Hausa novels

Zakuna Biyar Page 36 By Princess Teema

Kai tsaye benen su Noor suka nufa, ta hanyar sama ma suka bi. Already Abba ya sanar da daddyn Noor zasu zo, dan haka ya shirya tarba na musamman a garesu.Suna knocking ɗaya aka buɗe masu kofar, uncle ɗan kwalisan mu ne ya fara tarbansu, fuska ɗauke da wannan lallausan murmushin nasu na gado mai kwantar da hankali, yai masu sannu da zuwa, har da riko hannun Harleen yana ƙara masu sannu da zuwa. Ciki suka shigo, a saman sofa suka zauna, ga kayan cima kala-kala an jibga masu dan girmamawa a garesu. Sama Uncle ya haura. Jim kaɗan sai ga shi ya dawo da dikka family, Aunty Luna, Aunty Lusi da daddy. Aunty Lusi akwai izza jama’a, a family ɗin su Noor dik ta fi kowa izza, bata da yawan magana, sai kallo da ido, bata shiga sabgar kowa, kuma ta tsani a shiga nata, amma dik da wannan izza nata tana kallon Abba sai da ta ji faɗuwar gaba, ta gagara haɗa ido kai tsaye da shi.Dik suna sanye da pjs ne a jikinsu, da yake basu jima da tashi daga barci ba. Abba yana daga zauna daddy Noor ya ƙariso ya zauna a kusa da shi, sannan ya miƙa mashi hannu kan su gaisa, Abba bai bashi hannu ba, sai dai ya ce mashi salamu alaikum kawai, daddy Noor bai sa me ya ce ba, ita kanta musabahar ba wai ya saba yi bane, dan ya mutunta baƙin nasa ne yasa ya yi.Abba ne ya ce Harleen ya kawo trollyn da suka zo da shi. Jawo shi ya yi gaban Abba, sai satar kallon Aunty Luna malam Harleen yake ta faman yi, yana wani ɗaure fuska, kaman wanda aka sanya dole…… A mutunce aka gaggaisa, Aunty Luna and Aunty Lusi suka ɗaga wa su Abba gaisuwa. Aunty Luna sai satar kallon Harleen take yi ita ma, hakika ya yi kyau cikin tail coat ɗin nan, kyansa ya sake fitowa sosai da sosai!.A dake Abba ya ce. “A addininmu muna yin sadaki, ba zobe ba, dan haka wannan shi ne sadakin, idan yai masu kaɗan suna iya furta adadin abin da suke so sai a kawo masu, nan da jibi nike son a ɗaura wannan aure”. Babu wasa a tattare da shi yai magana, ga izza kamar shi ne ubansu har daddyn Noor ɗin!. Zuba mashi idanu suka yi. Abba ya kalli Aunty Luna a lokacin da ya buɗe akwatin kuɗin. “Ƴata idan kuɗin bai maki ba zaki iya faɗar nawa kike so” . Ya kai karshe daidai lokacin da yake zuge zip ɗin akwatin. Dollars ne zallah, sai ɗanyen gold guda biyu a ciki…… Ai dikka family babu wanda bai waro idanunsa waje ba ganin maƙudan kuɗin da Abba ya buɗe a cikin akwatin nan, ba su taɓa zatan Khaiza’an’s family suna da wannan kuɗin ba, suna kallon Abba matsayin bai wuci ɗan majalisa a kuɗi ba, ba su kaisa matsayin gwamna bama, basu san ko shugaban ƙasa ba za gwada mashi kuɗi ba.Hakikanin gaskiya ba su kawai ba, har su Faryan sun girgiza da ganin kuɗin nan da Abba ya buɗe, ya ilahi, Harleen da Faryan kallon juna suka yi, a cikin zuciyoyinsu suna tambayar kansu a ina Abbansu ya samu waɗan nan maƙudan kuɗaɗɗe? Ga gold, wannan kuɗi ai zai iya saya masu bene guda a CRYSTAL PALACE in da za’a sayar, sai dai a CRYSTAL PALACE ba’a sayar da gida sai dai ka kama haya!.To dik wannan kuɗin Aryan ne ya baiwa Abba, kun tina dama ya ce zai turo kuɗi, to shi ne ya turo a akwati, kuma wannan gold ɗin Aryan fa cewa Abba ya yi sadakin Rimsha ne ya biyawa Vash ɗan lele, amma kunga Abba da ƙoƙari gold ɗaya ya cire ya bari a gida wai na Rimsha, ya tattaro sauran dik ya kawowa su Aunty Luna dan baya son harkar raini, kada a rainasa! Yana son nuna masu muhimmanci ƴaƴansu, yana so su san ba wai kawai za’a auri ƴaƴansu bane, za’a kula da su ne sosai.”Abba babu komai, ni ba sai ka bani komai ba”. Cewar Aunty Luna, tana magana ta ɗago slowly zata saci kallon Harleen kenan suka haɗa ido da shi, dan shi ma ya ɗago zai saci kallonta. Kashe mashi ido ɗaya ta yi game da binsa da lallausan murmushi. Ai sai ga Harleen ya fara tari, yana neman ruwa. Da sauri uncle ya ɗauko ruwa a bottle, ya buɗe ya zuba mashi a cup ya miƙa mashi. Karɓa ya yi, ya fara sha, sai da ya sha rabi, sannan ya ɗago ya saci kallonta, still shi take kallo tana murmushi. Harara ya watsa mata, ita kuma ta ɗan turo mashi baki kafin ta sake kashe mashi ido ɗaya. “Kuna tinanin zaku sayemu da kuɗi ne kenan?”. A cewar Aunty Lusi, ta yi maganar a dake, bata ɗaukar raini na ce maku. Ɗago idanu a kanta Abba ya yi, take ta ji dik wani kwarin gwiwa ɗinta ya gudu saboda kwarjinin Abba, ƙawar da kanta gefe ta yi, kirjinta na bugawa da karfi, amma ta daure game da sauke ajiyar zuciya.A dake Abba ya ce. “Idan hakan muka so ma zamu iya, amma yanzu dai ba sayan naku muka zo yi ba, sadaki muka kawo!”. Cike da izza babu wasa a tattare da shi yai maganar, ya bata amsa ne dan yaga tana fa ilmi……. Uncle ne ya ce. “Lusi be patient please”…… Miƙewa Aunty Lusi ta yi zata bar wajen, a cewarta ba zata iya tsayawa ba, kun san tana ji da mulki tin da ƴar siyasa ce, gwamna take nema.”Koma ki zauna ayi komai a gabanki!”. Abba ne ya faɗa on a serious note. Ɗago da kallonta a kansa ta yi, sai ta ji ba zata iya ja in da shi ba, ta rasa kwarin gwiwa, dole ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.Daddyn Noor bawan ALLAH shi dai da ido kawai yake bin Abba, to aka ce faɗar da ya fi karfinka sai ka mayar da shi wasa. Su Harleen kam sun san waye Abba, sun san wlh da ya yi niyya sai dai yana zaune a gida yasa a ɗauko mashi family ɗinsu Noor gabaɗaya a kai mashi, har ita mai taƙama da tana neman gwamna ɗin, dik zai sanya a ɗaukesu a kaisu gida, ba zai zo da kansa ba, amma ya daure ya zo da kansa, ai sun samu martabawa sosai.Miƙewa Abba ya yi tare da cewa. “Wannan shi ne sadakin, mu a addininmu ba zobe bane, addininmu ya baiwa kowa ƴancinsa, ya fitarwa kowa haƙinsa”. Ya faɗa yana kallon daddy. Daddyn Noor mutum ne da baya son hayaniya, wlh kamar Noor yake, sai kawai ya bi Abba da ido, shi bashi da damuwa in har yaran nasa suna so ko yau a ɗaura auren.Daidai lokacin grandpa ya sauƙo, ai yana ganin Abba ya ƙara sauri yana dogara sandarsa, tin bai gama sauƙowa ƙasa ba yana faɗin. “Me ya kawoku gidan nan?”. Ai ko kallon in da yake Abba bai yi ba, sai gyara bisht ɗin jikinsa ya yi, ya juya yana faɗin. “Harleen mu je”. Cikin faɗa grandpa ya ce. “Ba zan barku ba, sai hukuma ta shiga tsakaninmu, ba zan hakura ba”……… Ko kallon in da yake Abba bai yi ba, ya wuce gaba, su Harleen ma babu wanda ya kulasa, suka wuce suka fice, sai bala’i yake yi, daddy Noor ya jawosa yana ƙoƙarin rarrashinsa.Abba kam ko a jikinsa, ba dai abin da ya kawo shi ya yi ba? Ai shikenan, bashi da lokacin su grandpa. Suna komawa gida suka isko Ammie da Rimsha suna ta shan hira. Rimsha na ganinsa ta nufesa da gudu tana oyoyo Abba. Da buɗar bakinsa sai ya ce. “Amarya yau kin ƙara kyau fa, ko dai fuskar taki tasan ke amarya ce?”……. Ɗan zazzare mashi idanu ta yi. “Abba amarya kuma?”. Kai Abba ya jinjina mata, ya riko hannunta suka wuce izuwa cikin parlo, a saman sofa ya zauna, Rimsha ta haye jikinsa.Abba na kallon face ɗinta ya ce. “Jikata kina magana da yayanki Vash kuwa?”…….. Ɗan turo baki ta yi. “Ni Abba Yah Vash yanzu ya daina sona, baya kulani, tin da ya zama soja ya zama masifaffe, lokacin da ya zo har marina ya kusa yi, ni yanzu bani ma da numbersa, bamu taɓa waya ba tin da ya tafi”. Ta kai karshe tamkar zata yi kuka. Hannunta Faryan ya matsa ya riko. “Zo mu je ɗaki, kyale Vash ɗin nan, zo mu je mu buga game”……. Da sauri ta bar jikin Abba, ta bi Faryan suka haura sama. Ammie dake binsu da kallo ne ta ce. “Faryan ya shaƙu da Rimsha sosai”. … Kai Abba ya jinjina alamar haka ne, amma bai yi magana ba.Wucewa sama Harleen ya yi yana tinanin irin salon Aunty Luna, ta fa buga ƙararrawar zuciyansa sosai…. Abba da Ammie suka cigaba da tsara yadda komai zai tafi a wannan biki na jibi da za’a yi. ————————–Slowly ya waro idanunsa a kan kyakkyawan face ɗinta da har yanzu hawaye yake ɗan gangarowa, ta kurawa face ɗinsa idanu. Ajiyar zuciya ya sauke, sai da ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce. “Cherry baki jin magana, baki ji sam-sam”……… Ɗan turo baki ta yi. “To daddy ai na ce ba zan sake ba”.Wani irin kallo ya dallah mata kafin ya ɗan yunkura ya zauna da kyau. “Kullum sai kin ce ba zaki sake ba, kuma ki sake, ke baki gajiya da bada hakuri ne? Kin san cewa ke kaɗai kika taɓa baiwa Champion na Iron Fist hakuri ya hakura ko? Bamu son kalmar sorry”. In a cool way ya faɗa. “Daddy waye champion kuma?”. Tana shessheƙa kaɗan ta faɗa…… A maimakon ya bata amsa sai ya kawar da zancen da cewa. “Kada ki sake ce mun daddy daga yau”….. Ɗan waro idanunta a kansa ta yi, sai kuma ta ce. “To daddy wani suna kake son in kiraka?”. Kallon gefen ido ya dallah mata da waɗan nan idanun nasa irin na Abba. “Da wani suna kika kirani a lokacin da kika shirya yaudarata?”…….. “Kai daddy, kai daddy, ni na yaudareka kuma?”. A shagwaɓe ta faɗa. Shiru bai amsa mata ba, yana dai kallonta.”Daddy ka yi magana”…….. “Awwww kin manta sunan kenan ko? Dama yaudara ce abin?”. Kai ta girgiza alamar a’a, sai kuma ta ce. “My gentle chaos”. Ta faɗa tare da ware tafukanta ta rufe fuska tana murmushi. Zuba mata idanu ya yi, yana kallon yadda wai sihirtaccen kyau yake bayyana a face ɗinta.Slowly ta zame hannunta daga kan fuskar tata, waro idanu ta yi da nufin ta sake yin magana, unexpected ta gansa dab da face ɗinta, ya matsota sosai. Ɗan razana ta yi, zata ja baya ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman waist ɗinta ta baya, ya jawota dab da shi sosai ta yadda suke shaƙar numfashin juna, idanunsa a kan kirjinta, slowly ya ɗago da idanun, ya yi sama izuwa kan dogon wuyanta kafin ya mayar da kallonsa a kan fuskarta.Ta zazzaro idanunta a kansa sosai. “My gentle chaos, this name melted my heart, kin iya zaɓan suna my cherry”. Yadda ya yi maganar a kurkusa da ita ya ALLAH, sai da zuciyarta ta yi wani sabon spark na kaunansa………. Kyakkyawan murmushi ta saki tare da sanya tafin hannunta ɗaya, ta shafi kyakkyawan soft cheek ɗinsa, ta sanya ɗan yatsarta a dimple ɗinsa kafin ta ce. “Daddy k…….”. Yatsar da ya ɗaura mata a saman soft lips ɗinta ne yasa ta haɗiye sauran maganar. Gabaɗaya sai ya ji yana buƙatar jin wannan soft lips ɗin a cikin nasa, taɓawar da ya yin nan ya jefasa cikin tsananin buƙatar kiss. Da sauri ya janye hannunsa baya, ya ɗan yi ƙasa da eyes ɗinsa sai kan kirjinta. “Don’t call me daddy again”. Da kyar ya iya faɗa saboda wani irin yanayin da yake jinsa a ciki. “Sorry my gentle chaos, mantawa nike yi, kuma kaga na saba kiranka daddy ne shiyasa”…….. Ɗan janye jikinsa baya ya yi daga dab ita, still idanunsa a kan kirjinta, a ransa yana cewa kullum sai ƙara girma take yi, yakamata ace a matsayin matarsa take ƙara wannan girma, ya koma saman sofa ya zauna. Ta gano yana kallon kirjinta, sai ta ce. “My gentle chaos, kaga yanzu kirjina yakara girma sosai ko? Har ya kusa kai na Rimsha, dama a school suna ta cewa bani da breast lokacin, yanzu ga shi na yi manyan breast nima, rigima zan dinga yi masu, dama a lokacin da muke school na Golden Root Rimsha sai ta dinga ɗaura belt a wajen cikinta dan breast ɗinta su fito sosai, nima yanzu rigimar zan dinga yi ina ɗaurawa”…….. Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi, shi fa yanzu ya daina mamakinta, dan ta rigada ta goge mashi hadda, yarinya babu abin da bata sani ba, uhm.”Waye ya ce maki ana rigima da breast?”. Ya faɗa ba tare da ya sake kallonta ba. “Ana yi mana daddy, ai breast shi ne mace, kaga da breast da hips suke diri, idan mace tana da shi maza za su sota, dole nima in gyara nawa, in ɗaura belt su fito sosai dan in ja hankalin maza……..”. Gagara ƙarisa maganar ta yi sakamakon wani irin kallo da ya wurga mata cikin zafa. Blinking eyes ɗinta ta shiga yi tana ja da baya. Da farko ya so ɗaukar zafi, amma ya fahimci yanzu ba ɗaukan zafi yakamata ya yi ba, already wannan karatu ya shiga kanta, so ba yadda za’ayi ya goge mata, zafa ko duka ba zai canza komai ba, kawai ya gwada mata illar hakan shi ne mafita, ya ci sa’a ma ai da bata zuwa ta yi gaban kanta, take faɗa mashi komai, kunga ya samu hanyar gyara. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. “Kina son jan hankali maza?”. Da kyar ya furta maganar saboda kishi, kun san larabawa da shegen kishi…… Kai ta gyaɗa mashi alamar….. “Me zaki yi da mazan idan kika ja hankalinsu?”…. Shiru ta ɗan yi, can kuma kai tsaye ta ce. “Sex mana daddy”……. Hasbunallahu waniimal wakil ya furta a cikin ransa sama da sau 30, shi dai boarding bata tsinana mashi komai ba face bakinciki.A cikin ransa ya ce zaki ga yadda ake sex, sai nasa kin tsani even jin wannan suna, ALLAH ya kaimu ranar da zaki zama tawa, daga ranar ko a kusa dake aka kira sunan sex sai kin firgita, ƴar ƙaniya, bata ma san ya ake ji ba, ita dai kawai an kwaɗaita mata abin, burinta kawai ta yi ta ji ya yake.Ganin ya tsareta da idanu ne yasa ta ce. “My gentle chaos kai ma kana son sex ko?”……….. Nisawa ya yi tare da ɗauke kallonsa daga kanta. Girgiza mata kai ya yi alamar a’a, sai kuma ya juyo sai yi mata magana kenan muryanta ta katse shi da cewa. “Amma kuma shi ne kake kallon breast ɗina? Me kake kallo a wajen idan har ba feeling………”. Gagara ƙarisa ta yi saboda yunkurawa da ya yi zai kai mata damƙa a wuya, ai a miliyan ta ƙarisa hayewa saman bed ɗin da baya-baya. Cikin zafa ya miƙe, ya yi ƙoƙarin danne kansa ya bita a hankali amma ta turashi bango. Baya ta fara yi tana son sauƙa gadon ta other side ɗin.Ai cikin zafa ya haye bed ɗin, danƙo kafafunta ya yi, ya jawota gabanta, in a harsh way ya ce. “A yaushe na faɗa maki ina son sex? Kuma a yaushe kika ga in kallon kirjinki?”. Babu wasa a tattare da shi yai magana, yana kallon cikin idanunta dake tsaitsaye na rashin jin magana. Kukan shagwaɓa mai narka mashi zuciya ta saka mashi, muryanta na rawa ta ce. “Sorry my gentle chaos, ba zan sake ba”…….. Wuyanta ya damƙo, cikin fushi ya ce. “Wai ya zan yi dake ne Seraphina?”…….. Aikuwa da buɗar bakinta sai cewa ta yi. “Ka aureni kawai”. Dintse idanunsa ya yi, koma menene laifin kansa yake gani, bai taɓa ganin laifinta ba. Slowly ya zame hannunsa daga wuyanta, in cool way ya ce. “Tabbas zan aureki, kuma tabbas zan canzaki, tabbas zan goge maku abubuwan dake kanki”. Ya faɗa yana ja baya daga kusa da ita.”Daddy yaushe zaka aureni ɗin?”. Ta faɗa tana riƙo hannunsa da ya cire daga wuyanta. Shi kam yanzu tausayi take bashi, da mahaifiyarta na raye dik wannan ba zai faru ba, rashin uwa babba ciwo ne…….. Tsayar da kallonsa a kanta ya yi. “Very soon zaki zama ta daddy, amma ki mun alƙawarin wasu abubuwa?”. Jinjina kai ta yi. “To daddy na yi”….. “Ki mun alƙawarin ba zaki taɓa kwatanta waɗan can abubuwan da na lissafamaki a baya na cikin littafin nan ba? Zaki tsare mutuncinki ki kama kanki”….. Da sauri ta ce. “Daddy ba zan taɓa yi ba”. Jinjina kai ya yi. “To yanzu faɗa mun meyasa kika ce zaki yi dressing ɗin da zai jan hankalin maza a kanki?”….. Tana ɗan turo baki, ta ɗan matsa hannunsa wanda yasa ya ji hakan har tsakiyar kansa….. “Ni daddy Rimsha ce fa ta ce yakamata mu yi samari ƴan gayu, wai mu yi dressing ɗin da zai ja hankalin maza a kanmu dan su yi rububinmu”.Dama tin da ta yi wancan maganar ya zargi Rimsha ce sila, ashe kuwa haka ne, ɗan ciza laɓɓa ya yi tare da cewa. “Babu ruwanki da maza, your gentle chaos ba ya isheki ba?”…….. Da sauri ta gyaɗa mashi kai. Zame hannunsa daga rikon da tai mashi ya yi tare da riko natan, in a cool way ya ce. “Idan Rimsha ta sake ce maki ku ja hankalin maza ki ce ke matar aure ce, matar gently chaos ɗinta ne”. Ya faɗa while a ƙasan zuciyansa yana tina ita ma Rimshar ai aurar da ita zai yi nan da kwanaki, zata gane kurenta ne, da kansa zai nemawa Vash excuse idan sun dawo daga wannan mission da suke a ciki, zai sanar da Azure komai.Faɗowa jikinsa ta yi, ta rungumesa tana faɗin. “I love you more my gentle chaos”……. “Love you too my cherry bloom”. Ya faɗa yana shafa hair ɗinta izuwa bayanta, yana jin wani irin yanayi mai daɗi na ratsa shi.”My gentle chaos yau ka kwana a nan kawai”. A shagwaɓe ya faɗa. Raba jikinsu ya yi, ya sauƙa ya koma saman sofa, wayarsa dake ƙara ya fitar yana faɗin. “Jeki kawo lunch in ciyar dake”…….. Da okey ta amsa tana sauƙowa ƙasa ita ma. Picking call ɗin ya yi tare da sanya nata yatsa ɗaya a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru, kai ta jinjina, a natse ya ce. “Hello”……. Daga ɗayan ɓangaren Lion ya amsa da. “Ina kake?”…… “Ina zuwa”. Ya faɗa a takaice. Guru ne ya karɓi wayar daga hannun Lion, fitowa balcony ya yi, dan dama suna ɗakin Lion ɗin, cikin zolaya ya ce. “Na baka 1 min ka dawo ko in tona maka asiri, kuma a matsayina na uban yarinyar nan ko I love you ban yarda ka ce ba”.”Kai gauro yakamata ka nemo mata in maka aure, dan ka san me duniya take ciki, naga ka zaƙe dayawa kana son shiga tsakanin mata da mijinta”. Aryan ya faɗa yana miƙewa tsaye, daidai lokacin Seraphina ta dawo hannunta rike da plate na jolof rice, a gabansa ta tsaya, cikin shagwaɓa ta ce. “My gentle chaos yau nima zan yi feeding ɗinka a baki”. Ta faɗa tana ajiye plate ɗin a ƙasa, ta riko hannunsa ɗaya.Dik abin da ta faɗa guru ya jita, sai ya ji abin ya burgesa, dan shagwaɓarta da yadda ta ce zata baiwa Aryan abinci a baki sai ya ji bayan soyayyar ƴan uwansa su Lion lallai yana buƙatar irin wannan soyayyar ma, wannan na daban ne. Muryan Aryan ne ta katse mashi tinani da cewa. “Ka samu mata in maka aure, wannan shi ne soyayyar mace, daban yake da kowanne, ba zaka gane hakan ba har sai ka ɗanɗa”. Ya faɗa mashi hakan ne dan yasan confirm ya ji me Seraphina ta ce.A shagwaɓe ta sake cewa. “My gentle chaos ɗan uwanka ne? Dama kana da ƴan uwa?”……. Kai ya jinjina mata alamar e, sai ya ɗan riko waist ɗinta ta baya, ya jawota jikinsa tare da kara mata wayar a kunne yana faɗin. “Ki gaishesa”………. Ɗan gyara murya ta yi game da cewa. “Ɗan uwan daddy good afternoon”. “Afternoon Seraphina, how’s your day?”……. “Fine what yoy?”……. “Cool”. Ya amsa da shi kafin ya sake cewa. “I’m your dad also, ki ce mun daddy not ɗan uwan daddy”…… Murmushi ta fara yi kafin ta ce. “To daddy yaushe kai kuma zaka zo in ganka?”…… Lokaci guda ya tina time da take gidan nasu zakinsu ya biyota ta shigo room ɗinsu, dai gata ta sume. “Soon”. Ya amsa mata….. Zata yi magana Aryan ya karɓe wayansa, dan in ya biyewa Seraphina ba zai tafi ba. “Scorpion ina zuwa yanzu” ya faɗa tare da katse kiran, ya ɗan sassauta riƙon da yai mata kafin ya ce. “Zauna ki yi lunch, zan dawo anjuma da daddare”…… Tana turo baki ta amsa da ka dawo da wuri. Sumbatar forehead ɗinta ya yi game da ce mata bye-bye, ya saketa ya nufi waje. Da kallo ta bisa har ya fice, zama ta yi a ƙasa saman carpet ɗin tare da jawo plate na abincin nata, a fili ta ce. “Daddy kenan, nasan kaima kana son sex sai ka ce mun ba haka ba, wai zaka gwada mun kai ba ruwan kan nan, nasan maganinka ne ai”..……….🤯Ta faɗa tare da fara cin abincinta, ta ɗauki wayarta ta kira Rimsha, nan ta fara bata labarin yadda suka yi da daddy, ke Rimsha da iya yi har da cewa. “Gaskiya daddyn nan naki anyi ɗan duniya, watau ke zai rainawa wayau ko?”…… Tana kai abinci bakinta ta ce. “Bai san kar nike kallonsa ba, ki kyalesa ne zan yi maganinsa ai”.Dariya Rimsha ta yi kafin ta ce. “Ki goge mashi hadda”.……. Dariya ita ma ta yi kafin ta ce. “Ke ai har yau ba ƙinƙi amfani da shawarar da na baki ba?”……….. Tana kwance kan gadon Faryan ta ce. “Wani shawara kenan?”. Nisawa Seraphina ta ɗan yi kafin ta ce. “Da na ce ki bugawa uncle Aryan ɗin nan baki wood a kai, ba ya ce shi mugu bane, ki daina jin tsaronsa na ce maki”….. Zazzaro idanu ta yi, a zabure ta miƙe zaune. “Seraphina baki da hankali, yanzu uncle ɗin zan bugawa wood? Kina son ki daina ganina a duniya kenan ko? Kin gaji da ganina! Uncle Aryan fa? Mutumin da duk family ɗinmu tsoronsa suke ji ɗin? Ke baki son a zauna lafiya na lura, ai da hanya ta haɗani da uncle Aryan gara na bi ta saman wuta in wuce, ke na lura kin fara zama muguwa, yanzu kin daina sona”. Wani irin dariya Seraphina ta fara yi har da riƙe ciki, ta dinga cewa Rimsha matsoraciya malalaciya, Rimsha ta ce e ta yarda su je a hakan in dau a kan shiga harkar uncle Aryan ne ta kirata da koma menene idan tana so. Suna tsaka da wayar katin Seraphina ya ƙare, turo baki ta yi game da ajiye wayar.Tana ajiyewa sai ga kiran Rimsha ya biyo baya, cike da murna ta ɗauka suka cigaba da hira har ta kammala cin abinci, ta tashi ta shiga wanka rike da wayar a hannunta bata katse kiran ba. ———————-🔥WS-HOSPITAL.Suna shiga cikin hospital ɗin kai tsaye suka nufi SECTION D. Sai da suka je suka duba lafiyar babys ɗin nan, sannan suka nufi in da darling yake, nan ma suka duba shi, izuwa yanzu ko motsi darling baya yi, sai idanunsa ne kawai ke motsawa, jikinsa ya yi wani irin fari sosai tamkar dattin haihuwa, fuskansa da hannayensa zuwa kafafunsa sun kumbura sosai wanda hakan yasa ya zama ƙato tamkar jariri ɗan wata 7, alhalin satinsa 4 yanzu a duniya.Ganin aikinsu a wajen yana tafiya daidai ne yasa suka fita izuwa ɗakin tiyata. To ALLAH ya sake dawo damu wannan rana ta tiyata a cire eggs. Wanna ɗakin ma mun bashi sunan ƊAKIN CIRE EGGSƳan matan gabaɗaya suna kwakkwance a saman gadajen jinyarsu, kamar ranar dik suna barci, dan sun sha alluran barci, babu sabbin fuska a cikin mata, dik na da ɗin ne……. Dik da yaran nan a kwance suke, da kunga jikinsu zaku ga alamar rauni, alluran da ake danƙara masu ya fara kashe dik wasu garkuwa na jikinsu, skin ɗinsu ya canzawa, sun yi wani irin haske sosai, kuma abin takaici dikkansu babu wacce ta haura 20 years, ga su kyawawan gaske, amma a haka su Dr James suke son salwantar da rayuwar yaran nan, sun zo duniya ta hanyar kyankyasa, basu da uwa bare uba, sannan zasu bar duniya ta hanyar cire eggs ɗinsu, dan waɗan nan shegun alluran da ake masu ba karamin ɓarna yake masu a jiki ba, an mayar da rayuwarsu tamkar ATM na ciran kuɗi, dik lokacin da ka ga dama zaka je ka cire kuɗi a bank ɗinka, to suma haka 3D ke masu, dik lokacin da suka ga dama zasu ciro eggs ɗinsu. Ya rabb. Nurses dake wannan asibitin sun shirya komai yadda ake buƙata, a gaban wani bed Dr James ya tsaya, wata na’ura ya ɗauko, ya ɗaura a kan cikin yarinyar dake kwance bayan ya ɗage rigar dake jikinta sama. Yarinyar ma fuskanta a kumbure kamar bata da lafiya haka. Idanunsa a kan computer dake jikin gadon, ya zuba yana kallon yadda cikin nata yake motsawa, a daidai mararta ya tsayar da na’urar, ya zubawa ovaries ɗinta idanu, can kuma ya ɗan yi ƙasa da na’urar izuwa saitin follicle ɗinta. Ya ɗan yi mamakin ganin ruwan cikin follicle ɗin bashi da yawa. Ɗago eyes ɗinsa a kan fuskarta ya yi, shiru ya ɗan zuba mata idanu na ƴan sakanni, sai kuma ya kai hannunsa ɗayan ya taɓa tsakiyar wuyarta daidai in da maƙogwaronta yake, kun san jijiyoyin wajen suna harbawa ai, suna amsawa daga bugun da zuciya take yi. Yatsunsa biyu ya ɗaura a kan maƙogwaron nata, ya kasa kunne sosai yana son ya ji yanayin harbawar ƙananan jijiyoyin dake wajen. After like 30 seconds ya ɗauke hannunsa daga wajen ya mayar saman forehead ɗinta, ya sanya yatsansa ya janye fatar idanunta sama, ya gwalo kwayar idanun nata waje.Can ya saki idanun tare da dawo da hannunsa saman kirjinsa, ya zame rigar ya ɗaura yatsunsa biyu a saitin zuciyarta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Da gaske yarinyar babu ita, babu rai a jikinta, komai na jikinta ya tsaya cak ya daina aiki, da alama daga alluran barci ta zarce lahira, rai ya yi halinsa. Fahimtar da ya yi cewa ta mutu da gaske ne yasa ya ɗan nisa tare da ɗauko siririn bututun da suke tiyatar, ya ɗauko audiga tare da wani oil a cikin roba, zuba oil ɗin yai a jikin audigan, ya goggoga mata a gabanta, ya cusa har can ciki kafin ya sake fitarwa, ta rigada ta mutu, komai na jikinta ba zai motsa ba, bai isa ya cusa mata wannan karfe a gabanta ba, saboda jikinta ya daina sakin ruwa, shiyasa ya saka mata wannan mai ɗin dan ya samu hanyar wucewa ciki. Ya rabb, ta mutum ma ba zai hakura ba, dan suna bala’in buƙatar alot of eggs sosai, so ba zai iya yafe mata ba, kai wannan wace iriyar musifa ce?Bayan ya gama shafe gabanta da mai har can ciki ne ya ɗauko bututun ƙarfen tiyatar tare da gyara na’urar dake kan cikinta, ya ƙara yin ƙasa da shi zuwa ta gabanta, dan yasan zai sha wahalar shigarta tin da babu ruwa a jikinta ta rigada ta mutu, so dole ya duba hanya da kyau kada ya fasa jikinta ya shiga wani waje.A wannan karon a hankali sosai ya fara zura karfen, dan in ya yi garaje yana iya huda cikin jikinta ya shiga wani waje tin da ba ruwan dake taimaka masu karfen ta wuce salun alum. Ya ɗan yi tafiya kaɗan sai kuma ya sake zaro karfen da sauri saboda haɗewar da jikinta ya fara yi, hanyar dake can ciki ya matse, kun san in mutum ya mutu haka jikinsa a hankali zai fara haɗewa har ka takure waje guda, so a wannan lokaci babu wani abin da zai iya shiga jikin mutun ta private part ɗinsa, to gawa idan ta yi minti talatin zuwa awa ɗaya ma babu abin da zai sake amfani a jininsa, in macece gabanta ba zai sake buɗewa ba bare baya, kamar yadda zaku ga hakwaranta ke datsewa ba zasu buɗu ba haka ne, shiyasa dole ya saka mai dan taimaka mashi.Oil ɗin ya ɗauko, ya shafe karfen da shi, ba zai dai hakura ba, a haka ya sake tura karfen a gabanta. Kai tsaye cikin cikin yarinyar ya nufa. Ya fara tafiya ya sake tsayawa yana kallon wajen mararta a cikin computer dake jinin gadon. Sai da ya ɗauki 3 mins yana kallon yanayin marar tata yana ɗan junjuya naurar dake kan cikin nata yana duba lungu da saƙo wajen kafin nan ya saki na’urar kan cikin nata, ya sa hannu ya ƙara gyara kafafunta, ya buɗesu sosai dan ya buɗe jikin nata da kyau, da alama dik da mai da ya zuba ɗin da wahalar wucewa, kuma yarinyar bata fi 15 mins da mutuwa ba, da ta kai 30 mins ma dik bala’insa bai isa ya shigeta ba, sai dai ya hakura.Cigaba da zura karfen a hankali ya yi idanunsa a kan computer dake gabansa, yana kallon hanyar da yake bi sosai ne, da kyar ya samu ya isa kofar ovaries nata, komai na ta ƙara tsukewa.Kofar follicle ɗinta ya buɗe tare da zura needle suction tube ɗin ciki, tsotse ruwan dake cikin follicle ɗin nata ya fara yi dik da yaga ba yawa sosai. Da kyar ya samu damar tsotse ruwan, sai da ya kwashe tas, sannan ya fara zaro bututun, da kyar yake jansa, saboda jikinta nata faman kama bututun, haka ya zaro shi ba imani ba tausayi. A cikin wani karamin kwalba ya zuba kwayayyen haihuwar da ruwan tata tare da sanya hannu ya ɗauko audiga bayan ya rufe kwalbar, a gaban nata ya cusa audigar can ciki, ya bar mata shi a ciki. Sai dai abin da ya yi mugun bashi madarar mamaki shi ne ganin alamar eggs sama da 50 a cikin wannan ruwa da ya yi, ya ga alamarsu sosai, bayan yasan dik alluran da suke masu basu taɓa samun mace mai eggs sama da 15 ba, to how comes yau sama da 50?. Ni kam na ce hmmm, ruwa rabin cokali ya ishi mai hankali wanka, amma kai ba zaka gane cewa wata aya bace hakan, kila zaka ɗauka nasara ce da samun cigaba, ai UBANGIJI ya iya yi wa kafurai irinku ɗaurin talala!Daga haka ya ɗan haɗe mata kafafunta waje guda kafin ya matsa zuwa gado na gaba cike da al’ajabin wannan eggs guda 50 ɗin. Haka suka bi yaran gabaɗaya suka kwashi eggs ɗinsu, a cikinsu sun samu yara biyar sun mutu, yara biyar ɗin nan kuma dikkansu sun samu eggs sama da 50 a jikinsu saɓanin a baya da suke samun 10. Sun yi matuƙar murnar ganin sun samu eggs guda 50-50 a jikin matattun yaran nan, kunga a take sun samun 250 eggs kenan, haba sai farinciki suke yi, suka sanya aka kwashi yaran aka mayar da su in da suke killacesu, aka ɗauki gawarwakin waɗan da suka mutun kuma, haka suka haƙa rami suka binnesu kamar yadda ake binne kare.Suka tattari eggs ɗin suka kaisu cikin wannan freezers room ɗin nasu, sun yi matuƙar farinciki yau, sun samu eggs almost 400 a jikin yaran, sun fara jin cewa burins na kyankyasan 2000 babys a wannan shekara zai cika, saura kaɗan.Bayan sun kammala suka fito suka nufi SECTION E. Suna kan tafiya ne Dr Kamal ya ce. “Jammy ina ganin mu bar yaran nan su huta na watanni 3 ko huɗu kafin su cigaba da karɓar alluran nan, naga gabaɗaya jikinsu ya canza, alamar alluran ya fi karfin garkuwar jikinsu, ya yi masu yawa, kaga har mutane biyar sun mutu, alluran yai masu overdose, kuma dikkanmu mun san cewa yaran nan tin shekarunsu bai kai karɓar wannan alluran ba muke danƙara masu shi, tin suna 13 years, jikinsu bai yi wani kwari ba, a wata allurai kala uku masu karfi muke yi masu, wanda haka kuskure ne a fannin lafiya, ka sani na sani!”. A taƙaice Dr James ya ce. “Ko mu dakatar ko bamu dakatar ba dikkansu mutuwa zasu yi, already alluran ya kashe garkuwar jikinsu, dan haka ba zamu dakatar ba, gara kawai a cigaba har zuwa lokacin da zasu mutu, kuma ai idan suka zo mutuwa sun fi bada eggs dayawa, baka ga 50 eggs kowacce daga cikin matattun suka bayar ba?”. Dr Mark ya ce. “Yanzu ma ai sun fara mutuwa, one by one haka dikka zasu ƙare, yau biyar, wani watan ma biyar ko sama da haka zasu mutu, a haka zasu ƙare, dan haka ba wani zancen mu dakatar da yi masu allura, already su tasu ta ƙare”. …….. Ya rabb, ku ji yadda suke magana tamkar ba ran ɗan adam bane suke mutuwa.Shiru Dr Kamal ya ɗan yi, dik da cewa yana son aikin nan nasu, suna samun maƙudan kuɗaɗe, amma a yau yaran nan sun ɗan bashi tausayi, dan ya ga jikinsu ya fara lalacewa sosai da sosai, alluran ya gama kashe. A haka suka shiga SECTION E. Sai suka shiga cikin wani ɗaki mai tarin glasai dayawa. Wajen tamkar lap ne haka, ga wasu halittu na ban mamaki dayawa a cikin glasses dake ɗakin, an yi glasses ɗin dogaye tamkar show glass haka, to a ciki ne waɗan nan halittu suke, tamkar suka ƙoƙarin yin wasu halittun ne. Tin daga kan yanayin matakan tsaron da suka zubawa wannan ɗaki zaku san ba waje ne na wasa ba, zaku san wane ne mai bala’in haɗari. Gaban wani tangamemen glass mai girman gaske suka tsaya. Wani irin jibgegen halitta ne a ciki mai kama da dabba mai kuma kama da mutum, yana da wasu irin ƙulu manya-manya a tamolon kansa, idanunsa tamkar ball saboda girma, gwanin tsoro.Wannan halitta ba komai bane face ɗaya daga cikin fitintinun da suke kirkirowa duniya, Dr James ya ja ragamar wannan project ɗin, shi ya harhaɗi kwayoyin halitta, su DNA ɗin nau’ikan dabbobi da mutane daban-daban, suka tacesu a lap, sannan ya fara kyankyasan wannan halitta, tin shekaru 8 baya yake yin wannan project ɗin, halittace mai matuƙar haɗari, yana daga cikin plan na WS dan hana duniya zaman lafiya, a wannan asibitin ba jarirai kawai ake kyankyasa ba, ba kuma magani kawai ake haɗawa ba, kazalika ba iya cututtuka kawai suke kyankyashewa ba, suna kyankyasar hadda dabobi, kai dik yadda kuke zaton asibitin nan ya zarce tinaninku, ku dai sai mun natsa cikin labarin.Yanzu ba zaku gane me zasu yi wa duniya da wannan halitta ba, amma gaba zaku gane, yanzu haka renon halitta suke yi yana ƙara girma, a wannan ɗakin akwai nau’ikan halittu daban-daban, kowanne kuma da amfaninsa da dalilin yinsa.Bayan sun duba halittar yana nan lafiya yana barci, sai suka ƙara gaba zuwa wajen wasu glasses ɗin, nan kuma wasu irin ƙananun halittu ne masu kamar ƙudaje a cike a cikin glasses ɗin, a gaban wajen suka tsaye, Dr James ya ce. “Waɗan nan halittu sun kusa barin wannan waje, a cikin week ɗin nan WS zasu karɓesu”. A tinaninku me za’ayi da su kuma?.Jinjina kai Dr Kamal suka yi, suna ƙara yabawa kansu a wannan project ɗin, dan sun sha baƙar wahala. Sun yi yawo a cikin wannan ɗaki sosai, sun duba halittu daban-daban dayawa kafin su fito su nufi office ɗinsu. A office ba Dr James suka zauna, a tare suka yi breakfast around 11 na safe, sannan suka ɗan taɓa aiki zuwa 1 kafin Dr James ya ce bari ya duba Zinta a gida. Fitowa ya yi ya bar su Dr Kamal a office ɗin, ya nufi gida. Tin da ya sako kafafunsa a cikin parlon nan wani irin musulmin kamshi ta bugi hancinsa, shaƙa ya yi ya lumshe idanu tare da ƙarisawa ciki. A cikin ransa yake cewa a ina suka samu wannan kamshi mai daɗin haka? Ko’ina tsab-tsab, watau batu na gaskiya 3D akwai mugun tsabta sosai, basa shiri da ƙazanta ko datti waje, komai nasu tsab da yake likitoci ne.Shi da kansa a yau ya shaida lallai yau mata na cikin wannan gida nasu, sama ya haye yana ta baza hanci yana shaƙar kamshi. A parlon sama ya isko Maya zaune tana karata wani littafi na lafiya da ta ɗauko daga room na Dr Kamal. Tana ganinsa ta zube ƙasa tana ɗaga mashi gaisuwa. A dake ya amsa tare da cewa. “Ina madan ɗin take?”….. Tana ɗan sunkuyar da kai ta amsa da. “Tana cikin room”…….. “Kun yi breakfast ne?”. Kai sister Maya ta gyaɗa mashi. “Mun sha tea”……. “Iya shi kawai?”. Kai ta sake gyaɗawa. Ciki ya wuce yana tinanin ɗure zai yi wa Zinta yanzu, ga komai suna da shi, kitchen ɗinsu shaƙe da kayan abinci fa, ace tea kawai zasu sha, bai yarda ba.Kofar room ɗinsa ya tura, wani kamshin na daban ne ta kai mashi karo a hanci, shaƙa ya yi tare da ɗan lumshe idanunsa kafin ya shigo, sister Maya ce fa ta zaɓo turarukan gida daga cikin turarukan dake ɗakin Dr Kamal, ta gansu kala-kala kwali-kwali, dan 3D akwai son kamshi da tsabta na faɗa maku, to wasu turarukan ma basu taɓa amfani dasu ba, basu san ya yake ba, ita kuwa tana zuwa ta dinga bincikawa tana taɓawa sai da ta ji wanda kamshin yai mata, sannan ne ta fito da shi, ta bi lungu da saƙo na gidan ta fesa, sannan ta ɗako wani daban ta fesa a ɗakuna.Can ya hango sister Zinta kwance saman bed, kudundune a cikin bargo, idanunta a lumshe. Karisawa wajen ya yi, a gefen bed ɗin ya zauna tare da kai hannu ya janye bargon ƙasa, wutar ɗakin a kunne, ko’ina tankar…….. Waro idanunta da suke jajir waje ta yi, kai tsaye sai kan face ɗinsa. Tana ganinsa ta fashe mashi da kuka. Hannu bibbiyu yasa ya ɗagota sai saman laps ɗinsa, ɗan zubawa kayan jikinta idanu ya yi, rigar ta tafi da shi, rigace shara-shara maras nauyi sister Maya ta ɗauko mata daga ɗakinsu. Cike da kulawa ya ce. “Sorry princess of my heart”. Ya faɗa yana taɓa goshinta da yau zafi sosai.Kwantar da ita ya yi, ya miƙe ya fito waje, kitchen ya shiga, akwai manyan gas guda uku a cikin kitchen ɗin, sai glass na pots, sai kuma ƙaramin store na kayan abinci a ciki. Da kansa ya dafa mata indomie, ya soya two eggs da kyau, samnan ya haɗa mata tea mai kauri da zafi, ya jera a saman tray, ya ɗauko ya nufi room ɗin. A daman carpet ya ajiye tray ɗin kafin ya nufi wajen drawers dake ɗakin.Wasu drugs ya ɗauko tare da kawowa saman carpet ɗin ya ajiye, ya nufi toilet. After 20 mins ya fito ɗaure da towel a waist ɗinsa. Shiryawa yai cikin pjs sky blue, ya dawo wajen bed ɗik, ƙarisa yaye mata bargon ya yi kafin ya ɗauketa cak. Bai direta a ko’ina ba sai a saman carpet ɗin, zama yai da ita a jikinsa, tana ta kuka.Cikin salo ya fara rarrashinta ta yadda dole ta yi shiru ba dan ta shiryawa hakan ba. Ya ɗauko fuck ya fara naɗar indomie ɗin yana bata a baki, da farko taƙi karɓa, amma da ya jawota jikinsa, cikin sanyin murya ya ce. “Idan baki ci ba zan ƙara yin abin da na yi”. Sai ta buɗe baki ta fara karɓa. Da ta ce yai mata zafi idan ya ɗebo sai ya hura mata da bakinsa yai sanyi, sannan ya bata.Haka ya dinga bata har sai da ta ci kusan rabi, sannan ta ce ya isheta, ya ɗauko tea ya bata, shi ma kusan rabi ta sha, sannan ta ce ta ƙoshi, ya ɓalle magungunan da ya ɗauko, ya bata ta sha, ya ɗauketa cak sai kan gado. Bayan ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, a gaban gadon ya tsugunna game da ce mata. “Zan koma office, sai yamma zan dawo, akwai wani abin da kike so?”. Kai ta girgiza bata yi magana ba, sumbatar ɗan bakinta ya yi tare da miƙewa ya nufi closet ɗinsa, ya shirya cikin suit, ya ɗaura rigar aikinsa a kai, ya fito ya koma office. Ya wice Maya a parlo yarda ya barta, ta dukufa a karatu haiƙam. Yana fita ta miƙe da sauri ta koma cikin ɗakin dan duba sister Zinta ɗinta.Bari mu leƙa DOL mu dawo.DEATH OR LIFE (DOL).Yana fita V ta fashe da sabon kuka tare da kwantowa jikin Angelina tana ɗan shessheƙa, yau Romeo ya yi fushi mai zafi da ita, da gudu ta miƙe ta yo waje, su Angelina na kiranta amma taki tsayawa, a tsakiyar tantunansu ta zube gwiwowinta cikin ruwan saman, yau tana jin kamar mutuwa zata yi.While su kuwa su Leo suna zauna a cikin room na Leo. Da Noor, Leo, Vash and Zaynish, Leo ne ya dubesu da kyau kafin ya ce. “Bani son dikkan sojojinmu su san me yake faruwa yanzu, zamu fita izuwa wancan wajen da hayakin yake, zamu je mu duba menene, sai mu dawo mu san irin shirin da zamu yi masu”. Jinjina kai suka yi, Zaynish ya ce. “Ina tinanin wata ma’aikata ce a wajen ko wani abin makamancin haka, duba da irin kurɓataccen bakin hayakin dake tashi, dole wasu sinadarai ne a haɗe a wajen”. Kai suka jinjina, Leo ne ya jawo laptop ɗnsa ya kunna, a tsanake yake fito da taswirar dajin, cikin sanyin murya ya ce. “Wannan waje yana ta yamma da Avaris ne, a yammar ma ba tsakiya ba, ya gota ta gudu kaɗan, yamma maso kudu kenan”………. Zubawa taswirar idanu suka yi, suna sauraron bayaninsa.Noor ne ya amsa da. “Wani lokaci yakamata mu tafi?”……. Shiru suka ɗan yi, can Leo ya ce. “This coming two days”. Kai suka jinjina alamar to, a sirrance suka tsara komai, basu bari sojojinsu sun sani ba. A can gefe kuma Angelina sun kamo V suka dawo da ita, sai kukan dai take ta faman yi. Zaman rarrashinta suka yi, da kyar barci ya saceta saboda ta ci kuka ta ƙoshi. Bayan ta yi barci Anglina ta fito da laptop ɗinta, ita kuma Dr Manassa ta ɗauki wayarta ta koma saman mattress ɗinsu ta zauna.Angelina na buɗe laptop ɗinta sai ga saƙon ɓoyayyen email ya shigo mata, da sauri ta shiga kan saƙo. Ɗan zazzare idanu ta yi a kan saƙon, dogon note ne kamar haka. “Assalamu alaikum my flowers, how’s your day and hope you’re enjoying this rain weather?. From the very first moment I looked into your eyes, I didn’t just see beauty, I saw strength, discipline, and a calm fire that only a true soldier carries, you wear your courage with grace, and your confidence with elegance, your beauty isn’t only in your face, it lives in your voice, your posture, and the way you stand firm even when the world tries to shake you, you are a warrior with a gentle soul, in a life where we are trained to face chaos, you are the calm that steadies my mind, your presence brings me peace in ways no battlefield ever could, when I think of rest, safety, and quiet strength, I think of you, we both know the weight of this uniform, we understand sacrifice, loyalty, and silence, yet with you, I feel understood without speaking, protected without armor, you remind me that even soldiers deserve softness, love, and a place to breathe, so today, I lay down my pride and speak from my heart, I have fallen in love with you, not out of weakness, but out of certainty, i choose you, not just as a fellow soldier, but as the woman who calms my storms and strengthens my spirit, If love is a battlefield, then you are the only one I would gladly stand beside in peace and in war”………… Aa lallai, irin waɗan nan kalamai haka, e lall mun shaida soldiers deserve love and peace, jama’a saƙon na sojoji ne fa, Unays ko Juraiz waye da wannan kalaman masu melting heart?.Tin da ta fara karantawa take murmushi har ta kai karshe, da sauri ta ce. “Manassa come and see something”……… Sauƙowa ƙasa Manassa ta yi, ta zo da gudu dan ta gani.

Back to top button