Halysaah Page 107 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 107Washegari har karfe sha biyu da kusan rabi Khaleesat na daki bata fita ba, tun da gari ya waye leg cramps yasa taki sauka daga saman gado banda wanka kawai da ta daure taje tayi ta canza kayan jikinta, ta dade bata yi irin ciwon kafar ba idan tana period sannan ya hade mata da lower back pain, tana ta kwance tana jiran zuwan Safiyyah don tun da sassafe ta kirata don yi mata korafin jiya tayi tafiyarta tana bacci babu ko sallama, shine Safiyyah tace mata anjima zata shigo da rana, kofar dakin aka bude tayi saurin juyawa tayi backing kofar ta rufe ido don tun bai shigo dakin ba tasan shi ne saboda kamshin turarensa, ya zaga har inda take facing yace “Get up and leave this room Malama….” At first tayi niyyar yin kmr bacci take but jin intonation da yayi using yayi maganar alamar he is not joking ta bude ido a hankali tana kallonsa, sosai ya hade rai yace “Ko baki ji na ne? You think i will tolerate you stressing my life in this House? Ni kike nufin zan kawo maki breakfast daki ko kuma kin zo da cook or any worker from Nigeria ne da zai dinga girki yana kawo maki daki? Or are you a baby?? Who do you think you are here to stress with ur problem?” Ƙin cewa komai tayi, a fusace yace “Am i making any sense?” Dauke kai tayi ta tura baki tace “I am not feeling fine” Ya mata wani kallo yace “What is making you not to feel fine?” Shiru tayi taki cewa komai, yayi mata tsawa yace “Kee” Kamar zata yi kuka tace “To wai ba cramps bane, I am having leg cramps” Tana fadin haka hawaye ya cika idonta, yace “And who did you tell that? Baki da phone number dina ne? Since you are a type of person that is always problematic from this problem to that problem, anytime any of ur so called problem arise don’t you have my number?” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya juya ya nufi bathroom din dake dakin wishing dama Yakumbo tana da Visa available da jirgi kawai zai biya mata ta taho ko zai samu rest of mind daga issues din yarinyar nan don bazai iya ba, gefe kawai zai koma ya zuba masu ido yana kallo a gidan, after a while ya fito daga bandakin yana kallonta yace “Ko tasowar ma baza ki iya ba zuwa bandaki?” Ta juya ta kallesa, ganin his face is very serious ta mike zaune ta sauko da ƙafafuwanta daga saman gadon a hankali, daurewa tayi zata tashi amma ta kasa mikewa tsaye, ya nufi inda take zaune ya hade rai ya mika mata hannu, dauke kai tayi giving him her hand ta daure ta mike tsaye with his help, daga nan kuma ta zame hannunta ta fara tafiya a hankali tana rike waist dinta zuwa bandakin, ruwa me zafi ba sosai ba ya cika mata a bath tub for Hot bath, suna hada ido bayan ta shiga bandakin ta kulle kofar, she felt so much relieve after the hot bath, after almost 40 minutes ta fito daga bandakin bayan ta maida kayan jikinta don kar ma ta fito daure da towel ta gansa a dakin, bata gansa dakin ba sai tray din abinci dake ajiye kan Carpet with some fresh fruits a bowl, wani kayan ta dauko a akwatin ta, bayan ta gama shafe shafenta ta saka kayan ta dau hularta ta saka, abincin da aka ajiye mata ta bude tana dubawa taga ko kadan ba shi da yawa kamar dai yanda turawa ke cin abinci, hakan ma yayi mata don da yana da yawa ma bata san yanda zata yi da shi ba tunda English breakfast ne da bai dameta ba, baked bean da aka yi micro waving sai omelette a gefe with few slices of bread da aka yi toasting and 2 sausage, sai hadin salad madaidaici a wani bowl wanda iya olive oil aka yi drizzling a kai, ta dau pain reliever dake kan tray din da goran ruwa ta ajiye su gefe sannan ta fara hada shayi don har da gwangwanin madara da Milo da cube din sugar ya ajiye mata, sai da tayi breakfast din sannan ta sha maganin, iya apple kawai ta ci a fruits din, after 15 mins ta mike zata fita da tray din don taji saukin cramps din ta samu relieve sosai, tana sauka downstairs ta gansa zaune parlor yana kallon TV at the same time yana operating wayarsa, bai kalli direction dinta ba har ta wucesa zuwa kitchen sannan ya juya ya bi ta da kallo har ta shiga kitchen din, bayan ta gama wanke utensil din da ta kai kitchen ta goge wajen sink din ta fito daga kitchen din dai dai sanda aka bude kofar parlon da sallama suka yi ido hudu da Safiyyah dake leko cikin parlon daga waje kamar mara gaskiya, sai kuma ta shigo parlon don sun hada ido da Ajay, Tana yake hade da sosa keya tace “Good afternoon” Sau daya ya kalleta ya dauke kai yace “Evening” Khaleesat taji dadin ganin frnd din nata ta karasa har inda take tace “Sannu da zuwa Sophie” Hannunta ta kama zuwa sama, ya bi su da kallon gefen ido yana ci gaba da danna wayarsa, suna shiga daki Khaleesat ta kulle tana kallonta tace “Kawai sai ki tafi jiya baki tasheni ba” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Wallahi da ke na kwana a rai Khaleesat, my head still can’t process what you told me yesterday, ganin abun nake kamar Movie fa, dama ana migrating aure?” Khaleesat ta kamo hannunta murya a sanyaye tace “Don Allah kina ganin akwai mafitar da zaki bani akan wannan auren Sophie? Wallahi har cikin raina ni dai bana son auren, ni ban ce ina sonsa ba aka aura min shi, hasali ma ban sani ba don babu wanda ya gaya min sai bayan aure da aka kai ni Bauchi na sani, we can never be compatible with him Safiyyah cause he is not my type and i am not his type too, i wish gidan Abdul ma na koma da wannan auren, i am soo heartbroken….” Tana kuka a hankali ta kare maganar tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta rike haɓa tace “Gidan Abdul? Eh lallai har yanxu baki da hankali kuma bana tunanin zaki yi, wallahi ba don Housemate ba da dai ki koma ma Abdul gwara maki Ajay din ki lallaba kiyi maneji da shi duk da kusan jirgi daya ya kwaso su da Abdul din kawai shi dai nasan bazai jibge ki yanda Abdul ke yi ba, amma duk same categories ne su biyun birds of the same feather, shi wannan ga shegen renin hankali da maida mutum ɗan iska, kina ji fa yanxu nace masa Good afternoon ya mayar min da evening, karfe biyun rana ne evening idan ba walakanci ba? Sau uku kenan yana min wannan iskancin a garin nan ina lissafawa bai sani ba, To wai wani irin al’amari ne wannan ya ja har aka daura aure da shi ne Khaleesat don nasan ba haka nan aka maida auren kansa ba? Bai san cin amanar ɗan uwansa yayi ba accepting auren ki da yayi no matter the circumstance on ground? Ai ana barin halal ko don kunya kuma a yanda yasan Housemate na bala’in son ki bai kamata ya amince da auren ki ba in da zuciya daya yake zaune da shi, gwara ace guduwa ma yayi aka neme sa aka rasa a duniyar da wannan abun kunyan auren budurwar cousin dinsa, yanxu da wani idon daga ke har shi za ku dinga kallon Yaya Jawwad? Wataran in bamu yi hankali ba ma mu ganki da cikin Ajay, Tabɗijam an ci amanar kauna wallahi, jiya da shock din Ajay na kwana a raina, gashi na gansa comfortable as if it’s normal yana kallon ki as his wife, don’t tell me kun ma kwana daki daya da shi, Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un…. Me yasa za ayi ma Housemate dinki haka bayan duk mun san irin azababben son da yake maki kema haka? Kai duk wanda ma ya assasa wannan auren da Ajay bai son ganin Jay ne a doron kasa kawai wallahi shine ya bi ta wannan hanyar don Housemate ya hadiyi zuciya ya mutu kinga ai baza ace shi ya kashe sa ba…” Khaleesat ta fashe da kuka sosai ta tafi gefen gado ta zauna ta kife kanta da Pillow tana rera kuka tana jin zuciyarta na mata zafi, Safiyyah ta zauna kan kujera ta rafka uban tagumi, wato shi yasa take ta yi ma Housemate Allah ya sanya alkhairi yaki kulata ashe ba shi ne mijin ba kaicoo, wani azababben ajiyar zuciya Safiyyah ta sauke tace “To meye amfanin kuka kuma yanxu? Ai it’s too late to cry, cuta dai kam an cuci Housemate, ke ma in er halaq ce ai kamata yayi ki gudu ki shiga duniya ki nuna baki yi na’am da auren ba, ba dole a warwaresa ba in aka ga kin gudu ma’ana baki son auren, wallahi nasan har ke sai Housemate yaji haushin ki ba Ajay ba kadai don gani zai yi kin ma yi accepting auren tunda gashi har kun taho Amurka, and the way I am seeing Ajay he look like someone that is very comfortable with the marriage, ya amshi auren hannu bibbiyu abinsa wato ya samu tsuntsu daga sama gasasshe, dama wa zai kalle ki yaki amsan auren ki, tabbb” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba kuka kawai take sosai, da kyar Safiyyah ta samu ta lallasheta don sai da suka fi minti talatin tana zaune kusa da ita tana lallashinta, daga karshe ta dena kukan cikin rawan murya ta ba Safiyyah labarin duk abinda ya faru da dalilin maida aure kan Ajay, Safiyyah dai haka ta hangame baki tana kallon Khaleesat da mugun mamaki, can ta sauke ajiyar zuciya ta koma gefe ta kama kanta don bata ma san me zata ce ba kuma, ashe dai uwar Jay din er iska ce bata sani ba. Wajen karfe biyar da rabi Khaleesat ta raka Safiyyah zata tafi shima don Ya Musty ne ke ta doka mata uban kira, sosai idanuwanta suka kumbura saboda kukan da tasha, a dai dai bakin kofar fita daga parlon suka hadu da Ajay zai shigo, Safiyyah dai ta koma gefe taki yarda su hada ido tana sosa kai, Khaleesat ta wani dauke kai bayan sun hada ido da shi ta koma gefe fuskarta daure, sae da ya shigo parlon sannan Safiyyah tayi masa sai da safe tayi ficewarta daga parlon tana zare ido, ita dai Khaleesat na biye da ita a baya tana tafiya a hankali, after some minutes Khaleesat ta dawo parlor bayan ta rakata har gun Lyft da zai dauketa, tsaye ta samesa a parlon alamar ita yake jira, ya juya yana kallonta calmly yace “I don’t want to see her in this house again, if you have anything to discuss with her, discuss it at school but not in this House” Khaleesat ta wani kallesa tace “Bayan ita ina da wani ne a nan Maryland? She is all I have in this state bani da kowa ni dai, don haka wallahi sai ta zo gidan nan, ae ba wajenka take zuwa ba and she is not coming because of you….” Tana kai wa nan ta nufi stairs kamar zata tashi sama fuskarta daure, ya bi ta da kallo baya ko kiftawa har ta haura sama, tunanin yanda zai yi maganinta ya fara yi, can ya zauna kan kujera kamar me wani nazari, Khaleesat na komawa dakinta ta dau wayarta ta kunna data ta shiga WhatsApp, kamar yanda tayi expecting Housemate bai mata replying message dinta ba, kuma har status update yayi a Whatsapp, kuka ta fara yi a hankali ta ajiye wayar ta koma can Edge din gadon ta rungume hannunta hawaye na ci gaba da zuba idonta, shkkn ita kuma haka rayuwarta zai kasance har abada bata da wani say din kanta sai dai a yanke mata hukunci ko yayi mata ko kar yayi mata, haka nan aka hadata da Abdul ba tare da son ranta ba, that not being enough ya turo ta makaranta wani kasa shi ma ba tare da tana so ba kawai she just have to obey, at the end aka daura mata aure dashi ba tare da ta sani ba sai da ta dawo ta tarar da hakan, after going through hell gidan Abdul Allah ya kubuto da ita, tun daga sannan tayi tunanin she now have her freedom and will be allowed to decide for her self and chose what she want, sai gashi an kara yi mata wani auren ba tare da an damu da ko zata so ba ko bazata so ba, kawai anyi depriving dinta yancinta na yi ma kanta decision din rayuwarta, tunanin hakan ya sa ta kuka sosai tana jin ba a kyauta mata ba, ba ayi considering din feelings dinta ba…. Sai wajen karfe takwas Khaleesat ta sauka daga saman gadon ta shiga bandaki don tayi wanka, bayan ta fito ta ciro kayan da zata saka, she wish zai kai ta apartment dinta kawai tayi zamanta ita kadai a can don ji take a ranta ko ganinsa bata son yi, fuska daure kamar irin tana ganinsa din nan ta gama shiryawa cike da jin haushinsa, bayan ta gama ta zauna gefen gado tana nazarin ko dai kawai ta gaya masa ita ya maida ita apartment dinta bata son zama a nan, tana cikin tunanin nan message ya shigo wayarta, ta jawo wayar tana duba message din taga numbersa ne, bude text din tayi taga content din, taɓe baki tayi ta mayar da wayarta ta ajiye, tafi minti goma zaune kamar bazata tashi ba, amma can ƙasan zuciyarta kuma tana shakkar ya shigo dakin ya sameta, Mikewa tayi daga karshe fuska a daure ta nufi kofa ta bude ta fita daga dakin ta fara sauka downstairs ko ina ruwansa da zai dinga sa ta sai ta ci abinci, tana tafiya a hankali ta shigo parlon, zaune ta samesa a parlor da Glass din juice a gabansa yana kallon football, ko kallonta bai yi ba, ita ma taki kallon direction dinsa fuskarta babu fara’a ta nufi hanyar kitchen, sai a sannan ya bi ta da kallo ya dau Glass din juice dinsa yana sipping, tana shiga kitchen din taga ba wani abinci, ta ma zata abincin ya siyo ya ajiye mata, taɓe baki tayi ta hada hot chocolate kawai ta debi cookies me tsada da ta gani sannan ta fito daga kitchen din, Da sauri ta juya zata koma kitchen din bayan ta hada ido da katon karen gidan, karen na kyalla ido ya ganta kuwa ya bi ta yana haushi fiercly kamar ya ga Alien a parlon, ta kurma wani ihu ta fasa shiga kitchen din ta nufi dinning area da sauri jikinta na rawa tana kallon karen ta ajiye cup din hannunta da cookies, ai ko ya bi ta da gudu yana ci gaba da haushi, gigicewa tayi ta fashe da kuka sosai tana kallon Ajay da idonsa ke kan TV yana shan juice kamar bai san abinda ke faruwa a parlon ba, zaga dinning din suka dinga yi da katon karen da bai fasa mata haushi mai gigita mutum ba, cikin kuka tana kallon Ajay tace “Wayyo don Allah Yaya ka taimakeni, wallahi cizo na zai yi idan baka zo ba” Ajay yaki kallon inda take yayi keeping serious face yana kallon TV yana shan juice, tsallen da taga karen yake kamar zai cakumota yasa ta tattara rigarta, shi dai Ajay kawai ganinta yayi a gefensa kamar an jefota tana neman hawa jikinsa don karen sai da ya biyota har nan, turata ya fara yi yace “Kee baki da hankali ne, meye haka” At the same time yana matsawa da sauri daga kusa da ita putting a throw pillow barrier between them amma bata fasa rike sa ba tana shige masa jiki, hakan yasa ya yunkura zai tashi daga wajen amma taki sakesa don gam ta rikesa tana rusa kuka tana kokarin hawa kansa shi kuma yaki barin tayi hakan, bai san sanda ya haure karen ba daga kusa da su ya kora sa, da gudu karen ya koma kusa da stairs ya tsaya yana kallonsu kuma bai daina haushi ba, Ajay ya dau throw pillow ya jefa masa instructing him to leave the parlor, da gudu kuwa ya bar parlon, sai a sannan Ajay ya kara turata daga jikinsa don she was still clutching onto him tightly amma taki yarda ta sakesa cikin kuka tana boye fuskarta jikinsa take cewa “Wallahi cizo na zai yi, don girman Allah ka rufa min asiri ka kaini sama kawai” Ganin ba sakesa zata yi ba ya kyaleta kawai ya dau remote ya kara volume din TV don ma ya dena jin muryarta, don kanta tayi calm don bayan ta dena jin haushin karen, a hankali ta dago kanta daga jikinsa tana bin parlon da kallo har sannan zuciyarta na bugawa da karfi, ta fara matsawa daga kusa da shi hawaye na bin kuncinta, cikin rawan murya tace “You are very wicked, I never knew you are this wicked, kuma ni bazan zauna gidan nan da karen nan ba ka maida ni apartment dina” Calmly Ajay ya ajiye remote din hannunsa yace “Legend….” Ta zaro ido ta fasa wani ihu ta kara shigewa jikinsa tace “Don girman Allah kayi hakuri, i am very sorry, wallahi wasa nake” Yayi mata kallon gefen ido, muryarta na rawa ta marairaice masa tana kara shige masa tace “Plss take me upstairs”*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* ur evidence via 07087865788
