Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 50 Complete Novel

*ASM Bk2050*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

……….tana fitowa ta nufi hanyar gate shi kuma Haisam ya nufi Motar shi dake a bakin part d’in dama a bud’e ya barta ya shige yay reverse kafin ya juyata ya nufi hanyar gate d’in a daidai saitin Hajiya ya tsaya ya sauke glass yace mata ta shigo, banza tay mashi tana cigaba da dogara sandar ta ganin haka yasa shi bud’e Motar ya fito ya sha gabanta tay mashi wani kallo kafin tace ya jaye ya bata wuri kawae sai ya kama hannunta ya nufi Motar da ita tana ya k’yaleta amman yak’i sakin ta har saida ya bud’e kopar baya ta shiga sannan ya koma gaban ya shige tuni Officer ya zuge mashi gate ya fice yabi Motar da kallo a ran shi yana tunanin ko lafiya, A daidai gaban gidan su ya parker da sauri ya fito ya bud’e ma Hajiya kopar bayan ta zuro sandar ta kafin ta fito ya maida duka kopopin ya rufe suka nufi gidan tana gaba yana biye da ita Amadu dake cikin shago yana ganin su ya bud’e ya fito yazo gaban Hajiya ya gaishe da ita ta amsa mashi kafin ta tambaye shi Dijen na ciki yace eh ta wuce ya k’ara gaishe da Haisam ya jinjina mashi kai kawae, bin su da ido Amadu yay lokaci guda hankalin shi ya tashi don ya fahimci akwae abunda ke faruwa tun ma d’azun da Haisam d’in ya zo neman Fatuu Addu’ar Allah yasa dae lafiya yay kafin jiki a sanyaye ya koma cikin shagon, suna shiga zauren gidan Haisam yaja ya tsaya Hajiya har ta shiga ciki ta juyo ganin bai shigo ba yasa ta tamke fuska tace “Wato ka d’auke ni mutuniyar banza ko ni ce zan shiga in sanar da aika aikar da kayi?” Yana kallonta yace “No just to ask for permission first” wata uwar harara ta zabga mashi tace “kai a tunanin ka yanzu kana da wata kamala ne wanda ya aikata abunda ka aikata ai bai buk’atar a bashi izinin shiga gidan mutane ba kamar Mutanen da ya za6i zubar ma da Mutunci ka shigo muje” wani kallo yake mata ya d’an girgiza kai yay mata alamar suje da hannu ta juya lokacin ta fara yin sallama saida tayi sau biyu sannan gwaggon ta amsa ta lek’o don ganin waye koda ta gansu da sauri ta k’arasa fitowa tana washe baki jikinta sanye da riga umbrella da zani na atamfa ta d’aura kallabi nufo su tay tana masu maraba Hajiya dake bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki yasa nan da nan tausayinta ya mamaye zuciyar ta don ta tabbatar da ta san abun da ke tafe da su to tabbas manta yadda ake dariya ma zata yi balle har tayi, gaida Hajiyar tay ta amsa mata tana kokarin daidaita natsuwar ta ta kalli Haisam still da fara’a tace “d’ana Haisam barka da juma’a ya k’arfin jikin?” Slowly ya amsa mata da Alhamdulillah Hajiya ta kya6e baki tana girgiza kai gwaggon tace su shigo cikin parlor, bayan sun shiga a kan one seater Haisam ya zauna Hajiya ta nufi 3 seater gwaggo kuma ta zauna akan 2 seater ta shiga k’ara gaida Hajiyar tana mata barka da juma’a ta amsa fuska a kwa6e shi kam Haisam tunda ya zauna ya sadda kan shi k’asa, shiru duk suka yi gwaggo sai d’an murmushi take sai dae a cikin ranta ta lura kaman akwae abunda ke faruwa ba kamar Hajiya data gani ba ko mayafi saida aka d’an d’auki lokaci sannan Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Gwaggo ta fara magana “Dije gamu mun zo saidae ba irin zuwan da aka saba bane zuwa ne mara dad’i mun zo maki da Al’amari wanda ban tunanin ya ta6a faruwa a kaf dangin ku….” Dakatawa tay sakamakon kukan da ya taho mata nan fa hankalin gwaggo ya tashi haik’am ba kamar da ta ga Hajiyar na kuka ga Haisam ya sadda kai baida alamar d’agowa bare tasa ran jin bayani daga gare shi a rud’e ta hau ba Hajiya hak’ura tana had’ata da Allah ta daina kuka k’arshe ma sai ta tashi ta koma kusa da ita tasa hannu tana goge mata kwallan tana cigaba da bata hakurin can ta shanye kukan tace “Dije nasan ki ke mace ce mai tsananin k’arfin hali ba k’aramin abu bane ke ta6a maki zuciya don Allah ina rok’on ki da ki k’ara kan wanda ke gare ki don Al’amarin da muka zo da shi zai iya tarwatsa maki zuciya wllh ni kaina da nake maki Maganar nan tuni zuciyar tawa ta tarwatsa Allah ne kawae ke bani iko nake yin komae” tuni jikin gwaggo ya fara rawa duk ta bi ta rud’e a kidi’me ta hau ce ma Hajiyar to tana ji in sha Allahu ba abunda zai faru da ita ta sanar mata abunda ke faruwa cigaba Hajiya tay “Dije kin san duk inda ake zaman lafiya Shaid’an bai da sukuni har sai yaga ya tarwatsa ni dake zumunci ne mai k’arfi a tsakanin mu tsawon lokaci Saboda dage wa da Addu’oi da su Azkhar yasa tsawon lokaci bai yi nasara akan mu ba sai yanzu, dije sai yanzu…..” Share k’walla taci gaba da yi hankalin gwaggo in yayi dubu ya gama tashi a lokacin ta rasa ma hasashen da zata yi kan abunda ke faruwa ganin Hajiyan tak’i fad’a mata abunda ke faruwa yasa ta juya kan Haisam tace “d’ana Haisam don Allah ka sanar dani abunda ke faruwa in sha Allahu zan fahimta ai ni musulma ce….” Tun kan ta k’arasa Hajiya ta katse ta da Fad’in “k’yale wannan Dije dashi shaid’an yay amfani yayi galaba yake son ganin ya tarwatsa mana farinciki zan sanar maki abunda ke faruwa amman ina rok’on ki da girman Allah ki fahimce ni” da sauri gwaggo ta hau jinjina mata kai alamar zata fahimtan Hajiya tace mata ina Fateema gwaggon tace mata bata kai ga dawowa ba har yanzu amman dae yau zata dawo Hajiyar tace mata ta kirata a waya yanzu ta ce mata duk abunda take ta bari ta taho gida da sauri baiwar Allah gwaggo ta mik’e ta nufi hanyar fita tana Fad’in bari ta d’aukko wayar to, bada jimawa ba ta dawo hannunta ruk’e da wayar ta fara kiran Fatuu ba tare da ta koma ta zauna ba saidai har ta yanke bata d’aga ba wasa wasa sai da ta kirata sau kusan goma amman ba’a d’aga ba Hajiya dake ta kallonta tace “halan tak’i d’agawa?” Kai gwaggo ta d’aga mata ta girgiza kai tace “dole ta k’i d’agawa don itama tana cikin tashin hankali” a razane gwaggo dake kallon ta tace “kodae wani abu ya faru da Fatun ne ko tayi had’ari ne, don Allah Hajiya ki sanar man!” ganin yadda ta rud’e yasa Hajiyar kwantar da murya ta na kokarin fahimtar da ita ba abunda take tunani bane ya same ta kawai dae akwai dalilin da ya sa ba lalle ta d’aga kiran ba, ta nuna mata lalle dole sai Fatun tazo zata ji abunda ke faruwa gwaggon tace to yanzu ya za’ai gashi ta k’i ta d’aga kiran, tambayar ta Hajiya tay ko tasan d’akin da Fatun take a can Makarantar tace a’a ta dai san Hostel d’in amman bata san d’akin su ba tunda bata ta6a zuwa ba Hajiyar ta sake tambayar ta bata san wata k’awar Fatun ba ta kirata tace ta sani amman bata da lambar wayar ta don duk in zasu gaisa da wayar Fatun suke gaisawa, shiru kowa yayi gwaggo dai na tsaye k’ik’am can Hajiya tace “ina ga tashi zamu yi mu tafi Makarantar tasu kawae alabashshi sai mu nemi d’akin nasu in mun je” shiru gwaggo tay fuskarta duk ta canza an barta a duhu sai faman sak’e sak’e take a ranta can tace ma Hajiyar “ina tunanin Amadu bai rasa lambar k’awar tata bari in mashi magana” da sauri Hajiya tace to taje taji in akwai ta juya har tana yin tuntu6e wurin fita daga parlon Hajiya na ta bi a sannu, bayan fitar ta ta maida idonta akan Haisam da still kan shi na sadde ta hau jefa mashi wani mugun kallo fuska a kwa6e, Saboda tsabar rud’ewa a yadda take ba lullu6i babu itama ta fita har bakin shagon Amadu yana ganinta ya bud’e ya fito ya hau tambayar ta lafiya ba kamar yadda yaga yanayin fuskarta murya na rawa tace “ban san abunda ke faruwa ba Amadu amman dai gaskiya da matsala gashi sun k’i sanar dani abunda ke faruwa wai sai Fatuu ta zo Hajiya harda kuka fa gashi anata kiranta a waya tak’i d’agawa” zaro ido Amadu yay ba kamar daya ji tace Hajiya harda kuka yama rasa mi zai ce Gwaggon ce ta tambaye shi ko yana da lambar Fauziyya da sauri yace “eh akwae Fatuu na kira na da ita” tace to ina wayar ya d’aukko mata ita yace to had’i da juyawa da sauri ya koma cikin shagon without wasting time ya dawo ruk’e da wayar ya fara kokarin kiran Fauzy………,

 

Tun bayan da ta yi mata allurar ta haye saman gadon ta ta jingina da bango duk ta takure a guri d’aya har yanzu jikinta rawa yake d’an yi Saboda zullumin abunda zaije ya dawo idanunta akan Fatuu dake kwance akan gadonta ta rufe ido bacci ne ya kwashe ta tana cikin jiran tsammani bayan da aka mata allurar, duk in tayi motsi sai gaban Fauzy ya fad’i daramm! Tana haka wayarta dake gefe ta fara ringing da sauri ta kalle ta kafin ta kai hannu ta d’aukko lokacin da tay arba da sunan Uncle Ahmad kamar yadda tay saving no d’in shi har saida gabanta ya fad’i tabi kiran da kallo har ya kusa yankewa kafin hannu na rawa tay picking yana jin ta d’aga da sauri ya mik’a ma gwaggo wayar ta karata a kunne ta rafka sallama wani irin rassss Fauzy taji murya na rawa ta gaishe da ita ko amsawa gwaggo bata yi ba ta jefa mata tambayar suna tare da Fatuu ne da sauri tace mata eh gata nan kwance tana bacci gwaggon tace “wani abu ya samu wayarta ne inata kira bata d’aga ba kema kuma baki d’aga mata ba?” A rud’e Fauzy tace “a….a’a banji kiran ba k’ilan ko wayar bata a tare da ita don ban ganta ba tun d’azun”

 

“To ki tasheta ki bata wayar taki ina son magana ne da ita” Fauzy ta amsa da to da sauri tana k’ok’arin sauka daga kan gadonta ta nufi Fatuu ta sunkuya ta kai hannu tana tashin ta a hankali ta bud’e idanunta da sauri don kada ta fad’i wani abun Fauzy ta kanga mata wayar a kunne tace “gwaggo ce ke son magana da ke kiyi magana” waro ido Fatuu tay saida ta had’iya miyau Kutt kafin tayi sallama gwaggon bata amsa mata sallamar ba tace “ina kika jefa wayar ki ne anata kira tana shiga amman ba’a d’agawa?” Kikkafta ido ta fara yi a d’an razane jin yanayin voice d’in gwaggon tace mata wayar na a silent ne shiyasa ita kuma bacci ya d’auketa cike da bada umarni tace “to duk abunda kike yi ki bari yanzu yanzun nan ki taho gida ina jiran ki” zaro ido Fatuu tay sosae gabanta ya hau fad’uwa cikin inda inda tace “s..sai anjima da daddare zan taho gwaggo zamu yi wani group……” Bata samu damar k’arasawa ba sakamakon tsawar da gwaggon tayi mata tace yanzu take son ta taho ba sai anjima ba da sauri Fatun tace mata to gata nan tahowa daga haka ta kashe kiran, kallon Fauzy Fatuu tay idanu waje itama kallon nata take a d’an kid’ime ta tambaye ta abunda ke faruwa Fatun ta yarfa hannu tace “nima ban sani ba tace dai komi nake yi in bari in tafi gida yanzu gashi a muryar ta kaman akwae alamun tashin hankali” wani kuka cikin Fauzy yay tace “to kodae tasan da Maganar cikin ne?” tay Maganar hannunta guda ruk’e da ha6arta Fatuu dake kallonta tace “taya za’ai ta sani baccin daga ni sai ke muka sani….” da sauri Fauzy tace “sai kuma Ya Haisam ba” wani kallo Fatun tay mata tace “kina nufin shi zaije ya gaya mata?” Fauzy tace “Eh mana shiyasa nace da kin d’auki kiran shi kin ji mi zai ce maki yana iya yin tunanin kar kije ki samu matsala wurin yin abortion d’in ya yanke gwara yaje ya gaya ma gwaggon” wani kallon anya kina da hankali Fatun ke bin Fauzy dashi tace “Saboda tsabar baida hankali ya aikata man hakan sannan yaje ya fad’i mata haba da Allah kema Fauzy ai baya ma fara ba wllh k’ilan dae akwae abunda ya faru kawae ba wannan ba” uhmm kawai Fauzyn tace,

 

“Ni tsoro na ma kada sai ina gidan cikin ya zube tunda har yanzu shiru, koda yake tunda ba wani babba bane nasan ba wani jini zan zubda ba in sha Allahu in ma ta fuskanci wani abu sai in ce mata period d’ina ne ya zo yau” tana k’arasawa tay d’an murmushin jin dad’in samun mafita ta mik’e Fauzy dae nata bin ta da ido gaba d’aya a tsorace take, bayan ta had’a duk abunda zata d’auka a jakar goyonta ta yafa mayafin jallabiyar jikinta tace ma Fauzy ta tafi jiki a mace tace bari ta rakata ta hau Napep, bayan sun fito daga Hostel d’in sun nufi gate Fatuu ke tambayar ta sai yaushe zata tafi weekend d’in Fauzyn tace sai d’an anjima bayan Magrib in ta gama kimtsawa, bayan sun fito suka samu Keke Napep Fatun ta shige Fauzy tace mata duk abunda ake ciki don Allah ta kirata don a tsorace take wllh Fatun tace ta kwantar da hankalin ta in sha Allahu ba game da wannan abun bane ta d’aga mata kai kawae suka tafi Fauzy ta juyo sukuku da ita ta koma Hostel,

 

lokacin da suka iso layin gidan nasu tun kafin su tsaya a kopar gidan ta hango Motar Haisam dake fake wani irin bugu k’irjinta ya shiga yi har Mai Napep d’in ya tsaya a gaban Motar ta fito da tsananin mamaki take kallon Motar, bayan ta biya shi ta juya suka had’a ido da Kawu Amadu dake kallonta ta cikin shago nan da nan ta sha jinin jikinta da k’yar ta d’aga k’afarta ta nufi wurin shi ta tsaya a gaban Shagon ta gaishe da shi duk ta kame kanta ya amsa yanata kallonta don shi kan shi ya lura da canzawar da tayi kafin yace mata ta shiga gwaggo na jiranta, a kid’ime ta tambaye shi Ya Haisam na ciki ne yace mata eh tay jimm kaman bazata wuce ba har saida yay mata magana sannan ta nufi hanyar shiga gidan k’irjin ta tamkar ana mata luguden ta6are kanta ya gama d’aurewa ta tabbata dae Ya Haisam d’in zuwa yay gidan su ya fad’a, tunanin abunda yazo yace ta shiga yi ba kamar yadda taji gwaggon na mata Magana da ta kira waya “ba dai kaina aka d’aura laifin ba!!!” ta raya a cikin zuciyar ta, lokacin data shiga zauren gidan d’an jimm tay kaman bazata shiga ba can dae ta shiga cike da fargaba ta nufi Parlor ganin takalman su anan tana zuwa bakin kopar parlon taja ta tsaya ido waje ganin Hajiya a zaune ita bata ma ganta ba saida gwaggo tace mata ta shigo ciki sannan Hajiyar ta juya ta kalleta, a d’arare ta shiga ta k’ara togewa a bakin kopar tana ta zare ido wani irin kallo gwaggo ke bin ta da shi Lokaci guda jikinta yay lakwas don ko ba’a fad’a mata ba ta gane mike faruwa da Fatun Hajiya ce ta nuna mata gefenta tace tazo ta zauna ta nufi wurin jikinta tamkar ana zare mata lakka, bayan ta zauna murya na rawa ta gaishe da ita kafin ta d’an saci kallon Haisam da idanun shi ke akan Carpet itama ta sunkuyar da kan nata tana kallon yatsun hannunta dake yin rawa ji take inama ta 6ace bat daga wurin Hajiya ce ta katse shirun da fad’in “Dije ga Fateema ta zo yanzu zan sanar dake abunda ke faruwa amman kaman yadda na rok’e ki kafin yanzu ina sake rok’on ki don girman Allah kiyi hakuri kiyi hakuri dije duk da wannan yayi kad’an ya hana zuciyar ki girgiza amman dai ina rok’on ki kar ki tashi hankalin ki sosae ta yarda zaki cutu don aikin gama ya riga da ya gama sai ayi tunanin mafita kawae tunda ko an tashi hankalin ba abunda zai canza….” d’agowa gwaggo tay ta kalli Hajiyar fuska a kwa6e ta jinjina mata kai kawae, d’an jimm Hajiya tay ita kanta bazata iya tuna ranar da taji fargabar sanar da wani abu irin yau ba gani take kamar zuciyar gwaggo zata iya bugawa ita kanta Fatuu tuni kwalla sun fara gangaro mata tasa hannu ta rufe bakinta ji take kamar kar a sanar ma da gwaggon don in dai wani abu ya sameta to bazata ta6a yafe na kan ta da kuma Haisam ba, sosae kuma tay mamakin k’arfin halin shi da har ya iya zuwa ya sanar da abu irin wannan, jin Hajiyar tak’i cigaba yasa gwaggo ce mata karta ji komae ta sanar mata kawae ita ai musulma ce ta yarda da k’addara mai kyau da kuma Maras kyau jin haka yasa Hajiya d’an gyara zama ido cike da k’walla tace “Dije Fateema dai…..CIKI ne da ita, kuma ba kowa ne yay mata ba sai wannan k’aton kawai d’in da bai dubi girman zumunci ba bai dubi girman yarda ba ya iya cin Amana har haka ta hanyar biye ma son zuciya….” Fashewa tay da matsanancin kuka Fatuu ma haka ita kuwa Gwaggo ta sadda kanta ta yadda bazaka iya gane halin da take ciki ba can Hajiya ta d’ago taci gaba “Don girman Allah dije kiyi hak’uri a taru a rufa ma juna Asiri tunda abun nan duk na gida ne iya cuta dae nasan an cuceku shiyasa ma ake baku hakuri…….” kallabin ta ta kwanto taci gaba da share hawaye da shi, duk da kasancewar ta tsufa kan cike yake da gashi wanda rabin shi duk hurhura ce anyi mata kitso all back, duk abun nan sai yanzu Haisam ya d’ago da kan shi ya kalli Hajiya kafin ya maida idon kan Fatuu da sadda kai tana ta kuka slowly ya maido kallon kan Gwaggo cikin sa’a ta d’ago da fuskarta suka had’a ido d’an jinjina mata kai yay had’i da d’an lumshe ido kafin ya mayar da kallon k’asa nan take ta fahimci abunda yake nufi, d’agowa Hajiya tay ta kalli Fatuu dake ta kuka tace “Fateema ya akai kika biye mashi, ki ka bari ya cutar da ke har haka keda nike ganin ki mai hankali da wayau baki tunanin ke zaki fi cutuwa ba a matsayin ki na yarinyar budurwa shi kuwa yayi auren shi!” d’agowa Fatuu tay cikin kuka tace “Wllh Hajiya ba laifi na bane shine yace zan raka shi dinner d’in abokin shi to da muka je bamu dad’e ba muka bar wurin…to da muka taho shine nay fushi Saboda bai bari mun dad’e ba shine ya wuce dani G.r.a bayan ya siya abubuwan ci, koda muka je ni ban so shiga cikin gidan ba hakanan na bi shi…..da muka je wani d’aki nan ma saida na tambaye shi abunda muka zo yi shine yace wai zan k’arasa abunda bai bar ni nayi ba a wurin dinner d’in har nike fushi……to bayan mun ci Abinci tare da shi sai aka kira shi a waya shine ya d’aukko laptop ya fara latsawa da na ga dare yayi sosae nayi mashi magana akan yakamata mu tafi shi…shine yace in bari zai d’an ida wani aiki ne to nan har nace bari in yi salla bayan na gama na koma kan kujera ina kallo sai bacci ya fara d’aukata ina haka na farka nace mashi mu tafi dare yayi sosae yace to ya mik’e nima na mik’e bayan na fita wurin kujeru shima ya tafi ya d’aukko makullin Mota kawae sai aka d’auke da wuta shi…….” Kafin ta k’arasa gwaggo ta daka mata wata irin tsawa tace “DUM HETSI FATUU!!!” a razane Fatuu ta kalli gwaggon haka ma Hajiya da mamaki take kallon gwaggon jin yadda ta daka mata tsawa bayan ita aka cutar idanun gwaggon ne suka ciko da kwalla gani take sam ba’a kyauta ma Haisam ba wannan tonon sililin har ina ya muzanta, cikin harshen fulatanci murya na rawa ta hau yi ma Fatuu Magana tana rufe baki a wani irin zabure Fatuu ta mik’e tana zare ido baki bud’e idonta akan Haisam da still kan shi na k’asa, cikin d’aurewar kai Hajiya tace “a’a Dije, a’a, kada muyi haka dake ya za’a cuci yarinya har haka sannan ki hau daka mata tsawa tamkar itace mai laifi bugunta za’ai kuma a hanata kuka? to mi Haisam d’in yayi maki da har ya shanye ki haka??” rai 6ace take Maganar ita kuwa gwaggon maida kan ta tay k’asa ba alamar zata yi magana Hajiya ta maida idonta kan Fatuu da ke tsaye cike da tashin hankali jikinta sai 6ari yake tace “fad’a man mi tace maki ne Fateema? ba don ma na watsar ba ai nima ina d’an jin fullancin za’a canza harshe a cuci yarinya” sake tambayar Fatuu tay kan ta fad’a mata abunda tace mata a d’imauce Fatun tace “C…cewa cewa tay w…wai shi MIJINA NE!” sakin baki Hajiya tay jin wata magana kamar ta wanda ya sha giya Haisam mijin Fateema ta ina!!! wani kallo Hajiya ke bin gwaggo dashi cikin d’aurewar kai tace “Dije ko dae kema chemicals d’in da Kike amfani dasu a wurin aiki suna bugar da ke ne da har yasa kike magana mara kan gado haka?” d’agowa gwaggo tay fuskarta share share da hawaye ta girgiza kai tace “Hajiya da suna bugar da ni zuwa yanzu ai da ban tunanin za’a same ni da cikakken hankali…..” Da sauri Hajiya ta katse ta tace “ai Maganar da ki kai Dije ta nuna babu cikakken hankali a tare dake kwata kwata Haisam fa kika ce wai mijin Fateema ne Saboda Allah har ki tunanin kina da Hankali? A yaushe aka d’aura masu auren da har mu bamu sani ba???” Shiru gwaggo tay ita kuwa Hajiyar ta kafeta da ido can ta juya ta kalli Haisam da still kan shi na k’asa ganin yadda bai ce komae bane yasa jikin Hajiyar idasa mutuwa don da alamu da gaske ne kenan tunda gashi bai ce komae ba cikin daka tsawa tace masu bazasu yi mata bayani ba ta ya akai Haisam ya auri Fateema?? Had’iye abu gwaggo tay cikin rawar murya tace “tabbas akwae igiyar auren shi ukku akanta hakan ne ma yasa aka fasa auren ta da wanda aka so aura mata bayan munje can ni da Abbas lokacin da ta gudo, saidae ita Kanta bata san da hakan ba Saboda wani dalili Abbas ne zai yi maki bayanin komae” da alama Hajiya mutuwar zaune tay don kuwa idanunta ko kyaftawa basa yi ita kuwa Fatuu jin wannan bayanin na gwaggo ya k’ara jefa ta cikin matsanancin tashin hankali nan take taji mararta ta fara murd’a mata ta kai hannu ta dafeta tana nishi da k’arfi, wani abu mai d’umi taji ya fara zubo mata ta k’afafun ta hannu na rawa ta d’an d’aga jallabiyar nan take idanunta su kai tozali da jinin dake ta zubowa tamkar ana koro shi a razane ta d’ago ta kai idon ta kan Haisam da shima idon shi ke akan jinin dake zubowar shi kadae ya lura da abunda ke faruwa, wani irin jiri ne ya kwasheta ta kai hannu ta dafe goshinta kafin ta tafi gaba d’aya zata kifa cikin zafin nama ya yunk’ura ya isa gareta ya tarbeta ta fad’a jikin shi……….

 

 

Yau akwae yak’i tsakanin team Fatuu da team Haisam🤣 Wllh yan team Haisam kada ku yarda ku bi mashi hakkin shi gurin duk wanda ya zage shi ko ya muzan tashi da munanan kalamai☹️

 

 

 

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268

….

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button