi, 

Har ga Allah sunan Ammah yake so ya saka, daman yana so ya bata dama ne a matsayin ta na uwa, gashi kuma ra’ayin su yazo ɗaya.

Ranƙwashi IYA ta kai ma zainab, Allah ya temake ta Abdul ya tare mata, tace

“Ja’ira, Allah yasa ki gane kin girma tunda har kin aje irin ki”

Sosai suka kwashi dariya a daren nan

A daren Abdul yayi ma ƴarshi huɗuba da suna “MURJANATU” 

Zainab tace da “AMMAH” zata kira ta.

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/12/kishi-da-aljan-chapter-11-complete.html

ALHAMDULILLAH!✍🏿

NAGODE MA UBANGIJI DA YA NUNA MIN FARKO DA KUMA ƘARSHEN LITTAFIN NAN, DAIDAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADA, KUSKUREN CIKI KUMA ALLAH YA YAFE MIN.

GODIYA TA MUSAMMAN GA

MIJI NA ABIN ALFAHARI NA, INA SON KA,DA ALJANA👹

BAMA KAMAR ƳAN GROUP ƊINA NA WHATSAPP DA NA FACCEBOOK, INA ƘAUNAR KU❤️

SE MUN HAƊU A NEXT BOOK ƊINA ME SUNA “MAKIRCI” SALON SHI NA DABAN NE, KAR KU BARI A BAKU LABARI

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.

08145225540.

 ALKAIRIN ALLAH YACI GABA DA BIBIYAR KA A DUK INDA KAKE❤️

FATAN ALKAIRI GA MAHAIFIYA TA “MURJANATU(AUNTY) INA ƘAUNAR KI, ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIA DA NISAN KWANA ME ALBARKA❤️

SANNAN INA MIƘO LUKUTAYEN GAISUWA NA BAN GIRMA GAREKU MASU BIBIYAR LITTAFIN KISHI 

Back to top button