Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 62 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Chapter 62 Book 2

The Father Of Soldier

Written By Boss Bature

Na sadaukar da wannan zazzafan page din,ga dukkan masoyan littafin Abban sojoji,especially members na paid grp dina,Abban sojoji paid grp,Father of soldiers,Abban sojoji Vip grp,da kuma Junaid romeo Much luv Allah yabar zumunci anatare insha Allah (08103884440)*😍😘

 

 

 

*Bazan manta daku ba,waɗanda suka ƙarfafamun guiwa wurin rubuta littafin nan,har yau ina alfahari daku,

Fadeela lamiɗo da kuma sadeeq abubakar CEO na Lafazi writer association,da kuma auntyna takaina,bazan fadi sunanta ba,sai na nemi ixninta saboda tsaro🤣😂😅

Da kuma sauran members dinda akayi fadi tashi dasu,suma duk zan fadi sunayensu nan gaba*

 

*Abban sojoji paid book ne,duk maison siye zaiyi mun magana kai tsaye ta layina,but pls banda kiran waya,only message ta whatsapp,bana shariya muddin mutun ya turamun saƙo zan duba ne,indae ina free,in mutun yayi payment zan tura mashi duka na baya da aka wuce shi har inda muke so*

 

 

❤🤍❤

 

 

*Junaid*

 

 

Tun bayan daya kai Sehrish school ya biya gidansu wani abokinshi,wanda tun suna secondry school suke tare,acan ya yini har bacci yayi awon gaba dashi asaman gadon mamarsu abokin nasu,saboda tsabar gatanci bama gadon abokin nashi ba,a ɗakin mamarsu yayi baccin,daga shiga su gaisa da ita,ya samu ta shiga cikin toilet,shi ne ya ɗan kishingida saman gadon ya shiga sharar bacci,wuraren ƙarfe daya ya farka ganin lokacin tashin su sehrish daga school ya kusa yi,nan  yayi sallama da mutanen gidan,jiki na rawa ya shiga motarshi tare da barin gidan,

da gudu ya fisgi motar saboda ya ƙarasa gida da wuri,ba don komai ba sai don alkawarin da yayi ma sehrish na cewa in zaizo ɗaukarta daga school zai nuna mata wankan da zai ɗauka na shaddar shi,

yana ƙarasowa cikin gidan bayan yayi parking din motarshi,ya wuce cikin main palour ɗin,a lokacin duk sun fita yin sallar azhar da ake cikin kira,bedroom dinshi ya shige tare da rage kayan da ke jikinshi ya faɗa cikin toilet,shaf shaf yayi wanka cikin minti goma sha biyar,ya fito daga cikin toilet din,jikinshi sanye da bathrobe,

Gaban dressing mirror dinshi ya zauna,yadda kasan mace haka ya zauna yana gyara jikinshi,sai da yabi ko’ina na jikinshi ya shafe da mai,sannan ya shiga gyara sumar kanshi,bayan ya kammala ya miƙe tare da komawa wurin wardrobe,ya buɗe tare da ɗauko shaddar,a natse ya shiga zura kayan ajikinshi bayan yasa vest da short farare kal,rigar takai masa har guiwarshi,sai wandon,lokacin daya kammala sanya shaddar ajikinshi dawowa yayi tare da tsayawa gaban madubi yana kallon fuskarshi ta ciki ya Allah!shi kanshi sai da ya tsorata da irin kyan da yayi,kamar shiya zana kanshi don kyau,shaddar ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,sae faman salƙi take ajikinshi kamar wani sabon ango,kyakkyawan murmushin nan nashi ya saki tare da cewa”junaid kenan yakamata ka zama namiji mana,ka cire duk wata fargaba yau ka tunkari sehrish gaba da gaba ka bayyana mata irin son da kake mata batare da jin shakkar komai ba,’

shiru ya danyi aranshi yana cewa”gaskiya ina jin fargaba fa,anya reesh zata amince da son da nake mata?in tace bata sona fa?tabbas zan iya rasa raina,amma zan jure yau dae na fahimtar da ita tsananin son da nike mata,’

Ƙarasa maganar yayi tare da ɗauko hula mahadin kayan wadda take tsadaddar gaske sai daukan ido take itama ash colour ya aza saman kanshi,hmmmm abun ba’a magana madarar kyau ba kaman da sumar kanshi ta dan fito daga  baya.

Zura takalmanshi yayi masu kyau da tsadar gaske suma mahadin kayan,sannan ya koma gaban dressing mirror ɗin ya ɗauko turarenshi ya shiga feshe jikin shi dashi ko’ina saƙo da lungu,nan take ƙamshin ya gauraye ko’ina na ɗakin,

Key ɗin motar shi ya dauko sannan cikin sauri ya fito daga ɗakin nashi ya sauko downstairs,babu kowa a falon duk sun tafi salla,

 

A hankali yake driving din motarshi fuskar nan dauke da annuri,sae da yafara tsayawa masallaci yayi sallah,sannan ya miƙi hanyar makarantarsu sehrish,shiga ciki yayi tare da yin parking ɗin motar sannan ya fito ya tsaya tare da jingina bayanshi a jikin motar,zuba ido yayi yana jiran fitowar sehrish amma babu ita babu alamarta,ga students sai fitowa sukeyi,wasu na hawa bus wasu kuma ana zuwa ɗaukarsu,

Gajiya ya fara yi da tsayuwar,

“Wai ina reesh ta shige ne,ta barni tsaye ina ta faman jiranta,’rai aɗan 6ace yayi maganar,

Juyawa yayi tare da kifa kanshi ajikin motar ya ɗan lumshe idanunshi,

adai dai lokacin Jahad ta fito hannunta ruƙe da school bag ɗinta,tana neman hossana duk atunaninta zata same tane a wurin da suke jiran osman yazo ɗaukarsu amma babu ita,da alama ma Osman ɗin bai ƙaraso ba,

guntun tsoki taja tare da juyawa zata koma ciki,karaf idonta suka sauka akan Junaid,cike da mamaki take kallonshi,tana ɗan leƙen fuskarshi daga inda take,

 

Bakomai ne ya faɗo mata aranta ba,face alƙawarin da tayi ma hosana nacewa zata nemo mata ya Omar,aranta tace”ya Omar yace ƙaninshi ne wannan,kodae naje na tambaye shi ina ya Omar yake,may be ya taimakamun wurin haɗa ni dashi,

ƙarasawa wurin motar junaid tayi ta ɗan tsaya daga bayanshi,tare da yi mashi gyaran murya don ya juyo,

jin shiru bai juyo ba yasa tayi mashi sallama”Assalamu Alaikum,”

Nan ma bai juyo ba,hannu tasa ta ɗan ta6a bayanshi a hankali,aikuwa a firgice ya juyo,ita kanta jahad sae da ta ɗan tsorata taja da baya ganin yarda ya juyo kamar ya tsorata,

Murmushi ta sakar mashi tare da cewa”am sorry,naga kamar ka razana,tun ɗazu nayi maka sallama baka ji ba,’

harara junaid ya watsa mata,har sae da tasha jinin jikinta,rai a6ace yace”yanzu abunda kikayi mun kin kyauta!kinsan tun yaushe nike atsaye nan ina jiranki!”

Gaba ɗaya jahad ta gama ruɗewa jin abunda Junaid ke cewa,

Cikin sauri tace”dama…am..inaso ne na tambayeka game da yayan…….’

Kafin ta ƙarasa maganar tuni junaid ya gama hasala,ruƙo hannunta yayi tare da buɗe motar,yace mata wuce ki shiga,

Murya na rawa jahad tace”bangane me kake nufi ba?

A tsiwace yace”Ni ki wuce mu tafi,’

duk yarda jahad taso ta fahimtar da junaid cewar ba ita bace wadda yake nema ba,amma yaƙi fahimta,shi duk atunanin shi sehrish ce,

Tursasa mata yayi har sae da tashiga cikin motar,sannan ya shiga yaja motar da gudu ya fisgeta suka fuce daga cikin makarantar,

 

A natse yake driving lokacin daya hau saman shantalelen titin,zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi,ta wutsiyar idonshi yake kallonta,ganin yarda ta zuba mashi ido yasa shi ɗan juyowa tare da sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi,

mamaki ne ya kama jahad,gaba ɗaya abun ya gama ɗaure mata kai,aranta tace kodae yana da ta6in hankali ne?in ba haka ba, nida bamu ta6a haɗuwa dashi ba amma kuma ya nuna ya sanni har ya tursasa mun na shiga motar shi,yanzu ni bansan ya zanyi na fahimtar dashi ba,kada hosana ta fito tayi ta nemana acikin school,

“Reesh banji kin yabi wankan nawa ba?ko banyi kyau bane,”yayi maganar a yayin da yake kokarin parking ɗin motar a gefen titi,sannan ya juyo yana kallonta,

zuru jahad tayi tana kallonshi,hakan ba ƙaramin 6ata mashi rae yai ba,cikin shagwa6a yace”Wai menene haka reesh,duk kin bi kin wani sauya mun,saboda ke fa na ɗau wankan nan don nazo na nuna maki,amma kin zuba min ido kina kallona kamar yau kika fara gani na,’

A tsorace take da shi,don tagama yarda cewa yana da ta6in hankali,cikin en ina tace”amm…ni fa…ba..’ kasa ƙarasa maganar tayi gabanta na faɗuwa,ganin yarda junaid ya matso dab da ita,ya ƙureta gaba ɗaya ƙamshin turaren shi ya gama kashe mata jikinta,

murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa”kallon ya isa haka reesh,let’s talk about serious issue,akwai abunda na jima inason sanar dake,amma inajin fargabar amsar da zan samu a wurinki,’ya ƙarasa maganar yana kallon cikin kwayar idanun jahad amatsayin sehrish,

a hankali jahad ke bin kyakkyawar fuskarshi da kallo,tun daga kan eye brows ɗinshi,dogon hancinshi da kuma red lips ɗinshi,komai nashi mai kyau ne kuma mai jan hankali,

Anatse yaci gaba da magana,”reesh,nasan cewa baki ɗauke ni cikakken namiji ba kamar saura,saboda na cika wasa da shiririta da kuma shagwa6a,kuma bani da aikin yi sae zama acikin gida kamar mace, nasan ba kowace mace bace zata so ta aure ni a haka” ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,wannan karon babu alamar wasa a fuskarshi,

 

natsuwa jahad tayi tana sauraran shi,

Hannayenshi yakai tare da ruƙo nata cikin nashi,nan take jahad taji gabanta ya faɗi,

ɗagowa yayi awani irin yanayi yaci gaba da magana”duk wannan abun da nake reesh zan daina in baki so,idan har kika amince mu kayi aure,xan zama kamar yarda kikeso,nidae burina ki amsa mun cewa kina sona,kuma zaki aure ni,ni ban ta6a son wata ƴa mace ba in bake ba,na shaƙu dake sosai kuma ina da tabbacin cewa in mukayi aure zaki bani kyakkyawar kulawa,pls reesh tell me will u marry me”?

Tamkar zai yi kuka haka yayi mganar yana jiran amsarta,

Shiru jahad ta ɗanyi tana yanke shawara da zuciyarta,tunda dae bai da cikakken hankali bari na jaraba biye mashi kona samu mu rabu lafiya

Ƙarasa zancen zucin nata tayi tare da mayar da idanunta akan nashi tace”bana tunanin cewa akwai macen da zata samu namiji kamarka ta nuna bataso,kai na daban ne,kana da komai da mace zata buƙata a wurin namiji,kayi mun sosai kuma ka kwantamun araina,tayin soyayyar da kayimun na kar6a hannu bibbiyu,kuma na amince zan aure ka…..’

Tsantsar mamaki ne ya kama junaid bai ta6a tunanin cewa rishi zata amince da soyayyarshi ba,cikin sauƙi haka batare da ta wahalar dashi ba,ajiyar zuciya ya shiga saukewa wani irin farin cikine ya lullu6e shi,mara misaltuwa a hankali ya shiga furta”Alhamdulillalh Allah nagode maka daka nuna min wannan ranar,dama sae da raina ya bani cewa reeshi ɗina bazata gujeni ba….”

Fuskar jahad ɗauke da murmushi take kallonshi har lokacin hannunshi na ruƙe da nata,

farin cikin da tagani a fuskarshi yasa taji aranta dama dagaske ita yake so,da ta bashi kyakkyawar kulawa,amma da alama akwai wadda yake so,tunda taji ya ambaci sunan reesh wannan ne yasa jikinta yin sanyi,

 

“Allah yasa ba mafarki nake ba,in ma mafarki nake kada ki tashe ni,’yayi maganar yana dariya tare da zame hannun shi daga nata,ya tallabo fuskarta da tafin hannayenshi,yana ƙare mata kallo,hakanan ya dinga jin kamar ta canza mashi,ƙura mata ido yayi kamar mai son gano wani abu,

“Reesh kin canzamin sosae,sai nike ganin kamar bake ba,’

Shiru jahad tayi tana cigaba da kallonshi,sakin fuskarta yayi tare da zura hannunshi cikin hijab ɗin jikinta,ae kuwa a firgice jahad ta ƙanƙame jikinta dake ta faman kerma cike da tsoran abunda zaiyi mata,

Cikin lallausar suman kanta yakai hannunshi yana shafa gashin kanta yace”meyasa baki ɗaure gashin kanki ba?bai takura maki ahaka?

atsorace jahad tace”ni na cire shi,yana acikin school bag ɗina,”

Zame hannunshi yayi daga cikin hijab ɗin nata,

“Zan ɗaure maki shi,ki ɗauko ribbom ɗin naki,”

Kamar karta ɗauko mashi amma tunawa da cewar yana da ta6in hankali in ranshi ya 6aci zai iya kai mata bugu,hakan yasa ta janyo school bag ɗin tare da zuge zip ɗin,ta curo mashi ribbom din ta miƙa mashi sannan ta mayar da jakar abayanta,

kar6a yayi tare da zura shi a cikin hannunshi,sannan ya ƙara matsawa kusa da ita sosai,cire hijabin jikinta yayi sannan ya janyota asaman chest ɗinshi,gaba ɗaya jahad ta gama rikicewa,ba ƙaramin yanayi junaid ya jefa ta ba,

lamo tayi ajikinshi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarenshi,

Xuba ma yalwataccen gashin nata ido yayi yana kallonshi,kafin daga bisa ni ya sanya hannunshi tare da tattaro shi wuri guda,ya ɗaure mata shi da ribbom ɗin,

muryarshi taji acikin kunnanta yana cewa”Reesh,ya akai naga launin gashin kanki ya canza?ba brown colour bane?yanzu kuma naga ya koma dark black,?kodai idona ne ke nuna min ba daedae ba’?shiru jahad tayi batace mashi komai ba,saboda bata da amsar da zata iya bashi,

jin tayi shiru yasa ya ƙyale maganar,hannu yasa tare da rabata da jikinshi,bin ta da kallo yayi ganin yarda take ta faman lumshe ido kamar mai jin bacci,

Cikin sanyin murya yace”Reesh,kina jin feelings ɗin da nake ji agame dake”?

buɗe ido jahad tayi sosai tana kallonshi da wata irin kasalalliyar murya tace”eh,’

jinjina kanshi yayi tare da cewa”nasani,dama nasan kema zakiji abunda nake ji,pls reesh just for today kawai,kiyimun kiss koda a gefen fuskata ne,inaso naji ya ake ji,’

Shiru jahad tayi tana tunanin ya zatayi da wannan ɗan tahalikin,gashi duk yabi ya kashe mata jikinta,ita tausayi ma yake bata saboda ta6in hankalin da yake fama dashi,tausayin shi ne taji ya kamata,mutun har mutun amma bai da cikakken hankali tunda inda yana da hankali ai ba yarda za’ai ya kasa gane ba itace wadda yake nufi ba,tunawa tayi da hosana dake fama da irin lalurarshi,amma nashi haukan yafi na hosana,don bata ta6a ganin wanda bata sani ba,ta liƙe mashi da sunan tasan shi,

bata ƙarasa zancen zucin nata ba,muryar shi ta kuma katseta da cewa”pls reesh,just for today,”

ajiyar zuciya jahad ta saki tare da kai bakinta zata manna mashi kiss acikin dimple ɗinshi,batayi wani aune ba taji bakinta acikin nashi tsulundum,sakamakon wata mota da ta bugi bayan motar shi,wannan girgizar da motar tashi tayi ne yasa bakinta komawa cikin nashi,gaba ɗaya junaid yabi ya rikice ya zauce ya haukace mata,sosai ya ƙankame ta ajikinshi,yana kissing ɗin bakinta ta hanyar zura tongue dinshi acikin bakin,ita kanta jahad a lokacin ta gaza control ɗin kanta,biye mashi tayi,

 

Sosai junaid ya shiga romancing ɗinta kamar zai zauce,duk yarda jahad taso ta kwace kanta a hannunshi amma yaƙi barinta,sai da yayi mai isarshi sannan ya zame jikinshi daga nata,cikin sauri jahad ta kifa kanta asaman laps dinta,tana faman sauke ajiyar zuciya,sam tagaza yarda cewa itace da kanta ta ba wani namiji damar kissing lips ɗinta abunda bata 6ata yi ba,to dama dae duk inda mace da namiji suka ke6e irin haka na ukkun su shaidan ne,Allah ya kyauta.

 

jikinshi ne yayi sanyi,shi kanshi baisan cewa abun zai kaisu ga haka ba,daƙyar ya iya tashin motar da wata irin kasala ajikinshi yake driving din,ya hau saman titi sosae tare da wucewa dasu gida,

 

_💋Boss Bature💋_

 

tashin hankali!Lokacin da Hosana ta fito a nan ta samu osman yana jiransu tsaye a bakin motarshi,

ƙarasawa tayi wurinshi tana cewa”ya Osman Ina jahad ɗin?ina ta nemanta banganta ba,nayi tunanin ta rigani fitowa ne,”

“Wai kina nufin jahad bata acikin school ɗin naku”?ya tambaya hankali a tashe yana kallonta,.

daga mashi kai tayi alamar eh tace”babu kowa acikin makarantar ya Osman,na duba ko’ina ban ganta ba,”

Gabansa ne ya faɗi rass,saboda kullum jahad ita ke riga hosana fitowa,yau kuma hosana ta rigata fitowa,tabbas akwai matsala,

cikin sauri yace”shiga ki zauna bari nashiga cikin classes din na duba ko zan same ta acan,Allah dae yasa ba wani mummunan abune ya faru da ita ba,’

Ya ƙarasa maganar tare da yin saurin shigewa cikin makarantar,buɗe motar hosana tayi tare da shigewa ciki ta zauna tana jiranshi,

lokacin da Osman ya shiga cikin classes din yana neman jahad,duk ajin daya duba babu kowa wayam duk sun tafi gida,ko’ina ya dinga bi na makarantar saƙo da lungu yana dubawa amma babu jahad babu alamarta,tun yana sa ran ganinta har ya fidda rae,yafi ƙarfin awa ɗaya da rabi acikin makarantar yana neman jahad amma bai ganta ba,

 

Cikin sauri ya fito jiki na rawa ya koma cikin motar,ya zauna a mazaunin driver,

Ganin ya dawo shi kadae yasa hosana cewa”Ya osman ina jahad din?baka ganta ba”?

“Na duba ko’ina banganta ba,bansan ina jahad taje ba,bari na fara kaiki gida nasan kin gaji sosai,”

jan motar yayi tare da fucewa daga cikin gate ɗin makarantar,duk yabi ya ruɗe saboda fargabar kada ace wani abune ya faru da jahad,yana jiyo hosana tana shessheƙar kuka tana cewa”Nashiga uku,Allah yasa jahad bata 6ace ba,bansan ya zanyi ba in na rasata ba,kamar yarda na rasa sehrish,”

“Kada ki damu jahad tana cikin ƙoshin lafiya,zan nemo maki ita,in ma ban sameta ba,zan kira major na sanar dashi halin da ake ciki,nasan zaiyi ma marshal Magana,”ya ƙarasa maganar a lokacin da yake shiga kwanar gidan Abusufyan,

 

Yana shiga ciki ya sauke hosana,sannan ya fisgi motar da gudun gaske ya fuce daga gidan,

 

Abunda ya faru bayan fitar motar osman daga cikin school din,Sai ga sehrish hannunta ɗauke da school bag ɗinta,daƙyar take iya tafiya saboda ciwon da tasha,ta jima acikin toilet din tana juyi kafin Allah ya kawo mata sauƙi harta samu ta fito,

ganin babu kowa acikin makarantar yasa taji gabanta ya fadi,nan tashiga fargabar Allah yasa junaid bai tafi ba,tasan dole ya gaji da jiranta,

Lokacin da taƙarasa wurin gate din taga babu kowa sai security guard din dake tsaron makarantar,tamkar ta aza hannu akai ta fashe da ihu haka taji,

Ganin yarinya tsaye cikin damuwa yasa mai gadin ya ƙaraso wurinta yana tambayar ko lafiya,

muryarta tamkar za tayi kuka tace”Mai ɗaukata nake nema,kuma naga babu kowa acikin makarantar,bansan ya zanyi ba,”

mai gadin yace”meyasa baki fito  kin tsaya anan waje ba?me kikeyi acikin makarantar ne”?

cikin shessheƙar kuka tace”bani da lafiya ne,bacci ne ya ɗauke ni kuma babu wanda ya tashe ni,shiyasa bansamu na fito ba akan lokaci,”

“Kuma baki da waya a hannunki”?acewar mai gadin,

ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

“Ko numbar wani baki ruƙe a cikin kanki ba,”

“Bani da numbar kowa,ban ruke akaina ba,”

Cike da takaici mai gadin yace”kaji matsalar,ni yanzu bansan ya zanyi dake ba,amma me zai hana ki ɗan fita daga wajen gate ɗin,wata’ƙil shi drivern naki ya dawo daukarki,nasan ma zai dawo ne,da zarar sunji shiru baki ƙarasa ba”,

Amsa mashi tayi da toh,sannan ta fice daga cikin makarantar ta tsaya a bakin gate din,tana ta ƴan waige waige ko zata hango motar junaid,

 

_💋Boss bature💋_

 

A hankali motar junaid ta ƙetare babban gate din gidan nasu,a lokacin jahad ta ɗago da kanta,ta cikin glass ɗin take hangen katafaren gidan,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,yau gata acikin gidansu ya Omar dinsu,koba komai zata hadu dashi harma ta sanar dashi halin da suke ciki na rashin ganin shi,addu’a tashiga yi acikin ranta Allah yasa Ya Omar na nan,

tsayar da motar junaid yayi tare da buɗewa ya fito sannan ya zagaya ya buɗe ma Jahad motar,cikin sanyin murya yace”Reesh,am really sorry game da abunda ya faru a tsakanin mu,na fita hayyacina ne shiyasa,kinsan cewa ba halina bane…..kuma bazan ƙara ba insha Allah,

Murmushi jahad ta sakar mashi ayayin da take fitowa daga cikin motar tace”just forget about it,komai ya wuce,na yarda dakai sosai nasan cewa bada son ranka hakan ta faru ba,

ba ƙaramin daɗi junaid yaji ba,ya jima yana mamakin nasarar daya samu akan reeshi ɗinsa,farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,

Bayan ya rufe motar ya ruƙo hannunta suka shige cikin gidan atare,a ruɗe jahad ke kallon katafaren gidan,jinjina kai kawai takeyi acikin ranta tana cewa”wai dama a wannan daular ya Omar ke rayuwa!gidan yayi mun kyau ya haɗu sosai,Allah yasa yana ciki,inaso na cika ma hosana alƙawarinta na ganin na haɗata da ya Omar dinta,

Download>>> Boddiya Complete Hausa Novel Document – Aihausanovels

Babu kowa acikin main palour ɗin,sakin hannunta junaid yayi tare da cewa”bari na shiga ciki na huta,da anjima zan shigo muyi magana,”

amsa mashi tayi da toh,cikin sauri junaid ya wuce bedroom din Abbansu,

tashin hankali,jahad fa batasan ina zata dosa ba,gata dae acikin gidansu Omar,batasan a ina zata ganshi ba,

Tsayawa tayi ƙiƙam batare da ta motsa ba,

Gyaran muryar da taji ne yasa ta yin saurin juyawa don taga wanene,

Azmee ce ta fito sai faman sakar mata murmushi takeyi,jikinta sanye da jallabiya,ta ɗaure kanta da mayafi,ta fito fess abunta,

Gaban jahad ne ya shiga faduwa aranta tashiga tunanin cewa kodae wannan ce mahaifiyarsu?Amma meyasa naga tana sakar mun murmushi kamar tasanni  itama…?

Bata ƙarasa zancen zucin nata ba,azmee ta ƙaraso tare da janyota jikinta ta rungumeta tana cewa”Sannu da dawowa kyakkyawata,ya school din?

Tayi maganar tare da raba jikinta daga na Jahad,

Zuru jahad tayi duk tabi ta dabarbarce ta rasa ganema wannan abun al’ajabin,tamkar a mafarki haka take ganin wannan ikon Allah,

“Rishi lafiya naga kina bina da kallo?kodae bakya jin daɗi ne?nayi magana baki amsa mun ba”

Cikin en ina jahad tace”am…um…lafiya lou,makaranta Alhamdulillah,’

Azmee tace”ko ke fa,shigo daga ciki na hada maki lunch ki ci,ko kya dawo daedae don na lura yau ba ƙaramar yunwa kika kwaso ba,”

Tayi maganar tare da ruƙo hannun jahad taja ta suka nufi dakin sehrish,da kanta ta buɗe mata kopa tare da shigar da ita ciki tace”ki zauna ki huta,yanzu zan haɗo maki lunch,”tana faɗin hakan ta rufe mata dakin,

Abun ya gama ɗaure mata kai,juyawa tayi tana ƙarema bedroom ɗin kallo ba ƙaramin kyau yayi mata ba,daga bisani kuma ta shiga damuwa akan wane hali hosana ke ciki,tasan cewa zasu nemeta sosai,kuma in basu ganta ba hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba,

komawa tayi daga gefen gadon sehrish ta ɗan zauna,ya zama dole in koma gida,kada hosana tayi ta kukan rashina akusa da ita,bansani ba ko zan samu ya omar acikin gidan nan ba,ni ba komai yafi ɗauremun kai ba face yarda suke nuna kamar sun sanni,bayan bamu ta6a haduwa da kowannansu ba,to kodae dukkansu suna da mental illness ne?ta jefa ma kanta tambaya,

 

Turo kopar azmee tayi tare da shigowa hannunta ɗauke da tray wanda ta shirya mata lunch,ƙarasawa tayi tare da ajiye mata tray din asaman bedside drawer dinta tace”Wannan farfesun da kike gani,hajiya azeema na shirya mashi,ƙanwar abbanku da nake gaya maki,tana nan ta iso,nasan bakisanta ba,amma kin ta6a ganinta lokacin da Sgr da Omar suka dawo daga U.S kin tuna”? Fuskarta ɗauke da murmushi takeyi mata maganar,

Jin ta ambaci sunan Omar yasa jahad cewa”Ya Omar na nan”?

Azmee tace”eh,yana acikin part dinshi,amma meyasa kika tambaye shi?maimakon ki tambayeni mutumin ki Sgr”?

“Babu komai,kawai inason ganin shi ne,”ta bata amsa,

Azmee tace”ki bari idan kin kammala shan farfesun sae kije ki same shi adakin shi,’

gyaɗa kai jahad tayi tare da cewa toh,nagode sosai,bari na fara sha,

Juyawa azmee tayi tare dayi mata sallama ta fuce daga dakin,a ranta tana tunanin ko wani abu ke damun rishin ne taga duk tayi sukuku.

 

Zama jahad tayi tare da dauko plate ɗin dake ɗauke da farfesun,sae uban ƙamshi ke tashi,duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hanata shan farfesun nan ba,sae da taci ta ƙoshi, sannan ta miƙe tare da shiga toilet ta wanko hannayenta,

Bayan ta fito komawa tayi saman gadon ta zauna cike da zullumin mai zai biyo baya,

 

_💋Boss Bature💋_

 

Marshal Omar na kwance saman gadonshi yayin da idanunshi suke kallon saman ceiling bakomai yake tunani ba face hosanar shi,kowane hali take ciki yanzu?taci abinci kuwa?tambayoyi iri iri ya shiga yi ma kanshi,

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document – Aihausanovels

yana cikin wannan tunanin wayarshi dake ajiye gefenshi ta shiga yin ringing,miƙa hannu yayi tare da daukar wayar,duba mai kiran nashi yayi ganin sunan Major ya bayyana akan screen din wayar yasa shi saurin ɗaga wayar tare da karata akan kunnanshi,

Ko sallama major baiyi mashi ba saboda tsabar tashin hankalin da yake ci,

“Yalla6ai yarinyar nan fa ta 6ace,an neme ta an rasa ko’ina na makarantarsu,ɗazu osman ya kira ni awaya yake sanar dani cewa yaje ɗaukarsu a school,hosana kaɗae ya gani banda jahad,mun duba ko’ina babu ita,”

Waro ido waje Omar yayi ba arziƙi ya sauko daga saman gadon yana cewa”Major!ban fahimci me kakeson sanar dani ba!kayi mun da yaren da zangane,”

Major yace”yalla6ai,jahad ce ta 6ace a school,’

Rai a6ace Omar yace”Garin yaya hakan ta faru!taya akai Osman yayi gangancin da har ya bari jahad ta 6ace bai ganta ba!’duk inda take ku nemo mun ita in ba haka ba,ran kowa zai 6ace don bazan lamunta ba,”

Yana ƙarasa maganar ya kashe kiran,gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji daɗi,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoronshi kar ace jahad ta gudu ne don taje nemanshi saboda halin da hosana ke ciki,

Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin nashi,zuciyarshi nata tafarfasa saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,abubuwa sunyi mashi yawa,yana cikin damuwa sosai,ga kuma wata damuwar da major ya ƙara mashi,na 6atan jahad,

ɗago da wayar ya sake yi a hannunshi ya shiga dialing wasu numbers,

sannan ya dannama numbar kira,nan take kiran Ya shiga aka ɗaga wayar,

tun kafin yayi magana wata murya kakkaura ta karaɗe kunnanshi da cewa”We are waiting for ur command sir,”

Cikin harshen turanci omar ya shiga basu bayani akan 6atan jahad,

Ya ƙarasa maganar tare da cewa yanzun nan zan tura maku da hoton ta,banason ta ƙara 1 hour awaje,duk inda take ku nemota,adawo mun da ita gida,”

“Okey sir,’suka amsa mashi,sannan yayi rejecting kiran nasu,

sai bayan daya kashe wayar sannan ya tuna cewa baida hotonsu,amma yasan baza arasa ba wurin osman,

Batare da 6ata lokaci ba,ya kira osman awaya,bugu ɗaya osman ya ɗaga kiran cike da fargabar abunda omar zai sanar mashi,

“Osman!”

Murya na rawa osman yace”Na’am yalla6ai,”

“Inaso ka turomin hoton jahad yanzu in kana dashi awayarka,inma babu ka ɗauko mun hoton fuskar hosana,ina jiranka yanzu karka 6ata mun lokaci,’

yana kai ƙarshen maganar tashi ya katse kiran,cigaba da zagaye ɗakin yayi yana jiran osman,

within 15mins,sai ga kiran osman ya shigo,

ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnanshi,

On the other hand Osman yace”yalla6ai na turo da hoton,ta cikin Whatsapp dinka,”

“Okey,” ya amsa tare da katse kiran,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin duba whatsapp dinshi,anan yaga hoton da Osman ya turo mashi,zuba ma hoton ido yayi yana kallonshi,nan take yaji kewarta ta kama shi sosai,hoton hosana ne Osman ya ɗauko mashi,da alama sabon hotone yayi mata da wayarshi,ko uniform dinta bata cire ba,fuskarta da alamun hawaye saboda kukan da tasha na 6atan Jahad,

Lumshe idonshi yayi tare da buɗesu akan hoton yana ƙare mashi kallo,a hankali ya furta”I love u so much hosana,nayi missing ɗinki sosai,kamar nayi hauka,nashiga damuwa sosai akan rashin sanyaki a idona,bazan iya jurewa ba hosana,kina buƙata ta a kusa dake,zanzo don na lallashe ki nasan zaki shiga damuwa sosai akan rashina da kuma rashin jahad akusa dake,

Tura masu hoton yayi sannan ya kira major awaya ya sanar dashi cewa ya jira shi a waje,gashi nan fitowa,

Yana kammala yin wayar cikin sauri ya fito daga part ɗinshi,ya sauko downstairs,da sauri da sauri yake nufar hanyar fita daga main palour din,

yana ɗaga ƙafarshi zai fita yaji an ambaci sunan shi”Ya Omar,”

gabansa ne yaji yayi wani irin bugu,aranshi yace”wannan ae muryar Jahad ce,

da saurin gaske ya juya tare da kai idanunshi wurin da jahad take tsaye sanye cikin uniform tana kallonshi,fitowarta kenan daga bedroom din sehrish,cikin sanɗa take tafiya zata gudu daga gidan,kwatsam ta hango shi sai faman sauri yake yi zae bar gidan,

Download>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel

Kanshi ya gama ɗaurewa binta yayi da kallo gaba ɗaya ya rikice aranshi ya shiga tunanin cewa anya ba kunnan shi bane suka jiyo mashi muryar jahad!wannan ae yarinyar gidansu ce sehrish,muryarta ce tayi mashi gizo yaji kamar ta jahad,

Murmushi ya saki tare da nufarta yana cewa”Sister har kin dawo daga school ɗin?ya karatun naku,ina fata kina mayar da hankali ko?

Kamar zatayi kuka tace”Ya Omar,Jahad fa ce! Nice jahad,ya Omar meyasa ka tafi kabarmu,”!

Zaro ido waje Omar yayi cike da mamaki yake kallonta, muryar shi na rawa yace”Jahad!dagaske kece kodae kunnena ne ke jiyemun ba dae dae ba”?

fashewa tayi da kuka tare da ƙarasawa wurinshi ta kwantar da kanta asaman ƙirjinshi tana cewa”Ya omar dama kana nan,da ranka da lafiyarka amma kadaina zuwa wurinmu?meyasa ya Omar?bakasan halin da muka shiga ba ni da hosana,na rashin ganin ka,’

tashin hankalin da ba’a sama shi date,

ruko hannunta Omar yayi tare da janta suka shiga cikin wani corridor inda ba kowa,sannan ya kalle ta cike da mamaki yace”Jahad!nagaza yarda cewa kece!taya akai kikasan gidan mu har kika zo?

cikin shessheƙar kuka tace”bani na kawo kaina ba,kawo ni akayi,wannan ƙanin naka junaid,wanda ka ta6a nuna mana hotonshi nida hosana a gida,shi ya ɗaukko ni daga school ya kawo ni gidan nan,bansan meyasa ya ɗauko ni ba,ya nuna kamar yasanni bayan bamu ta6a haduwa dashi ba…..’

Tun kan ta ƙarasa maganar Omar yace”subhanallahi!an samu matsala,junaid yayi kuskuren ɗauko ki jahad,Yarinyar gidan nan yaje daukowa a school,da yake kuna kama da ita sosai,komai na fuskarku iri ɗaya sak,shiyasa ya ɗaukko ki amaimakonta,’

mamaki ne ya kama jahad jin abunda Omar yace,sae lokacin ta tuna da sunan da Junaid ya dinga kiranta wato Reesh,taya akai suke kama da yarinyar gidansu har kanin nashi ya gaza banbantasu!” ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta,

“Jahad,muje na sauke ki gida,in yaso sai mu ƙarasa tattaunawa acan,”

Ya ƙarasa maganar tare da fitowa ruke da hannunta suka fice daga cikin babban falon,anan waje ya samu Major tsaye jingine da mota yana jiranshi,

Koda ya ganshi ruƙe da hannun jahad mamaki ne ya kamashi,dama shi bai ta6a ganin Sehrish ba,tunda ba shiga ciki yake yi ba,basu ta6a arba da ita ba,

Fuskarshi dauke da murmushi yace”Sir!anganta kenan”?

Omar yace”eh,ba rabon musha wahala,wai junaid ne ya ɗaukota daga school shi duk atunanin shi wannan yarinyarce ta cikin gidan nan,da yake kamanninsu iri daya sak,’

major yace”ikon Allah,amma ni ban ta6a ganin yarinyar ba,’

ya ƙarasa maganar a yayin da yake buɗe masu mota suka shige ciki,sannan ya tashi motar yabar gidan ɗauke dasu,

 

_💋Boss Bature💋_

 

A 6angaren sehrish kuwa,tana cikin tsayuwar nan agefen titi tana jiran zuwan junaid,sai ga motocin waɗannan fusatattun sojojin da Omar ya turo don su nemo mashi jahad,ae koda sukayi arba da sehrish,suka duba hoton da Marshal Ya tura masu suka ga iri ɗaya fuskar,sae ransu ya basu cewa itace yarinyar da Omar yace su nemo mashi,

Da sauri suka tsayar da motocin nasu tare da diddirowa daga saman motocin tamkar wasu zakuna haka suka tunkari sehrish,

Kamar ance ta juya,idanunta sukayi arba da waɗannan sojojin dake tunkararta hannunsu ruke da bindigu,bakomai ne ya fado mata a ranta ba face Ƴan boko haram da ƴan bindiga daɗin dake ta sace mutane agari,

ja da baya tashiga yi gabanta na faduwa

maimakon suyi mata magana cikin daɗin rae sai suka daka mata tsawa tare da cewa”ke zonan”!

Aikuwa a firgice sehrish ta watsa da gudun gaske ta saki jakar makarantarta ƙasa,bin ta sukayi da gudun gaske,tana gudu suna bin ta tamkar zata tashi sama,

yarda kasan wadda taci ƙafar kare haka ta dinga gudu,ita kanta batasan inda ta dosa ba,gudu kawai takeyi,

 

adaidai nan su Omar suka ƙaraso gidan uncle Abusufyan,Wayarshi ta shiga ruri,cikin sauri ya fiddota daga cikin aljihun wandonshi,yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanshi yayi sallama,

Muryar ɗaya daga cikin sojojin ce yaji yana cewa”Sir,munga yarinyar da ake nema,amma taƙi bari mu kama ta,’

Hankali tashe Omar yace”Kada ku bari ta kufce maku,kuyi ƙoƙari ku kamota,kuyi mata magana cikin sanyin murya,saboda yarinyar tana da tsoro sosai,kun firgitata ne shiyasa ta gudu,

“Okey sir,ya amsa mashi tare da katse kiran,

“Yalla6ai meya faru ne”!

Cike da takaici Omar yace”Major,an samu matsala!sojojin dana tura don su nemo mun jahad,sunyi arba da yarinyar gidan mu,dama na faɗa maka cewa kamanninsu sak iri ɗaya,ɗazu nace ma Osman Ya ɗauko mun hoton fuskar hosana,saboda in tura masu suyi amfani dashi wurin nemo min jahad,to da wannan hoton su kayi amfani wurin nemanta shine Allah ya haɗasu da ita yarinyar da junaid yayi musanya da jahad,’

Tunda yasoma magana jahad ke kallonshi cike da mamakin wannan wani irin kamanni ne,dayasa har ba’a gane banbancinsu!?

Major yace”Amma nayi mamaki yalla6ai!wannan wata irin kamanceceniya ce atsakaninsu da har ba’a iya bambanta tsakaninsu”!

Omar yace”nikaina major abun ya jima yana ɗaure mun kai wlh,da farko nayi tunanin cewa saboda ƙaunar da nakeyi ma su hosana ne yasa nake ganin fuskarsu akan fuskar yarinyar,amma yau da junaid ya dauko jahad a matsayin ita yarinyar,sai na tabbatar da cewar ba gizau bane,tabbas kamanninsu ne ɗaya!

Major yace”abun mamaki abun al’ajabi!yalla6ai kada kace na cika ka da surutu,dan Allah yaya kuke da ita yarinyar?ko ƴar wurin uncle ɗinku ce,’ ya ƙarasa maganar adaedae lokacin da yayi parking ɗin motar a cikin gidan Abusufyan,

murmushi Omar yayi tare da cewa”ƴar aikin gidanmu ce,sunanta Sehrish! Yarinyar tana da kirki sosai shiyasa Abbanmu ya mayar da ita tamkar ɗiyarshi,yanzu amatsayin kanwarmu take…………’

Waro ido waje Jahad tayi cike da tsananin mamaki ta furta”SEHRISH!!!!!!!!!!!!!!!!”

 

Download>>> Sexxy Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

 

juyawa Omar yayi yana kallonta jin yarda ta ambaci sunan kamar tasanta,shima major juyowa ya danyi daga zaunen da yake a front seat din suna kallonta,

“Jahad kin santa ne!”?

Muryarta na kerma tace”Ya…Omar…Bansan ko ita bace ba,amma akwai ƴar uwarmu da muka jima muna nemanta,kamanninmu sak iri ɗaya,Mu ƴan ukune dani da hosana da kuma ita,Sunanta Sehrish atare aka haife mu,ciki ɗaya muka fito tare da ita,arana ɗaya kuma a lokaci ɗaya…….’

Kallon juna Omar da major sukayi cike da mamaki suke sauraronta,sae da takai ƙarshen maganarta,sannan Omar yace”Dama ke da Hosana ba twins bane!!!”?

ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tace”WE’RE TRIPLET”.

 

 

Wannan shirin da kuke karantawa ba ammasco bane suka ɗauki nauyin kawo maki shi ba,Boss bature ce da kanta,ta shirya kuma ta gabatar,😂

 

Idan har kinji daɗin wannan update ɗin,kiyi following din acct dina a tiktok😍😂ga link can na bada daga sama

Back to top button