Hausa novels

Halysaah Page 198 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 198…Khaleesat ta juya da sauri jin an bude kofar kitchen tayi ido hudu da Ajay, tana rike da plate a hannunta ta zaga ta daya bangaren kitchen din ta marairaice fuska tana kallonsa, ya tura kofar ya rufe ya jingina jiki ya rungume hannunsa yana kallonta, da kyar tace “Abinci fa zan kai ma su Mami wallahi” Ya daga kafada calmly yace “Na hanaki?” A hankali tace “To ka fita plss” Yace “In fita in je ina?” Shiru tayi bata ce komai ba ta sauke idonta, sosai taji gabanta na faduwa don ta riga ta gama tsorata da lamarinsa, kallonsa kadai yanxu fadar mata da gaba yake, murya can kasa taji yace “Kika ce zaki bi Mami?” Taki kallonsa, a ranta kuwa tunanin hanyar da zata bi ta gudu daga kitchen din take, yace “Ohk zan bari ki bi ta, amma da sharadi….” Ta daga manyan idanuwanta tana kallonsa, ya gyara tsayuwarsa yace “Sai mun yi sau hamsin kafin Mami ta tashi tafiya, idan anyi sau hamsin zan amince ki bi ta duk inda zata je” Khaleesat tayi masa wani kallo, bata san sanda tace “Me za ayi sau hamsin din?” Yana kallonta kasa kasa yace “Abinda kike gudu mana…. Bari ma a nuna maki practically yanxu, kinga sai ya rage 49 more to go” Yana fadin haka ya nufe ta, sosai ta tsorata ta gudu daga inda take tsaye har jikinta ya fara rawa tace “Don girman Allah kayi hakuri, don Allah ka tausaya min….” Kuka ta fashe da shi tana zage kitchen din tana basa hakuri, taga dai da gaske kamata yake son yi, hakan yasa ta saki plate din tangaran hannunta, tayi er ƙara ta duka inda take tace “Wayyo na shiga uku kafa ta” da sauri ya karasa wajen ya duka yana kallon kasa duk zatonsa a kafarta plate din ya fadi, da wannan opportunity din tayi use ta ruga da gudu ta bude kofar kitchen din ta fice, ya mike ya bi ta da kallo yana murmushi, Khaleesat na waigawa taga ko ya biyota ta wuce sama da sauri gabanta na faduwa, ta bude kofar bedroom dinta zata shiga, kiris ya rage ta ci karo da Jay zai fito daga dakin nata, bai yarda su hada ido ba yace “Sorry Halysaah” ita dai ta koma gefe tana mamakin abinda ya shiga yi a dakin, bayan ya fita ta shiga ciki ta kulle kofar amma ganin babu key jikin kofar hankalinta ya tashi sosai, kallon kofar bathroom dinta tayi taji alamar Hadiyah na ciki, ta karasa ta zauna gefen gado, tana yi tana kallon kofar bedroom din nata, bayan wani lokaci Hadiyah ta bude kofar bandakin amma taki fitowa tana leko cikin daki, ganin Khaleesat yasa ta fito, Khaleesat dai kallonta kawai take, Hadiyah ta ɗan sosa kai tace “Ashe kin shigo” Khaleesat tace “Eh na shigo” Shiryawa Hadiyah tayi ta dau hijab dinta ta saka tana kallon Khaleesat tace “Darduma fa, ina son zan yi sallah” Khaleesat ta dauko mata darduma ta shimfida mata, bayan Hadiyah ta idar da sallah Khaleesat tace “Don Allah ki rakani mu je kitchen, abincin da yawa bazan iya daukowa ni kadai ba” Hadiyah ta mike tace “Toh mu je” Tashi Khaleesat tayi suka fita dakin a tare amma kana ganin ko wannensu kasan a dar dar yake don sai waige waige su ke kamar marasu gaskiya, a haka suka isa kitchen suka dauko abincin, suka koma sama zuwa dakin da Mami take. Har bayan la’asar duk suna zaune daki tare da Mami, Hadiyah dai na kwance tayi shiru bata cewa komai a dakin, Mami da Halysaah ne kadai ke hiransu, Mami ta gama phone call din da take ta ajiye wayar hannunta tana kallon Khaleesat tace “Ke baza ki wajen mijin ki ko yana bukatar wani abu ba tun daxu kina zaune a nan Halysaah?” Khaleesat tace “Mami ai ya warke gaba daya, baya bukatar komai” Mami tace “Nasan ya warke, amma bai kamata ki bar sa shi kadai ba ai har na tsawon wannan lokacin” Khaleesat ta gyara zama tace “Suna tare da Ya jawwad ne a parlonsa” Mami bata sake cewa komai ba, Hadiyah dake kwance ta kalli Mami tace “Jibi kenan zaki tafi Canada din Mami, naji kin ce ma Mama Shafa in 2 days time zaki je” Mami tace “In sha Allah” Hadiyah tace “Toh zan bi ki mu je, ina son haduwa da su Juwairiyya, it’s been long muka hadu….” Da sauri Khaleesat ta kalli Hadiyah jin tace zata bi Mami, Mami dake kallon Hadiyah tace “Ba sati muka yi dake zaki yi a nan ba Hadiyah? Why the change of plan?” Hadiyah tayi yake tace “A’a ai zan dawo nan din Mami, kawai ina son ganin su Juwairiyya ne” a hankali Khaleesat tace “Mami nima ina son in bi ku don Allah in gan su” Mami ta daga kai ta kalli Khaleesat, Khaleesat ta sauke idonta tana wasa da fingers dinta, Mami tace “Ke da ke jinyar mijin ki kuma ina zaki Halysaah?” Khaleesat ta marairaice tace “Mami wallahi ya warke fa, tun yaushe ya warke, kuma Ya jawwad yana masa komai, don Allah ina son in bi ku nima in ga su Juwairiyya Mami” Mami dai tayi shiru bata ce komai ba, amma a ranta tana mamakin dalilin da zai sa Khaleesat ta ce zata bi ta, sai taga kamar avoiding Junaid din take, Mami tace “To amma ai sai ya bar ki tukunna” Khaleesat ta gyada kai da sauri tace “Nasan zai bar ni” Mami bata sake cewa komai ba, ta kalli Hadiyah that is just moody. Har karfe takwas na dare Khaleesat taki fita ko nan da can tana makale dakin Mami, haka ma Hadiyah bata fita daga dakin ba, bayan isha’i Jay da Ajay suka shigo da Takeaway din abinci har uku a leda da suka yi ma Mami, Khaleesat tayi saurin dauke kanta bayan sun hada ido da Ajay, Jay ya ajiye abincin hannunsa yana kallon Mami yace “Good evening Mami” Ajay ma ya gaisheta, Mami ta amsa tana kallon Ajay, Jay ya juya ya fita daga dakin, Ajay yace “Sai da safe Mami” Mami tace “Allah ya tashe mu lafiya Junaid” Juyawa yayi shi ma ya fita daga dakin, Mami na kallon Khaleesat tace “Ke Halysaah tashi ki tafi gun mijin ki, sai da safe” Khaleesat ta kasa cewa komai at first, can kuma ta kalli Hadiyah a hankali tace “Hadiyah zaki je dakina ki kwanta ne?” Hadiyah ta girgiza mata kai tace “I will sleep here together with Mami” Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba upon how bad she felt, Mami tace “Gwara ta kwanta a nan don can anjima zan bukaci ruwan shayi” a hankali Khaleesat tace “To ta rakani mu je kitchen din sai in dafo maki ruwan shayin don ina jin tsoron gidan da daddare” Mami tace “A’a, kar ki damu ki tafi gun mijin ki, duk sanda nake bukata Hadiyah zata dafa min” Khaleesat bata sake cewa komai ba, after a while ta mike duk jiki a sanyaye, a hankali tace “Mami sai da safe” Mami tace “Allah ya tashe mu lafiya” Kofa ta nufa walking slowly, tana fita daga dakin ta dinga kalle kallen corridor kamar munafuka, da sauri ta nufi bedroom dinta ta bude kofar ta shige ciki ta tafi ta zauna gefen gado gabanta na faduwa, ji take kamar ta fara kuka gashi kofar dakin babu key, bandaki ta shiga tayi wanka ta fito duk a tsorace, sannan ta shirya cikin doguwar riga tayi shimfida daya bangaren dakin a kasa ta yanda idan mutum ya shigo dakin idan ba zagayowa yayi ba bazai san da mutum a kwance a kasa ba, sai da ta kashe wutan dakin sannan ta tafi kan shimfidar da tayi ta kwanta. Tana ta kwance kan bargo a kasa har wajen karfe goma na dare, taji an bude kofar dakin gently, ta rike numfashinta tana kara takurewa waje daya duk da ba hangota za ayi ba sai an zagayo ta wajen amma duk a tsorace take, kamshin turarensa kawai yayi announcing present dinsa, taga ya kunna wutan dakin, after a while ya kashe wutan taji ya jawo kofar ya rufe alamar dai ya fita, she felt relieved da bai gane tana cikin dakin ba, ta sauke wani ajiyar zuciya ta lumshe ido don sai yanxu taji tana jin bacci. Can cikin baccinta taji an bude kofar dakin, a tsorace ta bude ido da sauri, taji an maida kofar an rufe, muryar Hadiyah taji kasa kasa tana cewa “Wai don Allah menene haka, ni ka kyaleni pls, Halysaah na dakin fa zaka tasheta….” Duk khaleesat na jin su tayi ƙuri da ido cikin duhu mamaki ya cikata, bata sake jin muryar Hadiyah ba, kuma bata ji fitansu daga dakin ba, after almost a minute ta sake jin muryar Hadiyah da kyar tana cewa “Zan maka ihu fa Yaya, don Allah ka sake ni….” Miƙa Khaleesat tayi har da buge gadon just to let them know she is inside the room, murya can kasa kasa Hadiyah tace “Wallahi tana ciki, pls stop it….” Khaleesat taji an sake bude kofar dakin daga haka bata kara jin muryar Hadiyah ba, mikewa zaune tayi har sannan mamaki bai bar ta ba, ta kunna bedside lamp taga babu kowa cikin dakin, bayan few minutes sai ga Hadiyah ta dawo dakin da sauri ta kulle kofar, Khaleesat tayi kamar a lokacin ta tashi bacci tace “Ke ce dama kika bude kofa….” Hadiyah tace “Um, ni ce, ashe baki yi bacci ba” Khaleesat tace “A’a nayi na tashi ne yanxu” Mikewa tayi ta kunna wutan dakin, Hadiyah taki kallon ta, ta nufi gefen gado ta zauna tace “Sorry for disturbing you” Khaleesat tace “A’a ni kamar a mafarki naji an bude kofar, don’t even know it’s you” komawa daya bangaren gadon tayi ta kwanta tace “Kin dafa ma Mami shayin?” Hadiyah tace “Eh ban dade da kai mata shayin ba” Khaleesat tace “Ohk” Babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, after a while Khaleesat tace “Yaya Khalil fa?” Hadiyah ta ɗan yi shiru na few seconds, can kuma tace “He is fine” Tana fadin haka ta kwanta, Khaleesat tace “Naga tun da ku ka zo u are moody, ko bakya jin dadi” Hadiyah tayi shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta mike zaune tace “Ina cikin damuwa ne sosai Halysaah” Khaleesat tace “Subhanallah, damuwa kuma? Tell me what the problem is?” Hadiyah ta sauke ajiyar tace “It’s about my relationship with Khalil” Khaleesat tayi shiru tana kallonta, a hankali tace “Issue ku ka samu ne?” Hadiyah ta girgiza kai tace “Not all…” Wayarta ta jawo ta shiga message dinta sannan ta mika ma Khaleesat, Khaleesat ta amshi wayar tana duba messages that were sent via a phone number that isn’t saved, few of the messages Khaleesat ta karanta wanda babu komai sai zallan cin mutunci da gargadi cikin kakkausar lafazi, ta kalli Hadiyah da mamaki tace “Wa ya turo maki wannan?” A hankali Hadiyah tace “His wife” Khaleesat ta kasa cewa komai, babu abinda ya dau attention dinta a message din sai bazawara da matar ta kira Hadiyah da shi cikin tsigar rashin mutunci, Khaleesat ta ma rasa abinda zata ce, Hadiyah tace “Bai tsaya iya ita ba, har da sisters dinsa da sauran cousins dinsa fa suke min messages, da yake auren zumunci suka yi da matar tasa, kin ga she is also from royal home ita ma” Hadiyah ta amshi wayar tana nuna ma Khaleesat sauran messages din wanda zallan cin mutunci ne da zagi, kuma ko wani message akwai kalman nan na Bazawara a cikinsa, har kiranta suka yi da er kalan sarauta, tunda ubanta bai hada komai da gidan sarauta ba kuma da dangin uba ake tunkaho ba dangin uwa ba, Khaleesat was speechless, amma babu abinda ke yawo a ranta sai farkon aurenta da Ajay, yanda ita ma su Hadiyah suka dinga kiranta da Bazawara ita da cousins dinta har ma da iyayensu, sai gashi tun ba aje ko ina ba yayi backfiring, saurin kauda tunanin tayi a ranta cause she hold no grudges against Hadiyah anymore, tunda gashi saboda ta yarda da ita har tana gaya mata damuwarta, after some seconds Khaleesat ta daga kai tana kallon Hadiyah dake kallonta, a hankali tace “What’s ur take on this Hadiyah?” Hadiyah ta jingina jikin gado tana girgiza kai tace “Don’t even know what to say about this Halysaah, I am confuse, babu wanda na nuna ma message din sai Mami, kuma tace in kwantar da hankali na inyi ta addu’a” Khaleesat tace “Baku yi maganar da Hajja ba?” Hadiyah tace “Ban gaya mata ba saboda condition dinta, ita ma tana cikin damuwan abinda Aunty tayi a masarauta, ga kuma Walid that is paralyzed for life, ga kuma damuwar Ummina” Khaleesat dai kallonta kawai take jin tace damuwar Umminta, Hadiyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Kin san Ummina sun samu issue da babanmu har ya kai ga babu aure tsakaninsu a yanxu, but bayan Mai martaba da Hajja babu wanda yasan da wannan, Hajja bata son su Aunty Kilishi da sauran yan masarauta su sani don dariya zasu yi, ko da ta zo tarban Aunty Faridah ai bata tare da Abbana ya saketa, but she is still in Lagos up till now don kar a zargi wani abu a gidan sarki, kuma ita tayi linking dina da Khalil through one of her frnd” Khaleesat was completely speechless, ta ma rasa me zata ce ma Hadiyah, Hadiyah tace “Shi yasa ita ma ban gaya mata issue dina da Khalil ba bana son ta kara ɗaga hankalinta” Khaleesat tace “Amma me Khalil din yace concerning all this text da family dinsa ke turo maki?” Hadiyah tace “Wallahi kamar tsoron matar tasa ma yake the way I am seeing things, yaki daukan ko wani action….” Khaleesat tace “Hadiyah zan baki shawara ki hakura kawai da Khalil, cause in har kika auresa you will live miserably a cikin yan uwansa….” Hadiyah na gyada kai tace “I thought as much, na fara zeroing mind dina tun last week, matar tasa fa har screenshot din Whatsapp chat dinta da shi ta turo min a inda yake ce mata ai linking dinmu aka yi, shi tasan baya kule kulen mata, i was so frustrated Halysaah” Khaleesat tace “To ki ciresa gaba daya a ranki idan ma kin sa shi, don auren irinsu ma ba shi da amfani” Hadiyah ta gyada mata kai kawai, Khaleesat tace “Me ya Jawwad ya shigo yi daxu?” Hadiyah ta kalleta da sauri tace “Yaushe?” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Ai sau biyu ina ganinsa a dakin nan” Hadiyah bata sake yarda su hada ido da Khaleesat ba, can tace “Don’t mind him” Daga haka ta gyara kwanciyarta tace “Ni na ma fara jin bacci” Khaleesat dai kallonta kawai take tana murmushi, tace “Amma ki gaya min tsakaninki da Allah, do u still have feelings for Ya Jawwad?” Hadiyah taki cewa komai at first, can kuma dai ta kalli Khaleesat tace “Ni fa na hakura da shi” Khaleesat tace “Nasan har yanzu kina son Ya Jawwad, shi ma kuma yana son ki, tunda gashi yana bibiyanki” Hadiyah tace “To da ya bibiyeni me yace min? Ko na yarda zan koma ma Ya Jawwad fa wallahi bazai taɓa ganin value dina ba bayan duk abubuwan da suka faru, shi baya da mantuwa, zai iya dinga amfanin da past mistakes dina against me, shi yasa na hakura da shi har cikin raina…..” Khaleesat tayi shiru don ita dai Jawwad da ta sani ba lallai yayi using past mistakes din Hadiyah against her ba, shi dai bar shi da shariya ko ya banzatar da kai, kallon Hadiyah tayi taji ta bata tausayi har ranta, they were quiet for close to a minute, Hadiyah ta kalli Khaleesat tace “Me yasa baki tafi bangaren mijin ki ba” Sai da gaban Khaleesat ya fadi kawai wannan maganar da Hadiyah tayi, ta sauke idonta tace “Ai tare suke da Ya jawwad, yana can part din kin san he is still recovering….” Hadiyah tace “Ok na gane, Allah ya bashi da lafiya” Khaleesat tace “Ameen, amma don Allah kar kisa ma kanki damuwa Hadiyah, kamar yanda Mami tace kiyi ta addu’a kawai, Allah zai kawo maki mafita” Hadiyah ta gyada mata kai tace “In sha Allah, duk karfe biyun dare ma nake tashi inyi sallah” Khaleesat tace “Allah Ubangiji ya kawo maki mafita” Hadiyah tace “Ameen Nagode Halysaah, i feel relieved voicing out my problem to you” Khaleesat tace “Thanks for trusting me, nima kuma zan taya ki da addu’a er uwa” A haka suka kwanta bacci. Karfe biyu da rabi na dare Hadiyah na zaune kan darduma aka bude kofar dakin gently, juyawa tayi suka yi ido hudu da Ajay da ya shigo dakin, tace “Yaya” Yana kallonta yace “Ashe kina sallan dare” Ɗan murmushi tayi tace “Ina yi mana Yaya” Mikewa tayi ta dau wayarta da darduma yace “Ina za ki?” Tace “A’a zan je wani daki ne” Yace “Don’t worry, ci gaba da sallan ki, just came to check on her ban san kina nan ba” Tace “Ko in tasheta?” Yace “Kyaleta” Daga haka ya juya ya fita daga dakin ya kullo kofar, Hadiyah ta karasa kusa da Khaleesat ta duka tana tashin ta, Khaleesat ta bude ido ta mike zaune, Hadiyah tace “Yaya Junaid just came in now” Khaleesat ta hade rai tana murza ido bayan ta gama bin dakin da kallo tace “To me zan masa?” Hadiyah tayi murmushi tace “Oho ta yaya zan sani, ki je dai kiji ko da wani abu” Khaleesat tace “Wani abu kamar me?” Hadiyah tace “Uhmm, May be he needs you by his side mana” Khaleesat tace “A’a Ya jawwad is by his side, ni babu abinda zan masa kuma” Hadiyah tace “Ai shikenan, amma da kin je wallahi” Khaleesat bata sake tanka ta ba ta koma ta kwanta tana rufe har kanta da bargo, tabb ko cewa aka yi ba shi da lafiya yanxu iyaka ta kira masa 911, har yanxu she is uncomfortable down there, Hadiyah tayi murmushi a ranta ta fara tunanin to ko yanda Jay ke takurata a harkar Bedroom yake wahal da ita babu sararawa, ko ita ma Khaleesat hakan ne ke faruwa da ita, just this thought alone made her miss her Ex Husband so much, duk da wahalan da yake bata a harkan ita ma dai tana benefiting cause sai ya tabbatar ya kai ta cloud 9, ko yanxu ma da yake bin ta ita kadai tasan yanda take ji, da sauri ta kauda tunanin a ranta for the sake of her ablution ta mike ta koma kan darduma tana ci gaba da addu’o’inta. Washegari da safe a tare Khaleesat da Hadiyah suka je gaida Mami a dakin da ta sauka, suna cikin dakin Ajay da Jay suka shigo gaida Mami su ma, Khaleesat taki yarda ta hada ido da Ajay kuma bata gaishesa ba don kar Mami ta gane ba wajensa ta kwana ba, ta dai gaida Jay, Hadiyah kuma ta gaida Ajay, shi ma Jay din Hadiyah ta gaishesa without looking at him, ta gefen ido Jay ke kallonta, shi ko Ajay lokaci lokaci yake kallon direction din da Khaleesat ke zaune, Mami tayi breaking silence din tace “Mun yi magana da Mai martaba daxu, yau da yamma in sha Allah za su shigo garin nan” Jay ya kalli Mami yace “Amma kin fasa tafiyar taki?” Mami tace “A’a yana nan, ai sai gobe ko jibi zan yi tafiyar” Mami na kallon Khaleesat tace “Akwai Coffee gidan nan kuwa Halysaah?” Khaleesat ta gyada mata kai tace “Akwai Mami” Mami tace “Make me some, but with no sugar pls” Sai da Khaleesat taji gabanta ya fadi, ta dake tace “To Mami” Mikewa tayi tana tafiya a hankali ta fita daga dakin kiris ya rage tace Hadiyah ta rakata amma bata yi hakan ba, bayan fitar ta da just 5 minute Ajay ya kara wayarsa a kunne as if zai yi answering call ya fita daga dakin, Khaleesat har ta gama hada ma Mami coffee din taji kamar kamshin turarensa da sauri ta fito daga kitchen, tana jin alamar ana saukowa downstairs ta maza ta shige laundry room ta tura kofar gabanta na faduwa duk da babu key jikin kofar, yana shiga kitchen yaga bata ciki ga mug din Coffee a ajiye saman kitchen Island yana ta tiriri ya juya ya fita daga kitchen din ya nufi Laundry room, bude kofar yayi ta mike da sauri daga durkusawan da tayi a dakin wankin tana yarfe hannu tace “Don Allah kayi hakuri plsss, Mami ce fa ta sani aiki” Ya rufe kofar ya jingina jiki ya rungume hannunsa yana kallonta da lumsassun idanuwansa yace “Duk me kike gudu haka ne?” Ta kasa cewa komai gabanta na faduwa, yayi kasa da murya yace “Aikin lada kike gudu wife?” Ta dake tana masa wani kallo tace “Meye aikin lada?” A hankali yace “To bari a nuna maki” Yana fadin haka ya cire jallabiyan jikinsa.

Back to top button