Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 42 By Ayshercool

Jauhar ya fara samu da maganar, da daddare suna tare ya ce “Na ce ba””Ka ce me ranka ya daɗe?””Wani abu na yanke ne, ina son na samu Abbu, ya bani gadona na wurin ummi, in sayar da abun da zan sayar na karɓi kuɗi a wurin indabo na haɗa na fara wata sana’ar ina son barin sayar da wiwi gaba ɗaya”.Tayi murmushi ta ce “Alhamdilillah, tunani mai kyau, amma ba a yadda ka gaya mini haka zaka je ka gaya wa Abbun ba ko?””A yaya zan gaya masa?””Cikin kwantar da murya, zaka yi masa bayani, ka san iyaye sai ana lallaɓa su, ka sani ma ko ya kai ka kasuwa?”Ya ce “Ko ya kai ni ba na so, ya je ya cigaba da riƙe ‘ya’yan matar can. Dama alhkina ne ya sa yanzu ba shi da kuɗi kamar da”Jauhar ta ce “Haba master, Abbun ka ke gaya wa haka, kai zaka ji daɗi ka haifi ɗa yayi maka haka?”.Cikin ko in kula Al’amin ya ce “Duk tsanani, ba zan yi wa ɗa na abun da yayi mini ba””Master ka san shiga tsakaninka aka yi da Abbu, dan Allah ka daina irin wannan maganar”.Yayi mata shiru, ta sake cewa “Master yaushe zaka kai ni mu gaida su Hajiya?””Ba rana? Tun bayan kawo ki sun kuma zuwa?””Hmm master, Allah ya baka damarmaki, duk da ka rasa ummi da yaya sadik, da kuma uban gidanka. Ko yaya dole nan gaba yaranka su so ganin ‘yan uwanka, dan da dangin uba ake ado. Ni fa duk wannan abun da ake yi, bani da wayo sanin mahaifiyata ta rasu, ba ‘yar gari bace, yar jalingo ce, ba a taɓa kai ni garinsu ba, ba a taɓa nuna mini ko mutum ɗaya a danginta ba, kuma ban taɓa ganin kowa ya zo daga garinsu ba. Da na fuskanci babu uwata a gidan, na nemi ba’asin in da take, baka ga dukan da mama tayi mini ba, ban haƙura ba na tambayi baba, amma ya ce idan na kuma yi masa zancen dangin mamana, sai ya zane ni. Yadda yake nunawa da yadda su mama ke faɗa yana son mamana, amma nayi mamakin yadda yaƙi yadda a kai ni garin su na ga ko ‘yan uwanta, da naga ba ya so kawai na daina maganar. Kai kuwa da ka rasa uwa akwai makwafinta, yakamata mu je mu ga hajiya mu gaisheta, ni ba wanda zan kalla na ce daga wurin dangin mahaifiyata yake”.Yayi ajiyar zuciya ya ce “Kuma ba ki san a ina take a jalingon ba?”Ta girgiza kai ta ce “Ban sani ba, kawai iya abun da na sani kenan””Shikenan, zamu je mu gaida hajiya, amma sai na tambayi Abbu in da take a tofan ba zan iya tunawa ba””Yauwwa maigidan Allah dai ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora “Ya shafa fuskarta ya ce “Amin madarata””Yauwwa milona”Ya ce “Ga madara ga milo, sai Shan shayi” suka yi dariya tare.Washegari da safe bayan sun karya, ya bata magunguna ta sha, tana ta lallaɓa jikinta, za ta yi aikace-aikacenta, ya hanata ya fito ya yi mata share-share, har tsakar gida ya wanke mata.Kayan da ta cire yake wankewa, aka buga ƙofa, ya je ya buɗe hafsa ya gani a tsaye, hannunta riƙe da leda.Ya bata hanya ta shigo, a tsorace ta kalli Al’amin fuskarsa a haɗe ta ce “Ina kwana””Lafiya ƙalau”.”Dan Allah wurin jauhar na zo” da hannu ya nuna mata falo.Daga falon ta ce “Muryar wa nake ji kamar Yaya hafsa”Ta ce “Nice”Ta tashi ta taro hafsa ta ce “Sannu da zuwa”.Hafsa ta ce “Yauwwa sannu ya jiki?””Jiki Alhamdilillah, ya aka yi ki ka gane gidan?””Yaya saifu ne ya gaya mini hanya, kuma direbana da yayi tambaya aka nuna masa gidan ba wuyar ganewa”.Ta ce “Allah sarki yaya hafsa tun ina Asibiti nake tambayar kina ina, aka ce mini kina umara, na ce baki gaya mini ba muna chat, ai da na jero addu’a ayi mana ni da mai gida”Tayi murmushi ta ce “yanzun ma an yi miki, wai jauhar ɓarin da wahala ne, na ga kin rame haka kin yi fari?””Kai da wahala mana, jini na zubar sosai shiyasa na yi haka, amma kwanaki ai ƙiba na yi sosai, ashe ciki ne ban sani ba””Allah sarki, Allah ya kawo mai amfani, sannu””Yauwwa ai na warware “Al’amin ya shigo falon, jauhar ta ce “Master ba ka ganeta ba ne? Yayata ce da muka je gidanta fa, ba ka ga muna kama ba?”Kai tsaye ya ce “Na gani, kin fita kyau”Jauhar ta ce “Kai fa ka fiye son kai ta ina?””Ta ko ina” yayi maganar yana shigewa ɗakinsa.Hafsa tayi murmushi ta ce “Aikam kin fi mu kyau ai duk gidan nan”Jauhar ta ce “Rabu da shi, shi ma faɗa kawai yayi” suka cigaba da hira, ya sake fitowa ya shirya tsaf zai fita.”To yau me ki ke so? Kayan cikin ko ganyen wanne ki ke so?”Ta shagwaɓe fuska ta ce “Kai””Ni ki ke so?” Ta ɗaga masa gira tana murmushi.”Aikuwa zaki kwana da yunwa, me ki ke so?””Komai ka samu na gode”Ya ce “Abun da zai ƙara miki jini aka ce ai””Jininka zan sha” ta yi maganar tana dariya.Yayi murmushi ya ce “You are not serious, ki yi addu’a Allah ya sa na samu kuɗi, na sayo miki kaza”.Hafsa ta ce “Ai ga miya ma na yi miki, da kazar a ciki”Jauhar ta ce “Ashe zaku yi faɗa da master, tun da ki ka riga shi kawo mini kaza”Murmushi ya sake yi, wanda ya bawa hafsa mamaki, take bin su da kallo, gwanin burgewa.Har zai fita ta ce “Master”Ba tare da ya juyo ba ya ce “Kar na yi shaye-shaye da yawa, kar na yi faɗa da kowa, banda rigima da mutane” ta kwashe da dariya ta ce “Au ka haddace ma kenan, addu’a zan yi maka ai, Allah ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora ya wadatamu da halal ya nesanta mu da haram”Ya waiwayo ya ce “Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, ‘yar aljannata” ya juya ya tafi.Yana fita Hafsa ta ce “Innalillahi, jauhar dan Allah ya aka yi ki ka canza mutumin nan, dariya fa yake yi miki, kalli yadda yake yi miki, dan Allah jauhara ya ki ka yi ki taimake ni” tayi maganar cikin tsananin damuwa.Jauhar ta ce “Ban fahimci in taimake ki ba yaya hafsa, meyafaru? Wannan ai normal ne tsakanin ma’aurata, kodayeke shi ya koya mini rashin kunya, da ko kallonsa bana iya yi a gaban mutane”Idon hafsa ya cika da hawaye ta ce “Jauhar, wallahi tun da na auri Alhaji mu’azzam hankalina bai kwanta ba, bai taɓa bani awa biyar cikakkiya ba. Sai abun da matarsa take so yake yi, bai tare a ɗakina ba sai da matarsa ta amince. Ga kuɗin yana da su, yana kashe mini ya sakar mini amm ba su nake so ba, kulawarsa nake so da lokacin sa”.Juahar ta ce “Yaya hafsa ba fa abun da ki ke kalla a film ne soyyaya ba a ƙasar hausa da wurin mijin bahaushiya, dole ki fara kallon wane irin mutum ne shi, kin ga mijinki mutum ne mai hidindimu da yawa, ba zai yiwu ace kullum yana da lokacinki ba yakamata ki din ga yi masa uzuri””Uzuri jauhar, yana da lokacin matarsa da yaransa, gaba ɗaya auren ya fita daga kaina, na je na gaya wa anty, wai wallahi na ɗaga maganar nan, sai ta yi mini Allah ya isa, wai zan saka ayi mata dariya, na zama kamar hoto a wurinsa, ko ɗan abun ɗokin nan na amarci, duk fa ban san su ba. Ke da ki ka auri wanda ake yi wa kallon sai a hankali, babu imani da tausyai a zuciyarsa kalli abun da yake yi miki fa. Ni dai dan Allah idna wani malamin ne da ke, ki haɗa ni da shi”Cikin damuwa jauhar ta ce “Yaya hafsa ni wallahi ban san in da ake ganinsu ba ma, canza mutum daga wani abu da baka so zuwa wani, ba abu ne mai sauƙi ba. Kin san ni irin wahala da gwagwarmayar da na sha kafin mu zo wannan matakin kuwa?Da fari nima damun kaina na din ga yi, daga baya na kama addu’a babu dare babu rana, na haɗa da biyyaya da kuma haƙuri.Master mutum ne, kallon da mutane suke yi masa daban, wanda nake yi masa daban, biyayya da addu’a ne suka canza mini shi. Alkhairin da yake yi mini nake kalla kullum, nake yi wa laifukansa uzuri, har gara ke kina da uwa a raye, ni daga ni sai Allah, da na san bani da wata mafita, na bi abun da ƙaddara ta zaɓa mini, na rungumi abuna hannu bibbiyu. Kuma Allah ya shiga lamarina Alhamdilillah, mijina talaka ne, amma ba kowace mace take da ikon da nake da shi a gidan aurena ba. A zahiri shi nake bawa girman, shi ne jagoran amma a baɗini ni ce sitiyarin rayuwarsa, ina fatan kasancewa da shi har aljanna. Ke ma ki nutsu ki gano menene kurakuranki, sai ki gyara”.”Ba wani kuskure, ina kyautata zaton asri aka yi mini wallahi “”A’a yaya hafsa, ki daina faɗar haka, ki miƙa wa Allah lamuranki, wallahi zaki ga canji “Duk yadda jauhar ta so nusar da Hafsa muhimmancin haƙuri da juriya, da dagewa a kan addu’a amma taƙi ganewa kuma taƙi yadda.Zuwa azahar ta tafi, ta yi wa jauhar uban farfesun kaji, da abinci, ta kuma ajiye mata kuɗi ta tafi.Har a lokacin ba ta yadda har da hakkin jauhar a abun da yake faruwa da ita ba.Al’amin ne zaune a gaban Abbu, tun da ya gaishe shi, yayi shiru.Abbu ya ce “Ya jikin ‘ya ta?””Da sauƙi”Abbu ya ce “To Alhamdilillah yarinyar kirki, ‘yar aljanna Allah ya ƙara mata lafiya, matso ka haɗa shayi ga kayan breakfast nan”Sai da Al’amin ya kalli Abbu, ya girgiza kai ya ce “Na ƙoshi””Too, yau kai ne ka ƙoshi da abinci kuma?”Ya bashi amsa da “Eh na ci a gida” Abbu ya yi murmushi ya ce “Na manta ne, ashe fa magidanci ne, ya aka yi?”.”Sonake a sayar da gadona, zan ja jari, sana’oin da nake yi, ba sa iya riƙe mu sosai, gashi ina so ta koma makaranta, babu isasshen kuɗi a hannuna.Sai kuma ina son ka bani full adress ɗin hajiya, zan kaita ta gaisheta ta matsa a kan haka”Abbu yayi shiru yana ƙarewa Al’amin kallo, duk ya ɗan yi sanyi daga wani rashin mutuncin, babu uwar sumar da yake tarawa da faratan da yake bari zaƙo-zaƙo, gashi yadi ne a jikin sa saɓanin da, da idan bai ga dama ba da 3quater yake yawo da shirt damatsansa a waje, ya wani nutsu sosai.Abunka da uba da ɗa, wani irin shauƙi ya ji yana kama shi, a yadda ya ga tarin sauye-sauye a tattare da Al’amin.”Kai amma ‘yar nan tawa ta kyauta, amma wace sana’ar zaka yi?”Al’amin ya ce “Da wurin buga bulo nake so, ko wurin yin buredi, amma ban gaya mata ba tukuna, ban sani ba ko tana da wata shawarar”Abbu ya numfasa ya ce “Kana ji na Al’amin, tsawon shekarun nan, filayenka sun yi daraja sosai da sosai, idan ka bari suka ƙara kwana biyu sai sun fi haka sosai. Ka je ka rubuto business plan ɗin ka kawo mini, tare da list ɗin abun da za ayi mata na makarantar, sai na baka kuɗin, idan Allah ya dafa maka, aka samu cigaba, sai a sayar da ko gona ce a garinsu a ƙara, ka san kana da wasu kadarorin a tofa”Al’amin ya ce “A’a ni ba na son ka yi mini abu, daga baya azo a saka ka din ga yi mini gori, kawai dai a bani wanda na san nawa ne, kuma ma ni na fi son registration nayi mata da kuɗina da kaina, sai na fi alfahari da haka”Abbu ya ce “Gaskiya ne, kamar ba a nan ka zauna kana ce mini, ba ka son auren ba”Al’amin yayi shiru yana basarwa.”Ka rubuto business plan ka kawo mini, zan san abun yi, ka je ku yi shawarar ina jiranka.Gaba ɗaya haushi ya cika Al’amin, kawai ya ji ba shi ne ba zai yi ba, ya ce “Ina ne gidan hajiya a tofa”Abbu ya kwatanta masa, ya tashi ya fita.A waje suka yi karo da Rahila, bai ko kalli in da take ba ya fice.Ta shiga gidan da sauri, ta samu Abbu “Yanzu na ga Aminu ya fita, Allah ya sa ba wani abun ya aikata ba?”Abbu yayi murmushi ya ce “Al’amin ai rigima ta ragu yanzu, duk da wata rigimar ya zo yayi mini ya tafi. Wai gadonsa yake son a bashi, saboda yayi sana’a ya kula da matarsa” gabanta ya faɗi, ɗan kuwa ba ƙaramin harin filayen nan take yi ba, manyan filaye ne awon gwamanti ga gidaje guda uku. Ko da Abbu ya samu karayar arziki bai taɓawa Al’amin su ba.”Wace irin sana’a kuma, wallahi kar a sayar, ba shi da shi a ina ya samu kuɗin sayen leshin dubu tamanin ya bata ta saka, kalli a asibitin da ta kwanta fa na kuɗi, kalli uban kaji da naman da aka kawo gidan nan da salla, duk ba shi da kuɗin yayi haka? Ni ban taɓa zaton zai iya zama soko har haka ba a kan mace wallahi, yanzu saboda kula da itan ne za a sayar da wannan wuraren?”Abbu ya ce “Ba dai nasa bane ba, shi ya ga zai iya ai”Jauhar ta lallaɓa ta cigaba da sana’oin ta, yanzu tana iya aikace-aikacen ta, ta gama aikin, ta idar da sallar magariba, ta ji bugunsa.Ta buɗe ta kalle shi, ta ce “Malam lafiya ka ke yi wa mutane wannan bugun haka?””Zance na zo””A me ka zo”Ya ce “Ƙafata”Ta ce “Ko keke ba ka da shi ma?” Ta fito ta zauna a kusa da shi, a kan barandar gidan malam lawan ta ce “To me ka kawo mini “Ya ajiye baƙar leda ya ce “Gata nan gyaɗa ce marau, suyar yau mai zafi””Ka rasa me zaka kawo mini sai gyaɗa, anya ka na so na din ga fitowa zancen nan” ya saka hannu zai ɗauke ledar, ta riga shi ɗaukewa ta ce “Allah ya shiryeka, Allah master da da kanka a ka bari ka samo matar aure, za a sha wahala kan ka samu””In ji wa? Farinjini fa zan yi “”A hakan kana muzurai da zare idon? Kan na saba da kai fa na daɗe, tsoro ka ke bani da sosai “Ya ce “To yanzu fa?””You are my best friend ever, sauƙin kai ne da kai fiye da yadda ka ke tunani, miskilanci ne kawai matsalarka wuyatta na dafa abinci mai daɗi shikenan an wuce wurin “Suka kwashe da dariya tare, a kan barandar gidan, suka cigaba da hira, suna cin gyaɗa, kasancewar a cikin duhu ne, babu wuta, yake ba gaya mata yadda suka yi da Abbu.”To yanzu wanne zaka yi a ciki, wace sana’ar zaka yi?”Ya ce “Rabu da shi, idan muka je ƙauye zan saka a nuna mini gonakin, a sayar da wata na karɓo kuɗina””A’a kar ka yi haka master “”Haka fa za a yi, wallahi ba zai taimaka mini ba muddin shegiyar matar nan ta sani, ban da ina duba darajar amintar da suka yi da marigayiyya, wallahi da sai na tsinke mata laka””A’uzibillah, wannan wace irin magana ce?””Mu bar wannan maganar, ɗaukko key ki rufo gidan mu fita yawo ” ta ce to.Ta rufe gida, ya goya ta a babur, suka tafi ya din ga zaga gari da ita, ya kaita gidan su, ya ce ta shiga ta gaisa da baba mintuna goma ta fito, saboda ya lura shi ne kullum yake kiranta a waya, yana tambayarta ya jiki.Baba ya din ga murna, ganin ta warware, baba da kansa ya rakota, suka gaisa da Al’amin, ya yi ta yi musu fatan alkhairi, da fatan samun wani rabon mai amfani jauhar ta yi shiru, shi kuwa ya amsa da Amin.Ba su da wurin zuwa, ya cigaba da zagaye da ita, suna tafe suna shan iska, ya saya mata kayan ciye-ciye, su rake, awara, dafaffen ƙwai kasancewar dama ba iya cin abinci take yi ba.Har wurin sha daya sannan suka koma gida, ya ci abinci.Ganin yana ta kaiwa da komowa tsakanin falo da tsakar gida, bayan sun yi shirin kwanciya, ya sanya ta gane shaye-shaye yake son yi.Ta kalleshi ta ce “Master ka je ka sha, amma kaɗan dan Allah, ba da yawa ba, kar ka bugu” ya ce “To”Ya fita tsakar gida yayi abun sa ya gama, tana jin sa ya shiga ɗakinsa yana wanka, ya fito ya saka turare ya nufo ɗakinta, duk da yana ɗan warin sama-sama amma ƙamshin turaren ya hana warin yin tasiri.”Ba ki yi bacci ba?”Ta ce “Ban yi ba jiranka nake, na san ko na yi sai ka tashe ni””Allah sarki madarata” yayi maganar yana rungumeta, ya kwanta da ita a jikinsa.”Wace sana’ar ki ke ganin zan fara?””Ka yi tunanin ko kala uku ce, sai mu yi addu’a Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi “Yayi ajiyar zuciya ya ce “Babu laifi””Masterna, kai zaɓin Allah ne a gare ni, na gode Allah da bai sanya ni cikin masu yi masa butulci ba”.Ya ce “Ni ɗin?”Ta jinjina masa kai. Nan ta bashi labarin hafsa, ya ce “Allah ya ƙara, alhakinki ne ai, daga har ke turin jeka ka mutu suka yi mana mussaman ke, Allah ya ƙara””Master yayata ce fa””Koma wacece, ai Allah ba ya barin zalunci”.”Duk da haka master””Ni yanzu dan Allah da gaske kina jin daɗi rayuwar da muke yi a haka?”Ta ce “Gaya mini matar da aka taɓa goyawa a tarihi, aka yi tafiyar da aka yi da ita a baya, saboda ba ta da lafiya? Gaya mini matar talakan da ake ajiyewa masu kula da ita? abubuwa da dama da mata suka rasa a gidan aure ni na samu”.”To ai wannan duk ba wani abu bane ba a kan wanda ki ka din ga yi mini, dan Allah kina jin daɗin zamanmu a haka? Just recently kin kusa rasa ranki saboda ni?”Ta ce “Ba laifinka bane ba ai” ya yi murmushi cikin jin nishaɗi, yake ƙoƙarin canza hirar zuwa wani abu daban”.”Master””Mmm””Ban taɓa jin ka ce kana so na ba, ko dai kara kawai ka ke yi mini, saboda halaccin da kake iƙirarin na yi maka?””Nima baki taɓa gaya mini ba, kuma ina yi a aikace ai, ba dan haka ba, babu wanda ya isa ya saka na zauna da ke ai”.Tana dariya ta ce “Sai abinci””Ki kiyayeni da abincin nan, kina takura mini fa”Ta shafa bayansa cikin shagwaɓa ta ce “Ba ka ce ba””Me?””Ka na so na””Yanzu dai jirani tukuna, na gama caji, koma menene ya biyo baya”.”Ba zaka yi cajin ba, sai ka gaya mini””Yanzu na tashi na yi waje, zan je na yi wanda na saba, na manta komai, yanzu zaɓi ɗaya””Ni zaka yi wa wayo ko?””A’a ba wayo zan yi miki ba, zaɓi na baki”.Da safe jauhar ta fito falo, ta tarar da Al’amin a kan kujera, ta ce “Master da me ka yi wanka ne a banɗakina?””Sabulu””Wanne?””To ai abubuwan naki ne da yawa, kuma kina bacci kawai na ɗauki na wata roba, na zuba a soso””Master feminine wash ne fa”Ya kalleta ya ce “Me ke nan?””Abun kama ruwa ne, dan Allah yayi kama da abun wanka?”Al’amin ya ce “Kai, wallahi tsirfarki tayi yawa, kama ruwan ma, sai an yi masa wani abu, to sai ki din ga rubutawa a jikin robar”Cikin shagwaɓa ta ce “Gaskiya sai ka saya mini wani, dubu uku fa na saya”.”Iyee dubu uku, ke fa wasu lokutan kin iya damfara, dubu uku, wannan abun ne dubu uku, car wash ne fa””Morning fresh ne, wai car wash kuma yasin sai ka biya ni, ina jin daɗin amfani da abuna fa, kai da ba a gyarawa ka din ga lallaɓowa””A daina gyarawar, a bar mini abuna a haka, ko kuma ki karɓi car wash””Sai fa ka biyani, wuyatta na soya maka wainar fulawa da zoɓo mai sanyi, sai ka zazzage mini komai na aljihunka””Ai dama kin saba cin zalina, ki kwashe mini kuɗi”***Tun sassafe jauhar ta shirya, kasancewar yau za su tafi tofa, gidan Hajiya, duk da ya ce wuni kawai za su yi da yamma su dawo gida, ba ta damu da hakan ba, tun da dai ya amince za su je ɗin.Ta zata tafiyar mai nisa ce sosai ma, sai dai ba su daɗe ba suka isa garin, kwatancen babu wahala, suka isa har gidan Hajiya.Da ta amsa sallamar su ba ta gane su ba, sai daga baya ta gane Al’amin.Cikin hanzari ta tashi tana yi musu sannu da zuwa.”Al’amin, dama zaka tako ka zo in da nake?””Tun da ke kin watsar da ni ko?”Ta ce “Ba haka bane, ku shigo””Amarya, ki yi haƙuri ban sake zuwa ba, ina ta fama da ciwon ƙafa, kuma ina tsoron wulaƙancin matar mahaifinka, ko lokacin bikinka, ba ka ga abun da ta din ga yi mana ba, mahaifinka ma haushina yake ji, shiyasa na janye jikina daga gare ku”Jauhar ta ce “A’a hajiya ki yi haƙuri, ai laifin wani ba ya shafar wani, mu dai zamu din ga zuwa muna neman albarka””Allah sarki, aure mai gyara mutum, yanzu a dalilin auren ya sanya ka zo in da nake”Al’amin ya ce “Eh, ba dan ta matsa ba ba zan zo ba gaskiya, tun da kema ba ƙaunata ki ke yi ba”.Jauhar ta ce “Master ya haka kuma?””Ba ƙarya nayi ba, ki ke zare mini ido”Sai hajiya ta kama kuka, ta ce “Wallahi da gayya ba zan yi haka ba, ina son ‘ya ta ina son ku, amma an yi mini iyaka da ku, kusan kullum sai na yi kukan abun da mahaifinku yayi mini a kanku”.Jauhar ta ce “Dan Allah hajiya ki yi haƙuri, ki yafe musu, ke ce makwafin uwa a wurinsa dan Allah ki daina kallon abun da suka yi miki”.Al’amin ko a jikinsa, dan ita kanta tsohuwar haushinta yake ji, yadda laifin abbu ya shafe su a wurinta.Daga baya kuma cikin hikima, jauhar ta din ga jan su da hira, kasancewar ranar kasuwar garin take ci, har kasuwa suka je sayen ƙwan zabi, Hajiya ta haɗa wa jauhar sha tara ta arziki ta ce ita da jauhar take jikar, shi kuma ya je ya ƙarata.Yayi mata zancen gonakin mahafiyarsa, ta ce masa “Hayarsu ake bayarwa ana noma, duk shekara ana karɓar kuɗin, mahaifinka bai bani damar zama da shi mu yi magana a kan hakkinka ba, amma kuɗinka suna nan ana tara su, ƙanina ne yake ajiyewa, sai dai ya je Lagos yanzu””Idan ya dawo zan dawo nima””Allah ya kawo ka lafiya, kuɗi ne masu kauri sosai kam”.Sai yamma sosai, sannan suka koma gida.Ana ta kiran sallar magariba sannan suka shiga gida.Da daddare har sun yi shirin kwanciya, Anty zakiyya ta kira jauhar a waya, jauhar ta ɗaga ta ce “Anty lafiya kuwa?””Ban sani ba, wallahi jauhar ba kya tsoron Allah, kina so ki gama da duniya lafiya kuwa?”Cikin tashin hankali ta ce “Anty me na yi, lafiya?””Ban sani ba, yadda mugun abun uwarki ya koma kanta, kema da yardar Allah sai naki ya koma kanki”.”Anty haryanzu baki gaya mini me nayi ba?””Asirin da ki ka yi wa hafsa, gashi an dawo da ita gida, tana ta fizge-fizge tana kiran sunanki, wallahi ki gaggauta karya abun da ki ka yi mata, kafin mu gauraya da ni da ke, baƙar annoba kawai” ta kashe wayar.Cikin tashin hankali ta fita falo tana kuka, ta ce “Master””Yes yaya”Cikin kuka ta ce “Ka tashi ka kaini gida”.”Meyafaru a gidan?””Ka kaini gida kawai, ba zan iya bacci ba, wai an ce ni na yi wa yaya hafsa asiri, wai sai ihu take yi, tana kiran sunana, wallahi ni ban yi mata asiri ba”.Tashi yayi zaune ya ce “In ji uban wa?””Anty ce ta kira ni, dan Allah tashi mu je, wallahi ban yi mata komai ba” tayi maganar tana wani irin kuka.”Na ga alamar sai na taka wa ‘yan gidan nan naku burki a kan zaƙewar da suke yi, ba Zamu je yanzu ba, sai da safe, zan je ni su yi mini bayani”

Ayshercool 08081012143

Back to top button