Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 21 Hausa Novel

Kamar yanda ya fada kuwa kaca-kaca suka tarar da gidan, sai dai suna shiga suka fara kokarin gyarawa. Kuma da yake yana ajiyesu ya sake fita harda Afaf da Habib aka yi aikin, don haka cikin kankanin lokaci suka gama. A haka rayuwa ta cigaba; sai dai a bangaren Mustapha idan dai yana gidan ba a saka masa yara aiki, sai dai su suyi ta gara rashida komai ita zasu aika ko su saka. Khadeeja tana son ta tsawatar musu amma tana tsoron abinda ubans zai ce tunda ta ga sun dan sami natsuwa babu wata hatsaniya, bata so ta ja rigima. Don haka haka ta zuba musu ido; abu kadan sai a kwalawa Rashida kira ko da kuwa aikin Khadeejan take yi dole ta bari taje tayi musu yanda suke so.………. Ba a dade da sallacewa ba kuma aka bude gari, a hankali kowa ya koma harkokinsa.Ranar Lahadi da daddare bayan yara sun yi bacci; suna zaune a parlor shi yana kallon balla a Tv yayinda ita kuma take chatting a waya; ta dago daga kallon wayar ta dubeshi tace ‘Babe gobe fa za a koma makaranta.’Ba tare da ya dauke kai daga kallon TV din ba yace ‘Kin gaya min fa tun last week, kuma na siyo duk wani abu da ake bukata.’Ta gyara zama ta ajiye wayar tace ‘Nima zan shiga school din na gano, wata kila an kafe timetable, amma sai wajen goma zan fita.’‘Ok, to zaki dawo kafin 12:30pm kenan ko? Saboda dauko ‘yan makaranta tunda ni kin ga ina office.’‘Eh, zan yi kokari na dawo kuma idan ban dawo ba ma kafin na fita zan je da Rashida taga makarantar tasu idan lokaci yayi bandawo ba sai taje ta dauko Nasreen.’Ya gyara zama ya kalleta kamar a foirgice ‘Wai wannan yarinyar ce zata dinga dauko yaran daga makaranta kuma ta zauna ta zauna dasu a gidan ita kadai?’Cikin halin ko in kula tace ‘To ya za ayi, ai kaga dai nima dole naje makaranta ko? They will be fine fa, yarinyar tana da hankali sannan kuma ka ga ga Afaf tana nan idan ta dawo. Suma ita da Habib na gaya musu idan an tashi daga makaranta su taho tunda na ga ko nice ma naje daukosu idan muka rasa napep a kasa muke tahowa.’Ya kare mata kallo sanna yace ‘Wai me kike fada ne? su Afafa din ne kike so su dinga tahowa daga makarantar su kadai kuma a kas, sannan harda Nasreen? Wadda sai an tasheta da minti talatin sannan a tashesu?’‘To babe ya zamu yi? Ai ka ga dai kamar Afaf bashi da wani amfani ace sai Rashida taje sannan zasu taho tare ko? Ni kuma duk lokacin da ta kama ina gidan zan je na daukosu.’Suka yi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani.Jimawa kadan yace ‘Ni barin wannan yarinyar taki ma a gidan ita kadai gaskiya bai yi min ba, ya za ayi duk mu fice a barta ita kadai kuma a bar mata mukullin gidan? Ai idan muka dawo sai abinda muka gani kenan, za ma ta iya fara shigo da maza gidan ko ayi mata wayo ayi mana barna idan aka gane ita kadai ake bari a gidan.’‘To yanzu ya kake so ayi? Ka ga dai da ni da yaran ai dole duk muje makaranta ko?’‘Ni ma ban sani ba, kece zaki san yanda zaki yi. Zaki maiya fita da ita ki rufe gidan in ya so sai ku dawo tare ki dauko yaran, duk yanda dai kuka yi. Amma dai gaskiya wannan tsarin na barinta a gidan bai yi min ba.’Ranta ya fara baci; me yake nufi ne? so yake yace ta bar makarantarta kawai saboda ta zauna masa da yara ko kuwa mai aikin yake so ya korar mata? Wannan bayanin da yake yi ma sam ba zai yiwu ba gara dai ya sake lissafi ko kuma shi ya dinga baro office yana zuwa yana daukosu.Tace ‘Uhm, to ai ka ga ba ni nake rubutawa kaina timetable ba, wani malamin ma sai 1pm yake fara lecture kuma dole nayi attending idan dai ina son na gama degree din. Sai dai ko ka kawo wata dabarar da kai kake ganin za ayi da daukosu in ya so ita Rashida idan zan fita sai na fita da ita duk lokacin da na gama lecture sai mu dawo tare.’Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ya tashi ya jefar da remote din TV din da yake hannunsa ya shige daki.Ta bi bayansa da kallo tana mamaki; wai me mutumin nana yake nufi ne? shikenan sai ta jingine rayuwarta ta zauna ta kular masa da yara? To ai ita ko ‘yayan da ta haifa ma haka ko tana so ko bata so zata dinga barinsu da mai aikin ta tafi makaranta tunda dai haka taga masu yaran suna yi. Ko kuwa da yake ta auri tuburarre hakura zata yi da komai ta zauna sai yanda suka yi da ita?Haka suka kwana a wannan daren kowa da abimda yake ransa. Ko da gari ya waye tun asuba ta tashi uta da Rashida wadda ta tayata nan da nan suka shirya yara sannan suka hadawa kowa abinci. Kamar yanda ya saba sai karfe bakwai da kwata sanna ya fito, zuwa lokacin sun shirya suna jiransa; ya kwashesu ya kaisu ya dawo. Sai wajen karfe tara da rabi sannan ya gama shirinsa, lokacin fitowarta kenan daga wanka saboda sai da ta tsaya ta gama abincin rana ta juye a flask sannan ta fara shirin. Ya sameta a daki tana shafa mai rike da mukullin motarsa, yana daga tsaye a bakin kofa yace ‘Ni na fita.’Ta juyo da sauri tana cewa ‘La! Babe don Allah bari nayi sauri na saka kayana sai ka bani lift.’‘No ba ta hanyarku zan bi ba, ki wuce kawai sai na dawo. Kada ki manta min da yara.’ Ya fada yana ficewa daga dakin.Tabi bayansa da kallo da baki bude; lallai ma mutumin nan. Kiri-kiri dai shi baya son ya dauketa a motarsa idan dai makaranta zata, in banda haka ai ko ba hanyar makarantarsu zai bi ba ya sauketa a bakin titi ya rage mata tafiya. Ta juya ta cigaba da shiryawa cikin sanyin jiki tana tunanin son kai irin na Mustapha. Allah ya so ta ma Baffa ya tura mata kudi kuma ya sanar da ita duk wata zai dinga turo mata kudi saboda karatunta, idan tana son wani abu sai ta yi masa magana.Tabbas ta san da ace da Mustapha ta dogara da sai dai ta hakura da karatunta ta zauna ta kular masa da yara.Nan da nan ta karasa shiryawa ta fito ta sallami Rashida wadda ta barsu tare da Shukra bayan ta yi mata duk wani bayani da take bukata sannan ta kama hanya zuciyarta cike da damuwa da wasi-wasi.Kafin sha biyu ta gama duk wani abu da take yi a makarantar sai dai bata son ta dawo ta dauko yara; ba wai yaran ne bata son daukowa ba amma bata son ta daukosu Mustapha yaga kamar fadansa ne ya sa don haka duk lokacin da zata fita ya zata zai yi mata fada ta dauko masa yara. Don haka suka nemi inuwa ita da kawayenta suka zauna suna hira, sai wajen 1;30pm sannan suka karasa masallaci suka yi sallah kowacce ta kama hanyara gida.Ko da ta zo gida bata tarar da wata matsala ba, Rashida ta kai Shukra gidan su Ummi ta dauko Nasreen daga makarantar kamar yanda ta bata umarni. Su kuma Afaf da Habib kusan tare da ita suka shiga gidan.Ko da ya dawo tana jin sa yana tambayar taran wanda ya daukosu daga makaranta suna ba shi amsa, musamman Shukra wadda yake ta tambayarta me suka yi ita da Rashida a gidan bayan Anti ta fita. Haka tayi banza da shi ta cigaba da harkokinta.Haka suka cigaba da yi, sai ya zama kuma da yake ba a fara lecture sosai ba sati biyun farko kullum Khadeeja bata fita da wuri sanna kuma tana dawowa kafin ya dawo gidan, don haka matsalarsu da sauki tunda zai zo ya tarar da ita tana ta hidimar yara.…….Sati daya da komawa aka kafewa su Khadeeja timtable, kuma da yake babu lokaci sosai timetable din a matse take. Haka dai suka cigaba da karatun.Ranar Alhamis shine take da lecture 8am to 6pm, don haka ta san dole ta shirya ta fita tare da yara. Tun dare ta gama komai, tayi rabin aikin abincin safe sannan ta fitowa da kowa kayansa. Ta yiwa Rashida duk wani bayani da take bukata tunda yaran idan sun dawo daga makarantar boko babu islamiyya don haka nan zasu wuni a gidan.Tun kafin asuba ta tashi suka fara aiki tare da Rashida.Bayan Mustapha ya dawo daga masallaci sallar asuba ya sameta a kitchen, tana ta fama kaiwa da kawowa tsakanin dankalin da take soyawa da kuma hadawa yara abincin makarantarsu a lunch box. Bayan ya amsa sannu da zuwanta yace ‘Wai kin yi sallah kuwa? Na ga kamar a nan na barki fa.’Tayi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, nayi sallah mana. Sauri nake na gama saboda yau 8am to 6pm ne da ni kuma 8am din nan idan Prof. ya rigani shiga aji rufe min kofa zai yi wallahi shi yasa nake ta sauri don kullum sai yayi attendance.’‘Oh kenan yau sai 6pm zaki dawo gidan?’‘Eh.’ Ta amsa a gajarce tana kwashe dankalin da ya riga ya soyu.Ya kara hade girar sama da kasa sanna yace ‘To a ina zaki bar yara wuni guda?’Bata son hayaniyarsa don bata son abinda zai bata mata rai, ba tare da ta bar abinda take yi ba tace ‘A nan mana gidansu; Rashida zata dauko Nasreen su kuma su Afaf idan suka dawo zasu sameta a gidan sai suyi zamansu kafin na dawo, they will be just fine.’‘Haba ai dadewar tayi yawa, kenan haka zasu zauna suyi duk abinda suka ga dama ba tare da wata kulawa ba.’ Ya fada a fusace.‘Kada ka damu Rashida zata kula da su.’Kafin ya bata amsa suka jiyo ihun Nasreen daga dakinsu tana cewa ‘Wayyo Anti.’Ta riga ta san rigimar Nasreen, idan dai aka tasheta da sasafe zuwa makaranta sai tayi kuka ko ma waye ya tasheta, shima kuma ya san da haka. Amma ba tare da bata lokaci ba ya nufi dakin da sauri. Ganin haka itama Khadeejan ta ajiye abinda take yi ta bi bayansa, kusan a lokaci daya suka shiga dakin.Nasreen tana zaune a kan gadonsu da hawaye shabe-shabe a idonta yayinda Rashida take tsugune a gaban gadon tana rike da towel.‘Me aka yi miki kike kuka Nasreen?’ Ya tambaya kafin ya karasa shiga dakin.Khadeeja tana shiga dakin ta sauko daga kan gadon ta rungumeta tana cewa ‘Anteee.’Ya shafa kanta ‘Me aka yi miki?’Cikin shagwaba tace ‘Rasheeda ce.”Ya juya ya dubi Rashidan a fusace yace ‘Me kika yi mata?’Nan da nan jikinta ya hau rawa tana gyara tsuguno, kafin tayi magana Khadeeja ta shafa kan Nasreen tace ‘Nas me Rashida tayi miki?’‘Tashi na tayi daga barci…

Back to top button