Harijin Sarki Page 5 Romantic Hausa Novel
Cik tunanin Samha ya tsaya Zuciyarta ta buga da ƙarfi ta ƙame ƙam a inda take jiyo yanda ihun yake ƙaruwa a wannan parlour matar tana wani irin kuka tana roƙon a barta ta gaji ƙarfinta ya ƙare amma babu alamun an barta ɗin tun Muryarta na fita Saida ta daina furuci ta koma wani gunji da shassheƙa me sanya zuciya karaya, guri Yadam ya nuna mata yace ta zauna, ta zauna a ɗan tsorace tana kallon duk wata kusurwa ta parlourn Yadam ya danna wata na’ura can sai ga wasu mutane nan ɗauke da kayan ciye ciye suka sanya bisa table ɗin daya kawo kansa gaban Samha da Yadam, so take ta ɗauki wani abun ta sanya a cikinta amma tunanin halin da wannan matar me kuka take ciki da tunano irin wacce azaba ce tasa take furucin ta gama rayuwa a wannan Daula, shin me akeyi mata? Bata kai ga samun amsa ba wasu ƙartan mata suka shigo parlourn rirriƙe da wata mace tana kuka tana ihu harda barin wasiyyar idan ta mutu a kaita Casablanca a binneta a kusa da kabarin mahaifinta domin shine ya jefata a wannan masifa. Kan Samha ƙara kullewa yayi musamman lokacin da aka shiga da wannan mata tana kuka tana ihu waɗannan mata majiya ƙarfi suka ɗauko wannan me ihun jini yana zuba a jikinta suka wuce da ita, ta ƙarshen da alama ta nuna itace shugabar su ta tsaya tace “Likita Samha Sultan yace kiyi treatment Lalla Jalila……”Wata muguwar kartawa cikinta yayi ta dafeshi da sauri ta kalli Yadam, shima Kallonta yayi da fuska mara annuri yace “Yana cikin ayyukanki” tsam ta miƙe jikinta babu wani duk nau’i na ƙwari ta bi bayansu zuwa wani ɗaki da taga sun shiga da wannan mata, Saida ta kawar dakai ganin yanda suka bajeta a saman wani gado jikinta babu komai sai wani towel da suka lulluɓawa al’aurarta, cike da rauni.Samha tace “Bansan ta ina zan fara ba kuyimin bayani bansan damuwarta ba” sauran Hadiman duk ficewa sukayi ya rage daga Samha sai wacce tayi magana a parlourn, matar tace “Sunana Basrah Nice babbar hadimar Sultan Rashid mai kula da shige da ficen matansa, wannan itace Lalla Jalila Amaryar Mai martaba ce watan ta biyu a wannan masarauta, wannan ɗinkin da zakiyi mata shine ɗinki na uku kenan da za’ayi mata, ta kasance mara juriya gata da gautsi duk sanda Sultan ya kusanceta sai ta yage” cikin tashin hankali Samha tace “Saikace tsumma tayita yagewa ana ɗinketa wanne irin zalumci ne wannan, idan ta gaza a haƙura da ita mana ta koma gidan iyayenta” tunda ta fara maganar Hadima Basrah ta zuba mata idanu tana mata murmushin rashin sani yafi dare duhu irin na da Kinsan meye a gabanki da baki furucin nan ba.Fara duba Matar tayi tana rintse idanu jikinta na rawa ta fara duba kayan aiki abin mamaki ɓangare kamar asibiti haka yake komai na amfani akwai, haka tana hawaye da taimakon Basrah ta ɗinke Lalla Jalila ta zauna tayi zugum Zuciyarta ta cika da duhu wannan rashin imanin yayi yawa koda batasan Sultan ba taji ta cika da tsananin tsanarsa, wannan wacce irin rayuwa ce ta kama karya da rashin tausayin na ƙasansa, har yanzu tana jiyo ihu ta ɗago ta kalli Basrah tace “Nifa na kasa gane komai waccan da take ihu fah ita meye tata damuwar?” Ɗagowa Basrah tayi tayi murmushi tace “Lalla Najjisa kenan ita ce babbar matar Sultan Jiya ma a nan ta ƙarasa kwana saboda doguwar sumar da tayi a lokacin da Sultan ke tarawa da ita……” Zaro ido Samha tayi tare da dafe ƙirji tace “Na shiga uku suma kuma? Wai wahala ce da sex har haka dama?” Da mugun mamaki Basrah take Kallonta tace “Ke bakisan yanda sex yake ba?” Cikin tausayin kai tace “Ni ban taɓa yin aure ba” jinjina kai Basrah tayi tace “Kuma ko Saurayin da zaki bawa dama ya kaiki wannan duniyar mai daɗi baki taɓa yi ba? Likita Samha Jima’i nada matuƙar daɗi da haskaka zuciya musamman idan kikayishi da wanda kikeso kuma wanda ya iya kama sitiyarin abin, saidai su a wannan gida matan Sultan basu taɓa sanin daɗin jima’i ba saboda wata jarabta da Allah yayi musu da HARIJIN SARKI mafi ƙaranci a rana Sultan yana kwanciya da mace biyar a tsayin wayewar gari kuma kowacce yana mata cin sama da 2 hours idan kuwa abin ya juyo yakan ƙara ma akan biyar ɗin da biyu ko uku kuma kowacce sai ta fita a hayyacinta yake ƙyaleta, ke a takaice dai a yanda naji gurin Kasirsh Sultan yakan ɗauki wata guda ne baiyi release ba kuma Joystick ɗinsa bata kwanta ba”Ji sukayi an Turo ɗakin da ƙarfi suka ɗago a tare, zubar da Lalla Najjisa akayi a wani gadon itama Samha ta miƙe cike da tashin hankali itanma taimakon gaggawa take buƙata, wata likita ce tazo ta cajeta tsaf ta sauke ajiyar zuciya tace wannan karon bata ƙaru ba” cikin rashin sanin furucin ya kufce mata tace “Au su kullum a yage suke kenan abin ma ya zama jiki a garesu?” Kafin akai ga bata amsa wata Hadima ta shigo tace “Wai likita Samha taje inji Sultan” gaban Samha ne ya faɗi ta kalli Basrah, tayi ƙas da kanta cikin rashin abinyi ta ɗauki kayan aikinta ta fice daga ɗakin takawa takeyi ba tare da yasan inda take saka ƙafarta ba har ta isa parlourn da suka zauna ɗazun, har yanzu Yadam yana gurin kamar gunki. Kallonta yayi tare da nuna mata wata ƙofa ta tsaya cik tana kallon ƙofar tana Kallonsa ya jinjina mata kai yace “Sultan Baison jira yana buƙatar taimakon gaggawa kije kiganshi” wani yawu ta haɗiye muƙut ta ƙara jan siraran ƙafafunta ta danna bottle na ƙofar ta buɗe, Innanillahi nan Samha ta manta da tashin hankalin baya ta shagala da kallon wannan parlour a ranta tana tambayar kanta wai parlour nawa ne a wannan sashi ne? Batasan da mutum a gurin ba Saida taji anyi gyaran murya tayi wani firgigit ta dawo hayyacinta tare da sauke idanunta kan mutumin dake zaune da mugun sauri ta haɗe da jikin bango tanajin wani fitsari na neman ƙwace mata.Ƙasa tayi da idanunta tanajin yanda Zuciyarta ke harbawa fiye da aikinta, a fili tace “wannan wacce irin duniyar masifa na shigo Ni Samha ƙato a tuɓe…..” Maganar ce ta maƙale lokacin da taji hucin mutum a kusa da ita, ta ɗauke numfashinta cak jin ya sanya hannu ya ɗago fuskarta yace “Barka da zuwa Daulata Likita Samha El-Fahri.”Hatta iskar da take saƙa saida ta tsaya mata cak,Sarki Rashid Ibn Fayyad Al-Zirkan.Yana tsaye a cikin duhun hasken fitila, rigar sarauta mai baki da zinariya a jikinsa buɗaɗɗiya da bata rufe sirrin ƙirjinsa da ƙirarsa ta sadaukan gaske ba, idanunsa suna kallonta kai tsaye kamar suna binciken zuciyarta, Ta ji sanyi ya ratsata Ba tsoro ba ne, wani irin nauyi ne da ta kasa fassarawa ,Ta sunkuyar da kai cikin ladabi, tace cikin murya mai rauni“Ya mai girma, ni ce likitar da aka ɗauko daga Fes. An ce ina da alhakin kula da lafiyar Mai Martaba…”Tsayawa yayi kusa da ita, har ta ji ƙamshin turarensa mai matuƙar daɗi Ya ɗan murmusa amma idonsa bai nuna murmushi ba yace “Kin san dalilin da yasa aka kiraki?” Girgiza kai tayi tace “A’a, Mai Martaba. Na zo ne da niyyar yin aikin da aka ɗora min kawai” Ya yi shiru tare da maida idanunsa ga kallon hasken glub ɗin ɗakin idanunsa suka yi wata irin walƙiya kamar wuta, Sannan ya ce cikin sanyi “To, likita… ki shirya don yin maganin ciwon da babu likitan ya taɓa ganin irinsa.”Ta kalle shi a hankali, tana ganin wani yanayi mai zurfi a cikin idonsa haɗin azaba, iko, da sirri.A cikin zuciyarta, wata murya ta ce:“Wannan ba kawai majinyaci bane… akwai wani abu da ya fi jiki.”Amma ta shareTa lumshe idonta, ta ce cikin nutsuwa“Insha Allah, zan yi iyakar ƙoƙarina.”Ya ɗan matsa kusa sosai, har muryarsa ta zama kamar sirri a kunnenta ya ɗora hannunsa a kuncinta ya zagaya zuwa kan laɓɓanta yace “Samha… a nan, iyakar ƙoƙari na iya zama haɗari”Sai ya wuce cikin duhu yabar ƙamshin turare da nauyin tunani a bayansa Ta tsaya, tana kallon ƙofar da ya ɓace ta ciki, tana jin zuciyarta tana bugawa kamar tambaya“Me yasa nake jin kamar na san wannan mutumin tun kafin na same shi?”……


