Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 23 Book 2 Complete Novel

 

“haba khadija, yanzu dan sunnan zakice zaki zubarmin, ina son yara sosai, ki haifamin ko dayane seki tafi karatunki bazan hanakiba, mama tana matukar son yara, tanason jikoki, dan Allah kibari ki haifamin”

Mikewa tayi ta shige toilet tabarshi a gurin a zaune. Tana shiga bandaki tayi tsaki tace “in maman nason yara, se itama ta haifa aiba abun kunya bane, aikin banza nibahakane yakawoni ba” 

“ikon Allah Salma nata nema ido rufe tana Addu’a, itakuma Allah yabata zata zubar”

Haka Habib yaita fama da Khadija, a haka har yakoma Dubai, ta shirya ta tafi gidansu sunyi murna sosai da ganinta, khadija tanada kyauta tanayu musu aike sosai, kama daga Abinci sutura da kudi, amma idan Habib yayi niyyar yiwa yan uwansa kona Salma wani abu, indai tasani seta hanashi, amma itakuma ta nayiwa yan gidansu.

Ranar dataje gida seda ta tsorata dataga Saudat tayi rama matuka, tayu duhu duk wannan kwalisar babu, har cikin ranta taji babu dadi yanayin dataga Saudat, dan haka ta dan damu, daki tabi Saudat tacewa sauran kanensu sufita subasu guri, b musu kowa ya watse, tazo kusada Saudat ta zauna ta kalleta tace “yar uwata, meyake damunki haka? Saudat kinga yadda kikakoma kuwa?”

Tsaki Saudat tayi, ta juya mata baya

“Saudat nasan ban kyauta mikiba, amma rayuwa bazata tafi a hakaba, kisani dama can Allah be rubuta Habib mijinki baneba, idan kika cigaba da wannan rayuwar tozaki kashe kanki a banza ne, tunda kinsan Bazaki samu Habib ba, Saudat inaso mucigaba da zumuncinmu, kimanta da abunda yafaru ki karbi kaddararki, Allah yafito miki da miji, indai kudine Saudat duk abunda kikeso zanmikishi Insha Allah” mikewa zaune Saudat tayi ta kalli Khadija

“Zumunci nidake har abada wallahi, kin riga kin rusa alakar dake tsakanina dake, ke kinama yaudarar kanki ne da kike cewa wai mukoma kaman da, naji tawa kaddarar kenan da tasameni a sanadinki, kema ki saurari taki kaddarar, malama ki tashi kibaani guri, ficemin a daki”

“Saudat nikike kora haka?” 

“na korekin ko uwata ce tamin abunda kikayi min sena rama, dalla malama fita munafuka” 

“shikenan tunda haka kika ce, inkika dawo hayyacinki zaki gane me nake nufi” khadija ta mike ta bar dakin. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Bayan tafiyar Habib da yan kwanaki khadija Taje chemist tace subata maganin abortion, me chemist din yace shi gaskiya baya irin wannan harkar, take ta zube masa uwar kudi, take jiki na rawa yabata magani da yadda zata bi cikin ya zube, ta dauki maganinta ta tafi gida, yadda yace mata haka tayi amfani dashi, aikuwa ba adau wani lokaci ba mararta ta dinga ciwo wuni tayi tana murkususu a haka har seda cikin nan ya fita, tasha wahala matuka, gashi ba wanda tagayawa, ko Salma da suke zaune gida daya bata mata magana, haka tai wahalarta ita kadai ta gama. 

Saboda daukin cikin da Habib yakeyi, sati uku yayi ya dawo gida, gurin khadija yafara sauka, se wani sabon kalan soyayya yake nuna mata sabida duk zatonsa cikin yana nan. 

Da daddare yana cin Abinci shida khadija, ya kalleta yace “cwt Deejah, Wani suna kikeso musakawa babynmu inkin haihu, ina son in sanarwa su yaya hajjo, cewar munsamu rabo, ko baby” dan ya tsina baki tayi

“mhmm kaga dakabar wannan batun gayawa mutane ansamu rabo, bayan tafiyarka na fadi a toilet cikin ya zube, ban gayamaka bane saboda kar hankalinka ya tashi” 

Abincin daya hadiya ne yaji ya makale masa a makogwaro yaki wucewa, 

“kin zubarmin da ciki ko khadija?”

“niba zubarwa nayi ba zu….. 

” Shut up!!! “

Yafada cikin tsawa da sedata razana

” saboda kin rainamin hankali kike cewa zubewa yayi, wato baki hakura ba shine kika zubarmin da ciki, dan kinga ina lallaba ki ko? Nikikayiwa haka ko? Har innuna miki abunda nakeso amma ki shure kiyi son ranki, kin zubar Minda ciki nagode “

“Ahhh Hayatee wallahi….. 

” yimin shiru”

Ya katseta, ya tashi ya dau wayoyinsa yabar palourn, dafe kai tayi bata taba tunanin Habib ya iya fada haka ba, saboda gaba dayansa silent ne, bashida hayaniya sam. Amma fushinsa baze hanata cinma burinta na rayuwa ba. 

Wasa2 tunda yabar part dinta seda yai sati guda bata ganshi ba, ko ta waya, dan haka ta shirya ta nufi part din Salma, tana zuwa ta tarar Salma na kitchen tana girki batabi takan Salma ba ta nufi palour na biyu, 

“lafiya zaki shigomin ba sallama ki wucemin daki?” 

“ba ruwanki ba gurinki nazo ba” ta shige tabar Salma a gurin, tana shiga kuwa ta tarar da Habib a palourn yana karanta jarida, karasawa tayi ta zauna kusada shi 

“Hayatee kwana bakwai banganka ba, meyasa dana gayamaka abunda yafaru baka yadda daniba” shiru yayi yaki dagowa ya kalleta, hannunsa ta riko ya dago  a fusace

Amma seyaga fuskarta sharkaf da hawaye, nan take jikinsa yayi sanyi

“Hayatee, duk lokacin danakiraka Hayatee i mean it har cikin raina kai rayuwata ne, meyasa ka karyatani baka yadda bani na zubar maka da ciki ba, inason abunda kakeso tsautsayine ya gifta cikin ya zube dan Allah kayi hakuri” ta zube akan gwiwoyinta tana kuka, hannu yasa ya dagota ya rungumeta yana share mata hawaye

“is ok am sorry my deejat, ya wuce kidena kuka” a hankali tace “I miss you Hayatee, dan Allah karka kara fushi dani haka” 

“I miss you too baby, bazan kuma ba”

Khadija yar duniya ce yanzu kana zaune zata siyeka. 

ganin shirun yayi yawa yasa a fusace Salma tanufo palourn, Amma abunda idonta ya gane mata yasata ja da baya da sauri, jitayi kaman andoramata dutse a zuciyarta, kitchen takoma ta toshe bakinta tana kuka, tanaji tana gani anzo har cikin gidanta an kwace mata miji. 

Antyn Jalal ta kalli Jalila data tattara duk wata nutsuwarta kaman tana daukar karatu tace

“kinga rana tayi, shabiyu takusa, kuma da azahar zamu koma maiduguri, zan kara takaita miki labarin nan dannima bakomai nasani ba, Amma kinsan meyasa khadija tayi nasara ta kwace mijin Salma?” 

Girgigiza kai Jalila tayi 

“Salma ta zurawa Habib ido tana ganin kaman yadena sontane, maimakon ta tashi tsaye tayi fighting ta gwada masa soyayya, ta kwaci mijinta, seta karaya da wuri tana ganin kaman bazata iya kishi da khadija ba tafi karfinta, ta zuba musu ido” 

Haka rayuwa tacigaba, seda Khadija ta zubar da ciki kusan hudu Habib be saniba, data fuskanci tasamu ciki setaje ta zubar, daga karshema taje tai planing hankalinta kwance ba wanda yasani, tacigaba da cin amarcinta, yau suna wannna kasar gobe suna waccan kasar, khadija tayi duk me yuwuwa takara farraka tsakanin Habib da Salma baya Jin maganar kowa se khadija, khadija yar kwalisa ce yar gayu, ta iya gayu ga girki da iya magana, yanzu zatayi laifi amma take zata mantar dashi duk wani laifi datayi, seda khadija ta shekara uku tana cin duniyarta da tsinke ta taka wanda takeso duk meson wani abu a hannun Habib seya biyo ta gurinta, Salma kam yau da lafiya gobe babu saboda bacin rai kullum cikin guma mata khadija take, duk wani abu datasan zatayi ta bata mata shi takeyi.  Sedai ta shiga daki tayi kuka. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

A yan shekarun nan Saudat haka takeyinsu ba walwala tayi iya tunaninta taga hanyar dazata rama abunda Khadija tayi mata amma takasa samu, kuma tayiwa kanta Alkawarin kozata mutu wajen daukar fansa setayi, zata nunawa khadija ba ita kadai ta iya makirci ba, zata rama inda babu wanda ze gani balle ya tausayawa khadija. Saudat haka tasamu FCE ta shiga take zuwa makaranta dan ta ragewa kanta zafi. Tsawon shekarun nan uku zazzafar gaba Saudat tajeyi da khadija duk abunda tasan ya shafi khadija nuna masa kiyayya take muraran, har mutane suka fara fuskantar hakan, yan gidansu sunyi mamakin dama akwai abunda ze hada khadija da Saudat dazesa sununawa juna kiyayya kasancewar ba’ajin kansu. 

Khadija ta hurawa Habib wuta kan lallai ita seyasamo mata Admission a Dubai ko Egypt tafara karatu, ya nunamata yan uwansa bazasu yadda da hakaba, tayi hakuri duk makarantar datakeso a Nigeria ze kaita amma banda kasar waje, amma fafur ta badawa idonta toka taki, haka yafara nema mata Admission a Dubai ba wanda yasani seshi da ita, Allah ya temaketa tasamu, yasamu Salma yace itama ze nema mata se sukoma can gaba daya, Salma tace bazata ba sedai su barta anan duk sanda yayi niyya in yasamu lokaci yazo yaganta, ya kada ya raya amma Salma tace itafa bazata ba suje se sun dawo. 

Haka Habib da khadija sukaje suka tare a Dubai, ita tana karatu shikuma yana kasuwancinsa, seyafi wata uku bezo Nigeria ba gurin Salma ba inma yazo bayafin kwana goma ze juya, hatta mahaifiyarsa ta zuramasa ido, tana masa Addu’ar Allah ya shiryeshi, yana daga cikin kaddararsa Auren hatsabibiyar mace. 

Wani zuwa da mahifiyar Habib tayi itada kannensa mata nida yayata, 

Gidan bakowa se Salma kawai mama ta tambayeta ina Habib ina khadija nan ta fashe da kuka tagaya mama duk abunda yake faruwa, Mama hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta dinga yiwa Salma fada, danme bata gayamata irin rayuwar da takeyi agidanba kenan, nan da nan ta kira Habib tace kome yakeyi ya yanke su dawo Nigeria tana nan tana jiransa. Yagaywa khadija tace wallahi bazat bar karatunta ta taho ba, shidai ya tafi shikadai, haka Habib ya taho yabarota a can. 

Ba karamin bacin rai mama ta nunawa Habib ba tace masa yazama wajibi yadawo da Khadija Nigeria bata yadda da batun karatu a kasar waje ba tunda bashida hankali, ya tare a gindin mace yana zaluntar yar uwassa, yaita bata hakuri, gefe yana fargabar yadda ze sanar da Khadija batun fasa karatunta. 

Yaita bawa mama hakuri amma fafur taki yadda tace se khadija ta dawo kasa Nigeria, hankalin Habib ya tashi yarasa ya zeyi da wannan batuna A

Mama, haka ya shirya ya koma dubai yasanarwa khadija hukuncin mama, amma tace ita bazata dawo ba, yasan yadda zewa mama ta hakura amma ita karatunta yafara nisa dan haka yayi hakuri. 

Mama tanata matsa masa lamba akan ya dawo da khadija gida, ana cikin wannna halinne khadija ta fuskanci tana dauke da juna biyu abun ba karamin mamaki yabawa khadija ba, yaza’ayi ace tana planing amma tasamu ciki, nan da nan ta shiga damuwa. Tabass barin cikin nan shize hanata da ciigaba da karatunta, gashi bata san kowa ba a Dubai balle tanemi maganin zubar da ciki, dan haka ta samu Habib tace masa ta yadda sukoma Nigeria, ba karamin mamaki yayi ba yadda akayi ta yadda ta dawo Nigeria. 

Bayan sun dawo ne, taje inda tasaba samun maganin zubarda ciki tazo ta sha, seda ta kwana biyar tana zubarda jini ba wanda yasan me yafaru, da kyar tasamu jinin ya tsaya amma ba karamin galabaita tayi ba. 

Ammame bayan jinin ya dauke haka tacigaba da rashin lafiya, kullum ba lafiya tana kwance kusa  wata biyu taki zuwa asibiti seda taji tana neman ta mutu sannan ta shirya ta tafi Asibiti lokacin Habib baya nan, Asibitin dasuke zuwa taje sukayi mata gwaje2 suka tabattar mata tanada cikin wata uku da sati biyu, abun yabata mamaki dama cikin nan yana nan be fitaba, suka dubata suka bata magunguna, tana barin Asibitin bata zame ko inaba se chemist din da take karbar magani, tai masa bayani yabata wani maganin dayafi  wancan karfi, sannna ta tafi gida. 

Khadija na barin Asibitin, doctor Hisham yakira Habib ya sanar masa yanzu amaryarsa tabar Asibitinsu kuma tana dauke da juna biyu na wata uku da sati biyu. Habib yayi murna a take yaiwa Hisham transfer na kudi, tukuicin Albishir, yana katse wayar ya kira khadija 

“Madam sannu ya jikin naki” 

“Wayace maka banida lafiya?” *”Hisham ya sanarmin kina dauke da babyna, na wata uku Ashe shike wahalar min dake, Allah maji rokon bawa abunda nake ta nema tunda kikayi bari se yanzu Allah yasa aka kuma samu, Masha Allah, Allah yarabku lafiya my deeja” hade rai tayi kaman tana gabansa amma ta maze

“Hmm Hayatee ka kyaleni, nasha magani duk jikina ya mutu” 

“Eyya sannu, i wish ina kusa danamiki tausa, amma a satin nan zan dawo Insha Allah” 

“shikenan se anjima” ta kashe wayarta, lallai doctor Hisham munafikine shine har ya kira yagayawa Habib, to gara ma yadena rawar kafa dan “kafin kadawo na zubar dashi ta rariya sedai kai yadda zakayi se burina yacika, senayi karatu me zurfi a abroad “

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Haka takuma shan maganin zubar da ciki ta dinga malalar da jini, ta kira Habib tagaya masa hankalin sa ya tashi sosai, amma bata gayamasa wani abu ta shaba, yakira doctor Hisham ya sanar dashi, har gida sukazo don duba khadija, dole suka dauketa zuwa Asibiti, da kyar aka ceto ta saboda tasha wahala sosai, a satin Habib ya dawo an rike Khadija a Asibiti ana bata kulawa ta musamman still akayi scanning still cikin yana nan be fitaba, doctor Hisham ya gano tayi Amfani da Abortion pills amma be gayawa Habib ba. 

Ya sameta ya dinga mata nasiha, sannan yace idan makamancin haka yakuma faruwa ze sanarda Habib gaskiya, ze gayamasa tana shan Abortion pills ne. 

Sannan doctor Hisham ya sanar da Habib cewa zata samu sauki ya kwantar da hankalinsa. 

Tunda Habib yasamu labarin cikin nan yakuna tattare a gurin khadija, yake matukar lallabata, itakuwa khadija batun cikin nan ya tsaye mata a rai, sam bata kaunar cikin nan, ga cikin ya hanata sakat saboda laulayi yauda lafiya gobe ba lafiya Habib yana bata kulawa iyayinsa amma ita kawai yadda zata zubar da cikin nan takeyi, takuma shiryawa ta tafi tasamu me chemist din nan tace masa ita so take inba ze iyaba ya hadata da wanda zasu ciremata cikin nan. 

Me chemist din nan ya nuna mata illar yin hakan zata iya rasa ranta kokuma tajawa kanta mummunan ciwon daba lallai ta warke ba. Haka khadija takoma gida, duk yadda zatayi cikin nan ya zube wannan karon kin fita yayi, dukda basa jituwa da dangin Habib amma sunyi murna da cikin nan nata, 

Abun duniya yakara hadewa Salma, tarasa meyake mata dadi, gaba daya Habib ya canza kaman ba Habib dinta dasuka sha soyayya a bayaba, ga sharri da khadija take mata taita hadasu rigima da Habib, ga rashin lafiya data ketayi, tana zuwa  Asibiti Akai mata gwaje2, aka sanarmata mata jininta ya hau sam hankalin Habib da nutsuwarsa ya tattarasu akan Khadija. 

Salma ta shirya taje maiduguri tasami mahaifiyar Habib tace mata dan Allah tasa baki Habib ya saketa bazata iya zama dashi ba ta gaji, mahaifiyar Habib tai kokarin bata hakuri amma ta fashe da kuka “mama wallahi in Habib be sakeni ba zan iya rasa raina, dan Allah ki amince ya a raba Aurenmu” mahaifiyar Salma ma ta yadda tace a sakar mata yarinyar ta baze yuwu a kashe mata ya da bakinciki ba. Mama takira Habib tace tanason ganinshi ya shirya ya tafi. 

Koda yaje maiduguri mama tagaya masa abunda Salma ta bukataHabib kuma yace besan zance ba, mama tace yadda Salma takeson Habib harta bude baki tace ya saketa lallai abun ya kai makura dan haka ta goyi bayan ya saketa ta huta haka, 

Salma taje ta samu Habib tace

“Habib nasoka tun bansan meye soba, ka koyaddani sonka, Habib ina maka sona gaske shiyasa banason ka kasance cikin wanda Allah ze hukunta ranar Alkiyama, Habib banason Allah yakamaka da laifin rashin adalci a tsakanin matanka, shiyasa nakeso ka sakeni dan Allah Habib, sakina shize kara tabattarmin har yanzu akwai tausayina da kaunata a zuciyarka ka sakeni Habib ” tana zuwa nan a maganarta ta sume a gigice Habib ya dakko ruwa ya zuba mata amma bata tashiba haka aka kaita Asibiti jininta ya hau sosai, kwanam ta guda da wuni a asibiti sannan ta farfado, koda ta farfado da kuka ta farfado akan dan Allah Habib ya saketa, 

Mama ta titsiye Habib tace seya saki Salma, 

“Mama wallahi bazan iya sakin Salma ba ina sonta” 

“Kana sonta ka hada kai da makirar matarka kuke neman kasheta, Ka Saketa kokuma in maka baki” 

Jiki a sanyaye ya furta ya saketa saki daya. Take Salma tayi ajiyar zuciya tareda murmushi tace “Nagode Habib ina maka fatan rayuwar Aure managarciya da matarka, Allah yabani mesona har abada” 

Habib yayi zarya maiduguri akan Salma ta dawo amma fafur aka rasa me goya masa baya, Salma kuma tace itada gidansa har gaban Abada!!! 

Khadija kam ko a jikinta, Murna ma tayi tace zata cigaba da rayuwarta yadda takeso, dama kishi da ita se wadda tayi gagarumin shiri, ganin yadda Habib yatada hankalinsa yasata tayi duk yadda tayi ya manta da babin Salma suka cigaba da Rayuwarsu. 

Ba karamin kaduwa Saudat tayi ba dataji labarin Salma ta bar gidan Habib, bata taba tunanin hatsabibancin khadija ya kai taraba Salma da Habib ba. Dan haka abun yakara yiwa Saudat ciwo, yanzu duk wannan uban gidan da uwar dukiyar ita kadai ce matar gidan. Nan take taji Ranata yakara baci, “zaki gane baki da wayo khadija wallahi sena miki Abunda ga dukiya amma seta gagareki ci cikin kwanciyar hankali” 

Haka khadija tacigaba da rainon cikin da tayi kokarin yafita amma yaki. 

Wata tara labour yazo amma bazata iya haihuwa da kanta ba se cs akai mata aka ciro mata da namiji kato kaman Habib yayi kaki ya tofar saboda kama. 

Seda akayi sati biyu ta warke saboda cs din da aka mata sannan akayi gagarumin shagalin suna, sam be gayawa khadija sunan dazesawa jaririn ba se ranar suna, ya sanar da sunan yaron ABDUL JALAL, sunan mahaifin Salma kenan!!!!

Tabdijan da alama Habib ya debota da zafi sunan baban Salma fa yasakawa dan khadija. 

Saudat ta danyi shiru sannan tace “kumafa hakane amma tayaya kenan?”

“bari muje gida zan gayamiki meyakamata kiyi”

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Watarana Khadija ta shirya da dauki Jalal taje gidansu, suka wuni acan se magariba suka koma gida a hanyarsu takomawa ta hadu da Kabir, amma ta dauke kanta kaman bata sanshiba ta zuge glass din motarta tai tafiyarta, Kabir yayi mamakin girman motar da khadija take ja, kana ganinta zaka san tana cikin daula da jin dadi, gefe ga danta kaman ba dan hausawa ba kyakyawa dashi. Taja motarta tabar gurin ya dubi shikuma irin rayuwar dayakeyi ta wahala, ya gyada kai yace “wallahi khadija senayi silar kin fito daga wannan daular dan bazaki yaudareni a banza ba” 

Haka Rayuwa tacigaba da gara Kabir wanda hakan yasa yafara shaye2 miyagun kwayoyi. 

Bayan Rabuwar Salma da Habib an takuramata a gida akan lallai setayi Aure, wani Ambassador yafito yana sonta, akayi bikinsu, abun Allah ko wata guda batayi a gidansa ba Allah yasa ta samu ciki, Masoya da yan uwa sun tayata murna sosai har Allah yasa ta sauke lafiya ta haifi namiji akasamasa Mahmud, bayan mahmud ta haifi Yusuf da Yasmin, Mahmud shine wanda mukazo dashi, zakiga yana kama da Jalal. Amma Allah yayiwa Ambassador Ahmad Rasuwa shekaru biyar dasuka wuce. Dan haka tai zamanta a England. 

Khadija ta karbi makudan kudi a hannun Habib tafara kasuwanci, tana zuwa kasashe daban2 tayi sarin kaya ta sayar, tana da manyan shaguna a fadin kasar nan, wanda dukkansu mallakinta ne. 

Saudat ta haifi diya mace, bayan danta munir, wadda itace Ilham, khadija taita zaryar Asibiti akan tanason takuma samun ciki, amma abu ya gagara har wasu kasashen sukaje da Habib amma aka sanar matada bazata kara samun ciki ba, Mahaifarta tasamu matsala sakamakon rauni datayi saboda yawan shan abortion pills datai tayi, khadija ta damu sosai har tagaji ta hakura. 

Saudat ta nunawa khadija komai ya wuce, Khadija ta dinga mata barin kudi baji ba gani, Khadija tagayawa Saudat halin da take ciki

“Saudat naso ace nakuma samun haihuwa, ko mace in haifa, Jalal yasamu dan uwa” 

“tunda Allah yabaki Jalal dinma ai ki gode masa, dan wani har ya mutu bazega kwansa a duniya ba” 

Gefe guda Saudat tayi farinciki jin cewa khadija bazata kuma haihuwa ba, hakan yasa takara kudurcewa ranta seta Rama abunda Khadija tayi mata akan Jalal. 

Ummi ta dade bata haihu ba, sunyi girma lokacin da Allah yabata haihuwa, Tunda Allah yasa Ummi ta haifi yarinya mace, hakan yakara saka Jalal zaunewa a gidansu Jawwad, kullum suna tare suna Rainon Kanwarsu, Jalal yaitabin Uncle Aliyu kanin mahaifin Jawwad yana cemasa dan Allah asakawa jaririyar nan sunansa wato Jalal. Aliyu yabiye masa yace Jalal sunan mazane amma insha Allah zanmaka takwara, karka damu, Ranar Suna yasamata Jalila, yace yayiwa Jalal takwara, Habib yaji dadin karar da Aliyu yai masa, yadda suke nunawa dansa soda kauna, duk rikicin da Jalila takeyi intaji muryar Jalal yanzu zata fara murna, gaba daya Jalal jiyake Jawwad da danginsa sune komai nasa. 

Fafur khadija tahana adinga kai Jalal dangin mahaifinsa, acewarta tunda basa kaunarta danta ma basonshi suke ba, Amma a haka Habib yake zuwa yakaishi ko a ranar ne su juyo, duk dangin Habib sunsan Jawwad, Jawwad yanajin yaren kanuri kaman yadda Jalal ma yafara jin fulatanci saboda kauna da shakuwa. 

Jalila na karama sosai Mahaifinta yanemi Aiki a garin kaduna yatafi da Ummi da Jalila, saboda yawan tsangwama da iyalannasa ke fuskanta, dukda lokacin Jalal da girmansa yashiga secondary, amma haka ya dinga rikici yana kuka, Shi be yadda a tafi da Jalila ba ya saba da ita. Tare yake cin Abinci da ita, komai yagani na wasa se yace ita ze kaiwa, komai yaci seya ajiye nata. Jalal ya dade yana damuwa akan barin gari da uncle Aliyu sukayi, Abun har yafara bawa khadija haushi, yadda ya tashi hankalinsa akan wanda ba dangin iya ba na baba sun bar gari. Ummin Jalila seda tayi kuka lokacin dazata bar kano, saboda ta riga ta shaku da yaranta Jalal da Jawwad 

Bisa ga Shawarar zulaiha, Saudat seta dakko Ilham tace ga Ilham nan tabawa khadija ta dinga debewa Jalal kewa ze manta da waccan yarinyar, khadija tayi murna da wannan kyauta da Saudat tayi mata, lokacin Ilham nada shekara takwas khadija ta karbeta, amma sam Ilham basa shiri da Jalal dan sam bata da kunya shikuma ga son girma, dan haka har dukanta yake, Jawwad yaita masa fada yace Ilham kaman Jalila takefa itama kanwarmuce, Jalal yace “Jalila ba mara kunya bace, ni Jalila ce kawai kanwata ba wannan ba” 

Har yanzu khadija bata fasa yawace2 kasuwanci ba, Jalal ya tashine a tsakanin kwararo ba bu shakuwar uwa a tareda shi, Allah ne ya dubi Jalal ya hadashi da mutanene kirki irin dangin Jawwad. 

Jalal yanada matukar kwakwalwa, sarrafa abu da haddace shi baya masa wahala, dan suna Jss2 suka Sauke Al’qur’ani, suka juya hadda, wanda wannan nasara tasu da taimakon Allah da taimakon Ummine da mijinta, Saboda itake tsayawa taga sun iya dukkan wani karatu dasuka koyo a makaranta, sunyi nisa sosai a haddarsu dan sunkai izufi Arba’in Rayuwar Jalal tafara samun matsala, Jalal yana SS2 a secondary komai nasa yafara lalacewa, sakamakon haduwa da miyagun abokai dayafarayi, Jalal yanada kyauta ga faran faran da mutane, ba babba ba yaro kowa nasane, duk wanda yakeda bukata Jalal ze dauka yai masa, hakan yasa har manya suka fara girmama shi suna gaisheshi. 

Jalal lokaci daya ya canza watarana khadija bata kasa tana can harkar kasuwancinta daga Daddy se Jawwad da Jalal a gidan Ilham kuma tana gidansu, ‘yan fashi suka shigo cikin dare, suka kama masu gadi suka kullesu, suka shiga cikin gidan, Habib yace su dauki duk abunda sukeso a gidan amma karsu taba masa yaransa, suka sakasu kneel down, sannan tattara abunda suka samu a gidan har zasu tafi dayan ya juyo ya saita Habib da bindiga, gaba daya yaran suka fara kuka, dan fashin ya musu tsawa amma suka ki yin shiru, dan fashin ya saita Jawwad yace “bari in kashe tilon dannaka dan yafiye maka komai a duniya kuma da alama yana sonka sosai” zatonsu shine Jalal, dan haka ya saita Jawwad da bindiga, Habib yace dan Allah karku kashemin shi, gaba daya yaranane, tunda kun samu abunda kuke so dan Allah ku kyalesu garani kukasheni, dan fashin nan yamasa banza ya dan kunamar bindigarsa, kawai Jalal ya mike tsaye, bullet din ya shigeshi a gefen kirjinsa, yan fashin na ganin haka, suka kwashi abunda suka kwasa suka gudu. A gigice Habib da Jawwad sukayi kan Jalal amma yana kwance kaman ba rai jini nata malala a kirjinsa, hakan ya firgita Jawwad kwarai shima ya suma a gurin, misalin karfe uku na dare haka ya daukesu ya tafi dasu Asibiti. 

Da kyar aka cire bullet din a kirjin Jalal, ya galabaita saboda a gefem zuciyarsa bullet din yasameshi, shima Jawwad da kyar aka samu ya farka. Wannan fashi ana kyautata zaton dasa Hannun Kabir a ciki, amma ba’a tabattar da hakan ba. Seda Habib ya kai su Jawwad Dubai aka dubasu acam sannan hankalinsa ya kwanta, seda akayi kwanaki sannan khadija tasan meyafaru. 

Akaita zuwa duba Jalal, Allah yatemakshi ba’a dadeba ya warke suka koma makaranta. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Mahaifin Jalal ya hada mahaifin Jawwad da manyan mutane akan harkar kasuwancinsa, wanda silar hakan Allah yasawa mahaifin Jawwad nasibi a kasuwancinsa, yasai gida a Sharada NNDC, suka koma, Jalal yasamu daddynsa yace masa dan Allah yanaso yasaimusu gidan dayake makawabtaka danasu Jawwad sukoma, haka kuwa akayi suka tattara suka koma kusada juna, ga gida ga gida.

Har yanzu babu jituwar Arziki tsakanin Jalal da Ilham, ba Ilham bama kawai hatta mamanta Saudat basa shiri saboda hakanan Allah be hada jininsuba, wataran Saudat tazo gidan, tabawa Jalal kyautar turare, da yanuna baze karba ba, Amma Jawwad yasashi ya karba, yace masa ba a haka mutum yamaka kyauta ka gwaleshi, Tunda Saudat uwace a gurinsa, Ranar suna kwance cikin Dare, Jawwad yaji kaman ana jijjiga gadon dasuke kwance dan haka ya tashi da sauri ya kunna fitila, yaga Jikin Jalal yanata Kakkarwa, abun yabashi tsoro sosai, ya tattaba Jalal yace “Dan uwa meyasameka kobaka da lafiya ne” Jalal ya masa shiru, koda Jawwad ya cigaba da magana se Jalal ya bude idonsa seda Jawwad ya firgita wani irin Green yaga kwallarsa tayi, ga jijiyoyin kansa sun tashi sunfito sosai har goshinsa, Jalal ya rike Jawwad yace “Jawwad wani hayaki ya shiga jikina, kamin Addu’a amma karka gayawa kowa, ka dauki turarenda Maman Ilham tabani ka jefar dashi, daga ciki hayakin yake fitowa” Jawwad yadinga karanto masa duk abunda yazo bakinsa a haka har bacci ya dauke Jalal, sannan Jawwad ya dauke turaren ya boyeshi, Jawwad beggayawa kowa ba kaman yadda Jalal ya bukata. 

Tundaga nan Jalal yafara zama wani iri, Suna SS2 Jalal yafara haduwa da miyagun abokai, ciki hada wani hatsabibi waishi Jabir Junaid, suna ce masa Jeje, gaban Jalila seda yafadi jin an ambaci Jeje, 

“tunda Jeje ya shiga Rayuwar Jalal komai nasa yafara lalacewa, ya koya masa shaye2, Jawwad yai kokarin ya raba Jalal da Jeje amma abu ya gagara, Jawwad be gayawa kowa Jalal yafara shaye2 ba, yayai2 amma Abun na Jalal kullum gaba yakeyi, a haka har mutane suka fara ganewa. Habib yashiga tashin hankali daya fuskanci Jalal yafara shaye2, ya shiga dakin Jalal ya tarar dashi a kwance ga kayan shaye2 Jawwad na gefensa yayi tagumi, hankalin daddy ya tashi, ya tambayi Jawwad me yake faruwa haka, nan Jawwad yaiwa daddy bayanin komai, amma be gayamasa tun asalin meya faruba, ya dai ce masa shima kawai gani yayi Jalal yana shaye2, yayi2 ya dena yaki Habib yashiga tashin hankali jin tilon dansa yafada mummunar Rayuwa, A lokacin khadija kusan watanta guda bata Nigeria, Bayan Jalal yadena maye ya zaunar dashi yaita masa nasiha yana masa fada, amma Jalal fadan nan ko a jikinsa. 

Bayan dawowar Mummy Habib ya dinga yi mata fada yana cewa “Khadija a sanadin rashin kulawarki, da sakacinki Rayuwar dana ta tasamma rugujewa, Jalal yakama hanyar lalacewa, wace irin uwace ke” 

A fusace tace “Nifa baangane inda maganganunka suka dosa ba, da can bakasan inada sakacin ba se yanzu?” 

“ABDUL JALAL yafara shaye2, shaye2 yakeyi” Zare ido tayi “Kamar ya shaye, ni dana baya shaye2, Jalal baze hakaba” 

“koki yadda kokarki yadda yarage naki, sekije ki bincika” a gigice ta fita tanufi dakin Jalal, aikuwa tana shiga ta tarar dashi yanata busa hayaki, cikin tashin hankali ta karasa cikin dakin

“Jalal mekakeyi haka? Shaye2 fa kakeyi” 

Banza yamata yacigaba da abunda yakeyi, ta karaso ta nufo inda yake amma ya dakamata tsawa “Karki sake kizo inda nake tunda ba kyason bakya kaunata, bakida wata magana dazaki gayamin lokaci yariga ya kure, Mummy da hannunki kika rusa Rayuwata, kin fifita son zuciyarki akan Rayuwar danki, kifita ki barmin dakina, bana kaunar ganinki” 

“Amma Jalal…….. 

Jifa yafarayi da duk abunda yaci karo dashi cikin tsawa yake cewa” Kifita Nace bana son ganinki, kije kudi su baki farincikin da duk kike bukata, kifita kibani guri, Jawwad ne yashigo dakin da Sauri yaga abunda Jalal yake da sauri yaje ya rikeshi, Mummy ta juya cike da damuwa tabar dakin. 

Tundaga wannan lokacin Rayuwar Jalal tashiga rudani, yadena jin magana ibada ma baya iyayi, yadena ganin girman kowa, yadena ganin mutuncin kowa, kowa ya janye dansa daga shiga huldar Jalal, Jawwad ne kawai be barshiba, da mahaifiyar Jawwad ta fuskanci Halin da Jalal yafada setayi kokarin ta rabasu, saboda kar itama nata dan ya lalace. Amma abu ya gagara mahaifin Jawwad yace indai tai kokarin raba Jawwad da Jalal batayi adalci ba Addu’a yakamata tayi musu gaba daya, wasa2 abu yafara shafar kwakwalwar Jalal ya manta abubuwa saboda shaye2, a haka suka gama secondary suka shiga jami’a, Jawwad na mechanical engineering, shikuma Jalal yana karanta civil engineering, shima a university din haka yakara lalacewa da shaye2, kullum Jawwad kokari yake yaga Jawwad yadena abunda yakeyi amma abu ya gagara. 

Suna level 1 kakar Jalal mahaifiyar khadija ta rasu, Jalal yazama rikakken dan shaye2, yazamana in har Jawwad bega Jalal ba to a Club ze tsintoshi. Dukdahaka lokaci zuwa lokaci Jawwad yana raka Jalal maiduguri su gaida dangin mahaifinsa Khadija tacewa Jalal bata yadda yakuma zuwa maiduguri ba, inyakuma bata yafe ba tunda dangin mahifin sa basa sonta shikuma Jalal yace sedai katta yafe, ita mutum nawane sukace basu yafe mataba, Jawwad yace masa be kamata yadinga zuwaba tunda tace bazata yafeba hakkinta ze iya kamashi, dama dangin Habib tuni suka dena zuwa saboda wulakancin Khadija. 

Jalal yana shekararsa ta karshe a Jami’a abun nasa yakara ta’azzara, da yana iya karatu dukda yana shaye2, yana da kwakwalwar sosai dan yana daga cikin wanda ake ji dasu ga barin kudi dayakeyi, amma a final year kwakwalwar Jalal takara birkicewa, yakasa karatun ga mantuwa, makarantarma gaba daya yadena zuwa, se yawon club, abokansa yan iska suka kara like masa saboda yadda yake sakar musu kudi, gaba daya iyaye suka hana yaransu shiga harkarsa, suka shiga tsangwamarsa da an ganshi se a tashi abar guri yazama abun kyama, kowa ya gujeshi se Jawwad, hakan yakara tunzurashi yafara rashin mutunci yadena ganin girman kowa, memakon amasa nasiha ko Addu’a se akaita Allah wadaran da halinsa, hatta dangin Khadija basason yaje inda suke bayan abaya harsosuke yaje saboda sunsan indai yaje seya musu barin kudi, ana cikin wannan halinne Ilham ta nuna tanason Jalal a haka, hakan ya tabattar da akwai abunda Ilham suke shiryawa dan daukar fansa akan Khadija da danta, Amma hankalin khadija be kaiba itama ta goyi bayan hakan tana ganin tahaka ne zata wanke zuciyar Saudat akan abunda taimata, har zuwa wannan lokaci ake wannan turka turkar.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Kakar Jalal mahaifiyar Habib tayi kuka lokacin data samu labarin yanda jikanta yakoma, gashi kiri kiri an hanashi zuwa inda take da wannan bakincikin takoma ga Allah, tanawa jikanta fatan shiriya, amma ranar dasukazo gaisuwa suka juya, Mummy tahana Jalal kwana, wannan abun yakara bakantawa danginmu Rai, muka dauke kafarmu daga gidan Habib tsawon shekaru. Babban abun godiya ga Allah shine Jalal baya neman mata ba ruwansa da mata, ko a makaranta ko a club ba ruwanshi dasu, ze sha giya yayi askin banza, yayi rashin mutunci, baya ganin girman kowa musamman Mummynsa dayake ganin sam batayi masa adalci ba a matsayinsa na danta, tunda ta goyi bayan ya auri Ilham, da nufin ta wanke laifinta na baya yakara jin haushin mahaifiyarsa. 

Antin Jalal ta kamo Hannun Jalila da fuskarta ta jikebda hawaye tace “Jalila nagaymiki iya abunda nasani gameda rayuwar Jalal, wani abun nima har yanzu ban saniba, nasan zanbarki cikin dunbin tunani, amma Jalila bantaba zaton Akwai wanda ze iya karkata hankalin Jalal ba, duk lokacin daka dakko yimasa Nasiha ko ransa yabaci sekaga yafita hayyacinsa idonsa ya canza kala yafara jifa da abubuwa, kin dakko hanyar daidaita Rayuwar Jalal amma bata sigar dakika fara ba, duk lokacin dakika batawa Jalal rai seya gayamin, Jalila akwai abubuwa da bangayamiki ba saboda ba’a bakina yakamata kijiba, wannan tarihin danabaki nagaya mikine bisa Amincewar Jalal, yanzu mu tashi kinga azahar tayi wanka zanyi inyi Salla zamu juya. 

Jiki a sanyaye Jalila ta mike suka nufi cikin  gidan, Jalila kam waje tayi, ta tafi gida, tana zuwa gida ta tarar da Nana a harabar Gidan, Nana tana ganinta tace “Jalila ina kika shiga ne? Tun dazu nake nemanki nakira layinki amma wayar na daki” 

Jalila batace uffan ba ta wuce daki, tana zuwa ta zube akan Gado, ta fashe da kuka

“ban kyautaba, Mummy meyasa? Meyasa kikayi haka, Ashe shiyasa Jalal yake cewa Kinfiye sonkanki, Saboda kudi da son zuciya kin bata farincikin mutane da dama, kinyi sanadin Rayuwar danki, Jalal ka yafemin bansaniba” takara fashewa da kuka.

Sosai Jalila take Hawaye, tareda surutai a hankali, Nana ce ta shigo dakin, da sauri Jalila ta goge hawayenta, zuwa tayi ta zauna ta kalli Jalila

“Jalila lafiya kuwa, meyasameki? Meyasaki kuka kuma ina kika shiga tun dazu nake nemanki” Jalila bata san wace tambayar yakamata ta fara amsawa Nana ba, Jalila ta dan girgigiza kai tace “Bakomai karki damu”

“Yazakicemin ba komai, kuka fa kikeyi”

“Nana bakomai”

“Shikenan tashi muje, Bakin su Jalal zasu tafi, taso Anty Amina tace inkiramata ke” se yanzu Jalila tasan sunan Antin Jalal dinma, ba musu ta mike suka fito tare, suna shiga gidan suka tarar dasu sunfito zasu tafi, Mahmud ya kalli Nana yace “Nana gashi zan tafi bangama ganinki ba” murmushi Nana tayi “Nima bangama ganinka ba, kaje kayi zamanka a England, memakon kadawo Nigeria muma mu amfana da iliminnaka, kaje se wani uban kumatu kakeyi”

“Allah hajiya Nana, ke bakiga yadda kikakoma bane, kinzama wata madam, yanzuma Anti Amina mukayi waya, zasu zo nan kano, shiyasa nadawo nace nima suzo dani zan dade a Maiduguri kafin inkoma England” ya kalli Nana yayi kasa da muryarsa yace “Nana wannan ce Jalila ne?”

“itace kasanta ne?”

“A’a na tambayekine kawai, naga tana kama da wata ne, just forget, bani lambarki” 

“Seka biya tukuna” murmushi Mahmud yayi, “Yimata kudi ko nawane imbiya” Nana tai dariya ta karbi wayarsa tasamasa lambarta, Suna tsaye suna jira Jalal yafito suyi Sallama amma tunda Jalila taimasa abun nan da safe, ya shige daki yaki fitowa ko sallama suyi, Jawwad yanata masa magiya amma yaki bude kofar nan.

Anti Amina takamo hannun Jalila tayi gefe da ita, ta kalleta tace “Jalila kuka kuma? Meyasa? Munasa ran samun nasarar daidaita rayuwar Jalal ta hanyarki amma muga karaya a taredake, karkimana haka Jalila, banbaki labarin Jalal dan isaki damuwa ba” kaman ta ziga Jalila takuma fashewa da kuka, Rungumeta Anti Amina tayi tana sharemata Hawaye cikin kuka Jalila tace

“Anty dana san haka Rayuwar Jalal take daban zama daya daga cikin masu kara rusa farincikinsa ba nasan na dade ina bata masa Rai amma……. 

” Jalila kina yimasa hakane dan inyaji haushi ya dena abunda yake nasani karki damu kinji kidena kuka”

 Jalila ta jinjina kai, suka musu rakiya har mota suka daga suka tafi. 

Jalila jikinta a sanyaye takoma gida, daki takuma komawa ta kule akan gado tayi shiru nan ta shiga tunani daban2, 

“Kenan Kabir shine Oga Kb? , Jeje yataka Rawa gurin lalacewar Jalal, menen alakar Kabir da Jeje?” dafe kanta tayi tai tagumi hannu bibiyu tai shiru sekuma wani abu yakuma fadomata a rai

“Saudat tabawa Jalal turare, aranar yadinga karkarwa cikin dare yana firgita, kenan Saudat ma wani abun tayi masa kokuma mene? To wa zangayawa? Mema yakamata inyi ne? ” 

“Yasalam” Jalila ta furta da karfi tareda dafe kanta, da Hanzari Nana ta shigo dakin ta tarar Jalila ta dafe kai tana kuka

“Jalila lafiyarki kuwa? Tun dazu nake tambayarki meyasameki amma kinki gayamin se kuka kike kinga yadda idonki yayi Ja kuwa?” 

Murmushin dole Jalila ta kakalo, “Karki damu kaina namin ciwo sosai, allow me to rest” ta ture Nana ta kwanta, Nana ta dade tana mamakin meyake damun Jalila haka? 

Yadda Jalila taga Rana haka taga dare, banda zunzurutun tunani da tambayoyi ba abunda ke kai komo a zuciyarta, ga wani irin tausayin Jalal dake ratsa zuciyarta, antarwatsa Rayuwarsa akan abunda lokacin da ake laifin baya duniyar, gaskiya Mummy bata cancanci zama uwa ba, ta fifita duniya akan Rayuwar danta. Har gari ya waye Jalila idonta biyu, 

Halima da Nana ne suka hada breakfast, nanma sukayi sukayi taci Abinci takici, Abun yafara bawa Nana tsoro, dan haka taje tagayawa Maama halin da’ake ciki

“Nono kikeso inkamota in bata ko goyata zanyi inta jijjigata?” 

“Maama bahakaba, at least yakamata musan meyake damunta, kartayiwa kanta illa, tun jiyafa bataci Abinci ba tanata kuka, kinsan batada cikakkiyar lafiya fa?” 

A fusace Maama tace “fita kibarmin daki, kar Allah yasa taci, inta kashe kanta aita huta” 

“Amma Maama…. 

” Bazaki fita ba sena makeki” ba shiri Nana ta fito, ta nufi part din Jawwad amma bayanan, takira wayarsa harta katse be dauka ba, daki takoma tazubawa Jalila ido data kwanta ta rufe ido, amma hawaye nabin gefen idonta 

“Jalila dan Allah kitashi kici Abinci, wallahi gaba daya zuciya ta babu dadi, na damu matuka, dan Allah kici wallahi inbaki ciba nima bazanci ba” A hankali Jalila ta bude ido, ta mike zaune ta kalli Nana tace “zubo muci, banason kizauna da yunwa” 

Nana ta zuba Abinci amma Jalila ta dan cakala ta barshi. 

Wunin Ranar Haka Jalila tayi duk surutun nan amma yau tsit kakeji, Nana tayi tambayar harta gaji ta samata ido. 

Da daddare Jawwad ya shigo yasamu Maama a palour yake gaya mata Ankai Jalal Asibiti. Da sauri Jalila ta mike ta fito palour ta labe

Maama tace “meysameshi haka?” 

“kinsam jiya yan maiduguri sunzo, kuma dai kinsam babu jituwa tsakaninsu da Mummy, andai bata masa rai yaje ya kulle kansa a daki, yafasa abubuwa sosai sannan cikinsa da yunwa ya sha wani abun bansan meyasha ba, da kyar na bude dakin dazu, naganshi a sume shine muka kaishi Asibiti, yanzu can zantafi zan kwana dashi”

Maama ta kalleshi “ohhh Jawwad Allah yayemaka wannna Jaraba, wannan yaron Jalal kullum seyajanyo abun daze hanaka hutawa, sekayi tayi ai wahalalle” 

Murmushi Jawwad yayi yace “Maama kenan, ai duk dan halak baya manta alkhairi, bari in tafi seda safe” ko kallonsa bata kumayiba, har ya juya ze fita Nana tace “Yaya Jawwad amasa sannu dan Allah, kuma wallahi Baby ma inaga wani abu na damunta tunjiya kuka takeyi, taki cin Abinci da kyar nasata taci kadan” 

“Haba dai? Kuma kin tambayeta meyake damunta?” 

A fusace Maama tace “fita katafi inda zaka, bazasu hadu sukasheka ba kowa  ya kwaso iskancinka akanka ze sauke, kaidabaka san ciwon kanka ba” 

Jiki a sanyaye Jawwad ya juaya yafita, Jalila takoma daki ta kwanta tai shiru tamarasa tausayin wa yakamata taji. 

Jin batun Jalal na gadon Asibiti abun yadameta. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Har gari yawaye Jalila nata kasa kunne taji wanda zeyi zancen halin da Jalal yake ciki, har wajen azahar shiru, Jalila tace “Nana naji kaman yaya Jawwad yace an kai Abokinsa Asibiti?” 

“Eh acanma ya kwana, har yanzu kowaya beyoba, dazu Maama takirashi a waya amma bata shiga” 

“to ya jikinnasa?” 

“Nima bansaniba wallahi, amma bari mujira zuwa anjima” 

Jalila ta gyada kai, ta dakko wayarta tana dubawa taga missed calls rututu

Call logs dinta tashiga tatarar da missed calls na Zahrah, Jalila ta kirata a waya bugu biyu ta dauka

“Salam alaikum, Jalila ina kika shiga tun jiya nake kiran wayarki amma ba kya dagawa” 

“Am sorry ina wani mahimmin abune, se yau na dakko wayar, ya akayine?” 

“Hmm Jalila sarkin Sabga, dama gayamiki zanyi anbada belin Baban Samir Fa shida duk wanda aka kamasu, shine nace kina ganin ba abunda ze faru kuwa insuka ganomu” 

“Zahrah karki damu babu abunda ze faru, koda anganomu muka shirya wannan abun, to ki zame kibanni ba ruwanki balle baza’a gane ba, Burina ya cika na tonawa duniya asirin ya da Uba, duk wani cin zarafi da wulakanci dasu Saleema sukeyi dole sudena, saboda wannan mummunan abu. Kunya dasuka aikata, Amma tabbas zankuma gauraya dasu, Alhaji Kabir da Jeje, Nagode kigaida Umma” Jalila ta kashe wayarta, tacigaba da duba kiran da akayi mata takuma cin karo dana Hanan, da sauri ta kira Hanan, seda takusa tsinkewa sannan Hanan ta dauka, tace “Se yanzu zaki kirnaiko? Tun jiya nake kiranki amma kinki dagawa yar wulakanci kawai” 

“Yi hakuri Hanan, lokacin bana tareda wayar se yanzu na duba nagani” 

“To na hakura Allah ya temakeki, dama zamuje Bauchi nan da 2 weeks, Daddy yace zamuzo mu tambayi Abba inya yadda mutafi dake Inna taganki” 

Jalila tace “Hanan zanyi murna da zuwanki, ina cikin matsala inason inganki” 

“Matsala kuma Jalila? Meyafaru?” 

“Hanan na dade ina tafka kuskure, yanzu ina nadamar abunda nayi, abun baze yuwu ta waya ba, nafison mu hadu” 

“Subhanallah Jalila nadamar mekuma? Zaki banni cikin damuwa da tunani, ki gayamin menene?” 

Jalila ta dan share Hawaye tace “Hanan for all this time i have hurting Jalal, calling him with different bad names, he is innocent, Hanan an gayamin tarihinsa, Jalal abun a tausaya masane, inajin kunyar hada ido dashi, Hanan ban kyauta ba” 

“Is ok kidena kuka, ai duk dan adam baya wuce aikata kuskure, Calm down, abunda na dinga nunamiki kenan a baya amma baki ganeba, baka yankewa mutum hukunci kai tsaye akan abunda kaga yana aikatawa, idan nazo zamuyi maganar, amma ya akayi kikasan ba laifinsa bane?”

” Ai baze yuwu a waya ba, se mun hadu”

“Amma yakamata ki wanke lefinki” 

“Hanan tayaya, tunda na riga nayi” 

“Hakuri zaki bashi mana” 

“Hakuri kuma?” 

“Eh mana, yakamata kinemi ya yafe miki” 

“mhmm Inasu Yaya Abdallah? Inason ganinsa ma ina neman yamin wata Alfarma inze iya” 

“Wace Alfarma kenan?” 

“Ina ruwanki semun hadu nida shi, ki gaida Baba” 

“Hmm shikenan zeji Insha Allah” sukayi Sallama

Jalila kasa jurewa tayi ta dau waya takira Jawwad amma baya dauka, haka ta hakura. 

Washegari shiru2 Jawwad be dawo ba. Har bayan Azahar gashi baya daga waya, hakan yasa Jalila ta kara shiga damuwa, ta fito harabar gidan, dan tasamu ta kadaice tayi tunani, tana nan Zaune tayi nisa sosai a tunanin tarasa ta ina yakamata ta fara, gaba daya abubuwa sun hargitse mata. 

Motsi taji abayanta yasatayi saurin waigawa, Jawwad ta gani a tsaye tai sauri ta mike tsaye. 

“Baby meke damunki hakane? Tun dazu nake magana amma kinyi shiru, gayamin meke faruwa?” 

Murmushi Jalila ta kakalo, “Yaya Jawwad bakomai kawai dai banji bane, ina ka shiga bana ganinka nakiraka a waye baka dagawa” 

“Jalal ne ba lafiya, na kaishi Asibiti na manta wayata a gida” 

“Meyasameshi?” 

Ajiyar Zuciya Jawwad yayi sannnan yace “jininsa ya hau, yana damun kansa dayawa, Jalal baya iya controlling bacin Ransa, yanada saka abu a ransa, ga kinsan shan taba yana kara saka hawan jini, amma Alhamdilillah jikinsa da sauki an sallameshi tare muka dawo gida” jinjina kai Jalila tayi “Allah yabashi lafiya” 

“Ameen Baby, meyasamin ke kuka kika kasa cin Abinci Nana ta gayamin” 

“Nikuma ai kaina ke ciwo kawai itakuma tabi ta damu, amma na warke ai” 

“Anya kuwa, karya ba halinki bane, fuskarki ta nunamin kina cikin damuwa” 

“bana cikin wani damuwa ni, kako ci Abinci naga kaman a gajiye kake” 

“Hmm wato ba kyason incigaba da tambayarki ko?” 

“bahaka bane, banaso ka zauna da yunwa ne” 

Murmushi Jawwad yayi, “Ina jin yunwa kam, samomana wani abun, Jalal ma beci Abinci ba, yaki cin Abinci wallahi, nayi2 amma yaki, Yana cikin damuwa sosai, anyway samo mana abunda yasamu in lallabashi koze ci” gyada kai Jalila tayi ta juya da sauri ta tafi cikin gida. 

Tana shiga palour ta tarar da Maama tana mata wani irin mugun kallon banza, Jalila ta dauke kai kaman bata san meke faruwa ba tai kitchen abunta. Ta dafa masa jallof spaghetti, ta hada da juice bayan tagaama take tunani yanda Maama ta zauna a palou  tana mata kallon banza, yanzu in tace zata kaimasa Abinci wani bacin ran zata jawa kanta dan haka ta kirashi a waya tace yazo ya dauka, befi minyi bakwai ba sega Jawwad yaje kitchen ya dauki Abincin. Har yazo ze fita Maama takirashi, yadawo ya zauna a gabanta yace “Maama gani, Allah yasa ba laifi nayi miki ba” 

“laifi kuma tun yaushe kake sabawa umarnina, minyi magana akan muna son hada Aurenka Naja amma har yanzu baka kumabi takan zancen ba, sekara shigewa wannan algungumar yarinyar kakeyi, ban isa ingayamaka magana kajiba ko?” 

“Maama dan Allah kiyi hakuri, na yadda in Auri duk wadda kikeso, amma bazan iya Auren Naja ba” 

“Jawwad kake kallon tsabar idona kake cemin bazaka iya Auren Naja ba” 

“Maaama Naja yar uwata ce bazankita haka kurum ba amma… 

” Yimin shiru badai akan waccan hatsabibiyar kake rawar kaiba, idan ina raye ayi ingani, tashi kabani guri”

Jiki a sanyaye cike da damuwa Jawwad ya mike yabar palourn. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Tunda yan maiduguri suka tafi Jalila bata kara saka Jalal a idonta ba dan sam yadena zuwa gidansu, ga Jawwad yanata complain akan Jalal bayacin Abinci yana damun kansa sosai, ga matsalar da Jawwad yake ciki shima Maama nata tursasa shi tace se ya Auri Naja, amma ita Nana ta tirje tace bazata Auri faruk ba an kyaleta, Jalila tarasa yadda zatayi taga Jalal, duk abun yafara damunta. Ga yaya Jawwad dinma ta dena ganinsa ko waya basa yi, yadena shigowa cikin gida. Zaman cikin gida ya isheta dan haka ta fito danta sha iska, ta fito ba dadewa Jawwad ya shigo yayi parking, duk taga ya dan rame, yafito ya kulle motar, takarasa inda yake “Yaya Jawwad wai meyake damunka hakane, ka rame kuma tun shekaranjiya ban kuma ganinka ba” cike da damuwa yace mata “Baby Jalal, yana nema ya kashe kansa” 

“Kamar yaya?” 

“Ankuma kwantar dashi a Asibiti, tun shekaranjiya ina can, banason inkira Daddy kar adaga masa hankali, idan Mummy taje gurinsa, seyace seta tafi bayason ganinta yanzu haka jikinsa yakuma rikicewa, yanzu haka tun jiya yana ICU, maybe yau zasu fito dashi” nan da nan jikinta ya hau rawa, cikin rawar murya tace

“Subhanallah Allah yabashi lafiya, if you don’t mind zan rakaka in dubashi” 

“Shikenan naji amma kibari seda safe in Allah ya kaimu zanzo muje” ta jinjina masa kai takoma cikin gida

Yau Hannah har gidan Jeje taje nemansa tayi sa’a kuwa yana nan, Jeje yayi mamakin ganinta sosai “yau kece da kanki a gidana” 

“Eh nice amma kasan duk lokacin daka ganni bukatace ta kawoni, almost one week ina nemanka, bana ganinka layinka baya shiga, amma naji ana rumors ankamaka kai da megidanka a gidan karuwai meye gaskiyar lamari” shiru Jeje ya danyi ya kalli Hanna

 “Ni ina zargin dasa Hannunki akan abunda yafaru dani, shekara da shekaru inawa Oga Kb aiki inasamun rufin Asiri a gurinsa, ina hutawa da ‘yarsa ba tareda yasani ba lokaci daya aka masa cunen gidan danake zuwa yakamamu, yanzu ya sallameni tareda cin alwashin seyaga bayana, wallahi Hannah indai dasa hannunki a wanna cin zarafin da’ akamin bazaki tsira daga sharri na ba”

Murmushi Hanna tayi sannan tace “Aidama karshen alwa kasa, kuma ramin mugunta kurarrene, Jeje idan har zanmaka wannan manakisar yan sanda suka maka kaida uban gidanka to wallahi da duk yadda zanyi bazaka fita daga hannun yan sanda ba daga kai harshi, dara ce taci gida kawai, kakoma kayi tunani ka sake nazari waze iya aikata maka haka, kasan innice nayi maka wannan aikin bazanji tsoron gayamaka bako? tunda irin tarbar danasamu daga gurinka kenan shikenan nagode ni na tafi, amma kakiyaye shiga hanyata, kasanni ban da kyau”

 tanagama fadin haka ta juya tanufi motarta, yayi Yunkurin ya biyota amma ta tashi motar tabar gurin. 

Yauma Jalila ba bacci, saboda tashin hankali da damuwa, se addu’a da takeyi, Nana kam ta gaji da tambayar ta meyake damunta. Da Asuba Jalila tai wanka tai salla ta shiga kitchen ta dama kunun gyda da dankalin turawa, karfe bakwai tagama shiryawa tsaf tana jiran Jawwad, Nana tai juyi akan gado ta kalli Jalila 

“wai shirin mekikeyi hakane?” 

“Asibiti zan raka Yaya Jawwad muduba Yaya  Jalal” dan zaro ido Nana tayi, sannan tai murmushi 

“Yaukuma da kanki kike cewa Yaya Jalal” takuma murmushi tace “Zanso inje nima induba shi, amma wallahi bacci nakeji, kuyi masa sannu in an sallamoshi naje in duba shi, kokuma in Maama zata semuje tare” Nana ta juya tashige bargo, Jalila na nan zaune, wajejen karfe takwas Jawwad yakirata a waya yace tafito su tafi, da sauri ta dakko kwandon kayan Abincin ta fito, Jawwad ya kalleta yace “Baby hada hidima haka, Abinci kika mana” 

“Eh Yaya, koba kwaso?” 

“haba mu mun isa, taho mutafi” ta shiga mota suka tafi, suna zuwa Jawwad yaimata jagora har dakin da Jalal yake, suka tura kofa suka shiga ta tsorata da ganin Jalal, yana kwance akan gado dagashi se dogon wando da singlet, yanata sauke numfashi a hankali, ya rame matuka gashi yayi duhu se dogon hancinsa yakara fitowa sosai, drip yana shiga jikinsa a hankali, hawaye yafara bin idon Jalila a ranta tace “idan har Jalal ya mutu ina da alhaki, ninakara assasa bata masa rai” 

Jawwad ya dora hannunsa akan gadon da Jalal yake ya sunkuyar da kai, Yana dago ido Jalila taga kwalla a kwance a idonsa 

“Yaya karka karaya mana, zeji sauki” Jawwad yai murmushi yace “Baby Jalal wani bangarene na rayuwata, inajinsa a raina kaman wani bangare na rayuwata, banason rasashi, banason wani abu yasameshi da inada yadda zanyi in kawar masa da damuwarsa, danayi amma ba yadda na iya kaddara tariga fata, haka Allah ya kaddara masa, ina fatan Allah ya musanya masa da kyakyawar kaddara ” Jawwad yai ajiyar zuciya yace “Bari inje gurin doctor inji meze ce, kizauna anan anjima su Ilham zasuzo nima yanzu zan dawo, inkuma ya tashi kafin in dawo kikirani beci Abinci ba” ta jinjina kai, Jawwad yafita yabar dakin guri ta samu ta zauna akan kujerar gaban gadon Jalal, Hawaye tacigaba da sharewa lokaci zuwa lokaci tana dorawa kanta alhakin wannan rashin lafiyar da yake, 

A hankali Jalal yai juyi, da sauri ta goge idonta ta tsaya tana kallonsa bude idonsa yayi a hankali ya saukesu akan Jalila dake goge hawaye, kura mata ido yayi ko kyaftawa ba yayi. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool 

Back to top button