Halysaah Page 93 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 93…Calmly Ajay ke driving bayan sun baro masarautar, yana ta sauraron Nenne da tun fitowar su take fadin irin kirkin Mai martaba tana sa masa albarka, shi dai ba abinda yace don kawai gani yake ba a tare su da kyau ba, yasan dai Abbansa zai sake masu kamar yanda ya saba yi ma kowa amma mutanen cikin masarautar will never do so, ita dai Aunty Farida hankalinta na kan wayarta, Sai duk yaji bai ji dadi ba don ya fahimci ko ruwa basu sha ba balle har a basu wani abinci, ko da gangan Aunty zata iya hanasu barin ace ta samu labarin shi ya kawo su gidan, Nenne tace “Toh wai Ina Ahamad din, ko a masarautar ma fa bamu gansa ba” Sai a sannan Ajay yace “Ya je ajiye Baabarsa unguwa” Nenne tace “Allah sarki, iya sarki kawai mu ka samu muka gaisa da, kai ma kaga ko Baabar ka bamu gani ba” Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Ni Mahaifiyata ta rasu” Nenne tace “Allahu Akbar, Allah sarki, Allah ya ji ƙan ta, ya gafarta mata, to ko dai kishiyar baabar taka muka gani za mu fito parlon Mai martaba, wata tana nan ita ba fara ba, sannan tana ɗan da narkeken jiki ba can can ba, tana da matsakaicin tsayi” Ajay yace “Eh…” Nenne tace “Amma dai bata da kirki kwata kwata, saura kadan ta walakanta mu in gaya maka” Ajay ya kalli Nenne ta madubi yace “Ta maku magana ne?” Nenne tace “Ina fa, ina gaisheta ko amsawa bata yi ba ta sha gwala-gwalai, ni na zata ma uwarka ce shi yasa na ja bakina nayi shiru ban gaya maka ba” Ajay yayi shiru, kuma bai yi mamaki ba kwata kwata, after a while yace “Ku yi hakuri, yawanci bata son baƙi dama” Nenne tace “To er sarkin wani gari ce take wannan uban girman kan haka da rashin son talakawa?” Ajay ya ɗan yi murmushi bai dai ce komai ba, sun yi tafiyar kusan minti talatin kiran Mai martaba ya shigo wayarsa, dagawa yayi ya kai kunne tare da sallama, after some seconds yace “Eh muna hanya ne yanxu zan maida su, na zata kun yi sallama ranka shi dade….” After few more seconds ya ajiye wayar ya kalli Nenne yace “Dama baku yi sallama da Sarki ba?” Nenne tace “Cewa yayi a shiga damu a bamu abun sha, da naga ba arziki yasa muka ki bin yarinyar tana nan wata kitiɓir kitiɓir da ita, dama Parida da nasani ba zuwa zata yi ba don bata son rainin wayo” Ajay yace “Ohk, yanxu yake gaya min ai baku yi sallama ba” Nenne tace “Tun da mun gansa ai an wuce wajen kawai, wataran za a sake haduwa in sha Allah” Suna kusa gidan Aunty Murja after 40 Mins ride Ajay ya ajiye wayarsa da yake driving yana dannawa, bayan sun shigo unguwan ya kalli Aunty Farida yace “Mai martaba ya bada sako a baku, na tura a account din Jiddah” Aunty Farida ta ɗan yi shiru, sai kuma tace “To mun gode Allah ya saka da alkhairi” Nenne tace “Wallahi mu ba don ya bamu komai muka je gaishesa ba, banda shi din babba ne ai da nace kawai a maida masa, amma dai babu laifi, don Allah kayi masa godiya in ka koma gida tunda bamu da wata hanyar yi masa godiya” Ajay yace “In sha Allah” Suna shan kwanan gidansu Aunty Murja, Nenne ta fara hango Khaleesat karkashin bishiyar mangwaro dake gaba da gidan Aunty Murja da dogon sanda a hannunta ita da yaran gidansu Aunty Murja tana tsalle tana plucking Mangwaro, tsohon zanin Aunty Murja ta daura sai er karamar Hijab da slippers a kafarta, Nenne taji kunya ya lullubeta ta rike haɓa tace “Kwance fa muka baro ta sheme sheme daxu ba lafiya, yanxu meye wannan take yi cikin ‘ya yan cikinta fisabilillahi?” Khaleesat bata hangosu da wuri ba don da suna shan kwana taga motar zata gudu ta shige gida tun basu karaso ba, sai kawai yara taji suna Nenne Oyoyo bayan sun ga motar, ta juya suka hada ido da Ajay dake kallonta a gaban motar, sai yanxu ya kara tabbatar da ashe yarinya ce er karama sae rashin kunya idan ta samu waje, Tuni Nenne ta sauka daga motar tana kara yi ma Ajay godiya, Khaleesat ta bi bayan Nenne da sauri zata shige cikin gida, Nenne ta hade rai tace “Baki da kai ne, baza ki je ki gaishesa ba tunda kin riga kin kunyata mu, meye hadin ki da bishiyar mangwaro kamar mayya, yanxu da tare muke da Ahamad din shi ma haka zae ganki kamar almajira” Khaleesat ta wani turo baki tace “To haka zan je, ai ba sai na gaishesa ba” Nenne tace “Ina ruwan sa dake idan kin je a hakan? Wannan ai ba sa’an yin ki bane, kina ganin mutum kamili ga nutsuwa wanda magana ma sai ya ga dama, ai ke Ahamad din shi ne dai dai ke shi zai dau ko wani kalar shirmenki da wauta tunda shi faram faram yake, yanxu banda shirme godai godai dake ki shige cikin yara kina tsalle zaki tsinko Mangwaro da kodadden zanin Murja” Khaleesat tace “Wallahi bazan je ba, ai ba wajena ya zo ba” Nenne tace “Ni zaki kunyata? Mutumi ya gan ki kice baza kije ki gaishesa ba dubi yanda yayi ta sintirin zuwa unguwan nan da Ahamad suna zuwa duba ki, sannan ya zo yau ya dauke mu ya kai mu har gaban ubansa yau, ni dai ki rufan asiri ki je ki gaishesa, ai babu dadi haka Khaleesah, dama bai ganki bane wannan daban” Khaleesat ta kalli Aunty Farida dake tsaye jikin motar suna magana da Ajay, can ta fara tafiya zuwa wajen, tana isowa Aunty Farida ta wani kalleta sai kuma tayi ma Ajay sallama ta bi bayan Nenne zuwa cikin gida, Khaleesat ta jingina jikin motar tana kallon wani direction daban, dama tun shekaranjiya take jin haushinsa baya ce mata ya jiki duk ciwon da take ta yi, sai dai kawai ya zo yayi ta kallonta, tada motarsa yayi ita dai bata matsa jiki ba kuma bata kallesa ba, taji yace “Baza ki bar nan ba??” Sai a sannan ta juya ta kallesa, yana kallonta da kyau yace “In kika samu waje ba karamar kazama bace ke, i am telling you this for free….” Ita kanta bata san me yasa ta fara dariya ba kamar warce ake yi ma cakulkuli, reverse ya fara yi ta zaro ido ta koma baya tana kallonsa tace “Buge ni kake son yi?” ko kallonta bai yi ba a haka ya juya ya bar unguwan, kallon kanta tayi daga sama har kasa, sai kuma ta taɓe baki tayi wucewarta cikin gida yara na biye da ita da Mango din da suka tsinko… Da daddare Ajay na zaune parlon Abbansa yana saurarensa kansa a kasa, Mai martaba yace “To amma ku menene dalilin ku na boye min gaskiyar lamarin gaba daya? Ko kai ka basa shawaran kar ya gaya min gaskiya? Sannan duk saboda yana son ya aureta ne duk yayi mata wannan hidima?” Ajay yayi kasa da murya yace “Ko daya Abba, need din fadin gaskiyar ne bai yi arising ba sai yanxu ranka shi dade, taimako kuma kai muka yi kwaikwayo don da haka muka san ka, nasan Jawwad duk abinda yayi mata ba yayi mata bane saboda yana sonta da aure at first, he did all what he did for God sake ba don ya aureta ba, tausayinta ne yayi leading har yaji zai aureta, kuma idan ba auren tayi ba tsohon mijinta will keep on hunting her” Mai martaba yace “Kuma duk zuwa biyun da nayi Amurka tare nake ganin ka da yarinyar a maimakon Jawwad din ae” Ajay ya kallesa, sai kuma ya sauke kansa yace “I helped him with some responsibilities too” Mai martaba yace “Then why were you trying to cover that up? Kace komai shi yayi” Ajay yace “I am not hiding it sir, we were all protecting her from her Ex differently, shi yasa har kake zuwa kake samunta a gidan…” Mai martaba yace “Duk yanda zaka kare kanka you are very good at that Junaid, shi kuma Jawwad always take the Consequences no matter how deep it is for you” Ajay yayi shiru trying to understand what his dad meant, after some seconds Mai martaba yace “Shikenan…. Kai ya batun naka maganar auren?” Ajay yayi shiru bai ce komai ba don shi kansa ya gaji da tsara new excuse kullum, Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace “Karyar taka ta kare kenan?” Ajay dai bai ce komai ba. Ranan laraba Nenne ta gama hada kayanta a er jakar da Aunty Farida ta ara mata don a buhu ta so saka kayan nata tun daga Kano, Nenne na kallon Aunty Farida tace “Kar fa su zo su yi ta jiranmu Parida kiyi da jiki” Ita dai Khaleesat na zaune ta jingina da bango a dakin Aunty Murja idonta yayi jajir saboda kuka, Nenne tace “Ke da naga har kin saba da yaran unguwar, baki bishiyar mangwaro baki bishiyar Amburela ke da yara kuna tsinkar ‘ya yan itatuwa, to me zai dameki don ance ki zauna kiyi sati biyu ayi maki magani ayi maki gyara yanda ya kamata, kin zata gidan sarauta gidan banza ne da za mu bari ki shiga kamar gantalalliya kai tsaye, miliyan biyu sarki ya bada a bamu da Parida amma haka nan na kashe kusan dubu ɗari biyu akan ki ina nema maki taimako saboda Allah, sannan ga gyaran jiki da za ayi maki tunda ba wani lokaci me tsayi aka saka na auren ba, Ina laifina a nan daga abun arziki?? So kike mu kwashe ki mu koma Kano Awdul din ya ji dadin sungume ki mu shiga uku, babu abincin da yaron nan Ahamad bai ajiye maki ba a gidan nan na jin dadin rayuwa, gashi shi da ɗan uwansa suna zuwa ganin ki, har wata panka me tsada ya siya maki saboda zafi da daddare yarinyar nan ke kadai kike saita pankan dai dai inda kike kwanciya mu kuma zafi ya kashe mu, to me kike so da ya wuce haka? Ai gwara tun yanxu ki fara sabawa da zaman Bauchi tunda nan aure zai kawo ki, Kano da zan koma cikin gaggawa duk domin ki ne inje asan shirye shiryen da za ayi na biki tunda ga damin kudi har dubu dari takwas a lalita ta, ki fa ji tsoron Allah Khaleesah” Aunty Farida dai ko kallon Khaleesat bata yi ba don dama a ranta tace bazata sake lallabata ba tunda kamar tunzurata ake kara yi in ana lallabata, ita ai duk tunaninta tun bayan da Abdul ya koya mata rayuwa ta ajiye wani shagwaba da iskanci a gefe ta canza hali, ashe ba haka bane waje ne bata samu ba kukan banzan na nan har yanxu, a haka su Jay suka iso za su kai Nenne da Aunty Farida park, Ba Ajay kadai ba hatta Jay sai da yayi shock da Khaleesat a kofar gidan don tara masu jama’ar anguwan tayi da kuka da ruri a kofar shiga gidansu Aunty Murja ita baza a tafi a bar ta ba, Aunty Murja na aikin lallashinta, Nenne ta dinga kauda kai tana daura gyale a kai tana rufe fuska tsabar kunya, Aunty Farida dama tuni ta shiga mota don bata da lokacinta, Jay dai ya kasa cewa komai don bai san lamarinta ya kai haka ba, can ya kalli Aunty Farida yace “Aunty ko dai kawai ta dauko kayanta ku tafi” Aunty Farida tace “Ai babu inda zata je sai tayi kwanakin da aka ce tayi a gidan nan tunda gidan kanwar Babanta ce” kiris ya rage Ajay bai yi dariya ba a front seat yana kallon Khaleesat, bakin ciki kamar ya kashe Nenne don Khaleesah ta gama kunyatasu gaban surkai, Jay ya bude driver seat ya sauka ya nufeta, tana ganinsa ta bar wajen da sauri alamar bata ma son jin abinda zai ce mata kuma bata fasa rusa kukan da take ba, Nenne ta kalli Ajay cikin sanyin murya tace “Kaga mu yarinyar nan zata kunyata ta tona mana asiri a unguwan mutane ko? Gudun wancan yaron Awdul ya sa fa nace ta zauna nan ko na sati biyu ne shi ne take mana wannan tijara haka kamar mun ajiyeta wajen yankan kai” Ajay dai yayi murmushi kawai ya bude motar ya sauka ya koma driver seat ya zauna, da su Nenne basa wajen tsaf babu abinda zai hanasa korata da dorinar gaban motar, ya danna ma Jay horn alamar ya shigo su wuce, Nenne tace “Madallah, gwara ya kyaleta da halinta ya shigo mu wuce don ba sauraronsa zata yi ba” Da kyar Aunty Murja ta shiga cikin gida da Khaleesat, Jay ya dawo ya bude front seat ya shiga, Nenne tace “Mu bamu san har yanxu bata dena wannan shagwabar ba wallahi, ko kanninta basa mana wannan iskancin mu dai” Duk bayan sati hudu zuwa shidda ake shirya meeting a fadan dake bangaren sarki, wanda kusan kowa na family din ke halartan wannan meeting din barin wa enda ke gari har ma wasu da ba gari suke ba kuma suna da sararin zuwa, tun daga jikoki, ‘ya ya, kanni, yayyi, cousins da dai sauransu, akwai kuma meeting da ake yi bayan wata uku amma ba na kowa da kowa ba, duk meeting din da za ayi Mami bata taɓa halartan ko daya, don ko tana gari bata zaman meeting din, rabonta da zama ayi meeting da ita zai fi shekara goma, sai dai daga baya a gaya mata me aka yi wajen meeting din, duk aka yi mamakin ganinta a wajen ranan, shi kansa Jay was surprise seeing her at the meeting, sai da ta jira aka gama meeting lafiya sannan daga karshe tace tana da magana, Sarki na kallonta ya bata daman magana, Aunty ta gyara zama don duk tare suka shirya komai, Kai tsaye Mami ta fara magana tace “Ranka shi dade, duk da ni dai nasan bani da matsayin da za a sanar min abinda aka zartar kan Jawwad, amma dai na samu labarin har an kai kudin aurensa Kano, to ni duk wannan ba matsalata bace don yawanci duk abinda ya shafesa dama sai an zartar nake sani, to babban abun tambaya a nan shi ne haka aka je neman auren babu bincike kenan ranka shi dade?” Wata cousin sister din Mai martaba wanda duk ta girme ma matan dake zaune gun meeting din cikin fushi tace “Ki kula Fulani da sarki fa kike magana, ya kamata ki tausasa kalamanki ki kuma san abinda ke fitowa bakin ki” Mami ta wani kalleta daga sama har kasa, shi dai Mai martaba kallon Mami kawai yake, Ajay ya kalli Jay dake kallon Maminsa shi ma with shock, Mami ta ci gaba da maganarta babu yabo babu fallasa tace “To idan kuwa haka aka je neman auren yarinyar nan babu bincike ya kamata a koma ayi bincike kasan wacece kake kokarin hada ɗan ɗan uwanka aure da, ni da ya zame min dole tunda ɗa na ne shi nayi iya binciken da zan yi ban ga ta inda aure zai kullu tsakanin Jawwad da yarinyar nan ba, don kuwa shi din ba sa’an aurenta bane ta ko ina….” Bayan kusan minti daya Mai martaba yace “Fulani, no one is in the rightful place to question my decision in this palace, duk abinda na zartar hakan zai kasance in sha Allah, babu me canza hakan har ke da kike mahaifiyar Ahmad….” Mami tace “Kana nufin ka zartar da hukuncin Jawwad ya auri bazawara mara cikakken asali sannan er kananan mutane?” Tsawa Hajiya Shafa’atu da ta fara yi ma Mami magana tun farko a parlon ta sake yi mata tace “Kina cikin hayyacin ki kuwa Fulani? Shi Mai martaban kike furta ma wa ennan kalaman? Menene wannan ya same ki?” Rai bace Mami tace “In dai akan Jawwad ne baza a taɓa samuna cikin hayyacina ba, yau in uban Jawwad na da rai zai yarje ma Jawwad auren bazawara mara asali? Bazawara fa? Anya an duba ma uban Jawwad da ƙasa ta rufe ma ido kuwa? Yau don babu shi a duniya sai ayi ma ɗan sa haka?” Kowa dake zaune a fadan was speechless and shock at Mami’s action banda Aunty, Mami ta ci gaba kanta tsaye babu ko shakka tace “In lamarin gaskiya ne a aura ma Junaid da ko macen auren bashi da ita har yanxu mana, sai Jawwad da kowa yasan da maganarsa da Hadiyah?” Mai martaba ya ɗan yi murmushi, abubuwa da yawa suka sa yake raga ma Mami kuma zai ci gaba da raga mata saboda abubuwan nan, bazai taɓa daukan mataki akan ta ba, with calmness yace “Ai Junaid bai kawo min ita yace yana so ba Fulani, don haka shi Jawwad din da ya ganta yace yana so shi din dai zai aureta ko ki amince ko kar ki amince, idan kuma da inda aka haramta auren bazawara a addininmu Enlighten us” Yana kai wa nan ya mike, Hajiya Shafa’atu ta fara basa hakuri cikin girmamawa tana jero masa kirari, Jay couldn’t believe all what his Mami was saying, he was just shock and weak, Mai martaba na barin fadan Ajay ya mike shi ma zai fita, cikin fushi Aunty da Mami suka hada baki wajen cewa “Munafiki, me mugun nufi, duk kai ka hada wannan tuggun….” Shi dai ko kallon inda suke bai yi ba har ya fita, Mami ta ci gaba tana huci tace “Sai dai in bayan raina ne za a aura ma Jawwad bazawara wallahi, ai in an san wata ba a san wata ba” Tana kai wa nan ita da Aunty suka fice daga fadan, kuma duk wannan abun da Mami tayi bata yarda ko da wasa ta hada ido da Jay ba ko kuma ta kalli inda yake, yi ma tayi kamar bata san yana padan ba.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*07087865788
