Hausa novels

Abban Sojoji Page 60 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Page 60 Book 2

The Father Of Soldier

By Boss Bature

Abban sojoji paid book ne,ga duk mai buƙatar karanta cigaban shi yayi mun magana kai tsaye ta number ta 08103884440 Whatsapp only banda phone calls, 300 ne only 🤝

 

Zuba ma zoben ido tayi tana kallonshi hankalinta a matuƙar tashe,gabanta na faduwa,a hankali take jujjuya shi a hannunta,lokaci guda hawaye suka fara gangarowa daga idanunta cikin shessheƙar kuka take cewa”I can’t believe it! Ya omar ɗina ne yayi ƙoƙarin raping dina? Shine yaso  rabani da mutuncina?why ya Omar why!?innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Allah kasa mafarki nake ba gaske ba…….’kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta gaza ƙarasa maganar,nan fa tashiga shararar kwalla,abun ba ƙaramin ciwo yayi mata ba,bata ta6a tunanin haka daga wurin shi ba,wannan zoben nashi ne,shi ya tabbatar mata da cewa Ya omar ɗinsu ne yayi yunƙurin yi mata wannan aika-aikan,amma meyasa!?

 

tsagaitawa tayi da kukan tashiga girgiza kanta tana cewa”A’a ya Omar ɗina bazai ta6a yi mun haka ba,na yarda dashi sosai,nasan cewa bada son ranshi yayi mun hakan ba,Ya Omar bazai ta6a cutar da hosanar shi ba,ina yi mashi kyakkyawan zato kuma bazan ta6a tona mashi asiri ba,bazan bari kowa yaga zoben shi ba ko jahad bazan nuna mawa ba,saboda nasan ba dole ta fahimce shi ba,kamar yarda ni na fahimce shi,”ƙarasa maganar tayi tare da ƙankame zoben asaman ƙirjinta ta ɗan runtse idanunta hawayen naci gaba da sauka asaman fuskarta,

Dama ance so hana ganin laifi,hosana ta makance akan son ya Omar ɗinta,kuma ta yarda dashi 100%,

tana cikin wannan yanayin taji motsin mutum cikin sauri takai hannu tare da janyo bargo ta ƙudundune acikin shi,6oye zoben tayi acikin aljihun rigar jikinta,sannan ta sanya tafin hannayenta tana goge hawayen fuskarta,

Jahad ce ta shigo hannunta ɗauke da kakkauran tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,ƙarasawa tayi tare da samun wuri daga gefen gadon kusa da hosana ta zauna, a hankali  tace”ƴar uwata rabin raina ga tea na kawo maki, ki tashi kisha shi da zafi zafinshi karya huce nasan zaki ji dadin shi,’cikin lallami take yi mata magana saboda tasan a halin da take na fargaba tana buƙatar kalamai masu daɗi da zasu sanyata farin ciki,

lamo hosana tayi batare da ta motsa ba abunda yasa tayi hakan saboda tanason ta daidaita natsuwarta don kar jahad ta gano wani abu,

jin shiru yasa jahad,kai hannunta na dama ta ɗan bubbugi kafaɗarta tace”tashi mana hosana ko kinyi bacci ne”?ta tambaya tana kallonta naɗe cikin bargo,

Har jahad ta yunƙura zata tashi,hosana ta soma motsi alamar zata farka,komawa jahad tayi ta zauna tana jiranta ta tashin,a hankali ta yaye bargon tare da tashi daga zaune tana mutsistsika idanunta alamar yanzu ta tashi daga guntun baccin daya ɗauke ta,wartsakewa tayi ta buɗe ido tana kallon Jahad,

 

Murmushi jahad ta sakar mata tare da cewa”babyn Omar ya jikin naki?nasan har yanxu kina fargaba akan abunda ya faru dake jiya,dan Allah hosana kada kisa damuwa kinji?insha Allah koma wanene asirinshi zai tonu,zamu faɗama ya Omar zai gano koma wane tsinan………’a firgice Hosana ta toshe ma Jahad baki da tafin hannunta tana cewa”Jahad dan Allah kidaina maganar nan,kina tunamun abunda ya faru jiya,ni banason ma ana maganar nan,gabana faɗuwa yake yi,’ta ƙarasa maganar a sanyaye tare da zame hannunta daga bakin jahad,

Ajiyar zuciya jahad ta sauke tare da cewa”Shikenan mubar maganar,yanzu dae ga tea ɗin kisha,kuma sister camilla tace na tambayeki in akwai abunda kike buƙata a girka maki kici,”

Hannu hosana tasa ta kar6i cup ɗin da jahad ta miƙo mata sannan tace”Bana buƙatar cin komai yanzu,ni dai akira mun ya Omar yazo inason ganin shi,’

Murmushi jahad tayi tare da cewa”kada ki damu babyn Omar,nasan zaizo ne ina ta trying numbarshi amma taƙi shiga still switch off,amma nasan zuwa anjima zai kunna wayar ne,”

Jin haka yasa jikin hosana yin sanyi,don tasan dalilin dayasa Omar ya kashe wayarshi,bata ji daɗi ba saboda tasan zai sanya damuwa sosai aranshi,tausayinshi ne taji ya kama ta,babban abunda take fargaba shine kada ya hana kanshi zuwa wurinsu,

tashi jahad tayi tare da fuce wa daga bedroom din ta koma kitchen,yayin da ya rage hosana ce kaɗai saman gadon tana kur6ar tea ɗin a hankali,duk jikinta yayi sanyi,

 

After some days

 

Abu kamar wasa yau almost 1 week kenan ba Omar ba alamar shi,hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,kwana huɗu ba Omar ko layin shi suka kira kullum a switch off suke samun shi,hakan ba ƙaramin tayar masu da hankali yayi ba,sun shiga damuwa sosai na rashin zuwan shi,musamman Hosana duk tabi ta takure kanta,ko abincin kirki bata iya ci,ko isasshen bacci bata samu,kullum cikin kuka take na rashin ganin ya Omar ɗinta,duk bayan ƴan mintina sai taje ta ɗauki telephone ta danna mashi kira,da zarar taji wayar akashe sai ta fashe da kuka,daƙyar jahad ke samu ta lallashe ta,akwai lokacin da jahad ta farka tsakar dare ta samu Hosana saman darduma tana yin sallar dare abunda bata ta6a ganin hosana tayi ba,kuma duk don saboda ya Omar ta tashi yin sallar daren,tana roƙon Allah yasa Ya omar yazo karya rabu dasu,batasan yaya rayuwa zata kasance mata ba,batare da ya Omar ɗinta ba,tana yin addu’ar tana matse kwalla,a wannan lokacin ba ƙaramin tausayi taba Jahad ba,

A washe garin ranar jahad ta yanke shawarar zuwa tasamu Osman ta sanar dashi game da halin da suke ciki na damuwa da rashin ganin ya Omar ɗinsu,ko da Jahad taje ta samu Osman ta faɗa mashi,yayi mata alkwarin cewa zai bincika masu shi,

 

Download>>> Dr Bobby Complete Novel Document

 

Bayan tafiyar jahad,Osman ya nemi major a waya ya sanar mashi abunda ke faruwa,na halin da yaran suke ciki akan rashin ganin Marshal da basuyi ba na tsawon kwanaki ,jiki a sanyaye Major yace mashi yaci gaba da kwantar masu da hankali,insha Allah zaizo ne abubuwane sukayi mashi yawa.

Hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,lokacin da major ya sanar dashi halin da su jahad da hosana suke ciki,tsananin tausayinsu ne ya kamashi,musamman hosana da aka sanar dashi cewa ko isasshen bacci bata samu saboda damuwa akan shi,tamkar ya zubar masu da hawaye haka yaji,duk yarda yaso ya daure ya hana kanshi fargabar tunkararsu amma ya gaza yin hakan,ya nisanta kanshi dasu ne, saboda gudun karya ƙara jefa kanshi cikin matsala,shi kanshi daurewa kawai yake yi amma ba ƙaramin cutuwa yake yi ba,yana tsananin son ganinsu yanaso yaga wane hali suke ciki, amma ba yarda ya iya.

 

A 6angaren Sehrish kuwa ba ƙaramin jiki taji ba,a washe garin ranar da Sgr ya sanyata tsallen kwaɗi,ko school bata je ba,saboda jinyar jikinta da ta tsaya yi,ƙafafunta sunyi suntum,tun da ta lafe saman gadon ko motsi bata son yi,ba ƙaramin jiki taji ba sai da azmee ta taimaka wurin gasa mata ƙafafun da ruwan zafi,tayi mata tausa sannan taji sauƙin jikinta sosai har ta samu ta warware taci gaba da ƙiriniyarta kamar yarda ta saba.

 

Hayamm taji haushi sosai kamar ta binne kanta saboda tsabar baƙin ciki,tun washe garin ranar da azmee taje gyara part din Sgr,ta fito hannunta ɗauke da tray ɗin kayan abincin da baici ba,jiki na rawa hayaam ta ƙarasa tare da kar6ar tray ɗin tace tabar mata kayan takai kitchen,

tana shiga kitchen dasu ta shiga buɗe kayan don taga idan sgr yaci abincin,sai dae abun takaici bai ta6a komai na abincin ba,yarda sehrish takai mashi shi haka aka dawo dasu bai ta6a komai ba,lemu kawai yasha,kuma ta manta bata zuba gashin acikin abun shan nashi ba,taji takaicin hakan kamar ta aza hannu abisa kanta tayi ihu saboda haushi,amma taci alwashin cewa saita shirya mata wani tuggun tunda ta tsallake wannan.

 

A 6angaren su Twins kuwa sai dae muce Alhamdulillah,Yara sun zama mazajan gaske,rayuwarsu ta gyaru sosai,yanzu basa wasa wurin yin ibadarsu suna neman tsarin ubangiji,don wani lokacin atare suke tashi suyi ƙiyamun laili da sauran nafilfili,sannan basa komawa bacci bayan sallar asuba,zama suke yi suyi ta karatun alkur’ani mai girma har gari ya waye, Allah sarki rayuwa kenan ayayin da matsalar su jahan ta ƙare, shi kuma junaid wani mummunan al’amari ya soma faruwa dashi batare da sanin kowa ba,shi kaɗae yasan halin da yake ciki,kuma yaƙi sanar ma kowa saboda baison ya tashi hankalin Abbanshi da kuma na ƴan uwanshi,baka ta6a gane halin da yake ciki saboda babu abunda ya canza na daga ƙiriniyarshi, da kuma wannan kyakkyawan murmushin nashi,abun yana damunshi sosai, wannan ɗigon jinin dake fitowa ta ƙopar hancinshi, kullum ne saiya tashi tsakar dare batare da sanin Abbansu ba, ya shiga cikin toilet yana wanke hancinshi, abun sai ƙara gaba yake yi, ga yanayin da yake tsintar kanshi aciki,yanayi mara daɗi wata irin kasala da kuma yawan faɗuwar gaba,da kuma razanar da yake yawan yi,ko kiran sunan shi kayi da karfi sai ya firgita,ba kowa ya lura da hakan ba,tabbas rayuwar Junaid tana cikin hatsari sosai,a cikin jikinshi ciwon ke cin shi batare da sanin kowa ba, hmmmmmmm.

 

A 6angaren Commandern ƴan iska kuwa wato haroon komai ya gama hargitse masa,kamar wani zautacce haka ya koma wurin neman jakar kuɗin shi,sam ya rasa samun kwanciyar hankali gaba daya plan ɗin da ya shirya na barin nigeria yana shirin rugujewa saboda rashin kuɗin nan,a ƙarshe ya yanke shawarar turo ɗayan videon nan nasu jahan don ya sake yi masu barazana dashi,su ƙara mashi wasu kuɗin da zai samu yabar ƙasar tunkan asirinshi ya tonu,

 

Wannan kenan👌

 

Gaba daya an canzama gidan kamanni sai faman gyare-gyare akeyi mashi ta ko’ina,kwararrun ma’aikata aka ɗauko wurin tsara decoration ɗin da za’ayi ma gidan, yarda kasan za’ayi wani shagalin biki haka suka ƙawata gidan,duk wannan shirye shiryen da suke yi na tarbar manyan baƙinsu ne da zasu zo acikin kwanakin nan,a yau dae mutum biyu ne zasu fara zuwa,daga ciki akwai uncle Abusufyan da zaizo daga ƙasar turkey,sai kuma hajiya azeema da zata zo daga lagos,

gaba ɗaya tunanin matasan gidan Abbansu yasa aƙawata gidanne kawai saboda zuwan su Ammin sa ne,abunda basu sani ba shi da wata manufa yasa a gyara gidan, Tofah,

 

Wuraren ƙarfe 7:00am dai dai sehrish ta kammala shirinta na zuwa school,tana tsaye agaban mirror sai faman feshe jikinta takeyi da turare,bayan ta kammala ta koma wurin gadonta tare da kai hannu ta ɗauki hijab ɗinta data ajiye anan saman gadon ta zura ajikinta,

bata ɗauki school bag ɗinta ba saboda tana so tafara zuwa kitchen wurin su Aunty azmee ta kar6a ma babban yaya breakfast ɗinshi takai mashi,

fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin tana tafiya tana ƴan kalle kalle kamar zatayi tuntu6e,decoration ɗin da akayima gidan ba ƙaramin kyau yayi mata ba,don ba ƙaramin ɗaukar ido yake yi ba,

Ƙarasawa kitchen ɗin tayi tare da tsayawa daga bakin kopar tayi masu sallama,Azmee ce kaɗae acikin kitchen ɗin,jin muryar sehrish yasa ta juyowa fuskarta ɗauke da murmushi tace”Ƴan makaranta har an kammala kimtsawa ne?

murmushi sehrish tayi tare da cewa”ina kwana Aunty azmee,ya aiki”?   Azmee tace”Alhamdulillah,shigo daga ciki mana in haɗa maki breakfast ɗinki ki ci kafin ki tafi,’

“A’a Aunty azmee bana jin yunwa,idan naje school zanci acan,’ har ta ɗanyi shuru, cike da son jin gulma ta kuma cewa”Aunty azmee wai wanene zaizo zo yau”?

Murmushi azmee tayi tare da cewa”Masu kama dake ne zasu zo yau,’

“Masu kama dani kuma Aunty azmee”?ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki,

azmee tace”kwarai kuwa kuna kama da azeema kanwar Abbansu junaid dake lagos,amman kinfi kama sosai da Uncle ɗinsu, Abusufyan dake zaune a ƙasar turkey shima zaizo yau,’

wani irin farin cikine taji ya lullu6eta,saboda ɗokin ganin wannan uncle ɗin nasu da take yawan jin suna ambatar sunanshi,a ƙagare take da ta sanya shi acikin idonta,

 

Download>>> Deen Hausa Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

 

“Aunty azmee dagaske muna kama dashi?ko wasa kike yi mun”?

Azmee tace”dagaske nake mana,ban ta6a faɗa maki ba,amma maganar gaskiya kamanninki dashi har sun 6aci,kullum na kalli fuskarki sai ya faɗo mun araina,saboda komai na fuskarki irin nashi ne,tun daga kan idanuwanki,hancinki,da kuma bakinki duk irin nashi ne,ke hatta launin fatarki chocolate colour irin nashi ne,da ace Abusufyan ya ta6a yin aure,zan iya rantsewa cewa ke ƴarsa ce’

tunda azmee ta soma magana sehrish ta saki baki tana sauraronta,

“abun ya jima yana ɗaure mun kai,shiru kawai nayi,amma kamanceceniyarki da wasu daga cikin matasan gidan nan har taso tayi yawa,”

Cika da mamaki Sehrish tace”Aunty azmee wai dagaske”?

murmushi azmee tayi kafin taci gaba da cewa”na ta6a yi maki wasa ne irin haka”?

Girgiza kai sehrish tayi alamar a’a,

Cigaba da magana azmee tayi”kina yanayi da Abbansu junaid sosai kuma kina kama da Auntynsu Azeema,hatta junaid akwai kamanceceniya atsakaninku abunda yasa baza a gane ba saboda hasken fatarshi,amma kina kama  da shi,bayan shi kuma sai Marshal Omar,shima akwai kamanninshi atattare dake,da kuma kanal yousouf,na jima da lura da hakan,”

tunda sehrish taji wannan jawabin na azmee take ta faman sakin murmushi,daɗi kamar ya kashe ta saboda ance tana kama da uncle Abusufyan ɗinsu,

“Aunty azmee naƙosa na ganshi,Allah yasa kafin nadawo daga school ya ƙaraso,da kaina zanje inyi mashi sannu da zuwa sannan in kai mashi abun sha,”

Dariya azmee tayi tana cewa”Allah yasa toh,amma kin manta baki ce insha Allah ba,”

cikin sauri sehrish tace”Insha Allah Aunty azmee,”

Suna cikin firar nan tasu,sai ga junaid ya faɗo cikin kitchen ɗin ko sallama babu a firgice suka ɗago suna kallonshi,

daga shi sai gajeran wando fari ajikinshi,sai faman washe baki yake yi,kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna,

“Junaid anya lafiyarka kuwa?kaine yau kake yawo da short ajikin ka?ko ka manta akwai sehrish dani acikin gidan”? Acewar Azmee,

Murmushi ya saki tare da nuna sehrish da hannunshi yace”Wurinta nazo,inason magana dake reesh,in ba damuwa ki biyo ni muje bedroom ɗina,’

Kallon azmee tayi don taji me zata ce,

“kije mana,amma kada ki jima,”

Amsa mata tayi da toh sannan tabi bayan junaid suka fuce atare izuwa bedroom ɗinshi dake a upstairs,

atare suka shiga cikin ɗakin nashi,har wurin gadonshi yakaita sannan ya tsaya tare da nuna mata shaddojin daya jera asaman gadon nashi yace”Pls reeshi ki za6amun ɗaya mai kyau,inaso yau nayi shigar mutunci don na burge uncle Abusufyan yasan cewa na girma yanzu,’ashagwa6e junaid ya ƙarasa maganar,

Sehrish kuwa zuba ma tsadaddun shaddojin ido tayi tana kallonsu,kala biyar ne sun sha uban aiki ajikinsu,hannu tasa tana ɗaɗɗaga kayan tace”junaid ae ni nama rasa wadda zan za6a maka acikinsu,saboda kowacce kasa acikinsu kyau zatayi maka,bakasan cewa kaine keyi ma kayan kyau ba”? Tayi maganar tare da ɗan juyawa tana kallon junaid dake tsaye yana ta faman sakin murmushin jin daɗin yarda sehrish ke hura mashi kai,

 

ta jima tana ruwan ido kafin ta cankar mashi wata haɗaɗɗiyar shadda gezner Ash colour sai faman salƙi take yi, mika mashi tayi tare da cewa”Wannan tayimun sosai kuma ina da tabbacin cewa in har ka sanyata ajikinka,sai uncle abusufyan ya razana da ganin irin kyan da zakai,’

Kar6ar shaddar yayi daga hannunta yace”thank u so much reesh,amma fa ba yanzu zan sanyata ba,sai zuwa anjima in zanzo ɗaukarki daga school zaki ga kalar wankan da zan ɗauka,”

murmushi tayi tare da kama hanyar fita  daga cikin bedroom ɗin nashi tana cewa”Allah ya kaimu lafiya,yanzu dae zan jiraka,in ka kammala shirin ka fito mu tafi kar nayi late,’

Amsa mata yayi da toh,bayan ta fita ya tattara shaddojin duka ya mayar acikin wardrobe ɗinshi, ya zaro wasu jeans da t-shirt ya shiga zura su ajikinshi

 

_💋Boss Bature💋_

 

Lokacin da sehrish ta koma kitchen ɗin bata samu Azmee ba,sae dae Hayaam ta samu acikin kitchen ɗin,tana atsaye ta ruƙe qugunta kamar mai jiran wani abu,

Ganin sehrish yasata cewa”Sannu ko”

firgit Sehrish tayi tare da kai idonta inda hayaam ta ke atsaye tana sakin wannan shu’umin murmushin nata,

“Yawwa”ta amsa mata atakaice tare da wucewa wurin trayn da azmee ta ajiye mata saman table wanda  ta shirya ma sgr breakfast ɗin shi aciki,hannu biyu tasa ta ɗauki tray ɗin sannan ta kama hanya tare da fucewa daga kitchen din,hakanan ta dinga jin kamar bata yarda da hayaam ba,anya ba wani abu takeyi acikin kitchen ɗin ba?in ba haka ba meyasa ta tsaya atsaye ruƙe da qugu,kamar mai jiran wani abu,

haka tayi ta wasiwasi acikin zuciyarta har ta ƙarasa part ɗin sgr,

Sallama ta fara yi mashi,jin shiru ba’a amsa mata ba,yasa tayi tunanin ko yana acikin bedroom ɗinshi ne,

A hankali tasanya kafarta tare da shigewa cikin palourn komai agyare tsaf ta same shi,asaman table ta aza mashi tray din sannan ta tsaya tana jiran fitowarshi ko zai bukaci wani abu,

tana cikin tsayuwar nan tajiyo muryarshi daga cikin bedroom ɗinshi yana tambayar wanene anan!”

Cikin sauri tace”Ni ce,dama breakfast ne na kawo maka,”

kusan minti biyar da yin maganarta sannan taji yace”A shigo min da coffee shi kawai nake buƙata,”

murmushi ta ɗanyi tare da mika hannu ta ɗauki cup of coffee ɗin dake acikin kayan breakfast ɗin nashi,ta nufi bedroom ɗin hannunta ɗauke da cup ɗin,

sai da ta tsaya abakin ƙopar shiga Sgr ya bata izini sannan tasa kai tashiga,wani irin daddaɗan kamshin turarensa ne ya bugi hancinta,nan take taji wani irin yanayi atattare da ita,

lumshe donta tayi tare da buɗesu a hankali ta kallo inda sgr yake, a hakimce ya ɗan kishingiɗa daga gefen katafaren gadon nashi,

Gaza janye idanunta tayi daga kallon kyakkyawar surar jikinshi,wankan daya ɗauka ba ƙaramin fisgarta yayi ba,white trouser ne na suits amma bai sanya coat ɗin sama ba,iya vest ɗin ciki ya bari tabi shape ɗin jikinshi,daga ƙasan vest ɗin ta ɗan tattare hakan ya bayyana farar fatar shafaffen cikinshi, ya harɗe kafafunshi wuri guda yayin da idanunshi ke a lumshe,

tafiya take tana tunkarar inda yake idonta akanshi har ta ƙarasa tare da ajiye mashi cup ɗin asaman bedside table ɗinshi tace”Gm sir,ga coffee nan na kawo maka,ko akwai wani abu da kake buƙata”?

Bai amsa mata ba,a hankali ya dan buɗe idanunshi sannan ya yunƙara tare da miƙewa daga zaune ya sauko da ƙafafunshi ƙasa,

Zaki iya tafiya,ya ambaci hakan ayayin da yakai hannu tare da ɗaukar kofin coffeen yakai bakinshi yana kur6ar shi anatse,

Juyawa sehrish tayi ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin a hankali,ji take kamar karta tafi ta barshi,don bata gaji da kallon kyakkyawar fuskarshi ba,

 

Yana cikin shan coffeen nan wani abu ya sarƙe mashi adaidai saitin throat ɗinshi,a hanzarce ya ajiye cup ɗin tare da zura fingers ɗinshi guda biyu cikin bakin cikin sa’a ya ruƙo siririn abun,

Lokacin daya fiddo da abun daga bakin nashi yayi arba da dogon gashi,ware idanunshi yayi, hankali a matukar tashe yana kallon gashin yace”in my coffee…!

Jin wannan maganar tashi yasa sehrish saurin juyawa don taga menene,a lokacin har tasa ƙafa zata fita daga ɗakin,

Gabanta ne taji yayi wani irin mugun buga ganin siririn gashin da Sgr ya ruƙo a hannunshi,

Yunkurin amai yashiga yi,nan take ya miƙe da saurin gaske ya faɗa toilet,kai tsaye ya ƙarasa gaban basin yana kwarara aman,tamkar ƴan hanjin cikinshi zasu fito,kasancewar shi mutum mai tsaftar gaske ga ƙyanƙyami ya tsani ƙazanta a rayuwarshi duk mun ƙankanta,ranshi ba ƙaramin 6aci yayi ba,gashi a abun shansa kuma har ya shiga bakinsa!!,a wannan lokacin komai zai iya aikatawa he can’t even control him self, cos he has a very bad temper,kuma ta motsa.

Tap ya kunna,ruwa yashiga zubowa yana kora vomitting ɗin da yayi,sannan ya tarba tafin hannayenshi biyu tare da ɗebo ruwan ya watsa su a fuskarshi yana faman sakin huci,

Sehrish dake atsaye abakin kopan bedroom ɗin nashi,jikinta sai faman kerma yake yi,gaba daya tabi ta rikice kan ta ya gama ɗaurewa,taya akai aka samu gashi acikin abun shan Sgr?ita dae tasan cewa ba gashin kanta bane,saboda ta sanya hijab ajikinta,hasalima ba ita bace ta shirya mashi kayan breakfast ɗin nashi ba,tunkan taga hukuncin da zaiyi mata har tafara matsar kwalla,don tasan bazai ƙyale ta ba,dole ya hukunta ta,

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who Is She) Page 59 By Barakancy

A fusace ya fito daga cikin toilet ɗin,sai faman huci yake yi,ɗagowa yayi da idanunshi yana kallon inda sehrish take atsaye jikinta sai kerma ya keyi,tunda taga zufa na gangarowa a gefen fuskarshi, ta ƙara tsorata sosai,

tamkar wani zaki haka ya tunkaro ta,a tsananin tsorace sehrish ta shiga ja da baya tana girgiza kai cikin shessheƙar kuka take cewa”wlh bani da masaniya akan gashin nan,banawa bane bansan ya akai ya shiga cikin abun shanka ba,’

wata irin tsawa da Sgr ya daka mata nan take sehrish ta firgita agigice take zazzare ido tana kallon fuskarshi,

biting lips ɗinshi ya shiga yi,yama rasa wane irin punishment zaiyi mata,

Nuna ta da dogon yatsan sa yayi tare da cewa”as from today!bana son na ƙara ganinki a part ɗina!’

Cikin shessheƙar kuka sehrish tace”Am really sorry babban yaya……..ba laifi na bane bada sani na gashin ya faɗa aciki ba……….’tun kafin ta ƙarasa maganar ya ɗaga hannunshi da nufin ya sharara mata mari,runtse ido sehrish tayi tana jiran jin saukar marin nashi a kuncinta,

ji yayi bazai iya ba saboda tunda yake arayuwarshi bai ta6a gigin ta6a jikin wata ƴa mace ba da sunan bugu,tun suna yara Abbansu ya hane su da yin wannan,kullum yana tunasar dasu akan su dinga daraja ƴa mace,

Dunkule hannunshi yayi tare da yarfar dashi gefe guda,sannan yace”Get out from my bedroom!since before I show u my true colour!,

ya ƙarasa maganar tare da juyawa yabarta tsaye anan tana faman shessheƙar kuka,

Ji tayi bazata iya jure hukuncin da Sgr yayi mata ba, na hanata aiki a ƙarkashin shi ba,

gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi, a wani irin yanayi ta zube asaman guiwowinta,cikin sanyin murya,muryarta na rawa  tace”nasan na 6ata maka rai sosai,na cancanci kowane irin hukunci daga gare ka,amma ina neman alfarma a wurin ka……..’dakatawa tayi da maganar tana kallon bayan shi daya juya mata,

ganin ya tsaya da yin tafiyar yasa ta gane cewa ita yake sauraro,

anatse taci gaba da magana”ka yanke mun kowane irin hukuncin daya dace da laifin dana aikata,amma kada ka hanani yin aiki a ƙarkashinka,wannan horon yayi mun tsauri sosai,bazan iya jurewa ba,tun da nake maka aiki banta6a yin irin wannan gangancin ba,ina kiyaye wa sosai wurin ganin na tsaftace duk wani abu da zan kawo maka kaci ko ka sha,ba zanso wani abu da zai cutar dakai ba,wannan ma bansan ya akai hakan ta faru ba,don Allah kayi haƙuri ka yafe mun…………’ƙarasa maganar tayi cikin shashsheka yayin da hawaye ke cigaba da zuba a idanunta,

shiru Sgr ya ɗanyi na wani lokaci batare da ya motsa ba,hakan yasa ta fidda rai da cewar zai yafe mata,

Hannu tasa tana sharar hawayenta tana kallon bayanshi,cigaba da tafiya sgr yayi kai tsaye ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,hannu yasa tare da janyo drawer chest din dake ajikinshi,sabon scissors ya ɗauko cikin ledarshi, ya fiddo dashi yana kallonshi,

lokacin daya juyo hannunshi ɗauke da almakashin nan,hankali atashe sehrish ta zaro ido tare da miƙewa tsaye daga kneel down ɗin da tayi tana ja da baya tana girgiza mashi kai,alamar karyayi mata haka,

Gadan gadan Sgr ya tunkare ta,hannunshi ɗauke da almakashin nan sai faman salƙi yake yi,hannu sehrish ta aza asaman kanta tana cewa”Nashiga uku!innalillahi wa’inna ilaihirraji’un……….dan Allah kada ka datse mun gashin kaina ……’tana magana tana ja da baya yayin da shi kuma yake tunkararta,abu kamar wasa haka suka shiga zagaye ɗakin yana binta tana ja da baya,a ƙarshe daya fusata a zafafe ya damƙo hijabin dake jikinta tare da tun6uke ta daga jikinta yayi wurgi da ita gefe guda,yarda ya fusge hijabin daga jikinta gaba ɗaya ta tafi zata faɗi kasa,yakai hannu tare da janyo ta ta faɗo saman wide chest ɗinshi,kuka take kamar ranta zai fita saboda ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nan nata ba,ta kwallafa rai akanshi shiyasa kullum take ƙokari wurin gyara shi,har tasamu tatara shi da yawa bayan yanke shin da akai da zata fara aiki gidan,gashi yau akan kuskuren da ba ita ta aikata ba,za’ayi mata aski tana ji tana gani ba yarda zata yi,

tunda sehrish ta faɗa jikinshi gaba ɗaya ya rasa duk wani kuzari na jikinshi,ƙamshin turaren jikinta ba ƙaramin kashe mashi jiki yayi ba,abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,a hankali yakai hannunshi tare da Cire ribbom ɗin da ta ɗaure gashin kanta dashi,ya warwaro shi duka tare da yin wurgi dashi gefe guda ya fadi kasa saman hijab ɗinta,

Nan take lallausar suman kan nata mai laushin gaske ya tarwatse abayanta yayi mata tamkar hijabi,

Ai ina baku labari tunda boss man ɗin nan ya zura hannunshi acikin sumar kanta nan fa yashiga murza gashin acikin hannunshi,laushin gashin kan nata ne yake fisgarshi har yayi hakan batare da saninshi ba,

A hankali ya russinar da kanshi tare da kai tsinin hancinshi saman sumar kanta yana shaƙar daddaɗan kamshin dake fitowa daga cikin sumar kan nata,wani irin bugu zuciyarshi tashiga yi da sauri sauri take harbawa,

ƙankame shi sosai sehrish tayi ta hanyar zagayo da hannayenta abayan waist ɗinshi ta ruƙo shi sosai kamar wani zai kwace mata shi,ba ƙaramin yanayi ta jefa Sgr ba ta kara sanya mashi kasala ajikinshi,kamar yarda itama ta shiga yanayin,tunda ta lafe mashi ajikinshi tayi lamo,wata irin natsuwa ta ji

da bata ta6a ji ba atattare da ita,shessheƙar kukan nan da takeyi gaba daya ta neme ta ta rasa,tsit tayi tana sauraron heart beat ɗinshi,

Suna cikin wannan yanayin na shauƙi sai ga Abbansu ya faɗo cikin part ɗin nasa yana neman shi,ganin baya acikin falon yasa ya wuce izuwa bedroom ɗin shi,tunkan ya ƙarasa ya hange su manne da juna kamar tip da tyre, adaidai ƙopar shiga bedroom din nashi,abban nasu ya tsaya cike da mamaki yana kallon wannan abun al’ajabin,ko motsi basa yi,bakomai yafi ɗaure mashi kai ba,face yarda sgr yake cakuɗa sumar kan yarinyar acikin hannunshi sai faman murzar gashin kan nata yake,ga kuma hancinshi daya cusa asaman kan nata yana shaƙar kamshin da sumar kan nata ke badawa mai daɗin gaske,

Ita kuma ta ƙankame mashi qugunshi da hannunta,ta kwantar da kanta asaman chest ɗinshi,

baki asake Abbansu ke kallon wannan tashin hankali,jinjina kai ya shiga yi cikin ranshi yana cewa”Oh ni hussein!tun yaushe wannan al’amarin ya soma faruwa acikin gidan nan batare da sani na ba!Hmmmm yanzu haka zare mata ido yakeyi yana tsoratar da ita don ya samu abunda yake so,nasan maganinka Rafayet,”ya faɗi hakan tare da kama hanya yabar part ɗin nashi fuskarshi ɗauke da murmushi,don shi wannan abun farin ciki ne awurinshi,ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don tsabar farin cikin ganin rafayet tare da mace,baida burin daya wuce wannan arayuwarshi,shi dae yaga Sgr yafara kula mace da sunan soyayya,yau dae gashi Allah ya nuna mashi,

Janye hancinshi yayi daga cikin sumar kan nata,sannan ya tattaro gashin nata tare da sanya almakashin ya datse mata shi,sosai ya yanke gashin,yabar mata guntu wanda ko kafaɗarta bai sauko ba,’

hankali a matuƙar tashe sehrish ta raba jikinta da nashi, da sauri takai idonta akan hannunshi dake ruƙe da dogon gashin daya yanke mata,kamar a mafarki take kallon gashin nata daya yanke mata,

A hanzarce takai hannu tare da shafo kan nata don taji sauran daya rage mata,

Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita,dakyar takai hannu tare da ɗaukar hijab ɗinta, sannan ta juya tare da watsawa aguje tana kuka ta fuce daga cikin ɗakin nashi,

ajiyar zuciya ya sauke tare da takawa izuwa gaban dressing mirror ɗin nashi ya mayar da scissors ɗin aciki tare da gashin kan sehrish daya datse,duka ya tura shi aciki ya ajiye,sannan ya maida drawer chest ɗin ya rufe,

 

Komawa yayi tare da haye wa saman gadonshi ya kwanta,yanayin da bai ta6a ji ba atattare dashi ba yake ji,tsananin tausayinta ne ya kama shi,har ya dinga jin tamkar baiyi mata adalci ba daya datse mata gashin kanta,ya lura ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nata ba,lumshe idanunshi yayi a hankali yana tariyo abunda ya faru tsakaninta dashi,especially lokacin da ta watsa da gudu tana kuka,duk baiji daɗi ba saboda shi baiyi mata hakan da nufin ya 6ata mata rai ba.*

Back to top button