*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na goma sha uku_
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA’ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI… AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE…_
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS… THEY ‘VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED
_____________
………A ɓangaren amarya da ango kuwa kowa ya tashi da mabanbancin yanayi. Ango na cikin farin ciki da nishaɗi, duk da kuwa ya shaida ya kuma tabbatar da amarya fa batako kama ƙafar Khadijahn sa ba. Dan a daren jiya ya tabbatar da zancen nan na mata sun bambanta. Tunda yake da Khadijah bai taɓa ganin tasha wani magani domin gyara jikinta ba yanda yake jin mata nayi, har bincike yasha mata amma bai taɓa cin karo da komai ba. Amma yarinyar nan ALLAH yay mata baiwa ta musamman da shi kaɗaine yasan wannan sirrin. Amarya kam da fushi ta tashi, duk da ango yayi wasan kura da ita tamkar ba ƙaramin yaron data raina ba taji a ranta Abaan ɗinta daban ne. A lokacin data samu kanta a hannun Dafeeq hawaye taitayi, dan gani take taci amanar Abaan ne. Ta jima tana hawayen kafin barci ya saceta. Basu farka ba sai yanzu da hasken rana ya hasko windown ɗakin. Itace ta fara tashi, ta zubama Dafeeq dake barcinsa hankali kwance ido ƙurr tamkar mai son tantance wani abu a jikinsa. Zuwa can kuma taja siririn tsaki tana ƙoƙarin sauka a gadon caraf taji an riƙe mata hannu. Da sauri ta jiyo, sai ko suka haɗa idanu da Dafeeq. Murmushi ya sakar mata ita kuma ta ɗan kauda kanta. Lips ɗinta dake motsi alamar tana son yin magana ya zubama ido, kamar wanda ya gama karantar abinda take son faɗa ya wani fisgota ta dawo baya. Idanunta ta rumtse da ƙarfi, cikin son sassauta fushinta ta ce, “Ranafa tayi, gashi bamuyi sallan asuba ba”.
Bai tanka mata ba, sai ma shigewa jikinta yay da jan bargo ya rufesu yana magana cikin kunnenta a hankali. Idanu ta waro waje tana turesa a jikinta. Amma ko gezau, sai ma abinda yay niyya ya fara aiwatarwa. Tana ji tana gani sai da yay yanda yake so da ita kafin ya kalleta yana dariya cike da shaƙiyanci. “Hajjaju karfa ki manta sadaki na biya”.
Harara ta zabga masa, a zuciyata tana faɗin (kaji ɗan iskan yaro. Ka biya kona biya maka) kamar yasan mi take faɗa, ya wani lakace mata hanci da faɗin, “Duk da fa ke kika bani na biya ni ne dai na biya a idon kowa”.
“Hummm”.
Tace kawai tana mai yunƙurawa ta tashi, da kallo ya bita harta shige toilet. Jin ta rufo ƙofar harda murza key yay wani kalar kwashewa da dariya. Sauka yay a gadon ya jawo handbag ɗinta mai ƙyau sosai. Tsaff ya bincike jakar, babu komai a ciki sai gold nata da ƴan kunne da sarƙa da su awarwaro data sanyo jiya da dare, ya jima yana kallonsu kafin ya wani taune lips ya maida ya ajiye. Da kansa ya gyara gadon, gamawarsa dai-dai tana fitowa. Baiyi magana ba ya shige bayin. Shima dai wankan yay ya fito, bata ɗakin, ta kuma ɗauke handbag ɗinta. Salla ya gabatar, sannan ya jawo hularsa dake ƙarƙashin gado ya shirya ƙuɗaɗen jiya tsaff ya nufi wadrobe ya ajiyesu a ƙasan kayansa. Cikin ƙananun kaya ya shirya. Kai tsaye ƙasa ya sauka yanata bulala ƙamshi, ɗakin da ya jefa Khadijah jiya ya nufa, yasa key ya buɗe…
Tana zaune a inda tai salla har yanzu, gyangyaɗi take ga hawaye sun bushe mata a fuska. Idanu ya zuba mata na tsawon minti ɗaya. Haka kawai yake jin wani iri a ransa mai kama da tausayi. Da kyar ya ture tunanin gefe dan kuwa duk abinda ya shirya bazai fasa ba. Khadijah tana cikin plans ɗinsa akan mallakar Hajiya da komanta, sannan ita kanta Khadijah yay alƙawarin sai yay punishing nata akan baƙin ciki da hassada da kuma maganganun data gaya masa jiya dan nan gaba ta kiyaye. Saboda shi dai yasan wannan yaƙin da zaiyi sai tafi kowa mora ai.
Saukar mari ya saka Khadijah farkawa a gigice. Yanda take shuri yasa Dafeeq daka mata tsawa. Babu shiri ta nutsu, dan harga ALLAH tana tsoron Dafeeq. Saboda tafi kowa sanin baida mutuncin. Gaidashi ta shiga yi jikinta na mazarin rawa. Bai amsa ba, sai harara daya zuba mata ya juya zai bar ɗakin yana bata umarnin ta biyoshi. Sai da ta share hawayenta sannan ta miƙe ta biyoshi, dan tayi alƙawarin matar nan tasa bazata taɓa ganin kukanta ba, yanda ta ƙwace mata Dafeeq da asiri itama zata ƙwato abinta da addu’a. Babu kowa a katafaren falon, sai ƙamshi mai daɗi da sanyin safiya. Wani banzan kallo yama Khadijah da nuna mata wata hanya. “Ga kitchen, ki haɗama amaryata break fast mai ƙyau da daɗi, awa ɗaya na baki. Bake kina da bakin yimin rashin kunya ba, zaki gane kuranki ne”.
Komai batace masa ba ta raɓa ta gefensa ta wuce. Da kallo ya bita ƙasa-ƙasa harta shige, sai kuma ya kalli inda Hajiya take tsaye tamkar sai yanzu ne ya ganta. Kainaat da tun fitowarsu da ga ɗaki itama take sakkowa ƙasa da mamaki take kallon Dafeeq da shima tun fitowar tasu ya ganta amma ya basar. Kamar bazatace komai ba, sai kuma fuska a yamutse ta ce, “Dafeeq wannan fa?”.
Tasowa yay ya kama hannunta, kamar wata ƴar yarinya ya kawota ya zaunar a cikin kujera. Zama yay shima kusa da ita yana wani kwanta mata a jiki. Idanunsa a lumshe yana shinshinar ƙamshinta ya ce, “Uwargida”.
Idanu ta waro sosai, dan duk da tasan matarsa ance mata yarinya ce batai zaton haka sharaf ba sosai. Dan Khadijah nada ƙaramin jiki, sannan bata cika tsayi ba can. Idan ma baka sani ba bazakace takai 19years ba yanzu. Tana kallon fuskarsa sosai ta ce, “Haba Dafeeq. Yaya zaka saka matarka mana girki. Ni fa ban aureka dan ka wulaƙanta matarka ba, fatana ma mu haɗe kai mu zauna lafiya”.
“Nima burina kenan hajjaju, sai dai ta nuna ita ba haka take buƙata ba. Jiya ban san munafukin daya kai mata hotonki ba na samu bata gida da yammar nan bayan gama ɗaurin aure. Sai bayan magriba ta dawo bata san zata saman a gida ba. Koda na tambayeta ina taje sai cewa tai gidan Baba Hakimi. Na ƙwace jakarta na duba sai ga ƙulle-ƙullen maganin asiri da hotonki da nawa, wai mu zata kai gidan boka ama asiri yarinyar nan”.
Ruɗewa matuƙa Kainaat tayi, dan duk da tasan itama ta taɓa yima Abaan asiri bada kanta taje wajen bokan ba, Mommyn Nadwa ce ta aiki mai aikinta. Kuma tun daga nan bata sake amsar wani maganin tsubbu ba, wancan ma tayi ne dan bata da mafita akan Abaan. A tsorace sosai ta ce, “Na shiga ukuna ni Kainaat wajen boka kuma? Baby dan ALLAH idan da matsala ka sakan kawai nan da sati guda. ALLAH ina masifar tsoron harka da masu asirin nan”.
Wata dariyar ƙeta Dafeeq yay a ransa, dan Kainaat bata san yasan duk manufarta na auren kisan wuta bane ba. A zahiri kam sai ya gimtse fuska kamar zai yi kuka. “Haba-haba Hajjaju daina wannan batu dan ALLAH. Ai ni da ke mutu ka raba takalmin kaza. Sai dai wata ƙaddara kuma amma bata wannan shashashar ba mara aji. Ki barni da ita zan horata a gidan har sai ta zama baiwarki, kema kuma na baki damar sakata duk aikin da kike so dan ki sallami masu aikin gidan nan suje su huta ita zata cigaba dayin komai”.
“Kana ganin babu wani damuwa baby”. Kansa ya jinjina mata da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke a zahiri. A baɗini kam zuciyarta ce ke tafarfasa. Bata auresa dan shiga sabgar matarsa ba, balle ma wannan cilikowar da ko autan gidansu ya girmeta, ko shi Dafeeq ɗin sai dai suyi sa’anni da autansu balle ita. Amma kuma dolene kafin ta rabu da Dafeeq ta barma yarinyar nan tarihin ruwa ba sa’an kwando bane ba. Har ita zata kai gidan boka. An faɗa mata zama tazoyi ne. Fitowar Khadijah da tray bayan kamar awa ɗaya yasa Kainaat zuba mata ido, a cikin sakanni ta gama tsara gwada Khadijah taga shin da gaske yarinyar kishi take da ita ɗin….
________★
Gwaggo ita ta shigema JJ gaba wajen mahaifiyar Anoosh, dan kuwa mahaifinta ya rasu. Akwai mutunci da girmama juna tsakanin Hajiya Lailah da Gwaggo. Dan Hajiya Lailah na ɗaukar Gwaggo tamkar uwa a anguwa. Bata huɗɗa da kowa sai ita. Jin JJ nada alaƙa da Gwaggo ta bashi damar neman soyayyar Anoosh. Tare da roƙonsa kar yaci amarta. Ya mata alƙawarin da tabbatar mata sai dai ya zamewa Anoosh garkuwa bawai shi ya kutsama mutuncinta ba. Kalamansa sun tasirantu a zuciyar Hajiya Lailah, dan haka taji ta sake yarda da JJ. Dan kuwa dai da fuskar musulinci yaje gabanta.
Anoosh dai ita kaɗai iyayenta suka haifa. Mahaifinta ya rasu tun tana ƴar shekara bakwai a duniya. Mahaifiyarta Hajiya Lailah ta cigaba da kula da ita da bata tarbiyya duk da ta sake aure. Mahaifin Anoosh ya bar dukiya mai yawa, dan haka sabon mijinta yay amfani da wannan damar ya mamaye komai ya gudu. Lokacin Anoosh nada shekara goma. Wannan abu ya ƙona zuciyar Hajiya Lailah matuƙa, gashi bata san a ina zata nemosa ba, dan irin auren nan sukai na ƴan birni, tasan dai sunan garinsu amma bata taɓa zuwa ba shi kuma bai taɓa kaita ba. Gidansa da yake da matarsa zaune kuma sai bayan ya gudu tama san ba nashi bane, ya kwashe iyalan nasa sun gudu tare ashe haya yake. Haka taci kukanta ta haƙura dan ya bar mata takardar saki har uku. Taimakon da ALLAH yay mata sune sarƙoƙinta na gold da bai gani ba, wanda takema ɓoyo na tsiya, su kansu takardun kaddaririnsu ɓoyesu take, amma bata san yanda akai mijin nata ya gano takardun ba ya kwashe. Sarƙoƙin nan ta ɗiba dan hatta gidan da suke ciki ya sayar, ta tattara ƴarta mai lalurar rashin magana suka nufo garin Kano. A motar hayar da suka shigo ta haɗu da Gwaggo dake ta jan Anoosh da hira. Ance mai ɗa wawa, tuni Hajiya Lailah taji ƙaunar Gwaggo ta shigeta. Bayan sun iso Kano kowa ya sauka, Gwaggo tai musu sallama tanayi kamar karta rabu da Anoosh dan yarinyar ta shigar mata rai sosai, ga tausayi. Yarinya ƙyaƙyƙyawa ta gaske amma babu bakin magana. Har Gwaggo ta shiga napep Hajiya Lailah ta dakatar da ita.
“Dan ALLAH Baba idan bazaki damu ba zan so mu biki gidanki”.
Ɗan jimm Gwaggo tai tana kallonta, sai kuma tai murmushi da faɗin, “Karki damu shigo” dan dama ta lura matar na cikin damuwa tun a mota. Sosai Gwaggo ta karramasu, hakama mijinta. Bayan kwana biyu Hajiya Lailah bata ɓoye musu komai ba a kanta. Su Gwaggo sun tausaya mata, sun kuma cigaba da zama da ita a gidan har na tsawon wata bakwai, daga baya aka samu wannan gida dake kusa da su Gwaggo masu gidan zasu tashi sakamakon rasuwar mai gidan Hajiya Lailah ta saida gold nata suka saya. Duk da komawarsu wannan gida akoda yaushe Anoosh na nane da Gwaggo. Anoosh yarinya ce mai haƙuri sosai, bata da yawan hayaniya. Ga yawan murmushi. Duk da kasancewarta bebiya tana karatu, dan a yanzu haka ma jam’i takeyi anan b.u.k tana 100 level, suna gab da shiga 200. Tana da kaifin basira, gata ƙyaƙyƙyawa, duk wanda ya santa ya santane cikin hijjan akoda yaushe. Dan ko’a cikin gida zaka iya samunta da hijjab, sai ma idan Gwaggo ce ta tirsasa mata cirewa tasha iska. Shekararsu ɗaya a anguwar mijin Gwaggo ya rasu, mahaifin MB yaso ta tashi amma taƙi saboda su Anoosh, ga shi kuma gidansu ne sannan bata taɓa haihuwa ba. MB ba zuwa gidan yake ba sai salla-salla. Wani lokacin ma akanyi shekara biyu bai zo ba saboda karatunsa. Kusan yanzun ma hakanne, dan shekararsa biyu kenan rabonsa da gidan shiyyasa bai san batun su Anoosh ba sam.
Sj da su JJ abokan juna ne da suka zama ƴan uwa ma. Dan anguwarsu ɗaya, tare sukai secondary school suka kuma wuce ƴar aduwa University katsina karatu. Akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu, dan tun suna secondary sun iya yaudarar ƴammata. Iyayensu basu taɓa damuwa da abinda sukeyi ba, dan ana kallonsa a shirmen ƙuruciya har suka kammala secondary. Shigarsu JJ jami’a alƙibalarsu ta sauya, dan kuwa sunzo inda babu uwa babu uba babu wani ɗan uwa mai tsawatarwa. Ƙoƙarinsu a aji da iya gayu gasu ƙyawawa ya fara jan hankalin mata garesu, to dama gasu gwanayen yaudara. Tun ana iya yaudarar har suka fara huɗɗa da matan, takai in har zasu koyar da yarinya karatu sai sunyi duk yanda zasuyi sunyi amfani da ita. Tun suna samun irinsu har suka fara hure kunnen salihan yaran mutane. Al’amarin su ya gawurta dan har kawalci sukema malamai. Wannan hali nasu yasasu zama ƴan gaban goshin malamai, dama kuma gasu da ƙoƙarin su. Sun kammala karatunsu lafiya suka baro Katsina ana kewarsu, koda suka dawo gida maimakon abu yay sauƙi saima ya cigaba. Dan kuwa ALLAH ya taimakesu sun samu aiki da taimakon wani lecturer nasu da suka dingama kawalcin students. Duk da aikin ba wani bane koyar da yarane a makarantar boarding babu musu suka amsa. Wannan ma wani lasisi ne na cigaba da lalata yaran mutane a cikin makaranta da wajen makarantar ma, dan in har suka kwallafama yarinya sai sun cimma burinsu a kanta. Sai akai sa’a sunfi samun irinsu lalatattu, wanda suke lalatawa ta yaudara ƙalilanne. A yanzu haka suna shekara ta farko da fara aiki, sun haɗa kuɗi sun sayi mota acewarsu matan sunfi amincewa da mutum idan yana da mota…….✍️
Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 14 Complete Novel
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*