Hausa novels

Abban Sojoji Page 59 Book 2 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Page 59 Book 2

The Father Of Soldier

Written By Boss Bature

Cigaba da magana yayi”major yau ni da kaina nayi attempting rape,kuma ba kowa nayi yunkurin aikata ma hakan ba face hossana…..’

 

Jin abunda omar yace yasa major cikin tashin hankali yace”Subhanallahi!!yalla6ai garin yaya hakan ya faru!nidai nasan cewa bayin kanka bane,na yarda dakai sosai,Ni shaidane akanka yalla6ai,kai da kanka kake hukunta masu aikatawa,kana ɗaya daga cikin mutanan dake daraja ƴa mace,ba zaka ta6a yin hakan abisa son ranka ba,”

“Major naji haushi sosai,zuciyata batamun daɗi,duk nabi na tsani kaina,nayi abun kunyar da bazan ta6a mantawa ba,indama na godema Allah yaran basu shaidani ba,da idanunsu da ace sun gane ni ne da nasan cewa duk wani girma na da suke gani zai zube ne,kuma zasu fara tunanin cewa ba don Allah na taimaki rayuwarsu ba….”

tsananin tausayinshi ne ya kama major,da yana da halin da zai cire damuwar dake acikin zuciyar ogan nashi da tuni yayi exchanging heart ɗinsu,ba don komai ba sai don ya tsani yaga marshal acikin wani hali na ƙunci,

daƙyar major ya kwantar mashi da hankalinshi ta hanyar yi mashi tausasan kalamai masu daɗin gaske har sai daya ga ya shiga natsuwarshi sosai sannan ya tashi motar suka nufi gida,

kuka sosai jahad keyi ganin tana ta jaraba kiran layin Omar amma ba’a ɗagawa,a ƙarshe ma da ta ƙara kira sai ta samu wayar a switch off,jiki asanyaye ta mayar da telephone din ta ajiye asaman table ɗin,

dafe kanta tayi saboda wani irin raɗaɗi da taji yana yi mata,gaza tsayawa tayi da ƙafafunta nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume,

 

Tashin hankalin da ba’a samashi date!a can 6angaren sehrish ta sume,anan 6angaren kuma hossana da jahad sun sume,ko mai zai biyo baya?

 

Wuraren ƙarfe 1:30 na dare,Ayaan na kwance cikin kayan baccinsa,yaji hannun mutun acikin wandonshi,a firgice ya farka tare da ware idanunshi akan wanda ke lalubar jikin nashi,ganin jahan asaman jikinshi yasa yayi hanzarin yin wurgi dashi gefe guda ya tashi zaune rai a6ace yace”Jahan!banason wannan wasan!karka kuskura ka ƙara ta6a jikina in ba……’bai ƙarasa maganar ba saboda haɗe bakinsu da jahan yayi wuri guda yashiga ƙoƙarin zura harshen shi acikin bakinsa,

Hankali tashe Ayaan ya rurruƙe shi yana kiciniyar kwace kanshi daga hannun jahan amma abun yaci tura,kamar wani zombie haka ya koma mashi,

Muryarshi har shaƙewa takeyi wurin cewa”Ja…ja..jahan!ka rabu dani!wai meyake damunka ne!baka da hankaline kasan me kake ƙoƙarin yi mun ne,yayi maganar tare da janye jahan daga jikinshi yana kallon shi,

Wata irin zuface ke gangarowa daga cikin sumar kanshi saboda tsabar jarabar da yake ji,

A kasalance yace”ayaan kadaina mun wasan nan,kasan fa abunda nake buƙata awurinka,ka bani haɗin kai kamar yarda muka saba,baka ji yadda nake ji ba ajikina….’Ya ƙarasa maganar yana faman lumshe idanunshi,

Ayaan kuwa kallonshi yake yi gwanin ban tsoro,lokaci guda kuma ya tuna komai  yace”Jahan kayi haƙuri bazan iya ba,na ƙyamaci abun acikin zuciyata,ya fita raina gaba ɗaya,bazan iya cigaba da aikata wannan mummunan zunubin ba,bayan Allah ya yaye mun,idan harna biye maka muka aikata hakan,hukunci zai hau kaina,Allah bazai……’kafin Ayaan ya ƙarasa maganar tuni Jahan yayi kukan kura ya afka mashi,don bazai juri sauraron kalamanshi ba,saboda a ƙagare yake daya kawar da muguwar sha’awar data taso mashi mai tare da wani irin raɗaɗi,

Dambe suka shiga yi atsakaninsu,jahan na ƙoƙarin zame ma Ayaan kayan jikinshi,yayin da Ayaan ke ƙoƙarin kufcewa daga hannunshi ya gudu,wani irin ƙarfi jahan ke ji gaba daya ya zauce ya fara fita hayyacinshi burinshi ya biya mashi buƙatarshi,kafin wani lokaci jahan ya yayyaga ma Ayaan rigar jikinshi,yayi mata kaca kaca,ruƙo wandon jikinshi yayi tare da janshi ya zame gaba ɗaya,ya rage daga shi sai short ajinshi,a lokacin ya tattara dukkan wani ƙarfin shi yayi wurgi da jahan gefe guda saman gadon,sannan da gudun gaske ayaan ya sauko daga saman gadon ya faɗa cikin toilet ɗinsu tare da rufe ƙopar,yana faman sauke ajiyar zuciya,a bakin kopar ya tsaya tare da kasa kunne yana sauraran gurnanin da Jahan keyi,

tsigar jikinshi ce ta soma tashi tsaitsaiye,nan take idanunshi sukayi wani irin ja tamkar garwashin wuta,saukar bulali ya dinga ji ta ko’ina abayanshi nan take yabi ya gigice ya dinga sakin ihu yana kuka mai cin ran,

Runtse ido Ayaan yayi wani irin tausayin shi ne ya kama shi,saboda yasan irin halin da suke shiga aduk lokacin da basu kusanci junansu ba,tabbas Jahan bazai rayu ba muddin bai bashi haɗin kai ba,fashewa da kuka Ayaan yayi tare da sulalewa ya zukunna abakin ƙopar toilet ɗin yana faman shassheƙar kuka,

Yana jiyo yarda jahan ke ta faman ihu yana kuka,akan kunnanshi yaji sautin faɗowar jahan daga saman gadon,ta hanyar sautin da yaji timmmmmm!

rarrafowa jahan yayi daƙyar yake jan jikinshi har ya isa bakin ƙopar toilet din,muryarshi na kerma yace”Ayaan yau kai da kanka kake guduna!bayan kasan irin halin da muke shiga aduk lokacin da bamu aikata hakan atsakanin junan mu ba!so kake na mutu ko”? daƙyar sautin maganarshi ke fita,maƙoshin shi tuni ya jima da bushewa ƙamas,numfashinshi daƙyar yake fita,

Cikin muryar kuka Ayaan yace “am really sorry jahan,ina mai matukar takaicin gaza taimakonka a wannan lokacin,zanyi kuka sosai in na rasa ka jahan,bani da tamkarka aduniyar nan,ina tsananin kaunarka sosai ɗan uwana,kayi haƙuri ka yafe mun……..”kasa ƙarasar maganar yayi saboda kukan daya ciyoshi,

tamkar zaiyi hauka haka ya dinga ji,gaba daya rayuwarshi tashiga cikin ƙunci,idonshi ya makance,makoshin shi ya bushe,ya rasa duk wani kuzarin jikinshi,lokaci guda ya zama zautacce yabi ya burkice sai faman magiya yake yi ma Ayaan ya taimaka ma rayuwarshi amma ina Ayaan sam yaƙi buɗewa bama alamar zai buɗe,

Wani irin sauti Jahan ya shiga fitarwa tamkar ranshi ne ke fita,hakan ba ƙaramin gigita Ayaan yayi ba,muryar jahan yaji ƙasa ƙasa yana cewa”Ayaan maƙoshina ya bushe!mutuwa zanyi ka taimakamin da ruwa insha,”agalabaice yake maganar,

Da hanzarin gaske Ayaan ya buɗe ƙopar ɗakin,anan yayi arba da Jahan baje ƙasa rai hannun Allah jikinshi sai karkarwa yake,wasu irin sahun bulali ne a jikinshi ta ko’ina ga shaidarsu nan asaman farar fatar jikinshi,dama babu kaya ajikinshi iya gajeran wando ne ya bari,

ɗaga ƙafa ayaan yayi zaije ya ɗauko mashi ruwan,kamar daga sama yaji jahan ya ruƙo kafarshi da ƙarfin gaske nan take ya kife ƙasa timmmm,jan jiki Jahan yayi tare da hayewa saman jikin Ayaan ya ƙankame shi ruƙo bana wasa ba,sannan ya shiga biyan buƙatar shi,wa’iyazubillah!wannan wata irin masifa ce!

 

Gaba ɗaya jahan ya gama kashe mashi jikinshi,ko hannunshi bai iya ɗagawa,babban abunda yake tsoro kada wani ya faɗo ya same su acikin wannan yanayin da suke,

kiciniyar kwace kanshi ya shiga yi da iya ƙarfinshi na karshe amma hakan ya gagara,a ƙarshe daya rasa yadda zaiyi saiya daddage ya garza ma jahan cizo asaman ƙirjinshi,ko gizau baiyi ba,

wani irin juyi Ayaan yayi anan ya samu nasarar hankaɗe jahan yayi gefe guda ƙasa,shi kuma ya tashi cikin sauri yana gyara short ɗin jikinshi,

Har yasa ƙafa zai bar ɗakin,yaji gabanshi yayi wani irin mugun bugu,cikin sauri ya juya tare da kallon jahan da idanunshi ke kallon sama,kwata kwata baya motsi komai nashi ya tsaya cak da yin aiki,waro ido waje yayi da hanzarin gaske ya koma wurinshi tare da zubewa saman guiwar ƙafafunshi yana ambaton sunanshi hankali a matukar tashe!

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!Jahan!jahan!don Allah kayi magana!ɗan uwana kada ka mutu ka barni!bana fata ace ni nayi silar barinka duniya!na cuce ka jahan nagaza cetonka!ka yafe mun ba laifina bane!”

Kuka sosai Ayaan keyi yana jijjiga jikin Jahan,bai da wata mafita a halin yanzu,ji yake tamkar ya watsa aguje yaje ya sanar ma su Abbansu halin da ake ciki,amma fargabar kada ace jahan ba mutuwa yayi ba,in har hakan ta faru to tabbas zai iya farkawa agabansu ya cakume shi ya shiga ƙoƙarin biyan bukatar shi agabansu,tunda baya acikin hayyacinshi,

Yasha kuka sosai kamar kamar me,a ƙarshe ya yanke shawarar zuwa ya ɗauko ruwa don ya yayyafa mashi ajikinshi ya ga ko zai farka,

A hanzarce ya miƙe tare da kama hanya ya fuce daga cikin bedroom din,

Sauri yake yi tamkar zai tashi sama aranshi sai addu’a yake yi Allah yasa jahan ba mutuwa yayi ba,

 

Fitar shi ke da wuya daga cikin bedroom din nasu,Haroon ya faɗo cikin ɗakin afusace don yayi masu magana akan Money bag ɗinsa da yake zargin su suka ɗauke shi,koda yayi arba da jahan kwance aƙasa baya motsi,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,ta6e baki yayi tare da shigewa ciki,ya zukunna adaidai inda jahan ɗin yake kwance,yakai hannu tare da shafa ƙirjinshi,da yake shu’umine,nan take ya gane awane hali jahan yake,

sunnar da kanshi yayi tare da haɗe bakinshi wuri ɗaya dana jahan,zura tongue ɗinshi yayi acikin bakin jahan,aikuwa awani irin yanayi Jahan yayi motsi alamar yaji abunda yakeso,batare da 6ata lokaci ba Haroon ya shiga biya mashi buƙatar shi,

 

Ayaan na ƙarasawa wurin fridge ɗin yasa hannu tare da buɗewa cikin sauri,hannu yakai cikin jerin bottles water ɗin dake a jere cikin frigde ɗin,har zai ɗauki robar ruwan swan idon shi ya sauka akan Robar ruwan addu’ar nan da junaid ya ajiye ta sehrish,bakomai ne yaja hankalin shi akan robar ba,face rubutun Larabcin dake rubuce ajikinta,tunda akeyi masu order na abunsha,ba’a ta6a kawo masu kalar robar ruwan nan ba,mai rubutun labarabci ajikinta,zubama robar ido yayi yana kallonta nan take abunda ya faru ɗazu ya faɗo mashi aranshi,wasiwasi Ayaan yashiga yi acikin ranshi yana cewa”wannan roban ruwan kamar itace na ɗauka ɗazu nasha!kuma tunda nasha ta komai nawa ya canza,tabbas ina tunanin cewa tana tattare da wani abu ajikinta,amma kuma waye ya ajiyeta indai haka ne?don ina da tabbacin cewa ba’a kawo mana kalar wannan bottle water ɗin acikin gidan mu!bari na jaraba kaima Jahan ya sha,tanan zan gane abunda ke tattare da robar ruwan nan!”

Yana ƙarasa zancen zucin nashi batare da 6ata lokaci ba,ya sungumi robar ruwan a hannunshi,bayan ya rufe frigde ɗin,da saurin gaske ya wuce part ɗinsu,

Yana gab da shiga bedroom ɗin nasu,ya dinga jin wani irin gurnani mara daɗin ji,a wani irin tsorace ya afka cikin ɗakin,waro idonshi waje yayi saboda tsabar 6acin rai baisan sa’adda yayi wurgi da Robar ruwan dake a hannunshi ba,nan take ta faɗi ƙasa tana gangarawa murfinta ya cire,ruwan cikinta ya kwarare ƙasa gaba ɗaya,

A fusace ya ƙarasa tare da damƙar rigar haroon da iya ƙarfin shi na ƙarshe yayi wurgi dashi gefe guda,ɗagowa haroon yayi yana kallon Ayaan da idanunshi waɗanda suka canza launi izuwa jawur dasu,sai faman lashe bakinshi yake kamar wani tsohon maye,

Rai a6ace ayaan yace”wai kai wani irin daƙiƙin mutum ne dabba!kuma jahili wanda baisan ciwon kanshi ba!mugu azzalumi kawai,banta6a ganin fasiƙin mutum irinka ba!wanda baya tsoran Allah!”ran Ayaan ba ƙaramin 6aci yayi ba,yana magana hawaye na gangarowa daga idanunshi masu zafin gaske,

Duk a tunaninshi haroon zai ji haushin kalamanshi,amma abun mamaki fuskarshi ɗauke da wannan shu’umin murmushin nashi yace”Kwantar da hankalin ka mana!nifa ceton rai nike,duk irin son da kake ma Jahan ka gaza taimakon shi,kana ji kana gani zai mutu,ni kuma bazan so haka ba saboda inason ɗan uwana,shiyasa nayi hakan don na cetoshi daka halaka……’

Tunkan ya ƙarasa maganar Ayaan ya daka mashi tsawa tare da cewa”Karka kuskura ka ƙara ambaton sunan jahan a matsayin ɗan uwanka!kai ba jinin mu bane,mutun mai halin dabbobi irinka bazai ta6a zama jinin mu ba,yanzu bana doubting akan haka,Haruna kai ba ɗan uwanmu bane!ka wulaƙanta rayuwarmu,Allah ba zai ta6a barin ka ba,ƙarshen ka bazai yi kyau ba haroon!tun wuri ina baka shawarar ka tattara kayanka kabar gidan nan tun kafin lokaci ya ƙure maka!!!!”

fashewa da dariya haroon yayi,a yayin da yake miƙewa tsaye daga zaunen da yake a ƙasa,takawa yayi izuwa wurin da Ayaan yake sannan yace”naji duk bayananka akaina,kuma naji shawarar da ka bani,inaso ka sani cewa ko kaɗan banji tsoro akan kalaman da kayimun ba,ka ajiye wannan zamuyi magana akanshi,abun da ya kawoni ɗakinku shine Jakar kuɗin Da kuka kaimun ban ganta ba,an ɗauke ta daga ɗakina,kuma ba kowa nake zargi ba face ku,saboda ku kaɗae kukasan da zancen kuɗin,bayan ku babu wani da yasan da maganar!!ina jakar kuɗina take!!”

takaici ne yasa Ayaan kasa yin magana tabbas da ace yana da halin kawar da haroon da tuni yakai shi inda ya dace,

Cike da takaici Ayaan yace”maganar ɗauke jakar kuɗinka sam bata shafe mu ba,don haka tun wuri ka nemi wanda ya ɗauke maka kuɗinka!idan ma kanaso kayi amfani da wannan damar ne don kayi mana wayau ka ƙara samun wasu kuɗin awurinmu to inaso ka sani cewa ko sisi bazasu ƙara fitowa a wurin mu ba!bazamu baka ba!kaje kayi duk abunda kaga dama,’

Wani irin huci haroon ya runƙa fitarwa yana kallonshi yace”Kadaina yi mun magana A gadarance!taƙamarka kun goge videon dake a wurina to inaso ka sani cewa akwai wani videon a wurina!ni ba shashasha bane kamar yarda kukayi tunani!dama sai da raina ya bani cewa akwai wata ƙullalliyar da kuka shiryamun,don haka muddin baku dawomun da jakar kuɗina ba saina fallasa ku Uban kowa yaga abunda kuke aikata……..’bai ƙarasa maganar ba saboda Ayaan daya kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya,nan take kan haroon ya ɗaure yashiga mamakin dalilin dariyar ta Ayaan,

Sosai Ayaan yake 6a66aka dariya kamar kamar me,hada dafe cikinshi,tashin hankalin da ba’a sama shi date,kwatsam yake zuwa,

duk wannan surutan da suke yi Jahan yana kwance a ƙasa sai faman juyi yakeyi saboda raɗaɗin da cikinshi ke yi mashi,sam baya acikin hayyacinshi,saboda he isn’t satisfied,

“Me kake yi ma dariya”?haroon ya jefa mashi tambaya,

tsagaitawa da yin dariyar yayi yana Girgiza kai yace”Haroon ka gama yawo!wlh ka mutu!kai baka da tunani ne,bazan baka satar amsa ba,amma kaje kayi tunanin waye ya ɗauki jakar kuɗin nan!taya akai wani yasan da zancen jakar kuɗin nan har ya bi ɗakinka ya ɗauke ta!junaid kaɗae ne ya shigo cikin bedroom ɗinka a lokacin da muke tattaunawa,kuma kasan cewa junaid baya acikin sense dinshi ya shigo,koda ace yana cikin hayyacinshi bazai iya ɗaukar maka jakar kuɗin nan ba!to waye ya ɗauki jakar kuɗin?mu dai bamu bane!”?

shiru haroon yayi yana kallonshi gaba ɗaya ayaan ya burkita mashi tunaninshi,hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa,bai ƙara tanka ma Ayaan ba,cikin sauri ya kama hanya tare da fucewa daga ɗakin,

Ajiyar zuciya Ayaan ya sauke,jin hannun mutum a ƙafarshi yasa yayi hanzarin kai idanunshi ƙasa yana kallon Jahan dake ta faman fitar da numfashi sama sama,hankali tashe ya shiga neman robar ruwan daya shigo da ita acikin ɗakin,can ya hangota ta gangara wurin shoe rack ɗinsu,murfinta ya cire ga ruwan ciki ya malale ƙasa,dafe kansa yayi da hannunshi na hagu cike da takaicin ruwan daya zube,

ƙokari jahan yake yayi mashi magana akan ya kira mashi Abbanshi karya mutu baisa shi a idanunshi ba,amma kwata kwata sounds ɗin bai fitowa abakinshi,ko idonshi bai iya budewa bare ya iya yin magana,gaba ɗaya Ayaan ya rasa yarda zaiyi,kanshi ya gama kwancewa,kamar yayi hauka haka yake ji,yana cikin wannan yanayin dubara tazo mashi,juyawa ya kuma yi yana kallon roban ruwan,Ruwan ya malale gaba ɗaya kasa ya tattaru a wuri guda,

Da saurin gaske ya ƙarasa wurin robar ruwan,tare da zubewa saman guiwowinshi,hannu yakai tare da ɗago da robar ruwan ya zaunar da ita ta tsaya tsaye,sannan cikin sauri ya sanya tafukan hannayenshi tare da kwalfo ruwan acikinsu,ya dinga zubasu acikin robar,yana ɗebowa wani na zubewa ahaka ya samu ya ɗan tara kaɗan wanda bai wuce ayi mashi kur6a uku ba ya ƙare,

ɗaukar robar ruwan yayi da sauri ya koma wurin jahan tare da zuƙunnawa agabansa,sannan yasa hannunshi na dama asaman lips ɗin jahan yana ƙoƙarin buɗe bakinshi,ya rufe bakin gam,hakan yasa Ayaan ya gaza samun damar buɗe mouth din nasa,

tsoranshi kar ace jahan ya mutu,saboda yayi delaying wurin kawo mashi taimakon gaggawa,

“Jahan pls,ka buɗe nasamo maka ruwan ka sha!banaso na rasaka ɗan uwana,”muryar shi tamkar zaiyi kuka haka ya dinga rokon shi akan ya buɗe bakin nashi ya sanya mashi ruwan,amma ko motsi wannan baiyi ba,

hannunshi har kerma yakeyi wurin ɗaga robar ruwan ya kaita saitin idanunshi yana duba rubutun dake ajikinta,larabci ne kuma shi baijin harshen larabci,balle ya gane me aka rubuta ajikinta,

Ganin zai rasa ɗan uwansa yasa ya ajiye robar ruwan ƙasa,sannan ya daddage da iya ƙarfinshi na ƙarshe ya sanya dukkan hannayenshi biyu ya shiga ƙoƙarin buɗe bakin Jahan,cikin sa’a bakin ya ɗan saki,da sauri Ayaan ya ɗauko robar ruwan tare da kafata a bakin Jahan nan take ruwan ya dinga shiga acikin bakinshi daƙyar daƙyar,wani na shiga wani na fita,ahaka yasamu ya bashi,bayan ya kammala yayi wurgi da robar ruwan gefe guda,sannan ya zauna tare da zabga tagumi yana jiran ganin sakamakon da zai biyo baya,hawaye sai shararo mashi suke a idanunshi,aranshi yana cewa”idan na rasa jahan bansan ya zanyi da rayuwata ba,nima zan bishi ne kawai,”

Yayi maganar tare da runtse idanunshi yana matse hawayen dake fita daga eyes ɗinshi,

Kafin Ayaan ya ankare,wannan baƙin hayakin ya soma kurɗaɗowa ta cikin ƙofofin hancin jahan,yarda kasan an koro shi daga cikinsa,haka ya dinga fitowa kafin kiftawar ido,hayaƙin yayi disappearing gaba ɗaya,tamkar bai ta6a existing ba,

Fitarsa ke da wuya,zufa ta soma tsastsafowa a jikin jahan,kamar an watsa mashi ruwa ajikinshi,haka zufar tashiga feso mashi,a hankali bakinsa ya buɗe ya shiga ambaton”La’ila ha’illallah!

A wani irin firgice Ayaan ya ware idanunshi sai lokacin ya kalli jahan dake kwance zufa ta gama wanke mashi jikinshi,wani irin farin ciki ne ya cika Ayaan la66ansa har rawa suke yi wurin ambaton sunan shi”ja..jahan”

Amsa mashi yayi da”Na’am,”

“Alhamdulillah!Alhamdulillah!Allah na gode maka!” Ayaan ne ke faɗin hakan yayin da yakai hannunshi yana tatta6a fuskar jahan dake ƙoƙarin buɗe idanunshi,

Tunani yazo ma Ayaan aranshi yace tabbas Ruwan cikin robar can ba normal ruwa bane da suka saba sha,akwai wani abu atattare dashi,tun da gashi Yaba jahan yasha kuma ya tashi da irin yanayin daya tashi dashi ɗazu da rana daya sha ruwan,ya tashi yana zufa kuma shima Jahan gashi zufar ce ke fita,hakan na nufin cewa shima Jahan ya warke kenan,

Ƙarasa tunanin nashi yayi tare da kai goshinsa ƙasa yayi sujjada yana ma Allah godiya,🥰

Bayan Jahan ya gama farfaɗowa,Ayaan ya taimaka mashi wurin kaishi toilet yayi wanka,nan take yaji wata irin natsuwa ajikin shi,basu 6ata lokaci ba wurin hayewa saman gadonsu,tare da lullu6ewa da bargo saboda baccin da kowannansu ke ji,yau gaba dayansu sunyi bacci cike da kwanciyar hankali,kuma Ayaan Yaci alwashin sai yayi investigation akan wannan robar ruwan da suka sha,

 

(Banji daɗi da ruwan addu’ar nan ya zube ba,wlh nima ina buƙatar shi don nasha)

 

Yanayi mara daɗi,a daren ranar Omar ya kwana yana kukan zuciya saboda abunda yayi ƙoƙarin aikata ma Hosana, ya kwana da tunanin wane hali suke aciki?sunyi bacci kuwa?baida amsar tambayoyin shi dole sai inya gansu,gashi baya jin zai iya takawa yaje dubasu saboda fargabar karsu gane cewa shine yayi masu wannan abun kunyar,matsananciyar damuwar daya sa ma ranshi ne da tunane-tunane ya haifar mashi da wani irin severe headache na 6arin kai,yaji jiki adaren nan har magani yasha amma bai sauka ba,a haka ya kwana yana juyi asaman gadonsa,

Adaren ranar nan dai abubuwa dayawa sun faru masu daɗi da marasa daɗin ji,dama haka rayuwa take ba kullum ake jin daɗin ta ba,idan yau anyi farin ciki,gobe zai iya kasancewa baƙin cikine,idan yau anyi dariya gobe zai iya kasancewa kuka ne,haka rayuwar ke tafiya babu wani yanayi da yake kasancewa permanently,Allah yasa mu dace,yasa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu,kuma ya kare mu daga aikata aikin danasani,wasu sun ɗauki rayuwar duniya wani abu,da har suka ɗauke ta da zafi suna aikata abunda suka ga dama,sun manta da cewa acikin seconds za’a iya zare ransu su bar duniyar gaba ɗaya suje su fuskanci abunda suka shuka,duka nawa ne jin daɗin duniyar?basa tuna donme aka halicce su,ta wace ƙopa suka faɗo duniyar nan,taya zasu koma ga mahaliccinsu?daga kai fa sai likkafaninka za’a binne ka cikin ƙabarinka,sai kuma halinka daka je dashi,na gari ne kona banza,😢Allah yasa mu cika da kyau da imani🙏

 

Wuraren sallar Asuba Sgr ya farka daga dogon baccin daya ɗauke shi,a hankali ya buɗe eyes ɗinshi,yayin da bakinsa ke ambaton addu’ar tashi daga bacci,a kasalance ya miƙe daga kwancen da yake saman doguwar kujerar,mamaki ne ya kama shi ganinshi kwance a palour ɗinsa yana bacci instead of saman gadon shi,ya jima yana mamakin yarda bacci yayi awon gaba da shi adaren jiyan nan,sauko da ƙafafunsa yayi ƙasa,idanunshi suka sauka akan tray ɗin da sehrish ta kawo mashi na dinner ɗinsa da baici ba jiya,tsayawa yayi yana ƙoƙarin tuna abunda ya faru adaren jiya,yunƙurawa yayi tare da tashi tsaye daga saman sofa din ya soma takawa walking slowly,jin sul6in wani abu a ƙasan tafin kafarshi yasa shi yin saurin kai idonshi wurin yana kallo,mamaki ne ya kama shi ganin Mayafin yarinyar nan yashe a kasa,yasan cewa shiya cire mata mayafin amma abunda ya ɗaure mashi kai zaman me gyalenta keyi acikin part ɗinsa?

russunawa yayi tare da kai hannunshi ya ruƙo gyalen tare da ɗagowa dashi yana kallon shi,sai lokacin ya tuna abunda ya faru jiya tsakanin shi da ita,na commanding ɗinta da yayi akan tayi tsallen kwaɗi,to ina yarinyar take,tambayar daya jefa ma kanshi kenan,

Cikin sauri ya zagayo ta bayan sofas ɗin tunkan ya ƙarasa ya hangi yarinyar kwance magashiyyan a sume bata motsi,tasha wahala sosai sam baiyi tunanin cewa zata cigaba da yin frog jump ɗin ba,yasan ba komai ne yaja hakan ba face tsananin tsoronshi da take ji,shiyasa bata yi tunanin ta tafi ba,tunda taga bacci yayi awon gaba da shi,

A hankali ya ƙarasa takawa inda take sannan yaɗan zuƙunna agabanta yana kallon sumar kanta data rufe mata fuskarta,hannu yasa tare da ruƙo gashin kan nata,ya janye mata shi daga saman fuskarta ixuwa gefe guda,

Zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yayi yana kallon yarda tayi jaga jaga da hawaye duk ta yamutse saboda kukan da tasha,idonta sun kumbura,haka la66anta ma sunyi suntum dasu,tsananin tausayinta ne ya kama shi,baiji daɗin baccin daya ɗauke shi ba,da baibari tasha wahalar nan ba,ba da nufin ya cutar da ita yayi hakan ba,kawai yaso ya ɗan hukuntata ne donta kiyaye shi sosai,

miƙewa yayi tare da nufar wurin fridge ɗinshi,ya buɗe ya ɗaukko bottle water daga ciki mai sanyi,sannan ya dawo inda sehrish take ya cire murfin tare da ɗebo ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi a fuskarta,ruwan na sauka asaman fuskarta,taja dogon numfashi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,a hankali tashiga mutsu mutsu zata buɗe idanunta,

“Get up” yace,jin muryarshi yasa sehrish ware idanunta akan sgr dake zuƙunne agabanta,jikinta har kerma yake yi wurin yunƙurawa tare da tashi daga kwancen da take ta zauna,tun kafin taji me zaice ta shiga bashi haƙuri tana cewa”dan Allah ka yafe mun babban yaya,bazan ƙara maimaita kuskuran da nayi….,.’

Kasa ƙarasa maganar tayi,a firgice ta shiga girgiza mashi kai ganin yadda ya ɗago da hannunshi,duk a tunaninta marinta zaiyi amma sai taga akasin hakan,a hankali ya aza tafin hannunshi a saman lallausar fatar gefen fuskarta,ɗan zaro ido sehrish tayi tana kallon fuskarshi,yayin da shi kuma yake kallon brownish lips ɗinta dake ta faman kerma,

Almost 5 mins sannan  yace”Tashi ki tafi,”ya ambaci hakan tare da zame hannunshi daga gefen fuskarta sannan ya miƙe tsaye hannunshi ruƙe da bottle water ɗin yana maida murfin robar,daddagewa sehrish tayi tare da yunƙurawa daƙyar ta miƙe,aikuwa nan take ƙafafunta suka bada wani irin sauti ƙasss!,a gigice ta saki wata irin razananniyar ƙara nan take ƙafafun suka gaza ɗaukarta,gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa,sai dai ina kafin takaiga ƙasan tuni hannun sgr ya damƙi qugunta kwakkwaran ruƙo yayi mata da hannu ɗaya,gabanta ne taji yayi wani irin bugu daga bisani kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya ba ƙaramin tsorata tayi ba,har lokacin hawaye ne ke zubowa daga cikin idanunta,janyota Sgr yayi ta faɗo saman jikin shi gaba ɗaya,sannan ya ɗan russinar da kanshi tare da ɗago da ita,ya sanyata a saman kafaɗarshi,yadda kasan ya ɗauki wannan ɗiyar robar ƴar tsana,haka ya sa6i sehrish asaman shoulder ɗinshi,tafiya ya soma yi ɗauke da ita,ya ƙarasa wurin fridge ɗinshi tare da ajiye roban ruwan dake hannunshi,sannan ya juyo tare da kama hanya ya fito daga part dinshi kai tsaye ya nufi downstairs,ajiyar zuciya sehrish ke ta faman saukewa tayi lamo abunta,yadda take jin daɗin kafaɗar tashi tamkar ta hau Jirgin sama,

A natse yake taka matattakalar benen ɗauke da ita har ya ƙarasa saukowa da ita cikin Main palour ɗin nasu,bin ko’ina yayi da kallo babu kowa da alama basu kammala shirin zuwa yin sallar asubahin ba,duk da dama lokaci bai ƙarasa yi ba,a lokacin ake ta haramar fara kiran sallan,

Tunani ya shiga yi a ina zai sauke yarinyar,don shi bai ta6a sanin ma a ina yarinyar take rayuwa acikin gidan ba,har wani lumshe ido sehrish take yi saboda yanayin da ta shiga wata irin kasala ga baccin da take ji,ta gaza yarda cewa sgr ne da kanshi ya sa6ota asaman kafaɗarshi,jin abun take kamar a mafarki,duk da halin da take ciki amma har addu’a take yi cikin ranta Allah yasa dagaske ne ba mafarki bane,

Yana cikin wannan tsayuwar ɗauke da sehrish a kafaɗarshi,kwatsam Abbansu ya fito daga bedroom ɗinshi ya tunkaro main palour din,sai faman sauri yake yi don yaje ya tashi sauran su tashi su kimtsa lokacin sallah yayi,tunɗazu yake trying numbers ɗinsu don ya tashe su amma mutum ɗaya ne kawai yayi picking call ɗin,wato kanal yousouf,amma sauran babu wanda ya ɗaga alamar basu tashi daga bacci ba,

Da wa Allah ya haɗa shi?ae yana fadowa babban falon karaf idanunshi suka sauka akan Sgr dake ɗauke da Sehrish a kafaɗarshi,har sai da gabanshi ya faɗi,cikin sauri Abba ya ɗan ja da baya saboda kar Sg rafayet ya ganshi,har wani murza idonshi yake yi da hannayenshi don ya ƙara tabbatarwa da kanshi abunda yake gani,wai ko idanunshi ne ke nuna mashi ba dai-dai ba,lamarin ya ɗaure mashi kai,tsananin mamaki ne matuƙa ya kama shi,har ƙara leƙawa yake yi don ya tabbatar ma kanshi wanene acikin matasan nashi ya ɗauko mace a kafaɗarshi,

Hasken fatar sgr,da kuma wannan doguwar ƙirar tashi ne suka tona mashi asiri,uwa uba doguwar sumar kanshi,

Doubting ya shiga yi yana cewa”Anya kuwa shine?kodai idona ne ke nuna min ba dai dai ba,kodai tsufa ne yazo mun gadan gadan harya sa nake ganin hakan!kai wannan fa Rafayet ne ba wani ba,yarinyar daya ɗauko a kafaɗarshi kuma wannan yarinyar ce sehrish!ita kaɗae ce ƴar matashiya acikin gidan!idan har zargina ya tabbata toh me ya haɗa shi da yarinyar ne harya ɗaukko ta saman kafaɗarshi?Hakan na nufin a bedroom ɗinshi ta kwana”? Ya jefa ma kanshi tambaya,gaba ɗaya ya kuma ruɗewa,

Can dai yace”Ina yi mashi kyakkyawan zato,amma tabbas akwai alamar tambaya anan!”

Shiru ya ɗanyi yana ƙara leƙensu,abunne ya daure mashi kai sosai tunda yake bai ta6a ganin sgr da mace haka ba,aranshi ya shiga cewa kodai Ya fara kula mata ne?wata’ƙil akwai wata alaƙa atsakanin shi da yarinyar,’

Jinjina kanshi yayi tare da cewa”Biri yayi kama da mutum tabbas!sai yanzu na gane inda ya samu jan baki asaman ƙirjinshi,Oh ni hussein ina nan sake da baki ana mun aika aika acikin gidana!nagode ma Allah daya nunamin wannan abu akan idona,nasan me zanyi!”

Yana fadin hakan ya juya tare da komawa part ɗin nasu,don ya tashi sauran dama Upstairs ya nufa don ya tashi Omar,abunda yasa ya koma saboda baison sgr ya ganshi ya gane cewa ya ganshi ɗauke da Yarinyar a kafaɗarshi,

Jin takun tafiya yasa Sgr juyawa don yaga wanene,Azmee ce ta fito tana ta faman ƴan waige-waige,bakomai ne ya fito da ita ba face neman Sehrish, taje bedroom ɗinta donta tashe ta daga bacci taga babu kowa,hakan yasata fitowa don ta nemeta acikin gidan,

“Ke,zonan,”a ɗan firgice Azmee ta kallo inda yake,dama tunda taji an ambaci hakan tasan cewa Sgr ne,saboda shi kaɗai ke mata wannan kiran kai tsaye kamar wata ƙaramar yarinya,ko sunanta bai iya faɗi sai dae ke,don shi a yadda ya ɗauka duk wata mace ƙarama take awurinshi,

 

Fargaba ta shiga yi,ganin Sehrish kwance a kafaɗarshi,zullumi ta shiga yi acikin ranta,tsoranta kar ace wani abu ta aikata masa,

ƙarasawa tayi kusa dashi murya na rawa tace”Gani yalla6ai,”

Ko uffan baice mata ba,a hankali ya saukko da sehrish daga saman kafaɗarshi ya tsayar da ita akan ƙafafunta dake ta faman kerma,cikin sauri Azmee ta ruƙo hannunta,hankali tashe take kallonta ganin yadda ko’ina na jikinta ke kerma,cike take da son jin me ya faru da ita,Me ya haɗata da sgr da har ya ɗaukkota haka asaman kafaɗarshi,

Juyawa sgr yayi cikin sauri ya haye saman stairs da sauri da sauri yake taka steps ɗin sai da yakai step na ƙarshe sannan ya ɗan tsaya kamar mai nazarin wani abu,

 

A lokacin azmee ta ruƙo sehrish tana taimaka mata wurin yin tafiya,a hankali a hankali suka nufi part dinsu,gaba ɗaya sehrish taji wani irin yanayi a tattare da ita,sam bataso sgr ya sauketa daga saman kafadarshi ba,don ba ƙaramin relief ta samu ba,ita kaɗae tasan yarda take ji aduk lokacin da takasance tare dashi,

Runtse idonta tayi yayin da hawaye ke cigaba da zubowa sun jiƙa mata fuskarta sharkaf,suna cikin tafiyar nan,ranta ya bata cewa ta ɗan jiyo ta kalle shi,taga yana nan ko ya tafi,

A hankali ta ɗan juyo da fuskarta, ta kalli upstairs din,adaidai lokacin shi ma Ya juyo da fuskarshi a wani slow,kai tsaye idanunshi suka sauka acikin nata dake kallon shi,gaza janye idanunshi yayi daga kallon hawayen dake shararowa a fuskarta,wani irin tausayinta ne yaji ya kama shi,saboda yasan cewa shine silar zuban hawayen nata,kamar yarda yake kallonta,itama haka take kallonshi duk da sunyi nisa da juna,a hankali ya lumshe idanunshi tare da ɗauke kanshi daga kallonta ya ƙarasa hawa upstairs ɗin da sauri ya wuce bedroom ɗin shi,

Sai bayan da ya 6ace ma ganinta sannan itama ta  juyar da kanta tare da mayar da hankali wurin yin tafiyar,har cikin bedroom azmee takaita,ta taimaka mata wurin hayewa saman gadon,ta kwanta yayin da idonta ke kallon ceiling ba komai take tunawa ba,face yarda Sgr ya tarbo waist ɗinta a lokacin da tazo faɗuwa,da kuma lokacin da ya ɗaurota asaman kafaɗarshi,da kuma kallon nan daya juyo yana yi mata kafin ya tafi,

Zama azmee tayi daga gefen gadon tana kallonta tace”Me ya faru dake ne sehrish?meya haɗaki da sgr dana ga ya ɗaukko ki asaman kafadarshi”?

bata 6oye mata komai ba ta sanar da ita duk abunda ya faru a tsakaninta da sgr,

Jinjina kai Azmee tayi tare da cewa”u ave to be very careful rishi,tun farko saida na gargaɗeki akan shi,amma baki ji ba ko?

Muryarta tamkar zatayi kuka tace”Aunty azmee ina kiyayewa,wannan ma matsala aka samu har na manta da gyalena asaman gadonshi,banyi tsammanin zai dawo ba a wannan lokacin……’

Shiru Azmee ta ɗanyi kafin tace”Shikenan amma duk da haka ki ƙara kiyayewa nan gaba,karki ƙara yin  gangancin maimaita kuskuren da kikayi yau,”

Sehrish tace”Insha Allah bazan ƙara ba,”

“Allah yasa,ni zan wuce,ki daure ki tashi kije kiyi sallah,”

Amsa mata tayi da”toh,” sannan azmee ta miƙe tare da fucewa daga bedroom ɗin nata,ajiyar zuciya sehrish ta sauke,tunda ta kwanta ko kwakkwaran motsi wannan bata iya yi ba,jikinta duk yayi mata tsami,ta so ta tashi ta ɗan gasa jikin da ruwan zafi amma sam tagaza motsi,kamar an aza mata Bulo asaman jikinta haka ta dinga ji,yayi mata wani irin nauyi,a wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita.

 

_💋Boss Bature💋_

 

A washe gari

 

Around 7:00am

 

A firgice Jahad ta farka daga dogon suman da tayi,sakamakon jin saukar ruwan sanyi da tayi asaman fuskarta,a gigice ta tashi zaune,lokaci guda ta fara  ambaton sunan Hosana!hosana!

“Jahad ki buɗe idonki Ni ce fa”

Jin muryar mutum a kusa da ita yasa ta ware idanunta tana kallonta,bakowa bace face Nurse Camilla,zuwanta kenan ta shigo cikin falon taci karo da Jahad a sume ƙasa,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,da sauri ta ɗauko ruwa mai sanyi ta yayyafa mata,

A hankali jahad ke kallonta da idanunta waɗanda suka rune saboda kukan da tasha,

Sanye take cikin jeans da t- shirt tare ta ɗaure sumar kanta da ribbom,

a ɗan ruɗe tace”Jahad me ya faru ne?na shigo na same ki a sume menene ya faru dake ne”?

Cikin shessheƙar kuka tace”Hossana tana cikin ɗaki,bansan tana a raye ba ko ta mutu,jiya da daddare wani ya faɗo mana a cikin bedroom ɗin mu har yayi ƙoƙarin yin raping ɗinta……..’kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya kufce mata,hankali a matuƙar tashe camilla ta miƙe tare da nufar hanyar zuwa ɗakin nasu,

Miƙewa jahad tayi tabi bayanta cikin sauri,zuciyarta nata faman bugawa saboda fargabar a wane hali hossana ke ciki, karfa ace wannan mutumin ya ƙara dawowa don ya cutar da ita,

Yadda jahad ta bar hosana haka suka sameta,naɗe cikin bargon a sume bata motsi,

Hawa saman gadon camila tayi ta ƙarasa kusa da Hosana tare da kai hannu ta shafa wuyanta,kallon jahad tayi dake atsaye cike da fargaba tace”dauko mun ruwan da na bari a falo,” amsa mata tayi da toh sannan ta fuce daga cikin bedroom ɗin,within minutes sai ga Jahad ta dawo hannunta ɗauke da bottle water ta miƙa ma Camilla,hannu tasa ta kar6a sannan ta buɗe murfin ta debo ruwan tare da watsa ma hossana a fuskarta,nan take hossana tafarka daga suman da tayi,a wani irin razane ta zabura zata yaye bargon jikinta tana cewa”karka ta6ani Abba banso banso!ka ƙyale ni in tafi,inba haka ba Ya omar zai kashe ka….”

Cikin sauri Jahad ta haura saman gadon tare da rurruƙeta tana gyara mata bargon jikinta gudun kar tsiraicinta ya fito,ganin tana ta faman fisge fisge tana hargowa yasa Camilla tayi mata magana cikin sanyin murya tace

“Hosana!ki kwantar da hankalin ki,babu kowa anan da zai cutar dake,Ni ce Sister Camilla tare da ƴar uwarki jahad a kusa dake,dan Allah ki shiga natsuwarki,”cikin rarrashi takeyi mata magana,

Jahad tace”Hossana gani a kusa dake ki buɗe ido ki kalle ni,”

Jin muryar jahad yasa hossana ta buɗe idanunta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya,fuskar nan tayi sumtun saboda kukan da tasha,idanunta duk sun ƙankance,

 

“kiyi haƙuri hossana,koma waye Allah bazai barshi ba,nayi ƙoƙarin na kwace ki daga hannunshi amma Allah bai nufa ba,inda na gode ma Allah da bai ƙarasa nufinshi akanki ba,nayi ƙoƙarin na kira ƴa Omar,amma layinshi yaƙi shiga,amma zuwa anjima zan ƙara jaraba kiran shi,nasan zai ɗaga,”

Cikin shessheƙar kuka tace”Jahad ki kira mun shi,a kiramun ya Omar yazo,inason naganshi,shi nakeson gani,”

Jiki a sanyaye Jahad tace “Kada ki damu zan kira maki shi,insha Allah,”

 

gaba ɗaya lamarin ya girgiza Camilla,ta jima tana hasashen waye yayi ƙoƙarin cutar da yaran acikin gidan!duk irin tsaron dake gareshi,ba ita ba hatta jahad tashiga zargin waye yayi masu wannan zuwan da daddare don ya cutar da hossana,sun jima suna wannan tunanin, a ƙarshe dai bakowa suka fi zargi ba face ɗaya daga cikin security guards ɗin gidan,

Bayan sun gama jimamin nasu,Camilla ta tashi tare da fucewa daga bedroom din ta nufi kitchen don ta shirya masu breakfast,

yayin da ita kuma Jahad,ta taimaka ma hossana bayan ta sanya rigarta sannan ta kaita toilet ta taimaka mata wurin yin wanka da ruwa mai ɗumi yarda jikinta zai ɗan warware,sai da su kayi alwala sannan suka fito daga cikin toilet ɗin,

 

doguwar riga ta ɗaukko mata acikin wardrobe ta bata ta sanya sannan suka zura hijabansu atare,jahad ta shimfiɗa masu darduma suka hau sama tare da daidaita natsuwarsu suka kabbara sallah,har lokacin jikin hosana sai faman kerma yake yi,a tsananin tsorace take da abunda ya faru da ita adaren jiyan nan,bayan sun kammala sallar jahad tace mata taje ta kwanta tayi bacci,ita zata wuce kitchen wurin Camila,ta taimaka mata suyi aikin breakfast ɗin atare,

Bayan jahad ta fuce daga bedroom ɗin,hossana ta miƙe daga saman dardumar jikinta nata faman kerma ga rawar ɗari da take yi,saboda sanyin da take ji,lalla6awa tayi tare da hayewa saman gadon,takai hannu tare da janyo bargon ta ɗan kakka6e shi zata rufe Jikinta dashi,kwatsam taji sautin faɗuwar wani abu ƙasa,cikin sauri ta leƙa ƙasan gadon tana kallon abun nan daya fado daga saman gadon,

Diamond ring ne ɗan ziriri dashi sai faman ƙyalli yake,gabanta taji ya faɗi rass!ganin zoben da tayi ya faɗo ƙasa,yunkurawa tayi tare da tashi daga zaune sannan takai hannu ƙasan gadon tare da ɗaukko zoban,ɗago shi tayi a daidai saitin idanunta tana ƙare mashi kallo,

Zaro ido tayi hankalinta a matuƙar tashe ta furta”Ya Omar!!!!!!!!!” 😳

Domin Sauke Littafin book 3 Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button