Uncategorized

Innalillahi an fara garkuwa da mutane a cikin birnin Kano.

 An sace wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar a unguwar Kawaji da ke cikin birnin Kano ranar Asabar.

 Masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da ita, inda suka zo a kan babursu,  suka kama yarinyar suka yi awon gaba da ita 

 Wata jarida ta wallafa cewa ta lamarin ya faru ne da karfe 5 na yamma lokacin da ita da wasu yaran unguwarsu suke dawowa daga makarantar islamiyya.

 “Tsakin gidansu da makarantar Islamiyya babu wata tazara mai yawa.  Don haka yara kan yi tafiya su kaɗai zuwa makarantar tare da yan uwansu,” in ji kawun yarinyar mai suna, Suraj Zubair.

 “A cewar rahoton wasu yaran da lamarin ya faru a gaban idanunsu, masu garkuwar sun zo ne a kan babur uku, inda suka ce za su kai su gida.  Amman dukkansu sai suƙaƙi zuwa, sai Hanifa ce kawai ta je, su kuma yaran suka ruga zuwa gidajensu.

 Unguwar Kawaji da ke karamar hukumar Nassarawa na daya daga cikin unguwannin da ake fama da matsalar sace yara a Kano.

 HAR ILA YAU: Yusuf Nasiru

 A cikin unguwar kuma an yi garkuwa da Yusuf Nasiru dan shekara 9 a ranar 28 ga Disamba, 2020 bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya da yamma.

 Idan za a iya tunawa, a watan Oktoban 2019, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu gungun masu garkuwa da mutane shida bisa zarginsu da yin garkuwa da su, da sayar da su tare da tilasta musu musuluntar yara tara a garin Onitsha na jihar Anambra.

 Bayan da aka yi garkuwa da kananan yara a Kano a shekarun baya tare da kubutar da wasu daga cikinsu a kudancin kasar nan, Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin bincike don binciki yadda ake tauye hakkin yaran da aka ceto tare da bankado duk wasu shari’o’in.  wadanda suka bace daga 2010 zuwa yau a jihar.

 “Ina so in yi amfani da wannan kafar don kiran wadanda suke da bayanai masu amfani game da inda Hanifa take, su tuntubi ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko a kira wannan lambar: 08032668195.”

Back to top button