*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
_daga alƙalamin Boss Bature_
E4
Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba.
Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai,
A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya,
Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaÉ—ai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya’yan mutane,
A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector É—in ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,
Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance.
Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi,
Har kiran Angel a kayi daga office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne.
Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su,
Ba’a É—auki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta Æ™araso Cikin harabar station É—in, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking É—in motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station É—in, Lokacin da ta shiga Ciki, Æ´an sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi.
Cikin shessheÆ™ar Kuka Ta kalli Æ´an sandan tana faÉ—in “Why why!why pls? Laifin me suka aika ta da za ku yanke masu irin wannan É—anyen hukuncin,”
Copral ne Ya bata amsa da cewa”Ana zargin su da sace Ƴa’Æ´an mutane suna amfani da su”
Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallon su, har bata san lokacin da tace
“Amma baka da hankali Officer, Ka iya bakin ka, Shin kuna da hujja akan a bunda kuke zargin su ne? waye ke baisan Taj da uzair ba…..”bata kai Æ™arshen maganarta ba muryar dpo ta katse ta”Muke da Æ™waƙƙwara Hujja akansu,”
Idanuwanta jawur ta É—ago tana kallon Dpo É—in, Cikin sanyin murya ta furta”where’s the evidence”?
Kafin dpo ya bata amsa sai ga Angel tana fitowa daga Office É—in shi
A ruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani,
Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel, itace Æ™waƙƙwarar Hujjar da muke da ita, Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka a kan Wannan bawan Allahn daya sace ta, Ya raba ta da iyayen ta don baÆ™in zalunci,” yakai Æ™arshen maganar Yana nuna Tajuddeen,
Hankali amatuÆ™ar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami”You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce,” muryarta a disashe takai Æ™arshen maganar,
“Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faÉ—a mana cewa shi É—in ba mahaifinta bane satarta Yayi,” acewar dpo,
Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh, Girgiza kai tashi ga yi tana kallon angel,
“Wlh officer Ƴarshi ce sharri take yi mashi, Yarinyar bata da cikakken hankali ne,”
Da buÉ—e bakin angel sai cewa”Ni Æ™arya take yi mun officer itama hada ita suke yi ae”
Curo handcuff Inspector yayi tare da cewa”You are under arrest” ya ambaci hakan yana Æ™oÆ™arin sanya mata ankwa
Ganin dagaske Kamata za su yi ne yasa tayi saurin cewa”Ku dakata kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer, akwai hotunan yarinyar da videos É—inta a wayar Mahaifinta zaku Iya bincika wayar shi ku gani.
Girgiza kai Dpo yayi”Wannan ba hujja bace duk shirin ku ne”
Jinjina kai tayi to shikenan me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test, this is the Only solution”
Jinjina kai dpo “Good idea Copral”Dpo ne ya kira sunan shi
“Yes sir” ya amsa mashi.
“Ku tafi da Mutumin da yarinyar a yi masu gwajin DNA, ku tabbatar anyi komai agaban ku,”
“Consider it done sir” Ya ambaci hakan tare da sara ma shi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell É—in, Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa Æ™warin Jikinshi, sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da Æ™afafun shi, wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayin shi ba, ko son kallon shi ma ba ta yi,
A cikin mota suka sanya su, Aneelerh kuma Ta shiga motarta tare da angel,
Bayan zuwan su asibiti, Akan idon Police men É—in akayi komai, Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita,
Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba, Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu Sun sha mamaki, Lamarin Yayi matuƙar girgizasu, Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu, dpo yafi kowa girgiza, har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zargin su da suka yi Anan aka kwantar da Tajuddeen, Sam ya fita hayyacin shi,hada drip suka sanya mashi,
Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da su ka yi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin tsakanin shi da yarinyar ba, A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗa ta da manyan malamai su cire shaiɗanun dake ajikinta, ko kuma a kaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne,
Bin shi da kallo kawai aneelerh tayi don ita tasan Wacece Angel, Lafiyarta Æ™alou itace aljanar kanta da kanta, yarinyar da ana yi mata ruÆ™iya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi Lafiyarta qalou ”
Kwananshi uku a gadon asibitin saboda jikin shi da yaƙi sauƙi, cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya da shi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki ba, da yake suna waya dashi kusan kullum ne sai sun kira su kosu su kirasu, A ƙarshe suka koma gida da yin jinya, Har hutu Aka ba Taj wurin aikinsu jin Abunda ya faru da shi, Uzair ne ya sanar dasu amma bai fada masu ainihin abunda Ya faru ba, kawai ya sanar dasu cewa Sun yi hatsarin motane, ya yi hakan ne saboda sanin halin su na ƴan jarida, yanzu ka ji labari a social media,
Bawan Allah Taj kullum yana kwance saman gado, Wanka da sallah ne kaÉ—ai suke tada shi Wani sa’in yana É—angya shi haka zai samu ya lalla6a Ya shige toilet, Ko sannu angel bata ta6a furta mashi ba sai in tana jin yunwa ne zata addabe shi wai ya tashi yayi masu girki, in ba haka ba zata je ta daura da kanta,
In ta gaya mashi hakan Jiki na rawa Yake kiran Uzair a waya Ya sanar dashi, dama Cikin Æ´an kwanakin nan mai aikin su Uzair hada Su taj take girka ma abinci duk in za ta yi, bisa umarnin Uzair É—in,
Ana haka Yau kwana Biyar kenan bai zuwa ko’ina Yana gida, Wuraren Æ™arfe biyar na marece, ya fitowa daga wanka jikin shi sanye da short baÆ™i, saman Gado ya haye bacci mai daÉ—i ya É—auke shi Yayi nisa acikin Baccin shi, Yadinga Jin Hayaniya acikin gidan jiki a mace Ya miÆ™e daga saman gadon ya nufi Æ™opar É—akin, LeÆ™awa yayi don yaga su wanene
Waro ido waje ya yi ganin mutane maƙil Cike da falon, Kasa kunne ya yi yana sauraran me suke cewa
“Allah ya jiÆ™an shi, Taj mutumin kirki halinshi na gari Ya bishi,”
Can kuma yaji wani yace”A ina ne za’ayi jana’izar ta shi”?
Wani ya ba shi amsa da cewa”Mu jira Mutanan gidan su fito sai muji,”
Shiru yayi la6e bakin Æ™opar Ya kasa fitowa, Jikin shi duk yayi sanyi, tunani ya shiga yi wai wanene Ya mutu? dama akwai wani taj ne bayan shi”? sam bai da mu da rashin ganin angel ba yasan bata wuce Gidan su Uzair.
Komawa Cikin É—akin yayi Jikin shi duk ya mutu, Wayarshi Ya É—auka da ke a jiye saman gadon Yana kunnata Ya shiga call logs, Nan yaga missed Calls sunyi É—ari uku na mutune, abun ya É—aure mashi kai,
Number uzair yayi dialing Ya danna mashi kira, Tana fara ringing uzair Ya É—aga,
“Assalamu alaikum” batare daya amsa sallamar ba Yayi saurin cewa”Uzair kana ina ne”?
On the other hand Uzair yace”Gida mana”
Cike da damuwa yace”Uzair na shiga Uku, Yanzu kawai na farka daga bacci Naga dandazon mutane a falon gidana, Na kuma taras da missed calls a wayata Ya yi É—ari uku na mutane wai meke faruwa ne”?
Muryar uzair da É—an ruÉ—i yace”Kodai angel tayi wani abu ne? bata jima da shigowa Gidan mu ba, Take sanar dani cewa Ta É—auki wayarka kana bacci, Ta sanya yatsan ka ta buÉ—e ta “tunkafin Uzair yakai Æ™arshen maganar ta shi, Taj Yayi rejecting call É—in, Ya shiga laluban wayar shi, Sai ga Notification na facebook on the top of the screen yayi appearing, Likes ya dinga gani na mutane da kuma Comment da ake tayi, A hanzarce Ya shiga facebook dinshi, a nan Yaga hoton shi dana angel ta É—auka yana bacci tayi share É—inshi a facebook, a Æ™asa ta rubuta RIJF, Su kuma Mutane da suka Ga posting din dayawan su sunyi tunanin ko matarshi ce Tayi amfani da wayar shi donta sanar masu mutuwar shi, Shine suka kwaso Æ™afafuwansu zuwa Gidan don a yi jana’ixa da su.
jiri ne Ya soma ƙoƙarin kwasar shi, lalla6awa ya yi tare da samu wuri gefen gadon ya zauna yana ambaton Allahumma Ajirni fil musibati wa aklifli khairan Minha, Na jima ina tunanin Ranar mutuwa ta, da kuma abunda zai yi silar bari na duniya ashe ƴar Cikina ce, Laifin me nayi mata ne da ta tsane ni? sai ka ce ba mahaifin ta ba,ƴar ƙarama da ita sai Iya mugunta wayyo Allah na,
sai daga bisani Ya tuna inda tasan kalmar RIJF, a tv ne wani ya rasu ana sanar da ta’aziyar shi, daga Æ™asan hoton shi aka Sanya RIJF, Rest In jannatul firdaus, shine take tambayar shi wai me yake nufi, da yake ta iya tambaya kamar yar jarida, Bai yi tunanin komai ba ya sanar da ita ma’anar hakan, Shine tayi mashi aika aika.
Kiran Uzair Ne ya shigo wayar shi, A sukwane ya É—aga Kiran a nan yake sanar da shi abunda ta aikata mashi, Uzair yasha ruwan mamaki
A ƙarshe dai,Uzair da aneerlerh ne suka shigo gidan suna bama mutune hakuri akan cewa Taj bai mutu ba, Yana a raye mistake aka samu wurin Yin posting din, ƙin tafiya sukayi Har sai da suka ga Taj da ƙafafun shi tukunna suka bar gidan suna yi mashi Allah ya kyauta, A falo suka zauna gaba ɗayan su, Uzair da Aneelerh suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Taj kuma yana zaune a saman 2 seater,fuskarshi duk a hautsine,
“Yanzu menene mafita”? taj ne ya yi maganar yana kallonsu,
“Lamarin Angel Yafi Æ™arfin mutun sai dai Allah, ae ni tun ranar da aka kira malami yayi mata ruÆ™iya ta sace takalman shi, tun daga nan Jikina Yayi sanyi,” acewar Uxair,
“Benazir ta tafi tabarmun bala’e” tamkar taj zai fashe da kuka Yayi maganar,.
“Me zai hana ka jaraba Bugunta”? a É—an firgice ya kalli Aneelerh da tayi maganar,
Cigaba da magana tayi”Idan har ba za ka iya bugunta ba shawarar da zan bada shine, Kasan mafi a kasarin Æ™ananun yara akwai abunda suke tsoro, Ni ina ganin a jaraba samo Mage ko kare ko kuma Æ™adangare, Idan aka samu wanda take tsoro acikinsu, Sai adinga Yi mata Baraza na da shi, Koya kuka Gani”? tayi tambayar tana kallon Taj, wanda ya yi zugudum yana kallonta, yarinyar da take kallon Zombie tsakar dare, Taya zata Ji tsoron waÉ—annan halittun, Acikin zuciyarshi ne yayi maganar,
Jinjina kai Uxair yayi”Good idea idan na fita Yanzu xansa Almajirai su É—auko mun Æ™adangare a fara jarabata dashi, inyaso gobe sai a kawo karen Nasan dole asamu wanda take matuÆ™ar tsoro acikinsu,”
“Allah yasa dana fi kowa Farin Ciki” acewar Taj,
Sun jima suna tattaunawa kafin Su ka yi ma shi Sallama, Atare suka bar gidan,
Duk dabbobin da aka kawo gidan don angel ta tsorata amma abun ya ba su mamaki bata tsoron su, illa ma ita dabbar da aka kawo taji tsoronta, yarinyar ta zarce tunanin mai tunanin ga karfi Allah Ya yi mata, Ranar da taj yasa aka kawo mage agidan Sai da ya yi dana sani,
A lokacin Yana kwance yana bacci Ya barta a falo ita da magen da ta sanya ma suna Chu chu, suka soma kokawa tana kiciniyar kamata, magen ta watsa aguje tana kuka, tabi bayanta da gudu suka shiga zagaye palourn, Sune har cikin kitchen, Magen ta haye saman Dish racks, inda Jerin Plates na tangaran suke, Angel takai hannu da niyar ta cafkota aikuwa gaba ɗaya Ta 6aro da Kwanukan tangaran din, Suka tarwatse kasa duk suka faffashe, Tsalle magen tayi ta ruƙo jikin Cupboard wasu hadaddun Glass Cups ne dana tangaran, Ruƙo ƙafar magen Angel ta yi, Gaba ɗaya Cups din suka Rikito ƙasa duk suka tarwatse, Kubce mata magen tayi da gudu ta sauko ta nufi Store da kopar shigar shi ke anan cikin kitchen ɗin, Aguje angel tabi bayanta, Suka shiga yin yar tseral, Wasu jerin Crates din kwai Ne Magen Ta hau saman su, A ƙalla sunyi crates goma sha biyu, Gaba ɗaya suka kife kasa eggs ɗin suka faffashe, hayewa sama magen ta yi inda aka jera Sunƙi sunƙin bready, Ganin tsawonta bai kaiwa yasa ta janyo jarkar Manja, Ta haye samanta Ta cakumo wuyan magen, jarkar da ta hau saman kanta ce ta Karkace da ita da magen Da jarkar man, Da Ledojin breadin sunkutukum Suka Kife ƙasa, Nan take murfin jarkar ya buɗe Manjan Ya shiga gangarowa ƙasa, bari in takaice maku zance sai da Angel ta canzama Kitchen din halittarshi, tamkar Bola, uk Ta hargitsa komai ba,
Da ta ga Ta yi 6arna sosai, saita Saki Cucu, Ta ruga da gudu ta nufi gate, A lokacin baba mai gadi Yana Cikin yin alwalar sallar magrib, Ya hangota ta nufo shi,
Tunkafin ta Æ™araso Take nuna mashi gate ya buÉ—e mata, Sanin Tsiwarta yasa Ya buÉ—e mata Æ™opar jikin gate É—in ta fuce, Sai gidansu Aneerlerh lokacin da ta shiga Gidan, A bedroom ta samu aneerlerh ta kabbara Sallah, Saman Gadonsu ta haye Taja bargo ta kuÉ—unÉ—u ne, Bayan aneelerh ta kammala Yin sallar,t ana daga zaune saman darduma ta kalleta”Angel Lafiyar ki kuwa”
Kasa Æ™asa da murya tace”Zazza6i nake yi”
“kin sha magani”
“Eh nasha, daddy ne yace inzo wurin ki kiyi mun wanka,i n ya dawo daga masallaci zaizo ya dauke ni”
Mikewa aneerlah tayi, bayan ta cire hijabin ta tura a wardrobe,
“Tashi muje nayi maki wankan”
Yaye bargon tayi ta sauko daga saman Gadon, rigar jikinta duk ta cukuikuye, hada manjan daya gogu agaban rigar,
“A haka kika hau mun gadona? Ina kika samu manja ajikinki”
Ashagwa6e tace” nace maki bana lafiya, Ni bana iya magana sosai”
Sam aneelerh ba ta yarda da ita ba ta ƙyale ta ne kawai,
Within minutes ta yo mata wankan, suka fito daga cikin toilet, ta shafe ma ta jikinta da mai, canza mata kaya tayi, dama Saboda Ita ta sayi kayan Yara dai dai Size dinta, saboda sun ɗauke ta tamkar ɗiyarsu, pink gown ta sanya mata,ta kuma ɗaure mata sumar kanta da ribbom,ba ƙaramin kyau tayi ba, hada light make up aneelerh tayi mata,
“Aunty aneelerh,Z an koma saman gadon in kwanta, dan Allah ki hadamun fura, A sanya kwakwa da yogurt aciki da Æ™anÆ™ara”
Jinjina kai aneerlah tayi fuskarta dauke da murmushi tace”Okey My daughter in law, je ki kwanta,”da gudu taje ta haye saman gadon,
Bayan Aneerlerh ta hado mata furar a cikin Cup ta kawo mata Nan ta zauna tasha ta ƙoshi, kafin ta koma ta kwanta tuni bacci yayi awon gaba da ita,
A 6angaren Taj kuwa, Lokacin daya tashi toilet ya shiga, ya dauro alwala ya dawo Cikin É—akin Ya dauko Jallabiya Cikin Closet din shi Ya zura ajikinshi, Fitowa ya yi daga É—akin yana ta faman sauri Ya fuce zuwa masallaci,
Bai tashi sanin aika aikar da Angel tayi mashi ba, Sai daya Dawo daga masallaci, wata irin yunwa ta farmasa, ba arxiÆ™i Ya nufi kitchen shigar shi keda Wuya Tun abakin Æ™opar yaci karo da Fasassun kwanukan da angel ta 6aro, A razane ya dago yana kallon cikin kitchen É—in, har wani haya ki yake ganin cikin idon shi saboda tsabar 6acin rai, ashe bai ga komai ba sai daya Shiga Cikin store, Hannu ya É—aura akai yana ambaton”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un! Nashiga Uku! Na bani!
Ya Allah laifin me nayi aka jarrabceni da Angel? wani zunubi na aikata, dafe baki yayi da sauri jin sabon da ya yi yana mai fadin astagfurullah…..” yana cikin sambatun nan yaji kukan Mage, Aikuwa a harzuÆ™e ya juya ya kalli magen dake a bakin kopar store É—in, ShaÆ™o wuyanta yayi tare da jijjigata Yace”Ke da ubanwa ku ka yi wannan”?
Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete
Mu haÉ—u a next page, saoda wadanda su ka ce bai buÉ—e ba yasa na rage yawan page É—in, kar a manta da comment like and share
Naji dadin comment dinku, Amma in kuka ninka zaifi bada Citta, ni ina amfani da like da comment yana karfafa mun gwiwa, that’s why nake cewa ku daure kuna yi, idan kuna so ku taddo yan whatsapp, don sun wuce ku,