Hausa novels

Wace Ce Ita (Who Was She) Chapter 78 Complete Novel

*WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)*

                 Unique Barakancy🌹

SEVENTY-EIGHT📍

A hankali ya zare bakinsa daga nata amma be janye daga jikinta ba, kama haba sudais daya saki baki yana kallonsu yayi yace;
“Dama nasan za’a rina shiyasa nace bari inyi sauri in shigo kafin su mami su karaso, toh wallahi kayi takanka gasunan zuwa”…..
Sudais na fadin haka ya fice, tsaki deen yaja sannan ya janye daga jikinta, dawo da kallonsa kan wet lips dinta daya jikasu da nasa yayi yasa hannu ya gogeshi tsikar jikinsa na tashi kamar ba yanzu ya gama lashesu ba, dauke kai yayi ya fara tattara mata gashinta daya hargitsa sannan ya maida mata da hularta daya zame, sai da ya kara saukar mata da rigarta kasa sosai yanda ya rufe har kafa sannan ya fita daga dakin, kicibus sukayi da umm da mami dake kokarin shigowa, bece musu komai ba yabi ta gefensu ya wuce saboda yasan idan ya yayi magana tsap zasu gane halin da yake ciki….
Sudais na ganin fitowarsa ya taso ya samesa yana masa dariyar shakiyanci, sai da ya gama dariyarsa sannan yace;
“Kai duk warning din da aka baka baka dauka ba ko, saboda jaraba yarinya na kwance a gadon asibiti bazaka kyaleta ba, wallahi ka bari mutanennan suka kamaka zakayi bayani”…..
Unexpectedly sudais yaji naushi a bakinsa, dafe bakin yayi yana kallon deen daya daure fuska yana harararsa…..
“Eh in baka kiyayeni ba wataran sai na cire maka bakin gabadaya, akanme zaka kallan min gashin mata? Dakaga muna having husband-wife moment meyasa bazaka fita ka fadi duk abinda zaka fada daga waje ba?”….
Cewar deen murya a dishashe….
Kwafa sudais yayi yace;
“Ba lefinka bane lefina ne danazo na ceceka na kawo maka labari amma gobe bazan kuma ba, kuma idan na kalli kanta ai kan kanwata na kalla, ga ta da gashi me kyau masha Allah kamar in taba nima”…

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Ya karashe cikide zolaya…..
Wayam kawai yagani babu mutum a gurin, tuni deen yayi gaba abunsa, binsa a baya yayi yana basa hakuri shi wallahi wasa yake shi bema kalleta ba, amma kememe deen yaki kulasa badan besan wasan yakeyi ba, sai dan zuciyarsa bazata iya daukan irin wannan wasan ba shiyasa gwara ya taka masa burki tun wuri, rashin kulasan dayayi ma ba karamin daurewa yayi ba, ya tabbata da wani ne ya fadi haka ba sudais ba kila sai anbasa gado a asibitin amma saboda sudais ne shiyasa ze nuna masa bacin ransa ta haka yanda next time baze sake masa irin wannan wasan ba……

Three days later…..
Kwana uku kachal ne amma deen ganinsa yake kamar shekara uku, a cikin kwana ukun nan babu wanda yayi bacci me dadi a cikinsu musamman deen daya nemi ya koma gidan jiya dukda ya samu abinda yakeso, sosai baby tee ta burkice musu fiye da yanda basa tinani, data farka sunan khaleel take kira tayita fuzge fuzge sai an nemo mata shi ita tasan be mutu ba, babu kuma wanda ya isa ya lallasheta taji sometimes inta fara wasu surutan kamar wata zararriya, bappa yayi nasihan yayi nasihan yayi fadan yayi fadan ya fada mata mahimmanci tawakkali amma duk a banza dan ko nitsuwa ta sauraresa batayi, deen kuwa ta mai dashi kamar wani dodo dan kwata kwata batasan ganin koda me kama dashi ne, daya shigo takesa kuka har sai ya fita, in dai ya tabata to tana bacci ne amma idan idonta biyu dan yatsanta be isa ya rike ba, abun nata har tsoro yake basu, cikin ikon Allah wani likita guda daya kawai take kulawa, shi kadai yake bata abinci ko magani ta karba sannan shi kadai yake iya lallaba musu ita, wannan abun shi yake dagama deen hankali because it’s so disheartening kaga matarka bata kula kowa sai wani kato, da farko rikice musu yayi wannan likitan baze kara shiga ba bappa yayi masa fada sosai akan lafiyarta suke nema yayi hakuri na dan lokaci ne Insha Allah tana dawowa daidai shikenan, dole ya hakura yabi abinda bappa yace dukda yanajin zuciyarsa na dab da bugawa, sosai su umm da mami suke kwantar masa da hankali saboda yanda jininsa yake hawa kullum cikin treatment yake shima, sudais ma yana iya bakin kokarinsa gurin kwantar masa da hankali don tun a washegarin ranar da sukayi fada suka shirya, abu daya yasa sudais yake masa shine bin bayan likitannan duk sanda ya shiga dakin da take, labewa yake ta windown baya yana kallon duk abinda ke wakana, so far kuma sudais betaba kawo masa wani labari ba apart from abinci da magani da yake bata…..
Washe gari khaleel ya cika kwana bakwai da rasuwa, fortunately baby tee sai ta tashi jikin nata da dan dama dama….
Misalin karfe goma na safe bappa yashigo amenity din da deen yake, zaune ya samesu shi da sudais suna dan tattaunawa, gaishesa sukayi cike da ladabi sannan ya samu guri ya zauna yana fadin;
“Ya karfin jiki saifu?”….
“Alhamdulillah bappa”…
“Masha Allah, ka dai rage saka damuwa aranka”…..
“Insha Allah bappa”….

Also Download Ɗaudar Gora Page 8 By Billyn Abdul

“Ita rayuwa dama haka take cike da kaddarori, zara’u ce ma abun tausayi dan tinda tazo duniya take ganin jarabawa iri iri badan Allah baya sonta ba saidan haka allah ya tsara kuma hakan shine mafi alkhairi a rayuwarta, muna dai fatan watarana komai ya zama labari Allah ya bata lafiya me dorewa kuma”….
“Ameen ya Allah”…
Suka hada baki wajan fada shi da sudais…
Gyada kai bappa yayi yace;
“Daga gurin zara’un nake yanzu, alhamdulillah jikinnata da dan dama dama yau dan har hira muka dan taba, na fadamata yau sadakar bakwai na ibrahim khaleel ko zata iya zuwa ta musu gaisuwa tace zataje saboda haka yanzu kashirya ku tafi tare, jamila da fatima suna chan suma, nima yanzu na dawo”….
Girgiza kai deen yayi yace;
“She won’t like that bappa, kawai ka kaita da kanka”…..
“A’a ita da kanta ta tambayeni ina kake, nace mata kananan ko inkiraka ku tafi tare ne tace eh, ka shirya kawai kuje sudais ya rakaku, Insha allahu sauki ne ya samu”……
“Allah yasa bappa”….
Deen ya fada zuciyarsa cike da shakkun itace ta tambayesa kamar yanda bappa ya fada, saidai kuma yasan bappa baze masa karya ba…..
Sai da bappa ya kara jaddada musu su tashi su shirya su tafi sannan ya koma yacema ummi ta shirya baby tee dayake ita suka bari a gurinta…..
Har bakin mota ummi ta rakata, saif na hangosu ya bude mata gaban mota saboda shi zeyi driving, haka kawai yau yaji yana sha’awar driving din dukda sudais yaso ya karba yayi, ajiyar zuciya deen ya sauke ganinta sanye da hijabi har kasa, bece mata komai ba ta shiga yaja motar….
Shiru shiru tana jira taji ya mata magana taji shiru, kasa daurewa tayi ta juyo ta kallesa tana turo baki tace;
“Wai bazaka kulani ba?”…..
Banza yayi kamar be jita ba, ta sake fadin;
“Ni zaka share yaya saif?”…..
Kin juyowa yayi ya cigaba da bawa banza ajiyarta, ganin yanda ta damu sudais yace;
“Rabu dashi, in baze kulaki ba ai ni zan kulaki”…..
Sai a lokacin ta juya ta kallesa a nitse tace;
“Yaya sudais ina wuni?”….
“Lafiya lau kanwata, ya jiki?”….
“Alhamdulillah”…..
Shiru ne ya sake biyowa baya chan baby tee ta juyo ta kalli sudais tace;
“Toh saboda me baze kulani ba?”……
Murmushi sudais yayi yace;
“Wai saboda kema bakya kulasa”….
Da zuciya daya tace;
“Toh ba gashi ina kulasa ba?”…..
“Eh jiya da shekaranjiya yake nufi, kinata kuka bakyaso ya miki magana”…..
“Ni banyi haka ba”…..
Dan jimm sudais yayi a ransa yace toh kodai batasan tayi bane sai kuma yayi karamin murmushi yace;
“Rabu dashi dakansa ze kulaki kinji yar kanwata”….
“Toh”….
Tafiya suka cigaba dayi kamar babu deen a cikin motar, ga mamakin sudais yaga ta dora hannunta a kafadar deen a marairaice tace;
“Nifa sai ka kulani”…..
Ture hannunta yayi yayi focusing akan tukin da yakeyi….
Hannunta ta sake maidawa kan kirjinsa tana masa tafiyar tsutsa a kirji, besan sanda ya saki steering motar ba, motar ta fara controlling kanta kamar zasu kife, da kyar ya taka burki saura kadan su daki wata mota, a fusace ya juyo ya daka mata wani mugun tsawa yace;
“Baki da hankali ne zaki kashemu?”….
Kuka ta fashe dashi tace;
“Toh ba kai bane kaki kulani”……
A fusace yace;

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

“Lokacin da kika nuna wani gardi ya fiye miki kowa bakisan kinaso in kulaki ba, toh uban me kikeso na miki yanzu?”…..
“Boss check your phone”….
Cewar sudais daidai da text message na shigowa wayar deen, saki yaja sannan ya bude message din, yana gama karanta message din ya juyo ya hayayyako ma sudais….
“Kutumar ubanka sudais! Nace kutumar ubanka! Inda ta kashemu zanga da bakin da zakace min ba haka ake lallaba mace ba”……
“Allah ya baka hakuri”…
Shine abinda sudais yace yaja bakinsa yayi shiru…..
Juyowa kanta yayi ya hada girar sama da kasa yace;
“Zakimin shiru ko sai na wurgaki ta window”…..
Batayi magana ba ta cigaba da kukanta…..
“Fita ki koma baya, sudais dawo gaba”…..
“Ni bazan koma ba”…..
Ta fada cikin shesshekar kuka…..
Kwafa yayi yaja motar suka bar gurin, basu kara minti biyar ba suka isa gidansu khaleel, sudais ne ya fara fita deen yayi saurin sawa motar lock, hannu baby tee ta dora a handle din motar da niyar budewa ta fita itama tajita a rufe, kallonsa tayi taga ya lumshe ido, dauke kai tayi ta cigaba da kukanta….
Ta gefen ido yake kallon duk abinda takeyi sosai kuma kukanta ke karyar masa da zuciya saidai bayasan ta maimaita irin abinda tayi dazu, da watace tayi masa irin wannan shirmen ya tabbata sai ya faffala mata maruka ya kuma karya kasusuwanta, amma dayake itace ko tinanin ya tabata beyi ba…
Kwantar da kujerarsa yayi ya dan kishingida sannan ya dauketa chak ya dorata a jikinsa, lumshe ido yayi yanajin saukar hawayenta akan kumatunsa…
A hankali kamar bashi ya gama mata masifa ba yace;
“Stop crying baby girl”….
Kamar jira take ta kara karfin kukanta….
Hannu daya yasa yana dan bubbuga bayanta dayan kuma yana share mata hawayen, sai da yaga kukan ya tsaya sannan yace;
“Ina son kamshin turarenki zahrah, zaki sammin?”…..
“A’a”….
“Saboda me?”….
“Kana min masifa kuma baka kulani”..
Dogon hancinta yaja fuska ba yabo ba fallasa yace;
“Is that why you’re trying to seduce me? Saura kadan fa muyi accident, don’t try that nonsense again!”….
Bata fuska tayi tace;
“Toh ba kai bane inata magana ka ki kulani ba”….
“Ke yakamata in cewa bakya kulani, do you know how much you hurt me? For the past three days zahrah ko ganina fa bakyasan yi saidai wanchan likitan kawai kike kulawa, ”….
“I don’t know who you’re talking about, ni bance banasan ganinka ba”…..
Tabe baki yayi yace;
“Super story”…..
“I’m serious, ni inata nemanka banganka ba”…..
“Naji duk ba wannan ba, just promise me bazaki kara kula kowa ba sai ni, promise me ni kadai zaki yadda ina baki abinci da magani, if you can promise me that yanzu zamu shirya”….
“I promise!”…
Rungumeta yayi wani farin ciki na mamayesa yace;
“Thank you prettiest”….
Knocking sudais ya musu saboda shirun da yaji yayi yawa, sakinta deen yayi yace ta tashi su shiga ciki, har zata koma seat dinta yace kawai ta fita tanan, sudais na tsaye yaga ta fito ta driver seat , ba’a dade ba yaga deen shima ya fito, mamaki ne ya ishesa ganin ya kamo hannunta kamar babu abinda ya hadasu, gaskiya shiyasa ake cewa ba’a shiga fadan mata da miji dan sai kaji kunya, binsu yayi a baya suka shiga cikin gidan….
Suna shiga aka fara nuna baby tee a matsayin wacce khaleel ze aura, mutane sukaita mata gaisuwa, mamaki ne ya kashe deen yanda familynsa suka santa haka sai kuma ya tina tayi zaman gidan, a haka har suka isa main parlour din mahaifiyarsa inda yawancin familyn mahaifiyar khaleel suke, a chan suka tarar da mami da umm dama bappa yace musu suna chan, suma sunyi mamakin ganinsu tare dan kowa yasan yanda batasan ganin deen akan kowa, har gaban mahaifiyar khaleel deen ya raka baby tee ta mata gaisuwa da sauran mutanen dake dakin, rukota tayi tana kuka tace;

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

“Fatima kinga khaleel ya tafi ya barmu, tabbas kinyi rashin masoyi fatima, sannu fatima munzo mun dubaki nasan bakisani”….
“Wai dagaske khaleel ya rasu?”…..
Baby tee ta tambaya har cikin zuciyarta…
“Ya rasu fatima, Allahn daya fimu so ya dauke abunsa saidai muyi hakuri”….
Sai ta dora da bata labarin yanda aka kawo gawar khaleel jina jina da yanda accident din ya faru….
Fashewa da kuka me ban tausayi baby tee tayi tana rike da kanta, sai yau ta tabbatar da mutuwar khaleel tinda taji daga bakin mahaifiyarsa, shiru parlourn ya dauka babu wanda be tausaya mata ba, ganin yanda take rike kai yasa deen ya dagota sannan ya rungumeta yana bubbuga bayanta, dauke kai umm da mami sukayi kamar basa parlourn….
Kankamesa tayi tana kara fashewa da kuka tace;
“Shikenan khaleel ya mutu”….
Bubbuga bayanta ya cigaba dayi yana fadin;
“Sshhhh ba kuka zaki masa ba addu’a zaki masa”….
Kallo ne ya dawo kansu anata mamakin wayeshi a gurinta daya rungumeta haka a gaban mutane, a iya saninsu kuma basusan tanada dan uwa ba, saboda yawan zancenta da khaleel yakeyi sunsan abubuwa dayawa a kanta dama chan wasu kuma sun santa a gidan…..
Sallamar da akayine ya dakatar da deen daga bubbuga bayanta da yakeyi, dagowa yayi sukayi ido hudu da likitan dayake kula da ita, tsareshi da ido yayi yana mamakin abinda ya kawosa, wani irin bugawa kirjinsa yayi jin abinda baby tee tace!…..

 

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Back to top button