Uncategorized

Facebook, Whatsapp da Instagram suna fuskantar matsala

 An ba da rahoton cewa ba za a iya samun damar hawa Facebook, whatsapp da instagram ba, matsalar dai ta shafi shafi manyan birane na duniya kamar England, France, Italy da America. Matsalar dai ta faru ne tun karfe 11:30 na safiyar yau. Wasu suna ganin matsalar file ce yayin da wasu suke ganin ko masu datsa na’ura ne suka yi hacking din fayil ɗin da ke riƙe da adireshin IP  na Facebook, Instagram da Whatsapp.

 Tun da farko kamfanin ya sanar da bayani game da WhatsApp, yana mai cewa, “Muna sane cewa wasu mutane suna fuskantar matsaloli tare da WhatsApp a halin yanzu.  Amman muna aiki don dawo da abubuwa daidai kamar yadda aka saba.”

 Babban shafin kamfanin Facebook ɗin: Facebook.com yanzu haka yana a rufe.

 Ba a bayyana cikakken bayani game da matsalar da Facebook, whatsapp da instagram ɗin suka samu ba.

Back to top button