Hausa novels

Mijin Malama Page 4 By Nimcy Sarauta

*🌈 MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta

*_Please kuyi following Acct ɗina a arewabooks🫰🏿_*
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

*4……*
Mummunan hatsarin ya ja hankalin mutane da yawa, hatsari ne wanda za a iya cewa tsautsayi ne da kuma gangan cin driver da yake driving yana waya. Da gudu babbar mota tayi gaba bayan tayi wurgi da Tajju zuwa gefe guda, nan take kan Tajju ya fashe jini ya fara zuba hannunsa guda ɗaya ya fita fit daga jikinsa ko shurawa bai ba rai ya yi halinsa. Motar dake bin bayan babbar motar data buge Tajju ce ta tsaya, cikin sauri driver da wanda yake gefen mai zaman banza suka fito bakinsu ɗauke da sallati “General kira mana Ambulance” cikin sauri General ya ɗakko wayarsa tare searching asibiti mafi kusa da kuma motar asibitin. Hammad ya ce “Allah sarki, haka rayuwa take Allah ya jiƙansa ya yi masa rahama” General ya amsa da “Amin” da sauran jama’ar wajan suka amsa.
Har Hammad zai juya idanunsa ya sauka akan Envelope dake can gefe guda iska na kaɗata a hankali ya ƙarasa tare da ɗauka, a ransa yana tunanin maybe a samu wani bayanai akan mamacin. Ya ware Envelope ɗin first abin da ya gani shi ne ring irin na al’ƙawarin nan, ya juya ring ɗin sosai sai kuma ya zura acikin aljihu, gently idanunsa ya sauka akan headline na wasiƙar kamar haka.
*_BAD MAN, THE STUBBORN BOY, CRIMINAL, GANG BOY, THE LEADER_*

Also Download>>> Mijin Malama Page 1 By Nimcy Sarauta

Daga wannan rubutun idanun Hammad ya sauka ƙasan headline ɗin inda aka rubuta “The memories, was going on my mind, har abad, nasan ni mahaukaci ne da gaske kamar yadda ki ke faɗa Jee” jikin Hammad ya shiga rawa ganin General na ƙara suwa ya tura wasiƙar Aljihu “Lafiya?”
“Actually, good”
Kafin suyi magana Ambulance ta ƙara su aka ɗauki gawar Tajju tare da sanyata ciki, Hammad ya buɗe ya ɗauki wata number da yaga ana ta kira anyi saving da “Bad boy”
“His phone” cewar Hammad bayan kammala komai Ambulance suka tafi asibiti da shi. Suma su Hammad mota suka shiga driving kawai yake amma tuni ya yi losing mind ɗinsa, fatan sa kawai ya isa Gov. Abu-turab Alƙasim, ya san cewa yanzu ya koma gida kasa jurewa ya yi ya ɗauki Wayarsa tare da kiran keɓantacciyar number Abu-turab kusan kira uku kafin ya ɗauka cikin nutsuwa ya ce.
“Uhm” Hammad ya ce
“Your Excellency, akwai damuwa” a taƙaice ya ce
“Kace komai, banda rasa Majee” cikin ladabi ya ce “Am very sorry for that, amma bamu sameta ba, amma mun sami maganin matsalarta, ɗan waye, cikin waye, yadda aka samu cikin duk yana ciki” Abu-turab ya miƙe daga zaunan da yake ya shiga zagaye haɗaɗɗan parlourn nashi fuskarsa tayi jajir. “Ok, meet me at my house” yana faɗin haka ya kashe kiran. Tafiya kaɗan ce ta ƙara su da su cikin gidan Abu-turab wanda yake zaune tare da iyayensa, sojoji birjik ta ko’ina daka nuna rashin gaskiya zaka ji maza akan ka. Girman gidan ya zarce tunani, motoci kala-kala na kamfani daban-daban.
Ko a jerin masu kuɗi ba kowa zaka samu da wannan haɗaɗɗan gidan ba, gida ne 50 by 50 iya compound na gidan zai ja hankalinka balle ciki. Kasancewar ba wanda bai san Hammad ya sa ba wani wahala ya nufi cikin gidan, a Main parlour ya samu Mama na sakkowa daga bene ya yi murmushi ya ce
“Sannu da gida Mama” kallonsa kawai take fuskarta kwance da annuri amma kana ganin sanyin jikinta kasan akwai damuwa, kyakkyawar dattijowa mai nutsuwa da sanin ya kamata,ga ilimi na iya zama da ko wanne mutum ga kyakkyawar mu’amala. “Na ɗauka mun yi laifi yau ne” cewar Mama bayan ta zauna.
“Laifi kuma Mama?” Ta dubesa kafin ta ɗauke kai ta ce “Naga babu ko mai kama da kai, hala wani aikin ka ke” ya shafa kai yana rusunawa ya ce.
“Haka ne kam, ina Yake?”

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Ta ɗaga kai zuwa part ɗin dama da yake upstairs ta ce. “Ina son tambayarka dama, meke damun shi? Tunda ya shiga part ɗin sa bayan ya dawo bai fito ba, hatta wajan art ɗin da yake shiga yau shiru, lunch ma bai ci ba na kira phohe number sa na gida a kashe” ta tsare shi da idanu ya ce “Akwai wata tattaunawar sirri da yake da ita, maybe shi ne yake duba muhimman abu kasancewar tattaunawar sai 12 na dare”
Ta jinjina kai tare da faɗin “Allah ya taimaka, kasan ƴar rigimarsa ta hanani sakat ita dai Abbi” Hammad ya yi dariya sosai ya ce “Jiddatul-khairi ai ya saba mata ne” kafin Mama tayi magana sai gata ta fito da gudu ta faɗa jikin Hammad ta ce “Uncle, Abbina” ya ɗauketa ya shiga hawa upstairs yana faɗin
“Daughter me, bari muje muga Abbi sai muje siyan chocolate ko?” Tayi murmushi dimples ɗinta soka loma tana ta masa surutu har suka isa haɗaɗɗan part ɗin da kana ganinsa kasan Gov. Abu-turab Alƙasim ne a ciki. Hannu Hammad ya saka cikin wani screen dake ƙofar nan take ta fito da bayanan Hammad a hankali kuma ƙofar ta buɗe.
Jidda ta ƙwace daga hannun Hammad tayi cikin parlourn da gudu tana kiran sunan Abbi, yana zaune saman kujera daman alrdy ya san da zuwan Hammad ɗin, kayan shan iska ne a jikinsa fara Armless da black ɗin 3 gauter.
Hannunsa ɗaya riƙe da Black tea wanda aka sanya masa zuma a ciki, news yake kallo har Jidda ta faɗa jikinsa hankalinsa baya tare da shi. “Abbina”
Ya ware idanunsa idanunsa da suke a ɗan lumshe ya dubeta “First love” sunan da yake faɗa mata kenan, duk da kasancewarta ƴar shi guda ɗaya. “Abbi”
Ya juya bayan ya gyara mata zama a cinyarsa tare da kallon Hammad yana son ya ji wanne labari ne da shi wanda yake da alaƙa da Majeederh.
“Your Excellency barka da yammaci” jinjina kai kawai Abu-turab ya yi.
“Ga wannan wasiƙar, idan ka karanta sai ka ɗauki matakin daya kamata akai, ita kuma zamu nemota In sha Allah” hannu ya sa ya amshi wasiƙar tare da warewa zuciyarsa na harbawa, bai san mene ya sanya duk abinda ya shafi Malama Majeederh ya ke jinsa har ƙasan zuciyarsa ba, barci ya ƙauracewa idanunsa, ga ciwon kan dake ƙoƙarin kwantar da shi.
Duk Yadda ya so ya daure da riƙe kansa ya kasa ya miƙe tsaye da sauri yana ware idanunsa akan paper ɗin, tsoro,fargaba damuwa da kuma firgicin rashin sanin makomarsa wajan Majeederh ya taro ya haɗe masa waje guda.
Ya sanya hannu ya share zufar daya yanko masa, lokaci ɗaya ya hargitse wani zazzaɓi na neman kawo masa farmaki.
“Your Excellency, lafiya dai?” Ba tare daya kalli Hammad ba ya ce
“Ham…mad” “Yes, Your Excellency”
Ya juya gabaɗaya fuska a haɗe ya ce “Tun yaushe nake baka labarinta?”
Kai tsaye ya ce “Shekaru wajan biyar, tun ranar daka halarci musabaƙar da aka yi ta ƙasa”
Abu-turab ya jinjina kai, Elxty 5yrs kenan, a wannan musaɓar ya ji muryar Majeederh, muryar data sanya masa dafin so a zuciya ta zautar da duk wani tunaninsa, ya wanzu cikin muradinta a zuciyarsa, shi kansa ba zai iya sanin abinda ya sanya bai tun kare ta da wannan maganar ba, samun Majeederh Abdul’aziz Khan a garin nan ba wahala zai masa ba. “Har abada Majeederh kada ta san da wannan wasiƙar” da mamaki fal fuskar Hammad ya ce “Your Excellency amma kamar ba a kyauta mata ba, wannan wasiƙar ita zata fitar da ita daga zargi, kuma ita ce zata gane waye ya aikata mata haka” Abu-turab ya koma ya zauna kawo yanzu yasan Bp nasa tuni ya hau cikin kamilalliyyar muryarsa mai tsafta ya ce “Me ka ke nufi?”

Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document

“Ba mu yi mata adalci ba” cewar Hammad.
“So baya buƙatar adalci, kansa kawai ya sani, ayi hakkan ya tsaya ni da kai” Hammad ya kalli Abu-turab yana girmama yadda yaso kansa a fili sbd soyayya,idan har son gaskiya ne ba zai taɓa bari Majeederh taci gaba da zama da zargi akanta ba. “Shikenan, Your Excellency. Maganar meeting naka an gama shirya tattaunawar a guest house ɗinka, da kai da Deputy Governor, Secretary to the state of Government, Chief of staff” hannu bibbiyu Abu-turab ya riƙe kansa kana ya jinjinawa Hammad kai ganin yanayinsa ya sa Hammad cewa “yana da kyau ka huta haka, Jidda zo muje” ta maƙale ka faɗa jikin Abu-turab.
“Abbi baya jin daɗi” Abu-turab ya ware idanuna ya ce “Go”
Ta kwaɓe fuska cikin zafin zuciya ya ce “I said Go Hawwa’u Abu-turab Alƙasim!” Tsawar ta gigita mata lissafi ta fashe da kuka tana ƙanƙame Hammad ta ce
“Uncle” ya ɗauketa yana girgiza yana mamakin sauyawar Abu-turab lokaci ɗaya.
Dukkan abinda ya faru akan idanun Malama Majeederh Abdul’aziz Khan ya wakana, kasancewar bata fahimta kusan tunaninta duk ya jirkice ƙwaƙwalwarta na gab da fara daina aiki yasa bata fahimci su waye ba, motsi kaɗan zata ƙanƙame jaririnta kamar zata bayar da shi ciki, wani zubin kuma tayi ta surutu ita ɗaya sbd tarin abubuwan da suka cunkushe mata, yunwa ba a maganarta jikinta ya fara tashi sbd jini da rashin wanka.. duk wannan abun da lokacin Sallah ya yi zat nemi waje mai tsafta ta yi taimama tare da sallah, bata shagala da tunani istigifari da addu’ar neman samun sauƙi wajan Ubangiji bai bar bakinta ba.
Washe gari Abbu ne zaune a parlour da Mami sai Ruma da Raihana wanda aka kira su daga gidan mazajen su, sai kuma Aaliyyah dake zaune tamkar marainiyya Idanunta a kumbure ko gani ba tayi sosai, sai Uncle Isma’il da Uncle Bello. “Yanzu har a ranka kana jin kayi daidai?” Abbu ya dubi yayan nasa ya ce “Majeederh dai ni na haifeta, ni na samar da cikinta na kuma raineta, kuma na dawo na ce bani da haɗi da ita don haka a bar wannan maganar” Uncle Isma’il ya ce “An barta, amma ka bani mamaki a matsayinka na Uba kuma dattijon ƙwarai har ka iya shafawa idanunka toka ka ce wai ka sallamawa duniya Majeederh, sbd kawai kada sunan family da naka ya ɓaci? Familyn bazan sunanka ɗin banza, da rayuwar mace kamar Majeederh ta ɓaci ba gwara duka sunayenmu su ɓaci ba, wata rana dalilinta sunan namu ya samu ɗaukakar damu kanmu ba muyi zato ba, mai ya sanya mu iyaye idanunmu ya kan rufe idan tsautsayi ya samu yaranmu? Yanzu Majeederh ko tana sane wannan abun ya faru ba zaka iya yi mata uzurin akan rashin auren da take da shi ya ja mata wannan ƙadsarar ba? Ita ɗiya macace duk runtsi duk jimawa dole ta ɓukaci ɗa namiji wata rana” Uncle Isma’il ya girgiza kai sbd tsabar takaici ya ce “taya ƙasa zata gyaru bayan mu da kanmu bamu gyara zamantakewar data yaranmu ba, fine ka kori Majeederh zan nemota na riƙeta a wajena….,”
“Yin hakan zai ja mana babban kuskure yaya, duk wanda zai so ta bayana yake bi, don haka a barni kawai” Abbu ya tari numfashi Uncle Isma’il da faɗin hakan. Uncle Isma’il da ransa ya fara ɓaci ya ce “Zan taimaketa kamar yadda take taimakon addinin Musulunci, bawai sbd data kasance ƴarka ba Abdul’aziz Khan” Abbu rai ɓace shi ma ya ce “Kana iya yin haka amma daga ranar babu ni ba kai, ka cire ni matsayin ƙaninka, ka yanke mu’amala ta dakai” murmushi sosai Uncle Isma’il ya yi wanda ya fi kuka ciwo yana girgiza kai ya ce “In sha Allah, idan kero na yawo zabo na yawo tabbas za a gamo Majeederh zata baka mamaki” Aaliyyah dake kuka sosai ta ce “Abbu don Allah ka bawa Yaa Nura dama ya kawo kuɗin aurena, na ga ji da zaman gidan nan na tsani komai dake cikinsa” kai tsaye Mami ta ce “Fitowa za kiyi ki ce kin tsanemu, aure kuma dole sai kin kammala makaranta daman ke ɗaya ki ka rage cikin gidan..” sai a lokacin Uncle Bello ya ce “Aaliyyah aure ki ke so?” Duk kawaicin Aaliyyah ta shanye ta ce “Eh, Uncle”
“Ki faɗawa Nura ya zo ya saman a gida nan da sati mai zuwa In sha Allah zaki bar wannan gidan” yana faɗin haka ya miƙe tsaye ya kalli Uncle Isma’il ya kalli Abbu ya ce “Yaya taso muje, Allah ya bada ladan zumunci Sunan family kuma a rubuta a gaban ƙoshi ana yawo da shi”
Suka fice tare da barin gidan,Abbu ya nufi part ɗin sa zuciya babu daɗi shi kam Majeederh ta zame masa annoba, Aaliyyah ta shige nata bedroom ɗin tana zuwa ta ɗauki wayarta ta kunna network ta shiga facebook inda labarin Majeederh da Bar Aliyu Sufyan Alhassan yake ta trending a media. Ko photon Majeederh ta gani da gudu take skipping ta shige sbd tsaron zagi da mugun alkaba’in da ake mata, tana cikin dubawa taci karo da wani posting photon Majeederh ne sanye da abaya fara mai kyau fuskarta rufe hannunta riƙe da loudspeaker. An yi rubutu a saman photon tare da saka.

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

*She’s Innocent*
_Malama Majeederh Abdul’aziz Khan babbar malamar musulunci da muke da ita a wannan jiha, wacce ta samu damar zama zaƙaƙura wajan lashe musabaƙar Alkur’ani ta ƙasa, ita kuma ta ƙara jawo kima da martabar jiharmu, wacce take taimakon marayu, marasa gata take nutsuwar da matan aure akan darajar da aure yake da shi, duk da kasancewarta budurwa. Abin tambayar shin ta cancanci haka kowa? Kai da ka ke zaginta ko ki ke zaginta kina da tabbaci akan abinda ya faru, ko kina da hujja? Ko labarin ƙazan kurege aka baki har kike ɗorawa tare da aibatar ƴar jama’a, ta haifi wasun ku da yawa, ta fiki ilimi tunani da sanin ya kamata, ta fika kusanci da mahalicci amma kazo media ko sallar kirki a rana baka yi ka ɓuge da zagin babbar Malama? Ashe muna rayuwa da dabbobi bamu sani ba? Ko masu aikata zina sai an same su turbi da taɓarya tare da shaidu 4 sannan za a ɗauki mataki. MALAMA MAJEEDERH ABDUL’AZIZ KHAN SHE’S INNOCENT I STAND BY HER SIDE._

#Mrs No name

Wani murmushin jin daɗi Aaliyyah tayi 5 minutes da yin posting ɗin amma comments wajan 1k hakan ya tabbatar mata da Mrs no name yana da followers kuma babban mutum ne tunda har ya iya ɓoye sunan shi, kai tsaye profile ta shiga ya rufe komai da komai ko message ba za a iya yi masa ba, dole sai dai tayi magana ta comment section.
Har aka kwana aka tashi Bar Aliyu Sufyan Alhassan bai farka daga suman da ya yi ba, hankalin Hajia ya tashi tana da Papi tare da Almustapha, hatta korar da aka yi masa wajan aiki bai sani ba.
Misalin 8 na dare wahala tayi wahala jikin jaririn ya yi zafi kamar wuta, a yanzu ji take ko jama’ar gari za su kasheta babu abin da zai hanata fita ta nemi ruwan da zata bawa babyn nata, ta miƙe da ƙyar kusan gabaɗaya kayan jikinta sun ɓaci tana bin gefen hanya harta isa wani wajan da ake siyar da tsire kanta ƙasa tayi sallama, gabaɗaya mutanen da wajan suka dubeta wani ya ce “Baiwar Allah lafiya?” Ta jima kafin ta ce “Ruwa nake nema, zan bawa yarona” wani saurayi ya dinga kallonta kafin ya miƙe tsaye ya ce “Mene na rufe fuskar?” Ta ɗauke kai cikin sa a ya gano rabin fuskarta da jaririn hannun da ƙarfi ya ce “Masiƙa la’ananniyya mazinaciyya ku je feta ita ce Malama Majeederh” yana faɗin hakan ya sauke mata wani dutse a ƙoshinta ji ka ke tauu!! Nan take ya fashe jini ya dinga zuba, kafin ka ce me mutane sun cika kowa ya ɗakko duwatsu suka fara jifanta ta ko’ina ta durƙoshe ta rungume jaririn da jikinta, jama’a sunfi ashirin idan wannan ya jefa mata dutse aka sai Wannan ya jefa mata a baya…

 

Read Page 5 Here

 

Na’ima Sulaiman Shu’aibu
Nimcy sarauta
08119237616

Back to top button