Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 19/20
https://www.facebook.com/groups/1627491150723081/?ref=share_group_link
Masu amfani da face book sai kuyi join wannan group É—in .
_______________”So nake ka tafi da Æ™anwarka can garin naku,dan taimaka mata wajen gano iyayenta na asali”baffa ya faÉ—a yana kallon fattu ,wacce tunda baffa ya fara maganar take jin wani irin matsanancin faÉ—uwar gaba ,ji tayi maganar tasa ta sauÆ™a acikin tsakiyar kanta ,kamar sauÆ™ar aradu,”wace irin magana baffa keyi ne haka” anya kuwa yasan me yake faÉ—i?kai a’a gaskiya bai gane me yake faÉ—i ba shima.
Fattu ta faɗa cikin zuciyarta,tana mai sauƙe ajiyar zuciya ,dan ta fahimci baffa yana nufin innar ta kenan,saidai kuma bata da wani dalilin bin mutumin da bata sanshi ba,Gara tayi zamanta agurin baffanta ,inyaso innar tata inhar ta damu da ita ,zata zo gareta.
Ahankali fattu ta buÉ—e bakinta tace “baffa ina ganin babu buÆ™atar saina bishi wani garin ,dan neman innata,zan zauna anan É—in idan da rabon zamu gana wata rana zata zo gareni baffa”fattu ta Æ™are maganarta cike da mugun bugawar zuciya ,dan har lokacin kalaman baffa na mata yawo akanta.
Ajiyar zuciya baffa ya sauÆ™e cike da alhini abinda zai faÉ—a wa fattun ,kafin yace”ayya fattu amm ki saurareni, da kyau ,ki nutsu ,kuma ki sani kowane bawa da yadda Æ™addararsa ke zuwa masa.
HaÆ™iÆ™a Ni malam bukar bani ne na haife ki ba na tsincekine tun kina yarinya Æ™arama “baffa ya faÉ—i hakan yana mai sunkuyar da kansa cike da tausayin fattu.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un baffa me kake faÉ—i ne haka?dan Allah baffa kayi haÆ™iri idan nayi maka wani laifin ne,amma karka Æ™ara nesanta alaÆ™arka dani, baffa bazan iya jura ba,bansan kowa ba sai kai ,kai kaÉ—ai ne gata na baffa dan Allah karka rabu dani “fattu ta faÉ—a cikin matsanancin kuka marar sauti sosai.
Shide Adeeb kallonsu kawai yake cike da mamaki,how can that be possible ace wai ya tafi da wata yarinya har can ƙasar su ,yace a ina ya samota ?kuma ta yaya ma zai fara neman ahalin yarinyar .shifa gaba ɗayama lamarinsu ɗaure masa kai yake ,basu sanshi ba,ba wata alaƙa atsakaninsu dashi,amma yana ƙoƙarin bashi yarinya ya tafi da ita.
Kallon baffa yayi lokacin dayaji yana magana da cewa”nasan zaki shiga ruÉ—u da damuwa Aduk lokacin da kika sami wannan labarin fattu,saidai bani da yadda zanyi,yazama dole insanar dake gaskiyar abinda ke wakana,kisani fattu ina Æ™aunarki fiye da Æ´aÆ´an dana haifa na cikina dan kin fiyemin su sau dubu.amma son da nake miki bazai sa in cutar dake ba ta hanyar Æ™in faÉ—a miki gaskiya fattu , kisani ahalin yanzu zamanki arugar nan akwai haÉ—ari ,idan mai gari ya farka,kinsan hukuncin da zai zartar akanki bazai mana daÉ—i ba .dan haka kiyi haÆ™uri wllh badan cutarwa yasa nace tafi dake ba,saidan ko da baya nan to nayi niyar barin garin nan dake Dan tseratar da rayuwarki”
Baffa ya faÉ—a hawaye na zubowa daga idanunsa.
Kuka fattu kawai take cike da wani irin baƙin ciki marar misaltuwa, wannan wace irin ƙaddara ce ?yanzu shikenan bata ga tsuntsu bata ga tsarki,baffan da take gani matsayin mahaifinta ashe shima ba mahaifinta bane?kenan ita bata da kowa?tunda ta taso take cikin bakin ciki da damuwa ,amma ta kwance zamanta cikin wannan bakin cikin akan zuwan wannan ranar.kuka take irin wanda yake fitowa kai tsaye daga zuciya ba abinda take fata ahalin yanzu kamar ace ta farka taga ashe barci take ,tayi wannan mummunan mafarkin.to suwaye iyayenta?me tayi musu suka yarda ita?shin basa son tane ko yaya?tambayar da take tayiwa zuciyarta kenan,jikinta kuwa nan da nan ya ɗau ɓari,kan kace me tuni zazzaɓi mai zafi ya kamata.
Ahankali Adeeb ya kalli baffa na tsawon lokaci kafin ya buÉ—e baki cikin salonsa na rashin son magana yace “amma Abba ta yaya zaka bani Æ´arka i tafi da ita ?bayan baka Sanni ba,bakasan koni É—in waye ba ,infact baka saniba ma koniÉ—in mugune ,Amma kake don bani Æ´arka in tafi da ita why?Adeeb ya faÉ—a yana kallon baffa.
Dan murmushi baffa yayi,irin wanda yafi kuka ciwon nan,kafin yace “na yarda da kai nasan bazaka taÉ“a cutar min da fattu ba ,dan tun kana wata halittar wacce ta kasance muguwa kake taimakonta, bare yanzu da kake cikakken mutum.sannan na jima ina addu’a akan Allah ya kawo wanda zai zama silar farin cikin fattu ,sai haka Allah ya kawo ka,alokacin da mu bamuyi tsammani ba,kuma kallo É—aya nayi maka zuciyata ta aminta da kai ,nasan Allah ne ya karÉ“i addu’a ta.dan haka bani da wani kokwanto akanka.” Baffa ta faÉ—a cikin nuna yanayi na gamsuwa akan hukuncin daya yanke.
Ahankali fattu ta rarrafe zuwa kusa da baffa ,hannunsa ta kama ta riÆ™e gamm!cikin nata ,kafin tace “baffa su waye iyayen nawa?me yasa suka yarda Ni?a ina ka tsinceni?ta faÉ—a cikin kuka tana mai jan majina.
Kallon ta Adeeb yayi cike da tausayawa,dan sosai yaji ta bashi tausayi, she’s too young ace ta fuskanci wannan babban Æ™alubalen.
Baffa ne ya fara magana da cewa”kafin na auri hansai na auri wata kanwata,yar gidan tayar babata. Inda muka kasance duka marayune daga i har ita.itace matata ta farko ,minyi aurene irin na haÉ—in zumunci,tana da haÆ™uri da kawaici ,muna zaune cikin aminci da mutunta juna,har Allah ya bata ciki.
Munyi murna sosai da samun wannan cikin ,tare da addu’ar Allah ya sauÆ™eta lafiya.
Wata rana kuwa naƙuda ta kamata,ganin yadda take shan wahala ,saina tafi jeji dan ɗebo mata maganin gargajiya tasha,ina cikin tafiya nayi nisa sosai da rugar nan,kwatsam saina fara jiyo kukan jariri,haka nayi ta bin sautin kukan harna cimma gurin.
Kwance na iskeki kinata kuka gaba ɗaya jikinki yayi ƙura, sannan kin kukkurje dan ga jini jini nan ma ajikin rigar dake jikinki,
Addu’a nayi tare da É—aukoki na dawo gida .
Koda na dawo gida na iske matata tana kuka ga gawar jaririya nan gabanta.wato Æ´ar da ta haifa ta koma.
Munyi baÆ™in ciki sosai da rashin yarinyarmu,amma haka muka haÆ™ura muka mikawa Allah lamarinmu. Nan na bata labarin samoki da nayi,sai naga tana ta murna da farin ciki,batayi wata- wata ba ta karÉ“e ki ta fara shayar dake,koda nayi magana saitace”Allah ne ya dawo mana da farin cikinmu.dan haka zamu rikeki matsayin Æ´armu da muka rasa,idan kuma munji anyi cigiyarki saimu bada ke.
Nan da nan nima na yarda da shawarar ta ,dan lokaci ɗaya Allah ya samun ƙaunarki raina. Haka na gayyato mutane akayi suturar ƴarmu,yayinda nake faɗawa Mutane cewar ƴan biyu matata ta haifa ,ɗayar ta koma sai ɗayar.
Lokacin da muka tsinceki akwai wani sarƙa awuyanki,wacce da alama zata yi matukar tsada ,dan haka sai muka cire muka ajiyeta haɗe da rigar dana tsinceki da ita.
Munsha tambaya akan ya akayi baki biyo ko ɗaya daga cikinmuba,dan kin kasance kyakyakywa wacce kaf rugar nan ba wanda ya kama ƙafar kyanki,sannan gashinki ba irin namu bane.haka dai muke samun amsar da zamu rufe bakin mutane da ita.
Shekararki biyu a duniya ,Maryama ta koma ga Allah.munyi kuka daga ni harke na rashinta, kafin daga bisani muka haƙura.
Lokacin ne na auri hansai ,wacce ta kasance ba abinda ta iya banda mugunta da baƙin hali,sam bata ƙaunar ki ,da idan tayi miki wani abun nakan yi magana ,saidai daga baya kuma sainake kasa yin maganar,koda na yunƙuro da nufin yin maganar bana iyawa.
Wannan shine taÆ™aitaccen tarihinki fattu na.amma na tabbata ko ba daÉ—e ko ba jima zaki haÉ—u da asalin iyayenki,jikina yana bani kun kusan haÉ—uwa. Wanda idan har kikaci gaba da zama cikin rugarnan, hakan bazata faru ba.zan nemeki Aduk inda kuke fattu na “baffa ya faÉ—a cikin kuka abin tausayi.
Fattu ma kuka take sosai kamar ranta zai fita ,”baffa ina sarÆ™ar take “fattu ta faÉ—a cikin rawar murya irin ta mai zazzaÉ“i.
Tashi baffa yayi ya buɗe cikin jakarsa ta kaya ya ɗauko wata leda ya kunce,saiga wata sarƙa mai tsananin sheki da ɗaukar ido,sai wata ƴar riga mai kyau fara ta yara.miƙawa fattu kayan baffa yayi .
Ahankali ta karbi kayan ta rungume ajikinta tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Kallonsu kawai Adeeb yake ,dan zuwa yanzu ya gama ɗaukarwa kansa alƙawarin taimakawa fattu ta kowace fuska ,har saita ga iyayenta.
Baffa kansa kukan yake ,yana jimamim rabuwa da Fattun sa.
Tashi Adeeb yayi ,cikin tafiyarsa ta izza da cike jarumta ya ƙarasa kusa da fattu ,tsugunmawa yayi akusa da ita ,yana kallon fuskarta dake ta faman kuka ,gaba ɗaya tayi jajur da ita.
Hannunsa ya sanya ya ɗago habarta ya kura mata ido,buɗe idanunta tayi itama ta sauƙe cikin nashi,sun ɗauki kusan mintuna uku suna kallon juna,kafin Adeeb ya sauke wani kwauron numfashi ,sannan ya sanya babban ɗan yatsanshi ya share mata hawayen dake zuba a idonta.girgiza mata kai yayi alamun ta daina kuka.amma sam ta kasa dainawa.
Sarƙar hannunta ya karɓa yana kallo,sarkar zallar daimond ce sai sirin kwal,da gani wannan sarƙar ta doshi millions ,koma ina yarinyar nan ta fito to tabbas ƴar gidan manya ce,in Sha Allah zai haɗata da iyayenta na asali.
Sarƙar ya buɗe tare da nufar wuyanta wanda yake nan zafi ƙau da zazzaɓi,ya ɗaura mata sarƙar.nan da nan sarƙar ta ɗauki wani sheƙi da walwali.
Dawo da kallonsa yayi kan baffa wanda yake kallon duk abinda ke faruwa,zuciyarsa tana masa wani irin ƙuna da ciwo.
Saida ya É—auki kusan minti biyar kafin yace “Abba nayi maka alÆ™awarin zan taimaka wajen neman asalin iyayen yarinyarka,zamuiyi amfani da wannan sarÆ™a in Sha Allah everything is gonna be ok”ya faÉ—a cikin muryar sa mai daÉ—in amo .
Hannunsa baffa ya kama cikin farin ciki yace “na gode Allah yayi maka albarka,ka kulamin da fattu karka bari ta cutu “
Jinjina kai yayi shima yana mai riƙe hannun baffan, akaro na farko ya ɗanyi murmushi.masha Allah masu karatu bakuga yadda yayi wani sihirtaccen kyau ba,Dan murmushin ba ƙaramin kyau ya ƙara masaba.
Kwanciya fattu tayi akan sallaya ta juya bayanta tana ta kuka da rawar zazzaɓi,shikenan yanzu haka zata bi wannan bawan Allah da batasan koshi waye ba,meyasa iyayenta suka yarda ita?me tayi musu haka da zafi?dama baffa ya fasa ƙidurinsa na cewar saitabi wannan bawan Allah mana.
Baffa ne ya miƙe tsaye da sauri tare da leƙawa ƙofar ɗakinsa, dan tabbas yaga gilmawar mutum,aikuwa yana leƙawa ya hango zanin gwogwgo hansai tana shigewa ɗakinta. Ya Salam kenan taji duk abinda suke tattaunawa ?lallai dole su bar gidan nan kafin gari ya gama wayewa.dan yanzu kam asuba ta kawo kai,
Da sauri ya koma É—akin yace “Adeeb akwai matsala,yanzu yanzu zaku tashi ku dau hanya,dan kuwa hansai taji duk abinda muke tattauna,kuma na tabbata ko bari bazata yi gari ya gama wayewaba zata je ta sanar da mai gari”
Baffa ya faÉ—a cikin tashin hankali da damuwa.
Shikuwa Adeeb ko ajikinsa Æ™ara gyara zama yayi ,dan bazai iya kwanciya anan gurin ba ,kafin ya kalli baffa ya É—an taÉ“e baki yace “and so what idan ta faÉ—a masa”?
Ya faÉ—a cikin ko in kula.
“Bazaka gane zalumcin lamiÉ—o ba Adeeb zai iya sawa kashe fattu ,dan Allah ku tashi muje In fitar daku hanya ku tafi, ka taimaka min ka ceci rayuwar yata”baffa ya faÉ—a cikin kuka yana durÆ™usa akan gwuiwoyinsa.
Da sauri Adeeb ya tashi ya kama baffa ya miÆ™ar dashi yace “is ok Abba zamu tafi yanzu.ya faÉ—a yana mai kamo hannun fattu ya miÆ™ar da ita tsaye.
Ita kuwa fattu yadda yake jin zuciyarta bayani ace mai gari yasa a kasheta Bama,koba komai zata huta da ƙuncin zuciya da damuwa.tana mikewa tayi baya zata faɗi,dan gaba ɗaya ba ƙarfi ajikinta.da sauri Adeeb ya tallafi ga zuwa jikinsa,kallon fuskarta yayi wacce ta kumbura ,sai rufe idanu take tana buɗe wa,da gani tana shan jiki sosai.
“Muje bawan Allah ,fattu daure kinji”baffa ya faÉ—a cikin ruÉ—u ,ba abinda yake É“ukata irin yaga sun bar rugar nan.
Ganin fattu zata É“ata musu lokacine yasa Adeeb ya É—agata sama tsak!kamar Æ´ar tsana ya saba akafaÉ—arsa yacewa baffa” muke Abba”
Wata leda Baffa ya dauko,tare da rigar nan ta fattu ya cusa ciki,sannan yayi waje suka rufa masa baya……
Masu karatu me zakuce game da rabuwar baffa da fattu?
Mrs babi ce💘💘