Gargadar So Chapter 43 By M Shakur
Wuraren 5 Hawwa ke bude idanunta tana kallon saman dakin komi daya faru nadawo mata, hawaye masu dumi ne sakko daga idanunta, ahankali tafara mosti da idanun dake mata nauyi sosai tana juyowa kanta yayi sauki kaman ba nata ba yanzu tana iya juyawa yadena banging, Ammi ta gani a tsakar dakin kan dadduma ga charbi a hannunta tanaja maida idanunta tayi tarufe she can’t look at Ammi, knocking kofan akayi da sauri Ammi ta tashi tace “shigo” tadaga dadduma tana linkewa daidai Dr yashigo tareda Nurses yazo gaban gadon yana kallon Hawwa data lumshe idanu Ammi tace “Dr har yanzu bata tashi ba nadamu abinci fa”? Murmushi yama Ammi yana duba BP Hawwa dayasan ta tashi yace “maganin hawan jini nasa bacci amman karki damu zata tashi saitai wanka” ijiyan zuciya ya sauke yace “Alhamdulillah BP yasoma sauka” anatse yace “Miss Hawwa open your eyes” ahankali Hawwa tashiga bude idanunta tadan kalli Doctor kadan saikuma ta sauke idanun kasa kawai nauyin kowa takeji, Dr yace “ya ciwon kan? Akwai wani abu dayake miki ciwo yanzu?” Girgizamai kai tayi murya kasa kasa dabaya fita da kyau tace “no” Dr yace “okay that’s great” yakalli Ammi yace “Mama help her to change tadan gyara za’azo a gyara gadon akawo mata abinci kuma, an mata booking massage Yallabai yace bayanta na ciwo, masseuse zasu mata massage din, zatasa hospital clothes bama barin patient namu nasa kayan gida” gyadamai kai Ammi tayi tace “to” Nurses suka ciremata drip din suka fice Ammi taje gaban gadon tana kallon Hawwa da idanunta ke kasa ta kauda kanta gefe dasauri jin Ammi tazo wajen, Ammi dake kallonta tace “Jidda na ya jikin? Babu abinda ke miki ciwo kuma”? Gyadama Ammi kai tayi ahankali batare data kalleta ba tace “eh” cikeda so Ammi tace “tashi muje to kiyi wanka ki chanza” Ammi takai hannunta tadagota tasowa tayi da karfin hali ta sauka daga gadon Ammi tariketa har bayi tabata gadon Ammi tahada mata ruwan wanka, tadawo dakin tabude jakan kaya da Baba da Ramla suka kawo musu jiya taciro brush da zani, saikuma pad datasa Ramla tasa ajakan tadauki daya da wando takoma bayin ta ijiye mata tasake fitowa ta yaye zanin gadon daidai nurse tashigo da wani ta shimfida mata da hospital gown mai kyau na yan gayu sannan tafice saikuma masu abinci suka kawo mata fruits da oat, dasu chips da egg da salad da sausage ga bread saikuma maganin dazata sha a gefe cikin wani glass covered container Ammi sai kallo take komi na masu kudi daban ne.Kusan 15min tayi abayin Ammi takoma wajen bayin tace “kin gama Hawwa”? Ahankali tace “eh” Ammi tabude tashiga tana kallon yanda taki yadda su hada idanu, maidata gadon tayi tana kallon yanda white and blue flowers hospital gown din yamata kyau ta zaunar da ita tana daga tray na abincin tana ijiye mata tace “yi maza ci kafin sudawo” yatsine fuska tayi batada apatite ko kadan kauda kanta tayi asanyaye tace “Ammi bazan iya ci ba” sosai Ammi ke kallonta saikuma ta matso ta zauna abakin gadon anatse tace “Hawwa” asanyaye Hawwa tace “Naam” batare data kalli Ammi ba, lumshe idanu Ammi tayi tabudesu tace “look at me Hawwa” girgizama Ammi kai tayi dasauri lips nata suka shiga rawa tace “Ammi bazan iya ba” wani iri Ammi taji, hannunta tasa tadauke tray na abincin ta ijiye akan table na dakin sannan ta matso dab da Hawwa ahankali tace “Hawwa look at me” daidai lokacin hawaye yasauko daga idanunta tace “Ammi bazan iya kallonki ba, Ammi banmasan ta yaya zan kalli keda Baba ba” sai takai hannayenta biyu tadaura kan fuskanta tafashe da kuka mai tsuma zuciya she’s hurt, Ni’ima hurt her beyond duk yanda zatayi bayanin tace “wlh, wlh, wlh Ammi ni ba yar iska bace bantaba amfani da kaina ba, Ammi that’s not me, bazan tabama wani fyade ba” hawaye Ammi tashare daga fuskanta Hawwa tabata tausayi sannan takai hannunta takama hannun Hawwa tasauke takai hannunta tajuyo da habanta fuskan Hawwa yajuyo Ammi tanuna kanta tace “Hawwa ni mahaifiyarki ce kina gani aduniyan nan akwai wanda yasan yarsa sama da mahaifiyar ta? I know you Hawwa, nasan tarbiyan da muka miki, I know who you are? Dagani har Babanki babu wanda yama dauki maganar da Ni’ima tayi da mahimmanci, Hawwa yau koda haka kike ko kinfi hakama muna sonki and we will always love you, Hawwa ke y’ata ce inasonki aduk yanda kike aduk yanda kika zama, kinji yarinyana, ki manta da duk wani abu data fada, come here” dasauri ta rungume Ammi tana sake samin wani karfin guiwa iyaye daban suke idan suka nuna they’re with you and they stand with you kafi jinka very strong kankame Ammi tayi tana kuka harwani rera kukan take kaman marainiya tace “Ammi menama Ni’ima? Why all this hate? Sabida ni Ni’ima tazageku ta ma Baba rashin kunya, Ni’ima tamin gori tama Baba gori, Ammi me namata eh”? Tawani ja numfashi tana rera kuka tace “bazan taba auren mijinta ba, Ammi sabida bansami miji ba banda aure shikenan na zama dustbin? Kowa yadauko shiritanshi akaina? Ammi inaso nai aure nahuta maybe only then Ni’ima zata yarda dani I’m not after Baban Yaseer, Ammi babu abinda kemin dadi“ cikin dan fushi kadan Ammi tace “zaki kashe kanki akan Ni’ima ne? Hawwa that girl obviously doesn’t deserve you, abu dayane bazanyi supporting naki ba shine kisamakanki damuwan Ni’ima, Hawwa don’t kill yourself akanta, Ni’ima don’t deserve you Allah use this chance ya nunamiki waye ita, so is time kifita daga rayuwansu both ita da mijinta and move on, toxic people ne dukansu biyun, kiji sauki kidena tunanin komi, I didn’t train you to be weak or to be crying for any girl, Hawwa you are a strong girl wacce guguwan iskan mountain baiyi putting baki down ba saida kikai destination naki, shit happens in this life, friends comes and goes, relationship ends that doesn’t mean bazamu cigaba da rayuwa ba, close chapter Ni’ima and move on learn from your mistakes, no more room for wacce wishes you death, your secrets should be for your stomach idan ba ni ko mahaifin ki ba babu wanda ya isa yaji sirrin ki, move on and be a better person kinji, kihakura da Ni’ima, tace taja miki layi kema kijamata layin kinjini” gyadama Ammi kai tayi ahankali tana kuka har lokacin, Ammi ta matso ta manna mata kiss a goshi sannan tadauki tray na abinci cikin masifa tace “nayi tir da dabi’un Ni’ima ayahya taje zata gani indai duniya ne fadi gareta, Allah zai saka miki” tashiga bata oats tana sha, masu massage sukazo akama bayanta massage dataji kaman an mikar da ita an ciremata duk wani bending da ciwon jiki, no wonder massage keda tsada ashe haka akeji, duk wani tsamin jiki saida suka fitar bacci yayi awon gaba da ita haka nurse’s sukazo suka kara mata fixing drip din tana bacci mai nauyi.Tun asuba Allah sanya alkhairi akema Baba, kafinma yasamu yabar masallacin was around 8:20 sai farin ciki yake nanma wasu suka sake tsareshi anan waje anamai Allah sanya alheri wani kara son Baba ma akayi a unguwan Baba tsabagen murmushi kumatunsa har ciwo yake sai wajajen 9 yawuce gidansa da sallama ya shiga cikin gidan Maman Ni’ima daya gani a tsakar gidan kan kujera yasa yaci tura ya tsaya, Mama ta washe baki tace “ahhh Malam ka shigo barkanmu da safiya ai tundazu nazo nake jiranka” dan jim Baba yayi saikuma yakaraso ciki yace “Malama Maimuna ya kwana biyu ya yara ince dai kinaji daga garesu”? Murmushi Mama tayi tace “kowa na nan lpy, satin daya gabata ma Usaina ta haihu an samu Abdulwahabu” anatse Baba yace “Masha Allah, Allah ya raya” ya kwalama Ramla kira data fito daga dakin Hawwa tace “gani Baba” Mama yanuna mata yace “kaita ciki bari na zaga nazo” Mama ta mike tabi Ramla ciki tanabin dakin Hawwa dakenan tsaftsaf da kallo shikuma Baba yawuce makewaya.Fitowa yayi ko kallon Umma dake kitchen baiyiba itama haka yawuce dakin Hawwa inda Mama take, kujera yaja yazauna yakalli Ramla yace “jeki hadamana kari Ramla” gyadamai kai tayi shikuma yakalli Mama kai tsaye yace “ya akayi Maimuna wannan dakike nemana”murmushi sosai tayi tace “na farko dai Malam naji labarin dakebin gari sai shigowa makota suke sunamin Allah sanya alheri diyata Hawwa an daura aurefa shine nake kiran Ni’ima dan abankinta yakamata naji wannan labari amman saiba abakinta nakeji ba, nan fa Ni’ima tafara koro zance aiko saida namata tatas dan har mari na yanka mata, akan namiji zatai kalan haukan nan shine fa na zuro hijabi da sassafen nan nazo nabaka hakurin abinda Ni’ima tayi kuyafe mata Baba bakaga yanda ta damuba dan Allah ayakuri kaga tsakanin harshe da hakori ma ana samun sabani balle kawaye” Baba yace “wannan haka yake” Mama tace “Baba toh dan Allah kuyakuri mune iyayensu karmu zuba musu ido su lalata mana zumunta mu daidaitasu Baba, Ni’ima tayi nadama kwarai kawai shakkan ku take dakuma tana tsoro kar Hawwa taki yafemata amman dazaran kasa baki kowa yasan Hawwa zata hakura Malam”Mama tai shiru tana jiran amsan Baba, dan murmushi Baba yayi yace “Masha Allah naji duk bayanin dakikayi Maimuna” yasakeyin shiru yace “dan yafiya wlh na yafema Ni’ima, ni uba ne akan mene zan riketa azuciya bayan nima yarana zasu iya kuskure da shirme kaman nata, idan zancen yafiya ne nayafema Ni’ima har ranan gobe kiyama” dasauri Mama tace “Alhamdulillah,Alhamdulilah Alhamdulillah, shikenan yaranmu sun shirya” ta washe baki, Baba yayi shiru saikuma yakalli Mama yace “Maimuna dubeni nan, ni ubane kaman yanda kike mahaifiya, hakkine akanmu idan mukaga abinda zai cutar da yaranmu mu kauda abubuwan daga hanya” Baba yayi shiru yana lumshe idanu yana tuna yanda Ni’ima take ikirarin kashe Hawwa yace “idan Hawwa zata yafema Ni’ima bazan taba hanata ba amman idan Hawwa zata dawo da Ni’ima rayuwanta saina hanata!”Faduwa gaban Mama yayi dasauri takalli Baba bakinta tafara rawa, Baba yadan kada kafa yace “wato Maimuna jiya na karanci abubuwa da dama akan idanun Ni’ima, tundaga kissan data dinga ikirari zatama Hawwa, da fatan mutuwa data dinga mata, da yanda dudda mijin natane mai laifi ina shiyabi Hawwa? Shi yake sonta Hawwa bata sonshi amman batai kan mijinta ba kan Hawwa tayi, ga diyata agadon asibiti rai hannun Allah Ni’ima bataji tausayin ta ba karasata takeso tayi” yayi jimm yace “Maimuna ansan mata da kishi amman naga ko kishiyan ka ce take gadon asibiti zakadan tausaya karage wani abun” Dasauri Mama tace “Malam kishi kala kala ne, akwai masu zafin kishi kafahimta” adan zafafe Baba yace “Maimuna fahimtan danayi yasa nike miki bayanin nan, koda yaran nan sun shirya madaman Aliyu na kaunar Hawwa Ni’ima bazata taba kaunar Hawwa ba duk karyace! Ni’ima tariga ta tsani Hawwa! Naga kiyayya a idanunta kibar maganan nan kawai!”.

