Uncategorized

Allahu Akbar: Allah Ya yi wa Sani Garba SK a yau Laraba

Kulli nafsi za ikatul maut, Allah Ya yi wa fitaccen dan wasan finafinan Hausa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba da yammaci a birnin Kano, bayan doguwar jinya da jarumin ya sha.

Abdul Amart mai Kwashewa shi ne ya sanar da rasuwar jarumin.

Shi dai Marigayi Sani Garba SK ya rasu ne a asibitin Muhammadu Abdullahi Wase dage a unguwar Nasarawa cikin birnin Kano, kuma Allah Ya karɓi rayuwar sa a yammacin yau Laraba.

Shi dai Sani Garba SK ya kai kusan shekaru Uku yana jinya a tsaitsaye, sai dai baya-bayan nan ne rashin lafiyar ta taso masa sosai wanda har takai cewa ya shafe tsawon mako biyar yana jinya a Asibiti, a cewar furodusa Amart.

Za Ku Iya Karanta 

✓ Maryam Yahaya bata jin magana wallahi – Datti Assalafy

Furodusan ya cigaba da cewa tun farko cutar ciwon suga ce yake fama da ita, wacce daga bisani ta haifar masa da cututtukan irinsu ciwon ƙoda, hanta da hawan jini.

Yan satittikan da suka wuce dai anyita yaɗa jita-jitar rasuwar Sani Garba SK, inda ya fito ya musanta raɗe-raɗin cikin wani hali wanda ganin halin da yake yasa Jaruma Hadiza Gabon ta ba shi kyautar Naira dubu ɗari biyu da hamsin.

“Marigayin ya rasu ne ana tsakiyar yi masa wankin ƙoda” a cewar Abdul Amart wanda shi ke tsaye yana daukar duk wani nauyin kula da lafiyar Marigayin.

Sani Garba SK dai dan asalin unguwar Dage ne a cikin garin Kano, kuma kafin ya faɗa harkar fina-finai mai yabon Manzon Allah ne a kungiyar Usha’un Nabiyyu.

Furodusan Abdul Amart ya ce “Tuni aka tafi da gawar mamacin gidansa inda za a yi zana’idarsa a gobe Alhamis kamar yadda addini musulunci ya umarta” Muna rokon Allah Ya jiƙansa ya kuma yi masa Rahama Amin

Back to top button