Hausa novels

Halysaah Page 110 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 110 Da asuba Ajay ya shiga Bedroom dinsa zai dau darduma ya kunna wutan dakin mara haske sosai ya juya yana kallonta, ya kusa seconds talatin tsaye yana kallonta, can dai ya karasa har kusa da ita ya duka to be sure of what he is seeing, ya kara kunna wutan bedside lamp still looking at her, da mamaki ya kai hannu yayi raising gashinta yana feeling texture din, can ya cire hulan kanta da kadan ya rage ya fita daga kan nata yana kallon gashin gaba dayansa, lokaci daya Khaleesat ta bude ido jin hannu a gashinta tayi wani ƙara tana kokarin mikewa zaunewa tana kallonsa a tsorace tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Sai kuma ta dafe kirjinta ta jingina da gado feeling so much relieve ganin shi ne, tayi saurin daukar hulanta ta saka, da mamaki yace “Ke?? ƙarin gashi ne wannan kika yi? Are you okay??” Ta wani kallesa sai kuma ta koma ta kwanta kan pillow taki cewa komai, ya hade rai yace “Ba magana nake maki ba? A gidan nan zaki yi ƙarin gashi ko baki da hankali ne? Take that off immediately” On a serious note ya kare maganar fuskarsa daure, ta daga idanuwanta ta kallesa bata dai ce komai ba, ya ɗaka mata tsawa yace “Am i making any sense?” Mikewa zaune tayi tace “Naji” Daga haka ta sauka daga saman gadon ta nufi bandakin dake dakin, ya bi ta da kallon mamaki don da gaske yayi zaton saka gashin tayi kuma har ya zargi Safiyyah ce ta bata gashin ta saka, ya dau pray mat dinsa ya fice daga dakin…. Karfe tara saura Ajay ya shiga Bedroom dinsa cause he was expecting her to come out of the room and go to her room tun da asuba amma yaga bata fito ba, bacci ya sameta tana yi comfortably ta nannade cikin Farin duvet dinsa ba ma ta da alamar tashi anytime soon, ya hade rai yace “Kee” A hankali ta bude ido ta kallesa da sleepy eyes, yace “Garin ki bai waye bane har yanxu? Zo ki fitar min a daki malama” Miƙa tayi tana kallon agogon dake dakin, sai kuma ta mike zaune tana sosa kanta, ya bude mata kofar dakin yana nuna mata hanyar fita yace “Come and get out” turo baki tayi ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta gefensa ta bi ta fita daga dakin ya bi ta da kallo, sai bayan da ta fito zuwa parlonsa jikinta yayi sanyi tuno incident din jiya da daddare, kasa ci gaba da tafiya tayi ta juya a hankali ta kallesa taga kallonta yake, ta marairaice tace “Ni fa dakin tsoro yake bani yanxu ban san me yasa ba” Ya mata wani kallo yace “Kina saka gashin kanti ya baza ki dinga mafarki kina yi ma mutane ihu cikin dare ba, c’mon go to ur room my frnd, what do you mean? Ni zaki yi inconveniencing a nan” Juyawa tayi ta nufi kofar fita part din jiki a sanyaye, cikin rashin kuzari ta dinga tafiya gabanta na faduwa, tana isa corridor ta tsaya tana tunanin abun yi, gaba daya ta gama tsorata da Walid da lamarinsa ga kuma wukar da ya nuna mata wai zai kasheta, after a minute sai ga Ajay ya fito, tana jin Footsteps dinsa ta ci gaba da tafiya tana wasa da fingers dinta shi dai yana biye da ita a baya, dai dai nan sai ga Walid ya fito daga dakinsa rike da akwatinsa karami yana sanye da kananun kaya sai baza kamshi yake, sau daya ya kallesu ya dauke kai ba tare da ya kalli Ajay ba yace “I am leaving for England, na gama abinda zan yi a Maryland” Ajay yace “Safe trip” Walid ya daga kai ya kalli Khaleesat da tayi saurin sauke idonta gabanta na mugun faduwa har sannan tana wasa da hijab dinta, Gaisheta yayi yace “Ina kwana Aunty” cike da karfin hali ta mayar masa da gaisuwan tace “Ina kwana” yace “Toh sai wani lokaci kuma, ni na tafi….” Khaleesat ta gyada kai kamar kadangariya tace “Allah ya kiyaye hanya” Yace “Ameen” Daga haka ya sauka downstairs, wani boyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta nufi kofar dakin da take ciki ta bude ta shiga tana kallon Ajay da ya bi ta da kallo, kulle kofar dakin tayi. That same day da yamma Ajay na zaune parlor yana waya da Hajiya Shafa’atu wanda ba don komai ta kirasa ba sai don Khaleesat don babu wani bond na communication tsakaninsa da ita tunda yawanci a Turai take zama da Mai gidanta da yaranta kuma tana jimawa bata shigo Nigeria ba, mikewa yayi ya nufi kitchen yace “Tana kitchen bari in Kai mata wayar” Yana shiga kitchen din Khaleesat dake yanka Salad ta juya ta kallesa, ya karasa kusa da ita ya yagi babban tissue dake kitchen din ya daure fuska ya mika mata alamar ta goge hannunta bazata taɓa wayarsa haka ba, taɓe baki tayi ta amshi tissue din ta goge hannunta sannan ya mika mata wayar, yana tsaye har suka gama gaisawa da Hajiya Shafa’atu, duka bai wuce 2 minutes ba sannan ya karbi wayarsa ya fice daga kitchen din, Hajiya Shafa’atu tace “To yaushe za ku shiga England din naji satin nan da za a shiga ne convocation din ko? ni dai ba lallai ma in je ba don ina da wani babban uxuri, but idan na samu sarari sai in iya zuwan” Ajay yace “In sha Allah ranan zan je ni” Hajiya Shafa’atu tace “Kai kadai zaka je?” Yace “Eh in sha Allah” Hajiya Shafa’atu tace “Jiddan bata da Visa halan? Ai da kayi mata all this long while da aka dauka da komawar ku Amurka” Ajay yace “An mata ai” Hajiya Shafa’atu tace “To shi ne zaka je kai kadai kuma? A’a hakan bai yi ba Yarima, Ai yana da kyau ka kai ta duk ta hadu da yan uwanka su santa ta san su don nasan za su je ko ba duka ba, kuma ba kowa yasan ta ba kaga wannan wata dama ne da za tasan dangin ka, going without her isn’t an option” Ajay dai yayi shiru, but to bring an end to the conversation sai kawai yace “To in sha Allah Mama, za mu je tare” ya fadi hakan ne ba don zai je da ita din ba don babu wannan niyyar tare da shi, a haka suka yi sallama da Hajiya Shafa’atu ya ajiye wayarsa, banda ma rashin zuwansa zai zama wani issue din shi me ma zai je yi wajen convocation din Hadiyah……Karfe goma saura na dare Khaleesat ta gama karatun da take don ta gaji da karatun, ta kashe laptop dinta tayi plugging dinsa sannan ta dau wayarta don dubawa ko Umma tayi mata reply din message din da tayi mata tun da rana amma taga bata ma hau WhatsApp din ba, Sophie tayi ma reply din maganar da tayi mata few hours ago, sai kuma taga Ajay yayi updating status tun daxu, once a while yake uploading status or may be ita ce bata lura da ko yayi status din ko bai yi ba, ta bude status din nasa taga hoton Inteesar ne yana wishing dinta happy birthday, tayi ta kallon hoton da kamar ta masa reply tace ya tura mata numberta kawai dai ta fasa, sai kuma taga status din Jay, sai da gabanta ya fadi don it’s been a while bata ga status dinsa ba, ta bude status din tana kallon IV da yasa na Convocation din Hadiyah that is taking place in Oxfordshire England on Tuesday, caption dinsa ne yasa taji hawaye ya kawo idonta and she wished bata ma bude status din ba, ajiye wayar tayi ta kashe wutan dakin ta kwanta tana jin hawaye me zafi na zuba idonta. Wajen 12 na dare Ajay ya gama abinda yake yi a laptop dinsa ya kashe wutan parlon ya wuce sama, har ya nufi part dinsa sai kuma ya dawo ya bude kofar dakin da Khaleesat take, Flash din wayarsa ya kunna yana haska ta, bacci take amma bata rufe har fuskarta da bargo ba kamar yanda ta saba yi, ya karasa kusa da ita har sannan yana haska ta da fitilar wayarsa ya kai hannu ya cire hulan kanta, gashin da yace ta cire ya gani still a kanta, ta kurma wani ihu a mugun tsorace jin hannu a kanta, ta fara kokarin tashi zata bar wajen jikinta na rawa kuma bata fasa ihun da take ba tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Yayi saurin rikota yace “Ke, meye haka?” hannunsa ta riko bayan da taji muryarsa ta fashe da kuka sosai har lkcn jikinta na rawa tana cewa “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Gaba daya ta gigice har zufa ya keto mata a goshi, yayi saurin zaunawa kusa da ita bayan ya ajiye wayarsa ya kunna fitilar gefen gado yana kallonta yace “Are you alright?” Kalle kallen dakin ta ke yi har sannan tsoro ne kwance karara a fuskarta ga wani heaving da kirjinta yake ta matsa kusa da shi, shi dai kallonta kawai yake, har sai da ta yi calm down after almost 2 minutes, and everywhere was very silent, a hankali ta daga kai tana kallonsa kamar zata fara sabon kuka tace “Me yasa zaka bani tsoro? What are you looking for?” Ya hade rai yace “What did I tell you about the hair?” Ta marairaice tace “Which hair? Ni fa gashi na ne” Ya mata wani kallo yace “Do i look like i am joking with you?” Bai jira me zata ce ba ya kai hannu kan gashin yana taɓa soft scalp dinta, kauda kanta tayi da sauri tana komawa baya daga kusa da shi ta hade rai tana masa wani kallo tace “Meye haka? Saboda zan yi karyan gashina?” She could see the startle in his eyes yana kallon gashin, sai kuma ya sauke idonsa bai sake cewa komai ba kawai ya mike ya dau wayarsa ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, ta tura baki ta dau hularta ta mayar sannan ta kashe wutan bedside lamp da ya kunna har sannan tana jin kirjinta bai dawo dai dai ba. Washegari Lahadi Khaleesat ta gama duk abinda zata yi ta shirya, tun karfe takwas ta tura ma driver din da ke kai ta school text message tace masa karfe sha daya zata fita, tana rike da handbag dinta ta sauko downstairs tana ma Ajay kallon gefen ido, yayi ending call din da yake ya juya ya kalleta babu yabo babu fallasa yace “Ina zaki?” Ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da tafiyarta zuwa kofar fita daga parlon tace “School” Ya mata wani kallo yace “School on a Sunday? Are you sick in the head?” Ta hade rai ta tsaya sannan ta juya ta kallesa tace “Reading material dina da na manta ranan Friday zan dauko sbda gobe muna da Course din and I need to study before the lectures” Ajay ya mike yace “Mu je school din since you are a liar” Wani kallo ta dinga masa don gidansu Safiyyah take son zuwa, ya hade rai yace “Baki ji me nace bane?” A takaice tace “Bazan je ba kuma, na fasa” Tana fadin haka ta juya zata koma sama ya mata wani tsawa yace “Keee na fara wasa da ke ne? Zo ki fita kafin ki sha mari” Tsayawa tayi sai kuma ta juyo, kamar zata fashe da kuka ta nufi kofa ta fice daga parlon ya bi bayanta, makullin motar ya amsa hannun driver dake jiranta, fuskarta a daure ta shiga motar, har suka bar gidan bata kalli direction dinsa ba, bayan sun isa school yayi parking yace “Go and get the material ki dawo” Rungume hannunta tayi without looking at him taki cewa komai, Yace “Are you daft?” A takaice tace “Ba wani material, kuma ni ba school zan zo ba gidansu Sophie zan je za mu yi karatu tare a can” Kallonta ya dinga yi, ita kuwa taki kallonsa, kamar zata yi kuka tace “Bayan kace kar ta zo inda nake ni kuma sai ka dinga hanani zuwa wajenta bayan tare mu ke karatun mu during the weekends” Kuka ta fara yi ta rufe fuskarta da gyalen jikinta, shi dai har sannan Kallonta yake, can ya tada motarsa duk tunaninta zai yi considering kukanta ya kai ta gidansu su Safiyyah amma taga ya dau hanyar gida direct, wani mugun haushinsa ne ya cika ranta tuni ta dena kukan da take ta daure fuska, har suka isa gida yayi parking bai kalleta ba, ta bude motar ta fice daga cikin motar ta nufi cikin gidan kamar zata tashi sama, har dare bata sauko downstairs ba ranan balle ta nemi abinda zata ci, shi ma ya kyaleta tunda ba cikinsa bane yayi ma Driver order din abinci, shi kuma ya hada salad for himself for dinner.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* ur evidence via 07087865788

Back to top button