Uncategorized

Abban Sojoji Page 51 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

_💋Boss Bature💋_

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

*💋Boss Bature💋*

Bayan ta kammala gyara mashi bedroom lokacin da ta fito harya kammala yin breakfast É—in ya fice,tsayawa tayi ta gyara masa palourn ko’ina tsaf sannan ta É—auki tray É—in kayan abincin ta fita dasu,

Tunkan ta Æ™arasa saukowa down taji muryar azmee na kiran sunnanta,don haka cikin sauri ta Æ™arasa sauka,babu kowa a main palour É—in kitchen ta wuce kaitsaye,anan ta samu Azmee tana shirya drinks acikin medium tray, 

   “Gani Aunty Azmee,naji kamar kina kiran sunana,” 

  É—agowa azmee tayi tare da kallonta tace”eh,dama Abbansu ne zaki kaima wannan,yana a garden tare da abokin shi,

Amsa mata tayi da toh sannan ta Æ™arasa shiga ciki ta ajiye tray É—in hannunta sannan ta koma wurin Azmee ta kar6i try É—in data kammala haÉ—a masu drinks É—in,a hannu ta ruk’o su tare da kama hanya tabar kitchen É—in,

     Lokacin da ta fito harabar gidan,tsayawa ta É—anyi tana kallon su junaid dake buga ball tare da wasu daga cikin soldiers din gidan,kamar dae kullum sai faman wahalar dashi suke yi,ko ball É—in sunÆ™i bari ya É—auka,girgiza kai sehrish tayi tare da wuce wa ta kama hanyar zuwa garden É—in,

  A natse take tafiya a cikin Æ™ayataccen garden din tun kafin ta Æ™arasa cikin shi,ta hangi Abban nasu tare da wani dattijon mutum,suna zaune asaman darduma suna Tattaunawa,a gabansu akwai tray É—in yankakkun kayan marmari da azmee ta fara kai masu,

   Jin alamun tafiyar mutum yasa su É—agowa gaba dayansu suna kallonta,yarda wannan dattijon ya kafe ta É—an kwarkwarun idanunshi yasa nan take sehrish taji gabanta ya faÉ—i,

…Æ™arasawa tayi tare da ajiye masu tray din,sannan ta É—an tsugunna daga gefe guda tana gaishe su,”

Murmushi Abbansu ya saki tare da cewa”lfy lou my own daughter,wato sai da Azmee ta taso ki ko?sai da nace mata ta sanya junaid ya kawo mana,”

  Murmushi sehrish tayi tana É—an sunnar kai,

  Juyawa tsohon yayi yana kallon Abban nasu fuskarshi cike da mamaki yace”ince wannan ko Æ´ar wurin Azeema ce?

  girgiza kai abban nasu yayi tare da cewa”kaji ka da wata magana,azeema ae bata ta6a haihuwa ba,wannan Æ´a ce daga Allah nasamu,”

  Jinjina kai tsohon yayi kafin yace”yanzu husssein kana da zankaÉ—eÉ—iyar mace tsaleliyar budurwa acikin gidan nan,tana yawo kuma ka zuba ido kana kallonta!?

  zuru sehrish tayi tana kallon shi,

Fuska É—auke da mamaki Abba yace”kamarya kenan,” yayi maganar tare da yi ma sehrish alamar ta tashi ta tafi,

..miƙewa tayi cikin sauri tabar wurin,

Cigaba da magana tsohon yayi”Ina nufin zaman me take yi haryanzu baka samu daya daga cikin Æ´a’Æ´anka ba ka aura mashi ita,” 

  Murmushi Abban nasu yayi yana kallon shi batare da yace komai ba,

“tuntuni nake baka shawarar ka tattara yaran nan na wurinka ka aurar dasu amma kaÆ™i jin shawarata,ni narasa gane me yake damunka wlh,duk cikin abokanan mu da mukayi aiki dasu babu wanda yanzu bai ajiye jikoki ba,wani ma cikin jikokin sunyi aure,duk acikin mu babu wanda ya tara Æ´a’Æ´a maza kamarka,haba hussein ya kamata kayiwa kanka adalci Æ´a’Æ´a kusan goma sha wani abu ka tasa su gaba kana kallo,ni bansani ba ko shakkarsu kake ji ne shiyasa kaÆ™i aurar da su,” Æ™arasa maganar dattijon yayi yana faman É—aure fuska,da alama abun ba Æ™aramin ciwo yake mashi ba,

  Tunda ya soma maganar tashi Abban nasu bai katse shi ba sai da yakai aya sannan yace”Nima kaina bani da burin da ya wuce wannan,amma narasa yarda zanyi dasu ne,ba wai Æ™arfina suka fi bane,bana so na takura masu ne ko nace zanyi masu auran dole,nafison in Allah yasa sun samu wadda ta dace da rayuwarsu suka ji suna so sai in aura masu…….’

  bai bari abban nasu Yakai Æ™arshen maganar tashi ba yace”kaji matsalar!bakomai bane yajawo hakan ba face shegen son da kake ma yaran nan!shi ya hana kayi masu aure,kuma inaso ka sani wannan ba soyayya bace!tun da har zaka iya hana farin cikinka don ka faranta masu a matsayinsu na Æ´a’Æ´an daka haifa!har yaushe ne zaka zauna kana jiran su kawo maka matayen da suke so ka aura masu?kai da kanka fa kace ko soyayya ma basa yi!shin zaka zauna kana jiransu ne batare da ka cika burinka ba?yaushe kenan?bayan ka tsufa tukuf  ko kuma bayan ka mutu kenan? 

  Shiru Abba yayi yana sauraron shi,

“Ni dai ina baka shawara kaima ka jaraba yin irin nawa,Yaran nan fa kai kake da iko dasu kaine ubansu duk duniya basu da kamarka,kuma na lura yaran nan ba Æ™aramin sonka suke yi ba,sau da kafa haka naga suna binka suna yi maka biyayya,”

  Sai lokacin Abban nasu yace”naji kace,na jaraba yin irin naka,amma baka yi mun bayani ba,”

  Murmushi tafeeda yayi tare kai hannu zai É—auki lemu ya zuba acikin cup,cikin sauri Abba ya riga shi É—aukar roban lemun ya buÉ—eta tare da tsiyaya mashi acikin cup sannan ya mika mashi,

  Hannu yasa ya kar6a tare da kaiwa bakinshi yana sha,bayan ya gama kur6e shi duka ya mayar da kofin ya ajiye,sannan ya mayar da idonshi kan Abban nasu yace”shekara bakwai da suka wuce,kasan nima yaran nawa kamar na wajenka suke,banbancin kawai ni na wurina basa jin magana sun fiye taurin kai,kullum ina yi masu maganar aure babu wanda ke kulani acikinsu tunda suka dawo daga karatu kowa aiki yasa agaba,basu da lokacin kula mata balle suyi tunanin yin aure,wannan abun ba Æ™aramin Æ™ona mun rai yake yi ba,raina yana 6aci sosai,don haka nace badai nine ubanku ba,zanyi maku auran inga ta tsiya,a lokacin munje masallacin juma’a daya ke atare muke haduwa muje,bayan an kammala sallah nace akwai É—aurin auren Æ´a’Æ´ana da za’ayi amma basu da mata,duk wanda yasan yana da Æ´a mace da ta isa yin aure kuma ya shirya yi mata auren,yayi magana ga Æ´a’Æ´ana nan ashirye nake dana aurar dasu,hankalinsu ya tashi haikam jin abunda nake Æ™oÆ™arin yi masu,ina baka labari mutumina,ba mu bar masallacin nan ba saida aka shafa fatihar kowanne daga cikinsu,yanzu labarin da nake baka tun suna nuna 6acin ransu yanzu takai ga tsakanina dasu godiya ce,nace masu da kuka ce baku so, ga abun arziÆ™inan hada yaransu gwanin burgewa,”

  dariya sosai abba yayi aranshi kuwa yana ayyana abunda zai faru idan har ya kuskura ya jaraba irin na abokin shi tafeeda,tabbas ba Æ™aramin bomb zai haÉ—a ma kanshi ba,ba kowa ma ya fi jin fargabarsa ba irin RAFAYET,saboda wasu abubuwan nashi sak irin na mommynsu ne Alexandra,ita babu wanda ya isa yayi mata abunda ba tayi niyya ba,in kuwa hakan ta faru to fa za’aga tashin hankali,

  gaba É—aya Abba yayi nisa acikin tunanin shi muryar Tafeeda ce ta katse shi da cewa”Naji kayi shiru mutumina na,ni nasan cewa kana jin shakkar Æ´a’Æ´anka ne shiyasa bazaka iya yi masu hakan ba,amma inaso ka sani yanzu lokaci yayi da yakamata ace kayi abunda ya dace a matsayinka na Uba!hussein kayi Æ™oÆ™ari sosai wurin tarbiyyantar da Æ´a’Æ´anka,kowa yana alfahari dasu,duk in da naje naji ana yabon Æ´a’Æ´anka sai inji wani irin farin ciki araina,har ma in dinga cewa ae ya’yan aminina ne,kuma da zarar nace haka sai kaga ana ta respecting É—ina,hussein abu É—aya ya rage yanzu kayi masu shine aure,zasu yi alfahari da hakan sosai,kada kace na takura maka akan maganar ka aurar da Æ´a’Æ´anka,ina yin hakan ne saboda farin cikinka!saboda nasan cewa abun nayi maka ciwo sosai,hakan ne ma yasa kake yawan kirana a waya kana sanar dani damuwar da kake ciki,Hussein har yaushe ne zaka dinga la6ewa aÉ—aki kana matse hawaye akan yaran da ka haifa?

  Jiki asanyaye Abban nasu ya É—ago yana kallon abokin nashi,tabbas abunda tafeeda ya faÉ—a gaskiya ne,sau dayawa idan damuwar tayi mashi yawa yakan farka tsakar dare yayi alwala ya shiga jera nafilfili yana kai kukan shi wurin Allah duk akan rashin son auren Æ´a’Æ´an nashi,abun ba Æ™aramin ciwo yake yi mashi ba,gashi bai da wani buri daya wuce wannan,shi kaÉ—ae ne Last ambition É—in da yake dashi kafin yabar duniya gashi babu alamar cewa burin nashi zai cika nan kusa,

   Sosai Tafeeda ya shiga tunxura abban nasu game da aurar dasu ya kuma Æ™arfafa mashi guiwa sosai har yake jin cewa zai jaraba yin hakan,

  (TabÉ—ijancan)

     

Bayan sehrish tabar garden É—in komawa tayi wurin su junaid ta tsaya daga gefen ragar tana kallon wasan nasu,tun da yaga sehrish yake ta faman Æ™oÆ™arin yaga yaci kwallon amma abun yaci tura,saboda mugunta sojojin suke yi mashi,sai ya watsa da gudu zai tari kwallon sai asamu wani ya taÉ—iyo Æ™afarsa ya faÉ—i Æ™asa yaraf saman grass carpet É—in dake a wurin,tuni ran sehrish yayi mugun 6aci saboda ta lura da yarda suke zaluntar shi,maimakon su tausaya mashi su bar shi yaci ko da sau É—aya ne amma sai wurgi suke yi dashi,. 

Aikuwa suna cikin wannan yanayin sai ga Motarsu Sgr ta shigo cikin gidan,adai dai football field din Amstrong yayi parking É—in motar,sannan ya fito tare da zagayawa ya buÉ—e mashi mota,a hankali ya zura Æ™afarshi tare da fitowa daga cikin motar,tsayawa yayi tare da goya hannayenshi asaman wide chest dinshi yana kallon wasan ball É—in nasu,gaba daya duk basu lura dashi ba,lokaci guda ya gane cewa mugunta suke ma Junaid É—inshi, 

   juyawa yayi ya kalli Amstrong dake tsaye agefenshi,cikin harshen turanci yace mashi”kana ganin abunda nake gani kuwa”?

  murmushi Amstrong yayi kafin yace”Sir,yakamata kaje kaima ayi wasan dakai,suna buÆ™atar lecture,”

   jinjina kai Sgr yayi tare da wuce wa kai tsaye ya shiga cikin filin wasan, 

  lokacin da sukayi arba dashi nan take suka ji gabansu ya faÉ—i rasss,junaid kuwa da gudun gaske ya tunkare shi tare da faÉ—awa jikinshi yana kuka,

  Hakan ba Æ™aramin fusata Sgr yayi ba,hannu yasa tare da É—ago fuskarshi yana kallon hancin shi da jini ke É—iga alamar wurin ya bugu da kwallo,

   cikin sanyin murya Sgr yace”kana so na rama maka”?

  É—aga kai junaid yayi alamar eh,

“Okey ka koma daga waje,kasha kallo kawai,”

   Wani irin farin ciki ne ya rufe junaid cikin sauri ya fuce tare da komawa wurin sehrish dake tsaye,sam bata ji zuwanshi ba saboda idonta na akan Sgr dake acikin filin wasan,

  Hannu yasa tare da É—an bubbuga kafaÉ—arta,a firgice ta juyo tana kallon fuskarshi,

  “Ko tausayina ma ba kiji ba,kina tsaye kina kallon yarda suke ta wahalar dani,maimakon ki shigo ciki ki ramamun,”. 

  dariya sehrish tayi tare da cewa”junaid nifa nasan ciwon kaina,taya zaka shige cikin waÉ—ancan garadan masu fuskar shanu kace wai zaka buga ball dasu,ae sunfi Æ™arfinka,gayanan duk sun wahalar dakai abanza,

   É—aure mata fuska yayi yana murguÉ—a mata baki,

   girgiza kai kawai tayi tana dariya kafin daga bisani suka mayar da hankalinsu kan filin wasan,

    Tashin hankali,Æ™ananun namun dawa sunyi arba da zaki,

Sai faman mazurai suke yi suna kalon shi,kusan su shida ne acikin ragar,in aka haɗa da sgr sun zama su Takwas kenan,gaba ɗaya duk sun sha jinin jikinsu saboda sun san mai zai biyo ba,dama tun alokacin baya idan yazo nigeria da zarar yaji hannunshi nayi mashi ƙaiƙayi,sai ya tara duka acikin ragar suyi Boxing,ba ƙaramin bugu yake yi masu ba,duk yawansu haka zai tarwatsa su,

  Hannu yasa tare da cire rigar jikin shi nan take Æ™irar nan mai tsoratarwa ta bayyana,wurga ma junaid rigar tashi yayi cikin sauri yasa hannu ya cafke ta,

   “Junaid bani na ruÆ™e mashi rigar,”acewar sehrish,

  MiÆ™a mata rigar junaid yayi hankalin shi na a field din,hannu tasa ta kar6i rigar tare da kaita saitin hancinta tana shinshina Æ™amshin turaren jikinta,rungume rigar tayi sosai ajikinta,sannan ta mayar da idanunta akan wasan nasu,

  Tunda suka ga Sgr yakai hannu tare da É—aukar kwallon yana bubbugata Æ™asa tana dawowa cikin tafin hannunshi,yayin da kyawawan idananuwan nan nashi ke binsu É—aya bayan É—aya yana kallonsu,hakan ba Æ™aramin tsoratasu yayi ba,

   Wani daga cikinsu ne yace”Wlh kwara kowa yayi ta kansa da alama watan cin ubanmu ne ya tsaya,”

  Yana Æ™arasa maganar tashi ya nufi hanyar fita daga cikin ragar da gudu zai tsere,sai dae ina kafin ya Æ™arasa fita,Sgr yasa Æ™afarshi tare da buga ball É—in da Æ™arfin gaske kai tsaye ta sauka a tsakiyar goshin shi,wani irin jiri ne ya É—ebe shi sai gashi Æ™asa a baje yana faÉ—in”la’haula wala Æ™uwata illa billah ,’ 

  .gaba É—aya Sehrish da junaid suka shiga 6a66aka mashi dariyar mugunta hada dafe ciki,

   Ganin haka yasa sauran suka yi hanzarin É—aukar ball É—in don ayi wasan dagaske,gaba É—aya suka kacame suna Æ™oÆ™arin ganin sunci nasara akanshi,ba Æ™aramar wahala sukaci a hannun Sgr ba,domin kuwa da mugunta ya dinga buga masu kallon da wasa da wasa sai da yayi masu jina jina a hancinansu,dama ba wasan yakai shi cikin ragar ba,ganin yarda suke nuna Æ™arfi wurin junaid yasa shima ya shiga don ya nuna masu cewa gaba da gabanta fa,

a nan yabarsu baje ƙasa saman grass carpet ɗin sai faman wash wash suke yi,gaba ɗaya sai da ya tabbatar da cewa ya gama raunata ga66an jikinsu sannan ya fito daga cikin ragar,

   da gudu junaid ya Æ™arasa wurin shi tare da rungumo shi ta baya fuskarshi É—auke da dariya yake faÉ—in”My hero man,u did a good job,naji daÉ—i da ka ramamun nasan daga yanzu bazasu sake gigin ta6ani ba,”

  Hannu Sgr yasa tare da janyo junaid ya dawo ta gabanshi suna fuskantar juna sannan yace”junaid,u ave to be ur own hero,wannan ne burina,banason kana abu tamkar ba namiji ba,kai fa jini na ne!”

   murmushi junaid yayi tare da É—an sunnar dakai cikin jin kunya yace”insha Allah babban yaya zan zama kamar yarda kakeso,”

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

   “Yawwa,haka nakeson ji,ina rigata ne”? Ya tambaya yana kallon shi,

   juyawa juanid yayi yana kallon Sehrish dake rumgume da rigar sgr a hannunta,

  Murmushi yayi tare da cewa”Tana a wurin sehrish,ita tace na bata ta ruÆ™e maka bari na kar6a maka,”

  Juyawa yayi zai tafi,cikin sauri Sgr ya ruÆ™o rigar jikinshi tare da cewa”zan amsa dakaina,wuce ka shiga cikin gida banason ganinka haka,kayi wanka sannan ka huta sosai,’

  Amsa mashi yayi da toh sannan ya kama hanyar zuwa cikin gidan da dan gudu² kamar yarda ya umarta,

   A natse ya soma tafiya har ya isa inda sehrish take atsaye Æ™anÆ™ame da rigarshi a hannunta,sam batasan meke wakana ba,ta manna rigar a hancinta idonta a rufe tana shaÆ™ar kamshin turarenshi,da alama ba Æ™aramin yanayi ta shiga ba,

    koda ya Æ™arasa inda take tsaye,idonshi na akan rigar shi dake rungume ahannunta,hannu yakai tare da ruÆ™o rigar zai janyeta daga hannun sehrish,ae kuwa cikin rashin sani sehrish ta Æ™ara Æ™anÆ™ame rigar alamar bazata saki ba,duk a tunaninta junaid ne zai kar6i rigar,batasan cewa mai rigar bane yazo dakan shi,

   a karo na biyu ya Æ™ara kai hannu zai ruÆ™o rigar,cikin sauri sehrish ta cafke hannun shi tare da yin wurgi dashi gefe guda,fuskarta tamkar zatayi kuka tace”dan Allah junaid menene haka,bana ce kabarmin rigarba,zan kai mashi ita dakaina,”

   Sai da takai Æ™arshen maganar,sannan taso ma tunanin wai hannun wanene ma ta ruÆ™o!tabbas wannan ba hannun junaid bane akwai bambanci sosai ko ta wajen girman hannun,

A hanzarce ta Buɗe idanunta tare da sauke su akan ƙafar Sgr dake tsaye agabanta,wata irin zufa ce ta soma kartomata a fuskarta,nan take ta soma haɗiyar yawu,sai faman mazurai takeyi tana zazzare idanu,

  Ja da baya ta É—anyi murya na rawa a hankali ta shiga ambaton”nashiga ukuna!ashe shine da kanshi,wayyo Allah na wlh nayi tunanin junaid ne……..’

  Bai bari ta Æ™arasa maganar ba,yasa hannu tare da kar6e rigarshi,sannan ya wuce izuwa cikin gidan batare da ya zura rigar ajikin shi ba,

  ajiyar zuciya sehrish tashiga saukewa hannunta na dafe da saitin zuciyarta,a haka ta nufi cikin gidan tana zullumin karsu haÉ—u dashi,bakomai tafi ji ba fa ce yarda tayi wurgi da hannunshi cikin rashin sani,tabbas a lokacin da bai kai zuciya nesa ba,Mari zata sha zazzafan gaske,amma sanin cewa ba da gangan tayi bane yasa baiyi mata komai ba,

_💋Boss Bature💋_

Ba ƙaramin bacci hossana da Omar suka sha ba ahaka,har lokacin jahad na a cikin bedroom ɗinsu kwance saman gadon bacci yayi awon gaba da ita,hannunta na rungume da zanen fuskar junaid da tayi,ta ƙanƙame shi a ƙirjinta kamar wani yace zai ƙwace mata shi,

   wuraren Æ™arfe É—aya,Omar ya farka a hankali ya buÉ—e eyes É—inshi yana faman sauke ajiyar zuciya,mayar da idanunshi yayi akan hossana dake Æ™anÆ™ame dashi,gaba daya ta zura hannayenta tare da ruÆ™o waist É—inshi,kanta kuma na akwance saman kafaÉ—arshi sai sharar bacci takeyi abunta,gashin kanta ya zuba harya rufe side face É—inta,

  A hankali yasa hannunshi tare da ruÆ™o curly hairs din nata,yayi gefe dashi izuwa saman bayanta,hakan ya bashi damar kallon fuskarta da kyau,ba Æ™aramin kyau tayi mashi ba,musamman yarda lips É—inta ke motsi,dama jazamun ne hossana bata iya bacci batare da la66anta na motsi ba,haka zalika yatsun hannunta kullum cikin kerma suke saboda sabo da 6arna,

   Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta,kafin ya mayar da fingers É—inshi a saman brownish lips dinta,a hankali yake shafa tausasan la66an nata da hannun shi,dan tunani yayi hakan yasa ya fara Æ™oÆ™arin janye  yatsan nashi yaji ta cafke shi da bakinta,sucking É—inshi ta shiga yi batare da saninta ba,

  Murmushi Omar yayi yana kallon yarda ta Æ™ankame mashi yatsanshi acikin bakinta,tana tsotsa kamar wata jinjira,

   Da farko ya É—auki abun wasa,amma daga bisani sai ya dinga jin wata irin kasala na rufe shi,lokaci guda ya soma shiga yanayi na son kasancewa da ita,hakan yasa cikin sauri ya zame yatsanshi daga mouth É—inta gudun karya jefa kanshi cikin matsala,

   Lalla6awa yayi tare sanya hannunshi ya janyeta daga saman kafaÉ—arshi ya kwantar da ita saman sofa É—in,sannan ya miÆ™e tare da ruÆ™o Æ™afafunta ya haura dasu saman kujerar,

   Sannan ya dawo tare da zuÆ™unnawa adai² saitin fuskar hossana yana kallonta,

  A hankali yace”Me zan buÆ™ata bayan wannan arayuwata?na mallaki komai da nake buÆ™ata a duniyar nan,nagode ma Allah daya haÉ—ani da Æ™addarata cikin sauÆ™i batare da nasha wahala ba,tana sona sosai,kuma insha Allah bazan karya mata zuciya ba,a shirye nake dana mallaka maki kaina….duk da takasance mai ta6in hankali,a haka nake Æ™aunarta,shi so babu ruwan shi da wannan,burina nasamu wacce take sona tsakani da Allah badan wani abu dana mallaka ba,gashi kuma nasamu,ita wannan bata da cikakken hankalin da zata iya sona don wani abu,burinta kawai Ya omar É—inta ya kasance atare da ita ko da yaushe….zanje kawai na sanar ma Abbana cewa,Nifa na isa aure,kuma na samu wadda ta dace da rayuwata,yarinyar ta kwanta mun araina sosai tun ranar dana fara ganinta,ashafa fatiha kawai Abba akaimun ita É—akina,me ya fi wannan? 

   ya Æ™arasa maganar cike da zolaya yayin da fuskarshi ke É—auke da Æ™ayataccen murmushi,

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

   yunkurawa yayi tare da miÆ™ewa sannan ya juya cikin sauri ya fuce daga palourn saboda kiran salla da ake ta faman yi,

  sam Æ™afafunta sun gaza É—aukarta,jikinta ba Æ™aramin sanyi yayi ba,ashe tun lokacin da Omar yake zukunne agaban hossana yana furta waÉ—annan daddaÉ—an kalaman nashi take a tsaye tan sauraron shi,

Bata jima da farkawa daga bacci ba,fitowarta kenan tayi arba da wannan tashin hankalin,

  Allah sarki jahad,sosai tayi kuka daga tsayen da take,tama rasa kukan me take yi,shin na farin cikin cewa Omar yana son É—aya daga cikinsu ne,ko kuma na baÆ™in cikin cewa Hossana yake so ba ita ba?

  Jiki asanyaye ta Æ™arasa cikin falon,adai dai inda Omar ya zukunna saitin fuskar hossana dake kwance saman 3 seater É—in, itama adai dai nan taje ta zuÆ™unna tana kallonta,sai faman sharar bacci takeyi,

  Cikin shessheÆ™ar kuka jahad ta soma magana da wannan sanyayyiyar muryartata,

   “Ho..hos…sanah….ni bazanyi baÆ™in ciki dake ba,sam banji kishi ba da Ya omar ya bayyana soyayyarshi agare ki ba,duk da naso ace ni na mallake shi ba don komai ba sai don burin da nake dashi na ganin cewa na saka mashi da irin kyautatawar da yake yi mana,wannan ita kaÉ—ae ce hanyar da zamu iya faranta mashi,idan har ya auri É—aya daga cikin mu ni ina da tabbacin cewa bazai ta6a danasani ba,kawai abunda nake tunani shine,banda tabbacin cewa Hossana zata iya kyautata mashi sosai amatsayinta na wadda take da ta6in hankali,bansani ba ko hossana zata iya faranta mashi ba,idan har ya aureta taya zata iya É—aukar dukkan wata buÆ™ata tashi,taya zata iya?that’s the reason why naso ya aure ni kenan saboda ni ina da cikakken hankalin da zan iya yi mashi komi yakeso,zanyi mashi biyayya sosai,zan bishi sau da Æ™afa,amma sai dae kash ni ban samu wannan damar ba,hossana ke kika samu wannan damar,hossana you’re among the most lucky women in the world,ina tayaki farin ciki sosai,ki tashi kiyi godiya ga ubangijinmu Allah subhanahu wata’ala daya mallaka maki kyakkyawar zuciya irinta Æ´a’ Omar,that’s the most greatest gift hossana,”

   jiki asanyaye jahad ta Æ™arasa maganarta,sannan ta miÆ™e a kasalance tana ja da baya da baya,yayin da idanunta ke ci gaba da zubar da hawaye,

   “Shi kaÉ—aine namijin da nake da burin na aura aduniyar nan,akan shi ne nafara jin so,na kuma son ya raÉ—aÉ—insa yake,a duk lokacin da mutun ya rasa abunda yake so,”

   juyawa tayi da gudun gaske ta koma cikin bedroom É—insu tare da faÉ—awa saman gadon nasu,tana ci gaba da kukan da takeyi,

  Cikin kuka take faÉ—in”na rasa first love É—ina,Ya Allah ka bani makamancinshi duk da nasan cewa zaiyi wuya nasamu kamar shi,” hannu takai tare da janyo drawing book É—inta,É—ago da kanta tayi ta zuba ma zanen fuskar junaid ido tana kallon kyakkyawan murmushin nan nashi,

  Nan take taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta,hannu tasa tana shafa zanen,tana ci gaba da kallon shi,kamanceceniyar su da Marshal omar har taso tayi yawa,saboda junaid fuskar Abbansu ce sak,kuma marshal omar yana É—aya daga cikin masu kama da abban nasu sosai,hakan yasa kamarsu ta fito sosai,

     (Tashin hankali,son maso wani,junaid nason sehrish,ita kuma Rafayet takeso,yayin da shi kuma rafayet har yanzu baisan menene So ba,ga kuma jahad tafara faÉ—awa tarkon junaid,Ya kenan?)

  A Æ™arshe Ina taya Hossana murna,dama bai cancanta tasha wahalar soyayya ba,kasancewarta mai ta6in hankali,in har bata samu abunda takeso ba,to fa acan dawanaun kano zamu tsinto ta,amma duk da hakan kuna tunanin cewa Zasu samu Juna cikin sauÆ™i ita da marshal Omar!???????????

Tuni su Hayaam sun jima da barin maid suna kan hanyarsu ta zuwa Abj,kafin ta bar gida sai da Mamynsu ta haÉ—ata da magungunan data amso mata a wurin bokansu,kala kala wanda zata yi amfani dasu na mallaka,akwai na shafawa ajiki,da wanda akeyin turarensa,da kuma na zubawa acikin abinci ko abunsha wanda za ta zuba ma Sgr,tsaf ta kammala shirya komai saura aikatawa kawai ya rage,

  (Nace ba, Allah ya ba mai rabo sa’a)

  jin shiru babu kowa acikin gidan ya ba Amal damar tashi daga saman katifar da take kwance tana jinya tun jiya,ba Æ™aramin jiki taji ba baiwar Allah,tazama abun tausayi ga yunwa ga ciwo ga kuma rashin wanka, 

  dakyar ta iya fitowa daga cikin É—akin adaddafe take tafiya,tsayawa tayi tana tunanin mai yakamata tayi,

 Babu kowa a tsakar gidan,tun bayan da Sofwan yazo ya É—auki Hayaam,Mammynsu da Abra suka fita rakiyarta daga can kuma suka wuce gidan makwabtansu,gidan da suka saba zuwa zaman kashe buje,daga kaga mata sun taru agidan toh fa tsegumi ne da gulma yakaisu,tun daga kan sunan matar gidan zakasan cewa ba Æ™aramar guyababba bace,suna kiranta tsigai acan suke kai Amal wurinta in Amani tazo,su rufe ta aÉ—aki don karsu haÉ—u da Æ´ar uwarta,

 Shiru Amal tayi tana tunanin abunda ya dace tayi tunda babu kowa agidan yanzu lokaci ne da yakamata ta yanke shawarar yarda zata haÉ—u da Æ´ar uwarta,

  Cikin sauri ta nufi É—akin Mammynsu abrah gabanta na faÉ—uwa tsoranta karsu shigo su tarar da ita,a hankali tasa Æ™afa ta shiga cikin É—akin nata,tsayawa tayi tana faman waige waigen inda zata samu koda waya ce,

  Karaf idonta suka sauka akan kuÉ—aÉ—en dake baje saman gadon Mammynsu,sabbin Æ´an dubu dubu,da alama mantasu tayi a wurin bata kwashe su ba,

  nan da nan tunanin Amal ya kasu kashi biyu,

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

   “Amal kina buÆ™atar kuÉ—in da zaki je wurin Auntynki!wannan dama ce agareki,yakamata kiyi hanzarin kwashe kuÉ—in nan kafin su dawo,ki tattara kibar masu gidan,Amal kada ki bari damar nan ta wuce ki!!!ki je ki É—auka!ki É—auka mana!Amal ki tafiiiii!!!!!!!”

  zazzare ido tayi lokacin da taji abunda zuciyarta ke sanar da ita,

  Wani tunanin kuma ya sake zuwa mata

  “Amal kada ki ta6a kuÉ—in nan!wannan sata ce,in kika É—auke su Allah zai kamaki!ki hanzarta barin É—akin nan tunkafin kiyi danasanin zuwan shi!kiyi haÆ™uri kibarma Allah komai mai wuce wa ne,”

  Runtse ido Amal tayi yayin da idanunta ke fitar da hawaye masu zafin gaske,

   “Ni ba 6arauniya bace,bazan É—auka ba,saboda bana son Allah ya kama ni da laifin sata,” cikin shessheÆ™ar kuka ta furta hakan abayyane,

  Sannan jiki asanyaye ta kama hanyar fita daga É—akin,har tasa Æ™afa zata fita daga cikin É—akin,kwatsam kwakwalwarta ta soma tariyo mata wani abu daya ta6a faruwa,a lokacin Mammy tayi ma Amani Æ™aryar cewa za’a je nemo Amal,amma ana buÆ™atar kuÉ—i saboda za’a haÉ—a da manyan malamai domin suyi addu’ar neman dace wa,jiki na rawa Amani ta turo da kuÉ—i kusan dubu É—ari uku acikin acct É—in Abra da niyyar akaima malam kuÉ—in don suyi addu’a akan lamarin,A ranar da abra ta ciro kuÉ—in a banki,tunkafin tadawo gida ta wuce kasuwa tayi masu siyayar kaya masu yawan gaske,

  Æ™iri-Æ™iri suka hana Amal ko sisi acikin kuÉ—in nan,kuma ita mammy da kanta ta kira Amal tare da jan kunnanta ta janyota har cikin É—aki ta nuna mata kuÉ—in da Amani ta turo da kuma kayan da suka siya saboda rashin imani, aranar Amal tasha kuka sosai,

  Cike da Æ™warin guiwa Amal tace”Bazan bar kuÉ—in nan ba!haƙƙina ne su!nima sunci mun kuÉ—ina,”

  Cikin sauri ta juya tare da nufar cikin É—akin,kai tsaye ta tunkari gadon Mammyn tasu,hannunta na kerma zufa na tsastsafo mata a fuskarta,haka tasanya hannu tare da tattara kuÉ—in gaba É—aya ta haÉ—esu guri guda acikin hannunta,a Æ™alla sunyi dubu hamsin,

   kamar daga sama taji motsin wani ya faÉ—o acikin É—akin,a wani irin firgice Amal ta watsar da kuÉ—in tare da juyawa tana kallon bakin Æ™opar shigowar idonta azazzare~~~~~~~~~~

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Wannan kenan

  Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa

Cup cake etc 

Contact me 09063302182or 09012179727.

   Kada abaku labari

Back to top button