Mejo Najeeb Page 7 By Autar Alheri
“Tace Kai najeeb rabida ita Hakan karka K’ara dukankata kajiko Kabarta…Chak yatsaya da marinta dayayi niyyaryi yasauke hannunshi Yana huci…itako wani mugun kallo mama tawatsa mata kamun tace “Maza kibarnan kamun tinanina yacanja akanki shed’aniyar yayinya kawai..aitinkamin mama tarufe Baki tamik’e dasauri zatabar wurin Amma Takoma fad’uwa sabida tabugu sosai a kafarta alokacinda yake ball da ita, ihu tasaka sekuma Tayi saurin rufe bakinta tana zare Ido. Shikuwa najeeb inbanda tafarfasa babu abunda zuciyarshi keyi, cikin k’unarda yakeji aranshi yake nunatada yatsa yace “daga yau karna k’ara ganin fuskarki a part d’ina wlh ballema kisamudamar zuwama abokanaina da banzan iskancinki mikike tinanine? sud’in Y’an iskane marasa class dakamun kai kome? Tobarakiji ingaya Miki dukkanin abokaina babu D’an akuya acikinsu balle kizo kinamusu tallar kazamun jikinki wanda keda sandar slucer bakuda banbanci Humm nasan duk wannan iskancin kinayine sabida general aliyu tokisani manyan baby’s ma Basu isheshi kallo ba belleke inbanda asara mima namuji zeyida mace matanda babu komai acikinsu se ciwonkai datarin k’azanta balle ballagaza irinki…shiru yayi sabida hannunda mama tad’aga mishi batareda tace komaiba tajuya tabar part d’in sa’annan Mansura tabi bayanta akunyace.Rik’oshi general aliyu yayi tareda zaunarda shi yad’auko ruwa acikin Frigg d’in dake parlor yabud’e yad’ora mishi abaki. Bamusu kuwa yakarb’a yasha seda yakusan shanyesu kana yajanye bakinshi Yana sauke ajiyar zuciya. Cikin lallami general aliyu kefad’ar “kayi hak’uri mejo nasan ba Dad’i Amma hukuncin daka d’auka yayi tsanani bazata iya d’aukaba please karage wannan zuciyar ko Umma bazataji dad’in wannan dukan dakayi mataba…ahasale yad’ago Yana fad’ar”bazataji Dad’iba tabarta tazo gunmu ahakan kamar wata karya? Yana gama fad’ar Hakan yamik’e zuwa bedroom d’inshi tareda banko k’ofar cikin dacin rai…da kallo general aliyu yabishi harya b’acewa ganinshi kamun yagirgiza kanshi kawai dumin Allah yasani yanajin tausayin najeeb harcikin ranshi. (To general aliyu mutun da uwarshi da ubanshi gashida abun hannunshi y’ay’an banki kenan💵 Kuma kace Yana baka tausayi🤔to Allah ya kyauta)Sukuwa suna saukowa mama tadubeta awuk’ance tace “Dedekenan najeeb shine maganinki gobema kyak’ara zuwa wurinsu tsirara tana gama fad’ar Hakan tashigewarta bedroom d’inta.. Hajiya Umma kuwa harara kawai ta b’allawa mansurar tareda Jan tsaki tana k’ara Saka autarta ajikinta wadda tatsere tin lokacinda mejo yafara dukan mansurar domin Tayi bala’in firgita. Yayinda dady yamik’e kawai yabar perlor… Munir kuwa seda yazo Dede inda take tsaye yace “yayi Dede wlh Allah yak’ara marar class kawai keta kijanwo hankalin namuji da tsiraicinki Kuma agaban yayanki, Humm aiko kinjawo sosaima kuwa Dan nasan yau datinaninki general aliyu zekwana Kuna soyewa😂 yak’arasa zancen cikin shakiyanci tareda zagata yawuce. Itakam Ummi tana’nan zaune inbanda rawar d’ari babu abunda takeyi domin tasan wannan bala’i ne mansura tajawo musu agidannan gun yah najeeb…..wani Irin kukane yazowa mansura metada hankali Hakan tarushe dashi tanayin Allah wadai da family nata dasuke alak’anta abunda Tayi da general aliyu tayiwa domin itasam ba’akanshi take hariba yayan natadai shine mafalkinta Kuma sabida shi Tayi wannan abun wato MEJO NAJEEB.😱GombeAbakin rafin sukayi tsaye mekamada teku itadai halima dudda cewar ayanzu zuciyarta tacire tsoron maahh d’in Isseta Amma takasa sakewa awurin..itako Isseta cikin farin ciki take kasancewarta awannan wurin domin idan tazo jitakeyi kamar anyaye mata dukkan wani kunci na duniya, cikin tsananin happy kasancewarta anan tabud’e Baki dak’arfi cikin sexy voice d’inta tace maaaahhhh kamar yadda tasaba kiranta….Aiko atake ruwan sukad’auki rugugi sekawai ga wutsiyar jelarta tafito kamun Tayo saman ruwan Baki d’aya tafito, fuskarta d’auke da kayataccen murmushi na farin cikin ganin y’ar tata.Dasauri Isseta ta kwab’e fuska kamar zatayi kuka…maah Bata bari Tayi maganaba tawaro manyan idanuwanta tana kallonta kamun tasake sakin murmushi tace “wai nikam yoshe maryama zata girma ne?🤔 Kodai Sena samu suruki? Tafad’a cikin sakin fuska….Aiko suka shek’e da dariya atare suka had’a Baki wurin fad’ar barkada safiya maahh. “Yawwa barkanku dai y’anmatan maahh. “Murmushi suka karayi atare suna kallonta yadda take kad’a jelar kifinta se abun ya birgesu..juyawa Tayi Taga abunda suke kallo sekawai Tayi murmushi tareda cewa “ya garin yakuma gidanku maryama? Ai Isseta najin wannan tambayar idonta yacikoda k’walla kamar zata saka kuka tace “wlh maah badad’i komai se k’ara lalacewa yakeyi narasa mike damun mutanen gidan kowannensu bana Gane gabanshi balle bayanshi maah wasu sukan nuna tsanarsu gareni a Fili wasu kuwa b’oyewa sukeyi senarasa dawa zan jingina inji sanyi yanzu abun yakai har….ya’isa Hakan maryama maah takatseta kana tad’ora dacewa “duk abunda kenan nasani kuma tabbas bazaki fahimci abunda gidanku kecikiba se gaba Amma inaso kik’ara hak’uri kik’ara kawarda kanki akan komai Kuma kik’ara dagewa da addu’a tabbas tubalinda zekasance garkuwa agareki yana’nan bayya Bada jimawaba kedai kik’ara hak’uri wata Rana se labari Amma tabbas duk ranarda Kwan gidanku zefashe to ze iya kasancewa k’anzantar dazata fallatsawa kowa sedai muce Allah yakyauta… ameen y rabbi suka amsa mata. Kana tace “to maryama kuje kuci abunci seki d’auki kud’in maganin mamarki kuyi sauri kuje yadda zaku dawo dawuri Allah yabata lpy. “Ido halima tazaro kana tace “laa maah ya’akayi kikasan munkaita asibiti? Murmushi maah Tayi domin kawarda tambayar halima tace “kuyi sauri kuje kuci abunci lokeci na tafiya tana gama fad’ar Hakan Takoma warta cikin ruwan kamar Bata wanzu awurinba……Gurin wannan dutsen suka nufa inda Isseta tad’auki kud’i aranar suna zuwa suka samu abunci merai da lpy awurin shinkafa da miyah ga Naman kaji soyayye aciki, atake tsohuwar yunwarda ke cikin Isseta tamotsa Toba itakad’aiba halima ma hakance takasance agareta Aiko suka dirarma abuncin kamar wani ze kwace musu dudda cewar a plate abuncin yake sunaga kamar baze ishesuba Amma sunaci sunaganin kamar ana k’arashi domin babu inda yake raguwa harseda suka k’oshi Sega ruwa awurin sukasha tareda hamdala awurin abun giji kana suka d’auki kud’in dasuka gani awurin suka kama gabansu.A majalisa koyanzu suka samu yah shamsu inda suka bashi sak’on innah tareda kud’in dasuka karb’o awurin maah wanda shikanshi yah shamsu seda yayi mamakin a’ina sukasamu wannan uban kud’in, bedena mamaki ba harseda yatambayesu sedai kafin sukaiga bashi amsa akashafe musu zancen kud’in dukkansu dagasu harshi Hakan yasa suka shiga adedetasu kawai tareda nufar asibitin kaitsaye.Suna zuwako suka samu anbawa wannan mahaukaciyar d’aki itakadai tana zaune kamar yadda tasaba sedai ga abunci agabanta an’ajiye Amma bataciba Tayi shiru kawai tana kallon gefe d’aya….sosai Isseta taji dad’in yadda Taga mamar tata sedai fa taji Bada Dad’i yadda Taga tasaka abunci agaba bataciba Hakan yasa tarok’esu akan subed’e mata zata shiga…bamusu kuwa suka bud’e tinda sunga batayiwa kowa komai tanashiga tazaune tareda dafata tace “mama…ahankali matar tad’ago tana duban Isseta domin tagane muryarta dudda batada cikakken hankali. Murmushi kawai Isseta tayimata tareda d’auko abuncin takai bakinta, Aiko takarb’a tanaci ahankali Hakan Isseta tabata abuncin Nan seda tacinye tabata ruwa Tasha kana tamik’e cikin sauri mahaukaciyar tarik’o gefen doguwar rigarta. Cikin mamaki tajiyo tana kallonta domin Bata tab’a yimata Hakanba se ayau hakan yasa Takoma tazauna domin tagano abunda matar kenufi kenan…tana zama kuwa itako takwanta agefenta. Sudai su yah shamsu da ma’aikatan wurin dukkansu da kallo kawai suka bisu…cikin k’ank’anin lokaci bacci yayi awun gaba da ita se alokacinne Isseta tasauke ajiyar zuciya kana tamik’e tana share k’wallar idonta suka biya duk wani abunda za’abuk’ata kana sukabar asibitin zuciyarta atunkushe..Yauma se kusan magarib sukadawo cikin gari zuciyar Isseta inbanda bugawa babu abunda takeyi domin se ayanzu tatinada abunda yafaru adaren jiya dakuma yau dasafe, cikin tsoro da fargaba sukayi sallama itada halima dakuma yah shamsu kowannensu yanufi nasu gidan Amma fa halima tad’an tsorata da yanayin k’awar tata domin fargabarta tafito Fili Kuma duk abunda ke faruwa agidan tasani sedai wanda Isseta d’in tab’oye mata Kuma Koda batasaniba ay’ankwana kinnan Rakata datakeyi Gurin maah dolizata fahimci akwai wani abun idan Tayi dubada kalaman maahh agareta Amma dai koma minene zata bari dasafe suyi zancen idan Allah yakaimu doline tasan minene Kuma Yakoma b’ullowa arayuwar Isseta yanzu. Dawannan tinanin tashiga gidansu….itakuwa Isseta yau kam kowa babu a tsakiyar gidansu Hakan yasa Tayi alwala tareda shigewa d’akinsu kaitsaye anan duk tasamu y’anmata gidan kowana sha’anin gabanshi…itadai daga sallama Bata Kara cemusu komaiba domin yanzu sosai tashiga tsoron su anty hawwa da anty bilki.Bayan tagama sallah ne jidda tashigo da kwanon abunci ahannunta ta ajiye mata tana fad’ar “anty Isseta gashi inji mama bintu Kuma tace anjima idan akayi isha’i kizo tana namanki. “To jidda kice mata ngd zanzo insha Allah. “To jidda tace kana tajuya tabar d’akin…..itako Isseta abuncin taci sosai kana tawanke bakinta taje tayi wanka harta fito bataga giftawar kowaba dagacikin iyayen nasu, seda tashirya cikin kayanta na bacci kana Tayi sallar isha’i Amma me tana gamawa wani nannauyan bacci yad’auketa batareda taje Kiranda mama bintu kemataba….seda dare yaraba sosai yauma akasake zuwa mata cikin bacci taji ana lalabarta Kuma yau har ansamu nasarar sab’ule mata hannun rigarta inda duk rabin k’irjinta awaje wanda ba cikin bra ba Kuma ahakan ana k’ok’arin k’arasa cire mata rigar…arazane tafarka domin Jin abun Tayi kamar amafalki cikin tashin hankali tashiga Ture wadda kejikin nata tareda k’ok’arin kwatar kanta Amma abun yafaskara, atake danbe yakacame atsakaninsu sedai ga dukkan alamu kowacece tad’anfi Isseta girma Hakan yasa Tasha wahala sosai ahannunta wurin kwatar kannata….kamar daga sama sukaji anty hawwa da zuwaira sunbuga ihu alokaci d’aya suna fad’ar wayyo allah atemakesu kwarto acikin d’akinsu. Hakan yasa wannan matar saurin sakin Isseta tahantsila tafice daga d’akin aguje…Kuma wannan ihun Nasu zuwaira shine yayi sanadiyar fitowar mutanen gidan gaba d’aya ciki kuwa hadda samarin gidan da Abba, gadan gadan sukayo d’akin nasu inda suna shigowa yah Kabir yakunnah hasken d’akin Hakan yasa idon Abba saukan akan…!


