Labarai

Fatalwar Delu Part 17 End

Fatalwar Delu Part 17 End 

 

🤡 FATALWAR DELU 🤡

 

Part 17 End

 

Kingboy Isah 👑

 

Short story

 

 

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

 

 

Ko da ganin haka sai wannan karen yayi mugun tsalle ya nufo ni da gudu, yayin da itama Fatalwa Delu tayi tsalle sama, sai gata ta dira a gabana, cikin zafin nama ta cafki hannuna gudu tayi wulli da ni gefe, sai gani nayi sama na wulwula cikin matukar galabaita na fado kasa can gefe fuskarta ta hadu da kasa, kafin in yi wani yunkuri karen nan ya yo kaina, nan take ya sa kafafu ya kai mun wani irin yakushi da farcen kafarsa. Ba shiri na kwalla uban ihu, nan fa suka shiga lallasa ni, a duk lokacin da wannan Fatalwa tayi kwallo da ni sai wannan kare ya bini da yago duk sai da ya karkarce mun jiki, A dai-dai wannan lokacin babu abinda nake sai kara da ihu saboda masifar zafi da nake ji. Ana cikin haka Fatalwa Delu ta nuna ni da hannu, nan take na ji wasu irin hannuwa da ba’a iya gani sun shake mun wuya sun dagani sama kafufuna suna reto a cikin iska. Nan fa naji lumfashina yana fita da kyar, ba shiri na fara ihu magana na fitowa da kyar ina basu hakuri hade da hadasu da Allah su kyaleni, domin a matukar firgice nake musamman da ganin suffar Fatalwa Delu.

 

 

 

Wata iriyar dariya Fatalwa Delu tayi kana ta kwarara uban ihu mai matukar kara, sannan ta fara magana murya ba dadi sauraro, “Karya kake yaro, tabbas ka aikata laifi mafi muni a rayuwarka baka cancanci afuwa ko yafiya ba. Inda ka aika ‘yata Surayyah kaima sai kaje wajen yanzun nan ba bata lokaci”. Tana gama fadin haka na ji an kara shake mun wuya, nan take na cigaba da wuntsile-wuntsile ina ihu da kyar ganin lalai kashe ni take so tayi. Har na fara lumshe idanu saboda jigata can kuma ko me na tuna, cikin gaggawa na bude ido na fara karatun Qursiyyu a hankali. Nan take Delu da Fatalwar kanin Surayyah suka saka ihu, dan jin wani irin radadin zafi da ya ziyarce lokaci guda kuma basu san ko daga ina yake ba. Ba shiri ta sakar min wuya na fado kasa a galabaice, a hankali cikin dauriya na mike tsaye domin duk jikina ko ina ciwo yake, karatun na shiga yi da dukkan sauran karfin da ya rage mun, murya a shake amma haka nake karanto duk ayyar da ta zo bakina, ba shiri su Delu suka fara sakin ihu suka durkushe a wajen. Ganin hakan na lallaba a hankali har kusa da su ina cigaba da karatun da dukkan karfina ina kuma tofawa a kansu, nan take Delu da yaron suka fara bani hakuri suna fadin in yafe musu sun tuba zasu daina zalintar mutanen kauye.

 

 

Nura kuwa ko sauraronsu baiyi ba ya cigaba, ba’a dade ba sai gani yayi jikinsu ya kama da wuta yana ci, ai kuwa ya cigaba da kara kaimi wajen karatun yayin da su kuma suka fara kara mai matukar karfi suka mike suna bige-bige domin kashe wutar jikinsu amma ina. Ana cikin haka da Fatalwa Delu ta gane lalai-lalai mutuwa zatayi, sai ta tsaya tsaye cik! Duk da wuta na ci a jikinta ta fuskanci Bukar hade da daga kai sama ta kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya. Daga bisani kuma ta fashe da kuka kana ta ce, “Lalai yaro kayi nasara a kanmu, amma ba yinka kanka bane, tabbas abinda kake karantawa ne. Na tabbata in da ace mutanen kauyen nan sunyi riko da irin abinda kake karantawa to da ba muyi galaba a kansu ba, haka zalika kaima da ka shagala da rokonmu baka gano dabarar yin addu’a ba da tuni ka bakunci lahira. Amma yanzu ma ba kyaleka zanyi ba, domin kuwa yadda zan mutu kaima dole ne ka mutu”. Tana fadar haka na ga ta nufo kaina a guje, ai kuwa na juya da nufin in tsere amma ina, yanayin ciwokan da ke jikina na kasa gudun.

 

Fatalwar Delu Part 16

 

Don haka tana karasowa ta sa jikinta tayi mun wata irin bangaza wacce ta sa nayi sama kana na fado kasa ina mai kundun bala a kasa na mirgina, nan take wutar idanunanta dauke, tun ina jiyo ihun su har na daina ji daga nan kuma ban sake sanin abinda yake faruwa ba. Farkawa kawai nayi na ganni kwance cikin daki, da kyar na yunkura na tashi zaune da kyar ina karewa jikina kallo, hannuna an yi mun dauri da alamu karaya ce, dukkan jikina kuma bandeji ne hakan na nufi naji rauni ba kadan ba. Dakin da nake na shiga karewa kallo na tabbata wannan ba dakin Nura bane, Sallama naji anyi an shigo dakin, na daga ido ina kallon mai sallamar Hamsa’u ce yar Mai Gari, tana ganina zaune ta fita waje a guje tana fadin “Mama ya tashi wallahi ya farka”. Ai kuwa ba dadewa na ga sun dawo tare da matar wacce ga dukkan alamu itace mahaifiyar tata. Sannu suka shiga jera mun ina binsu da yawwa ni har lokacin ban karasa tabbatar da abinda ya faru ba, zuwa yanzu dai na tabbata a gidan Mai Gari nake ganin Hamsa’u.

 

 

Ba jimawa aka sanarwa Mai Gari tashin nawa cikin dan lokaci kankani ya taho tare da wasu da suke kofar gida tare. Nan fa suka nuna matukar farin ciki da tashin nawa, inda a nan suke shaida min fiye da awa ashirin da hudu ina kwancen nan tamkar ba rai a jikina. Wai sai da suka nemo likita ne ya tabbatar musu cewa ina da rai sai dai doguwar suma. Bukar na tambaya nan Mai Gari ya shaida mun cewa shima Bukar yana gida yana jinya domin ya sama raunuka sosai a jikinsa sai dai bai karye ba. Na so ace na je naga halin da yake ciki amma ba dama. Bayan na tambayi Mai Gari ta yadda aka samomu nan take ya fari bani labari kamar haka, ya ce, “A daren ranar da kukayi tafiyar nan gabaki dayanmu ba muyi bacci ba saboda fargabar abinda zai faru, ga Hamsa’u da har a lokacin bata daina zabure-zabure ba tana neman tashi ta zafga a guje, don a lokacin har daureta sai da mukayi a cikin dakin ganin tana neman fin karfin wanda suke rike da ita. Ana cikin haka can wajen karfe hudu na dare sai gani mukayi Hamsa’u ta daina sambatu da mike-mike da take nan take bacci ya dauketa. Lokacin da safe sai mu ka ga Hamsa’u ta tashi garas ba wata matsala a tare da ita, wannan yasa muke zaton kunyi nasara a tafiyarku muka cika da murna.

 

 

Amma sai murna ta koma ciki bayan ganin har wajen karfe 7 a cikinku babu wanda ya dawo, ba kai ba Boka ba Bukar. Wannan ne yasa hankalinmu ya tashi baki daya muka hadu dattijai ciki harda Baban Bukar, da wasu matasa muka nufi gidan Boka domin ganin ko shi ya dawo kune baku dawo ba. A lokacin da mukaje gidan Boka sai muka samu dakinsa rufe daga ciki, nan take mukaje muna ta kwankwasawa amma shiru ba’ayi magana ba balle mu saka ran za’a bude. Ganin anki budewa yasa na umarci wasu matasa suka balle kofar ta langa-langa, suka kutsa kai cikin dakin. A nan kuwa suka hangi Boka kwance saman katifa ya kudundune kamar mai jin sanyi yana karkarwa, wannan matasa sukaita kiran sunan Boka amma yaki amsawa sai ma karkarwar da yake ta karu, don haka suka yace bargon da ya rufa da shi, ko da suka yace sai Boka ya tashi zauna a tsorace ya dingi kallonsu daya bayan daya yana kwala uban ihu yana fadin, “Fatalwa Delu kiyi mun rai, ki yafe mun wallahi fadan nan ba dani ake ba. Laifina daya jifarki da nayi da laya kuma kin rama”. Baki daya mutane basu fahimci me yake nufi ba an dai gane cewa a tsorace yake, nan dai an dau lokaci kafin Boka ya dawo hayyacinsa.

 

 

Lokacin da muka tambayi ina kuke sai ya ce ai duk kuna can Fatalwa Delu ta kasheku shima da kyar ya sha. Ko da jin haka tuni hankalin kowa a cikinmu ya tashi musamman mahaifin Bukar, nan dai muka tasa Boka gaba domin ya kaimu inda ya baroku amma ya kafe ya nace shi fa ba zai sake bin hanyar nan ba ko yanzu da rana. Ya dai fada mana kusa da makabarta ne, idan muka je wai zamu ga gawarwakinku amma shi ba inda zaije. Haka kuwa akayi muka runkuta da gaggawa muka nufi hanyar makabarta, Bukar muka fara cin karo da shi kwance a matukar galabaice yana fitar da lumfashi sama-sama. Nan muka shiga tambayarsa inda kake amma ina babu halin magana a wajensa, don haka matasa suka bazama cikin dajin dakyar aka ganoka kaima a kwance tamkar matacce haka aka daukkoku. Lokacin da aka kawo ka nan sai aka kira likita ya zo ya dubaka sannan ya sa magani a wasu ranuka na jikinka harda karaya da ya gano a hannunka dan haka muka nemo mai dori ya doraka. shine ma ya tabbatar mana da cewa baka mutu ba”.

 

 

Ko da naji haka sai na sauke ajiyar zuciya hade da mika godiyata ga Allah domin shi ne ya ceto ni daga hannun shedanun aljannun nan. Nan nake shaidawa Mai Gari abinda ya faru tsakaninmu da Surayyah da kuma Fatalwa Delu, ba karamin farin ciki suka shiga ba jin cewa na hallaka su Fatalwa Delu yanzu shikenan garinsu ya fita daga barazanar fitowar dare. Hakika sunyi matukar farin ciki domin wannan Fatalwar ba karamin koma baya ta sa garin nasu yayi ba a ‘yan shekarun nan, don haka suke matukar jin dadi na cewa yanzu komai zai dawo dai-dai. A ranar na kira mahaifana na shaida musu abinda ya faru daga farko har karshe, na bawa mai gari shima ya dora musu da biyani don haka washe garin ranar sai gasu sun zo garin harda kanina suka zo. Boka kuwa ba karamin mamaki yayi ba a lokacin da ya zo ya sameni a raye, ko da na bashi labarin abinda ya faru sai ya cika da matukar al’ajabi. Nan na shiga yi mashi wa’azi a kan ya saki duk wani tsurkulle ya kama Allah, ya kuwa ji wa’azin domin shi ya ga abinda ya gani. Ya ga mutuwa karara yayin da abubuwan tsafi da yake takama da su suka kasa cetonsa, don haka yayi alkawarin daina Bokanci ya ce ma zai shiga neman ilimin addini. Ba shi ba hatta ‘yan garin Mai Gari yayi alkawarin nemo fitattun malaman addini domin su zo wayar da kai kana a samu a gina makarantar addini. Domin duk rashin ilimi shine ya jawo abinda ya faru har suka kashe Delu daga baya kuma suka kasa kare kansu daga sharrin aljannun da sukayi fatalwarta.

 

 

A takaice jikin Bukar yayi sauki har ya fara zuwa wajena dake na fishi dakuwa ya rigani fara fita gashi ni harda karaya a hannu. Kafin iyayena su koma Mai Gari yayi alkawarin bani Auren Hamsa’u idan har ina sonta da gaske. Na kuwa karba hannu bibiyu amma na roki mai gari a jinkirta auren har in sama lafiya in kammala shiri tukun. To wannan dai shine karshen labarin ziyarata garin Gangare wajen abokina Bukar. Duk da kasancewar na sha matukar wahala, amma dai na tsira da riba biyu, na farko nayi sanadiyar yayewar Annoba a garin, na biyu kuma na samo matar aure. Abokan Nura da yake ba labarin suka jinjina kai hade da cewa, “Tabb lalai Nura ka ga rayuwa, amma na so ace Fatalwa Surayyah bata mutu ba, da munga inda ake aure tsakanin Mutum Da Fatalwa”. da jin haka suna Kyalkyale da dariya. 😅😅😅

 

 

To Alhamdulillah a nan nake kawo karshen gajeran labarin Fatalwa Delu

Madallah da jimirin bibiya

 

 

Masu jiran Littafin Aljanar Fatima Book 3 Ku dan kara jira kadan, a halin yanzu tabbas ina busy ba zan sama damar rubuta dogon labari ba. Amma da zarar na sama dama in sha Allah zaku ganshi a bazata. Na ku har kullum (King Boy Isah).

 

Fatalwar Delu Part 16

Back to top button