Description/Story:
Description
Ummi tana tafe tana yan wakokinta, tareda gudu hade da tsalle. cinikin ummi ne gudu, sam bata tafiya a hankali, daga can gefe ta hango wata yarinya wadda bazata wuce sa’arta ba. Tace,”Yauwa, ga Firdausin data tsokane ni” ta nufi, wurinta tashiga gabanta ta rike kugu. “Firdausi wa kike tsokana?
Fiddausi tace “Ban tsokane ki ba fa” Cikin tsoro tayi maganar ummi ta shako mata
wuya. ina jin lokacin da kika ce ummi tsiga. Ban ce ba inji fiddausi ummi ta hankada ta tare da cewa “Allah yaso ki.”
Nikam garin da fiddausin tayi ya ta kasa tace “kin gani ko? wallahi sai kin biyani” ta soma kuka, Ummi ta sheka da gudu, sai gida. Tana ajiye man gyadan data siyo ta nufi ba daki don fitsari ya matse ta umma dake zaune tana fadin. “Da mutum! Da mutum!!” saida ummi ta bude. Ganin yaya Abba tayi, da gudu ta juyo ta fada dakin umma,jiki na bari bayan tayi bol da dakakken yajin da umma ta daka zata soya mai don cin abincin rana. Sai kuma ta tuna cewa bata tsira ba,don Abba tsaf zai binciko ta. Ta fito da gudu ta nufi dakin tsohuwa.
Tsohuwar tana sallar azahar Ummi ta tsallake ta ta kutsa kasan gado nan ma tayi ciki da furar da tsohuwar keson sha da zarar ta idar da sallah. Alhaji babba tasa ya aiko mata da furar daga kasuwa don tasha da rana. Abba ya fito wanka ranshi a bace dakin umma ya nufa yana fadin “ummi ke ummi zonan”
Ya samu Umma tana tattara yajin da Ummi ta zubar, tana fada. Ya ce, “Umma ban san irin dukan da zan wa Ummi ba yau. Ta ce, “Abba ka mata dukan mutuwa, na gaji da halin Ummi.
Yarinya sai ka ce ‘yar fata? Ka dubata ta tafi dakin Tsohuwa, don ta san zata hana a dake ta.” Ya ce, “Allah sai dai Tsohuwa ta yi ta fadanta, amma ba zan barta ba. Ya juya zai tafi, suka ji muryar Tsohuwa tana fadin. Ba zan yi fada ba, ka kashe ta ka ji mai sunan Malam, ba na son ka barta da rai. Ta dubi Umma” ke kuma Suwaiba dama kin san ba za ki daraja sunana ba ki ka sa a ka sa miki don kiji dadin ci min fuska?” Umma ta ce,” Ba haka ba ne Tsohuwa, Ummi ba ta yo halinki ba. Ita fa rashin hankali ne da ita. Yayanta fa ke wanka ta zo ta leka shi, nan kuma tazo ta zubar min da barkono. Abba ya ce, “Umma don Allah kiyi shiru ki kyale Tsohuwar nan, ai ita ta 6ata Ummin, duk abn da yarinyar nan tayi sai ta hana a yi mata fada. Uhm duk fadanki yau sai na dake ta, ba sunan ki ba in ma kece, “Tsohuwa tasa kuka gami da salati. “Yanzu mai sunan Malam ni kake fadawa haka?” ya ce, “An fada miki.” Umma ta ce, “kai Abba zan sa6a maka jeka.” Ta juyo wurin Tsohuwa, Don Allah kiyi hakuri……………
Some of related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.