Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 47 Complete Novel
*ASM Bk2047*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……….A can k’arshen barandar Classes d’in su Fauzy ta hangota tsugunne bayan ta fito ta nufeta da sauri tana zuwa ta duk’a ta dafa Shoulder d’inta tana kallon yadda take faman maida numfashi gaba d’aya ta amayar da breakfast d’in da ta ci cike da damuwa Fauzy tace “Sannu Zarah abun har ya kai haka” shiru tay tana cigaba da yin nishi ta d’age kai sama Fauzy ta sake cewa “to ko cikin ki ne ya 6aci?” a hankali ta girgiza mata kai alamar a’a Fauzyn tace “to gaskiya ina tunanin Malaria d’in ce dai muje famfo ki wanke Fuskar ki sai mu wuce cikin Asibiti kiga Doctor” sauke ajiyar zuciya tay tana kokarin daidaita natsuwar ta a sanyaye tace “ba sai mun je ba Fauzy nasan Malaria d’in ce ma kawae in mun koma Hostel zan sha magani” cike da damuwa Fauzy tace “to amman ai bamu da maganin Malaria d’in iya paracetamol ne sai na ciwon ciki” tace “shikenan bari muga zuwa a tashi in ban samu sauk’i ba sai mu siya in mun fita” shiru Fauzy tay ganin Fatun na kokarin tashi yasa ta kai hannu da sauri ta taimaka mata suka nufi famfo ta wanke face d’inta sosae da bakinta ta sha ruwan kafin suka nufi Class, lokacin da suka shiga gaba d’aya aka maido idanu kan su Malamin su dake tsaye yay mata sannu ta amsa kafin ya tambayi abunda ke damunta Fauzy ta bashi amsa da Malaria ce ya jinjina kai suka nufi seat, tunda ta zauna ta kife fuskarta akan desk nan da nan bacci ya kwasheta har akayi break sannan Fauzy ta tada ta ta tambayeta mi take so ta siyo mata tay d’an shiru don ji take bata son komae can tace mata ta amso mata youghort kawae ta amsa da to ta tafi, bada jimawa ba sosae ta dawo lokacin har taci gaba da yin baccin Fauzy ta tashe ta ta bata bayan ta bud’e mata ta amsa a hankali ta fara kur6a Fauzy na mata sannu tana d’aga kai sai gashi har ta shanye kuma bata ji zuciyar na tashi ba, sosae Fauzy taji dad’in ganin ta d’an warware har tana dariya da suna magana koda malamin su ya shigo bata koma ta kife kan ba ta tsaya ta saurari abunda yake koya masu, cikin sa’a har aka tashi bata sake yin aman ba suka nufi Hostel suna zuwa suka fara shirin tafiya Weekend Fatun tace ma Fauzyn tazo suje gidan su tayi weekend d’in acan in Haulat ta dawo sai suje tace to bari ta tambayi Aunty Mareeya, koda ta kirata ce mata tay Fatun ce bata lafiya zata kaita gida daganan za tay weekend d’in a can Aunty Mareeyar tace Subhanallahi miya sameta tace mata ba ciwo bane Sosae Malaria ce harda amai ta sata tayi mata Addu’ar samun sauk’i tace taje dama itama gobe Daura zata je sosae Fauzy taji dad’i tayi mata godiya da Allah ya kiyaye hanya Fatuu ma nata murmushin jin dad’i, gaba d’aya riga da skirt na lace suka sa sukai d’an makeup kowacce ta rataya jakar goyonta bayan sun yafa gyalensu sun yi kyau sosae abun ka da farare a tare suka fita suka rufe d’akin kafin suka tafi Lokacin k’arfe ukku na rana, lokacin da suka isa gidan gwaggon bata nan sai kawu Amadu shima bacci yake a d’akin shi, a d’akin Fatun suka sauka wannan ne zuwan Fauzy tayi Weekend a gidan na biyu don lokacin da Suke aji d’aya ta ta6a zuwa, bayan Fatuu ta aje jakar ta ta cire mayafi ta fito ta nufi kitchen don ta zubo masu Abinci waina da miya taga anyi ga kuma tuwon dare shima anyi murmushin jin dad’i Fatuu tay a ranta ta ayyana gwaggo ba dae kokari ba har tayi Abinci haka kafin ta tafi, wainar ta zuba masu ta nufi d’aki itama Fauzy tana ganin wainar ta washe baki don ta kwana biyu bata ci ta ba sosae suka ci Fatuu harda sud’e plate, saida akai sallar la’asar sun fito yin Alwala suka had’e da Kawu Amadu shima ya fito yin Alwalar yana ganin Fatun yace mata yaushe suka zo tace mashi yanata sharar bacci lokacin da suka zo gashi ya bar ma Mutane gida a bud’e salon a shigo ai masu sata ya wurga mata harara yace ta bar ganin fa ta girma har yanzu bata wuce bugu a wurin shi ba Fatun tay wata yar iskar dariya tace “ni yanzu Kawu Amadu ai mai buguna sai dae ko ruwan sama amman ko gwaggo ai na mata girma da bugo balle kai” jinjina kai yay ya d’an cije leben shi na k’asa yace “kawai dae kawae shikenan…” Fatuu ta katse shi tace ya fad’a mana kawai dai mi yana yar dariya yace “kawae dai bazan buge ki ba don kada Romeo yasa a kama ni don naga shima kaman ya shigo hannu” ya k’arasa yana tik’ar dariya ba kamar da ya ga yadda ta tamke Fuska Fauzy ma sai dariya take ganin yadda suke drama sai kace ba kawunta ba sai lokacin ta gaishe da shi yana murmushi ya amsa yay mata ya Makaranta tace lafiya lau daga haka ya wuce ya d’ibi ruwan ya nufi hanyar waje yana cigaba da yi ma Fatuu dariya, sai bayan sallar isha gwaggo ta dawo suka tare ta tana ganin Fauzy ta washe baki tana amsa mata sannu da zuwan da take mata tay mata ya Makaranta da Auntyn ta tace lafiya lau daga baya ta wuce d’akinta Fatuu tace ma Fauzy tazo su zuba Abinci suka nufi kitchen tare bayan ta zuba suka kai cikin parlor ta fito ta nufi d’akin gwaggo lokacin ta gama cire kayan aikin Fatuu tace mata ta taho Parlor suci Abinci tana yar dariya tace to a bari tayi wanka sai tazo ta mak’e mata kafad’a sai kace wata k’aramar yarinya gwaggon nata dariya saida ta tasata gaba suka tafi parlon a tare ta zuba masu tuwon alkamar da miyar karkashi mai kyau gwanin yauk’i taji kifi tarwad’a da suka fara ci sosae tuwon yay ma Fatuu dad’i don har wani lumshe idanu take wasa wasa sai gashi har suka k’oshi amman ita bata k’oshi ba saida ta k’ara gwaggo na fad’in bari cikinta ya fashe duk sukai dariya bayan sun gama suka fita da kayan gwaggo ma ta fita don yin wanka tana fitowa tay sallar isha ta haye gado su kuwa suna a parlon suna yin kallo saida dare yay sosae Fatuu ta kashe kayan kallon suka nufi d’aki don su kwanta, Washe gari a tare suka gyare gidan tsab bayan sun gama suka d’aura girkin rana koda gwaggo ta fito don ta kama masu ce mata sukae sun yafe taje ta huta tana dariya ta shi masu Albarka cike da farinciki suka amsa ta koma d’akin, bayan sun gama suka zuba mata Fauzy ta kai mata d’akin ta Kawu Amadu ma aka zuba mashi su kuma suka yanke su fara yin wanka sai su ci, bayan duk sun yi wankan lokacin gwaggo ta tafi aiki saida sukai sallar Azahar sannan suka zuba abincin suka shiga Parlor akan Carpet suka zauna, Fatuu na fara cin Abincin wanda shinkafa da wake da miya ne taji zuciyarta ta fara tashi hakan yasa ta d’an dakata ta gumtse baki kwata kwata Fauzy bata lura ba don tana ci tana kallon Tv gaba d’aya hankalin ta ya tafi saida ta d’an d’auki lokaci jin tashin zuciyar ya lafa yasa taci gaba da ci can wani irin yunkurin amai ya taso mata ta tashi da sauri ta nufi hanyar waje hakan ya maido hankalin Fauzy kanta ta bita da ido can ta jiyo ta tana ta Kwara amai da sauri ta mik’e ta fita ta nufi inda take a duk’e ta tsaya kanta tana ta mata sannu sai ga Kawu Amadu ya fito ya nufo inda suke ya tsaya da d’an alamun razana ya tambayi Fauzy miya faru take amai haka itama duk damuwa ce akan fuskarta tace mashi tana tunanin Malaria ce ke damunta dama jiya a School ma saida tayi yace to bata je taga likita ba Fauzyn tace eh da yake tunda tayi bata k’ara yi ba kuma duk alamu sun nuna malaria d’in ce don harda jiri tace tana ji da yake yanzu haka take ma Mutane, jinjina kai yay ya kalli Fatun dake k’ok’arin mik’ewa yay mata sannu ta d’aga mashi kai ta nufi famfo ta kunna tana wanke fuskarta da bakinta ta kora aman, Amadu dake kallonta yace inta gama ta duba d’akin gwaggo yasan ba’a rasa maganin Malaria d’in ta d’aga mashi kai yace mata Allah ya sawak’e ya juya, bayan ta gama kama hannunta Fauzy tay zasu koma Parlor Fatuu tace mata bari taje d’aki kwanciya take son yi tace to taje ta d’aukko maganin sai ta sha bari ta kawo mata ruwa ta saki hannunta ta nufi Parlor don d’aukko ruwan, a d’akinta ta iske ta bayan ta d’aukko ruwan tana ruk’e da Maganin data d’aukko ta bud’e mata ruwan ta bata ta sha maganin bayan ta gama ta mik’a mata robar ita kuma ta kwanta gefenta Fauzy ta zauna cike da damuwa tace mata to yanzu mi zata ci tunda ta amayar da wanda ta ci da sauri ta girgiza mata kai alamar bazata ci komae ba kafin ta lumshe ido nan da nan bacci ya d’auketa duk sai Fauzy taji Abincin ma ya fitar mata a rai ta mik’e ta koma Falon ta kwashe kayan ta kai Kitchen bayan ta fito ta nufi d’akin a gefen Fatun itama ta kwanta bada Jimawa ba itama bacci ya kwasheta, sai bayan da akai sallar la’asar Amadu ya shigo ya tashe su don suyi salla tun Fatuu na cikin yin sallan ta ji wani irin kwad’ayin shawarma ya kamata bayan sun sallame ta kalli Fauzy tace mata bakinta ba dad’i ta zo suje su siyo shawarma daga nan sai su biya shagon Aunty Zee su siyo ma Babyn Haulat kaya tunda tana hanya tace to, gaba d’aya jallabiya suka sa sukai rolling veil d’in kowacce ta rataya yar side bag lokacin da suka fito Amadu na ganinsu yace ma Fatuu yo har ta warke tana d’an murmushi tace mashi eh da sauki bata son ta kwanta ne ciwon ya rufeta zasu je su dawo ya tambayeta ina zasu tace bakinta ba dad’i shawarma zasu siyo yana murmushi yace “to ta Romeo a had’o dani” tura mashi baki tay taja hannun Fauzy dake murmushi suka tafi, shagon Zee suka fara zuwa sosae tay farincikin zuwan su ta kar6e su hannu bibbiyu suka gaida ta bayan sun zauna tay masu ya karatu daga baya suka fad’i mata abunda suke so cike da zolaya tace ma Fatuu ko tayi aure har zata Haifa masu baby bata sani ba ta d’an waro ido tana dariya tace “ai in nayi Aunty zee zaki sani don zan fad’a maki” jinjina kai tay tace “hakane nima ina wasa ne ai in sha Allahu tuwo na mai na za’ai kinga mune k’irjin biki kenan” yanayin fuskar Fatun ne ya sauya still da d’an guntun murmushi ta d’an sunkuyar da kai anan Zee ke mata zancen rashin lafiyar Senator tace su Jidderh ne suka fad’a mata Fatuu da ta d’ago tace mata eh yana Germany aka ce tace eh haka aka fad’i mata Addu’ar Allah ya bashi lpy tayi duk suka amsa da Amin ta mik’e tace su shiga sai su za6i kayan da suke so, bayan sun shigan kaya sosae suka siya tarkacen kayan jarirai harda su mayukan su sannan ta siya ma Haulat itama atampa mai kyau da harda lace ma taso ta siya mata to bata da isassun kud’i gashi tasa ma ranta bazata ta6a wanda Haisam ya turo ba, saida suka baro shagon sannan suka biya wani Cafe suka sayi shawarmar harda ice cream da youghort kafin suka wuce gida, da daddare bayan gwaggo ta dawo ta gama kintsawa suka kai mata kayan don ta gani sosae ta yaba kyawun su tana fad’in su Fatuu fa anyi D’iya dole a gwangwaje ta duk suka yi dariya har suka baro d’akin ba wanda yay zancen ciwon Fatuu don ta gyagije baka cewa ma itace tay amai d’azun, a ranar sai wurin goma ta wuce su Haulat suka iso ita da wasu yan uwansu lokacin data kira Fatuu ta sanar mata ta iso sha d’aya tayi cike da zumud’i Fatuu tace in Allah ya kaimu tana nan zuwa a shafa mata kan Baby ace Mamanta na mata sannu da zuwa Haulat na dariya ta amsa da to Maman Baby, Washe suna gama gyara gidan suka shirya don tafiya gidan su Haulat da yake gwaggo bazata je aiki ba ita zatayi Abincin rana ta basu sak’on suyi ma Haulat barka da zuwa sai ta shigo anjima suka amsa da to suka tafi, Lokacin da suka shiga gidan a tsakar guda suka iske innarsu da fara’a tay masu sannu da zuwa duk suka gaidata ta amsa tana fad’in “Fatima yan Makaranta karatu ya 6oye mana ke” d’an murmushi kawai Fatun tay tace Allah ya bada sa’a suka amsa da Amin kafin sukai mata barka d’an murmushi tay tace ai ita za’a ma barka su shiga Haulat d’in na cikin d’akinta suka amsa da to had’i da nufar d’akin, da sallama Fatuu ta shiga idonta suka sauka akan Haulat dake zaune saman gado tayi wanka tana sanye da riga da zani na atampa tana rungume da babyn itama an yi mata wanka an shiryata tana Feeding d’inta d’akin sai k’amshin jego yake suna had’a ido suka sakar ma juna murmushi Fatuu ta nufe da sauri ta d’an yi mata side hug tana fad’in “Allah sarki Aminiyata nayi missing d’inki over wllh” dariya Haulat tay tana fad’in itama haka Fatuu ta zauna gefen gadon Haulat ta kalli Fauzy dake tsaye tana murmushi tace mata ga wuri ta zauna mana ta nufi wurin daga gefen Fatuu ta zauna, k’ura ma Babyn ido Fatuu tay yadda take ta shan nono abunta ta bud’e ido mamaki kawae Fatuu ke yi wai Haulat ce da D’iya Haulat dake ta kallon Fatuu ganin yadda take kallon babyn yasa tace “halan mamaki kike?” Da sauri ta kalli Haulat tace “wllh abun ba wuya da anyi aure sai kiga an haihu” Haulat dake dariya tace “Uhm dama ai yanzu haka zaki gani sai zaki haifa ma Ya Haisam tukunna zaki gane inda wuyar ko babu” d’an 6ata fuska tay had’i da ta6e baki Haulat d’in tace “ko an daina yayin shi ne anyi new catch?” Kafin tace wani abu Fauzy dake murmushi tace “yana nan daram a cikin zuciyar don ta shi ce ba sauran space da wani zai samu” Haulat dake kallonta tana yar dariya tace “Fauzy bamu gaisa bama ya karatu?” tace “Alhamdulillah barka mun samu karuwa Allah ya raya mana ya Albarka ci rayuwar ta” Haulat ta amsa da Amin da sauri Fatuu ta kai hannu ta d’an bugi gefen hannunta tace ba’a amsawa fa rashin kunya ne dariya kawae Haulat ke yi Fauzy tace “barta ta amsa abunta wllh ita tasan kwakwar da ta ci kafin ta same ta sai kuma ayi Addu’a tak’i amsawa, ko ni da zan yi aure in haihu duk wanda yay ma babyn Addu’a sai na amsa” Haulat dake dariya tace “ai zaki yin in sha Allah da lokaci yayi” d’an girgiza kai tay tace ta yafe ba sai tayi ba Haulat dae murmushi kawae take don tasan labarinta tun bayan da suka had’u da Fatuu ta bata labarin ta can Fatuu ta kai hannu tace ita dae gaskiya ta gaji da jira duk ta k’osa ta d’auketa Haulat ta mik’o mata ita ta kai hannu ta amshi babyn, Fatuu na murmushi take kallon yarinyar Tubarkallah kyakkyawa da ita gata fara hasken babanta ta d’aukko don yafi Haulat d’in haske amman fuskarta tana kama da Haulat sosae, kallon Haulat tay ta tambayi sunanta tace Umma Salma Fatuu ta d’an 6ata fuska tace maimakon a saka mata sunanta duk suka yi dariya Haulat ta kalli Fauzy tace “Fauzy ya fama da k’awar nan ta ki” tana dariya tace “ai ke kika sha fama ni yanzu da Sauk’i ta girma tayi hankali” juyawa Fatuu tay ta d’an harareta tace da bata da hankali kafin Fauzy ta bata amsa Haulat tace da Sauk’i dai hankalin nan gaba d’aya suka kwashe da dariya, hira suka cigaba da yi Haulat nata ba Fauzy labarin kuruciyar Fatuu tana ta tik’ar dariya suna haka har Azahar tayi suka tashi sukae salla bayan sun gama ne k’anwar Haulat ta kawo masu abinci a cikin yar babbar kula ta koma ta kawo plates da ruwa daga baya ta kawo ma Haulat nata ganin sun k’i fara ci tay masu magana tace ma Fauzy don Allah taci itace bak’uwa tana murmushi tace itama ai yanzu ta zama yar gida Haulat tace hakane, hannu ta kai ta bud’e warmer d’in dafa dukan shinkafa da taliya ne a ciki ta fara zubawa a cikin plate bayan ta gama ta rufe ta kalli Fatuu tace suci kowa ta d’auki spoon suka fara ci, d’an kad’an Fatuu taci jin zuciyarta ta fara tashi yasa ta aje spoon d’in Fauzy dake kallonta tace har ta k’oshi ta d’aga mata kai alamar eh, sai bayan da suka gama suka ba Haulat kayan da suka kawo mata sosae tay farin ciki ta hau yin godiya har da k’wala ma innar su kira ta shigo itama ta ga kayan tay godiya sosae tana fad’in lalle Mama Fatima ta fito da d’iyarta wannan kaya haka k’arshe tay Addu’ar Allah yasa suma su ga yaran su kowa ta sunnar da kai suna d’an murmushi Haulat na fad’in su Fatuu ashe yanzu an san kunya innarsu dake dariya tace ai daman can da kunyarta daga baya ta fita, har akai la’asar suna gidan bayan an gama salla gwaggo tazo itama harda kayan ta kawo masu sosae suka ji dad’i sai bayan Magrib sukai masu sallama Haulat na tambayar Fatun yanzu Makarantar zata koma tace eh amman zata dawo cikin satin ta k’ara ganin Baby tace to Allah ya bada sa’a suka amsa da Amin kafin su tafi aka basu naman suna mai uban yawa har gwaggo na fad’in kar su kwashe ma mai jego fa innar su tace a’a bakomae godiya sukai suka tafi.
Washe gari da safe sukai shirin tafiya bayan sun gama yin breakfast suka je d’akin gwaggo sukai mata sallama tay ma Fauzy godiyar ziyara harda kud’i ta basu ta rako su har bakin zaure Kawu Amadu ma ya fito sukai sallama, Lokacin da suka isa Class kawae suka wuce don duk suna tare da jakunkunan su da akayi break suka fita, tun bayan da suka dawo zuciyar Fatuu ta fara tashi ga wani ciwon kai daya far mata lokaci guda daurewa kawai take bayan da malamin su ya shigo yana cikin yi masu bayani yau ma kamar rannan amai ya taso mata ta fita da gudu Fauzy ta d’auki excuse ta bi bayanta, saida ta gama ta kamata suka je bakin famfo ta wanke fuskarta da bakinta bayan ta gama Fauzy dake kallonta cike da damuwa tace gaskiya suje taga likita ciwon ya fara yin yawa Fatun ta d’aga mata kai don itama abun ya fara damunta class Fauzy ta koma ta fad’i ma malamin zata kaita taga likita ya bata izini ta d’aukar masu jakun kunan su, lokacin da suka isa Opd office d’in wani Doctor Madugu suka nufa don sun san shi son Fatuu yake ita kuma tak’i saurarar shi ba kamar da yake tasan halin shi ya cika son mata, saida suka jira patient d’in dake ciki ta fito sannan suka shiga yana ganin su ya sakar masu murmushi suka zauna a kan kujerun gaban table d’in shi yabi Fatuu da wani kallo yana sakin k’ayataccen murmushi ta d’an d’aure fuska Fauzy ce ta fara gaishe dashi sannan Fatun kaman an mata dole yace ba zai amsa ba in bazata saki face en ta ba k’ara tamke fuskar tay Fauzy ce tace mashi bata lafiya ne d’age gira yay ya tambayi abunda ke damunta har Fauzy zata bashi amsa yace ita yake son yaji daga bakinta d’an shiru fatun tay kafin ta fara mashi bayanin abunda ke damunta bayan ta gama yana d’an murmushi yace “kinga da mun yi aure sai in yi tunanin ko mun samu rabo ne” a d’an harzuk’e ta kalle shi bata dae ce komai ba ya fara rubutu a Computer d’in gabanshi can ya d’ago yace suje lab ya tura test ayi mata suka mik’e yabi bayanta da kallo har suka fice, suna zuwa lab d’in ba 6ata lokaci akai mata awon don sun san masu yi awon Malaria da typhoid ne aka mata bayan an tura ma likitan suka koma Opd d’in lokacin daya duba result d’in akwae malaria d’in amman ba typhoid ya fad’i masu kafin ya tura masu magunguna yace suje pharmacy bayan sun mik’e ya kira Fauzy ya bata kud’i yace su biya tay mashi godiya suka tafi, bayan sun amshi magungunan suka tafi ganin an kusa tashi Fauzy tace su wuce hostel kawae sai ta sha magungunan ta d’aga mata kai, bayan ta fara shan magungunan sosae ta samu sauk’i ta daina yin aman saidae bata da appetite ba komae take iya ci ba tafi shan youghort sai kuma lemu Fanta sai abu mai d’an tsami ko yaji a haka har Friday tayi suka tafi weekend, lokacin data koma gidan gwaggo bata nan bata dawo ba sai dare Fatun ta fito tsakar gida ta tareta tay mata sannu da zuwa tana niyyar zuwa kitchen don ta kawo mata Abinci tace mata ta barshi in tayi wanka zata ci ta ce to ta koma d’aki, washe gari bayan ta gama gyara gidan tay wanka ta shirya cikin doguwar rigar material tay rolling veil d’in ta shiga d’akin gwaggo lokacin tana kishingid’e saman gado amman ba bacci take ba a bakin gadon Fatuu ta zauna suna kallon juna da gwaggon da ta d’ago kanta tana kallon Fatun sosae tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa tace mata zatace gidan su Haulat shiru gwaggon tayi tana ta kallonta saida Fatun ta maimaita mata sannan ta d’aga mata kai alamar to har ta mik’e ta nufi kopa tana fad’in sai ta dawo taji gwaggon ta kirata ta dakata ta juya da kai tay mata alamar ta zo ta koma ta tsaya daga d’an gabanta tace gata gwaggon ta yunk’ura ta tashi zaune sosae tana kallonta tace “wani abu na damun ki ne??” Cikin rashin fahimta Fatuu ta tambayeta wani abu tace tana nufin bata lafiya ne d’an murmushi Fatuu tay tace “Eh ciwo nayi har ma naje naga likita ya tura ni aka man test aka ga malaria ce ke damuna sosae ya rubuta man magunguna yanzu haka cikin shan su nike amman na samu sauk’i ai sosae” shiru gwaggo tay kafin tace mata basu saka net ne in zasu wanta tace suna sawa wllh kawae ciwon ya kamata ne kuma kafin su shiga net d’in saurayen na cizon su ko in sun fita class da daddare,jinjina kai gwaggon tay tace taje Allah ya sawak’e amman dole su k’ara kulawa tace to ta tafi, tunda tazo gidan wani ikon Allah lafiya lou take cin Abinci washe gari lahadi harda cin cin tayi masu ranar Monday da safe ta tafi.
tun bayan da ta koma sai ciwon ya k’ara dawowa sosae ga yawan amai da take yi kusan kullum sai tayi amai a class wani lokaci in Malam na ciki ko kuma da break haka a Hostel ma in ya taso mata ta window take zura kanta tai tayi ga magani tana ta sha amman abun yak’i lafawa har fuskarta ta d’an rame tayi wani fayau da ita ranar laraba Fauzy tace mata kodae ta rakata gida amman sai tace tunda har anzo ranar ta bari Friday ta je tace to kodae ta saka mata drip ko taji k’arfin jikinta Fatun tace eh, da kanta ta fita taje ta siyo drip d’in bayan ta dawo ta saka mata shi lokacin daya k’are sosae ta samu k’arfin jikinta washe gari Alhamis taje class lpy lou har aka tashi, da yamma Fauzy taje siyo abu a shop bayan ta dawo ta nufo Hostel hannunta ruk’e da leda taji ana k’wala mata kira ta bayanta ta tsaya da ta juya sai taga wata yar class d’in su ce mai suna Zainab Muhammadu wadda ake ce ma suda (sarkin labari) tana ta sauri ta k’araso ta tsaya gaban Fauzy tace “dama tambayar ki nike son yi ya jikin Fatima Ard’o?” Wani kallo Fauzy tay mata tace bata ganta bane yau a class da sauri tace ta ganta taga ma duk ta rame Fauzy tace eh ai ciwo take ko daga haka ta fara kokarin wucewa Zainab d’in tace “wai kinsan abunda ake fad’a kuwa game da ciwon da take?” Cakk Fauzy ta tsaya tana kallonta tace mi ake fad’an yar in ina ta fara tace “j….ji nayi ana cewa wai kamar ciki ne da ita don ciwon da take yayi kama da laulayin ciki” rassss gaban Fauzy ya fad’i ta zaro ido waje gaba d’aya hannunta guda dafe da bakinta can ta cire cikin bacin rai tace “uban wa yace ciki gareta dama mara aure na samun ciki ne ko kuwa ana sha a ruwa ne ban sani ba???” Yarfa hannu Zainab d’in tay tace “nima fa bani nace ba abunda aketa fad’a ne nagaya maki don ku sani” daga haka ta wuce tay tafiyarta Fauzy tabi bayanta da kallo fuska a matuk’ar d’aure can ta wuce fuuu itama ta shige cikin hostel d’in idonta har rufewa yake Saboda tsabar bacin rai da bibbiyu ta rink’a hawa staircases d’in ta nufi d’akin su, lokacin data shiga Fatuu na kwance saman gado tana jiranta ta kawo mata Fanta gado ta nufa ta aje ledar hannunta gefe ta zauna fuska a d’aure ta kumbura baki ganin yanayinta yasa Fatuu yunk’urawa ta tashi zaune ta fara tambayarta lafiya bin ta da ido kawae tay kaman bazata tanka ba can cikin bacin rai tace “wllh magulmaci bai ji dad’i ba yaji haushin asara!!” A d’an rud’e Fatuu ta hau cewa ta fad’i mata gulamar mi akayi don Allah tace “wai shikenan mutum bazai yi ciwon Allah da Annabi ba sai an ja mashi sharri yanzun nan da zan shigo wai Zainab Muhammadu ta tsaida ni take fad’a man maganar da ake tayi game da ciwon ki..” a rud’e Fatuu tace mi ciwon nata yayi kaman bazata fad’i mata ba ganin yadda take mata Magiya yasa tace “ke wai ciwon da kike wai kaman ciki gare ki don ciwon yayi kama da laulayi Kiji jan sharri don Allah kawae don aja maki, ta ina zaki samu ciki tunda ba aure gare ki ba!!” Zaro ido waje Fatuu tay tasa hannu guda ta dafe kirjinta a kidi’me ta maimaita “ciki kuma!” Wani uban tsoki Fauzy taja jikin Fatuu har ya fara rawa kaman zata yi kuka tace “ni a ina zan samu ciki bacin kowa yasan ba aure gare ni ba!” Wani tsokin Fauzy taja tace “dalla rabu dasu magulmantan banza kawae an fad’a ne tunda kika ji Zainab Muhammadu ta fad’a don in dae tace abu to tabbas an yi ne ki k’yale su ta Allah ba tasu ba duk mai neman ki da sharri saidae ya koma mashi wllh” tana k’arasa Maganar ta fiddo mata Fanta d’in ta mik’a mata hannun Fatuu sai rawa yake ta amsa sai ta aje ta a gefenta kawae tsananin tsoro da fargaba ne suka kamata jin abunda zuciyarta ke ayyana mata na kada ace daga abunda Ya Haisam yayi mata ta samu ciki sosae kirjinta ke bugawa tunanin yaushe yakamata tayi period ta shiga yi a lissafin ta gobe Juma’a wata guda kenan da abun ya faru kuma tayi wanka da kwana d’aya hakan ta faru kenan yanzu kusan kwananta talatin da yin wanccan tasan kuma bayan kwana ishirin da d’aya wato sati ukku koda biyu take yin sabon period yanzu kenan lokacin ya wuce kuma ko alamun zata yi bata fara ji ba wani abu ta had’iya Kutt lokaci guda zufa ta fara tsattsafo mata ta koma tamkar an dasa ta a wurin ko kwakkwaran motsi ta kasa yi kallonta Fauzy tay ganin halin da take ciki da alama ta rude yasa tace mata wllh kada ta sake ta wani damu da zancen munafurcin su tunda ita dae ai tasan ba shi gare ta ba ko, zuru da ido kawae tay ma Fauzy k’arshe Fanta d’in ma kasa sha tay don ko kallonta ma bata k’ara yi ba Fauzy ta hau lallashin ta tana don Allah ta d’auka tasha kada ta tada hankalin ta a banza ita data san haka zata shiga damuwa da bata fad’a mata bama, a wannan daren yadda Fatuu taga rana haka ta ganshi sam bacci ya k’aurace ma idanunta sai juyi take tana zullumin kada ace da gaske ciki ne da ita don duk alamu sun nuna kaman laulayi take yin da gaske yin wannan tunanin har saida tasa hannu ta rufe bakinta, akan kunnanta aka kira sallar Asuba da k’yar ta iya yin salla tana gamawa ko Addu’a kasa yi tay ta koma gado ta kudundune lokacin da gari ya waye Fauzy ta d’an bubbuga ta tace ta tashi ta shirya kada su makara tana a kudundunen tace mata ta shirya ta tafi ita bazata je ba jin hakan yasa Fauzy zama a gefen gadon da take tace “kamar ya bazaki class ba kuma, ko don Maganar jiya to ke miye abun wai damuwa har haka ne tunda kin san kina da gaskiya ki tashi kawae ki shirya mu tafi in mutum ya isa ya tunkare mu yayi mana Maganar mu mana” duk yadda tayi da ita ta kafe kan bazata je class ba har ran Fauzyn ya 6aci tace “to ko dae Zarah da gaske cikin ne da ke???” shiru Fatun tay bata bud’e fuskarta ba kirjinta na wani irin bugu can Fauzy ta kai hannu ta yakice bargon data lullu6a Fatun ta kalleta da sauri suka zuba ma juna ido baiwar Allah duk ta firgice sai numfashi take da k’arfi wani irin kallon tuhuma Fauzy ta fara yi mata ganin haka yasa Fatun sunkuyar da kai cikin d’aurewar kai Fauzy tace “Zarah na tambaye ki baki ban amsa ba ki fad’a man gaskiya ko dae Maganar da ake gaskiya ce??” Girgiza kai ta fara yi da k’yar ta d’ago ta kalleta idanunta sun ciko da Kwalla tace “Fauzy ya zaki fad’i hakan kema bacin kin fi kowa sanin wacece ni kuma kin san ba aure ke gare ni ba” sauke Ajiyar zuciya tay tace “to don mi zaki k’i zuwa class??” Cikin rawar murya tace “h…. hakanan kawae, hankali na ya tashi sosae da jin Maganar ban so inje class haka su k’ara tabbatar da Maganar su gara in tafi gida kawae in fad’i ma gwaggo halin ciwon da nike ciki a nema man maganin hausa” da k’yar ta kai Maganar, shiru Fauzy tay tana nazarin Maganar can tace mata shikenan ta fahimta amman ta bari a tashi sai ta rakata gidan tace mata to kawai, saida ta matsa mata sosae sannan ta d’an sha ruwan tea da yar wainar kwae, tun bayan da Fauzy ta shirya ta tafi class take ta faman kai da kawowa a cikin d’akin gaba d’aya ta gama firgicewa kanta ko kallabi babu ta rasa tunanin da zata yi tsoron ta ace da gaske tana da ciki duk in tayi wannan tunanin sai yan hanjinta sun juya can wata Zuciyar ta raya mata taje ta siyo Pt strip ta auna in shine tun wuri ta d’auki matakin daya dace, yin wannan tunanin yasa da sauri ta nufi kayan su ta d’auki hijab ta bud’e jakarta ta d’auki kud’i har zata fita tay tunanin ta saka nikab d’in Fauzy ta tafi dashi ta juya ta d’aukko shi ko sakawa daidai bata yi ba a haka ta tafi…….
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.