Novel Document

Dattijon Arziki Novel Document

Dattijon Arziki Complete Novel Document By Rahma Ladingo

Description/Story:

Dattijon Arziki! Novel Document Written By Rahma Ladingo 

 

Description

K’asar Tchad cikin garin Ndjamena.

Lokacine na yanayin sanyi, amman na yau yafi na kullun.

Yau an ta shi da wani irin mugu-mugun sanyi mai shiga jiki dukkan sassan jikin ‘dan adam,wanda garin yake d’auke da wani irin hazo sosai, dayawa daga cikin mazauna garin, wad’anda suke waje domin kasuwancin su na yau da kullun, su na sanye cikin kayan sanyi, sabida sanyi yau ya fita daban da ko yaushe.

Unguwar (Ambassadna)

Wani katafareran gidane wanda tin daga gate d’in gidan za ka gane gidan na kece raini ne, kallo d’aya zaka masa kasan eh mai shi ba k’aramin mutum bane.

Gidan tamfatsetesne an had’a komai na jin dad’in duniya acikinsa, babu ce kawai babu.

Ko ina ka bi acikinsa an k’awata shi da shukar flowers masu kyau da k’amshi, wani tafkeken lambune, mai d’auke da shuke-shuken ‘ya’yan itatuwa daban², iccan dabino strawberry inabi mangwaro lemon zak’i iccan kwakwa gwaiba.

Gefe d’aya wajan kiwon tsintsaye ne, wasu manyan keji ne gudu 5 dana d’awisu talatalo jimina k’wak’wa tantabaru irin na turai, sai kejin aku (uban mgna).

kai! tsayawa fad’in tsaruwar gidan abubuwan burgewar da suke cikinsa zai jamu da nisa, amman tsarin gidan da komai ya ji ma Sha Allah.

Masu gadine mutum biyu sanye da uniform, k’arfafan gaske kallo d’aya zaka musu, kasan Tchadian ne.

Wata k’atuwar rumfar shan iska mai d’auke kyawawan kujero, gefenta, babbar rumfar ajiyar motoci, manyan motocine kala² na kece raina, ajere har gudu 10 cif acikin rumfar.

Wasu motocine gudu biyu jibga-jibga d’aya fara tass d’aya bak’a sud’ik, guda biyu, an fito dasu ana gogewa, security’s nata zagaya wajan motocin rik’e da bindigogi ahannunsa, sai kai komo suke suna bubbud’e hanci.

Matashiyar budurwa ce sabon jini, ‘yar kimanin shekaru 18 aduniya.

Tsaye jikin k’ofar bedroom d’inta wacce tsayawa baiyana kyawun d’akin nata da dukiyar da aka kashe mata wajan makwancinta da abubuwan more rayuwata, b’ata lokacine, duk da ta kasance ba k’asar take karatu ba.

Sanye take da abaya mai taushi blue colour, mai adon duwatsu masu matuk’ar tsad’a farare tass. Ta yane kanta da d’an kwalin abayar, wacce ta zauna jikinta cif Ma sha Allah.

Jelar gashinta mai tsayi ta zubo har gadon bayanta.

Sam ita ko sanyin da akeyi bata ji, sabida ta wadatu da na’urorin d’umama d’aki a bedroom d’inta, haka ita d’in mai son sanyi ce sosai, yanzu abin sanyi data sauka ta sha ta kasa bacci sabida yunwa.

Ahankali ta fara taka matattakalar banin cike da nutsuwa, domin saukowa beni na d’aya, (Kasancewar ita a hawa na 2 ta ke.)

Wata irin tafiya take wacce ta sanya dukkan jikinta motsawa, tamkar tarwad’a, sai k’ananun pinky labb’anta take motsawa tana d’an lasarsu, k’ananun fararen shanyayyun idanunta ta ke d’an lumshewa tana bud’ewa wayace *iPhone 13 pro max*.

Kallo d’aya zaka mata kasan ruwa biyu ce, sai dai akallon farko zaka san ita d’in jinin larabawace, sabida yawan tulin gashinta, ga dogon siririn hancinta zuwat amik’e, bakinta d’an k’arami mai taushi kalar pinky, tana da gashin ido gazar² masu tsayi da gashin gira mai kyau idanunta ‘yan k’ananu ne tamkar tana jin bacci farare tass, tana da gashi har tsakiyar bayanta, fatarta kwance luwai ga taushi kyakkayawace, amman ba irin mugun kyau can-can ba, sai dai fa itad’in cikakkar macace duk da kuwa k’arancin shekarunta, Allah ya k’erata Masha Allah, ita d’in ma’abuciyar son k’amshi ce, yanayin fatarta irin ta ruwa biyu ce, ita bata cika fararen mata tass ba, haka ita kuma ta fi chocolate hasken fata.

Doguwace amman ba can ba, sabida d’an kaurinta kad’an ya b’oye asalin tsawonta, tanada matsagai cin jiki, mai d’aukar hankalin duk wani namiji mai lafiya. K’irjinta cike yake da dukiyar fulani tsayayyu masu kyau.

Tana da hips mai d’aukar hankali haka Masha Allah bom-bom d’inta tamkar na manyan mata suke masu ‘dan girma ba can-can ba, batada dimples haka batada wushirya, amman hak’oranta k’ananu farare tass ajere cases.

tana da sanyin hali bata fiye mgna ba sam bata shiga abinda bai dameta ba, miskilace sosai, amman tanada kirki da tausayi, ga kyauta.

Halinta dai na rashin son mgna ko hayaniya, sai ku wuni da ita bata ce maka k’alaba, hirata Abie d’inta ne, dan ko da Raiyana matar Abie, basu fiye mgna ba, duk da kuwa yadda take sonta amman sam ta kasa sakin jiki da ita. Dan ko Jaddatu Rahamu bata fiye mata surutu ba, sai idan ta yi abin dariya kasancewar Jaddatu Rahamu mafad’aciya ce ta k’arshe.

Dab da zata k’arasa saukowa beni na d’aya jikin k’ofar Abienta, ta taji muryan Ammi Raiyana tana ruwan masifa.

Da sassarfa ta k’araso jikin k’ofar bedroom d’in ta tsaya, da niyar bud’ewa ta shiga dan zaton ko Latifa ta saka aiki gyara b’angaran Abie ta mata shirme.

Wata irin tsinkewa taji zuciyarta tayi, sakammakon tsinto mgnar Raiyana da tai tana fad’a masa bak’ak’en maganganun da taji karaf akunnenta, ta fad’awa mahaifin nata mafi soyuwa azuciyarta.

Jikinta rawa ya soma, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu uku².

Ta dafe setin zuciyar tata, da sauri ta runtse k’ananun kyawawan idanunta wanda suka fara rikid’ewa sukayi jajir, sabida mummunan b’acin ran da ya ziyarci zuciyarta.

Wani irin wahalallan numfashi taja da k’arfin gaske, kafin ta shiga sauke shi da sauri² ajere² kamar tayi gudun tsere, yayin da dukkan jikinta yake tsuma.

Wani irin abu taji na yawo adukkan sansan ajikinta kamar tsutsotsi.

Yayin da take wani irin fitinannan sanyi ya kawoma jikinta farmaki, wanda ta soma game jikinta waje d’aya, sabida k’ark’ashin tafukan k’afafunta da tafukan hannunta suka d’auki wani irin mugu-mugun sanyi, take ji wanda yake ratsa dukkan k’ofufun mahudar gashin jikinta baki d’aya, har ya kai tana had’e hak’oranta waje d’aya.

Wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke yayin da take ciza k’ananun pinky lips d’inta masu taushin gaske.

Ta runtse k’ananun shanyayyun idanunta, ta sanya dukkan tafukan hannunta ta toshe kunnuwanta, tana fizgo numfashinta da ya ke kai komo, ta bud’e idanun nata taja k’afafunta dakyar ta koma sama, tana mai jin mugun tsanar Ammi Raiyana.

 

Dattijo ne farin balarabe dogo mai matsagaicin jiki, d’an kimanin shekaru 50 cif aduniya, amman tsabar jin dad’i zaka d’auka bai fice shekaru 45 ba.

Kyakkyawan gaske ne ma’abucin fara’a, yana d’auke da doguwar fuska mai zagaye da k’asumba da saja da wani gemu mai tsayi kyau wanda yake shan gyara, yanada yalwa gashin jiki sosai,yanada dara-daran idanu masu haske wanda k’wayar idanunsa golden ne, idanunsa nada wata irin baiwa acikinsu, wanda da zaran kun had’a idanu sai kaji shakkarsa, dan ko Raiyana da ta gama masa tijara ba ido cikin ido take masa rashin kunya ba.

Yanada gashin idanu masu kyau haka girasa mai kyau labb’ansa jajadattakza Rahama irin labb’ansa ta d’auko, sai dai nata pinky ne nashi jajaye masu taushi da shek’in jin dad’i.

Yanada dogon hancin da doguwar hab’a hak’oransa farare ajere reras yanada wushirya ta k’asa yanada dimple d’aya mai lob’awa sosai ko mgna yake lob’awa yake bare yay murmushi dan bai fiye yawan dariya amman murmushi bayada ruwansa.

Tsaye yake a gaban wani tafkeken dressing mirror yana sanye da tsadaddun manyan kaya na alfarma na kece raini, yalwatacciyar suman kansa ta sha gyara sai shek’i take, yana fesa wani shu’umin tsadaddan turare mai azabar sanyin k’amshi.

Waya yake cike da nutsuwarsa da dattakunsa cikin harshen larabci, yana sakin murmushi tamkar ba yanzu aka gama gasa masa mgna ba, gefen fuskarshi dimple d’insa na lob’awa.

Daga bathroom ta fito, farace siririya ita ba gajeraba ita ba doguwaba, kana kallonta kasan shuwa Arab ce, sabida gashinta har gadon bayanta, zatakai shekaru 32 a haife.

Manyan Idanunta wanda suke cike da wutar sha’awarsa ta tsira masa tana jin kamar ta rungumeshi, amman kwarjininsa ya hanata.

“Malam ina mgna kaji.â€

Ta k’arashe mgnar tana rik’e k’ugunta Juyowa yay fuskar shi atsuke ba fara’a cikin zazzak’ar murya shi ya ce“Ok zan zagaya asibitoci ne idan na dawo zamuyi mgna karka damu yallab’ai Nga sosai bye.â€

Ya tsinke kiran ya jefa wayarsa irinta Rahma aljihun gaban rigarsa ya nunata da yatsa ya ce“Ni kika fad’ama mgna irin wannan mai d’aci? Kinci darajar masu daraja Raiyana, banawa mutum gori amman ya na aureki? Kema baki fi sauran matan ba, duk wacce bata cika sharud’ana ba ta kuma ci jarabawata ba zata tab’a samu naba, har abadan sabida kun farkar dani daga bacci kun d’and’anamin azaba, darajar mahaifiyata kawai ta saka nake zaune dake, ashe kema mage ce mai kwanciyar d’aukan rai. (Na Sajida niger) .

“Good bazan sake ki ba sabida inada kima da daraja Wa idanun al’ummah kici gaba da zama kici arzik’i iya cinki, amman ki kiyaye harshenki.

Fita ban waje jeki d’akinki.“

Ya k’arashe mgnar yana nunata da yatsarsa.

Raiyana ta kauda kanta daga kallomsa sabida wani irin sonsa da yake azalzalar zuciyarta, ta ce“Wallahi nima dab nake da fad’awa duniya tasan kai waye. Kuma wajan Rahma d’iyarka wacce kafi so,zanje na mata bayani…â€

Fincikota yay cikin wani irin zafin nama, abinka da k’aefafan namijj, duk da kuwa an kwana biyu, amman k’arfinsa na nan.

Ihu ta saki sabida azaba yadda k’asusuwanta suka amsa.

Ya d’aga hannunsa zai mareta ya fasa, ya hankad’ata gefe.

sabida ba halinsa bane dukkan mata, dan duk tarin matan da ya yi bai tab’a dukan kowaba.

Tsawa ya daka mata

“Barmin d’akina idan kika sake shigowa ba tare da izini na ba, kiyi kuka da kanki bani ba.â€

Ya k’arashe mgnar yana dafe kansa da yake barazanar tarwatsewa.

Cike da mugun shakkarsa taja k’afafunta ta fice tana rufo masa k’ofar da k’arfi, tana tsoron hukuncin da zai d’auka dan ba k’aramin so take masa ba, kawai tana masa barazana ne dan ya mata abinda take so, shi kuma kaifi d’ayane.

“Astagfirullah wa’atubu ilak!

Ummu Aymana kin tafi kin barmu da Chakwakiyar duniya ni da Baby Ummina. Ance na auri babbar mace ga tanan na aura ba hankali, ba wayo sai jaraba da son abin duniya, shin wai ta ina zan fara neman matar da zata fahimce ni ta zauna dani tsakani da Allah yadda nake so mu rayu inuwa d’aya cikin aminci? Oh! Ya Rabbi!â€

Ya k’arashe mgnar cikin harshen larabci yana k’arasa shirinsa, ya fesa turaren ya d’auki sauran wayoyinsa

biyun kasancewar waya uku yake anfani da ita, kowace da muhallinta.

Agaggauce ya fito ya murza k’ofar wacce take zallar glass mai duhun gaske key ya nufi wajan Rahma ya ganta dan yasan ba lallai ta tashi ba, kasancewar tazo hutun makaranta har tsawon wata 2 zatayi, kafin ta koma (Espagne). Tinda ta zo yau tsawon kwana 7 kullun cikin baccin hutu take, idan tai breakfast ta koma bacci sai azuhur ta yi sallah ta sauko ta yi lunch, ta zaga cikin gidansun, ko ta fita wajan shak’atawa.

Wani had’add’an falo ne ya tsaru an kashe masa mahaukatan kud’i, wajan had’asa yaji kayan alatu, wasu irin manya kujerune masu zubin na sarauta, sukama falon k’awanya.

Wata farar dattijuwa ce ‘yar kima nin shekaru 67 kallo d’aya zaka mata kasan balarabiya ce, zaune take hakimce, cikin shiga mai kyau, sanye take da rigar sanyi doguwa irin ta ‘yan saudiya, har k’asa irin mai kaurin nan, ta yane kanta da madedecin gyale mai kauri, falon k’amshin turaren wuta da wani irin d’umi mai dad’i da na’uran d’umama d’aki ta d’umama k’aton falon.

Idanunta akan tafkekiyar Tv plasma, tana kallon tashar Aljazeera, cup d’in shayine ahannunta tana kurb’a hannunta d’aya tana jan casbi.

K’aton agogon da yake manne jikin bangon ta d’aga kanta ta ga 11:00 am.

Cup d’in ta ajiye cikin harshen larabci ta Ce.

“Ya Rabbi! Yaron nan me yake har 11 ta yi bai fita zuwa abinda zai k’ara masa kusanci da mahaliccin sa ba!? Ga shi gobe zai wuce zuwa Gabon. Wannan shagwab’abb’iyar d’iyar tasa sai ta farka ta b’ata masa lokaci, tinda naga da safen shayi kawai ta Sha, Rahma bata iya bacci da yunwa.â€

Ta k’arashe mgnar tana kallon hanyar beni, tana kiran.

Latifah!“

Cikin rawar jiki ta k’araso tana zubewa gaban tsohuwar, cikin harshen larabci ta ce.

“Jaddatu Rahamu ga ni Allah yasa ba laifi na yi ba?â€

Idanu ta k’ura mata tana janyo sandarta. Wanda ganin hakan yasa Latifa matsawa can nesa.

“Wlh Latifa cikin harakokin ki akwai munafurci, idan ba haka ba, daga kiranki sai kice kinyi laifi? Kaji munafukar yarinya, kina zaro min jajayen idanu kamar gauta. Jeki d’auko min wayata ad’aki saura ki shiga duba abinda baki ajiye ba, banda Rahma ta nace tuntuni kinbar gidan nan.â€

Latifa tai k’asa da kanta kamar zata fad’in abin arzik’i, sai ta fara mgna da harshen hausa sanin batajin hausar, ta ceâ€Zama daram agidan nan bid’ar kud’i nazo Allah ya datar dani kyayi kya barni munafukar tsohuwa kawai, wlh darajar d’anki mai kirki kike ci, da ina neman kud’in zamu samu muhalinmu na kanmu, da na jima da lakad’a miki duka na gudu, daga baya na rok’i gafara.â€

Latifa ta k’arashe mgnar tana mik’ewa ta nufi hanyar da zata kaita d’akin Jaddatu Rahamu.

Jaddatu Rahamu ta ce“Ke!! Zo nan, me kika ce da hausan?â€

Latifa ta ce“Jaddatu addu’a nai miki.â€

“A’a k’arya kikeyi, jeki aikin na fasa naji ai me kika ce zakimin sata ko? Je ki

kira min Ummin Adnan.â€

Latifa ta rusuna ta ce“Tom an gama Jaddatu.â€

Ta k’arashe mgnar ta fice zuwa kiran Ummi Adnan.

Rahma tana shigowa bedroom d’inta saman wani tamfatsetsan Royal bed mai girman gaske, ta kwanta taja wani irin jibgegen bargo kalar pinky mai taushin gaske, yana fitar da wani irin mahaukacin k’amshi, ta rufe dukkan jikinta, yayin da dogon gashinta ya baje ya rufe mata fuska, ta rungume wata k’atuwar Teddy wacce girmanta ya kusa ita.

Sannu ahankali take kuka mara sauti, cikin shashek’ar kukan ta fara mgna da harshen larabci cikin sansanyar muryata mai dad’i kamar sarewa.

“Ammi Raiyana ashe a idanun duniya kike nunawa Abiena so? Me yasa kika furta masa wannan mgnar wacce nasan ta masa zafi…â€

Jin k’aran bud’e k’ofar ya sanya tai saurin………!

Dattijon Arziki Novel Document txt

File Name   Dattijon Arziki… Hausa Novel Doc.
Title    Dattijon Arziki Complete
Author    Rahma Ladingo
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    04/09/2024
File Size    1000KB
Format Size     TXT
Book Price     500
Phone No    22796515805
Download Dattijon Arziki Novel Document By Rahma Ladingo 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button