Halysaah Page 154 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 154…Karfe takwas na safe Khaleesat ta shiga dakin da Safiyyah ta kwana, tana rike da tray din breakfast din da Yakumbo suka kawo part din, Khaleesat ta dinga kallonta da mamaki ganin har ta gama shiryawa tana kokarin zuge zip din akwatinta tace “Ina kuma zaki da sassafen nan Sophie?” Safiyyah ta daga kai ta kalleta tace “Dama ba nace maki yau zan tafi ba, so kike Daddy yayi disowning dina ashe, gaskiya da safe nace ma Ya Musty zan taho, kusan kwanana goma sha daya yau fa” Khaleesat tace “Amma ni dai ba wurina kika zo ba on a serious note, kawai wajen cousin sister dinki kika zo a Gombe, all in all ko kwana hudu fa baki yi a gidan nan ba Sophie” Safiyyah tace “Ina kwanciyar hankalin yin kwanaki a masarautar nan Khaleesat, ba ruwana aje zuciya ta debeni in doki er mutane a daureni, mun ma yi magana da safen nan da Ajay ya sa driver ya kai ni har Kano, yanxu haka drivern na jiran in fito ne, ashe ku ma tafiya za ku yi da yamma shi ne baki gaya min ba” Khaleesat tace “Tafiya kuma? Tafiya zuwa ina?” Safiyyah ta rufe baki da sauri don bata san Khaleesat bata sani ba, can tace “Nima haka na zarga, na zata dake za ku je Abujan ai” Khaleesat bata ce komal ba ta karasa cikin dakin ta ajiye mata tray din breakfast din hannunta, ta zauna gefen gadon a hankali tace “To yanxu sai yaushe Sophie?” Safiyyah tace “Sai ranan da kika zo Kano, don kwana kusa dai babu abinda zai kawo ni garin nan” Zaunawa Safiyyah tayi kan Carpet tace “Sakko mu yi breakfast din, driver din fa na jirap hankali Khaleesat ta zamo kasa suka fara break din tare, Khaleesat tace “Ko zaki sha shayi in hado maki?” Safiyyah tace “A’a wainar ma ya isa” Khaleesat bata sake cewa komal ba don duk sai bata ji dadi ba Safiyyah zata tafi ta bar ta gashi Ajay baya nan, Safiyyah tayi breaking silence din da ya ziyarci parlon tace “Jiya Jay ya min message asking me when I am leaving shi ne nace masa yau da safe zan tafi, in gaya maki ya turo min 1M” Khaleesat ta daga ido ta kalleta tace “Da gaske? To kin gode, Allah ya saka da alkhairi” Safiyyah tace “Ameen, ai naji dadin kudin, ina komawa Kano zan shiga kasuwa in canza wardrobe” Khaleesat tayi murmushi tace “Lallai kam” Safiyyah tace “Ajay ma fa abinda ya turo min kenan kaman hadin baki” Khaleesat tace “To duk mun gode, Allah ya saka da alkhairi” Khaleesat bata wani ci abincin da yawa ba ta mike, ta tafi inda boxes dinta suke ta bude, atamfofi masu tsada uku ta cire ma Safiyyah da Abaya biyu, sai turarruka da kayan make up, har da inner wear set uku, sai da tayi da gaske Safiyyah ta yarda ta amshi kayan, don har sai da ta bata rai, tana mata packaging kayan tace “Bayan ko kayan akwatin ma baki gani ba har yau, kuma babu abinda na baki a ciki balle ki ce baza ki amsa ba don na baki yanxu, to ya ma zan yi da kayan nan gaba daya” Safiyyah tace “To ba dai na amsa ba, ai sai ki shafa min lafiya kuma haka” A tare suka fita Khaleesat zata rakata zuwa parking space tana rike da ledan kayan da ta bata, ita kuma tana dauke da akwatinta, suna fitowa daga bangaren Ajay Khaleesat ta kulle kofar da key ta cire makullin, tun mafarkin da tayi jiya taji kowa na gidan na bata tsoro kuma y Yakumbo ce kawai taji ta yarda da ita dari bisa sun dan yi nisa wata mal aiki a gidan ta taho cikin ladabi zata amshi kayan hannunsu, Khaleesat tace “A’a bar shi, mun gode” Mai aikin tayi insisting, Khaleesat dai bata yarda sun bata kayan ba suka ci gaba da tafiyarsu, Safiyyah tace “Allah sarki baza muyi sallama da Yakumbo ba, tana da kirki wallahi” Khaleesat tace “Ai ban san inda take ba yanxu, and I am still not familiar with the house” Ko rufe baki bata yi ba suka hango yakumbo ta billo daga wani corridor by their left, tana ganinsu ta karaso da sauri tace “Ba dai tafiya kawar taki zata yi ba Gimbiya” Safiyyah tace “Wallahi tafiya zan yi Mama, yanxu nake tambayarki sai ga ki” Yakumbo tace “Allah sarki, kuma bangaren Yariman nake niyyar zuwa in ji ko kuna bukatar wani abu” Zata amshi akwatin hannun Safiyyah da ledan hannun Khaleesat duk suka ki bata, Yakumbo tayi kasa da murya tace “Ranki shi dade ai hakan ba komai bane, aikinmu kenan a gidan nan, bai kamata kina matar dan sarki guda a ganki kina yawo da leda a hannu ba” Khaleesat ta dan yi murmushi tace “Ba komai fa Mama” A haka suka fita compound, Drivern dake jiran Safiyyah ya taho da sauri ya amshi kayan hannunsu yana gaida su, wani dogari ya bude ma Safiyyah bayan motar ta shiga tana murmushi ta daga ma Khaleesat hannu tace “To kawata, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bar zumunci, Nagode sosai, ki taya ni yi ma mijinki godiya” Khaleesat ta wani harareta, Yakumbo tayi mata addu’a da fatan sauka lafiya, daga haka suka juya zuwa cikin gida da Khaleesat dake cike da jin kewanta a zuci. Har sha biyun rana Yakumbo na tare da Khalees bangaren Ajay suna zaune Main parlor tana labarin mahaifiyar Ajay da gwagwarmayar da ta sha a gidan sarauta kafin Allah ya dau ranta, Yakumbo na gyara zama tace “Duk suna kwakwalwata ban mance ba Gimbiya, ganin abubuwan nake kamar yanxu aka yi, tunda a lokacin zanyi shekara sha hudu kinga kuwa ai da wayo na, kuma Baabata warce ita ce Jakadiyarta ta sha bani tarihinta ko bayan da ta rasu, shi yasa sam bana wasa da lamarin Yarima a gidan nan sosai nake jin sa a raina, uwarsa tayi zaman amana da Baabata har ni na sha kwana sashinta, kuma Baabata ta mallaki abubuwan arziki a wajen marigayiya wanda ita ma ta mutu ta bar mana da yan uwana muna cin moriyarsu yanxu haka, kinga bangaren nan da muke ciki yanxu? To sashinta kenan a sanda take da rai kawai fasali Mai martaba ya sa aka canza, yan gidan nan kuwa kamar bakin ciki ya kar su da sarki ya bar ma Yarima nan bayan ya girma, don yana da shekara sha takwas bana mantawa ya dawo sashin nan, tun rasuwan marigayiya babu wanda Sarki ya bari ya kara zama nan sai da dan ta ya tasa aka mallaka masa, da ace kina shiga sashin Fulani zaki ga komai iri daya ne da bangarenta shi yasa take bakin ciki, ita kuma dan ta daki daya ne da parlor daya aka basa” A hankali Khaleesat tace “To amma relatives dinta suna nan garin ne? Ina nufin yan uwanta” Yakumbo tace “Wai Marigayiya?” Khaleesat ta gyada mata kai, Yakumbo tace “Ayya, ai ba er Najeriya bace, da er nan kasar ce ai zaki san su kema, don dole zai kai ki gun dangin Mahaifiyarsa kuma ina da tabbacin za su ja ki jiki, can kasar Ethiopia Mai martaba ya aurota, mahaifinta sananne ne a Ethiopia, sun yi karatı da Babansu Mai martaba wato marigayi Sarki Anyd, abokai ne sosai kuwa, wani lokaci da dadewa Mal martaba na yanxu yayl tafiya suka yi transit a Ethiopia sai rashin lafiva sosal va kamasa a can, a sannan mahaifinsu ke kan kujeran mulki, kinsan tsakanin Mahaifinsu da kuma baban Jawwad shekara shidda ne kacal, Mai martaba Sarki Aliyu wanda shi ya haifesu ya rasu akan mulki aka nada Baban Jawwad, bayan shekara shidda baban Jawwad ma ya rasu, shi ne aka nada Mai martaba na yanxu” Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “Allah ya gafarta masu gaba daya” Yakumbo tace “Ameen ya Allah, to da rashin lafiya ya kama Mai martaba na yanxu sai mahaifinsa Sarki Aliyu ya sanar ma abokinsa na Ethiopia halin da dan sa ke ciki na rashin lafiya a kasar, sai shi Mahaifin Sarauniya me rasuwa ya dauko Mai martaba ya kawosa gidansa don basa kulawa, to kinji yanda Mai martaba ya hadu da mahaifiyar Junaid har Allah yayi aurensu, bayan shekara hudu Mahaifiyar Junaid bata haihu ba, Hajja ta tursasa shi sai ya kara aure, shi ne fa Gimbiyah Firdausi ta masa tayin kanwar aminyarta wato Fulani Hafsah, ubansu korarren hadimin Sarki ne a wata jaha, sam bashi da hali mahaifin Fulani Hafsa, yanxu zancen da nake maki kullum Gimbiya Firdausi da ta sanin wannan hadin take don tuni ta babe da aminiyar tata su ne har kotu abun kunya ga masarautar nan, Fulani Hafsah kuwa sam bata ganinta da mutunci ko na minti daya, gashi ta shiga ta fita ta hana Mal martaba aure, Hajja ta sha hadasa da ‘ya yan sarakuna duk ya ki, kuma duk mun san ba yin kansa bane, akwai wani lokaci ma da tayi ma Gimbiya Firdausin zagin cin mutunci sosal a gidan nan abun dai ba kyau, har sal da hawar Gimbiya ya tashi aka yi asibiti da ita a rikve Yakumbo na kai wa nan tace “To bara in koma asalin labarin da nake baki, tun da aka auro Fulani Hafsa mahaifivar Junaid tavi bankwana da kwanciyar hankali a gidan nan, bakin kishi Fulani Hafsa ke yi da ita don Fulani Mai Jiddah ta fita komai tun daga kyau, ai kin san yanda matan Ethiopia ke da kyau uwa su suka yi kansu, yanda kika ga mijinki wallahi haka uwarsa take, ita ba fara kal ba, kuma ita ba me duhu ba yanda dai fatan yan Ethiopia yake, hatta gashin kansa al duk na uwarsa ne, sannan uwarsa ga tsantsan ilimi, Ita ya gado wallahi, Allah da ikonsa bayan an auro Fulani Hafsa sai Mahaifiyar Junaid ta samu cikinsa, a sannan Fulani Aseeyah tana da cikin Jawwad ita ma, ko wata uku ba ayi da auro Fulani Hafsa ba daga shigowarta gidan Mahaïfin Jawwad ya rasu akan mulki, ya rasu da wata uku aka haifi Jawwad, bayan wani wata ukun aka haifi Junaid, Mahaifiyar Junaid ta sha wahalan Fulani Hafsa sosai don sai da Hafsa ta san yanda tayi duk gidan aka juya ma Mahaifiyar Junaid baya har da Fulani Aseeyah, duk Fulani Hafsa ce ta hada wani babban makirci wanda yasa uwar Junaid da Uwar Jawwad suka dawo ko ga maciji basa yi a gidan nan, wanda shi ne dalilin da yasa Mami bata wani duba Junaid ba bayan rasuwar uwarsa ita ma ta banzatar da shi yanda kowa yayi duk da ita bata masa mugunta kamar sauran, Junaid ya taso cikin kyara da tsangwama a cikin wannan masarauta da kike gani, a wajen ubansa kawai yake jin dadi sai kakarsa warce ta kan yi wata uku har shidda bata leko masarautar nan ba, ya taso bal da kowa sai Allah, ga dangin uwarsa basa kusa, kuma Mai martaba bai karfafa masa dinga zuwa wajer kasar Ethiopia ba saboda yana tsoron kada wataran su ja ra’ayinsa ya ki dawowa, sannan akwal wani babban sirri da zan gaya maki wanda ba kowa vasan sa ba a gidan nan saboda na varda dake Halysaah, kuma nasan babu Inda zaki je ki fadi maganar nan” Juyawa duk suka yi jin an bude kofar parlon, Ajay ya shigo da sallama ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, Yakumbo sal yi masa barka da zuwa take cikin ladabi, ya amsa gaisuwanta sannan ya nufi parlonsa, Yakumbo tayi kasa da murya tace “To ranki shi dade na bar ki lafiya, ki tafi ki kula da mijinki, idan da wani abu da ake bukata sai ki kirani ko ta waya, in sha Allahu zan taho” A hankali Khaleesat tace “To Mama” Mikewa Yakumbo tayi ta nufi kofa ta fita daga babban parlon ta kullo kofar. After some seconds Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali ta nufi parlornsa, ganin baya parlon ta karasa ta bude kofar bedroom dinsa ta gansa tsaye yana unbuttoning shirt dinsa, ta dan kallesa a hankali tace “Ya hanya?” Karasawa yayi kusa da ita ya jawota jikinsa yana kallonta yayi kasa da murya yace “Is that how to welcome ur Mister?” Shiru tayi tana dan turasa don a yanxu idan akwai abinda taji bata so kwata kwata shí ne taji jikinsa a nata ko yaya ne, unlike before da idan yayi haka take jin wani iri yanxu kam reverse is the case, sauke idonta tayi tace “Girki nake yi a kitchen” Yace “Baki bani amsa ba” Ta dan hade rai tace “Amsan me?” Yace “I asked if this is how you are suppose to welcome ur Mister” Turasa tayi tace “Who is my Mister?” Ya dago kanta yana kallonta murya can kasa yace “Ur Bedmate” Kauda kai tayi, bata ce komal ba, shi ko bai fasa kallonta ba, can ta turo baki ta juya zat wajen tace “Sal dal Housemate” Jawota yayi ta jikinsa ya kai bakinsa kunnenta kamar me rada yana kallonta kasa kasa yace “Baki san da banbanci ba?” Taki yarda su hada ido tace “Ba wani banbanci, pls ka sakeni” Yace “To bari a nuna maki banbancin” Da sauri tace “Ni don Allah girki fa nake yi a kitchen, pls ka sake ni in je in duba” Kallonta kawai yake babu ko kiftawa, can ya sauke idonsa yace “Ki kashe girkin Yakumbo ta tafi da shi, za mu yi tafiya ne….” Kallonsa tayi jin abinda yace, tace “Ina za mu je?” Yace “Wani kauye” Bata sake cewa komai ba, yace “Ki shirya kayanki a box, we are leaving in 2 hours time” Daga haka ya saketa, ya karasa cire kayansa ya shiga bandaki, maganar da Safiyyah tayi mata da safe ne ya fado mata, ashe da gasken tafiya za su yíamma bai gaya mata ba, juyawa tayi ta fita daga dakin….. Biyu saura Ajay ya nufi bangaren Hajja Khaleesat na biye da shi a baya, kusan duk shi ya hada mata kayan da za su yi tafiyan da shi a akwatinta, Yakumbo ta kai su can gun mota, Hajja na parlonta suka sameta da Gimbiya Firdausi sai Ummi da Hajiya A’isha, Hadiyah da Shahuda ma suna zaune parlon, tun washegarin ranan da Hajja tace Mai martaba ya soke meeting din da za ayi, Gimbiya Firdausi ta bar gidan sai yau da suka dawo gaida Hajja tare da Shahuda duk da zuwan nasu na da manufa, Ajay ya zauna kan kujera ya gaida Hajja da sauran mutanen dake parlon, Khaleesat ta zauna kan Carpet ita ma duk ta gaishesu kanta a kasa, sal wani kallon sama da kasa suke mata, Shahuda ta kauda kai taki kallon direction din da take zaune, Ajay yace “Za mu yi tafiya ne Hajja” Hajja tace “Tafiya kuma zuwa ina?” Yace “Kasar waje” tace “Ikon Allah, to yaushe har ta samu kantad ku wani yi tafiya Junaid?” Gimbiya Firdausi ta kalli su Hadiyah da Shahuda tace “Ku tashi ku bamu waje” Tashi suka yl duk suna ma Khaleesat kallon banza suka bar wajen, Hadiyah taji kamar ta mutu don bakin ciki, tunda suka yi aure da Jay babu inda ya taba kai ta sai Convocation da suka je aka yi a UK, she was extremely Jealous of Khaleesat, a fusace ta tafi daya parlon ta zauna, Gimbiya Firdausi ta maida dubanta kan Hajja tace “To nima shi nagani Hajja, yaushe taji saukin da har za ayi tafiya? Ita da take bukatar sati uku mai kyau ana kula da ita sosai” Hajja tace “Zuwan kawarta ne ma yasa nace a rakata sashinta jiya tunda dai kawar bazata zaunar min a nan ba gaskiya, kuma nufina idan kawar ta tafi a dawo min da ita har ta warware gaba daya, to ban gane tafiyar da yake nufi ba, karfin zamana gidan nan fa saboda yarinyar nan ne don in saka ido a kula da ita yanda ya dace, banda haka da tuni na koma gidana” Hajiya A’isha tace “Gaskiya kam, kai Junaid ka bar ta har sai taji sauki gaba daya sannan ka tsiro da batun wani tafi, yanxu ina zaka kai ta tana tsaka da jinya kamar baka da masu fada maka gaskiya, ko so kake rashin lafiyar nata ya dawo sabo?” Ajay yayi facing dinta a takaice yace “I can take care of my wife, i am capable of doing so, don haka zan iya tafiya da ita duk inda na so” Gimbiya Firdausi tace “Ohh abinda ka saba ne zaka yi ma mutane a nan din ma?” Hajja ta kalleta da sauri tace “Me ya saba? Ai da gaskiyarsa zai iya kula da ita tunda kwararren likita ne shi, sai dai kawai baza a ba kura ajiyar nama ba” Hajiya A’isha tace “To ai shine abun dubawa Hajja, dama ai duk abinda ake gudu kenan ba abu ba” Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tama wasa da veil dinta, Ajay ya kalli agogon wrist dinsa yace “Our flight is in few hours time Hajja, za mu karasa maganar ta wava” Mikewa yayi yana kallon Khaleesat yace “Let go” Gimbiya Firdausi tace “Babu inda zata je, in kai baka san abinda ya kamata ba mu mun sani don haka bazata je ko ina ba a wannan halin da take ciki….” Hajja ta kalli Gimbiya Firdausi tace “A’a baza ki ce haka ba Firdausi, Jiddah tashi ku tafi Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare” Khaleesat ta mike tsaye kanta a kasa tayi masu sallama ta bi bayan Ajay da ya nufi kofa, Ummi ta bi ta da wani irin kallon tsana, Gimbiya Firdausi sai kallon Hajja take, sai da Khaleesat suka fita sannan Hajja tace “Ai shi likita ne yasan abinda ya kamata da wanda bai kamata ba, kilan tafiya zai yi da ita wata kasar su huta, kuma haka kawai bazai tsiro tafiya babu izinin Sarki ba, don haka bamu da hurumin hanasa tafiya da matarsa duk inda yake so” Hajja na kai wa nan ta mike ta nufi hanyar bedroom dinta ta wuce ciki, Hajiya A’isha tace “Ai shikenan, dama ai gudun ya jangwalo wani aikin ne yasa muke ganin bai dace ya tafi da ita ba, amma Hajja tace ba haka ba, idan aka koma gidan jiya ai sai dai mu ce Allah ya kyauta” Bakin ciki ya sa Gimbiya Firdausi ta kasa cewa komai don da shiri suka zo ita da Shahuda, to yanxu ya zata yi da wannan abu da aka ce Shahuda ce zata kai bangarensa da hannunta ta ajiye, har fadan Sarki Ajay ya tafi ya gaida Mai martaba sannan yayi masa sallama suka bar gidan da Khaleesat a motar da zai kai su airport, Ajay ya juya yana kallonta, he just can’t wait ya amayar mata da tulin tambayoyin da yake kwana yake tashi a zuciyarsa, hannunta ya kamo yana murza hankali, ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, suka hada ido, ya jingina da motar a hankali yana matsawa kusa da ita sannan ya dora kansa aHajja na dinta ta wuce ciki, Hajiya A’isha tace “Ai shikenan, dama ai gudun ya jangwalo wani aikin ne yasa muke ganin bai dace ya tafi da ita ba, amma Hajja tace ba haka ba, idan aka koma gidan jiya ai sai dai mu ce Allah ya kyauta” Bakin ciki ya sa Gimbiya Firdausi ta kasa cewa komai don da shiri suka zo ita da Shahuda, to yanxu ya zata yi da wannan abu da aka ce Shahuda ce zata kai bangarensa da hannunta ta ajiye, har fadan Sarki Ajay ya tafi ya gaida Mai martaba sannan yayi masa sallama suka bar gidan da Khaleesat a motar da zai kai su airport, Ajay ya juya yana kallonta, he just can’t wait ya amayar mata da tulin tambayoyin da yake kwana yake tashi da su a zuciyarsa, hannunta ya kamo yana murzawa a hankali, ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, suka hada ido, ya jingina da motar a hankali yana matsawa kusa da ita sannan ya dora kansa a shoulder dinta ya lumshe ido, ita dai kallon gashin kansa kawai take babu ko kiftawa, can ta kalli gaban motar taga driver yayi concentrating a driving din da yake, lumshe ido tayi ta dora lips dinta a gashin kansa.



